yake buƙata anan gaba ba tare da wata tangarɗa ba.
Goran ruwan dake a Centre table ɗin dake gaban gadonsa ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa, Sai da ya shanyesa tas sannan yayi cilli da bottle ɗin. Sake furzar da huci mai zafi yayi a karo na babu adadi yana sake nutsar da kansa. Sosai abubuwa masu yawan gaske suka shiga ƙoƙarin zeroying Brain nashi. Kamar su ɓata masa daidai lokacin da yake gab da kammalawa, irin alamomin rashin gaskiyar da suke tare da wasu daga cikin ma'aikafansu, Tamkar kuma wanda aka zabura ya miƙe aɗan zafafe yana yin gaban ƙofan Glass ɗin dake a shafe da Pics manya na emoji me ɗauke da hoton lion, babbar yatsar hannunsa ya sanya a take wurin dake a shafe yayi On tamprint na yatsunsa, zuuuuuuu wata haɗaɗɗiyar ultra door ta baiyana. Wasu manyan Computers ne A ɗakin dasu jojjone ta ko wacce kusurwa dake ɓangaren, akan wani ƙayatacce dogon table ya kai zaune, wacce ke ɗauke da macbook, Zama yayi cikin hanzari tare da ɗaukar MacBook ɗin dake kan kujerar, buɗewa yayi yafara aiki cikin ƙwarewarsa da kuma baiwar iya sarrafa ko wanne abu, yakai kusan 45min yana danne dannensa, kafin ya saki wata shegiyar ajiyar zuciya ya tashi yana barin ɗakin da yafi kama dana bincike. Amma kuma har zuwa lokacin zuciyar sa bata dena zugi ba. Dan haka cikin loƙaci kaɗan kamanninsa suka san ja, jikinsa na ɗaukar rawa wanda kallo ɗaya zaka masa kasan cewa he is not on his mood,musamman yadda yanayin jikinsa ya sanja tare da wani irin tsumewar da yayi. Cigarettes ɗin dake jere gabansa wacce ya fito da ita ya ɗauka, tare da kunna lighter yana fara zuƙanta a haukace, cikin ƙankanin loƙaci ya gama hargitsa ɗakin da hayaƙin cigarettes ɗin.
Sai dai ya zuƙe wajen kara biyar kafin yaji zuciyarsa ta ɗan risina.
dafa kanshi dake ɗan juyamai sosai yayi yana ƙoƙarin saita kan shi, sedai hakan bata samu ba se kuma tunaninta ɗaya faɗo masa. Hakan ya sanya a wani irin zuciye yay ball da plastic chair ɗin dake gaban sa.
Directly ɗayan bedroom ɗin da ƙofarsa ke manne da da wanda yake ciki ya nufa, kai tsaye wani irin mahaukacin bedroom ne da yaci uwar na farkon haɗuwa da komi da komai, wanda yake haɗe da ploorn da aka gama ƙawatashi da wasu Italian fashion rug masu masifar haɗuwa da burgewa, gaban wani ƙaton deep pridge ya nufa,wanda seda ya loda mata wasu nombobi kana fridge ɗin ya buɗe, wanda kai tsaye fridge ɗin ke shaƙe da Wine with alcoholic drinks gaba ɗaya. Wata farar rug ya janyo zuwa gaban wurin tare da kaiwa zaune, hannunsa ɗauke da kwalbar wine in daya ɗauka, ɓalle murfinta yayi yana kafa kansa bai ɗago ba sai da ya shanye tasss, kana yana kuma ɗaukar wata haka har seda ya sha kwalba uku. Ahankali ya fara jin wani sanyi a cikin zuciyar tashi, kafin duniyar ta shiga jujjuya masa yana tafiya duniyar gajimare kai tsaye. Ƙafansa ɗaya kan ɗaya hake yake zaunen idanun nan sun kaɗa sunyi jazur, sun jirkice daga launinsu zuwa kalan na maye, wanda zuwa lokacin har ya fara ganin komai bibbiyu. Haka be san iyaka lokacin daya ɗiba a haka ba se can tsakiyar dare ya miƙe yana faɗa wa saman lafiyayyen gadon daya nuna kamar ba'a taɓa kwanciya akai ba.
