Share this page
nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank* ♡♡♡♡♡♡♡♡ ꨄ Tana zuwa ɗakin ta ta zube saman gadonta, tare da rufe fuskar ta da tafukan hannayenta, tana me furta, "Me yasa hakan yake son zama sanadiyyar rugujewar kyakkyawar alaƙar dake kulle a cikin zuciyoyin mu?, Me yasa na chanchanta wannan hakuncin ehhh ƙaddara, shin ni ban chanchanta zama. ♡ Tana a cikin wannan halin ne mahaifiyar nata ta shigo ɗakin ta same ta, zama daga gefen gadon tayi tare da ɗago kanta tana ɗora kan Nufaisa ɗin kan ƙafafunta, cikin wani irin sanyin murya ta furta. "Nufaisa keba yarinya bace nasan zuwa yanzun kin jima da fahimtar komai, kuma daga baya ma na miki bayanin cewa Aliyu ba ɗan da muka haifa bane daga cikin cikin mu daga ni har mahaifinki, So dan haka nake son alakarku ta tsaya a iyaka haka nan Nufaisah, No more.... Bana son wani magana ya fita daga baya kina jina??, domin kuwa wutsiyar raƙumi har abada tay nesa da ƙasa, domin kuwa shi ɗan sarki ne jikin sarki. Kuma Sarki na gaba me jiran gado a cikin Masarautar ADAPHAN. Don haka b careful Nufaisa karki nema da ki jefa zuciyarki inda bai dace ba." tin da ta fara maganar kallonta kawai nake cike da mamaki, me ke damun Ammey ne haka yau? Duk da hakan ban fasa daga mata kan ba, wasu abubuwa na nemar fasa kaina, don kuwa ji nayi kamar irin an ɗora min dutsen dala ne ba ganmo... Da haka ta fita bacin ta sake min wasu nasihun masu ratsa jiki tana fita, fitan nata kuma babu jimawa na sake jin an sake turo ɗakin, don haka ma ban ɗago ba dan nasan Ammeyn ce ta sake dawowa. Jijjiganin da naji anyi ne ya dawo dani hankali na daga cikin duniyar tunanin da na cilla. "Hey babe!! Come back to your senses mana!!" ɗan zabura nayi ina kallonta a tsorace kafin kuma in harare ta, tare da furta "What?, wai ke tsaya ma me ya kawo ki gidan nan yanzun?" na faɗa almost shouting, kafaɗuna ta dafa tare da cewa "Ai ke ya kamata in fara tambaya, you were deep in a thought and you suddenly became teary, me ke faruwa dake ne duk yau Nufaisah?" tayi maganar tana dangwalo ruwan hawayen da bansan da zuwan suba, yatsa na na kai na dan taɓa idanuna, da gaske kuwa I was about to cry dan ga ruwan hawayen kwance a saman fuskana. Tsareni tayi da idanunta tare da furta. "Nufaisah wai me ke faruwa dake ne tsakankanin ƴan kwanakin nan ne?, da gaba ɗaya duk kika bi kika sauya wajen son takura kanki da yawan tunanen Ya Aliyu ko?... " ɗago kaina nayi na kalleta da sauri kuma cike da mamaki, gashi dai tambaya ce tamin mai sauƙi, haka kuma amsar ta ba wata mai wahala bace. Kaina na ɗan girgiza mata, tare da furta "REEMAH me kike tunani ne wai?" wani ɗan harara ta cilla min, "Nufy bafa cewa nayi ki tambaye ni ba, A ahhh amsa ta kawai nake da buƙatar ji; Meke tsakaninki da ya yanki? nd kuma Mohan yace min tin daren jiya baki amsa call nashi ba, seda ya ƙira ki da wayan Sis nashi kana kika amsa!" ɗan shrugging kafaɗana nayi ina ƙoƙarin nuna babu komi, "Me ke tsakanin mu kuwa REEMAH? He's just brother Friend, Wanda muka fito