yawa akansa.
Domin shi Captain AA ba cikakken mutum ne kamar kowa ba, duba da murɗaɗɗen mutun ne shi wanda baka taɓa gane gaban sa bare bayan sa, kullun cikin gindayar da mutane yake, sai ka rasa ma ina ya dosa kwata kwata. Idanunsa yaja yana lumshe wa a cikin zuciyar yana me furta. _Wuta ta ruru bayan tumu, tabbas babu wanda ya isa yama ɗan doya rumfa ubansa be noma ba_
Kafin kuma wani shegen murmushi ya subce masa aransa yake hasko wutar bal balalin masifar da zata kunnooooo......
Hhhhhhhhhh Ni kuwa AMMEY LAYLERH nace to ai shikenan🤗 😅🥰 A gimtse 🫰 🙃♥️
_Domin ni ban san asalin wannan karin Maganar na mahaifin Captain AA ba..... _
08104493215
*BY AMMEY LAYLERH ✍️ *
༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻
# 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Book One paid
♡
Page 11&12
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
# Be a Person
# Who Was?
# Money in Pocket
# Power In rocket
# Knowledge in Mind
# Kindness in heart
# Confidence on face
# Responsibility in Soul
# Love Romance scene
# A.k.a Ammey Laylerh
♡♡♡♡♡♡♡♡
Hannuwansa goye a bayansa yabar wurin, inda se a sannan ne Captain AA ɗin ya ɗago da kansa yana bin bayan mahaifin nasa da kallo. "WUTA TA RURU BAYAN TUMU?, BABU WANDA YA ISA YAMA ƊAN DOYA RUMFA UBANSA BE NOMA BA?" ya furta saman lips nashi yana dasama juyayyun kalaman mahaifin nasa alamar tambaya. Be wani jima a wurin ba ya tashi kai tsaye yana nufar samansa tare da kaiwa zaune daga gefen bed nashi, tare da janyo system nashi me yayi wasu ƴan rubuce rubuce, engine machine ɗin sa ya jona tare da jan glass cup yana siyanyar coffee tare da fara dan sipping nashi a Ahankali, kana ya shiga wasu ƴan sarrafe sarrafe kafin ya janye ta kai tsaye kuma yana nufar. _CCTV CONTROL ROOM_ nashi again, inda zuwa loƙacin gidan ya ɗauka wani irin shiru, babu motsin komai sai ƙamshin flower's ɗin dake ratsa ko ina na gidan. Don haka ya fara gudanar da bincikensa tamkar yanda ya saba.☆ ★★★ Ko a washe garin ranar ma sosai yasha barcin sa mai rai da lafiya a safiyar ta yau. kasancewar a daren jiya ya jima bai kwanta ba. domin ya raba dare ne yana gudanar da aikinsa. Don ko sallar asuba ma daƙyar ya fita masjid dake cikin anguwar yayo, Ahankali ya soma buɗe lumsassun Idanunsa da har yanzu suke cike da barci, santala santalan fararen sawayensa ya fara zubowa kan tattausan carpet ɗin dake gabansa. A nutse kuma ya miƙe yana nufar haɗaɗɗen bathroom nashi, shower ya sakamar kansa sosai ruwan ya dake shi, kana ya tara ruwa masu ɗumi da daɗin ƙamshi a cikin bathtub ɗin, Yaja tsahon loƙaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe sky Colour mai azabar taushin tsiya
dan har wani maski-maski take yi tsabar taushi da kuma laushinta,hannun sa ɗaya kuma na ɗauke ne da mini towel yana tsane jiƙaƙƙiyar tulin sumar dake kansa mai tsaho, Fuskar nan a tsuƙe Samm babu alamun rahama a cikinta.
Gaban ƙaton mirror'nsa ya nufa cikin tafiyar jin kai da kuma isa.
Hand dryer dake saman mirror ɗin sabuwa fil ya ɗauka ya jona a socket, ya shiga busar da himilin sumarsa da tafi kama data ƴan ƴaƴan larabawa, lotions ɗin dake jere saman mirror'n nashi ya shiga shafa wa jikinsa sama sama. Saida ya mulke jikinsa da spray's nashi masu azabar ƙamshi da tsada, kafin ya nufa gaban wardrobe nashi data kusan cinye bango guda.
