ta miƙe tana mitar wllh ba zai sha mata iyaka COFFEE ba yau dan ma yaji da wai.
"Ya fama da aiyuka Aliyu?"
Abbu ya faɗa yana fuskantar yaron nashi. "ALHAMDULILLAHI Abbu Naaaaaa muna ta fama dai"
ƙara duban yaron nashi da kyau Abbun yayi yana me sake faɗin.
"kiddnapping ɗin nan da akayi na canal wllh sosai ya taɓani Aliyu, wa ku jami'i ai ma fa kenan? Ina kuma ga sauran Al'umma tin da har suka fara ta kan manyan jami'ai irin su canal bappah, na rasa mene mutane suke naima har haka a cikin wannan duniyar, dan ALLAH Zaki a tsananta binciken nan!, ga mutuwar abokin aikin nan naka Sameer shi fa" ya ƙare zancen cikin muryan tausayi tsantsa. Shi kuwa A A cikin ladabi irin nashi da girmama maganar mahaifin nashi yace. "IN SHA ALLAH Abbu zanyi iya yina iyaka tsanani kuma, har kamo gaskiyar wannan cukurkuɗaɗɗan al'amari ya baiyana kansa IN SHA ALLAHU"
"ALLAH ya shige gaba a dage Sosai Kamaala" Abbu ya faɗi wanda jin sunan da Abbun ya ƙira shi dashi ya sanya Seda ya ɗago ya kalle shi, inda shi kuma Abbun ya nuna irin bema san abinda ya faɗa ɗin ba.
"Ameern ya rabb, IN SHA ALLAH zan tsananta Abbu" ya amsa yana aiyana abubuwa masu dama acikin ranshi, barin ma *KAMAALA* ɗin da ya ƙira shi dashi, domin se yake jin tamkar sunan nashi kenan, kuma ya sha amsa wannan sunan a darare da yawa cikin mafarkan da ya kan saba yi sau da dama. Fitowar Ammey daga kitchen, hannun ta ɗauke da plate with cup ne ya sanya shi dawowa daga ɗan takaitaccen tunanin da ya tafi. soyayyan cheef ta haɗa mishi da tomator ta soya mashi sama-sama, da kuma haɗaɗɗan coffee nashi, wanda yasha kayan ƙamshi, gaban sa ta ajje masa kai tsaye tana zama a nata wurin zaman. Inda Abbu ya furta. "Ummmm iyeee kaga ɗan gatan ammeyn shi ba, shi ne ta ware ka kai kaɗai ɗin ta soya maka abu me daɗi mu kuma ta bar mu da ɗumamen tuwan jiya se black tea" Abbu ya faɗi hakan yana shafa kan yaron nashi.
Wani smile ne ya kwace mishi wanda baiyi niyar barin sa ya fito ba.
Iya tsanani kammm suna ƙaunar junansu babu laifi, Hankali kwance yake sipping coffee nashi Sannu a hankali, har yayi rabin cup ɗin ajjewa yayi kana ya janwo plat na soyayyan cheese nashi.
lomar farko da ya kai ne yasa shi wani ɗan lumshe luhu luhu eyes nashi tare da rolling na eye balls nashi, daɗin abin na ratsa duk wata sassa da gangar jikin shi zuwa saman harshen sa. Ya sani tabbas cewar
*AMMEYN SHI* gwanace wajen iya sarrafa girki, ko yaya tayi girki sai kaji kamar kada abincin ya ƙare...
Suna kammala dinner nasu yama iyayen sa sallama kana ya wuce wurin aikinsa, kasancewar shi ne da alhakin wannan cese ɗin. Directly Computers rooms nasu ya nufa yana wannan tafiyar ta cikakken namiji, kana ganin tafiyar kasan tafiyace ta zaratan mazan gaske. yana shiga room ɗin cikin girmamawa gaba ɗaya suka miƙe suna ƙamewa, hannun su saman goshi nan su.
Kai kawai ya ɗaga musu yayi abinda zaiyi yafita abinsa yama bar ɗakin baki ɗaya. Cikin motor shi ya nufa da kuma da fitowan nashi inda alamu suka gama nuna wani wuri ya nufa. Har wasu daga cikin soldier's na ƙoƙarin rufa masa baya amma ya dakatar dasu, tafiya yake cikin kwanciyar hankali da tarin nutsuwarsa. Ahankali yake mirza starryn motorn, yana bin sautin karatun alquranin dake tashi acikin motar na Afif Muhammad taj.
