irin wannan, dauriyarta gazawa take yi.
ALLAH ƙadai yasan iya adadin lokacin data ɗauka a haka, kafin ta ɗago kanta da fuskarta da tayi baja baja da ruwan hawaye da zufa da majina, nan take ta sake jinginar da kanta da jikin gadon. Tana kallar yaran ta tana sake jin yadda suke sauƙe ajiyar zuciya, haka itama take sauƙe nata ɗaya bayan ɗaya.
Ɗan kwali ta dauka ta yafa a kanta, ta mike tsaye akan kafafunta da suka yi mata nauyi kwarai, ta daga labulen dakinta ta fita tsakar gida.
Gidan da unguwar, dama duniyar gabadaya, sun dauki shiru a dai-dai wannan lokaci, ba kamar hayaniya da cunkuson jama'a da suka saba dauka ba. Ta shiga bandaki tare da kimtsa kanta. Duk da cewa bata yin sallah, hakan bai hanata yin alwala ba ta fita ta koma dakinta. Abin sallah ta shimfiɗa tare da ɗaukar doguwar hijabi ta sanya a jikin ta, sallah tayi sosai a cikin tsakiyar daren, bayan ta idar ta zauna, tana gyara zamanta tare da gyara murya, ta fara rero karatun al-qur'ani mai girma cikin tausasa kalaminta, da kuma nutsattsiyar muryarta a cikin suratul-Aal_Imran. A hankali take rera karatun cikin muryar rauni, ta yadda ita kanta ba duka kalmomin ke shiga cikin kunnuwanta ba sai ɗaiɗaiku, har ta gama ta shiga suratun-nisa'i itama ta gama, sannan ta ninke ƙafafunta ta ɗaga hannuwanta sama, ta fara jerowa ALLAH kirari da kyawawan sunayensa ɗari ba ɗaya, kafin ta fara karanto mishi buƙatunta na rayuwa daki-daki, ɗaya bayan ɗaya cikin kaskantar da kai. Ta shafa wasu hawaye na cika mata idanu tayi kokarin mayar dasu, sai taji jikinta da zuciyarta sunyi sanyi a take, kuma taji kamar an ɗauke mata wasu gingima-gingiman kaya a kanta. Filo ta ja ta ajiye kawai ta ɗora kanta a kai ta ɗauki carbi ta fara ja. Kanta na kallar P. O. P na ɗakin. Ranar haka ta kwana cikin yanayi na damuwa da son barin wannan gidan, sedai idan ta juya ta kalla yaran ta da suke mata rai huɗu se taji zuciyar ta ya mata nauyi, zata iya jure komai a kansu, ciki kuwa harda sa daukar da rayuwar ta a kansu. Tasan dai a farkon fari, kowanne labarin duniya yana da tushe yana da mafari me tushe, kamar wani abu daya faru haryay silar jirkicewar jirkitattun al'amuran mutum irin haka, kamar yadda nata labarin ya soma.
