wata can da kika ɗauko riƙo ragamar kulawa da mijin ki?, tin da ga lokacin data buga lissafin tin a farkon taga ba lissafuwa ze yi, ta jingine hakan gefe. Kuma se ALLAH ya sa mata dangana da haƙurin hakan, sukaci gaba da shering mijin nasu su uku. Yo su uku mana zata ce, ta tabbata abu ƙalilan ne ya raba su da Husna ɗin, shima kuma idan ba ALLAH ne ya kare ba yana nan tafe me ɗungurin uwar du ɗin.....
Zuwa lokacin kuwa duk wannan uban ramar babu, sedai ba kar ku ce hakan ba damunta yake ba, A Ahhhh sedai salamar da ubangijinta ya sama mata ne samun sauƙin ta....
Acp Maleek faaaaa?......
```LITTAFIN RAMIN KURA ba kawai labari ba ne kaɗai, labari ne me tafe da tarin ƙalubalai masu zafi, wanda nake da tabbacin zai motsa zuciyarku ya kuma tabbatar muku da kasancewarsa a tsagin irin labaran da kuka jima FATA da KUMA BURIN SAMU...... 💃 💃```
_A kwai Soyayya me zafi, akwai cin amana me raɗaɗi, akwai ƙalubalei, akwai haɗarurruka masu girma_
*Akwai cin amanar ƙasa, akwai ha'intar kai, akwai zanba cikin amin, na tabbata a cikin tafiyar yanzun ne AMMEY'NKU LAYLERH ta sanya ɗan ba a cikin wannan nazartaccen labrin, akwai bomb,,,,, akwai 🔥 🔥 🔥 🔥 🔥 🔥 a gaba sosai, wani show ma se mun antaya ƙasar ADAPHAN......*
Paid book
Book 2
# 1k
Via WhatsApp chat
08104493215
Account number.
For details only Wanda ya shirya.
3206656358
Maryam Nasiru
First bank
Or
8104493215
Maryam Nasiru
Opay
Duk ta yacce kika yi niyya Hajiyata, zaki iya biya..
Ga ƴar wata garaɓasa ma, wasu suna cewa suna son littafin amma ya musu tsada, to maza ku matso kusa zaku iya biyan 700 only na zabtare muku 300, domin ayi tafiyar manya daku... 💃 💃 💃 💃 💃 💃 💃 Welcome 🤝 Hajiyoyina sena jiku bla bla bhuuu da ruwan kira da message na wannan daddaɗa kuma nazartaccen littafin namu me suna RAMIN KURA...... 👋 👋 👋 👋 Sena jiku mutanen amana...... 💃💃 💃 💃 💃 🙏 🙏 🙏 🙏
*BY AMMEY LAYLERH 💐*
08104493215
༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻
# 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Book One paid
♡
Page 39&40
Last free page....
End of the Book one
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
# HE WILL FIGHT
# WAR
♡♡♡♡♡♡♡♡
ꨄ Apc Maleek kuwa an gabatar da zaman farko, wanda dukkan alamun nasara suka gama bayyana, an ɗage zaman ne se zuwa wata ranar Monday ɗin da safe, wacce ranar tayi daidai da ranar da AA ze bar ƙasar, gaba ɗaya hankali da nutsuwar Inspector Hannah sun kasu kashi daban daban, daga ƙarshe ma se dena fita ko ina tayi, domin kuwa sau biyu ana kai ma ita kanta hari, wanda take da tabbacin cikin yaran su green snake ɗin, wannan ƙungiya ta macizai tana shan la'anta da kuma tsinuwar mutane daga bakuna maban banta, sedai kuma wani abin girgiza zukatan daya faru a daren ranar da anan ne za'a gabatar da zaman ƙarshe aka nema Apc Maleek aka rasa, wanda kai tsaye hakan ya tada hazo a media. Me hankalin Hajiyarsa tare da hanna za su yi inba tashi ba, tare da duk sauran family nashi. Se dai kuma tsintar farar wata takarda me ɗauke da wani guntun rubutune ya sake jan hankulan jama'a gaba ɗaya. Don tini gidan yarin da yake suka fitar da guntun rubutun da suka tsinta ɗin...
