Share this page
irin kwarjinin da yake da. Cikin zafin nama yake taka wa zuwa harabar inda tarin sojojinsu ke tsai tsaye zagaye da gawar kanal, facing cap ɗin dake kansa ya zare a loƙacin daya isa inda gawar ke shimfiɗe, take haɗaɗɗiya kuma kamilalliyar fuskar sa me cike da kamala ta bayyana, wanda ya sanya asalin kyawunsa bayyanuwa take, Aura ɗin sa kuma na baibaye duk jama'ar wurin. Take suka soma ja baya yana bayyana kansa ga gawar, seda ya kawar da kansa gefe jin warin da gawar take da, nose mark ya amsa sabo daga hannun wani soldier yana kaiwa tsugunne akan gawar. Nan ya shiga haske hasken shi da dube dube, kafin yace a shigar masa da gawar zuwa E Room clinic, wnda ke cikin barracks ɗin. Haka manya da ƙananun soldiers suka wuni shige da ficen caje ko wanne sashe na jikin gawar har zuwa dare, iyaka abinda ke fitar dasu sallane kawai, Se ƙarfe 5 na yamma kana aka miƙa gawar mamacin ga iyalansa, da duk suma suke a barracks ɗin, daga nan fa bayan gama janazarsa, soldiers aka dawo bakin aiki kusan kowannensu a wuya. ♡ Kai tsaye Captain AA be sama kansa ba se wajajen tara da rabi na dare, don haka yake jin kansa a wani irin mugun ga jiye, sakamakon shige da ficen da suka cinye yinin sur suna yi dangane da mutuwar Kanal. da kyar ya iya kawo kansa gida saboda tsananin wahaltuwa, ze iya rantsewa da ALLAH iyaka ruwane a cikin sa, domin zaman kansa be samu yiba bare kuma harya sama zaman cin wani abu. A ɗan hanzarce ya diro daga cikin car nashi yana nufar cikin gidan. Cikin wani irin taku dake nuna zallan kwarjininsa haka ya nufa hanyar da zata sadashi da babban parlourn gidan nasu. Daidai da lokacin da Nufy ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da flask na tea da kuma cup. Ahankali ya mirza door handle na ƙofar parlourn yana shigowa, Inda shigowansa cikin parlourn yayi daidai da fitowannta daga cikin kitchen ɗin, haka zalika yayi daidai da kai dubanta zuwa ga ƙofar shigowa parlourn, wanda a adaidai lokacin ne kuma narkakkun idanunsa suka sauƙe akanta, inda ita kuma ganinsa da kuma kallonta da taga ya mata, daidai da jin sarƙewan da taji numfashinta ya mata, sedai ko kafin ta dawo daidai ɗin ta ya ɓace ɓat a wurin, ita kuma ta ɗago da nufin masa sannu ne se taga wayam, samun kanta da jingina da jikin ƙofar kitchen ɗin tayi tana sakin wata wahalalliyar ijiyar zuciya mara saiti. ♡ Ɓangaren AA kuwa samun kansa da yayi acikin makeken bedroom nashi ne yasa shi soma ƙoƙarin zare rigar dake jikin sa, A natse tamkar wanda hakan ya zame masa tamkar ɗabi'ansa ne ya kai hannunsa ya shafi gefen cikinsa, wanda ke ɗauke da wani tambarin da shi kansa buɗar idon sa shima yay ya gansa dashi, a duk lokacin da zai wannan tambarin se yaji wani tsikar jiki tattare dashi, ɗan rumtse idanunsa yayi yanzun ma yana ƙarasawa gaban madubin dake jikin bangon ɗakin, take yayi ido biyu da murɗaɗɗiyar surar jikinsa da kuma buɗaɗɗun muscles ɗinsa. tare da manya manyan 6 packs ɗin dake kwance acikinsa, wanda kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar da cewan shi ɗin ma'abocin motsa jiki ne, wanda kusan ma ya maida hakan babbar ɗabi'arsa, still sake kai hannun nasa gefen cikinsan yayi ta ɓangaren dama yayi, inda wannan tambarin ya sake bayyana tamkar irin wanda a ka yi ma masa zanen tattoo ɗin nan awajen, ɗan sake shafa zanen da kai tsaye wani ze iya ƙiransa da tattoo yayi tare da lumshe idanunsa, yanajin tamkar abinda wannan tambarin ke ƙumshe a cikin sa akwai dalili. Ɗan