So take ta zama kaman kowacce mace.....wadda ke ɗauke da responsibility na mijinta,kula da duk wani welfare nashi da al'amuran da suka shafe shi, sedai anyi mata katanga tare da shamaki da hakan. Wanda har take jin kamar lokacin hakan ba zai taɓa zuwa ba, amma idan tai duba da cewar. Wasu lokutan ALLAH kan jinkirtawa ne ba wai don yana mantawa da mu ba. Sai domin mu koyi jiriya da zuciyar nagarta, Se taji wani sanyi na ratsa ta, domin juriya tana ɗauke da lada da kuma rahama ko duk wani muminin kwarai mai yinsa. Kamar yadda ubangiji ya ce, _Jinkiri daga ALLAH ne gaggawa daga SHAIƊAN ne_ so don haka ko babu komai zata ji gaba da zaman jira da tsammanin wa rabbuka. Zata jinkirta har zuwa lokacin da ƙofofin nasararta zata ƙwanƙwasa mata ƙofa, zata ci gaba da zaman haƙuri wata ƙila kofar nasarar nata yana ƙarshe ne, me bi shi ne cikon na casa'in da tara, ƙila nasarar na a cikon ƙofa ta ɗari ɗin ne. Haka ta sake yin shiru very comly tana tunanin wannan kalmar da aka ce wai 'Opportunity comes once (Dama tana zuwa ne sau daya) to shin ita mecece tata damar?. Da haka safiyar ranar ta risketa har zuwa lokacin da ta fara ma yara shirin tafiya school. Ƙarfe bakwai da minti arba'in uban ya fito daga ɓangarensa, a lokacin tana tsakar gida. Gaida shi tayi ya amsa sama² a wani ɗage, bata damu da hakan daga gareshi ba. Harya gitta ta tace "Amma Abban Nuwairah baka ce zaka bani kuɗin nan nawa ba da muka yi maganar jiya" Kawar da kansa daga kallonta yayi yana sauƙewa akan jiddah da ta fito daga ɗakin Husna tana masa ina kwana. Don haka tayi saurin ɗauke kanta daga kallon su, ganin yanda hankaliin mijin nata ya bar kanta, zuwa kan ƙanwar matarsa Husna. Seda ta koma ɗakin Husnar kana ya ɗan kalle ta tare da furta. "Se dai fa kiyi haƙuri yanzu haka maganar da ake yi babu kuɗi a hannuna, don
duka-duka shekaranjiya na biyawa yara kuɗin school fees su ma, ga kuma sauran hidimar gida dake kaina, me bi se idan na dawo daga kasuwa" daga haka ya sa kansa yana ficewa abin sa. Ita kuma ta nufi kitchen don ɗora girki.......
♡ *ADAPHAN SUDAN............*
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
_Shin fan's sun shirya tafiya MASARAUTAR UMMULYOODAH kuwa?, Duk ku biyo ni *AMMIEY LAYLERH* don warware muku zare da abawar dake cikin wannan littafi na *RAMIN KURA_
_Wanda taken sa yake koda kuɗinka saida rabonka, Hajiya idan kin shirya jin kitumurmurar dake cikin wannan littafin saiki biyo *AMMEY LAYLERH* da 1k ɗin ki domin ayi tafiyar manya dake Hajjaju🙅🙌. Kibar zaman tagumi😱 nibance kowa yayi tagumi ba domin ALLAH _
To ai shikenan saimu gimtse haka nan ko?😊😁😀 Slide clips to delete Them....
08104493215
༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻
# 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Book One paid
♡
Page 25&26
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
# HE WILL FIGHT
*Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank*
♡♡♡♡♡♡♡♡
𝘼𝘿𝘼𝙁𝘼𝙉-𝘾𝙃𝘼𝘿𝙄........
♡ Iska mai daɗi ce take Kaɗawa a yammacin ranar cikin birnin ADAPHAN, yayin da da gajimare yay samaniya wani irin ƙawanwa ya mata zobe ta hanyar haɗuwar hadarin ɗin kawai, duk da cewan duhun hadarin ya sanya garin ya koma kamar irin tsaƙiyar daren nan ,Amma hakan bai hana ƙwantaccen hadarin dake ƙasan gajimaren bayyanuwa ba. Yayin da gajimaran ke haske yana bada wani ƙara mai nuni da cewa hadarin gab yake da zub da ruwa. Musamman yadda garin yay jajir baka jin sautin komai sai na rugugin cida da tsawar dake sauƙa. Se kuwa ƙara ƙainar ababen hawa. Yadda hadarin ke ƙara haɗe wa da wani bada kalar sauti mai rugugi yana ƙara shaidawa mutanan garin cewa tabbas ruwan gab yake da sauka, sabo da yadda gajimaran yake ta gudu yana haɗa kansa hakan ya data hankalin tsuntsayen dake saman bishiyoyi da Flowers damar tashi domin samun mafaka. Kafin a ɓarke da wani ruwa me ƙarfi da ƙara irin na lokaci gudan nan ba tare da yayyafi ba. Ruwan sama akeyi me ƙarfin gaske me haɗe da iska, wanda sanadiyyar hakan garin yayi duhu sosai, bishiyoyi da flawoyi ta ko ina se kaɗawa suke yi suna rangaji tamkar zasu faɗi ƙasa, Tsit kakejin garin yayi, domin kuwa ruwan irin me ƙarfin nan ne da tsoratar da ba yin ALLAH. Sosai garin ya sake murtukewa yayi baƙi sosai, sai ƙarar sauƙar ruwan kawai kake ji ne haɗe da iska da ake tayi ba ƙaƙƙautawa, baki ɗaya duk ilahirin ɗauƙaƙin mutanen dake cikin garin yana ɓoye ne a ƙarƙashin kulawar ruffunan kwanukan gidajensu.