ciki ɗaya and I stayed with them for a while I think that's all!" wani kallon karki renamin wayo ta cillo min tana me furta "That's all fa kika ce ?!" Kai na jinjina mata cikin tabbatarwa, "yes!, da kyau" Se kuma ta ɗan yi shiru tana kallona kafin ta sauƙe ajiyar zuciya, Tana kallona cike da tuhuma, sake jinjina mata kan nayi nima alamar tabbatarwa, tare da ɗauke kaina daga kallonta kawai, ina ƙoƙarin kawar da komi, domin I wasn't ready to discuss the matter with anyone a lokacin, I wanted to dealt with anything on my own don haka na sha re ta kamar ban san abinda take nufi da hakan ba, Se can kuma kamar daga sama naji sauƙar muryanta tana me furta. "Da ba zaki magantu ba ma, ai Ammey ta sanar dani komai" Wani kalan saurin kallonta nayi jikina har na kamar tsuma tsuma. Kanta ta jinjina min alamar d gaske take min kenan, kafin ta shiga faɗin. "Beb dama ni koda Ammey bata sanar dani komai ba, nasan da cewar Son Yaya Aliyu kike, So kuma irin wanda yake fitowa tin daga ƙarƙashin zuciyar nan, wanda duk guje guje da ɓoye ɓoyenka dole ne wani ya fahimta hakan, amsa ta 1 kenan, 2 ɗin kuma yadda kike fusatuwa tsantsa idan wani daga cikin classmate namu ya furta kalmar SO a gareshi, Sam baki iya ɓoye kishin ya yanki a ranki Nufy, a gaban kowa da kowa, tin daga lokacin na dasa ma wannan dangantakar naku alamar tambaya, don haka pls kiyi ƙoƙarin shanye komai, kin ga gobe ko jibi za a kawo kayan lefenki, don ALLAH ki daure duk abinda kike ji kima iyayen ki biyayya nd daɗi da ƙari ma kuma kinga kene kika zaɓa Mohan, zaɓin kine, shima ze baki duk farin ciki da kulawar da duk kike buƙata daga wurin kowanne cikakken namiji.... " Wata doguwar ijiyar zuciya na sauƙe ina ɗan sobbing kaina, kamin kuma in pleadingly na kalle ta ina mata alamar data barni haka nan, don nasan halinta tsaf zata iya takura ni, hakan kuwa daidai yake da fasa kukan da nake ta ƙoƙarin ganin na riƙe, domin kuwa duk yacce zan kwatanta muku irin ɗaci da azabar da nake ji a cikin tsaƙiyar ƙirjina ba zaku taɓa fahimtar ya abin yake ba. Daga nan bata sake tada min da maganar ba, Se can zuwa yamma ta fita dani zuwa E damodaly Cleaning skin. Gyaran kai kawai aka mana, Se lalle haka, daga nan muka je Mall har zuwa dare, sauƙeni kawai tayi tana min alamu da se munyi waya. Kaina kawai na ɗaga mata ina wucewa zuwa cikin gidan namu, mask ɗin fuskana na zare dake indai zan fita dashi nake fita. Bayan kwana biyu kuwa iyayen Mohan suka kawo akwatina gidanmu, guda takwas sai kit, wasu azababbun akwati nane ƙirar Italy na zallan fata kalar pink, kayan dake ciki kuwa kama daga shadda, lace, materials, atamfofi, takalma ma kadai daga na kamfanin vincci, dg, poster, crishtian Dior, ga wasu shegun jakunkuna da jewelries duka babu ƙanana gaskiya ba ƙaramin ƙoƙari Mohan ko nace iyayen sa suka yi ba wajen haɗa kayan nan, sedai duk ni ba hakan ke a gabana ba nikam. Gaba ɗaya sema hankalina daya sake tashi, akan kusantowar bikin, duk ƙawayenmu sunzo sedai banda Nasma, wanda hakan yayi matuƙar ɗaure min kai, at