sake shafo ƙasar ƙeyarsa yayi seti da bayan kunnen sa, inda shikam wannan zanen tattoo ne already, wanda tashen samartaka da zafin kai ya sanya shi biye wasu abokanan sa na secondary suka je takanas aka musu, nashi photon Eagles aka zana masa, har abokanansa a lokacin suka ta dinga masa dariya, don a lokacin daga masu zanen lion se tiger, Se masu rubuta suna yen ƴen matayensu, be damu ba a lokacin domin yana son tsuntsuwar, yana son hangen nesansa yakai nata koma fiye da haka. wannan ra'ayin ya sanya shi sanja ra'ayin sa na son zama babban Architecture zuwa soldier. Cikin nutsuwa ya zare dogon wandon dake jikin sa, tare da ƙarasawa gaban makeken drawer glass ɗin dake cikin ɗakin nasa yayi, wanda komai dake cikin drawer'n ana iya gani daga waje, wani sabon fari tas ɗin towel ya ciro daga cikin drawer'n, tare da ɗaura towel ɗin akan waist na sa. Rantsatstsen agogon fatar dake hannunsa ya soma ƙoƙarin cirewa, bayan ya kammala ne ya ƙarasa jikin wata ƙofa, wanda da dukkan alama ƙofar toilet ne, murza door handle ɗin ƙofar yayi ya shige kaitsaye. Inda komai dake cikin toilet ɗin na original royal glass ne, hatta bath in wanka kewaye yake da royal glass me ɗaukan idanu, ƙarasawa gaban shower ɗin yayi tare da sakarma kansa ruwa. Haka ya ɗauki sama da 30 minute ruwan na dukan jiki da kuma kansa, kafin kuma ya wanke jikinsa, koda ya gama alwala yayi sannan ya zira lallausar sky bathrobe a jikin sa. Koda ya fito daga toilet ɗin gaba ɗaya jikinsa ɗauke yake da damshin ruwa, musamman ma gashin kansa wanda har ɗigar da ruwan yake, A gaban dressing mirror nashi ya zauna tare da ɗaukan wani ɗan ƙaramin towel ya shiga tsane gashin kansa, yana kammalawa kuwa yasa handrayer ya busar da gashin kannasa, wani haɗaɗɗen body lotion ya murza ajikinsa, tare da shafe jikinsa da wani fitinnanen turare. A natse cikin nutsuwarsa ya ƙarasa gaban drawer nahsi, wasu tsadaddun riga da wando ya ciro na barci farare masu taushi laushi, kamar yanda ya saba dayin komansa cikin nutsuwa, haka yanzun ma anutse ya saka kayan, wanda suka matuƙar fito da kwarjini da kuma faffaɗan jikinsa, sosai kayan sukayi masa kyau kasancewar fatarsa na da haske sosai, Salla yayi raka'a biyu tare da duba wasu file ta cikin email nashi, ya jima sosai yana aiki da iPad ɗin dake hannun sa kafin yayi adda'an kwanciya barci. ♡ Washe garin ranar kuwa sosai ya sha barcin sa don warware gajiyan dake tattare dashi, Se ƙarfe tara ya fito zuwa ƙasa, yana sanye ne cikin shigar black jeans da wata jar riga wacce take da adon baƙi da fari a gaban ta, sai kuma wata blue ɗin denim jacket ɗin daya ɗaura saman rigar, Se wasu tsadaddun white sneakers shoe ɗin dake ƙafansa, sosai shigar tasa tayi kyau ba kaɗan ba kwarjininsa kuwa na sake bayyana, wata farar facing cap me ratsin baby pink colour ya ɗaura a kansa . Se MASHA ALLAH don sosai yayi kyau, dan babu wata macen da zata masa kallo ɗaya ta kuma iya ɗauke kanta daga gareshi, baga mace ba harma ga kowa, Domin kuwa CAPTAIN AA irin mata san nan ne da ƴan mata ke rububin samu, kasancewarsa kyakkyawa ne shi na gasken gaske haka za na gaban kwatance, sannan yana da abubuwan burgewa masu tarin yawa,uwa uba tsarinsa da kuma murɗaɗɗiyar surar jikinsa, na matuƙar jan hankalin mata da dama, wanda idan ka ganshi kai tsaye ba zaka taɓa ƙiransa da sunan ɗan Nigeria ba, domin kuwa da ƴaƴan larabawa yafi kama ko daga yanayin farin fatar sa idan mutum ya kalla, zai gane cewar shi ɗin ba asalin ɗan Nigeria