_𝙂ᴬℕ𝘚𝚃𝞔Ʀ ˢɑⅈ ɠօԃⅈ𝑦ᴬ 🙏 🙏 🙏 🙏_
Kamar yadda suka Gani a rubucen kuwa haka suka ɗora, har dama screenshot na paper ɗin. Wanda kai tsaye media ɗin ta sake hargitsewa da kwaramniyar abinda ya farun, wasu na tunanin kodai ma'aikatan da haƙƙin kula da gidan ne, wasu manyan suka haɗa baki dasu aka ɗauke Maleek ɗin dan a kashe shi. Hankalin Hajiyar Maleek idan yayi dubu to a tashe yake kafin zuwar wayewar garin, Hannah kuwa data zube bata sake sanin ainihin inda take ba se a washe garin ranar. Wanda ta farka da kyakkyawan saƙo daga Maleek ɗin nata, cewar ta zama cikin salama yana a inda ya dace ne, duk da haka bata yarda ba, sedai ta ƙira No nashi, Amma kuma sweat off wayan, don haka kai tsaye Hajiyar Maleek ɗin ta ƙira, nan ta sake kwantar mata da hankali akan cewar su har waya ma sukayi dashi, yana hannun wanda ya dace ne kada ta damu. Wannan magana ita ce ta ɗan kwantar mata da hankali sosai harta sama kwarin gwiwwar sosai na hakan itama.
ꨄ
A hankali AA ya ɗago manyan fararen idanunsa da suke a lumshe tare da kallon taswirar ƙasar data kasance mahaifiyace a gare shi, daidai suna isa tsakiyarta garin chadi, tun da suka iso yankin haka nan yake jin wani irin salama da kwanciyar hankali na samun wurin zama a kowacce tsiga ta jikinsa, gefe guda kuma ga wata irin nutsuwar da yake ji gaba daji na sauƙar masa tin da suka shigo yankin ƙasar ADAPHA ɗin, haka yake jin wani irin sanyi da more happy ɗin da yake rasa daga ina yake, sedai yanayinsa be bayyana hakan ba, a can ƙasar zuciyarsa hakan ke taso masa haka kawai...
Wani numfashi mai sanyi ya fesar tare da ƙara ware manyan idanunsa yana kallon garin ta window'n jirgin.
Haka nan yakejin tamkar yabar duk wata damuwa tashi ne baki ɗaya acikin ƙasar GOA da Nigeria, tare kuma da dukkan wani ƙuncinsa a cikin GOA ne. Haka cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yake ci gaba da bin ilahirin tsarin dogayen benayen gidajen garin da kallo....
Misalin ƙarfe 7:20 daida Jirgin daya ɗaukosu daga ƙasar GOA yayi sauƙar angulu a cikin babban Airport ƙasar ADAPHAN. Daidai da lokacin da jirgin nasu ya gama daidaita da'irar tsaiwarsa a babban filin airport ɗin, Wanda jirgin na dedeta kansa, yaji wani irin yankewa tare da faɗuwar da gabansa yayi. A hankali ya fesar da wata sassayan numfashi, tare da fara taka step na forko, wanda ya fito da kanshi zuwa sararin garin ADAPHAN ɗin, _Yah Rahman_ ya furta a cikin zuciyarsa, sabida wani irin ni'imtaccen iskan daya shaƙa mai cike da salama na wani irin ratsa Jinin jikinsa, Wani rin amintaccen numfashin mai cike da yanayin sauƙe ajiyar zuciya ya sake sauƙewa, sema steps ɗin da yaci gaba da takawa yana saƙƙowa zuwa farfajiyan airport ɗin, wani lallausar cashmere ne a jikinsa, se rolling tace nashi da yayi da wani ash da farin shiramin da yay, se zagayayyen shade ɗin daya toshe idanunsa dashi, bakinsa kuma na ɗauke da adda'a. Wani saurin runtse idanunsa yayi, lokacin da ya dire tafin ƙafarsa na farko akan ƙasar ADAPHAN ɗin, yanki kuma da UMMULYOODAH, don duk mazaunin anguwa guda suke, inda gefen hagu da yankin nan hotels ɗin da yay bookings yake. Amma kuma se an hau abin hawa don akwai ƴer tasara a tsakaninsu, fara taka diga digansa kan dandanin ƙasar ne kuma ya haifar masa da wani irin tsuma,haka yaji naman jikinsa nayi tun daga can cikin jikinsa da zuciyarsa yake jiyo irin yadda namomin jikin nasa ke tsumar, be bar komai a ran shi ba sema ta'allaƙa hakan da yay, da mebi weather na garin ne hakan,
