a haka ba, har seda naji naji knocking na car na da ayi da ɗan ƙarfi, Abbu ne tsaye don haka nayi saurin ɗauke duk yana yin da nake ciki na tsantsar damuwa, sedai ashe hakan be iyuwa ba, sakamakon zaman da abbuna yayi daga gefe da inda nake zaune, Kafaɗana da naji ya ɗan dafa ne ya sanya ni ɗagowa da sauri na kalli abbun, Inda a lokacin da ya shigo ɗin na riga nayi nisa a duniyar tunani ban ma san lokacin daya zauna ɗn ba. Fuskar sa dauƙe da damuwa yace min "lafiyan ki lau kuwa Nufaisah? Tun ɗazun naga shigowanki tin ina ta jiran fitowanki amma se naji shiru, faɗamin meke damun ki?" kai kawai na girgiza masa to ince masa me ne don ALLAH?, In ce masa yayana nake so ko nake feeling love?, don haka na ɓame bakina nayi shiru, it's better to deal with it on my own. A natse ya furta "you are lying Nufaisah! ga damuwa nan kwance akan fuskar ki ina gani, kar ki ɓoye min komi Tell me, me ya faru?" kallon mahaifina kawai nake yi tare da sake girgiza masa kai wani kuka na shirin kwace min, Cikin aro jarumta na azawa kaina na ƙaƙaro wani murmushi tare da cewa "Babu komi fa Aabbu it's just a minor headache, mun yi yawo da yawa ne" na furta ina miƙewa tare da ledojina inda nake ta jin idanun mahaifin nawa bisa kaina, amma na daure ina ƙara sa fita a motan, sedai da wanda idona suka min tozali ne ya sanya nutsuwa ta kusan guduwa, amma na daure hakan ina seseta yanayina ina ƙaƙaro wani murmushi tare da ɗaga masa wani ina me furta. "Hi barka da gida lolly, Kazo muci kayan kwalam tin da ka daina fita dani, gashi yau nayo mana shopping ni...." nayi maganar tamkar a da can baya da nakan saba masa magana ba wani shakku ko gargada.
*Jan gida*
"MANZON ALLAH (S.A.W) ya gaya mana cewar kar mu kusanci zina, amma kai baka da aiki ita kullum kake janyowa tattare da kai jikinka Abban Nuwaira, shin kai baka tuna makoma da rayuwar naka ƴaƴan ne??!" Maman nuwairah dake tsaye a gabansa idon ta tab da ruwan hawaye ta faɗi, domin shigowa da tayi ƙiriri ta kama shi yana video call da wata da bata san ko wacece ba, don saurin kife wayar yayi akan cikinsa da babu riga, daga shi se pyjama's maroon. Wani haɗe fuska yayi tare da mata nuni data fice masa a ɗaki, ƙiyawa tayi dan haka ya taso a matuƙar fusace da niyarrr.......
08104493215
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
~Lots of Love and Hearts 💕 ¿~
༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻
# 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Book One paid
♡
Page 21&22
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
# HE WILL FIGHT
# Yakin sunƙurun ummih
*Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank*
♡♡♡♡♡♡♡♡
ꨄ
Cikin yanayi na fusatuwa da zallar ɓacin rai, da wani abu ne kama da tsana tsanar dake taso masa game da ita yake nufar ta, kan shiga masa hurumin da kullum kwanan duniya take yi, kai tsaye ya dire gabanta yana huci tare da duban ta cikin wani irin mugun yanayi. "Ina ruwan ki da rayuwa nane Nafeesah?, rayuwar ki ko tawa da zaki ce dolen dole se kin shiga cikin ta?" yay maganar yana fesar da wani numfashin ɓacin rai, "Ba rayuwar ka bace wannan Abban Nuwaira Rayuwar Ƴaƴanace, domin kuwa kai ne majiɓancin goben su, idan ka aikata sharri yana kansu haka in ma alkhairin ka aikata duk wa su ɗin ne dai to na gaji!, wllh na gaji da kallon wannan baƙar Rayuwar haka nan Auwal, don me ba za ka ji tausayina wajen gina gobe da tarbiyyar yaran muba? Bayan kuma kasan wannan ɗin tabbataccen al'amari ne tin daga rabbis samati wal ard cewar duk abinda ka aikata da ɗan wan..........