bane, kana kuma shi ɗin ya kasan ce wani irin mutum ne shi me murɗaɗɗen hali, wanda ba a taɓa iya gane gabansa bare bayan sa kana miskiline na ƙarshe. sannan bai fiye yawan magana ba, saidai yana da zafin nama sosai akan komai musamman ma a ɓangaren aikinsa, hakan nema ya sanya sunansa ke yawo ako ina faɗin Abuja dama kewayenta. A natse yake duba wayarsa me ƙirar iPhone 17 pro max yanaci gaba da saƙƙowa cikin takunsa na isa. Kai tsaye yana nufowa zuwa cikin ainihin parlourn nasu. Bayyanuwarsa yayi daidai da fitowarsa daga sashinsa yayi daidai da shigowar Abbu parlourn. "Sannu da gajiya Aliyu ƴan kwanakin nan kuna shan aiki" "Ba laifi dai Abbu abin ba'a cewa komai wllh" yayi maganar a karon farko ya ɗanyi murmushi kaɗan, wanda iya kansa kan laɓɓan bakinsa, saidai kuma abun da bai sani ba, sosai murmushin ya masa wani irin matuƙar kyau, da ƙarama fuskarsa haiba da cikar zati. Zama yayi akan kujeran dake facing da Abbunsa, Inda Ammey keta hidimar kaiwa da komowar haɗa musu gabansu da dinner, Sake lafewa a jikin kujerar dining ɗin nufy tayi, wanda tun kallon farko da tayi masa bata sake yarda tayi na biyu ba, wanda a nashi ɓangaren shima kallo ɗayan ya mata wanda bai wuce na second 2 ba. ya ɗauke idanunsa daga kanta bayan ya amsa gaisuwar da take masa. Koda suka kammala dinner ɗin shikam cikin ɗan gaggawa ya kammala nashi, tare da miƙewa yana cusa hannayensa cikin aljihun wandon dake jikinsa tare da musu sallam duk da kasancewar ba wai wurin aiki ya nufa ba. A gaban shegen parking lot ɗin dake shaƙe da manyan motoci masu kyaun gaske ya tsaya, ♡ One last look nake tsaye a jikin mirror na, tare da tabbatar dana fita yadda nake so. Domin yau ne ranar da zan dena teaching ɗina na ƙarshe a *Nawuwa Clinic* probably rana ta ƙarshe da zan taka ƙafana a hospital ɗin a matsayin teaching inba tare da wani dalili ba. Ƙafafuna sanye cikin sneakers baƙi tare da wayana dake riƙe a hannuna na fita zuwa parlour, karfe sha ɗaya lokacin dana fito zan wuce fuskana ƙawace da Kyakkyawar murmushin da na san yana min shegen kyau bana wasa ba. Iyaka Ammey ce ta rage a gidan lokacin, tana kitchen tana gyara kayayyakin da muka yi dinnern safe. Leƙa ta nayi tare da mata sallama tana bina da fatan Alkhairi da kyakkyawar sakamako me kyau, har na tafi na dawo na bata peak a goshi wanda ya saka ta yin dariya. Yau bana jin yin tuƙi don haka na fita zuwa bakin titin da kana fitowa daga gidan mu shi zaka tarar, kuma dama tin a daren jiya Mohan ya ƙira ni yace yau baya da aikin komi shi ne zai kaini ya kuma ɗaukoni, wanda dama ba yau muka saba hakan ba. Wannan ma shi ne abinda ya sake sa kani ƙin fita da motan nawa, wacce Ya Aliey ne ya semin daidai lokacin da zan fara tifin ɗin. Ina tsallaka titin dake damana kuwa muka yi clashing da Mohan ɗin kuwa, ɗan murmushi na masa ganin yacce tin tsallakowana titin yake kasheni da murmushinsa, duk da kasancewar bawai dan har zuwa wannan lokacin ina jin koda ɗigon son sa bane, A ahhh sai dan kawai in sake karkafa kai na wa shi ɗin. Wani murmushin ya sake sakar min appreciatingly yana sake bina da idanuwansa. ♡ Sallama na masa domin kawar da wannan mayataccen kallon nawa da yake daga gare shi, amsa min sallamar yayi scowling tare da buɗe min murfin motar ina shiga. Komawa mazaunin driver yayi nan ya ja motar muka lula saman kwata. Fira muka fara dashi sama sama game da wurin aikinsa da. Nan yake faɗa min wai ashe anyi posting na shi ne zuwa Lagos, mebi ma satin