Share this page
ya saki yana kallon AA da yake sanye cikin wasu guntayen kayan gym. Cikin harshen nasara baturen nan yay magana da AA da bata fi ta 10 mints ba tare da bashi wani card. Yana komawa cikin motar sa ya ja ta da shegen gudu....Suna kaiwa gida ya buɗe ɗakinsa ya maida shi, bayan ya ɗan shafa saman kansa tare da zuba masa ruwa a tsakiyar kan nasa. Tamkar wani mutum ya yi wani irin girgiza tare da fesar da ruwan dake jikinsa, Ahankali yabar wurin yana nufar compound na gidan. Shi kuma yana shigewa cikin gidan, a natse yaci gaba da kutsa kansa zuwa cikin ƙayataccen building ɗin daya gama haɗuwa. Wan nan gida dai sai dai muce MA SHA ALLAH dan ta ko ina gidan ya gama haɗuwa da tsaruwa. Kai tsaye staircase ɗin sa ya nufa cikin zafin nama, Seda ya fara sa karma kansa ruwa kana ya fito yana tsane ruwan dake jikin sa,kayan shan iska ya saka yana kaiwa zaune saman sofa sky blue,gaba ɗaya ya gama tattare hankalinsa akan Laptop nashi, da yake ta faman aikin sarrafa wa a natse, a natse wani irin daddaɗan ƙamshi yake fitowa daga kowani sashe na jikin sa, irin me kwantar da hankalin nan. Yayi zurfi kenan a cikin aikin nasa gefe dashi ga glas cup nan me ɗauke da wine, kaɗan kaɗan yake ko rawa a yangance. Ƙarar da wayar shi tayi ne ya dawo dashi cikin tashi duniyar, sunan ABBU daya gani yana yawo a saman screen ɗin ya sanya shi dakatawa da latsa laptop ɗin nashi. Cikin nutsuwa ya gayda mahaifin nasa cike da girmamawa, magana sukayi me ɗan tsayi kana su kayi sallama suna yanke wayar. Kansa ya kwantar akan sofar yana jan idanunsa ya lumshe. Shigowar personal person nashi me suna wrong number ne, ya sanya shi buɗe kyawawan idanunsa da suka ɗan rine sukayi jaaa, da sallama a bakin sa ya ƙara sa shigowa room ɗin,yayin da hannunsa ke ɗauke da tray, Seda ya ɗan fesar da wani numfashi me ɗan zafi kafin ya amsa masa sallamar, ba tare daya ɗago ya kalle sa ba,ƙarasawa shigowa wrong ɗin yayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman empty table ɗin dake a gefen shi, laptop nashi kuma na saman cinyar sane dama. Serving nashi dinner yayi zuwa lokacin kuma wajajen sha ɗaya ne da wasu ƴan mintuna, da hannu ya masa alamar yaje, yana sake kwantawa a saman sofar, zuciyar sa na bugun tara tara dan tsoron abinda ze iy zuwa ya tarar. Kaitsaye yayi kundunbalar shiga cikin WhatsApp nashi, harya lalabu chat nashi da mahaifinsa, Seda zuciyar sa ta sake bugawa ganin photo ne Pappun ya tura masa, bai buɗe ba hoton kasancewar da tan ba a kunne take ba, cikin ɗan sauri da rawar jiki ya kunna data ɗin,nan take pisc ɗin ya shiga loading yana ƙoƙarin buɗe wa ,a hankali hoton ya soma bayyana, wanda ya ƙara ƙarfin bugun zuciyar AA, ƙur haka ya ƙurama wayar ido yana jiran pisc ɗin ya kammala buɗe wa. Gabansa ne yaji yayi wani irin mummunan faɗuwa,Wani kalan waro idon sa waje yayi a ɗan gigice, Hannunsa har kerma yake yi wurin yin zooming pisc ɗin, da wani kalan kallo ya shiga bin pisc ɗin da shi, wanda a take yaji jinin jikin sa na wani kalan harmutsawa,gaba ɗaya ya gama kiɗima,wata irin zufa ce kawai ke tsatstsafo masa, Zuciyarshi ce kawai yaji tana masa wani kalan tafasa da zafi, nan da nan idanunshi yayi jajir wani sabon gumim na sake yanko masa daga saman goshin, ƙara ƙurawa photon ido yayi yana jin yadda duk wata ma gudana ta jini dake aiki a jikinsa suna narkewa... Wani guɗa guɗa yaji kamar ana masa a cikin