ꨄ 𝙈𝘼𝙎𝘼𝙍𝘼𝙐𝙏𝘼𝙍
𝙐𝙈𝙈𝙐𝙇 𝙔𝙊𝙊𝘿𝘼
A daidai wannan lokacin a can cikin masarautar Ummulyoodah kuwa, itama tsitttt ɗin take. Shiru babu alamun kowa, domin kowan kuwa yana ɓoye ne wurin a irin daidai wannan lokacin da sheƙa ruwa kamar da bakin ƙwarya. Masarautar tayi wani irin shiru sosai me sanya tsoro, wanda a daidai wannan lokacin ne wasu mutane biyu masu sanye da uniforms, yayin da ɗaya ke riƙe da wata royal blue gothic chair, ɗayan kuma na ɗauke shima da wata plat chair. daga ta bayan su kuwa wani perri mian ɗin ne riƙe da umbrella a hannu sa, Duk da kasancewar ruwa ake kamar da bakin ƙwarya. Amma haka suke tafiyar ɗaya a gaba biyu a baya. Baka ganin fuskar shi wanda akema irin wannan hidimar, domin kansa yana a ƙasa ne, kuma fuskar nashi rufe take da mask sedai kaji ƙarar sautin takunsa a bayyane, da ƙafafun nasa suke sanye cikin wani lafiyayyan takarmin fata baƙi, irin na gidan sarautar nan, Se shigar dake jikin sa kuwa ta wasu shegun outpit riga da wando, gaba ɗaya damatsan hannun sa a bayyane da suke nan wasu irin lafiyayyun farare dasu, haka suka shiga ratsa cikin masarautar da dukkan alamu ko dai zuwa zagaye suka fita ruwan ya ritsa dasu, me bi kuma dai dama niyar fitar ne sukai amma se ruwan ya dawo dasu. Sosai Emirates Place ɗin yake da wani irin mahaukacin girma da kuma tsaruwa.
don duk wanda yaga wannan gidan to kuwa tabbas gidan ya gani ba muna gida ba. Don ko makaho ya laluba ya san ehh kwarai wannan gida ya gama amsa sunan sa tsaff na Emirates place ɗin. Wani bafade ya zube gaban sa, jikinsa na rawa ya shiga furta. "In kaji ana duhun dare mai ɓatar da Rigar sarki to kai ne, yarima sarkin gobe, Sarari kake mai ƙare gudun doki, kaja sunja basu ga da kyau ba, jeji kake kafi gaban Ayi maka ƙyaure, Jan zaki Maganin Abokan gaba, Sadauki Adalin Jagora kana gaba kullum suna bayan ka, dama da hauni Lafiya Alheri *PRINCE SHAMEER AFUUD*, idan na ganka haske kake zamemin maganin duhu me gayya, waye yace da kai ba kai ba?, yanzu ya zamo sheƙaƙƙe..... " ɗaga masa hannun da yay ne ya sanya wannan bafaden dakata, wanda shi kullum aikinsa indai ze kalla shameer ɗin seya masa ire Iren waɗan nan tarin kirarin. P cap ɗin dake kansa ya zame kaɗan ba da yawa......