sama zai shirya tafiyan nashi. Fatan alkhairi na masa tare da mishi addu'ar ALLAH ya taimaka. Daga nan hirar ta koma ta masoya, ya fara amayo kalmomin soyayyarsa gare ni. Inda nidai jinsu kawai nake yi suna shiga suna fita ta cikin kunnuwana, ban sani ba kuma ko akwai ranar da zanji wani yace yana so na, in yarda da hakan? Inji zuciyata ta mamaye da haske da farinciki sanadiyar jin hakan, wanda har jina nake anya kuwa akwai wannan ranar?, Nayi nisa cikin tunanin totally zoned out. Wani abu daya zame min jiki da zarar naji mutum ya fara amayo kalmomin nan, ban san lokacin da hakan take faruwa ba, kawai sai dai in tsince ni nayi nisa a duniyar tunani irin haka I couldn't help it. Mohan ya ɗan murza yatsunshi biyu a fuskana, wanda sautin da suka yi ne yasa na dawo daga duniyar tunanin dana lula. Tare da kallon sa sosai ganin yacce yake kallona ina furta "me kace?". Nan take fuskarshi ta nuna alamun damuwa da kulawa, yace "cutie pie, ban san sau nawa kike so in faɗa miki cewar bana jin daɗin ire iren abubuwan nan da kike yimin ba. Sau tari sai ina magana akan soyayyata se a lokacin zan ganki kinyi nisa cikin tunani, hakan yana kona raina kuma ina jin babu dadi, Se nake kallar kamar ba Sona kike ba kamar wata alfarma ce kika min. So pls don ALLAH ki faɗa min, idan wata damuwa ce take damun ki kawai ki fito ki faɗa min inyi miki maganin ta idan ina da halin!" a sanyaye wannan karon kam na girgiza kaina ina ƙaƙaro mishi wani murmushi a sanyaye, "Babu abinda yake damuna Mohan, kaima kasan cewa da da akwai zan faɗa maka ne". Kansa ya juya zuwa ga tuƙinsa yana me sake furta. "A binda kike cewa kenan kullum! Sedai har yau babu canji. Shin Har zuwa yaushe ne don Allah? Sai inga kamar baki jin daɗin kasancewa da ni ne kawai". kallon shi nayi cike da mamaki tare da furta "Meyasa ka yin wannan tunanin? Ni fa na faɗa maka babu abinda yake damuna, idan akwai ɗin kuma ai zan faɗa maka kai ma ka sani". Wani ɗan rausayar da kansa gefe yayi, "To ai shikenan cutie pie, yadda kika ce haka za a yi dole" daga nan shiru ya ratsa motan zuwa can kuma se naga ya buɗe dashboard ya ciro wani kwali. Yanayin tsayin kwalin yasa nayi zargin waya ce a ciki hala. Miƙo min kwalin yayi bakin nan tamkar ya yage gida biyu. Yana cewa. "Ɗazu na ganta a shago naje Sema Ikram iPhone da tace tana so, Se sena kalla iPhone 17 ɗin sabuwar shigowa ce a cikin wannan satin ma ta shigi, So don haka ma ban yi tunanin kowa ba sai ke lokacin dana ganta wannan shi ne.... " hannu na sanya ina amsa tare da buɗeta, saurin waro idanu waje nayi ganin exactly irin ta hannun Yayace, da tsakanin kwanakin biyu na ganta a hannunsa, wanda nasan ba ƙaramin maku ɗan kuɗi ne zata yi ba. Cikin alamun tambaya nace "Amman me yasa saini? Hala kuma kana manta cewar ina da wayar ne ko,?" Murmushin fuskar shine ya ɓace take tare da furta "Na sani dama ba wai Sona kike yi ba Nufaisah!" yatsa ta na kai tare da shafo saman hancina, wani abu da nake yi unconsciously idan magana bata karɓu a wajena ba kenan, ko kuma idan maganganun mutum were so bored. Wayar ya ɗora min saman cinyana tare da cewa. " To dai ko miye ganan waya Nufaisah gadamarkine kiyi amfani da ita, ko aka sin haka." Yayi maganar wani irin murmushi na kwance akan face nashi, idanunshi kuwa na karaɗe fuskata da kallo, ɗan matso da face nashi yayi dab da nawa wanda hakan da yayi ya sani saurin janyewa, ya ƙara matso ni tare da furta, "Amma zaki iya bani dan kiss, a matsayin tukuici