I will be in future! _ ta furta a zuciyar ta, a bayyane kuma tana me furta...................
ꨄ"YA ALLAH kai ne ALLAH!!!. ALLAH nayi tawassali da sunayenka tsarkaka, ALLAH don soyayyar ka da Habibinka ANNABI MUHAMMAD (S.A.W), ALLAH don alfarmar annabawa da manzanninka, Ya ALLAH don isar ka da ikon ka, ya ALLAH don matsayin Alkur'ani Littafin ka, ya ALLAH ba don halayenmu ba, ALLAH kai ne mai amsa adda'ar bayin ka, ALLAH ni me rauni ce gabanka, ALLAH kaina a ƙasa hannayena a sama na ke yin wannan roƙo. ALLAH kai ne ka faɗa mana inna ma al'usru yusrah. ALLAH ka kawo min sauƙi a bayan wannan tsananin jarabar taka da ka jarrabeni da ita ya ALLAH. ALLAH kafimu sanin daidai ALLAH karka barmu da son zuciyoyinmu. ALLAH Kai ne ALLAH!!!, kai ne kaɗai kuma zaka iya maganin waɗan nan matsalolin, ka kuma sha re hawayen wannan killatacciyar baiwa taka a wannan loƙacin ma. ALLAH ga Yara nan a gareka, Ka tsaretar min dasu daga duk kan wani sharri, ya ALLAH!!!" Se kuma wani irin kuka yaci ƙarfinta yana sarke mata ƙirji. Amma tarin abin mamakin sammm babu ruwan hawayen. Kanta ta ɗago wanda yasa a take seda na ɗan zabura, amma kuma dana tsaya na mata kallon tsanake, bawai irin na tsoro ba kamar kallon farko, har bansan sanda bakina ya subce ba wajen furta kalmar.
_ MA SHA ALLAH tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai daya halicci wannan halitta mafi kyawu mai cike da haiba_ ★ hannuwanta ta ɗaga sama tana me furta. "Ya ALLAH ka kawo min mafita da ƙarahen wannan wasan, ka kuma yayemin wannan azabar da nake ji cikin raina. Ka kuma bayyana kuma cikon iko da amincinka ya ALLAH ya kuma nuna musu cewar ADEENEERH AL-HUSSAIN KUWAIT, ba mahaukaciya bace, sedai ina rasa hankalina sau da tari, ta hanyar allurar da ake min wacce take fin ƙarfin kai na , wanda nasan kariya da kuma ikon ka da kuma ƙarfin tafasashshen jinin dake gudana a cikin jikina ne, yake ƙin bama hakan haɗin kai wajen ruguza tarihin rayuwa ta....... Ya ALLAH ga abinda wasu daga cikin bayinka suke shukawa a ɓoye, to ALLAH sun gama shuka tasu, sun kuma tsumayi ranar girbin, don haka ka bayyana musu abinda suka jima shukawaaa... "
*SHAMEER*
tamkar wanda aka zabura, haka ya miƙe tsaye yana fatali da Pape na shishan shi, yana nufar bedroom nashi, haka kawai yaji jinin jikin sa na wani kalar tafarfasan da bai taɓa jin kwatancin saba, don haka ya shiga tuɓe kayansa anan tsakar ɗakin, yana me nufar bathroom. Kai tsaye cikin bathtub ya kwanta tare da rufe idonsa, yana ƙoƙarin siffanta wannan halittar da ta jima tsorata shi, a duk wani lokacin da zai kasance cikin shan wani abu na maye, tin yana ɗaukar hakan ba komai ba har dai ya zo yake kallar abin a wani mizani na daban. Sake kwanciya plat yayi a ruwan, yana karonto duk wasu adda'o'in da suka zo masa, domin samun nutsuwa azuciyarsa har tsawon lokaci, kafin yayi wankan ya fito ɗaure da towel milk color, yana nufar ƙatuwar closet nashi, ya ɗauki kaya marasa nauyi na shirya kansa ciki, tare fesa turare mai sanyin ƙamshi ya nufi gadonsa ya ɗan kwanta a hankali, sosai ya sake shigewa cikin lallausan duvet ɗin tare da zira hannu ya kashe wutan ɗakin, yana lumshe ido da niyar wai ko bacci ze ɗan sace shi, kafin sallar magrib, Se dai ina baccin yace bega wurin zuwa ba, haka wasu abubuwa masu kama da famarki, suka dinga gimla masa a ido biyu.