ka, gefe guda kuma ga wasu fuskokin mutane biyun nan daya gama gani yanzun nan suna gilma masa, tamkar me cutar gane-gane _hallucinations_ haka yake ganin kansa, kamar almara kamar a mafarki haka yake ganin komai, Lumshe idanunshi yayi yana shaƙar numfashin dake son barin gangar jikinsa. Hannun sa ya saka yana kife kyakkyawar fuskarshi da shi. Wani numfashi yaja da ƙarfi tare da fesar da iska daga cikin bakinsa, yana jin kansa na wani irin sarawa gaba ɗaya duniyar jinta yake tana juya masa, all his life bai taɓa shiga wani ruɗu irin haka ba. Domin kuwa ganin abin yake kamar wani dreaming ko reflection. Duk dai dama ya jima yana zargin hakan, no wonder ashe akwai mafari akwai tushen faruwar komai. Mikewa tsaye yayi cikin tafasar jini yake takunsa, wani irin fushi lulluɓe akan kyakykyawar fuskar sa, dake nan tamkar irin hadarin nan daya ƙunshi ruwa yaƙi ya fashe, Haka yay kummmm ya kumbura.... Babu jimawa se gashi ya fito cikin shigar ash wandon fendi da farar rigar rugby shirt, sai blue Lorenzo snickers ɗin dake sanye a sawayensa. Fuskar nan saye cikin Sun glasses tare da nose mark daya sanya. Sakamakon ɗazun da babu komai a fuskar nashi. Fitowarsa cikin takun nan nasa na isa da izza tamkar babu wani abinda ke damunsa, haka ya nufa harabar gidan, cikin wani irin taku yaja ya tsaya a gaban wani rantsatstsen power bike. hannunsa ya ɗaura akan key na machine ɗin, tare da wani irin tsalle ya haye kan power bike ɗin, tare da masa key. wani irin kuka machine ɗin ya ɗauka, sake daidaita machine ɗin yay cikin salon ya cilla kan machine ɗin saman titi. Da wani kalan masifan gudu yaja machine ɗin yana fita daga building ɗin baki ɗaya. Da goggle map yay using wajen nufar inda ya nufa ɗin, da haka harya isa inda yake son kaiwa... Wani irin sakin kan machine ɗin yayi lokacin daya isa bakin wani gaɓar ruwa. Inda babu wani motsin komai a wurin, Se jefi jefi wasu turawan kan wuce tare da ƴan matayensu domin shanawa. kasancewar wurin me kyau ne kuma na musamman, sedai masu aikata miyagun laifuka sun fi zama a wurin, hakan shi ya bashi damar ƙarema street wurin kallo ta cikin hular matsin ɗin da shade ɗin daya toshe idon sa dashi. Sai da ya gama ƙarema wurin kallo tamkar me nazartar wani abu, kana ya ciro wata ƴar ƙaramar munafukar waya yana ɗan daddanata, idanunsa kuma na zagaye da kowa dake wurin wanda suke nan tsilli tsilli. Har idon sa ya isa kan wani Bad Man, wanda gaba ɗaya jikin sa ke kewaye da zanen tattoo kasancewar kusan zanen tattoo ɗin shine ɗabi'ar turawa. Wani sakin kan power bike ɗin yayi yana yin kan baturen daya amsa wayar gefen sa yana manne da wata baturiya, shuuuuuu haka yaji wucewar wani abu ta gitta shi, daga ko kafin ya dawo tunaninsa machine ɗin ya sake yin sama da shi yabi ta kansa. Wanda wannan ƙarar machine ɗin da kuma ƙarar da mutumin yayi wanda daga ita be sake ba yace musu ga duniyar nan. Shi ne ya janyo hankulan jefi jefin jama'ar dake wurin. Ashe wannan shuuu ɗin da yaji bullet ne ya ratsa ta cikin ƙeyarsa tare da ficewa fitttt, tuni gang bang ɗin dake wurin su kayo kan AA ɗin, kansu yayi da machine ɗin tare da fara harbin ƙafafunsu. Nan wanda ba'a harba ba suka so ma ja da baya suna guduwa su faɗa cikin ruwan. Shi kuwa daga nan ya sake buga machine nasa yana barin wurin, Sega waɗan nan gang ɗin sun biyo bayansa a nasu sabbin machine ɗin, suna ƙure masa wuta tare da