Tin kamin ta kai ƙarshen ya wani irin tare da ihu yana furta. "Ƙarya kike yi Nafeesah babu abinda ze faru da yara na, sedai ya ƙare a iyaka kan ki ke kaɗai" yayi maganar yana sauƙe wani huci da zabin zuciya. Wani murmushi me ciwo tayi tare da kallarsa cikin ladamar auren sa da tayi tare da furta. "Taya kake son raya tunanin da kasan ba shi ke nan ba?, wato kai kaga garin wasu amma kai ba a ga naka ba Ƙarya ma kenan" daga haka ta fice tana barin sa a ɗakin shi kaɗai ya fara safa da marwa, domin kuwa yana son yaran sa baya son komai ya faru dasu, Akwai wata rana ya dawo daga wurin kasuwancinsa ya tarar da yaran Jiddah biyu suna wasa sun ruhu a cikin shijjabin uwar su, a take jikin sa ya soma wata iri yar rawa tare da doka musu wata uwar tsawa yana kamo hannun su, tare da nufar ɗakinsa da yaran da suka kasance duka maza, kasancewar ƴaƴan husna ɗin duka maza ne abokiyar zaman nuwairah. Domin kuwa ko da wasa baya iya jurar ire iren hakan daga yaran sa, don haka saura ƙiris ƙafarsa ta goce da ƙafar benensa da yake shirin shiga, wannan ce ta ceci yaran, haka idan wani daga cikin mata san family nashi suka bama ƴaƴan sa kuɗi seya tambaya ke farko uban daya baka, idan suka faɗa masa seya amshe kuɗin ko kuma yace ka mayar wa mutum idan ya ƙara gani wani ya baka abu ka amsa seya ci uban mutum, kasancer ya san yanzu a wannan duniyar da kuɗi ake sayen komai ciki kuwa harda mutumci da kimar ƴan matan da ya kamaci ace gidan auren ta takai wannan kimar, sedai kwadayi da son zuciya sukan rinjayesu har su faɗa hanyar halaka daga baya kuma Kaga anzo ana dana sani. Da wannan ya shirya cikin shirin sa na fita kasuwa yana barin gidan ba tare daya bari kowa ya gansa ba, ciki kuwa harda Jiddah ƙanwar matarsa Husna da idanunsa ke mararin gani, amma ya san ai zasu yi chart idan ya isa kasuwa.
♡ A ta can ɓangaren Su Maman Isah kuwa haka rayuwa take dama musu tare da ummih ƙanwar Maman Nu'aima. Tin abin na musu wani banbarakwai har yazo ya dena, haka za a haɗu ga wa ga kuma ƙanwar ta suna rayuwa gida ɗaya rayuwa irin ta aure, ita babbar tana auren ƙanin mijin ƙanwar nata, ita kuma ƙanwar tana auren babban yayan mijin yayar nata Maman Nu'aima. Sedai har zuwa tsayin wannan watannin da suka shuɗe wajen uku zuwa huɗu Maman Sarki bata fasu ba, wanda kowa yake fassara shirun nata da ba abu bane me kyau, kasancewar kowa ya san irin alaƙar dake tsakanin Maman Sarkin da kuma Maman Nu'aumar, duk wasu shige da fice na harkar dahuwa da dake daken magun mata da tsime tsime Maman Nu'aimar ita ke mata, Se gashi sama ta ka kuma ƙanwar ta uwa ɗaya uba ɗaya ta auri mijin ta wannan cin amanar har ina. Kamar yadda ta ja bakinta ta gimtse haka ma sauran matan gidan kowa ya ja ya ɓame nasa bakin, Se ɗan ƙus ƙus ɗin da ba'a rasa mata dashi dake gudana tsakanin wasu wanda suke gaza yin shirun, haka Ummi zataci wanka ta fita tsakar gida ayi fira da ita. Ahankali Ahankali ta fara shiga cikin rayuwar Maman Nuwairah, wacce shigar ta cikin tata rayuwar ya fara kawo mata wani haske na ban mamaki, domin kuwa Ummin irin shegun ƴan duniyar matan nan ne, duk wani hanyar kujuba kujuba da faɗi tashi suna san sedai zuciyansu sam bata da nufin fara nufar kowa da sharri, Se in har shi wannan mutum ɗin shi ya fara shiga cikin tasu rayuwar to kuwa akwai tarin rashin kirki bana wasa ba, Tana rayuwar ta ƙalau da kowa lamin lafiya kuma sau ɗaya Inspector Hannah taje gidan, daga shi bata sake zuwa ba domin tasss tama Yayar