Share this page
yen maciya amana!, maƙaryata, Maha'inta ne su na gaban kwatance, A dukkanin kafatanin rayuwa kuma babu abinda yakai ciwo irin cin amana ha'inci ko yaudara daga wajen wanda ka miƙama dukan yarda amincincinka daga ƙarshe yaci amanar ka tamkar yadda Abban su nuwaira yaci nata amanar, wanda a maimakon ka samu ninkin abinda ka bayar ɗin, ko kuwa ka samu koda ace kwatankwacinsa ne, a'ah sai ka samu akasin dukkannin abinda kai ɗin ka miƙa, tabbas ba kowanne yanayi muke fahimta ba.har sai lokacin da muka samu kanmu a kwatankwacin irin hali ko yana yin kwarai da gaske. Tana zaune ta wulla cikin duniyar wannan tunanin har ma bata san lokacin daya birbira sallar saba yana bar mata ɗakin daya kasance mallakinsa ne. Dama sallar asuba ta shigo tashin sa dake itace dashi, duk kwanan duniya in dai a ɗakinta yake seta shigo tashin sa sallar asubahi ɗin, se dai in a ɗakin su Husna yake tin da har ita me jiddan da take Ƴar uwa ga husnan ya jima da maida kamar matar da ya biya sadaki ya aura. Tabbas shigowar Husna cikin rayuwar auren ta da Auwal jaraba wace, kuma ƙaddara me tafe da wani irin ƙalubale me wuyar a fahimta, wani irin riƙe kanta da hannuwanta biyu tayi tuno wasu daga cikin munanan kalamansa gareta, yace shi yanzu ba zaman sa take yi ba, zaman iyaye da ƴaƴanta take yi, wannan ya faru ne lokacin da yace ta tafi gidansu ze ne mata akan ta faɗa masa gaskiyar ya gyara halayensa, da mahaifiyarsa tace maza yaje ya dawo da ita, kuma idan ya sake saɓama uwar gidansa akan wannan murjanatun matar tasa me kama da buhun kwaki se ta ci mutumcinsa buɗar bakin sa me ko ji nauyin mahaifiyar nasa ba yace da ita. _Shi fa a dena shiga sabgarsa da husna, don ko wuta zata cinna masa shi bazai taɓa ganin laifin taba, ko da ace namar jikin sa zata sanya wuƙa tana yanka_ don ALLAH kai da jin wannan kalami ai ka san an goce hanya ɗoɗar ma kuwa. Shi yasa take shanye duk wasu baƙin ciki da ɓacin ranta iyaka ita kaɗai ɗin ta. Se dai kullum bata gushewa wurin miƙawa ALLAH kukan ta kan ya kawo mata mafita ko ƙarshen wannan tashin hankalin. Ɗakin ta ta nufa kai tsaye tana ƙoƙarin danne mikin dake son taso mata. Tana shiga ɗakin ta zauna bakin bed nata wasu mugwayen ruwan hawayen data ta roƙon ALLAH zuwan su ne suka sama damar ɓalle mata. Wannan ƙaddarar har ina?, anya kuwa lokacin beyi nisa da tsayi ba?, shin dama haka auren ya ke, wasu iyayen gidan su ne da gidan, wasu kuwa amaren su ne da gidan, yayin da wasu suke kasancewa tsaka tsakiya, kowa befi kowa iko da mulki ba. Inda wasu kuma lafiya lau suke zaune da abokayen zamansu lafiya, sedai basu da yawa ba masu yawa bane irin masu zaman takewarsu sunfi yawa. Tsoron ALLAH a gun wasu matan yayi Ƙaranci. A bayyane ta shiga furta "Hasbiyal-lahu la ilaha illa huwa, Alayhi tawakkaltu, wahuwa rabbul-Arshil-Azeem. Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir³ Rabbi inni magalubun fantasir³ la haula wala quwwati illa billahil aliyal azeem³, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ³" haka ta shiga ambata tare da sauran tare da nanatawa. Ajiyar zuciya me sanyi ta sauƙe a natse tanajin hankalinta na dawowa jikinta take taji ɗacin zuciyarta ya ragu sbd yadda adda'o'in data karanto ɗin suka ratsata sosai tare da zuciyarta. Daga nan ta shiga shi din dimun yaran ta don tafiya school. ♡ *CAPTAIN AA* A hankali yake juya steering motar kamar baya so. Yayinda gaba ɗayan hankalinsa da tunaninsa ke kan nazarin Nufaisah, Shin murna ya kamaci ace yayi ko kuwa yaya?. A yanzun wannan fitowar nashi da zai yi ya jita tana waya da wata ƙawarta kan cewar ita fa ta gama yanke shawara kawai zata bama Mohan Khaleel damar auren ta kawai. Gaba ɗaya juya maganar nata ya ke yi a cikin ransa, yana jin tamkar ba haka bane, tamkar wani abu baya tafiya daidai a cikin tafiyar. Gaba ɗaya ya shagaltu da tarin wannan cukurkuɗaɗɗun abubuwan, gaba ɗaya ma ya rasa wanne tunani ya kamaci ace yayi akan komai dake gudana a cikin rayuwar su. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, Yayinda abubuwa masu yawa ke ci gaba da masa kaikawo a cikin rai da ruhinsa, ganin hakan yake tamkar sun faru sun wuce ne a cikin a cikin wata duniya ta daban. Haka har ya kawo wurin aikin sa, directly babban office nashi ya nufa yana kaiwa zaune saman lafiyayyar kujerar office ɗin nashi, tare dama PA nashi gargaɗin baya buƙatar kowa ya shigo masa office. Tin daya shiga office ɗin be fito ba duk kuwa da uban aiken da kanal Musa Bappa babayo yake masa akan yazo PA ɗin yaƙi barin kowa ya shiga, har lokacin sallar zuhr yayi. Se bayan daya dawo PA as parsonal parson ɗin sa ke sanar dashi maganar ƙiran da ake masa, don haka kai tsaye ya nufa babban offishin Kanal Musa bappa babayo ɗin. Yana zaune tarin file gabansa da duk kan alamu ma bai ko fita sallar ba. Yana jin sallamar Captain AA ɗin yay saurin cusa takaddun dake gabansa cikin loka na teburin dake gabansa, wanda kyal idon sa me kama da mayen ƙarfe harya kyallaro masa musa sunan Taj Mustapha Al_Mustapha'n dake rubuce jikin file ɗin, wato wannan babban Criminal ɗin daya gama gagarar ƙasar gaba ɗaya. Sara masa yayi tare da kamewa daga inda yake tsayen. Cikin matsewar fuska kanal ɗin ya turo masa wasu file har guda biyu tare da furta. "Ko wanne irin aiki gareka ka jingine shi gefe, ina son ka samo min baganai a kan masu waɗan nan file ɗin" yakai ƙarshen maganar yana tura masa file ɗin da ta farko take ɗauke da sunan green snake da manyan baƙaƙe. Sake sara masa yayi tare da ɗibar file ɗin yana ficewa a office ɗin. ♡ Yamma ci ne mai daɗi dake tafe da sassanyar iska mai cike da tsananin daɗi, da kuma sanya shauƙi da nishaɗi ke busa wa, wanda a dai dai wannan lokacin, cikin ƙawataccen gidan abincin dake wannan haɗaɗɗiyar anguwar ta Bombila Barracks, Nufaisa ke zaune tare babbar aminiyarta Najma don ta wuce ƙawa a wurin ta suke zaune, Sosai wurin ya kasance na musamman ko dan yadda aka ƙawata wajen da wani irin tsari mai ban sha'awa da burgewa kwarai. kwatankwacin yadda zai ja hankalin abokan kasuwanci