last ma zan iya cewa ƙarshen magana na da ita, shine wani status da tayi cewan a taya ta murna za tayi aure. Sena tura mata da emoji na harara, tare da guntun short na rubutu, bata amsa niba a lokacin duk da kuwa cewar ganan ina kallonta online, Se daga baya ta min reply da wasu cukurkuɗaɗɗun kalmomin da suka gaza kauce wa daga cikin zuciya ta, don kuwa kalmomi ne masu kama da hannun ka me sanda, ko harshen damo. Tun daga lokacin kuma ban kuma ji daga gareta, kona ƙirata bana samu, ban kuma san ko miye dalilinta na yin hakan ba. Tin da na gama fahimtar take takenta se nima gaba ɗaya na fita daga rayuwar ta gaba ɗaya. Wata guntuwar ijiyar zuciya na sauƙe, idanuna na cika da wasu ruwan hawaye masu zafi. Tsam na miƙe tsaye na fara dawurwuri a cikin ɗakina, ni kaɗai a cikin zuciya ta nake raya cewar, _Ko zuwa yanzun Lolly ya duba saƙona?, ko kuwa be duba ba, shin idan ya duba saƙon nawa zuwa yanzun a wanne matakin yake?_ Se kuma naji gabana yayi wata irin yankewa yana faɗuwa haka kawai. Shigowar Ammey hannun ta ɗauke da wani bowl ne ya katse min tunanin dana faɗa. Ajje min tayi kan madubi daga tsayen da nake tana me furta. "Lallai ki tabbar kin shanye duka, kuma da yamma karki manta ki haɗe kayyayakinki, zaki koma gidan Auntynki Zeenatu dama na faɗa miki" Aunty zeenatun wata amintacciyar Ammeyn muce wacce ita ce ta fara zame mata dangi, a cewarta, wai sanda suka shigo garin Abujan, daga nan dangin ta suka zama nata dangin itama, sau da dama nasha zama in tambayi Ammey wai ina dangin mu suke ne, nata dana Pappu?, seta ce min su marayu ne, danginsu kuma suna can wata duniyar ta daban.... Da wannan na tashi bayan na shanye abunda ke cikin bowl ɗin kana na shiga haɗa ƴan komotsaina wuri guda. *BLUE RESTO BAR* Wani irin Babban lafiyayyen Hotel Bar ne da aka ware shi takanas don marasa jin ƙasar GOA ɗin, inda yake da rassa masu yawan gaske, sedai a cikin hotel ɗin ma ba kona ake iya ratsawaba ba a wasu wuraren dake cikin sa, kamar idan ka ɗauka ɓangaren Blue Resto Bar ɗin, duk kuwa to wanda ka gani a cikin wannan ɓangaren lallai to ka sani cewar wani ne na daban a cikin shegun duniyar, don haka tin daga farkon shigar AA ɗin yake ƙarema ko ina dake wurin da wani irin natsatstsen kallo, me cike da nazarta... Wani Dark personal parson Room ya nufa, ta hanyar Bluetooth ɗin dake manne a kunnensa dake bada ja da koriyar danja, ta haka suke masa kwatancen. Duk inda ze ratsa se anyi check na shi out, kafin a barshi yayi gaba, wasu shegun riga da wando ne a cikin sa baƙaƙe, sedai ko ina na cikin jikin sa a rufe yake ruf, babu me iya ganin koda kwayar idanunsa ne. A daidai bakin wata mahaukaciyar ƙofa yaja ya tsaya, kafin kuma cikin bin umarnin wanda yake bashi umarnin ya sanya hannunsa da suke ɓoye suma cikin handglov ya tura wannan ƙofar. Yana shiga wani irin dark blue night ɗin dake mamaye da ɗakin ne kusan zance ya fara masa sallama, warin ya shiga bi da ido, babu kowa a gaba ɗaya parsonal room ɗin, Se wasu shegun mahaukatan cough with sofa's in