Gaban wani Lafiyayen plat house yayi parking car nashi. Inda gidan ke zagaye da wani irin tsaro na musamman, kai tsaye suka buɗe masa get na gidan ganin shi ne da kansa. Cikin harabar gidan ya nausa da ƙatuwar motar shi kai tsaye, sai da yayi kamar minti biyu sannan ya diro daga cikin motar, Sanye cikin kakin sojojin daya gama amsan jikin shi ya fito, Se p-carp ɗin dake kansa inda ya ƙarama Kyakkyawar fuskar sa kyau da zati. Izinin shiga ya aika a tambayo masa jin ko waye kuwa yasa take aka bashi umarnin shiga cikin gidan. da Ƴar sassarfa ya nufi cikin babban parlourn gidan, Manyan mata ne biyu zaune a ƙayataccen parlourn daya gaji da haɗu wa, Se wasu samari da suka fi kama da twins ne, Se kuwa wata matashiyar budurwa wacce shekarunta na haihuwa ba zasu wuce 21 zuwa 22 ba se kuwa yara su uku irin tafi in bika ɗin nan. Da sallama ɗauke a bakin sa ya shigo Parlourn, inda gaba ɗaya mutanen parlourn suka ɗago suna kallon mai sallamar haɗi da amsawa. Gaida shi suka shiga yi saboda tsabar kwarjinin daya musu, a natse ya amsa su yana sake tambayar su Canal ɗin baya da wasu abokan gaba ko a cikin abokanansa haka?, duk suka amsa suna cewa gaskiya basu sani ba kawai dai yan ta'addar ne suka ɗauke shi. Daga haka ya musu sallama bayan ya bama ɗan ƙaramin yaron da tin da ya shigo rafas na kuɗi.
daga nan wurin aikin sa ya koma yaci gaba da bibiyar shige da ficen kowa daga Headquarters ɗin, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya saki loƙacin da yaci karo da wani abinda ya hargitsa tunaninsa dama lissafin sa. Yana nan zaune ƙira yashigo wayarsa CHIEF Of ARMY, shine kwance saman screen ɗin wayan nashi, Cikin girmamawa ya amsa ƙiran yana karawa a kunnenshi.
"Ka shigo office nawa yanzun ina son ganin ka, daga haka ya datse ƙiran. Ko second be ƙara ba ya fita yana bi ta elevator yanda ze fiya masa saurin isa.
Cikin wani tsararren babban office ɗin da yafi kama da building elevator ɗin ta tsayar dashi, inda sunan *CHIEF OF ARMY STAFF* (COAS). Ya bayyana ɓaro² gaban door na office ɗin, Kai tsaye ya shige office ɗin cikin tafiyar nan ta mazajen fama mazajen gaske wanda ruwa,iska,tsanani, bayasa su gudu a filin yaƙi. Yana jin knocking haɗi da sallamar AA ɗin ya sauƙe wata ijiyar zuciya. bayan daya gama ganin komai ta glasses ɗin, ɗakin wanda aka seta da ctvv Camera na ɗakin, kan kujerar sa yakoma yana kuma sauƙe wata ijiyar zuciyar again. Da wurin zama ya masa nuni inda daga nan suka juye baki zuwa wani yare na daban, sun ɗebi wasu time masu yawa kafin su gama tattauwar da su kayi, inda ya dinga hashaska masa wasu wurare da wasu mutane tare da masa bayanansu da wasu yarukan da AMMEYN LAYLERHNKU ta gaza ganewa.... Daga ƙarshe ya miƙe yana sara masa, inda shegen Chief ɗin nan ashe yana jin hausa, Seda yaga AA ɗin ya miƙe kana ya furtam
"Captain AA kana ganin wannan karon ba zaka bar wannan aikin a hannu naba kuwa?, domin ta ko ina rayuwarka kewaye take da magautanka, kana ganin wannan karon ba zaka fito musu a mutum ba, domin ganar dasu RAMIN KURAR da suke shirjn jefa kansu?" Hannayensa ya AA ɗin ya miƙar tare da lankwasa su, cikin girmama ogan sa, wanda yake masa kallon tamkar mahaifi ne a wurin shi yace.