Wani irin shiru yayi tin da ya lafe cikin tsaƙiyar gadon, wasu abubuwa yake gani, wannan ƙofar tare da matar dake razanar dashi kawai yake kalla tana cikin wani mawuyacin hali, wacce be taɓa samar koda ganin kwayar idaniyarta bace, kawai tana zuwar masa ne a siffar mace ta juya masa baya. Wani kalar riƙe kansa yayi wani ya wani kalan mugun sara masa, ga jinin jikin sa da yaji yana wani kakar masifar tafasar shima. Kunnen sa ya toshe da duka hannuwansa biyu, tare da fasa ƙarar da seda gaba ɗaya masarautar da ɗauka, wanda ba don ruwan saman da ake sheƙawa kamar da bakin ƙwarya ba, da babu abinda ze hana kowa dake cikin masarautar jin wannan ihun, wata kafurar nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, ahankali kuma wani hawayen wahala na gangaro masa da yake jin ƙunarsu na ƙoƙarin ƙona masa fuska, yana kwance aka ƙira sallar magrib amma ALLAH be bashi ikon tashi ba, har aka ƙira isha'i, Se wajajen ƙarfe tara kana ya iya tashi, da kyar ya kai kansa toilet, wanka yayi da kyau tare da gasa jikin sa, kana ya fito yana gabatar da sallolin dake kansa, ko abinci be buƙata ba dayay karatun Qur'an ya koma ya kwanta, yana kwanciyar bada jimawa Fulani Rumana mahaifiyarsa ta bada umarnin ganin sa, zaune ya tashi cikin ɗan ƙarfin jikin daya samu ya fita zuwa parlournsa da take jimansa, tana zaune ƙafarta ɗaya kanta, gabanta ɗauke da dinner tare da matashiyar yarinya, ɗan yana yin fuskar sa ya saki don baya taɓa haɗa son mahaifiyarsa da wani, cike da kallon so me tafe da harara take kallon sa, ɗan sumar kansa ya shafo yana zama a kujerar dake pacing da ita. Gaida ta yayi cikin kulawa sosai, amsa shi tayi da kulawar itama tana tambayar sa duk me yasa wunin yau bata gan shi ba. Ce yay da ita fita outing yayi cikin gari, ɗan ɓata fuska tayi, tana tambayar sa amma dai da mask a face nashi ya fita. Seda ya ɗago ya ɗan kalle ta, Ba yau ba ba jiya ba yake ma kansa ire iren wasu tambayoyin ga Ummun nashi, wai shin me yasa bata taɓa barin sa fita ba tare da mask ba?, me ya sa sau da tari take son daƙile shi akan wasu abubuwan?, ba shi da ikon ɗora zargi akan mahaifiyarsa amma ba don haka ba da tuni ya jima da ɗorawa...... Fira ba da yawa ba suka taɓa Ummun nashi ta masa sallama ita da budurwar nan suka tafi, ɗakinsa ya koma ya sake kwanciyar sa. Ƙiran sallar asubar farko a cikin kunnuwansa, dan haka ya miƙe tare da adda'an barci a bakin sa, kai tsaye toilet ya wuce. ruwan wanka ya haɗa. lumshe idonsa yayi tare ɗan fara wasa da ruwan. A ƙalla seda ya ɗauki mintina kafin yayi applying showe gel nasa mai sanyin daɗi, kana ya wanke jikin sa tass sannan ya fito.