da suka zagaye room floor ɗin. Zaune yakai kan wata zebchair kamar yadda aka umarce shi, gefen sa ya kalla kamar yadda aka faɗa masan kuwa sega wani madannin dake gefen sa, ɗauka yayi yana dannawa take ko ina na ɓangaren ɗakin ya soma ɗaukar haske, sannu ahankali kuma wasu fuskoki maban banta ke bayyanuwa a cikin ginin ɗakin, kafin kuma kamar sauƙar aradu yaji wannan muryar me bashi umarnin yana me furta. "Da kyau ALIYU ABDULLAHI, lallai jarumta da kuma salon aikin ka na burgeni, tabbas zamuyi wannan tafiyar da kai, domin kuwa kwarai na yaba da salon naka aikin....." Se kuma mutumin yayi shiru yana zubawa AA idanunsa, shima don karantar yanayi sa. Wani kalan gyara zaman sa yayi tare da furta. "Menene yasa ba zamuyi magana fuska da fuska ba?" "Sabo da wurin bai dace da hakan ba, sannan kuma bana da lokacin ɓatawa da yawa. Kafin nan dai Aikin captain AA yayi matuƙar birgeni, abinda bamuyi tsammani ba shiya faru, aiki ne me kyau. Na yi matuƙar jinjina maka kwarai nayi matuƙar jinjinamaka tare da ƴan clab's nawa koba haka ba guy's???." " Yeah's" Gaba ɗaya suka haɗe bakin su wurin murta kalmar hakan a jimlarce. Shi kuwa ɓangaren AA, wani lalataccen murmushi ya saki yana me furta. "Idan na fahimta gaba ɗaya ayyukan da nayi a wurare mabanbantan kaine wanda ka bayar dasu?" Wani ɗan sara masa Boss ɗin yayi kamar a gaban sa tare da furta. _Da kyau BAD, wannan ma namu ne, domin yana da basira, haka zalika kwakwalwarsa na gudu ne fiye da tunaninsa ngd...." Se kuma ya ɗan shiru dan haka wani daga cikin su ya ci gaba da furta. " Tin daga lokacin bayyanuwarka,muka san ko kai wanene da irin sheke sheken da kayi, tabbas kana da TAURIN ZUCIYA, don haka muma shiƙar ce zaka mana gaya mana mecece ladarka? " Yay maganar yana ɗan janyewa daga jikin screen paper ɗin room ɗin. Wani Numfashi ya ɗan fesar tare da furta. "Ƙa'idata ni guda ɗaya ce kawai a biyani farashin, ba wannan ne abinda ƴan ta'adda kuke so ba?" Yay maganar yana ɗaukar Alcoholic drink ɗin dake kewaye gabansa, "Mu Ba ƴan ta'adda bane, mu ƴan kasuwane..." Ƙafarsa ɗaya ya ɗauka ya sake ɗorata akan ɗayar, yana me furta. " Ohh!!!, Miye da meye kuke sayarwar?" A wannan Karon kam Boss ɗin nasu ne ya furta. "Komai da komai, kamarsu, ƙasashe, gwamnatoci tare da tattalin Arziƙi, duka abinda yake faruwa mu ne nan muke tsara shi.. "POWER da kuma CONTROL" "No karkai tunani hakan, mu kawai rukunine da muke juya duk ƙasar da muka so, kana muna da mutane da dama da suka gama karaɗe ko ina a cikin duniyar suke mana aiki da kyau" Tsaye ya ɗan miƙe shima tare da soma ɗan jujjuya wa yana me furta. "Kawai ku biyani kuɗaɗe ku faɗi aikin da zan muku" yay maganar ne kuma yana komawa zaunen da yake ƙafarnan ɗaya kan ɗaya. "Ka sani wannan ba contract bane AA, wannan abu ne da yafi contract muhimmamci, domin kuwa muna so mu gwada tunaninka ne, domin mu baka wata babbar dama wacce inhar kai nasarar shallake wa to kuwa tabbas zaka zamo ɗaya daga cikin rukuninmu....." "Se dai ni nake yankema kaina abinda nai niyya" Boss ɗin