harma yasa suji basu ƙagara ko gajiyawa da zuwa kashe yunwa da ƙishirwarsu zuwa wajen ba. Inda ita kaɗaice zaune saman kujerun dake zagaye da teburan dake jere a wajen bisa tsari na rukuni rukuni, inda daga hannun damanta ta bayanta kenan Najma ɗin itama ke zaune, suna jiran isowan Mohan, duk kuwa da cewar yadda gabanta ke mata dukan tara tara. Tana jin kamar ba daida bane zata aikata amma wata zuciyar tana dannarta akan tabbas hukuncin data zaɓarma kanta shi ne daidai. Inda wannan kyakkyawar fara sol ɗin fuskar nata ke cikin yanayi na ba yabo ba fallasa. Inda tsananin kyaun daya gama cakuɗuwa da tsantsar kulawa tsafta da kuma hutun da take a ciki, A natse ta ware oily eyes nata da kai tsaye ba zaka ce suna da girma ba har sai idan taso fidda girman nasu ne gaba ɗaya tamkar dai yanzun. Kafin a hankali ta shiga motsa siraran laɓɓanta masu kalar pink da suka dace da taswirar tsai war hancinta mai tsaho da tudu wanda ya haɗe da kwantacciyar eyebrows ɗin ta dake bisa tsari kamar an zanta. Wanda dukkan alamu suka gama nuna cewar magana ce take son yi amma kuma bakinta ya mata nauyi wajen kin bata haɗin kai wajen furta ko menene take son furta war kuwa. Hakan ya sanya ta meda idanunta tana lumshe wa, inda take sanye cikin wata Turkish kimono ash color, data mata wani irin mugun kyau bana wasa ba, inda ta yane kanta da madaidaicin mayafin a bayar, sai hakan ya sake bama kwantaccen gashin daya kwanta daga gaban goshinta damar fitowa tsaf,wanda duk bayan minti ɗaya zuwa biyu take sanya zara zara yatsun hannunta tana jan mayafin da kyau tana sake rufe gaban kanta da kyau. Ƙafafunta kuwa na sanye cikin wasu lafiyayyun plate shoes wanda suke mahaɗin ƙaramar handbag ɗin dake gaban ta na companyn Christian sadly. Cikin wani irin coolness take latsa haɗaɗɗar wayar ta dake riƙe a hannun ta, inda gaba ɗaya zaman wurin ya fara isar ta har tana jin yanda ranta yazo mata iya wuya, domin jira yana ɗaya daga cikin abin da tafi tsana a cikin rayuwar ta fiye da komai. Har zuwa lokacin kuwa wuri ɗaya idanuwanta suke kalla ba tare data barsu sun gusa daga kallon hanyar shiga da ficen cikin restaurant ɗin ba. Har lokacin da idanunta suka sauƙa akan Mohan ɗin dake tinkaro wurin cikin Ƴar tafiyar sassarfa, da duk kan alamu shi ma bai ji da ɗin wannan late ɗin da yay ba, "I'm very sorry Nufy🙏." ya furta yana me haɗe hannuwansa wuri guda alamar tuba yake, ganin irin yanayin kamar ƴar fusatar data wanzu saman kyakkyawar innocent face nata. "Have a seat" ta faɗi a takaice ta ɗan kawar da yanayin damuwar dake face nata, tare da tsareshi da kaifafan idanuwanta na wasu ƴan sakanni. "Sweet dreams....." yay hanzarin ƙiran sunan ta domin idan tana masa irin wannan tsarewar gaba ɗaya rike cewa yake ya diburburce, kansa ya langwaɓar gefe guda yana tallafar haɓarsa da hannun sa ɗaya yana me furta. "Kiyi haƙuri ki daina min irin wannan kallon haka,gaba ɗaya sani suke in daburce, first ki fara da min kyakkyawar albishir ɗin da kika ce zakimin!!!" ya ƙarasa kai