A hankali ya fito daga toilet ɗin yana fitar da wani ƙamshi, har yazo tsaƙiyar ɗakin da har an gama gyara shi tass kamar wata rai me numfashi be taɓa kwanciya ba, akan wani vanity table ya kai zaune, tare da jan plat chair yana ɗora ƙafarsa ɗaya a kai, zama yay yana kallon kansa olive skin nasa sai glowing take yi, farar jallabiya ta maza ya saka yana miƙe wa ya fice zuwa masallacin masarautar, Tsayawa yay cak ya samu kansa dayi, a daidai wannan ƙofar da ya sha auna shigar ta, amma be taɓa samar nasara ba. Tsittt masarautar take babu motsin kowa, dan haka ya yunƙura da niyar tinkarar ƙofar, sedai cak yaji kamar an gina shi ne a wajen, sake gwada cira ƙafarsa yayi a karo na biyu amma hakan take, gwada tafiya wata hanyar daban yayi, ga mamakin sa kuwa se yaga ya tafi, don haka ya dawo da baya amma irin ta farkon dai, A take kuma namomin jikin sa suka soma ɓari, idonsa na rikiɗewa su yi ja sosai, Ambatar suna yen ALLAH ya shiga yi, Tamkar gilmar abu haka yaga gilmawar Ummul abeed. Wani kalan runtse idonsa yayi jikin sa ya fara jijjiga, tabbas akwai wani lamarin da ba haka ya kamata ace yana tafiya, dole akwai wata kulla kullar da aka jima ɓoye wa a cikin wannan masarautar, Idonsa dake lumshe ya buɗe da ƙarfin bala'i, tino wannan baiwar data taɓa bashi kwatan kwacin labari akan wannan ƙofar, ba ta kai ga bashi labarin ba washe gari aka tsinta gawar ta a gaɓar ruwan masarautar, kenan hakan na nufi dole akwai wani abu da ake ɓoye masa, Me yasa mahaifiyarsa koda wasa bata son ganin ya kusanci wannan ƙofar?, abubuwa dai suna da yawa da suke faruwa ba'a daidai ba dole. Sake gilmawar fuskar wannan kuyangar ya gani. Kafin ta bayyana gabansa tana me furta.
"Tabbas kai madara ne me kama da nono yaro, giji kuma se giji, babban goro kuma se magurjin ƙarfe, WUTAR KUMA TA GAMA RURUWA BAYAN TUMU, Kibiyar ajali kake wacce sulƙe baya iya ratsa shi, ɗan zaki ka gama girma, dan haka kowa ya yunƙuro ka bar shi ya doso, kowa kuma yay faɗa da damisa ya duba jikin sa, ko an kashe biri biri yay ɓarna, hadari kake sa gabanka inda kake so, ka sani jeji kake kafi gaban ayi maka ƙyaure.... Kaje!!!, kaje ga mahaifiyarka ta haƙiƙa, kaje domin ta jima jira yin wannan rana, ka tuna kai ɗin damisa ne, ɗan ɗamisa, ka farka ka tashi, ka tashi ka nuna musu cewar. *RAMIN KURA SE ƳAƳANTA*,Tabbas ina mamakin wannan duniyar, ƙarfin hali yama wasu mutanen yawa, ta yanda abu ba mallakinka doke kace Seka mallake shi koda da ƙarfin tuwo ne, wannan shi ake ƙira da shiga hurumi, kaje zaka yi nasara, domin lokacin ta ne ze fara daga yau daga yanzun har zuwa lokacin da da za a yi walƙiyar...... " Hhhhhhhh Hhhhhhhh Hhhhhhhh se kuma sautin dariya ya biyo bayan maganganun da ya gisu tamkar shuɗewar wasu abu..... Da wani kalan bala'in ƙarfi tare da adda ɗauke a bakin sa yaja jikin sa da ƙarfi, Se gashi tsaye cankarkar gaban ƙofar nan, da dukkan ƙarfin sa ya daki ƙofar, sedai ko gezau ƙofar nan ba tay ba, da wani ƙarfin ya sake dukan ta, be tashi aune ba se tsintar kansa da yayi can nesa da wurin sosai zube warwas...... _Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un_ bakinsa ke ambata cikin firgici da rawar jiki, sakamakon farkawar da yay, don shi a tunaninsa ɗaya ne daga cikin irin mummuna mafarkan daya saba yi. Yau ɗin ma ya riske shi a cikin barcinsa. Kansa ya dafe da take yaji yaba masa wani irin sarawa na ciwo tamkar ana masa luguden taɓaren daka a tsakkiyar kansa, gaba ɗaya jikinsa ya jiƙe da zufa tamkar wanda ya gwada wasar tsere, sedai sanjawa salon mafarkin nasa daya gani ne saɓanin na baya, shi ne abu na farko daya fara tsaya masa a rai da bashi tsoro. Domin kuwa mafarki ne mafi tsoratarwa kuma kusan mafarkan ɗaya ne ke maimaita kansa a kowane barcin sa idan ya kwanta. Sai dai mafi tashin hankalin a yau yayi kamanceceniya da na wasu dare da tarihin su bazai taɓa mantuwa a cikin brain nashi da rayuwar shi ba..... Tsaiwar wasu daga cikin mutanen da suka fito domin zuwa masallaci ne ya sanya shi gaskata cewar ba mafarkin yake yi ba
tabbas a zahiri ne......