♡
Ya subhanallah ALLAH gwani wajen tsara halittar ko wanne bawa, to fa ni dai AMMEY LAYLERH daga inda nake tsaye na furta hakan, domin idan har dai idanuna ba gezai suke son min ba se na kalla kamar Captain AA ɗin mune wannan bawan ALLAH, se daga baya dana sake ƙure shi da ido na gane ashe ba shi bane. Amma dai ko waye wannan halitta suna matuƙar kama. Daga nesan da nake amman hakan be hana ni tantance iyakar haɗu wa da guy ɗin ke da ba, shi kansa gaba ɗaya gashin kansa zube yake a jikinsa, wasu ta Saman fuskar shi, wasu kuwa ta saman shoulder nashi, luf-luf haka gashin yake kwance a kansa, baƙi ƙirin dashi se kyalli yake yana shining na kyau da ɗaukar hankali. Gashin girarsa kuwa da take irin thick ɗin nan, sai ɗan silky sajen dake kwance ɗan madaidaici dashi siriri wanda yayi carving nashi, Dogayen eyelashes nasa kuwa wanda suke gwanin birgewa dasu, kwayoyin idanunsa farare ne tass irin wanda idan mutum ya haske ka dasu kake gaza jurema kallon cikin su. Se bakinsa dake nan very light red ɗan madaici dashi irin filic ɗin nan, Duk da cewar Kyakkyawar innocent face nashi a ɗaure take amma hakan be hana dimples nasa ɗaya dake kumatun damarsa lomawa ba,kallo ɗaya zaka masa kasan cewar shi ɗin dogon dirarren namiji ne, yana da faffaɗar ƙirki da kuma cikakkiyar sura ko a ido. Ofcourse naji ana yawan cewa ɗan Adam bai cika goma ba, but za’a iya ƙiran wannan hallitar da ta cika goma, amma ban sani ba halan ya gaza ta wani ɓangarene ko a hali. amman inde ta hallita ne kam se MA SHA ALLAH , ALLAH ya basa, don ban tsammanin akwai macen da zata ga wannan bazara ten matashin samrayin ta kalle shi sau ɗaya bata kuma kallonsa ba. I mean ba mace kaɗai bama kowa in all. Tafiya suke amma hannun sa ɗaya na riƙe da p-cap nashi daya riƙe a hannun sa, kalaman waccen yarinyar ne kawai ke nemar taɓa tunaninsa. Hannu kawai ya iya ɗagama bafaden, domin tsintar kansa da yayi da maganar yarinyar da suka haɗu ɗazu a mall da yaje wanda shi ne sanadiyyar da ruwan saman ya tare su, da dukkan alamu ita ɗin bakuwace shi yasa har zata tsaya gabansa, ta duba tsabar tsaƙiyar idanunsa ta furta masa wannan mummunar kalmar.
_Are you mad?, kana hauka ne? Ko kuwa dai ka sama taɓin hankalin ne ban sani ba?, da har zaka nufoni gadan gadan baka da alamar janyewa?_ ★ haka baƙar maganar ta ratsa har cikin kwakwalen kansa, cikin zazzakar muryata mai daɗi da daɗin sauraro. Da yanda take wani frowning fuskar ta mai fidda zallan kyau. Haka sukaci gaba da tafiyan wasu kuyangan na mara musu baya, Wannan tsadadda kuma lafiyayyar olive skin in nashi sai shining take. Duk inda ya gimla ji kake tamkar mutuwa ta gimla wurin ne. Kasancewar sun kawo babban mahaukacin wani ƙayataccen parlour na daban.....