_Alhamdulillah!!!_ Ya furta saman lips nashi, tare da wasu adda'o''in , sabida tunda ALLAH ya halicce shi bai taɓajiba irin yanayin da yakeji a yanzu ba, duk kuwa da yanda yake yawan tafiye² don duk babu inda aikinsa baya kaishi. Ci gaba da tafiyar yayi yana me bin ayarin sauran matafiyar shima, yana kuma ci gaba da shaƙar sassayan iskan, Ɗan dube-dube ya fara na nemar abin hawa, sega wata lafiyayyar baƙar jeeb nan ta ratso, tare da yin parking gaf da inda yake tsaye, wani kamilallan matashin magidanci ya leƙo da kansa yana tambayar ina ya nufa, cikin yaren larabci ya furta, _FUD PEOPLE✓ MART hotels_
Da sauri driver ɗin ya fito tare da buɗe masa car ɗin ya shiga, kana yaja suka fita daga cikin Airport ɗin bayan yasa masa kayansa a side me mazaunin banza. Kansa ya kwantar akan kujerar motar, idanunsa a lumshe yayi miƙa tare da sake gyara kwanciyarsa jikin kujera na motar, daidai kuma da lokacin da suka ratso ta cikin unguwar *UMMULYOODAH*
Anguwace ta masu alfarma ta masu sarauta, haka yasa tsarinta na musamman ne daban da ko ina dake cikin birnin. haka nan ya sake jin yanayi na weather ɗin wurin ya sake masa masifar daɗi da kyau.
Gashi yanayin garin se yafi kama da yanayi irin na damuna,dan kuwa wata lafiyayyar iska mai sanyi da ratsa jiki ce ke kaɗawa , gashi duk ta inda ka wulga ido bishiyoyin dabinone masu kyan tsari ke rausayawa suna rangaji gwanin birgewa. 7:38pm suka isa gaban wani haɗadden hotels me wani irin kyau da tsari, Wanda samansa yake ɗauke da rubuta me kyau da tsari shima. Kai da ganin masifar kyau da tsaruwan hotel ɗin kasan zaiyi masifar tsada. _ALHAMDULILLAH_ ya furta lokacin da yake ƙarema hotel ɗin kallo, Ya ƙare maganar ne kuma da lumshe idanunsa jin sautin ƙiran sallar da akayi cikin masallacin hotel ɗin. Numfashi mai sanyi ya fesar tare da buɗe Idanunsa da suke a lumshe kana ahankali ya shiga motsi da bakinsa alamar adda'a yake.
Lumsassun idanunsa ya ware yana bin gini dama cikin hotels ɗin kansa da kallo, domin kuwa wani irin hotel ne mai masifar kyau da tsari da girma, Abu na farko da zai fara maka marhababin a cikin hotels ɗin shi ne ƙaton masallacin da shi ne Abu na farko d zaka fara cin karo dashi, daga nan kuma se farfajiyar hotels ɗin da yake wani irin wangamemen gaske, da yake da wani shegen kyau da tsari. daga ta can ɓangaren dama kuma wajen Parking na motoci ne, wanda aƙalla zai iya ɗaukar motoci ɗari biyu kima fiye da haka.daga ta jikin doguwar katangar kuwa bishiyoyin dabino ne zagaye da ginin daga can gefe kuma wasu irin flowers ne dake wadace da damshin ruwa, wanda baa raba jikinsu dashi kullum hakan ne ma yasa jikinsu kullum ke fidda sheƙin ruwan. daga ta cikin ainihin compound ɗin kuwa tafiya kaɗan zakayi ka sama kanka a side na shiga Reception. Ata tsakiya daga gefe da gefen kuma wata hanya ce kana daga baya wani ƙaton garden ne wanka kai tsaye idan kai dogo ne ma kana iya hango bishiyoyin dake ciki, daga nan inda yake zaune cikin motar ma har yana iya jiyo sautin kukan tsuntsaye kala daban daban.