♡
*AFUUD*
A wani kalan masifar firgice ya farka daga mummunar barci me tafe da mummunar mafarkin da yayi. Idon sa kai tsaye be sauƙa akan ko ina ba se kan... zoben shi na gwal dake kan wani ƙaramin tebir na zinare, wanda ya dauƙi wani irin haske kaman fitila. Sai kuma ɗiff hasken ya ɗauke tamkar almara tamkar kuma a film, a take zoben ya yi wani irin baƙiƙƙirin kaman gawayi. Kai ba za ka taɓa tunanin cewa zoben gwal bane. Zuwa can kuma se ɗakin ya ɗauka wani yuuuuuu, kafin wata irin iska wacce tafi kama da guguwa ta zagaye ɗakin. Wata irin wantsalowa ya yi, Se gashi ya faɗo daga saman gadon tare da nufar inda zoben yake, ɗaukar zubon yayi cikin matsanancin mamaki yana sake duban sa da kyah. Meke nan? Me kuma hakan ke nufi? Me kuma yake gani?. Jinin Ashfud fa kenan hakan yake nufi ya bayyana, jikin sa har wani kalan rawan tashin hankali yake.....
"Wannan ɗin sheda ce fa dake nuni da cewar jinin ASHFUD ɗan da ADEENERG ta haifa na raye a doron ƙasar nan har yanzun?....." ya faɗa cikin zafi kafin ya hau safa da marwa cikin zafin zuciya.
Tamkar kiftar ido wani baƙin tuƙuƙin hayaƙi ya bayyana, take baƙin hayaƙin nan ya riƙe ta sega siffar wani ƙakkarfan aljani ya bayyana.
"Tabbas wanda ya aikata hakan yana a cikin wannan masarauta, yana kuma da babban shirin da yafi namu. Ina kuma ji a jikina wannan ɗin wata ƙofa ce zata buɗe babba, ta fara babban yaƙi?, yaƙin da zai shafi kowa da kowa dake cikin wannan masarautar, yaƙin da in aka fara babu ranar dena wa, shin dama ba sai dana taɓa faɗa maka ba cewar akwai irin wannan ranar da zata riskeka ba, jinin ADEENERH yana da ƙarfi yana kuma da zafin da samm samm ba zamu iya ja da su ba, tin da har wannan ranar ta zo da wani ya tinkari baƙar ƙofa, tabbas mabuɗin wasan ze fara..... An gama wargaza mana shirin mu na farko, dan haka zamu tafi na biyu. Zakayi yanka na baƙaƙen manyan raƙumma guda casa'in da tara a daren goma sha uku, domin dole mu san ja sabon salo, ta hanyar da zamu iya kama tsuntsu mai wayon ta cikin ruwan sanyi.........." Ɗan dukawa yayi tare da jinjina kai alamar ya amsa kafin ya furta."Angama uba mai sha re kukan masu kuka, me cikakken ikon da babu kamar sa, mamallakin duniyar me juya ta a duk lokacin da ya so, ba a ja da kai ba'a gudun ka a fannin aiki, kai me faɗa da cikawane gwaniiiii..........
Wata irin mahaukaciyar dariya mai amsa kuwwa aljanin ya fasa, kafin kuma hayaƙin daya koma ya ci gaba da Ƙyalkyala dariya, sai da ya ɗauka tsahon lokaci ya na yi kafin ya tsagaita, tare da tsuƙe fuska tamkar bai taɓa dariya ba. Wannan guguwa da rugugin Iskar da ɗakin ya ɗauka kuma ya ɓace ɓatt, kaman an ɗauke ruwa. Juyawa ya yi tare da kallar madubin dogon yaron dake ɗakin, ɗan shafar madubin yayi sai dogon yaron ya rabe gida biyu kamar ƙofa. Yana shige wa ciki a she wani irin boyeyyen ɗaki ne da yake gudanar da dalasaman tsafinsa.... Wani kalar saurin waro manyan idanuwa nayi, don ganinnnnn.........
A guje na fito daga ita kanta masarautar ina yowa nan gida Nigerian’s.....
Domin kuwa acan nafi wayoooooooooo
*NIGERIA*
_CAPTAIN AA_
©Maryam Naseer Mirrah
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻
# 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Book One paid
♡
Page 27&28
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
# HE WILL FIGHT
*Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank*
♡♡♡♡♡♡♡♡
ꨄ A natse Captain AA da Babban yaronsa jamaal suka fito daga motar da shine yayi driving nasu, dai-dai da lokacin da Lieutenant Nassar Bunza ya fito daga harabar farfajiyar wurin, nufo inda suke yayi, ganin hakan ya sanya Jamaal ɗan basu wuri yana yin gaba. Tafiya suke yi a natse suna tattauna wasu maganganun da bansan kona miye ba. Office na shi suka wuce wanda suka ɗan sake jimawa a ciki kafin Nassar Bunza ɗin ya fito ransa a ɗan mugun ɓace.