makamansu, wasu wuƙaƙe wasu kuma bindigu ne, nan aka shiga fafata wuta akan machine's ɗin, haka AA yake zame musu kuma yana cin uban su, tin yaran na binsa cikin armashi da shauƙi har suka gaji, dan kwana kwana ya dinga bi dasu da wani bala'in gudu kamar ya tashi sama. Da haka suka gaji suka koma gaɓar ruwan domin ɗaukar gawar Scorpion da AA ɗin ya sheƙe. Kafin su isa kuwa har ƴan jarida tare da motar ambulance sun zo, an kwashi waɗan da suka ji raunin, shi kuwa scorpion ana ɗaukarshi daban. ♡ *DARK HOUSE* Place ne me girman gaske daya gama ƙunsar duk wasu dabar tantiran da suka ga gari al'umma, domin kuwa a wannan dabar tasu ta _Buried Bo-Death_ duk wasu marasa ji ke ɓuya, idan ya gama ɗebo buyagin hayaƙinsa. Parlour ne babban me girman gaske, sai dai gaba ɗaya fitulun cikin sa a kashe suke, sai wasu candles da basufi five ba kacal aka bari suna ci, suma ɗin tsilli tsilli cikin kwalbe suke dan haskensu bai da wani tasiri mai yawa sosai. Yanayin duhun wajen ne ma ya ɓoye ainahin fuskokin mutanen dake zaune a cikin Parlourn, kuma dadi da ƙari ma duka fuskokinsu a rufe suke da masks, ta yanda koda ace akwai hasken wutar baka isa ko ainihin su waye suba, bare har ka sama zarrar tantance su. Inda gaba ɗaya saman table ɗin dake tsaƙiyarsu yake shaƙe da P0p P0wer energy drinks, wine, coc, se tarin cigarettes ɗin dake wurin himili guda. Magana suke yi cikin wani irin ɓoyayyen harshe, shima indianci ba, haka shiba na fulde ba. (Fulfulde_or fillanci), haka suke maganar cikin wannan juyayyen harshen. Wasu glas cup ne ɗauke a hannun su, suna sipping wine something energy drinks, yayin da wasu kuwa ke busa hayaƙi, wasu kuwa pepe na shi sha ne gabansa suna buying hayaƙin ta hanci ta bakinsu. Ɗaya daga cikinsu ne ya miƙe tsaye tare da pep na shi shan dake hannun sa, wanda gaba ɗaya jikin sa ko ina ke zane raɗau da zanen tattoo, har kansa daya sha tankwal kuwa zanen ne daram shima kwance a kansa, karkuyi mamaki idan nace maku duka zanen dake jikinsa na macizai ne, wani wurin ƙaton kan ne iyaka, wani wurin kawai tongue ne na macijin, irin ya ziro da da fin nan nasa. *SNAKE BLACK EYES * babba kuma shugaban duk wani tantirin da yake jin kansa ya kai wani mataki na shege, ko da ganin miƙewar nasa yasa take gang bang ɗin dake zagaye dashi duk suka nutsu, tare da maida dukkan hankalinsu garesa. Cikin wannan mara dadin yaren ya soma magana. "Wannan mutumin da kuke kalla ya jima yana lalata duk wasu tsare tsarenmu akan ƙasar Nijeriya, Se dai hakan ma so fine tin da shi kansa yanzu wani terror ne dake ji da kansa, domin kuwa ya shigo har cikin ƙasata harma ya sama zarra taɓa ɗaya daga cikin yarana...... " yay maganar ne kuma tare shafan wani glas emoji na snake dake tsaƙiyan table ɗin. Take kuwa duka ɓangarori na ɗakin suka kawo wani haske, Se ga pisc na *CAPTAIN AA* namu ya bayyana, glas emoj ɗin ya ɗan sake shafa, wanda nafi zaton na'urace a wurin, Sega video'n kashe wannan baturen da yay na bakin ruwa ya bayyana. Inda su kuma gaba ɗaya gang ɗin suka tsaya kallar tsayayyen jarumin daya cike ko wanne bango na ɗakin, da ko'a hoton ma kallo ɗaya zaka masa kasan cewar eh lallai da gaske shi ɗin gwarzon namiji ne tsayayye, da samm babu kowanne irin tsoro tattare dashi. Wata iska wine block ya fitar daga cikin bakin sa, yana jin wani abu me kama da sha'awan na jikin photon na kama shi nan take, dan haka ya sake kafe AA