♡ Inda ita kanta ƙofar shigar take kewaye da wasu uban jigba jibgan guards da jikin su yake a murmurɗe. Daga ta tsakiyar parlourn suka yanki wata hanya daban, suna nufar wata shegiyar doorglass da aka yi da zallar Crystal stones'. Suna nufar ƙofar ta buɗe take wani tsararren glass staircase ya bayyana, wanda ƙafar benen take kewaye da tsil tsillin kuyangai maza, benen ya suka fara taka wa, wanda zuwa lokacin duk wanda suke bi biye dashi sun dakata se iyaka mutane biyun nan da suke ɗauke da chairs ɗin nan, daga na suka sake nufar wata ƙofar itama
Kaman dai yanda ko ina yake zagaye da dakaru haka ita ma nan ɗin take kewaya da dakarun, Wata hanyar suka sake bi doguwa nan ma kaman corrido mai ɗauke da ƙofofi wajen shida ko wacce a garƙame da matakan tsaron. Daga nan ƙofar tsakiyar wacce tafi ko wace girma da kyau tana fuskantar su suka dakata. Kai ba ka ce ƙofar bace a wurin kasancewar ta glass ce irin me narai narai ɗin nan da aka yi kaman da gold sai sheƙe yake, daga saman ta an rubuta EMPEROR SHAMEER AFUUD..... Shine sunan dake walƙiya ta saman FLASHES WELPAPER ɗin dake haskaka glasses ɗin da difference color's. Dakurun dake zube gaban ƙofar ne suka amshi chairs ɗin kawunansu a ƙasa suna komawa su kame, wanda na ƙarshen ne suka amsa, Se suka koma a farkon baki ɗayansu suna sake sanƙamewa, wanda a kallo ɗaya zasu iya bama mutum matsanancin tsoro. Shi kaɗai ya shige ƙofar, su kuma suna saurin bin bayansa da da chairs ɗin, anan parlourn daya kasance mallakinsa shi kaɗai suka dakata suma, suna saurin juyawa su fita, Zaune ya kai akan gothic chair ɗin da suka ajje masa, yana ɗaukar ƙafansa ɗaya ya ɗora kan plat chair ɗin, tare ma da ɗago ɗayar ya sake ɗorawa a kan ɗayar yana crossing nasu. A natse ya sanya gwiwar hannun sa yana tallaɓar haɓar sa da yatsun sa daya haɗe su guri ɗaya. fuskarsa babu wani expression akai, double dimples nashi da suke a ko wanne kunci ne suka ɗan loma, gimlawar Kyakkyawar fuskar ta daya kalla. Se kuma a take jikin sa ya shiga tsuma yana yin fuskarna haɗe wa tino wannan ƙofar da a duk sanda zeci katari da ita se yaji kamar tafasa jinin jikin sa ake. A take yaji ransa yana ɓaci don haka ya mika hannunsa yana janyo Pape na shishan shi ya shiga zuƙa yana fesar da hayaƙin. Don kalla ƙofar kawai ji yake kamar ana tafasa jinin jikinsa ne, tin da ya taso a kulle yake kallar ƙofar, daya taɓa tambayar maminsa me ya sa ba'a buɗe ƙofar can, tace dashi. Wata mahaukaci ya data kashe mijinta ta kuma jefa jinjirin da tana haifar sa a cikin rijiya, ya sha auna zuwa wurin sedai daya tinkara ƙofar zeji ana wani irin kwalla masa kira kamar za a tarwatsa kansa. Me yasa yake jin kamar ba haka abun yake ba?, me ya sa yake jin wani emotions na daban a duk sa ilin da kawai ze haɗa ido da iyaka ƙofar kawai?, me ya sa? Me yasa yake jin abubuwa da yawa dangane da hakan?, Ba shi dame bashi amsa don haka yasake jin ƙansa na dada ɗaukar chaji.... Comfortably yake shan shi shan yana sake streaming waɗan nan jerarrun abubuwan......
*PRINCE SHAMEER AFUUD* kenan lamba ɗaya a wajen tantiranci, domin kuwa duk masarautar babu wanda baya jin shakka da tsoronsa, idan ka ɗauke Mahaifiyarsa *FULANI RUMAANA* tare da ƙanin mahaifinsa *AFUUD KAMAALA RAHEEM DAWOOD* to kuwa baya shakkar kowa a duka masarautar, yana da wani irin zafin kai na gaban kwatance na ƙarshe, yana da wata kalar zarrar da yayyensa ma tsoronsa suke, don ya sha laka ɗa musu na jaki, barin ma Yareema *ZAYED* ɗa ga *FULANI MARDIYYA* duk da kuwa kasancewar uba ɗaya suke, Ƴaƴane ga margayi. *SARKI ASHFUD KAMAALA RAHEEM DAWOOD*.