☆
11:06am
Ahankali ya shiga ware lumsassun idanunsa da suka yi jajur dasu, hannunsa ɗaya yasa yana dafe kansa dake ɗan sara masa kaɗan kaɗan, wanda ya farka haka nan gaba ɗaya duk bayajin ƙarfin jikin sa. wanda hakan kuma baya rasa nasaba da ƙarfin wine ɗin daya sha daren jiya. dan ko sallar asuba ma daƙar ya tashi yayi ta cikin room ɗin. Kasancewar ba sosai ya fiye shan wine ɗin ba, shi yasa a duk lokacin da ya sha take ɗan bugar dashi.
A natse cikin kasala ya ɗan cije jajayen laɓɓansa. Yana sauƙowa daga saman gadon cikin ɗan kuzarin daya may saura a jikin sa. Kai tsaye bathroom ya nufa, tun daga bakin bathroom ɗin kuwa ya soma rage kayan jikinsa, kafin ya faɗa tsabtataccen bathroom ɗin yana sakarma kansa shower, lumshe oily eyers nashi yayi yana sakin wata iriyar nannuyan ajiyar zuciya.
A haka ya kwashi sama da 40 minutes yana tsaye ruwa na dukan jikinsa, koda ya fito daga bathroom ɗin towel ne fari ƙal ɗaure a waist nashi, gaba ɗaya jikinsa ɗauke yake da damshim ruwan da yay wankan, yayinda itama lafiyayyar gashin kansa tayi lub, wanda take ɗan digar da ruwa ahankali. Wani mini towel ya ɗauka wanda dashi ya goge kai da kuma jikin sa. Gaban dirrower mirror ya nufa yana shafe jikin sa da tsadadden kuma fitinannen body lotion nashi me ƙamshim gaske, haka ya shiga shafe lallausar fatar jikin nasa, kafin ya shige cikin clothes ɗin sa, wanda ke shaƙe da kayan sa. Kai tsaye ɓangaren kakinsa, koda ya sanya kayan a jikin sa ba ƙaramin ƙyau da matuƙar amsan jikin sa sukai ba, kai tsaye kuma se haɗuwarsa da kwarjinin sa suka sake bayyanuwa , gashin kansa kuwa sai shining yake domin yasha mayuka masu ƙyau da tsada... Wasu white shoes ya sanya a ƙafafun sa sannan ya fita a room ɗin yana komawa hasalin na jiyan daya baro, kai tsaye wayoyinsa ya ɗiba yana fita a cikin sa shima.
Ido ya rumtse ya na jin zuciyar sa na bugawa ɗan ƙarfi sakamakon komai daya shiga dawo masa. "Ya rabb?" ya ambata cikin wata macacciyar murya. Amma cikin dakiya da ƙarfin zuciya ya shanye hakan yana fita a ɗakin kai tsaye baki ɗaya. Koda ya fito zuwa parlourn gidan lokacin babu kowa se iyaka dinner dake jere, hakan na bashi tabbacin har sunyi nasu lunch ɗin kenan. Kai tsaye dinning ɗin ya nufa yana ɗibar iyaka abinda ze iya ci ba da yawa ba. Kaɗan sosai yaci yana jin cikin sa na cunkushe wa. Seda ya shiga har room na Ammeynsa ya gaida ta, kana ya mata sallama yana nufar wurin aikinsa.....