ya sake magana har yanzun, tare da burta "Daga lokacin daka tinbatsa baka da damar yankewa kanka abinda kai niyya, domin kuwa hatta da ƙasar taku se abinda muka tsara take yi....." Yaƙin cigarettes ɗin daya kunna ya fesar, tare da furta. "Menene abinda kuke buƙata?" Wani shegen murmushi *SNAKE EYES* ya saki tare da sake furta. "Da kyau AA wani ƙasurgumin jami'in soja ne!, wanda kuma ya kasance me taurin zuciya irin ka, shi zaka sheƙe mana...." Wani lumshe ido yay tare da buɗe su tar akan dukan su, yana me furta. "Ba mamaki a baya na taɓa aiki ko?" Se kuma ya ɗan jijjiga kansa yana daga zaunen da yake tare daci gaba da furta. "Badamuwa" Ya furta tare da miƙewa tsaye yana fuskantar duka mutanen dake kewaye da room ɗin, amma ta cikin jinin ɗakin, Se kuma ya zube duka hannayensa cikin aljihun rigar sa tare da furta. "Wanene wanda kuke da buƙatar a sheƙe ɗin?" yay maganar da alamar tambaya. "Juya yana bayanka" yay maganar yana ɗaukar drink energy ɗin dake gaban sa yana ɓalle murfin ta ya zuƙa, Wani kaikaitaccen kallo AA ɗin ya masa, ta cikin ɗakin tare da kafe drink ɗin dake hannun Snake Eye ɗin, Se kuma ya juya bayan nasa a natse, take yay ido biyu da CHIEF OF ARMY dake ɗauɗɗaure. "Idan ka sheƙe shi, Wannan shi ne abu na farko da zai sanya ka zamo ɗaya daga cikin mu....." haka ya sake jin maganar Snake ɗin tamkar sauƙar aradu da rugugin tsaya..... Cikin wani irin taku na kamar ze tashi sama ya nufa inda chief ɗin yake ɗaɗɗaure, tare da tsaiwa a kansa yana ƙoƙarin riƙo hannun ogan nasa a da. Bayan ya kwance masa hannayensa, tare da buɗe masa baki, kaɓar da hannun nasa chief yayi, tare da ƙaƙaro wani kake ya tofa a fuskar AA ɗin, wanda yay saurin juyar da kansa gefe.... "Ɓarayin banza shashashu marasa amfani da nemar aljanna, to ku sani babu abin da zaku iya...." A wannan Karon kam wrong number ne ya furta. "Da wa yace zamu ma wani abu?" Boss ɗin nasu ne ya miƙe tsaye a karon farko kamar ya tsago bangon ya shiga ɗakin, tare da taryan numfashin wrong number ɗin ta hanyar furta. "Me yasa bazaka fahimta bane?, duka muna wannan abin ne domin neman duniya, babu wanda yake yi da zimmar neman samun ladar aljannah..." _Tubbb_ "Da banzan shashasha kuna matsoraci, wanda ya je ya laɓe ko fuskarka ka gaza bayyanawa, kuma a hakan kake tsammanin zaka iya juya ƙasar tamu?....." wata mahaukaciyar sheɗaniyar dariya duka suka fashe da ita, tare da nuna shi da yatsa, Wine block ne ya furta." Matsalar ƙaramin tunani kenan, ana maganar duniya waye yake ta wani Nigerian’s ɗin banza..... " 🙌 Da wannan alamar Boss ɗin nasu ya jinjinama Wine block ɗin.... Kamar kuma wata almara, kamar a shirin film duka mutanen jikin ginin ɗakin suka ɓace. Suna ɓacewar kuwa AA yay hanzarin zubewa gaban chief ɗin yana warware duka ɗaurin dake jikinsa, yana miƙar dashi tsaye. Janye jikinsa ana AA ɗin chief yayi tare da furta "CAPTAIN me kake shirin aikatawa ne haka?.... " Sir zan tseratar da kaine kamar dai yadda aka saba..... Wani murmushi me ciwo da ɗaci chief ɗin yayi, tare da