Tsabbb yayi shirinsa cikin wasu cikakkar shigar sa ta kakin sojoji, sai glass ɗin daya sakaye idanunsa a ciki tare da facemask ƴar gadon, phone's nashi kaɗai ya ɗiba yana nufar main Parlour, cikin takun cikakkun mazan dake ji da kansu. Dake ya ɗan makara shi yasa be tarar da Nufaisa ba harta fita wurin nata aikin. Se iyaka iyayensa, kai tsaye lafiyayyen abincin da Ammeyn sa ta masa ya zauna yaci, inda daga nan ya musu sallama suna bin shi da addu'ar ALLAH ya tsare....
♡
*JAN GIDA*
A bayyane sunan wannan family
house ɗin jan gida, amma a taiƙace da baƙin gida ya kamaci da aƙira shi koma zarce haka, domin kuwa wata iri yar badaƙalar rayuwar da ake tabkawa a cikin sa, yayi yawan da baki ba zai iya furta shi ba, Wannan gidan maɗaukar babban zunubi ne a taƙaice. Wata iri yar rayuwa ake gabatarwa a hagumce a cikin wannan gida, domin kuwa a neman duniya babu mazan babu matan, kowa na gidan yana da nasa ɓangaren labarin. Cin amana iya cin amana, zanba cikin aminci, soyayyar ƙarya, Hassada mugunta duka babu abin da babu, yin alkharin ƙarya dan gani a yaba ace kafi wane sakakken hanu, su kuma waɗanda ake ma ɗin idan suka ja baya basa da abin zagi sai shi wannan me kyautata musun, shi a son shi dole a ce shi ne gwani kuma yafi kowa. Yes hakan ta samu harma fiye da yadda yake son ɗin, inda a takaice zamu taɓo ko ina daga cikin labarin....
☆ Zaune take ta haɗe kanta da gwiwwarta,idanunta sunyi wani irin jajir ɗin kaiwa maƙura a tashin hankali da ɓacin rai, daga inda take cakuyen take me roƙon ALLAH inama ya bata damar fashewa da gursheshen kuka. Se dai tayi duk yacce za ta yi amma ina kukan nan yaƙi iyuwa ya, tabbas se a yau take sake yarda wani kukan ma rahama ne, lallai ta sake yarda da zancen nan na mutane da suke cewa idan baƙin ciki yay baƙin ciki kukan baya taɓa yiwuwa, Shin me rayuwa take nufi da ita, a duk sanda take cikin irin wannan halin se take ganin ko dai ALLAH manta wa ya ke yi da ita. Ko kuma a ranta ta ringa tunanin ita kuwa wanne irin laifi ta aikatawa ALLAH da kullum wayewar yake sake jarrabarta da wasu sabbin ƙaddarorin, masu nauyi irin masu sa mutum ɗin nan ya faɗi farat ɗaya ba tare da anfarga ba. Tunani take yi shin ina wannan tarin mahaukaciyar soyayyar da Auwal ke mata?, tunani ta ke yi akan cewar shin dama wai da gaske wasu mazan idan sun ƙara aure matarsu ta gida tashi take yi a aiki?, ko kuwa dai ita kaɗai ɗin ta ce ta tashi a nata aikin a wurin Auwal?... Aysha ce da tin ɗazun take tsaye a kanta ta sake Ambatar sunanta a karo na ba adadi "Maman Nuwairah!!!" ta sake ambata da ɗan ƙarfi wanda ya sanya ta ɗago jajayen rinannun idanunta tana zubawa akan Aysha ɗin dake tsaye kanta.