"Kabar komi a hannuna sir. Kamar dai kullum ɗin, kada ka manta niɗin horon kane. dan me kakejin kamar zan gaza wannan karon ma, Fito musu a mutum kuma ba shi ke nufin kawo ƙarshen ire irensu ba, ta hanyar rainin hankalin da suke bi muna ta hanyar ne zamu bi domin tarwatsa zukatan su, idan kuwa muka ce zamu fito musu a mutum ɗin hakan ba shine mafita ba, domin hakan bazata taɓa sanja rawa ba, Idan zaka kama tsuntsu mai wayo ta wuya ake kama shi sir, Idan tsanani ya yawaita, akwai bukatar rikiɗewa ka zama shaiɗani domin kawo ƙarshen sheɗanai...."
Ya faɗi maganar yana kallon wani gefe daban,ba kamar da da yake kallon chief of army ba. Da wani irin kallo chief of army ya shiga bin AA dashi, kallo ne irin na alfari lalle sai yanzun yake sake yarda ɗari bisa ɗari tabbas wannan ɗin renonsa ne ba kamar sauran ba, kai ya shiga gyaɗawa yana tafa hanna yensa yana faɗin. "weldone zaki weldone lion haka akeson mazan gaske tamkar dai kai ɗin nan" Sajen fuskar shi yashiga shafawa haɗi ta faɗin
"wannan ɗin *horonka ne* sir."
Tare da sake sara masa cike da wani irin girmamawa yana fita a office ɗin duka.....
3 day's
Cikin wasu haɗaɗɗun riga da wando na campanyn Christian Dior saddle brook ya fito brown se ɗaukar ido kayan suke, ba ƙaramin amsar jikinsa kayan suka yi ba, abinka da cikakken namiji me jini a jika da ɗan sassarfa yake saƙƙowa daga stair ɗin, Zazzaune ya samu su Ammeyn sa tare da nufaisa kasancewar weekend ce yau ɗin, zama yay tare da gaida iyayen nasa yana yin Breakfast nashi, ya ɗan jima a zaunen suna taɓa fira kafin ya musu sallama yana cewa ze leƙa companies nashi. Da fatan alkhairi iyayen nasa suka bishi, inda shi kuma kai tsaye yana nufar inda tarin car's nashi suke, soldiers din dake harabar gidan ne suka nufo shi suna ganin fitowarsa, da hannu ya musu alama su dakata, tare da nufar wata mahaukaciyar black merkadez benz ya hau. Kai tsaye ya cilla hancinta Saman kwalta yana nufar
katafaren unguwar asokoro wadda take nan da manya manyan ƙerarrun gine gine na zamani, duk inda ka kalla zaka so kara kalla a wurin, domin kuwa tamkar ba'a Nigeria ba haka anguwar take, ko ina ka ɗaga idanu ka kallah sai ka ji baka son kawar da kanka daga wannan wajen, tsaruwa iya tsurwa, haɗuwa iya haɗuwa kammm anguwar ta gama haɗu wa. Gaban wani shegen gini yayi parking tare da danna zira card ɗin dake hannun sa, take wurin ta buɗe ƙaton jibgegen get ɗin. Kai tsaye ya danna hancin motor nashi zuwa cikin gidan. Haka ya shiga ratsa get kusan ukku, kana yay parking a wani shegen parking space ɗin da ya gaji da haɗuwa, inda suke shaƙe da wasu shegun tsadaddun motoci, tamkar companyn kera motoci haka wurin yake, kowani mota ka ɗaga idanu ka kallah sai ka sake kallah saboda tsabar tsananin kyau da tsadar motar, kallo ɗaya zaka ma dogon ginin da yafi kama da masarrafin kera motoci. A kusa da wata car wacce ta gama nuna cewar ba'a dade da hawan ta yay parking tashi car ɗin, Wani basamuden mutum ne ya fito daga wata hanya yana fito masa motar, cikin zallar izza ya fito yana ƙara gyara zaman p-carp ɗin dake saman kansa, wanda lallausar sumar kansa ta fito ta ƙasar ƙeyarsa.