furta. "A wannan karon kam baka da wata mafita ko zaɓi *CAPTAIN KAMAALA ASHFUD RAHIM DAWOOD, dole ka sheƙe ni....." yay maganar ne kuma ba tare da ya tsaya dubar koya reaction na AA ɗin yake ba, Shi kuwa yana ambatar KAMAALA ASHFUD RAHIM DAWOOD, ɗin yaji wutar kansa tayi wani irin ɗauke wa, amma kuma yana kawar da tunanin hakan a cikin ransa, dan sau da dama yakanji wannan sunan na masa amsa kuwwa cikin kunnuwansa, don haka ma yanzun ya bar hakan a ire iren wannan amsar kuwwar ne kawai, yana dawowa cikakken hayyacinsa tare da furta. "Sir kafi kowa sanin bana ƙarɓar umarni...." "Stop My friend!, Shin dama ba seda na taɓa gaya maka ba, cewar wannan aikin shi ne mafi haɗarin da zaka taɓa tinkara a kaf cikin rayuwarka baki ɗaya ba?..." Yay maganar yana tsare AA ɗin da idanunsa, saurin kawar da nasan AA ɗin yayi tare da furta. "Da akwai wata mafitar yallaɓoi...." "Wannan ita kaɗai ce mafitar mu, domin kuwa ko baka sheƙeni ba, dole su zasu sheƙe ni Captain, da mutuwa a hannun azzalumi ƙara mutuwa a hannun adali me zuciyar lu'u-lu'u irin ka KAMAALA, idan kayi hakan zasu fi yarda da kai, kai kuma ka sami damar kutsa kanka cikinsu, ka harbeni......" Kansa yake jijjigawa idanunsa na taruwa da abinda besan ko miye shi ba, kafin cikin wata murya me kama da rauni ya furta. " Kaima ka sani bazan iya ba yallaɓoi, kayi tunani akan irin ka da kuma ni, kaifa Sojan ƙasa ta ne, kuma shugaba na, nima Soja ne. Idan muka tsaya muka yi nazari muna da wata mafitar, bawai muyi ta sheƙe kawunanmu sabo da tsoron ƴan ta'adda ba yallaɓoi...... " " Ka sheƙeni Aliyu, umarni nina ne wannan ɗin.... " Cheif yay maganar ya tsawa ce, wanda ya sanya AA seta kansa da bindigar dake hannunsa, wacce da zai shigo aka bashi a ƙofar ƙarshe. " Bazan iya ba yallaɓoi" AA ɗin ya sake faɗi wannan abin da yaji ya cika idanunsa na nemar zubo masa, sedai ya hana hakan iyuwa kasancewar ya san ruwan hawayene zasu zubo. Cikin cira sauti da ɗan ƙara ji da zafi a maganar irin na sojoji chief ɗin ya sake furta... "Ka tuna da alkawarin daka ɗaukarma ƙasarka, da kuma alƙawarin daka ɗaukar min kafin fara wannan aikin. Idan baka sheƙeni ba, to ka sani kamar kaci amanar ƙasar kane, domin ka samu damar da zaka iya ceto ta amma son kai ya hana ka hakan Aliyu, dole seka shiga cikin rukuninsu, sannan zaka iya gano ko su waye da waye a cikin rukunin, sannan har ka iya kawo ƙarshensu ka magancesu, kayi wannan abin don ni!, kuma don ƙasar ka...... " Yay maganar ne kuma tare da kamo bindigar hannun AA ɗin ya seta a goshinsa yana me furta. "Mutuwa kafin zubewar mutumci!" Cheif ɗin ya faɗi ya faɗi idon sa a cikin na AA. "MUTUWA KAFIN ZUBEWAR MUTUMCI " shima AA ɗin ya faɗi muryarsa a rarrabe. "yin aiki kafin son kai!!" Cheif ɗin ya sake faɗi. "YIN AIKI KAFIN SON KAI!!" "Nigeria a farko!!!