maganar nashi cike da ɗoki. Yi tayi kamar bata ji shi ba, kamar kuma ba tayi maganar ba, tamkar kuma ta fasa faɗin masa abin da ke ran nata data gama yanke wa, amma data tuna irin girman halakar da zuciyar ta ke son jefa ta se tayi hanzarin dubarshi. Cikin yanayi na ba yabo ba fallasa ta furta. "Ina son iyaye su shiga cikin maganar, don ina son muyi aure" ta kai ƙarshen maganar tana juyar da kanta gefe wasu ruwan hawayen da bata san ko na miye ba na shirin tarin mata. "Da gaske? Don ALLAH da gaske mafarkina!, kar ki ce da wasa ne kiyi hakuri kimin wannan alfarmar ki bani wannan damar pls My dreams." yayi maganar yana miƙewa tsaye tare da zagawa ta inda ta juyar da kan nata, yana kaiwa tsugunne gabanta tare da furta. "Kuka kuma? Kamar fa ruwan hawayene cikin idawanki, wacce ya kamaci ace ba wannan nake gani ba tsantsan farin ciki ya kamaci ace na gani kwance saman wannan kyakkyawar fuskar ba akasin hakan ba." yayi maganar da niyar shafo hawayen daya sama damar zubo saƙƙo mata, saurin kawar da kanta tayi tare da miƙewa tana surar handbag nata tare da phone nata, tana me furta." Idan ka tsaya wasa a kowanne lokaci zan iya san ja shawara akan hakan" daga haka ta kama hannun najma da tin farkon miƙewar nata itama ta miƙe suna fita kai tsaye daga wurin suna nufar wurin da motar su ke fake. Najma ɗin ce ta amshi driving ɗin ganin yanayin aminiyar nata kai tsaye suna nufar gida. Bayan komawarsu gida tin da najma ɗin ta tafi bata ko sake leƙo parlourn ƙasa, da yamma ma har ɗaki Ammey tasa aka bita da dinner nata. Se a yanzu da Ammeyn da kanta ta shigo ƙiran ta kan ta fito dinner kuma Bappansu yana son magana da ita. Tin da taji ta ambaci bappan na son magana da ita gabanta ya faɗi. Amma tana danne hakan tare da watsa ruwa tana saka sauƙaƙan kaya masu rangwamen nauyi ta fito zuwa dining parlour area ɗin. Tana zama babu jimawa mayen ƙamshin sa ya sanar da ita fitowar nasa. Inda cikin nutsuwa da kuma kwarjinin da ALLAH ya masa ya kutso kansa cikin parlour'n cike da wani irin majestic takunsa. Tinda ya tinkaro parlour'n taji numfashinta na fita da sauri bugun zuciyarta na ƙaruwa ahankali idanuwanta na kasa ɗaukewa daga kansa, Wannan nutsatstsen ƙamshin nasa mai sanyin daɗi da kai tsaye yake tabbatar da tsadarsa a shaƙa ɗaya na gwamewa da sanyin ac/n daya taho da ƙamshin nasa kai tsaye yana shige mata hanci, yana sauya numfashin main babban palourn gaba ɗaya da kamshinsa. Sake buɗe kyawawan idanuwanta a kanshi tayi tana kallo tin daga fararen yatsun ƙafarsa da suke wani irin fes kaman baya fita dasu sanye cikin versace slippers. Yana sanye cikin shigar lallausan fararen riga da wando masu kyau da tsada, fuskansa da take wani irin fresh na sake shining, hannuwansa dake cikin aljihun wandon dake jikinsa ya zare. Cikin sakewan fuska dake tafe da girmamawa ya furta. "Ammey Naaaa barka da dare" dake tare suka shigo da bappa daga masjid, Yana zaunawa bayan yama inda take zaune kallo ɗaya yana ɗauke idanuwansa akanta, sakamakon raight jeans