nata, Maman Nuwairah da kuma Ummin da suka yi auren cin amanar da suka ƙulla. Amsar da Ummin ta bama Hanna a lokacin da _ Kara ni a bayyane kowa ya san cewar nayi aunty Hanna, to ina ga wanda gata nan a gidan rayuwa suke wacce ma tafi ta wasu ma'aurantan, Kuma da kike maganar cin amana ai yaya Zaynab ta jima tana bamu irin cin amanar da ƙanwar Husna take yi da mijin ta, ba tare data lura da hakan, wanda a bayyane kowa ya gama sani kafff gidan ciki kuwa harda abokiyar zaman Husna ɗin Aunty Nafeesah, amma kowa ya gaza ganar da ita husnar gudun karda tace sherri akama Ƴar uwar ta, ganin kamar dama gidan a hannun ta yake kuma yanzu abin yaci uwar nada ko nace yaci gaba yanzun haka harda ƙanin ta da suke uwa ɗaya ya dawo hannunta da zama, Malama kin ji inda ake ƙira da hasalin cin amana da zamba cikin aminci, a yanzu haka ma zamcen da nake miki ya ɗauki Jiddahn a motar su sun fita wai ganin likita ulser nata ne ya tashi, Shin ke a karan kanki zaki iya jurar ganin wannan mummunar badaƙalar akan mijin ki?.... _
Tin da Hannan ta tafi ta tarin maganganun da ummin ta faɗa mata a ranta bata sake waiwar gidan ba, domin kuwa ita tsoro ma take kar wutar alhakin dake gidan taje wata ran tana can laifin mutanen gidan ya rista da ita. Ita kuma ummin tana da nata Maanar akan kowa dake rayuwa a cikin gidan, idon ta buɗe yake akan kowa da duk wasu masu shigi da ficin cikin su, Tarin wasu abin mamakin ga ummin cikin son ta farkar kana ta fusatar da Maman Isa take yaɓa mata magana idan wata ƴar cacar baki ta haɗasu da Maman Isan ta kan ce da ita. _Aini bana tsayawa bata lokaci na akan macen da bata gama cika mace a idanun mijin taba_ Tabbas tana yin nasara akan ire iren waɗan nan maganganun nata ga Maman Isan, domin kuwa kusan kowa ya san al'adan mu ce Matan Hausawa da mace ta jingine wasu yara fiye da goma ko takwas ta dena gyara jikinta, alhalin kuma tasan tana da mijin, ko wai don kawai tana da yara manya a gidan ko ta taɓa auren Ƴaƴa kamar ita Maman Isan yanzu da take da za ratan matasan samarin ta su biyu, ɗan shekara ashirin da huɗu da kuma ashirin da biyu, wanda kai a ganin ka ai ka tara manyan yaya a gidan babu yacce za a yi miji ya rabu da kai, sedai yanzu ba haka take ba, iyayen mu na yanzu suma idon su a tsakar ka yake da auren yayan cikinsu, ko dai wacce bata kai ta gidan tsufa ba, su kuma su shigo suna gyaran su ke kuma can an barki Bono a kwana ba dole miji ya dena ganin kima da martabarkiba, wllh wasu masu irin haka babu boka babu mallem suke amshe mijin daga uwar yaran data gama shan wahalar gina mijin nata sama taka, Se kiji ana ai wance ta kwace gida se abinda tace ake yi a gidan, to mu sani harda ire iren waɗannan abubuwan da muke ɗaukarsu ba a bakin komai ba, tuni kuwa Maman Isa ta dage ita haka dai a cikin ƙawanta da ƴan uwanta take sa a mata wasu abubuwan a sacen itama, tin da dai yanzu rayuwar ta haka ta zama, kowa abu a sace yake yi baya son wai ya san yana yin abu kaza daya danganci magungunan matan. Se kuwa gashi Alhaji Ibrahim ɗin ya fara rage tsangwamar nata da yake yi, Se a lokacin ta zauna tayi karatun ta nutsu ta gano kuskuren data Jima aikatawa kanta, wanda a fakaice seta fara ma Ummin albarka, don ko babu komai ta dawo mata da martabarta data rasa baya, ahankali ahankali ummi ta fara seta Jan gida ta ƙarƙashin ƙasa. Ciki kuwa harda tsoma kanta cikin rayuwar auren su Maman Nuwairah tare da abokiyar zamanta husna dama dadiron ƙanwarta Jiddarh.....