Ahankali ya ɗago daga jingina da seat ɗin da yayi. Yana Jin zuciyarsa na wani irin harbawa kaɗan kaɗan, cikin ɗan sauri² da sassarfa mai motan ya fito tare da zagoyo ta gefen da AA ke zaune, yana buɗe masa murfin motar kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
"Mun iso sir zaka iya fitowa ur welcome" yay maganar da bashi hanyar fitowan. "Thanks u" ya furta cikin wani irin sanyin daya tsinta kansa dashi, Kana ya ziro ƙafafunsa woje ahankali ya sauƙe aƙasan interlock ɗin dake ƙawace da wurin, da sauri ya janye ƙafar yana rumtse idanunsa tare da kuma buɗesu a lokaci guda, yana jin wani irin abu mai masifar sanyi na ratsa masa tun daga tafin ƙafarsa har zuwa ƙwaƙwalwar kansa irin dai abinda yaji daya taka ƙafarsa a Airport. cikin sauri ya kuma lumshe idanunsa tare da furta.
"Yah ALLAH!!!"
Sassanyan idanunsa ya lumshe tare da sake jingina bayansa da jikin kujerar motar,wani irin bugawa yakejin zuciyarsa nayi,yayinda abubuwa da yawa keyi masa kamar zasu fasa kkwakwalwar kansa. Maida kansa yayi ƙasa ahankali, tare da sake lumshe idanunsa,Wanda cikinsu ke bayyana abubuwa da dama. A hankali kuma ya sake saƙo ƙafafun nasa da gangar jikin nasa waje, sunan ALLAH ɗauke a bakinsa, Wanda a daidai lokacin da gangar jikin sa ta ginu da wajen wurin, a daidai lokacin ne kuma zuciyarsa ta tsananta bugawa, wata sassanyan iska ce ta taho ta hadarin, wacce ke busawa ne ya saki fuskarsa, Wanda hakan ya sashi ɗan lumshe idanunsa, shi kuma wannan farin matashin na binsa da kallo sosai....
Cikin wani irin ƙarfin daya ziyarce shi lokaci guda ne ya sanya shi daidai tsaiwarsa cak, kan diga digansa yana jin wata iriyar nutsuwa na ratsa shi barin ma daidai wurin kalmar shahadar da akazo. fara tafiya yayi ma'aikatan hotels ɗin na binsa da lug bag nashi, shi kuma Cikin nutsuwa da kwarin gwiwwa ya fara bin kalmar shahadar, cikin ɗan sauri kuma yana bin bayan mutane biyun da ke ɗauke da kayansa, ta cikin wannan hanyar da flowers ɗin ke ajere suka bi, Wanda daga tsakiyar wajen wadatacciyar hanya ce,
Ahankali yakai ƙafarsa kan step na farkon hawa ƙofar wurin, taku ɗaya yayi ana biyun tare da ukun ya dakata yana me ambatar.
_Masha Allahu laƙuwwata Illah billah!!!" Sosai komai na hotel ɗin keda tsari na Muslunci da burgewa.