ɗin daya lafe jikinta da white Cardigan ɗin dake jikinta masu sauƙin nauyi. Janye nata idanuwan itama tayi ahankali tana ƙoƙarin danne ganinsan da tay. Wani numfashi me ɗan nauyi ta haɗiye tare da danne ruɗewanta tana sanya dogayen yatsun hannunta farare tana kare fuskanta. Shi kuwa duk da yacce zuciyan sa ke sake ingiza shi akan sake kallon nata amma samm ya ƙiyama hakan. "Barka da dare loll...... Se kuma ta gaza ƙarasa lolly ɗin da take ƙiran sa dashi. Inda kowa be kawo komai ba se shi kaɗai da ya san me hakan ke nufi, da kai ya amsa mata yana janye idanunsa daga kanta. Nata idanun taja tana lumshewa ita kuma tana ɗaukan hanyar barin parlour'n. "Maganar iyayen Yaron da kika turo fa" haka ta tsinkayi muryan bappanta, wanda ya sanya ta kusan cin tintiɓe sedai kan ta kai ƙasan taji anyi saurin taro ta, yana tsayar da ita kan diga diganta. A wani kalan nitse ta ɗago kanta tare da sauƙe ganinta a kansa da yake riƙe da hannuwanta, kyakkyawar fuskar nan a ɗin ke tsaf tamkar wanda bai taɓa sanin ko inda fara'a take ba bare kuma dariya. "Kin shirya zaman aure da manemin mata ba?" yayi maganan yana ɗauke kansa tamkar irin sannun nan ya mata yana raɓata a koma cikin parlourn. Ita kuma tana ɗiba a guje ta wuce samar ta inda gaba ɗaya su duka ukun suka bi bayan ta da kallo. dole bappan ya kyale ta zuwa safe sayi maganar don shi ma a ɗazun bayan salla zuhr bappopin yaron suka same shi da zancen. Shi ne ya fara tashi a wurin yana barin iyayen nasu zaune su biyun, wanda dama spece ɗin hakan suke da buƙata. Ammey ce ta fara dubar mijin nata tare da furta. " Anya kuwa ba babban kuskure muke shirin aikatawa ba QASIM HABEEB?, Shin kai baka lura da makahon SO da ƘAUNAR da Nufaisa ke ma Aliyu, taya zaka zaɓi sadaukar da farin cikin Ƴar da ka haifa ta cikin ka akan wani daban!" tayi maganar wani hawaye na zubo mata. Wani irin juyowa gareta a fusace mijin nata daya da yau ɗaya naji ya tashi daga ABDULLAHI zuwa QASIM. namomin jikin sa har wani rawa yake wajen furta."KAMAALA JIKAN KAMAALA ƊAN ASHFUDDEEN DAWOOD RAHEEM KAMAALA ɗin ne wani daban a wurina JUNAYNAH?, Shin kafin na yarda ki biyo ni na aure ki a wancan lokacin ba seda na baki sharaɗi akan hakan ba?, Lokacin bayyanuwar gaskiyar ne be yi ba, da saurin lokacin har yanzu. Maganar su kuma ki bar musu kayar su idan ALLAH ya nufa NUFAISA MATAR KAMAALA CE dole zai aure ta, zata aure shi....... " Daga haka ya miƙe shima yana barin parlour'n gaba ɗaya bayan ya gama buga mata worning akan idan har magana me kama da makamancin hakan ya sake faruwa zeyi mummunar saɓa mata.... # NUFAISAH* Tana isa bedroom nata ta zube saman lafayayyen gadonta tayi, lumsansun idanunta na'a lumshe wanda suka canja launi na zubar ruwan hawayen da suka tara, abubuwa da dama sun haɗu sun mata yawa a kwakwalwarta. buɗe idanunta ta yi tana mai furzar da iskan bakinta haɗe da yamusta fuskanta, zuciyarta na kamar zata ɓallo rufin fata bakwai ɗin dake taaƙiyar ƙirjin nata ta fito, lumshe idanun ta yi ta shiga karanto addu'ar