Tun ƙarfe huɗu na yamma garin ya fara haɗa gagarumin hadari, wanda alamominsa suke nuna zai zubda ruwa mai yawa. Duk da har zuwa lokacin yana office nashi, hakan bai hanashi fahimtar canjin da garin ya samu ba, a ɗan natse ya miƙe ya fara taku zuwa jikin window ɗin Office ɗin ya leƙa, tabbas hadarine mai ɗauke da alamomin iska kuma, duba da yanda garin yayi jaaa, ya kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa yana huro iska a bakinsa, yana da sauran ayyuka da yawa, gashi baya son ruwannan ya samesa a waje.
Barin Window ɗin yayi ya koma gaban desk ɗinsa, wasu files ya haɗa waje ɗaya kafin ya fito da ga office ɗin da ɗan hanzarinsa irin na masu cikakkiyar lafiya. Kai tsaye Office ɗin chief of army ya nufa, dan tun kusan mintuna goma baya ya aiko ƙiransa, so se bai sama zuwa ba saboda wani ɗan aikin da yake son ƙarasawa ya kai masa gaba ɗaya. Sallama yay a ƙofar Office ɗin kafin ya shiga, su uku ya iske a office ɗin, gaba ɗayansu kuma suna cikin manya-manyan soldier, gaisuwa yay irin ta girmamawa a garesu, tare da miƙama chief of army takardun daya gama haɗa wa yana faɗin, "Sir ganan na kammala da wannan, I'm sorry for the delay late da nayi, na ƙarasa aikinne"
"Babu damuwa Captain, dama tunanina ya bani hakan, shiyyasa ban damuba, duk da kuwa jiranka muke mu duk nan" sir ɗin yayi maganar yana duban waɗan da suke taren. "Sorry Sir's" AA ɗin ya faɗa yana maida kallonsa ga sauran mutane biyun dake zaune .
Ɗaya a cikinsu ne ya fara magana fuskarsa sam babu walwala, Se ma cikin tsare AA ɗin da idanu yace, "CAPTAIN ALIYU ABDULLAHI ko?" Cikin girmamawa AA ɗin yace, "Yes Sir!" Zama wancan ɗin ya gyara sosai yana me fuskantar AA ɗin, ya fara magana cikin dakiya da kuma tsuƙe fuska. "AA kai jami'in soja ne, wanda ƙwazonka da ƙwarewar aiki irin naka, ke ƙara maka ɗaukaka ga kowa dake a cikin hukumarnan, banda zagayen jama'a r dake faɗin Abuja da kewayenta, So kamar yanda muka baka yarda a baya, So yanzun ma shi ne dalilin damƙa na Kanal Bappa Babayo a hannunka, dan tabbas mun san kai kaɗai ne zaka iya wannan aikin, saboda kana da jajircewar da ba kowa yake da irin taba, ga uwa uba NAGARTA irin ta jami'in sojan ƙwarai, shi yasa duk wani aiki me zafi kai ne kan gaba, domin kuwa kai ake ɗamkamawa, Se dai miye dalilin da ya sanya har zuwa wa. Wannan lokacin babu wani bayani dangane da case ɗin dake hannun ka na mutuwar Kanal?..." mutumin ya jefa masa tambayar kai tsaye fuskarsa a tsume sam babu fara'a ko annuri, daga taayen da yake ya sake haɗe kyakkyawar face nashi tare furta." Sir ina kan ƙoƙarina akan hakan, duba da cewar niba Allan misru bane, domin kuwa bana da ilimin sanin gaibu akan aiki na, Se dai ina da naci da kuma jajircewa a kan duk abinda na sanya gaba, Kaga kenan se an jinkirta...." yay maganan yana ɗan ja baya tare da sa rawa, kana ya ɗan sake numfasawa ganin yacce duk suka bishi da ido idan ka ɗauke chief of army kawai da dama ya gama sanin halin kayansa.
"Wata alfarma ƙwara ɗaya kawai zuwa biyu nake nema a gareku, dan hakanne zai bani dama akan nasarar da kuke fata daga gareni..." yay maganan a ƙame cikin wani ɗan iskan style.