ɗin da ido tamkar shi zatin sane tsaye a gabansa. "A daren jiya AA yay wannan aikin, wanda dama duk a cikin shirin mune hakan, dama can idan baku manta ba Roshan baya tare damu, dunduniyarmu kawai yake ci, yana fitarma da wasu dabar sirri kanmu, dan haka na aika White Snake wurin shi AA ɗin a daren shekaranjiya. Wanda gashi kuma ruselt namu ya fita yadda muke so, sedai ba da gaggawa haka zamu bayyana kanmu wa shi ba, amma first target namu na farko shi ne jawo hankalinsa zuwa ga ƙungiyar namu....." se kuma ya dakata yana kallar white snake ɗin, Dan haka ya san kome *BOOS* ɗin yake nufi, take shima ya miƙe yana sake basu cikakken bayani akan AA ɗin. Da kuma yadda suke son ya shigo cikin su kai tsaye, wanda dama shi white ɗin da sukayi magana harya bashi kwangilar kisan Die Roshan ɗin, sun riga da sun gama maganar komai. ♡ AA..... Zaune kawai yake a kan couch ɗin dake babban parlourn nasa, ya bada baya ta hanyar jingina bayansa da jikin kujerar, idanunshi lumshe kuma, tun da ya dawo daga Sallar subhi heart nashi ke racing a hankali, baccin da yake son ya sake ɗaukarsa a karo na biyu amma yaƙi zuwa ya ɗauke sa. Gama ɗaya ya gama yin relaxing a cikin couch ɗin, har zuwa lokacin kuma idanunshi na a lumshe ne, sosai wannan abin me kama da hallucinations ya shiga maza giza ko yawo ma ze haka yake ji yake kuma. Wani ihun ƙiran sunansa ake ko yace ake ambatar sunan *KAMAALAH* a cikin kan nasa. Show glas ɗin dake gabansa, wanda suke jere da extreme milk shake tare dasu strow berry syrup, su pink edible glitter. Ahankali ya motsa daga kwancen da yake, yana miƙa hannun sa tare ɗauka suua buttelyn pink edible glitter ɗin yana kaiwa bakin sa, tare da sipping nashi ahankali idanunsa a lumshe, sanyi da kuma garɗin edible glitter ɗin na ratsa bakinsa da kan halshensa. A ƙalla se da ya sake ɗaukar sama da 15 minute a wurin, kafin ya tashi yana faɗawa bedroom nashi, yana shigewa toilet kai tsaye. Koda ya fita a gaban madubi ya tsaya daga shi sai towel jikinshi, ginannen jikin nan da yake fari tasss sai ɗaukar ido yake, saboda ruwan dake bin murɗaɗɗun damatsanshi zuwa parks da ya tara a ciki, madubin ya sake ƙurama idanu yana tunanin irin yanayin da yake ciki a yanzun, da kuma wanda ya shiga daren jiya. da ƙarfi ya runtse idanunshi da suka yi wani irin ja nan take yana fesar da hucin numfashi daga bakin shi, wani ɗan tsiririn tsaki ya ja a karo na ba adadi yana miƙa hannusa zai ɗauki lotions kenan hannun sa ya sauƙa akannnnn........ _Hhhhhhhh to ai shikenan saimu gimtse haka nan ko?😊😁😀_ _To fa wannan shi ake ƙira da rigiji gabji, dan abubuwan fa da yawa suke, dan wannan labarin da kuke gani cakwakiyar cikinsa ta musamman ce. Wanda ƙulli da makircin tare da gwagwarmayar dake cikin sa ya zarta *MIKIYA* Rikici haɗi da kitumurmurar dake cikin sa ya zarce tunaninku_ _Kai abin dai ba'a cewa komai, dan ba lallai ku gane abinda nake son sanar muku ba, sai in har kun sayi maku cikin sauƙi, kun karanta littafin *RAMIN KURA* Wato labarin nan ko hammm ni kaina fa gindayar dani tare da chakar da kaina yake aha...... To bari dai nayi shiru kawai🤭 gudun kar na cikaku da surutu, Se dai amma kafin haka ina son ku sani cewar, ta kowanne fanni wannan labarin yazo muku ne da wani irin sabon salo na daban... _ ~RAMIN KURA~ fa aka ce. Wanda takensa yake *SE ƳAƳANTA*, Shin su waye kura yen?, kuma su waye Ƴaƴayen?