samun nutsuwa da kwanciyar hankali a cikin zuciyarta. amma dake ance so jarabta ne so masifa ne, duk yacce ta kai ga munana hakan da ɓatawa amma hakan yaƙi tasirin tuwa a cikin brain nata, Innalillahi ta shiga natatawa tana jin tamkar ana mata dakan ɗaka ne a cikin tsaƙiyar ƙirjinta. Wani kuka ne ya kufce mata me ƙarfi tana saurin sanya hannuwanta ta toshe bakinta, tare da ambatar. _"Allahmma inni as'lukas sabbas fil amr, wal azimatu alar rushdi, wa as'aluka shukra ni'matika wa husna ibdatika,wa as'aluka kalban saliman wa lisaanan sadiƙan, wa as'aluka min khairi ma ta'alam wa a'uzubika min sharri ma ta'lam wa astgfruka lima ta'lam innaka anta allumul gayub"_ Tana me sake rushewa da wani sabon kukan daya sake ɓalle mata tana furta. "I LOVE YOU SO MUCH LOLLY, AND I HATE I My HEART" _To fa shin masu karatu sun fara gane tafiyar?, ko dai har zuwa yanzun kan a duhu yake? _ ★ Wannan fa shi ake ƙira da ana wata ga wata. _Taya wai ma aka samu sauyin yanayi irin haka ne ne?, me wannan tsohon yake nufi da mune?, kuma wacce gaskiya ce lokacin bayyanuwarta be yiba?_ _Duk yacce aka yi akwai wata kulla kullar a ƙasa da dukkan alamu_ _To ni dai AMMEYNKU LAYLERH nace muje zuwa kawai yanzu ne zamu sa kau cikin tushen labarin. *Karfa ku manta akwai fa rikita rikita da yawa a cikin wannan littafi namu na RAMIN KURA, fatar baku manta mana da ɗayan jarumin mu Acp Maleek a gefe ba?, kana ita kanta Hannah, again ga kuma labarin JAN GIDA, Inda labarin ZAINAB wacce muka fi sani da MAMAN NUWAIRAH ke can shima yana jiran mu. Kun ga kenan tafiyar akwai 🔥 🔥 🔥 🔥 🔥 🔥 🔥 🔥 🔥 fire kenan? * _Kun shirya bin wannan alƙalamin ko kuwa dai da saura?, rikita rikitar tana da yawa gaskiya, dan sena rikitar daku fiye da MIKIYA, Sena gindayar daku fiye da littafin TA DABAN, Sena baku mamaki fiye da littafin DUNIYARMU, Se kuma na Nishaɗantar daku fiye da littafin SO DAN RAYUWA, kana sena raba hankulanku fiye da littafin KAREN BANA, In kuma Saku Nishaɗi fiye da littafin JALAAL AREEF, In sanya ƙwaƙwalenku ɗaukar ɗumi fiye da littafin ƘAUNA BIYU. In kuma baku tausayi fiye da littafin DUHU na DUKAN duhu, ya kuke tunanin tafiyar zata kaya?...... _ ♡ 08104493215 Hhhhhhhhhh to ai shikenan 😅🥰 A gimtse 🫰 🙃♥️✅ *BY AMMEY LAYLERH ✍️ ✅* ༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻ # 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Book One paid ♡ Page 17&18 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. # HE WILL FIGHT *Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank* ♡♡♡♡♡♡♡♡ ꨄ Tin da bappa ya shige bedroom nashi aikin safa da marwa kawai yake yi, hannuwansa goye a gadon bayan sa mikin baya can da jimawa na taso masa, da ƙarfi ya sanya hannunsa yana dakar madubin ɗakin sa take ya tarwatse kuwa. Sakamakon tinu yanda ya lumawa SHUGABANSA me ADALCI SARKI ASHFUD RAHIM ƙahon da yayi, yana fasa zuciyar sa gida biyu da yayi. "Bani bane, ina bani bane A ahhhh ba ni bane ba zanyi haka ba!, don me zanyi haka" maganar yake yana fatali da duka kayyakin dake