"Se hakuri da rayuwa Maman Nuwaira kici gaba da hakuri, komai yay farko yana da ƙarshensa tabbas,kuma IN SHA ALLAHU kina zaune se ALLAH ya saka miki duk waɗan nan tarin abubuwan da ake miki....." itama tayi maganar cikin ɗacin murya sosai. A natse ta ɗago kanta cikin ƙaryewar murya ta ce. "Ba rayuwata ba! rayuwar Ƴaƴana Aysha, makomarsu, makomarsu nake ji, tsoro nake!, tsoro nake ji kar laifin da ba nasu ba ya hau kansu, tsoro nake ji a cikin raina wannan badaƙalar tayi munin da nake jin tamkar zata rabani da numfashi na, agaban idon mu nida ya rana Mai jiddah zata haye saman benen auwal da sunan gyara zata masa ko dai zata gai dashi. Shi a tunaninsa babu uban da ze gano kome yake aykatawa da yarinyar, connecting wayar ta da nashi fa yayi!, duk saurayin da ze wurin ta daga yace maye ne se yace ai wannan zubin ƴan daudu gareshi, Daga ƙarshe ma wa yan hannun sa daya bata ya amshe abin sa, shin wannan be ishi me hankali cewar da abin da yake nufi da ita ba, haka ze ɗauke ta gaban mota suje inda suke so, idan kuwa jinya take kwana yake yana zarya a kanta baya iya bacci, Yanzu jiya kayayyaki ya sawo mana amma kafin kowa cikin mu daga ni mara amfanin har me amfanin babbar mara hankalin Husna be fara nemar kowa ba se ita, ita ya fara bama dogwayen riguna guda biya, kana se ƴar lelen nasa itama ya bata dogwayen riguna har dama riga da sket, amma ni kinsan dame mena tashi dashi?, na rantse da girman zatin ALLAH iyaka dogon wando guda ɗaya ya bani, a kan idona shigana ɗakin sa kenan naga wata mini sket a gabansa yay saurin janyeta yana cusata ƙarƙashinta, amma na share nayi tamkar bansan da ita ba, Nan bulaguro idan Husna zata yi se ya bata sama da dubu talatin, ni kuwa wllh³ rabo na da kuɗin motar sa ya shiga tsakanin mu nafi shekara uku, duk inda kika ga naje wllh to kuɗi nane, Jinya wannan kuna kalla ai idan Husna ce ko yaranta da kansa yake ɗibarsu a mota ya kaisu, ni kuwa se dai naje da sayyarar ƙafa ta, idan kuwa yaranane ƙannansa yake sawa su kaisu, amma duk waɗannan ɗin basa gabana, burina kawai ya dena ire iren waɗannan abubuwan na neman mata sabo da goben ya rana, Mahaifiyarsa tsoronsa take ji, sau da tari idan kamar nayi yunƙurin naje na gaya mata wasu abubuwan se kawai na fasa don duk na san kaina abin ze faɗa, a cikin gidan nan kuma a ɗauka dani duk ba'a ganin irin abubuwan da ake min, Ina jin ciwo, ina jin ciwon hakan matuƙar.....
☆ Daga nan kuma se wani irin kuka ya ɓarke mata irin me ciwon nan, me fitowa daga can cikin zuciya da ruhinta, ko ba komai yau ta samu ta zubar da hawayen da ta jima tana son yi. Wayen da suka zubo daga cikin idanun aysha ta sanya bayan hannunta tana share wa tare da furta....
☆
"A duk lokacin da rayuwa take Zuwarma ko wanne bawa a hagunce to ki sani bawai zaɓin shi wannan mutum ɗin bane, Hakan ya sa ba ma tunani wurin yanke hukunci domin madafar gobenmu.Wata rayuwar ba tamu ba ce Maman Nuwairah, Wata ƙaddarar ba sakacinmu ba ne, domin kuwa ƙaddara ba canki in canka bace bare kace zaka zaɓarma kanka kala rayuwar da kake so, ki sani da wani na da iko ko halin canja ƙaddarar wani da tuni ko ni nan na jima da cireki a halin da kike ciki. Don haka kirki taɓa sarewa da rayuwa, karki tsaya ko sunƙuru ko da ƙaya koda an harbo kibiya ki dage sannu a sannu cikin wannan tafiyar IN SHA ALLAHU se ALLAH ya baki kyakkyawan sakamako, ke dai karki gaji komai akai miki karda kiji, duk da kasancewar tafiyar da akwai yaji sedai sakamakonta da alkhairi.