Se kuwa masha wuyan *YAREEMA TAJUDDEEN AFUUD*, Haka ze kama ya lakaɗa haka Sarki Afuud ze sanya dogarai kama SHAMEER ɗin su jibga suma, abin se ya zame musu kamar wani game's, kullum da kakar da suke bugawa, zuwa yanzun kuma da yayi hankali seya dena kula su, amma fa kowa shakkarsa suke yi, har zuwa yanzun, don basu manta baya ba, baya shakkar shaye²nsa gaban kowa ko uban waye. Tin mahaifiyarsa najin ɗaci da ciwon abin, har hakan ya dawo ya dena ɓata mata itama.
Se da ya ɗebi fiye da 50 mints zaune a wurin kana ya miƙe idanunsa nayin luuu kamar zasu lumshe, ya nufa ƙofar da nafi tunanin bedroom ne, jikin tafasar jini yake taka ƙafafunsa kan tattausan carpet ɗin da yake tin daga farkon palon har zuwa ƙarsbensa, hannun sa ya sanya yana tura ƙofar bedroom ɗin, yana zubewa tsaƙiyar ɗakin, ana masa amsa kuwwa tsakar kansa har zuwa lokacin, throw pillown dake gefen sa ya janyo yana ratayo kansa da hannuwansa yana ɗora ƙeyarsa kan pillow ɗin, tare da ɗora ƙafarsa akan wani daya jefa, don fa shi a tsarin PRINCE SHAMEER duk inda yake dole zaka same shi ne ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, inda wannan ɗabi'a tashi take baƙanta ran sarki AFUUD don ko shi da yake sarkin be iya irin zaman da shameer ɗin yake ba, sake gyara ƙafar yayi akan zagayayyun pillow ɗin da dama mafi aka sari aka fi gani a gidan sarauta, domin dama mostly na gidajen sarauta ne ta.
♡ A hankali ta maida idanunta ta lumshe tana haɗiye wani yawu ahankali daya jima ƙafe mata, zafi take ji, zafi irin mai mugun raɗaɗi a zuciyar nan, ji take kamar ana gasa mata zuciyar a oven ne, kuma ana tarfa mata narkakkiyar dalma ne. Abinda take ji bazai iya misaltuwa ba, koda zata mu salta ma bazai musaltuba, domin ba zaka zaka gane ba inda ba tsintar kanka kayi a cikin irin halin da take a ciki kayi ba. Wanda bata fatar ko maƙiyinta ya shiga irin wannan halin da take a ciki. Tana son hawayen da suka jima janye mata ne, yau ɗaya tayi nasarar fitar dasu ta hanyar kwaranyowa, ko zai wanko mata wannan ginannen mikin daya jima ɗin ke mata, su zubo mata ko yaya ne amma shiru kakaji, so take tayi amma ya gagara, domin idanunta sun jima da bushe wa, tuni sun dena amsar kukan, domin anyi babu iyaka, zuciyar kuma ta soye kukan kuma is nowhere to be found.
Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe ahankali tare da shiga duniyar tunanin rayuwa.....