♡
Yana zaune akan arm chairs ɗin dake cikin office nashi, yana sake na zartar komi daki daki. Wanda hakan ya ta'alakka da kashe wani jami'insu Sameer da akayi wajen binciken ƙungiyar _Buried Bo-Death_ Ahankali yaji zuciyar sa tana tafarfasa kan wasu maciya amanar da suke ɓuya a bayan kakinan jikin su suna cin amanar ƙasar su. Tabbas beyi mamaki ba da sunan Kanal bappa babayo ya fito a jerin suna yen yaran ƴan ta'addar da Acp Maleek ya turo mishi. Tare ma da bayanan shi canal ɗin shi ya bama ɗaya daga cikin ƴan bayanai akan babban amininsa captain Sameer, wanda se gawar sa aka turo musu yan ta'addar sun sheƙe. Wani abu ne yazo ransa nan take wanda yake ganin kawai shi hakan shi ne babbar mafitar da yake da a halin yanzu. Se bayan sallar Isha'i yau kam ya bar wurin aikin nasa, dake a gajiye ya dawo ko dinner be fito ba na dare, wanda dama ba wani abu me nauyi yake iya ci ɗin ba inda da dare ne. Har ɗakinsa Ammey yau da kanta ta kai masa fruits se coffee da dangin su snacks haka. ko a washe garin ranar ma sosai aiki ya sha kansa sosai wanda be sake samar kansa ba se dare a yau ɗin, don yau kam ma se wajen sha biyu ya dawo gida, sabi da haka se haɗu war ma ta fara musu wuya tsakanin sa da Nufaisah, sosai ayyuka suka caɓe masa cikin satin wanda sanadiyyar hakan gar wata ƴar ramar wuya yayi. Ana cikin wannan tsaka me wuyar kuma a daren ranar larabar ranar aka nemi Kanal bappa babayo aka rasa a hanyar shi na komawa gida. Wanda wasu daga cikin manyan sojojin suke ganin kamar yan ta'addar ne su kayi kidnapping nashi, wanda kuma aka ɗora alhakin aikin nemo shi akan Captain AA.
♡ Don haka ma seya zama gaba ɗaya hankulan jami'an tsaron ƙasar atashe yake. sakamakon kiddnapping ɗin Kanal bappa babayo ɗin da aka yi, domin kuwa kiddnapping ne na ban al'ajabi da ban mamaki da firgitar da zukatan duka soldiers, domin taya za a yi ma a ce an samu damar ƙwamushe, duk irin tsaron da yake da, wanda duk inda zashi yana kewa da soldier masu bashi kariya, inda dai daga ƙarshe aka gano cewa wata waya aka ƙira shi like irin ta anyi masa barazanar nan. Shi yasa ya fita a sace shi kaɗai ɗin sa. Kuma mafi ƙarin mamakin ma shi ne a nan kusa da Headquarters nasu aka tsinta motar sa, shi yasa hakan yake sake zama kamar wani babban al'amarin ne kuma na daban. tayama za'ace anyi kiddnapping kamo Headquarters nasu kamo abinda befi ajiyar numfashi da sauƙewa ba, lalle kosu waye waɗan nan masu kidnapped ɗin manya ne, don hatta wayoyinsa a cikin motar aka bari bayan an anyi hacked na duka callings ɗin daya samu daga ranar, ta yanda duk iya kwakkwafin mutum be isa samar ko wanne irin sheda bane daga wayar don anyi blocked na komai. Kafin kace mene sega zancen ya zama very lates a media. Gidan jaridu, television's, radio Babu inda basu yaɗa wannan babban al'amarin ba.
♡ NIGERIAN ARMY HEADQUARTERS ABUJA
Su kansu gaba ɗaya sansanin nahiyar filin sojojin, cike yake maƙil da manyan sojojin ƙasar Nigeria dama ƙananun ma'aikata, kowa sai faman kai wa da komowa yake. babban burin kowa A wurin bai wuce ace terms nasu ne sukayi winning wannan cese ɗin ba. Don haka kowa yake ta famar shige da fice. A natse motar sa ta faka daga compound na adana motocin, be fito ba yana zaune daga cikin motar nashi, Se ƙafarsa ɗaya daya ziro waje yana karkaɗawa ɗayar kuma tana ciki yana nazartar kowanne motsi na soldiers ɗin daga harabar wurin.