~ # Shin me kalaman Waɗannan mutane suke nufi ne kam wai AKAN CAPTAIN AA ƊIN MU?# ~Shin su kansu waɗan nan mutanen ma wai su waye?~ _Shin to wai ma menene ya kai AA ɗin namu zuwa ƙasar GOA? _ # Shin ku a naku kalan tunanin ma, wai wanne kalan wasane za'a buga tsakanin AA da kuma ƙungiyar _Buried Bo-Death? _ *Ku na son sanin wannan amsar? To nace Duk ku biyo ni *AMMIEY LAYLERH* don warware muku zare da abawar dake cikin wannan littafi na *RAMIN KURA* _Wanda koda kuɗinka saida rabon ka, dan haka Hajiya idan kin shirya jin kitumurmurar dake cikin wannan littafin saiki biyo *AMMEY LAYLERH* da 1k ɗin ki domin ayi tafiyar manya dake Hajjaju🙅🙌. Kibar tagumi😱 nibance kowa yayi tagumi ba.... _ *Idan kin shirya saya saiki min magana a wannan number'n* 08104493215 *Idan kuma kai tsaye account naw kike da buƙatan shima ganan* 3206656358 Maryam Nasiru Fisrt Bank Or 8104493215 Maryam Nasiru Opay *Sayen na gari maida kuɗi gida koba haka ba😟😵😰 Don Allah karmu ɓatama juna loƙaci idan baki shirya saya ba karkimin magan* ༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻ # 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Book One paid ♡ Page 33&34 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. # HE WILL FIGHT # WAR *Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank* ♡♡♡♡♡♡♡♡ ꨄ Hannunsa ya sauƙa akan wata wata doguwar farar envelope, chak ya dakata kuma tare dabin hannun nasa da ido, da wannan kyakkyawan handwriting ɗin nan nata idon sa ya fara masa tozali, Se yanzun yake tuno wa jiya ne da zai fito da system nashi daga Jakarta envelope ɗin da faɗo, shi kuma yana mantawa be mayar da ita ba, dan haka se kawai ya sauƙe wata ijiyar zuciya yana ɗaukar envelope ɗin ya manna a ƙirjinsa, wata ijiyar zuciya me sanyi ya sauƙe yana sake meda envelope ɗin cikin bag na system ɗin. Lotions ɗinsa ya shiga shafawa kamar yadda yayi niyya tin farko, daga nan wasu ayyuka ya ɗan yi se wajajen ƙarfe ɗaya kana ya kwanta. Haka yaci gaba da gudanar da rayuwar sa cikin kwanciyar hankali a ƙasar GOA, *HANNAH'S* ..........A kullum kwanan duniya canja ma ko wanne bawa ajin ta na karatu take, abinda kawai na sani nafi fahimta yanzun shi ne cewar, yau ɗin kace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙaddarar jiyanka. Rayuwa mataki biyu ce, kowacce ka zaɓama kanka zaka isa zuwa makomarta ne ba tare da wata tan garɗa ba, saɓanin anan shi ne kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurɓatacciya. Tabbas rayuwa ta da Sir MALEEK ta baya ta gama canjamin ta kowanne ɓangare, dan a lokacin da muna tare sauran MA'AIKATANMU, Sukanji shakkar min wani abun, amma yanzu kam ƙiri-ƙiri wasu kan nuna min hasali da yanda tsarin su yake akan ayyukan su na almin dahana. Matsala ta farko dana fara fuskanta a wurin aikina shi ne cin zarafi da rashin ɗa'ar da wasu kan zuwar min da ita mai ƙona zuciya da barin tabon da ba'a mantawa shi ne har gaban abada, a wannan ranar zuciya ta ta ƙara sa ƙaiƙashewa, domin kuwa dama wasu mutanen sukance, komai fara koya shi ake, a kowanne mataki, domin kuwa na rikiɗe ne na juye musu i zuwa wata HANNA ɗin ta daban ba wannan HANNA AYUB ME KANO ɗin bace, A ahhh wannan ɗin wata sabuwar Hanna ɗin ce, wacce ta rikiɗe ta sanja, tin daga lokacin da commissioner ya nemi daya keta mutumcina ta hanyar fansar MASOYINA, Abin ƘAUNATA MALEEK. Tin daga wannan lokacin na sanja, domin da hara haren sauran