♡
Tin daga lokacin da aka gama lalata mata rayuwarta, ta hanyar rabata da jariranta biyu da kuma rabata da adalin mijin ta mafi soyuwa a cikin duniyar ta, ta jima da shaida cewar lallai wannan duniyar abace mai ɗauke da nau' ikan darasi da tarin ƙalubale na rayuwa. Ta sani cewar sautin bugun Numfashi yana ɗaya daga cikin tasirin Rayuwa, sa'ilin da kyakkyawar Ma'amala da zamantakewa suke kasancewa jigo ne na sanin abinda ita kanta rayuwar ta ƙunsa. Tabbas a cikin Rayuwa akwai dumbin darasi, ma'abota ilimi da kowacce halitta yaci ace tana da kyau ta samu damar nazarin hakan, domin yin hakan shine zai bamu damar aiwatar da rayuwar mu cikin sauƙi. Domin mafi yawa a cikinmu muna da ilimin Sanin MAƘIYA ne, amma bamu da tabbaci akan MASOYAN da suke son mu da gaskiya. Domin wannan al'amari ne da Rabbil Izzati kaɗai yasan wannan. Idan muka duba zamantakewa da kuma rayuwar kanta, ta yau zamu iya cewa. _kowane ɗan adam bazai rasa MAƘIYA ba, kamar yadda wasu suna can ata gefenmu suna yi mana SO na gaskiya. Ita a da can rayuwar su ta baya gani take duk wani wanda ze raɓeka masoyin kane, Se daga baya ta fahimta, tabbas tin daga waccan ranar ta jima da haddar nan ta kalmar. _MAKASHINKA YANA NAN TARE DAKAI_ Domin kuwa zahirin ta gani ganin idonta, an kashe mata miji, an kuma rabata da jariran da ta haifa, wanda ko damar kallarsu da kyau ba tayi ba, Haƙiƙa Rayuwar yanzu cike take da nau ikan ƙaddara, Se in ka ka zauna da kyau ka fahimceta, shima wani abune da kan iya zama wani sashen koyon ilimi tare da Fahimtar abinda Ubangiji ya tsara a gare mu tattare da wasu mutanen. Sau da yawa wasu mutanen kan cewa wai _Kyakkyawan aikin mu, shi ne zai bamu damar yin kyakkyawar rayuwa_ sedai ita a nata ɓangaren ta jima da Musa hakan, domin sunyi kyakkyawar aikin, amma daga ƙarshe makomar nasu bame kyau bace. Wasu kuma suna cewa _Kawaici da Alkunya suna saka mutum yayi ƙarko_ sedai su a nasu lokacin duk hakan ba tay musu aiki ba. Wasu kuwa cewa suke, _Furucin mu na Alkhairi yana ƙara wanke zukatan mu ne, su kuma zukatan mu sune matattarar sirrikan mu, dan haka sai mun daidaita Furucin mu sannan zamu samu damar Ajiye Sirrika kyawawa._ ta jika da fahimtar hakan. Kamar yadda ta jima da samin cewa, Ƙalubale a Rayuwa ba sa taɓa ƙarewa....Tabbas a yau ita Adeenerh Al-Hussain ta shaida ewar. Rayuwa filin gwagwarmaya ce da faɗi-tashi. Daga an fita daga wannan matsalar wata ake faɗawa. Haka za'a cigaba har zuwa sanda rai zai yi halinsa. Don haka ake son mutum ya dena ɗauka cewar zai samu hutu ko kuma jin dadin rayuwa ba tare da wata matsala ba, Matsalolin rayuwa ba sa yanke wa, saidai su yi sauƙi. Don haka kada ku yi tsammanin samun hutu a cikin ta. Wani irin numfashi ta sake domin kukan yaƙi zuwa ya gudu ya barta, zuciyarta da idanuwanta sun bushe, wani shegen wahalallan numfashi ta sauƙe, tana jin yanda jikinta yake wata irin rawa, idanunta kawai ta ja tana kulle su da suke wasu jajir dasu. Ko dan irin yadda ake danne ta ta ƙarfin masifa da bala'i a mata allurar mahaukata, idan ta tuna hakan wani irin gashi take amsa daga zuciyar ta. Komai bakinta baida kuzarin furta wa, don bata da ikon furtawa saboda hakan na nufin ruwan sama zai wanke jinin ta,bayan anraba jijiyoyin da suka riƙe kanta da wuyan ta. Saidai ba zata iya hana zuciyarta ƙunci ko radadin zuciya ba, _Ya ALLAH let me enemies live long to see what
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 23