Idan kikai duba da cewar ita kanta wannan duniyar me wahalar zama ce, tattare take da tarin ƙalubale naban mamaki da kuma son kai da suka taru suka haɗa ƙarfi da karfe wajen rusa mutanen dake cikin *DUNIYARMU* suna mata wani irin Ƙawanya na tsantsan son kan ta suka gama lulluɓe ko ina suna mana garkuwa..." Tin da ayshan ta soma maganar Maman Nuwairah take binta da rinannun idanunta, da suka cike tafff da ruwan hawayen tausayin kanta da kanta, Idonta da yake mata zugi da zafi sosái ta sake rumtsewa, cikin ranta tana me ayyana kamar haka ne shafin rayuwarta ya buɗe, ta soma karanta shi cike da tarin ƙalubale me ɗauke da ƙunar zuciya. Wasu lokutan ta yi hawayen jini wasu lokutanma zuciyar kaɗai ke suya da raɗaɗin duk dai a ƙaddarar aurenta da auwal. Ita da kanta ta zaɓama kanta mijin auren da ko dai tace hukuncin da ƙaddara ta yanke mata, kafin igiyar aurensa kakkaifa ta koya mata darasin rayuwa tare da sanyata yin waiwaye zuwa bigiren da ta jima mantawa. Igiyar da ta yi sanadiyar yankewar duk wani farin ciki nata, tana raba ta da komai nata idan tace komai ɗin kuwa to kuwa tabbas tana nufin komai neee, A daidai lokacin da take ganin kamar ta kusa makara ne, sai dai ba ta karaya ba a dai shi wannan lokacin domin ta gamsu cewar azumtar nafila a watan ramadan runton zunubi ne. Tamkar yadda adda'o'in suke tasirin saurin yayema bawa dukan buƙatunsa. Ta sani ita kanta ƙaddarar rubutun Ubangiji ce akan rayuwar bawansa shi ne tabbataccen al'amarin da babu mai iya taresa. Ba shakka matuƙar zamu duba Rayuwa da abinda yake cikin ta, to kuwa tabbas hakan bakomai bane fa ce dumbin darasi da tarin Ilimin da zamuyi guzuri dashi izuwa gidanmu na gaskiya. Jiyanta ta riga da ta gama wucewa ta sani, amma goben yaran ta mata huɗu take fafutukar nema da lalube. Wani numfashi ne ya kufce mata wanda ya sanya Aysha saurin kallon ta tana me furta. "Kiyi haƙuri Maman Nuwairah!, Kaddararmu tana hannun Ubangijin mu ne, dan haka kar muyi kuka kokuma Kunci a Sa'ilin da muka tsinci kanmu a wani hali, ALLAH Yana sane damh kuma shi ne zai samar da Sauƙinsa a gare ki kema. Duk mai Imani ya san cewa tilas ne mutum ya rungumi Ƙaddarar da ALLAH Ta'ala Ya ƙaddarta masa a rayuwa, tabbas ƙaddara tana da matuƙar ciwo da zafi, zafin da bayyane yakan iya narka duniyarma baki ɗayanta, Amma ita kuma Addua ta na sassauta muguwar ƘADDARA me cike da tarin ƙalubale!!!.." A take a wurin bayyane ta shiga ambatar.
"Ya wadud,ya zal'arsheem majeed Alhamdulillh, Alhamdulillh!! Alhamdulillh ya Rabb ALLAH na gode maka.....
A hankali itama Ayshan ta shiga nanata adda'ar domin kuwa itama Ayshan, tana da nata ɓangaren, tana da nata labarin se dai banbancin kawai ita nata mijin ba'a ɗauke masa hankalin daga kanta ba, kana shi ba me neme ne men matan bane. Don haka a natse ta sake duban Maman Nuwairan, duba irin na natsuwa da haƙiƙanin abinda ke rai da ruhinta ta sake furta. "A rayuwa ba komai ake so ake samu da sauri irin haka ba
Nuwairah. Wasu lokutan sai an sha wuya an yi juriya sannan a ga canji.