Ya Ilahi wannan gida kacokam ɗinsa saidai mu ƙirashi da aljannar duniya, ga wasu haɗaɗɗun beneye wajen hawa ashirin da wani abu. Wanda hakan yake nuni da cewar ko dai wata masana'antace aka gina kuma ba'a buɗe ba, kodai irin suit hotel ɗin nan ne, tafiya ya soma cikin tsananin zallar iya sarrafa tafiyar kanta, wannan matashin na take masa baya, wata rantsatstsiyar ƙofa ya dosa wannan karon ma da card ɗin yayi amfani, take kofar ta buɗe sai gashi cikin wani irin azababben parlour, Baki ɗaya parlourn ɗauke yake da wasu uban lumtsuma lumtsuman kujeru wajen set huɗu, ga ta ko ina na parlourn kewaye da na'u'rorin sarrafa abubuwa, gaban wata kerarriyar ƙofar glass ya nufa, bayan ya shiga cikin lifter ɗin ya danna Black C floor 13 zuuuuuuu lifter ɗin tayi ƙasa dashi idanunsa Lumshe a haka har ta kawo shi floor ɗin, still wasu kofofin da suka kusa kwance kai na ya kuma nufa, nan ya ringa ratsa parlouna yana wucewa har ya isa gaban wani ɗaki da yafi kama dana masu bada horo.
Nan ma Saida yayi amfani da card kafin kofar ta buɗe ya sanya ƙansa cikin ɗakin, tare da ɗan yin baya da blue jacket ɗin dake saman shigar sa.
Cikin ginshira dajin kai captain AA da ya kai zaune cikin kebantaccen Ross glass ɗin dake wurin, ya miƙe
tsaye ya kan diga digansa. Wannan matashin ne ya farkar da mutumin dake ɗaɗɗaure da manyan igiyoyi, kai da ganin mutumin kasan A jigace yake gashi kuma babban mutum, dan Aƙalla zai iya kaiwa shekaru sittin da ɗori, jikin sa duk yawani cakuye fatar tayi laushi sosai na tsabar hawaltuwar da yayi. Yau kimanin 6 days kenan da kawo shi nan gurin, kullum sau biyu ake bashi abinci a rana safe yamma,
Yunwa duk tabi ta cinye mashi ƴa ƴan hanji, tin da kuma aka kawo shi wurin kuma wani kafirin mutum ɗaya kawai yake ta gani, babu duka babu zagi sedai zaman wuri ɗaya da ɗauren da yake.
Cikin takun nan nasa yake tunkarar mutumin. Wata farar kujera ya ja zuwa gaban mutumin. P-carp tare da shade ɗin daya ɓoye baiyanuwar ainihin fuskar sa kai tsaye ya zare sahde ɗin. haɗi da zare p-carp ɗin ma baki ɗaya, wanda ya sanya mutumin dake daddaure saurin wani irin kwalalo idanuwa waje. Wanda ya sanya Captain AA sakin wani cutie smile, yana ɗaga mishi gira ɗaya alamar yadai ka tsorata ne?.
Cikin zallar tsagwaron mamaki Kanal bappa babayo ya shiga nuna captain AA ɗin da hannuwansa yana faɗin.
"AA! AA!! AA!!! kai ne, kai ne kasa akayi kiddnapping nawa tsayon wannan loƙacin?.. Hannuwansa ya harɗe a ƙirjinsa fuskansa shimfide da murmushin daya masifar sake fito da tsananin kwarjininsa, yana me furta.
" Hala kasha kai ɗaya ne mutumin da ya iya buga wasa ko?" Cikin zallar nuna isa da nuna ya isan yayi maganar. Ganin yadda Kanal ɗin keta motsa bakin yana son yayi magane ya sanya AA furta cewa.
"Kar kayi magana a loƙacin da babu abin faɗa, koda da abin fadanma kasani shuru bai taɓa zama illaba, rayuwar duniya kamar series film haka take, episode episode take zuwa, amma duk yawan film ɗin dole ne ya ƙare wata rana" Wani kalan duba Kanal ɗin yama AA tare da furta. "Lallai da dukkan alamu baka san RAMIN KURAR da kake son jefa kanka ba AA, Kai Yaro ne, sau da tari wasu loƙutan kana ganin kamar kayi nasara shine faɗuwa, haka ma wasu loƙutan ka yadda ka faɗi shi ne nasararka" Kafafunsa dake a harɗe ya gyara zaman su tare da cewa.
"Kanal ina son ka sani cewar sawa a rai ne yasa falke baya jin wahalar tafiya, kunce yanzu aka fara buga wasan, don haka nima nace bari in shigo mu fara tare don da dukkan alamu wasar za tayi armashi sosai...."