Kafin ya fito daga cikin motorn sanye da uniform na kakinsa.
cikin takun ƙasaita da cikakkiyar kamala, da haibar da subhanahu wata'ala yayi masa haka yake tunkarar babban filin taron soldiers ɗin kai tsaye. Tuni sojojin wurin suka fara sara masa, tare da ƙara shiga taitayinsu. saboda tsabar cikar zatinsa yasa idan yana tsaye a wuri babu wani mai iya ɗaga idanuwansa ya kalle shi, bare kuma kasami zarrar haɗa idanunka da nashi. wanda ya amsa sunan shi 'a matsayin namijin mazajen fama, wanda duniya take alfari dashi kasan cewarshi soja mai tsananin aiki da gaskiya. Don haka cikin wani irin zallar izzar da yake da, yake tunkarar compound ɗin da sojojin ke tsaye. A hankali yayi sallama a wurin wanda yaja hankulan jami'an tsaron wajen gaba ɗaya wanda basu san da tsai war sa wurin ba. Fuskar nan a matuƙar haɗe sammmmm babu annuri, ko wargi acikin sa. Nan take kowa na wajen ya shiga ƙoƙarin solid nashi. Lieutenant Nassar Bunza ne dake tsaye daga gefen sa hannun sa riƙe da wasu files. Ya sara mishi tare da miƙawa Captain AA. Files ɗin dake hannun sa wanda El-lateeb yay saurin warcewa daga hannun Nassar ɗin cikin sauri. Wani irin matsiyacin kallo da Captain AA ɗin ya watsama El-lateeb ɗin ne yasa shi sakin files ɗin ba shiri, har jikinsa na ɗan karkarwa, dan wani irin ɓoyayyen sirri dake ɓoye cikin idanun AA ɗin, hakan yasa idan harya watsa ma idanun kake diriri cewa ka shika hankalin ka take kuma. Halama yama Nassar ɗin daya biyoshi a baya,hakan kuwa akayi jiki na mazari Nassar ɗin ya bishi a bayan kamar yacce ya bukata ɗin. Kai tsaye babban office nasa ya nufa cikin tafiyar nan ta jinkai da jin ya isa, saida ya zira yellow card kana ƙofar ofishin ta buɗe, shiga yayi da sunayen ALLAH ɗauke saman laɓɓansa, yana shiga El-lateeb ɗin ma na shiga, yana shiga kai tsaye kujera yaja ya zauna ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya. kana yama El_lateeb ɗin nuni daya zauna shima. zaman kuwa yayi bayan yayi solid nashi halamar girmama ogan nashi,files ɗin hannunsa ya zube gaban sa wanda dukkan bayanai ne da su ka shafi wannan cese na kiddnapper's ɗin ne a ciki. Se da suka tattauna wasu maganganu masu ɗan tsayi tsakaninsu kana El-lateeb ɗin ya fita. Bayan bayan fitar El-lateeb ɗin ne AA ya ɗauko wasu decoment irin waɗan cen files ɗin exctly... Wanda abin ya bani mamaki nima a karan kaina. System nashi ya janyo yayi wasu ƴan danne-danne, kana yamayar system ɗin ya rufe, yana sassauta fushin dake kwance saman cute face nashi kafin ya saki wani lalataccen murmushi a bayyane yana me furta. "Ka shigo hannu" daga nan ya shiga wasu rubuce ² a laptop nashi har zuwa dare, salla ce kaɗai ke fitar dashi.