Bazance kar kiyi haƙuri ba domin haƙuru shi ne jigon rayuwa mai kyau. Kamar yadda shi ke kawo zaman lafiya, shi ke hana faɗa shi ke sa mutum ya fi ƙarfin duk wata jarabawar raƴuwar da Ubangiji ya ƙadartama bawansa. Maman Nuwairah kalmar yi Haƙuri ba kalmar rago bace domin kuwa ba rauni ba ne, kuma hakan alama ce ta wayewa da tunani. Duk wanda ya iya hakuri zai fi samun nasara fiye da mai yawan fushi da gaggawa...." Se kuma ta ɗan dakata tare da fesar da wani numfashi kana taci gaba da furta. "Kiyi haƙuri da mutane duk abin da zakici gaba da gani Maman Nuwairah, kana ki yi hakuri da ƙaddara, ke inda hali ita kanta rayúwarma ki yi haƙurin da ita. Duniyar nan da kike ganinta tamkar littafi haka take, Kowacce rana sabon shafi ne yake sake buɗe ma ko wanne bawa, Abin da ya faru jiya ya riga ya zama tarihi, Ki dage da jajircewa haɗi da ƙoƙari ki yarda da ƙaddararki Maman nuwairah. Rayuwa tana da sauyi ba kullum take ba. Wani lokaci rana tana haskaka maka, wani lokaci kuma ana ganin gajimare. Ki zauna lafiya da mutane, domin komai yana wucewa, wahala bata taɓa dawwama kamar yadda karin magana ke cewa, _Ko da ruwa ya yi ƙarfi, ba zai hana rana fitowa ba_. Ma'ana duk nisan tsanani de akwai ƙarshensa, kuma tabbas haka wannan maganar take, Idan kowanne bawa ya kasance mai godiya ga ALLAH, Sai kiga yana kyautatawa,kici gaba da haƙuri da kyawawan halayenki da hakuri domin shi kyakkyawan hali yafi zinariya, Domin kuwa haƙuri na janyo Albarka da kwanciyar hankali. Faɗin annabin mune cewa wanda ya yi haƙuri kamar ya gama cin nasarar komai ne a Rayuwa IN SHA ALLAHU....." Daga haka ayshan ta gaza ci gaba da maganar tana saurin juyawa tabar wurin. Inda Maman nuwairah take bin ta da kallo na ƙauna. Se a yau take sake tabbatar da kalan ƙaunar da ayshan ke mata domin ALLAH ne, Saɓanin wasu a gidan da ada su take ma kallon majingina abin jinginar ta, se gashi a gidan kowa yasan matsalarta, amma babu me ƙarfafa mata gwiwwa da bata hakuri akan duk wasu abubuwa gurɓatattun dake faruwa wa rayuwar ta. Lallai tabbas ta sake yarda wasu mutanen da kake tare da su kullum kana musu dariya, kana zaune dasu da zuciya ɗaya, amma a zuciyarsu akwai hassada da ƙiyayya me ƙarfi alhalin kai kuma baka taɓa musu komai ba, bama kasan da hakan ba, saboda zuciyarka me kyau ce tana da tsarki, Sai wani abu ya faru da kai irin haka.....
☆ Bayan fitar ta da kyar ta iya tashi tana gabatar da sallar Isha'i da aka jima yi tana zaune, Tun da ta idar ta sallar kuwa take zaune daga inda take ta ko gazayin motsi, ta jima Sosái tana sake nazartan rayuwar kanta. Wato dai a zahirance duk inda Kalmar ƘADDARA take, To kuwa kowa yasan kalma ce dake motsa zuciyar ko wanne bawa, kuma kalma ce me nauyi domin kuwa tabbas wannan kalmar ta ƘADDARA kalmace me girma da faɗi wacce ta ƙunshi abubuwa da yawa cikin ta masu yawan gaske. don kuwa Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya tamkar ƴan uwan juna haka suke. haka kuma kowacce rayuwa tafe take da nata salon ƙaddarar me tafe da ƙalubale. Inda idan har kowanne bawa zeyi haƙuri wajen jure tarin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin kowanne rai mai numfashi game da duk abinda ALLAH ya riga da ya ƙaddara a cikin rayuwarshi,To kuwa tabbas duk abinda ALLAH Ya zaɓa maka shi ne mafi alkhayri agareka. Don haka itama IN SHA ALLAH ba zata taɓa yankewar daga roƙonsa.♡
☆
*Acp Maleek*
Tin daga wannan rana sukaci gaba da gudanar da ayyukansu tare da inspector Hannah cikin aminci, da taka tsantsan da iya taku. A hankali kuma soyayyar junansu ta fara ratsa zukatan su. Sau da tari idan ka kalle su suna wasa da dariya abinsu se abin ya mugun burge ka. Ko a yanzu ma zaune take gaban motar sa, lokacin bayan sallar magrib ne sun dawo ne daga wani aiki. A natse ta sanya hannunta zata fita a motar, se dai hannun ta daya riƙo ne yana ɗan zuba mata kaifafan idanunsa, tare da rankwafo da kansa zeyi kissing hannun nata. Fararen idanunta ta zuba mishi tare da janye hannun ta tana me furta.