jami'an mu besa na sanja ba, se daga wannan lokacin. Don haka da haka rayuwar tayi matuƙar sauyawa, kuma ta ci gaba da shurawa, har yau ana zancen wajen 3 Months kenan da tsare SIR MALEEK, kuma babu wani batu ko tsayayyar magana, har seda yayansa ya nemi wasu kwararrun lauyoyi masu aiki da gaskiya, kana aka fara maganar shari'ansu, don da kamarma sun manta da maganar ne haka sukayi. Kana daga bisani aka fara maganar shari'an nasu, harma aka tsaida rana da kuma lokacin yi da sauraran nasu..... *Headquarters Abuja* Cikin wani irin tsantsan ɓacin rai General murtala na gona ya shiga furta. ♡ "Shin wai har se zuwa yaushe ne zamuci gaba da ɓoye ɓoyen ayyukan mune game da wannan tantirin, da za a ce kaf cikin tarin soldier's ɗin nan ace babu me iya bin sa ya bishi ya same shi har inda yake uyummmm" Yayi maganar ne tare da tsare duka soldier's ɗin dake fuskantar sa da ido, kafin cikin dakakkiyar sautin sa ya kalli ɗaya daga cikin soldier's ɗin yana me furta. "MG Fawaz har yanzu kana kan bakar ka na kawo mana AA?, domin kuwa da ace shi ne a wannan matsayar da ake ciki da tuni an wuce wannan shafin an tafi wani, dan haka a karo na biyu MG fawaz har yanzu yana tare damu ne akan maganarsa ta farauto mana CAPTAIN ALIYU ABDULLAHI?, "Yes sir." Wanda aka ƙira da MG fawaz ɗin ya faɗa tare da sara ma mr. General murtala na gona. "Se dai ina son ku dukan ku ku sani cewar AA tsohon jima'in mu ne, inda a halin yanzun haka ya haɗe kansa da kungiyar ƴan ta adda, yana zaune ne kuma a wurere biyu ma ban banta, GOA to Spain. Nasan dolen dole a cikin waɗan nan ƙasashen biyu dole ne a same shi a wuri ɗaya, Domin A halin yanzu shi ne mutum mafi haɗari a duniya, kwakwalwarsa tana gudune kamar engine, yana da matuƙar ƙarfin dantse, da kwakwalwa da tsananin kaifin basirar data wuce zarrarsa, yana da tsananin wayo tare da sanin makamar aikinsa. Don haka nake son a wannan gaɓar dole ne mu kawo ƙarshen zafin kan CAPTAIN ALIYU ABDULLAHI" Ɗaya daga cikin soldier ɗin ne ya miƙe tare da furta. "Sir, har yanzu ina mamakin wannan abu sir.Ace mutumin da yafi kowa bamu horo sannan kuma ya kashe ƴan ta'addar da babu adadi, babu iyakarsu!, me Ze sa ya zama ɗan ta'addar shi?" Wani lalataccen murmushi Mr president ya saki tare da tsare wannan soldier's ɗin da firgitattun idanunsa, cikin dakakken sauti ya furta."Da duk kan alamu har zuwa wannan lokaci Lieutenant Nassar Bunza, tare da babban yaron wannan ɗan ta'addar a da wato LC jamaal na tare da Criminal Aliyu Abdullahi!?, hakan na nufin har zuwa wannan lokacin kuna son AA kenàn?" yay maganar domin yana ankare da sune dama, idon sa yana kansu tare da duk ku wasu motsin su.... "Kwarai sir amma ba kamar yadda muke son ƙasar mu, domin mun koyi hakan ne daga gareshi, son ƙasa kafin son kai, aiki da zuciya tare da bada rayuwa wa uwa gijiyarmu ƙasarmu ta gado NIGERIA" suka haɗe baki wurin furta hakan suna solid na general ɗin. Cikin tsare su da ido mr. General murtala na gona ya furta "Idan har ɗaya daga cikin ku ya samo shi zaku iya harbin sa?" Lieutenant Nassar Bunza ne yay saurin miƙewa tare da solid na general ɗin kana cikin Amon murya ya furta. "Kwarai sir zan iya!, amma idan na gama tabbatar da cewa baya da laifi, nayi ma wannan alƙawarin sir." Cike da jin zafin Nassar ɗin MG fawaz ya miƙe cikin fusata yana fuskantar Nassar ɗin. "L. NASSAR BUNZA kodai kana tare da AA

Chapter 18 of 23