"Ita fa Duniya kamar jirgin ruwa take, zata iya kaika inda kake so, kuma zata iya kaika inda take so. don haka be careful respect your self yaro, ba lallai a wannan karon ta kaika inda kake so ɗin ba kuwa, domin baka san irin masifar da kake son jefa kanka ba..... "
"Bani da loƙacin ɓatawa loƙaci loƙacin sa ƙungiyar _Buried Bo-Death_ tana da ɓoyayyun ƴan wasa kuma kana ɗaya daga cikin su don haka nake son ka bani bayanai akan ko su waye su, tamkar yacce ka saba basu namu muna, ina da buƙatar ka bani na sun nima..." wani razana Kanal ɗin yayi ta yaya aka yi wannan tsageran yaron ya san hasalin sunan ƙungiyar nasu?, lallai ya sake yarda wannan yaron ba ƙaramin tantiri bane....
Amma kuma cikin basarwa da taurin zuciya da taurin rai irin nasu na manyan soldiers, ya shanye tsoron nasa sema kallar AA ɗin da yayi tare da furta. "Kayi kuskure ko kaɗan ba haka bane AA"
"Su waye ragowar sauran?bayan kai?" "Ta inda ka samu sunan ƙungiyar ta nan ya kamaci ace ka koma da baya ka gano ko su waye hasalin masu ƙungiyar ko kuma su nawa ne..... Aikawa take AA ɗin ya take wayar wutar lantarkin da dama da ita ne suka daddare shi ɗin. Nan take ya tinka kakkafewa jikin sa yana san dare, Yana janye ƙafar nasa ya zaro pistol nashi daga bayan wandon shi yana harbin ƙafar Kanal ɗin. Nan yaci gaba da gana masa ba kar azaba. Wata irin jijjiga jikin Kanal ɗin ya shiga a wani kalan mugun galaɓaice ya ce. "Na rantse AA bansan minene abinda kake magana a kai, dan ALLAH ina rasa fa jini da yawa ka ƙira motar asibitiiiiii" igiyar lantarkin ya sake take wa da ƙafarsa tare da furta ka faɗamin su waye ƙungiyar _Buried Bo-Death_ sena ƙira motar asibitin yanzun.... " yay maganar yana janye ƙafar nashi.
Jikin sa na mugun shocked ya shiga faɗin."Mutum uku ne su kwara uku ne na rantse.... A ɗan zafafe wannan karon ya sake tambayar shi da."Su waye?" kansa yake jijjigawa yana kuma kallar yanda ƙafarsa ke zubar da jini, jikin yanayi na soma fita a hayyaci ya ce. "Ni kawai iya mutumin da nake bama bayanai na sani ka yarda dani" "Miye sunan shi wanda kake bama baya nan ina da bukatar sunan..."
"FATA ABDUL-PHATA Neeeee" Cikin rashin tausayi da imani AA ya sake take igiyar nan ya shiga ihu yana cewa don ALLAH ya bar shi ya kyale shi.....
"Kaine ka bashi bayanai akan Sameer ba?" ya sake jeho masa wata tambayar, tare da seta kansa da pistol ɗin dake hannunsa. "A ahhh karka sheƙeni ka bani dama AA zan maka ƙarin bayani plsss.....
Wata shegiyar dariyar dashi kansa AA ɗin baisan zata zo masa bane ya sheƙe da ita. Yana tafa hannayensa tare da ɗan dakata wa kuma yana me furta. "Aikuwa zan baka a jahannama.....
Ya sake harbin ɗayar ƙafar Kanal ɗin, wanda ya sashi sumewa nan take, Uban naushin da yaji an sauƙar masa saman fuskar sane, ya dawo dashi hayyacin sa da dawowa duniyar mutane ba ta sumewar daya tafi ba. " Captain AA ina son ka tuna cewar tare kake da Kanal bappa babayo, shi da matsayinsa kake duka a dokance ka saɓa aikin hukumarmu ta soldier..... " Kai nake duka, kana kuma kai nake taɓa wa ba matsayinka ba, kana bada gudun mawa a sheƙe wani jami'i shima saɓa shari'a ne, amma banda ƙalubalantata akan aikina da kuma ƙasata, duk kuwa wanda yake da zarrar hakan bismillah, Ni nan da kake gani tsaye a gaban ka gaba ɗaya hawayena na ƙasata ne, ina son kasa cewar NIGERIA tamkar zuciya ta ce. Duk kuma wanda ya sake yace ze yi min wasa da zuciya ragargasa nake.........