Cikin yanayi na ɗan gajiyawa ya ƙarasa gaban waɗannan ma'aikatan da suke, cike da mutuntaka da martabawa suka bashi hanya ya shiga cikin Lifter, kana suma suka shiga cikin minti biyar suka isa hawa na 12 inda nan ɗakin daya kaman yake. Ɗaya daga cikin ma'aikatan dake binsa ne ya buɗe masa ɗakin da kansa, kana ya shimfiɗa sabon bedsheets tare da blanket, kana ya wuce da sauran kayan kamarsu towel da bathrobe da makilin da brush duk sabbi,ya ajiyesu bathroom ɗin tare da feffesa Air freshner kana ya fito tare da wucewa.
cike da tsantsan gajiyawa ya zube woyoyinsa saman bed ɗin, yana mai shaƙar ƙamshin Roomfreshner ɗin tare da kallon tsarin komai na ɗakin, komai na cikin falon Ash & white colour ne mai masifar kyau kama daga Cottins carpet dama kujerun. Kamar sun san best color nashi kenan, Cike da gajiyawa ya faɗa bathroom al'wala yayi tare da fitowa da sassarfa ganin lokacin sallar na neman janye masa, dan har an shiga ma, Lifter yabi ya sauƙa kana kai tsaye masallacin dake farkon hotel ɗin ya shiga da sassarfa jin ana nemar kai raka'ar farko. Cikin wani irin nutsuwa da limamin masallacin yake rera karatun sallar, me tafe da wani irin yanayi na nutsuwa da kwantar da hankali. Ahankali jamaa suka fara fita shi kuma yana sake kutsa kansa cikin masjid ɗin, wurin alqur'ani me girma ya nufa, tare da ɗauka ya buɗe shafin farko, kansa a ƙasa ya bayan karanta fatiha ya shiga baƙara, ahankali yake rera karatun nasa, cikin ƙira'arsa me kyau, da burgewa. Tin da ya fara karatun farin dattijon limamin daya yunƙura da niyar miƙewa ya koma yana zama, sakamakon muryan da yaji na ratsa cikin kunnuwansa ahankali ahankali,ta wata daya taɓa sani a cikin rayuwarsa tsayin shekaru masu ɗan gwaɓi. Se yaji wani sanyi da nutsuwa na ratsa shi, so kawai yake yaga ainihin waye, sedai fuskar dake rufe da mask ya ɓoye hakan, gashi kuma surar daya ɗauko me zurfi ce, cikin wani irin yanayi ya miƙe ya fita yana jin kamar yayi missed wani muhimmun Abu ne anan cikin masjid ɗin, gashi yanayin ƙira'a da karatun mutumin yayi shige koma yace fitik da wanda ƙaninsa yake yi ne, kaf duniyar a wurin ƙaninsa kawai yake jin irin wannan ƙira'ar, daga yanayi na suturar jikinsa se fahimtar da kai cewar shi ɗin bafade ne, kodai wani me aiki a cikin fada... Shi kuwa AA tin yunƙurin mutumin na farko da kuma komawar da yay ya zaune yake ankare dashi, har yanda yaji idanuwansa na yawo akansa, har kuma fitarsa, karatun sa yaci gaba dayi har wajajen tara da rabi, daidai da lokacin da yakai ayar ƙarshe a surar, daidai da lokacin da wani matashin samrayi bazarate ke shigowa masjid ɗin kamar an wullo shi, shi kuma daidai da lokacin da AA ya yunƙura da niyyan tashi,
Saurin fito da Idanunsa waje yayi cike da tsananin son tabbatar da ganinsa ba gezau suke masa ba, ko kuwa dai ba gane gane idon nasa ya fara masa ba, da wani irin sauri ya miƙe tsaye ganin me irin fuskar nashi tsaff na shirin fita daga masallacin don harya kai ƙarshe ma. Sake Jan mask tare da shede na idonsa yay, yanda babu wanda zai iya ganin face nashi. Ya shiga bin wannan photocopy ɗin nashi da ɗan hanzari, cikin sauri yake binsa sedai wannan matashin mota ya shige, ɗan haka yayi hanzarin amsar car key na wata mota daga cikin hotels ɗin yabi bayansa. Har zuwa gaban ƙaton Emirates place ɗin masarautar UMMULYOODAH....