*After isha'i*
A hankali yake mirza starryn motan nashi tamkar baya so ko irin wanda aka ma dolen nan. Daga can ƙasar zuciyar sa kuma wani nishaɗi yake ji amma baka isa gane hakan ba kai tsaye, don a bayyane ma fuskar nan tsuke take tammm ya dafaffen kunun kanwar da be samu haɗi ba lolz😂. A natse ya danna horn sau ɗaya inda Get man dake zaune daga jikin ƙofar ɗakin sa, yana sauraran labaran yau da kullum yayi saurin tashi yana buɗe ƙaton get din gidan. Kai tsaye ya harba hancin motor nashi zuwa harabar gidan, "Ginshi ƙin dutse kowa ya yi karo da kai shika faɗi, Soja mazan fama! Namijin mazaje An buga dakai an barka, Sai dai su buga su barka kaiɗin ajiyar ALLAH kake murucin kan dutse neeee" haka ya tsinta kalaman get man nasu wanda sau da dama dama ya kan tsinta ire-iren hakan daga gare shi. babu kowa a palourn nasu yau ma kamar kullum kowa harya kama makwancinsa, kai tsaye hanyar upstairs nashi ya nufa cikin tafiyar sassarfa, "Aliyu!!!" haka yaji sauƙar muryar Mahaifiyar shi har tsakar kansa tana fitowa daga kitchen hannun ta ɗauke da plat da cup. Tana me furta "Sai yanzun kake dawowa yau ɗin ma?" Ta furta da alamar tambaya. "Wllh ayyuka ne suka mana yawa sosai Ammey"
"To madalla ga dai lunch naka yana jiranka idan ka gama shiryawa" ta faɗi tana ajje masa a dining na duka mahaɗan babban palourn gidan.
"Banjin cin woni abu Ammey naaa coffee ma is ok kawai" ya bata amsar yana wani ya tsine Kyakkyawar cute face nashi. "ALLAH yanzun Mazan fama baza ka daina wasa da cikin kan haka nan ba ?. wajen kin son cin abinci ba ko?, kai koda yaushe ba zaka ware kaci abincin kirki har hakan na nemar zamar maka ɗabi'a ma ko?" "Zan dena soon Ammey" ya yi maganar yana hayewa samansa, a ɗan gurguje ya shiga zare kayan jikin sa yana rage daga shi sai short,don hatta farar best ɗin ma daya cire cilli yayi da ita a tsakar ɗakin. toilet ya shige ya tara ruwa masu ɗumi da ƙamshi a cikin bathtub, Nutsewa yayi a cikin ruwan, ƙamshi da ɗumin ruwan na ratsa dukkan wata sassa na jikin shi. After just 40 mint ya fito yana ƙamshim shower gel, ɗaure da fari tass ɗin towel ya fito sai uban ƙamshi yake zubawa. clothes nashi ya shige yana shiryo kansa cikin fararen kayan bacci masu tsananin taushi, Inda gaba ɗaya siffar cikakken namiji ya gama baiyana ajikin shi,damatsan hannunsa kuwa yadda kasan irin na prabhas ɗin nan haka yake. dadduma ya ɗauka yana shimfiɗawa, yayi sallar daya saba kamar kowanne daren duniya rakaa biyu, parlourn nasu ya nufo kai tsaye daga saman shi, cikin tafiyar nan ta zaratan maza wanda sukayi fice wajen sadaukarwa wa aikin su. Coffee ɗin kawai ya sha kana ya koma saman sa, zaune ya kai gefen gadonsa yana janyo jakar laptop nashi, Akan cinyarsa ya ɗaura laptop ɗin kana ya debo wasu files ya shiga wasu ƴan danne-dannensa, copying komi yayi cikin laptop nashi kana ya rufe. Adda'ar bacci yayi cike da tarin nutsuwarsa, kana ya kwanta tare da tasbihi wa cen ƙasar ranshi. Ahaka har barci yazo yayi gaba dashi cike da wasu irin mafarkai barkatai.
*WASHE GARI*
Gaba ɗaya suna zaune a babban parlourn nasu, Abbu, Ammey, Nufaisa dukka suna kan dining table ɗin zazzaune, kowa yaja plate na abinda yake so gaban sa, ƙarasowa yayi yana faɗin. "Barka da safiya abbu naaa" "Barka Aliyu"Cewar Abbun yana amsa yaron nashi.
"Yauwa abbey naaa" yayi maganar yana gaida Ammeyn sa again,
"Barka da safiya Yaya" Nufaisa ta gaida yayan nata. Kujera yaja ya zauna bayan ya amsa gaisuwar autan Ammeyn. Tare da furta "Ammey coffee" ya faɗa hakan yana wani ya tsine fuska, sammmm yau bayajin daɗin jikin shi, kuma yasan baya rasa nasaba da aykin daya kusa kwana yi a daren na jiya.
"Coffo...... Ammeyn
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 23