" A ahhh captain Aliyu za kayi nadama daga baya mutanen suna da matuƙar hadari, kashe ni kuma tamkar ruguza ahalinkane, da tarwatsa Nijeriyar kanta, kana ina son ka tina da ƙarfin ikon da kujerata take dashi...." ƙafar sa ya sanya ya take jikin kujerar da Kanal ɗin yake tare da cewa.... "Ƙarfin ikon ba'a kujerar yake ba, ya ta'allakene ga ƙarfin na kan kujerar wannan tabbatacce ne, ka sani tin farkon fara wasan bana da runduna haka bana da ayari domin datsa makiya, Ni kaɗai na zarta wadata, ni rundunane, jikina shi ne makamina, sanyawar albarkar al'ummata kuma shi ne ƙarfin zuciya ta tare da adda'ar iyaye da sanyawar albarkar ALLAH..... Duk sena ruguza masu tsohon buri ire irenku, wanda son zuciya da nemar duniya yake sanya wa idanu ku su rufe, bayan kashe kashen rayuwakan da kuka sawa akeyi ta ƙarƙashin ƙasa! A baiyane kuma wai kune masu bama al'ummar tsaro, Shinku ko kunya wai bakwayie?, bakwa tunanin idan kun mutu kuma me za ku ce da mahaliccinku?" daga haka ya seta gun nashi take ya fasa kan Kanal, wannan basamuden ya ƙira su kayi wata magana cikin wani juyayyen yare, abinda kawai na gani, shine a kafada wannan basamuden ya saɓi kanal da rai yayi halinsa yana fita da shi daga gidan baki ɗaya.......
Hhhhhhhhhh to ai shikenan 😅🥰 A gimtse 🫰 🙃♥️✅
*BY AMMEY LAYLERH ✍️ ✅*
🤙 Or WhatsApp
08104493215
Tofa wannan shine ana dara ga kuma dare yayi
༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻
# 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Book One paid
♡
Page 23&24
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
# HE WILL FIGHT
# Yakin sunƙurun ummih
*Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank*
♡♡♡♡♡♡♡♡
ꨄ A washe garin ranar wasu masu ɗibar bola suka ga wani abu da yafi kama da gawa a buhu, don haka kai tsaye suka ƙira wata kotun ƴan sanda mafi kusa da wurin suka zo suka gani, ana buɗe wa aka ga gawar Kanal Bappa babayo ce kumshe a cikin bahun. direct headquarters suka ƙira suka sanarmawa, nan fa gaba ɗaya media ta hargitse, kafin kace mene Sega ƴan jaridu sun cika wurin, yan sanda da sojoji na aikin su suma na nasu aikin na yada Labaran tsintar gawar kanal ɗin da aka yi a safiyar ranar, da shine ya zamewa al'umma kalacenta na safe a ranar........ Inda duk da ganan harbin bindiga a jikinsa amma seda lokacin dake cikin sojojin nasu suka sake check na jikinsa, sedai shi kam tasa ta ƙare, domin kuwa ko gezau beyi ba har suka ƙaraci aune aunensu, sedai shi ko a jikin sa bai motsa ba wai an mintsini kakkausa, don wannan rubutacciyar ƙaddarar da aka sanya alƙalamin da baya ƙarya aka zana wa'aɗin da aka ɗibarma wannan ruhin ya cika, sedai akwai sanadi!!! Ehhhhh tabbas akwai sanadin hakan don haka yanzune ma suka sanya ɗan bar binciken case ɗin.
ꨄ
Ahankali ya zuro da ƙafafunsa waje wanda suke sanye da wasu tsadaddun takalma irin na sojoji, cikin nutsuwa ya gama fitowa daga cikin motar, sanye yake da wando irin combat ɗinnan amma na kakin sojoji, sai kuma wata black t shirt me kauri daya saka ajikinsa, a kansa kuwa sanye yake da facing cap wanda take itama na soldiers ne, wanda kallo ɗaya tak zaka masa kai a karan ka bama kanka amsar ko wanene shi, wato jajirtacce kuma tsayayyen Namiji, wanda haɗuwarsa ya zarce duk wani misali, yana da wata irin murɗaɗɗiyar surar jiki abun burgewa,uwa uba kuma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 23