Kusan a tare motarsa data matashin samrayin suka kutsa kansu cikin masarautar,sedai tashin bata kai ga ƙarasa shiga ba jiga jigan kattan samudawan suka rufe get ɗin, don idan har mota bame ɗauke da tambarin masarautar ba, ba'a taɓa barinta shiga cikin fadar. Don haka yayi gaggawar fitowa tare da taɓa door bell na get ɗin, within 1 mins kuwa sega wani basamude sanye da uniform irin na masu aiki ya buɗe kofar tare da leƙowa da niyar kartama wanda ke tsayen rashin *M*... Sedai yana leƙowar daidai da lokacin da wata iska me bala'in ƙarfi ta ɗage mask tare da shede ɗin dake fuskar nashi, suna hade ido da AA ɗin ya wani irin tsayawa cak yana kallonsa jikinsa na ɗan girgizar tsoro me tafe da tashin hankali, kallonsa ya sake a karo na biyu cikin haɗiye wani yawu a fixge, daidai da lokacin da AA ɗin ya gama meda mask ɗin. Yana kallar inda mutumin yake, Wanda yayi saurin ɗauke idonsa a kallonsa yana bashi hanyar shiga, cikin sake ƙare masa kallon ruɗewa don ganin kamaninsa sak da *PRINCW SHAMEER*.
♡
Shi kuwa SHAMEER kai tsaye sashen Sarki AFUUD ya wuce, yana ratsa
katafaren Parlourn gidan ya wuce, Wanda ya gaji da haɗuwa me wani irin girma da tsaruwa daya gama jin duk wata alfarmar duniyar,ga wasu shegun royal chairs golden and red ɗin da suka ma ɗakin ƙawanya. Se wasu manyan labulaye da chandelliers suma golden colour sai baza kyalli suke, kana duk wani Abu daya kasance ya ƙawata Parlourn shima ya kasance golden nd red colour ɗin ne da wasu irin manyan turkish carpet, gefe guda kuma ga wasu manyan Airmores da incence burners kusan kowacce kusurwa, suna aikin bada daddaɗan ƙamshin turarruka na alfarma da kuma iska mai sanyi, wanda already sanyin dama ya gama kama Parlourn ta ko ta ina wata irin dukiyace ta musamman aka narka acikin Parlourn...... Babu kowa acikin Parlourn nasu na farko, wanda kuma kai tsaye shi ne zai sadaka da babban Parlourn na biyun, wanda ya kasance shi ne Parlourn da nan mutanen ɓangaren suke zaman meeting, kai tsaye ya sake ratsa dogon Parlourn SHAMEER yayi,yana nufar ƙofar da zai sada shi da ainihin Parlourn Sarki AFUUD ɗin na musamman, se dai yana isa dakaru masu tsaron ƙofar suka dakatar dashi, wanda ya sanya shi wani irin ɗago kansa, tare da auna musu wani mugun kallo me cike da gargaɗi, cikin takunsa me zafi irin na zaratan mazan dake ji da kansu yake takun, kai tsaye yana isa katafaren parlour na alfarmar da aka gama ƙure aidiya ta duk wata kwalliya a cikin parlour ɗin, komai na Parlourn black ne, gefe guda kuma ɓangaren dusty rose ne da wani irin cool black furnishings, wanda floor ɗin ya ɗauki wani irin shiru irin na mutuwar da wajen yay ne, ze baka tabbacin mazaunin wurin bame son kowacce irin kwarabniya bane, Yana zaune ƙafarsa ɗaya kan ɗaya a cikin wani dogon corridor crew na glass, wanda tin farkon shigowarsa ɓangaren ya sani, don haka kai tsaye ya ɗago kansa yana sauƙe ganin nasa akan ɗan yayansa *SARKI ASHFUD* A da......
Yana sanye cikin shiga ta alfarma wanda tuni shigar tay bajintarta na fallasa siffarsa na kyakkyawan namiji mai cikar zati,jarumtacce kuma mai cikar ƙirar halitta da dirarren siffar jiki. Kallon second yama SHAMEER ɗin yana saurin ɗauke ganinsa akansa, dan yanda kyau da kuma cikakken kwarjinin SHAMEER ɗin me girma da rikitarwa yake da shi, wanda sak yake irin na mahaifinsa, wanda hakan sau da dama shike kusan ruɗar dashi akan yaron,
Me ya tuna kuma se yay saurin daidaita kansa da natsuwarsa, tare da tattaro kansa duk wata nutsuwa da ginshira haɗi da ƙarfin izzarsa.