"Karkai gaggawa mu ajiye se daga baya" tayi maganar da alamar murmushi ɗauke saman kyakkyawar fuskar ta, "daga baya kamar ya kenan?" yay maganar yana bin ta da wani kalan kallo tare da karkatar da kanshi gefe. "Se rana me tabarraki." ta sake bashi amsa da hakan again tana sake yunƙurin ficewar, bayan ta zare hannun ta a nashi "Ko dai kema kin dena so nane Hannah kamar sauran matan da suke guduna?" yayi maganar yana komawa seriously nashi. Wani kyakkyawan murmushi tayi me kyau tare da kwantar da kanta da kujerar motar, tana me furta."Ma so ɗan tsuntsu ai shi yake bin sa da jifa. A ko ina ina son ka ringa tuna cewar kai kankat ne a duk tsawon lokacin nan, kuma dama dan kai kaɗai aka halicceni shi yasa sauran matan ke gudun ka *MY JAAN*" tana kaiwa ƙarshen maganar nata ta buɗe motar tana guduwa, inda ya shiga binta da wani kalan mayen kallo me cike da so da ƙaunar da yake jin yana mata, da duka rai da ruhinsa.......
08104493215
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻
# 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Book One paid
♡
Page 13&14
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
*Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank*
♡♡♡♡♡♡♡♡
ꨄ Da kaifafan idon sa ya shiga binta har lokacin data shige gida, kafin a natse ya janye fararen idanun nasa tare da yin reverse yana barin wurin gaba ɗaya. Directly yana nufar plat house ɗin daya kama. A bakin ɗan madaidacin wurin adana motoci yayi parkin car nashi abin sa, Dake yayi sallarsa wanka kawai ya shiga, ya ɗan jima sosai a ciki kafin ya fito yana sharce ruwan dake ɗigo masa. Kayan bacci masu ɗan nauyi ya sanya kasancewar iskar da hadarin daya haɗu ya bada, nafila yayi raka'a biyu tare da adda'o'i, yana idarwa ya haye saman gadonsa tare da ɗaukar wayar sa don ƙiran hajiyarsa, zuciyar sa cike fal da farin cikin sanar da ita sabuwar budurwar da yayi, wacce yake jin a jikinsa IN SHA ALLAHU seya aure ta, ring biyu kuwa hajiyar tashi ta ɗauka. A natse ya mata sallama tana amsa shi cikin kulawa cike da soyayyarta gareshi, gaida ta yayi nan ma ta amsa tare da tambayar sa ya yana yin wurin aikin nasa, kansa ya ɗan shafo tamkar yana gabanta tare da ce mata alhamdulillah komai yana tafiya a daidai. Wata iniyar zuciya ta nutsuwa hajiyar nashi ta sauƙe bayan ta sake tambayar sa inda matsala ya faɗin mata, yace wllh be fara fuskantar komai ba duk da kuwa ba jima da zuwa, amma yaga alamar babu wata matsala wllh. Daga yacce suke wayar ta fahimci zallar ɗoki da farin cikin da yaron nata yake a ciki, don haka itama cike da tarin nata farin cikin ta furta. "Abdulmaleek! Duk yacce akayi akwai magana a bakin ka ko?" Dama ya san zata fahimta, don haka ya sake gyara kwanciyar sa cike da murnar sa ya furta "Damaaaa......"
"Dama me?" Hajiyar ta katse shi cike da ɗoki, "dama nayi sabuwar budur......." Innalillahi budurwa kuma Abdulmaleek?". tana riƙe ƙirji tamkar tana kusan shi," Ehhhhh Hajiya, wannan inaji a jikina zan aure ta babu abin da ze faru kin ji In sha Allahu, ki kwantar min da hankalinki don ALLAH!!! " wata bahaguwar ajiyar zuciya ta sauƙe tana me furta," UBANGIJI ya tabbatar da alkhairinsa, ya tsare ka daga duk sharrin abinda ke bibiyar rayuwarka Maleek... " Da Ameen ya amsa ta daga nan suka ɗan taɓa fira cikin sake wa sosai kafin su yi sallama tana ƙara jaddadamasa ya riƙe adda'o'i da nafilfuli In sha Allah babu abinda ze kuma faruwa......
☆ JANNAH.
Tun daga soron gidan nasu take jiyo muryan Baba Asabe kakar su data haifi mahaufisun malam ayuba tana ta faman zazzagawa Ummansu tijarar data saba mata indai zata zo gidan. Domin kuwa taka nas bappansu ya ware ma baba Asaben gidan ta, sabo da rikicin da suke yi tamkar wasu kishiyoyi, yanda kaga saga hanjin juna haka suke. Wata bahaguwar ajiyar zuciya ta sauƙe don inda sabo yaci ace ta saba da wannan halin nasu, don tun bata da wayo da wanan hali ta buɗe idanuwanta a gidan. Kusan kullun fitinan Baba Asabe ne ke tayar dasu daga barci na yau daban na gobe daban, Kafin a ware musu gida.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 23