"Alfarma dai?, wacce alfarma ce wannan kuwa?" Wanda tin da aka zauna beyi maganar bane ya kalla AA ɗin tare da tambayar nasa. Gyara tsai war AA ɗin yayi yana ɗan satar kallon chief of army, chief ɗin da shima AA ɗin yake kallo ya jinjina masa kai hi ahead..... Da wani yaren da dukkan alamu su kaɗai suka san kayansu AA ɗin yaɗan ɗaga masa kai, kafin ya maida hankalinsa sosai ga sauran mutane biyun. Shirun da yay ne yana kallonsu, ya sanya su suma zuba masa idanun.... "Shiru shima wata alamace ta tsora tarwa, domin kuwa a duk lokacin da aka jefeka da wata mummunar kalma kayi shiru, su kansu waɗan da suka ji shirunka zuciyarsu tana girgiza ne. Domin kuwa basu san matakin da shirun ya ke nufi ba, wata ƙila abun da zai biyo baya sai sunyi dana sani don bame kyau bane..." Cikin izza da jin yakai jarumin na gaske ya ɗago kai yana kallon general Toufiq Ali wada, sai kuma ya sake wani lallausan murmushi da ya saka kumatunsa duka biyu loɓawa.
"Gudun rashin samun nasara kuke yi?, ko kuma dai kuna gudun yazam ba'ai nasarar ba......." Yay maganar wanda ya sa su duka ukun zuba masa na mujiya suna kallarsa, lallai se yau suke sake tabbatar da tsaurin idon yaron nan da suka jima ji... Shi kuwa daga haka ya ma fice yana barin su da hangamammen baki a sake.... AA yana fita ɗaya daga cikin Wannan soldier ɗin da suka zo daga KD domin sanya idanunsu akan takun kowa suka fara tattauna wata maganar daban, dangane da lamarin da suke son ɓulloma wannan case ɗin. Yana nan cikin barracks ɗin har dare, duk da kuwa yanda aka kece da ruwan nan kamar da bakin ƙwarya. Chief ne ya ƙira shi a waya bayan ya ɗan jima da fita yace ya same shi a waje, tare da masa kwatancen inda yaken. Komai cikin taka tsan tsan suke yi tsakaninsa da boss ɗin nasa. Da Umbrella nashi ya fita yana faɗawa cikin motar, Janta yayi har zuwa wani plat house. Ruwa ya ajje ma AA ɗin tare da energy drinks. Dubansa da kyau Chief yayi yana me furta. "CAPTAIN anya kuwa ba zamu bar wannan aikin ba?, duba da cewar ta ko ta ina anbi an sanya tsaro sosai, karmuy abinda zai sa ka zo ka rasa aikin ka daga ƙarshe, duk kuwa da cewar ni akan kaina banso ka harbe Kanal ba....." Se kuma ya ɗan fesar da numfashi yana share wata zufa a goshinsa. Tsaye ya miƙe daga zaunen da yake tare da furta."Itafa rayuwar duniyar nan lissafi ce, kana idan har muka ce zamu sare tin daga yanzun to miye amfanin lilliɓawa kura fatar akuya?. Domin tai nasarar cafkar abin farautarta ba tare da tasha walaha ba, tay yaga yaga da zaman sa.... Ka sani a wasu lokutan se an ɓata akan samu hanyar gyara wata ɓarakar. Ina so kasa a ranka cewar se mun kawo ƙarshen wannan baƙar ƙungiyar, Zamu damƙesu a hannun mu, mu gurzasu yanda muke so sir, Domin isa wajen da muke son zuwa, dole mune zamu hau bayan doki, ba shine zai hau bayan mu ba, don haka
Nothing to worry about......I'm just fine sir....... Say maganar a ɗan kausashe. fuskarsa babu wani expression akai, duk yacce chief ya so faɗin wani abin haka ya gaza, domin kuwa tuni Aura ɗin AA ɗin da yake daban ako ina ya gama baybayeshi, don duk inda yake ya fita daban cikin mutane. Wata doguwar ijiyar zuciya ya ja yana miƙewa tsaye kafin ya juyo a hankali ya fuskanci Captain ɗin.... Shi kuwa yaya yana jin yanda idanun chief ɗin ke prerciing ɗin fuskarsa amma yaƙi ɗagowa. "Ina jin a raina tabbas zaka yi nasara Aliyu, matuƙar zaka zama jajirtacce kuma ka sanya gaskiya da tsoran ALLAH a ranka da cikin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 23