“ Ya sake faɗi. "NIGERIA A FARKO!!!" Ya faɗi hakan tare da maida kansa ƙasa, ahankali tare da sake lumshe idanunsa, wanda cikin su ke bayyana abubuwa da dama... Bindigar ya cira tare da harba ta sama har sau uku, tare da furta. "Karka manta Sir,kai ne kasha faɗa min cewar _A cikin wannan zamanin da muke ciki a yanzun, ya zama dole seka zama jarumi a cikin rayuwar waɗan su, sannan kuma dole seka zama uban daba ata waɗan su.... Don haka daga yau ka ɗauka cewar lokacin mutuwar ka ze fara a yanzu, wanda mukullin buɗe hakan yake a hannunsa. Kawai ya sake harba bindigar sama, tare da cilla wani fari ƙal ɗin hankacif saman fuskar Cheif ɗin....... Araoun 12th pm ♡ AA zaune yake tin bayan dawowarsa daga blue resto bar ɗin, yake kan iPad nashi, yana gudanar da wasu muhimman ayyuka, yana cikin aikin ne kuma kamar daga sama yaji ƙaran shigowar messenger cikin Samsung nashi, dage gefe dashi, sunan Pappu daya gani ne ya sanya shi ajje iPad ɗin, yana ɗaukar wayar nashi. Akan rubutun dake kwance jikin screen na woyar nashi idanunsa kai tsaye suka sauƙa. _Ka gafarceni KAMAALA ASHFUD RAHIM DAWOOD KAMAALA, Na hasalin ɓoye maka ko kai ainihin waye da nayi, Kai ɗin cikakken ƊA NE ga me Martaba sarkin mu, Sarki me adalci, wanda duhun wasu zukutan ya sanya suka kawo ƙarshensa, Mahaifinka ASHFUD Ƙasaitaccen sarki ne da yake gudanar da mulkin ƙasarsa cikin wani irin aji da kuma kulawa cikin kamala, Sarkin da yasha banban da dukkan sarakunan da sukayi shura da kuma mulkin ƙasar kafin shi, sarkin daya kawo gagarumin sauyi ya kuma canza garin dama wasu ƙetare na ƙasar gaba ɗaya, daga irin mulkin kama karyar da ake gudanarwa da ire irensu a can baya,zuwa wata sabuwar duniya da tasha banban da kowanne zamani gaba ɗaya. SARKI ASHFUD Ƙasaitaccen sarkin ne shi ma'abocin izzar dake barazana tare da kaɗa zukatan duk wasu masu zuciya biyun dake zaune dashi a wancan lokacin , Mahaifinka ASHFUD KAMAALA Rahim DAWOOD, Ƙasaitaccen SARKI ne da iya ka kwarjinsa yake iya keta kowanne hijabin dake lulluɓe da magautansa, .Me girma SARKI ASHFUD KAMAALA RAHIM yana da wata irin ƙasaitar data dasa shakku da kuma tsoronsa da a cikin zuciyoyin magautansa, kwarjinin daya zama wanzajjen abu dake matuƙar tasiri a wurin masu ɓoyayyun fuskokin dake zagaye da fadar UMMULYOODAH, ya kuma sanya zukata da yawa sallamawa....... Me Martaba Sarki ASHFUD KAMAALA RAHIM DAWOOD, Yana da wani irin qualities tare da wata irin ZARRA me tafe da jajircewa. Amma duk da haka be tsira ba daga iyaye da kakanninsa, har seda ya zamana sunga bayansa ta hanyar raba shi da duniyar baki ɗaya, ka tuna da can baya, ina yawan baka wani daddaɗan labari, akan wasu marriage couple's, to waɗan nan ɗin ba kowa bane face mahaifiya da kuma mahaifinka, kaje tana nan tana dokon tsimayin jiranka, tana dokon jiran kaje ka nuna musu kai ɗin KIBIYAR AJALI NE, WANDA SULƘE BAYA IYA RATSAKA, Ka nuna musu kai ɗin jinin ASHFUD KAMAALA RAHEEM DAWOOD KAMAALA ne, ka nuna musu cewar kai ɗin jeji kake kafi gaban Ayi maka ƙyaure, Ka kuma nuna musu cewar Jan zaki kake me maganin Abokan gaba, ka nuna musu duhun dare kake me ɓatar da Rigar sarki, Sarari mai ƙare gudun doki. Ka nuna musu cewar lokacin dana ɗibar musu ALLAH yayi, ka Amshi Masarautarka ta

Chapter 20 of 23