♡ A can bakin get kuwa,AA na sanyo ƙafarsa zuwa dandanin compound na sararin masarautar wata iska me ƙarfin gaske na tashi, me kama da guguwa, Wanda kuma acikin hakan ne aka sake sakin wata walƙiya mai masifar haske, irin walkiyar nan mai zuwa tamkar an watsa dogon bulala koko tafiyar maciji me tafe da rugugi wanda yafi kama da sauƙar aradu. Tuni iska me ƙarfin nan ta cukuwkuye katafanin compound ɗin, daidai ana sake sakin wata walƙiyar me masifar haske da tarsatsi, kafin wata iriyar tsawa mai masifar ƙarfi yabiyo bayansa, wanda ke fitar da sautin ruguginta da masifar ƙaraji da gigita dukkan bani adam. Wanda cikin wani irin masifar tsoro da gigitar daya dirarma AA farat ɗaya ne ya sanya shi furta.
"Hasbunallahu wani'imal wakil. Subhanal Lazi yusabbihul ra'adu bi hamdihi wal Mala'ikatu min hiyfatihi!!!" A take kuwa aka sake sakin wani walƙiyar haɗe da wata iriyar firgitacciyar tsawa mai masifar ƙara mai razana dan adam dasa hanjin mutum kaɗawa. Wanda gaba ɗaya ya amsa duka gidan dama duniyar, Cikin wani irin tsananin tsoro da masifar gigita ta duka mutanen dake fadar kowa ya shiga cakumar na kusa dashi, kowa gaba ɗaya ilahirin jikinsu na rawar wani irin tsoron daya kamasu lokaci guda, saboda hasken walƙiyar da ake tayi babu ƙaƙƙautawa, har yana tsaga wasu ƙofofin gilasan...
A can ɓangaren SARKI AFUD kuwa, wani irin bugawa yaji zuciyarsa tayi da masifar ƙarfi, yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ya ɗauki rawa, shuuuuuuu haka yaga kamar gilmawar abu ta cikin idanunsa, daidai tsawan na tsayawa wanda ya sanya shi saurin dubar inda SHAMEER ke tsaye, sedai wayammmm. Ya yunƙura da niyar yayi magana kenan wani irin tsawar ya sake sauƙa mai masifar rugugi.
A take jikinsa ya shiga wani irin masifaffen tsuma, saboda tsananin tsoron daya dirar masa na lokaci guda, jikinsa har na ɗaukar kamar ɗumi ɗumi me tafe da zazzafan zazzaɓi.
♡
AA baki ɗaya jikinsa be dena tsumar da yake ba, gashi jikin again se wata rawa yake kar³ haka jikinsa ke rawa yayin da baki ɗaya tsikar jikinsa suka gama miƙewa, tin daga tsaƙiyar kansa har zuwa babban yatsan ƙafarsa, ga zuciyarsa dake wani irin buga masa wanda ya sauƙar masa da wani azababben ciwon kan nan take.
Akuma lokacin aka sake sakin wata tsawa da walƙiyar, Wanda ya sanya shi riƙe kansa yana me furta.
"Hasbunallahu wani'imal wakin, Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n, La'ilaha Illah anta's subhanaka Inni kuntu Minal zhalimin, Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha!!!..." Daidai da kai ƙarshen adda'an nasa daidai da lokacin da kece da wani irin ruwa me masifar ƙarajin daya sauƙa da bala'in ƙarfin tashin hankali. A kuma daidai lokacin ne ya faɗo ainihin compound ɗin tamkar wanda aka jefo, ya fara zagayawa domin jinsa yakeyi tamkar ana tafiya dashi ne a cikin sararin samaniya bisa gajimare.....
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 23