shirye tsaf saman mirror'n. Haka Ammey ta shigo ta same shi, hakuri ta bashi sosai tana tattara wurin daya ɓata bayan ta zaunar dashi daga gefen bed tana sake tausarshi. ☆ AA kuwa tin da ya shige cikin Master bedroom nashi ya kai kwance kan tsakiyar Raoun bed nashi, me tsananin laushin da kai tsaye idan mutum ya kwanta yake yin luf ya lafe cikin bed ɗin yake kwance. Lafiyayyen bedroom ne na musamman wanda kana sanya ƙafarka kuwa a cikin parlour'n abu na farko da zai fara maka maraba, Shi ne sassanyan ƙamshin turaren da humidifier ke bayarwa me haɗe da ƙamshinsa, gaba ɗaya kansa ya gama ɗaukar ɗumi da abin da ke famar addabar rayuwar sa a kanta. "Tabbas akwai LAUJE CIKIN NAƊI, akwai abin da yake tafiya ba daidai ba a cikin rayuwar mu....." ya furta yana miƙewa tsaye tare zare kayan dake jikin sa, wannan lafiyayyar farar fatar na bayyana tana ɗaukan ido, saboda samun hutu da tsadaddiyar gyara da original skin products masu tsada da kyau da yake amfani dasu. Kai tsaye bathroom ya faɗa tare da sa karma kansa shower yana lumshe idanuwansa ruwan na sauƙa akan fuskansa suna ganganrawa jikinsa suna sanyaya jikinsa a hankali. Ya jima sosai sosai a ruwan yana wankan, kafin ya fito ɗaure da babban towel me ɗan kauri brown, jikinsa na fidda ƙamshin shower Soap ɗinsa na Ocean seaweed. Hannun sa ɗaya na riƙe da wani mini clean blue towel ɗin daban yana tsane jikinsa a natse. Agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya kalla, wanda gargasa ke kwance luf luf gwanin birge wa abin ta. Ganin se yanzu ne ma sha ɗaya ke cika ya sanya shi fitowa zuwa control room nashi, inda ya fito a natse shirye tsab zuwa ainihin control room ɗin nasa, wanda yake nan neat ba hayaniyar komai a room don kuwa komai is so gentle unique simple and luxuries ne kawai, se zallar wasu mahaukatan cameras da kusan su ne ɗakin dama. Zaune yakai kan wata arniyar ɗunƙulalliyar kujera yana fesar da hucin numfashi, Wasu ɓoyayyun ayyuka ya gudanar, kafin kuma ya dawo bedroom nashi tare da ɗaukar iPad nashi yana tarin saƙonnin da aka turo masa ta cikin Gmail nashi. Anan yaci karo da bayanan da ya bada cikin sirri a duba masa dan gane da case ɗin dake hannunsa na ƴan ta'addar nan. Idanunsa yaja yana lumshewa ɓacin ran da ke ƙoƙarin taso masa yana ƙoƙarin maidasa da ƙarfin bala'i. Sedai ina hakan ya gagara. Tsaye ya miƙe babu riga a jikin sa se iyaka farin dogon wandon baccin dake jikin sa. Yanda ya zauna shiru ya dafe kansa da hannayensa kai zaka ɗauka ciwo yake masa ne ma. Amma sam ba haka bane Abubuwane kawai suke neman birki ta brain nashi, dan gane da yanayin aikin nasa, duk da kasancewar ba yau bane ya fara cin karo da matsaloli da ƙalubalen wurin aiki ba, domin zai iya cewa kusan a haka ya rayu, Amma na yau ɗin sai yafi koda yaushe ƙona zuciyar sa fiye da sauran, domin kuwa waɗan nan ɗin duk sun zo masa a bazata ne. Hakan na nufin ya sakankance da yawa kenan?, Sannan dole ne ya sake shiri in har yana buƙatar abubuwa su tafi masa a yanda

Chapter 8 of 23