na" yayi maganar yana sake matso da fuskar shi gare ni, wanda ya sanya ni ɗaga kai na kalli tsaƙiyar idanunshi, babu alamun wasa ko kaɗan a cikin su, inda alamunshi suka gama bayyana da gaske yake. Duk da haka sai na maida abin wasa, nayi Ƴar dariya kawai tare da matsar da fuskana daga gare shi. Ina me daɗin "Daɗina da kai ka cika ban dariya wani sa in wallahi Mohan... Nayi maganar daidai da motar lokacin da motar mu ke tsayawa a harabar hospital ɗin, Ban jira ji daga gareshi ko ya bani amsa ba, na yunkura da niyar fita daga motar. Amma se kawai ji nayi murfin motar ya koma ya rufe, tare da wani ƙaramin ƙara alamun an sama motar lock ne. A karo na biyu na sake kai hannu da niyar buɗe motar, sai dai na sake jinta gam a rufen. juyawa nayi ina kallonshi, fuskata a ɗin ke tsaf babu alamun wasa balle yayi tunanin sake kawo min maganar shirme nace "Wai me ke damun kan ka haka Mohan?, bana son wasa buɗe min mota in fita don ALLAH" Beyi motsi ba sema zaman sa daya gyara sosai yana furta. "Taya kike tunanin zan barki ki fita ba tare da kin ɗauka wayar ba, ko dan kawai nace kimin kiss?, Haba mana se kace ba wayayyar mace ba, dibe kiba Nufaisah a shekarun haihuwa kin zarce 24, amma kice har zuwa wannan lokacin baki waye ba haba don ALLAH, Na kula duk lokacin dana fara furta miki abinda yake cikin raina, sai ki banzatar da maganar ki mai da ta wasa, ko an faɗa miki ni ɗan wasan kwaikwayon ban dariya ne?, Alhalin ƙare war tama har sa dakin aure nane a kanki,ni fa in faɗa miki gaskiya na fara gaji haka nan Nufaisah!, Na gaji! You are officially my girlfriend!!. Yakamata ace zuwa yanzu mun wuce kan wannan maganar, ba tun yau ba yakamata ace wannan maganar a tsakaninmu ta wuce, ace mun wuce wannan matakin. Nima fa mutum ne kamar kowa, Nima ina so ace ina ɗan taɓa ki ko yaya ne, ace zuwa yanzu jikinki ya riga ya saba da nawa, amma kullum sai ma ƙara janye jikinki gare ni da kike yi sake yi, ni ne wanda zan aure ki karki manta OK...... " Daga inda nake zaunen tsananin mamakinshi ya nemi daya daskarar dani a zaunen da nake, don haka na gaza yin koda Kyakkyawar motsi ne. Baki na kuwa se motsawa yake ina so inyi magana, in maida mishi martani ko yaya ne, amma kamar ansa zare da allura an ɗin ke min shi, haka naji a lokacin domin kuwa na kasa buɗe shi balle in mayar masa da muggwan maganganun da har ya mutu ya bar duniyar ba zai taɓa mancewa dasu ba... Don haka naci gaba da bin sa da wani irin mugun kallon ɓacin rai. Wata Ijiyar zuciya ya sauƙe yana me furta "Come on mana Nufaisah! Ni fa ban ce ki bani kanki ko wani abu ba, kawai ƙananun abubuwa nan da can ne fa, what's the harm in it? At least ki dan dinga appreciating nawa ko yaya ne mana!." Se a lokacin na sama zarrar watsa mishi wani ɗan iskan kallo tare da furta. "Kai dama a wurinka ai ba abu bane me girma, Se dai ka makaro Mohan, domin ni bana ɗaya daga cikin irin wannan ƴan matan da suke watsar da kai da kimarsu sabo da abin duniya open the car pls........ Ƙoƙarin riƙo hannuna yake yana cewa ai dama shi ba abu ne girma ya buƙata ba ɗan ƙaramin abu ne da bai fi kiftar idanu da buɗe wa ba anyi an wuce wurin. "Kwarai kai a wajenka ba komi bane hakan, saboda shaiɗan ɗin daya riga ya rufe maka idanu ba, amma ka sani ni a wajena it's a big deal. Kada ka manta mun taɓa yin wannan maganar da kai baya, na taɓa faɗa maka idan kasan wani abu kake buƙata daga gareni yafi mana sauki mu yanke alakar dake kokarin jina kanta tsakanin mu out. don babu abinda zaka iya samu daga gare ni, ba zaka taɓa taking advantage nawa ba Mohan IN SHA ALLAH, ba zaka taɓa yin amfani da kayan banza ka yaudare ni ba wallahi, in ALLAH ya yarda nafi ƙarfin haka. Don haka ka buɗe min kofa in fita tun muna shaidar juna ni da kai wallahi. Kuma ga wayar ka nan ka sani bana so, bana da buƙatarta, kai bana so ma in ƙara ganinka ma a cikin rayuwa ta nan da kwana kusa!!". Daga haka na hau kici-kicin buɗe ƙofa da sauri kamar wadda ta fita daga cikin hayyacinta. Ina ji yana ƙiran sunana amma nayi banza dashi. Ban tantance ba naji sauƙar hannunshi yana dafe min hannu, banyi wata-wata ba na wancakalar da hannun nashi can gefe. Bai daddara ba dai ya sake dafa kafa ɗata, wannan karon dana kama hannunshi, twisting nayi da karfina duk da nasan ba lallai yaji zafin hakan ba, duba da yanayin jikinsa kuma namijine. Cikin tsananin ɓacin rai da tunda muke dashi bai taɓa ganin kwatankwacinsa ba, na ɗaga murya da tsawa nace "Ka da ka sake taɓa ni!!, Kada wannan wulaƙantaccen hannun naka ya sake koda yunƙurin kuskuren sake taɓa nine.!! Kuma wallahi ka cuce ni da kayi tunanin zaka iya saya na da kyale-kyalin banza, IN SHA ALLAHU sai ALLAH ya saka min kuma ka buɗe min ƙofa" Na ƙara sa maganar da tsananin ihun da nayi ni kaina ya bani mamaki balle shi, Ina jin hakan ne yasa bai ma san lokacin da hannunshi ya danna madannar ba, ina jin na taɓa murfin ya buɗe, na fita daga motar da sauri. Fitowar shima yayi ya hau auna min ƙira babu kakkautawa, Se dai ina nikam ko waiwayensa ban yiba sema saurin dana ƙarama ƙafafuna ina shige wa apartment namu da sauri. Domin Jikina rawa yake sosai, da sauri Najma dake tsaye da dukkan alamu ni take jiran ƙarasowana ta nufoni, tana me furta, "Beb wai kina nufin duk uban ƙirar nan dana dinga miki baki gani ba hala?" kai kawai na iya gyada mata wanda se a lokacin ta kula da yanayin da nake ci na tsantsan ɓacin rai, da sauri ta matso wajena fuskarta ɗauke da alamun damuwa, "lafiyarki lau kuwa Beb? Me ya faru??"duk ta haɗe min tambayoyin wuri guda. Kai na shiga girgiza mata kafin da kyar na iya furta "Babu komi fa!" "Kin san kuwa yanzu ƙarfe nawa ne Nufy, and baki dai duba agogo ba, wllh kin kusa jaza mana ƙarin kwanaki, don wllh wannan shegen Md ɗin cewa yayi muddin sha biyu da rabi tayi se wani months ɗin..." tayi maganar tana sauƙe Ijiyar zuciya, hannuna kawai ta kama muna yin office na Md, har an sallami ƴan wasu garuruwan ba, muna shiga Janan itama ta nufo mu fuskanta da damuwa muna wucewa kawai..... *Jan gida* ♡ Misalin ƙarfe sha ɗaya da rabine na dare, inda Maman Nuwaira ke lafe a jikin fuskar gadon ɗakin ta, jikinta a dunƙule yake waje guda kamar kullin kaya, ta naɗe ƙafafunta yayin da ta sanya hannuwanta tana zagaye gwiwoyinta dasu, inda ta nutsa kanta a tsakankanin cinyoyin nata. Kanta masifar buga mata yake yi kamar ana kada mata ganga. Ita kaɗai tasan irin yanayin da gaba ɗayanta take a ciki, inda kai tsaye matsanancin kukan da ta ci a ɗakin Auwal ya dirar mata da ciwon kan lokaci guda, ga wani irin zazzafan da fin zafin da take ji a cikin ƙirjinta daya san yata jin kamar ana mata suya ne a ƙirjin. Idanunta kuwa suma da suka kwashe tsayin mintuna suna ɗigar hawaye babu abinda suke mata face zafi da zugi, Macece ita mai matuƙar dauriya da haƙurin shanye kowanne irin abune kuwa duk girman sa, ba ƙananun abubuwa bane suke sanyata zubar da hawaye irin haka ba, amma a yawancin lokut, lokaci dai kamar

Chapter 13 of 23