☆
*Acp Maleek*
Tin da suka zauna suka sake tattauna maganar binciken da suka bata ya rage samun cikakken lokacinsa, aikinsa kawai yake yi cikin wata irin baiwa da basiri yana ɓangarar da tunanin su ta hanyar amfani da HANNAH ɗin. Sedai babban abinda ya girgiza su shi ne wani kama babban yaron green snake ɗin da yayi, wanda yama ɓoyeshi ba'a cikin Headquarter nasu ba. Dan haka daga sama faka faka suka turo masa da shedar ƙarin girma ta hannun Cp . Yana zaune cikin office nashi tare da Hanna wani ɗan sanda ya shigo yace dashi Cp ilayasu na son ganin sa, Wani shegen lalataccen murmushi yayi yana kashema Hannah ido ɗaya wacce take haɗe masa wani record file. A take ya marama ɗan sandan nan bay zuwa wawakeken office na kwamishina ɗin, Solute nashi yayi yana kamewa tare da gaida shi. Da hannu ya masa alaman daya zaune kan plastic chiar ɗin dake pacing inda yake zaune.
"Am Acp ABDUL_MAEEK MUSTAPHA WAZEER, dama na ƙira ka ne nan bisa wani ƙarin girma da aka ma tin daga sama. don haka dukkannin wasu binciken file na green snake dake hannunanka zaka miƙo min suc wata ƴar dariyar renin hankali yayi mai cike da ma'anoni kafin yace. "Kayi hakuri yallabai ina tsaka da wannan aikin ne yanzu, me yasa gwamnati zata bukaci ƙara yimin matsayi?, ke nan hakan alamu ne na ƙaƙarin tallafawa masu son zuciya, don haka bana bukatar wannan ƙarin girman sir." ya furta a dake sammm babu tsoro a tare dashi. "Wannan fa ba hukuncin bane da yake a hannuna ba Maleek, umarni ne daga wajen commissioner" ya furta yana wani ɗan jujjuya ƙafafunsu da jikin kujerar da yake kai, shi kuwa tsakiyar idon sa ya kalla tare da miƙewa tsaye yana zuba hannuwansa duka biyun a aljihun wandonsa tare da furta. "Matuƙar ban kammala wannan aikin ba babu wani karin matsayin da zan karɓa, domin kuwa bana da buƙatarsa" daga haka yasa kansa yana ficewarsa a office ɗin. Yana fitowa daga office ɗin wayar sa na ɗaukar ruri. K mashi dikko ne duk da kasancewar zuwa yanzun ya goge no nashi daga cikin wayar sa, sedai tsafff ya gane cewa no ɗin tashi ce. Don haka kai tsaye ya amsa wayar tare da karata a kunnensa. Daga ta can kuwa ɓan garen me ƙiran jin amsa shi ne ya sanya shi sakin wani murmushi me cike da tarin ma'anoni masu yawa tare da furta.
"Zuwa yanzu ko a wanne hali Acp maleek yake ciki? Karka wani damu fa abinda ka jima kana so ne ni kuma nasa akama, wato ƙarin girman da kake ta kokawar seka samu ta hanyar jajircewarka a wurin aikinka, so ni kuma da nake ɗaya daga cikin manyan masoyanka shi ne nasa a ƙara maka ɗin, ohhh na ma manta harta takardar transper ka dawo kusa dani don ina son jajirtacce irinka kusa dani" yayi maganan cikin wani shegen shegen taka tare da kaiwa ƙarshen maganar da fashewa da dariya irin ta mahaukatan nan.
"Da zaka cire hannun kowa a cikin wannan wasan da yafi K mashi dikko!, ta yadda ba seka kutse karin girma domin dakatar da binciken da nake kan yi ba, domin ni da kai kaɗai ne ya kamaci ace mu ci gaba da buga wasan har daya yaci nasara akan daya" ya yi maganar yana jin ace ina ma a kusa dashi yake ya shaƙo maƙogwaronsa" Daga tsayen da yake a lambun gidansa yana ɗan za gayawa da ɗirtsetsen cikin sa gaba ya furta. "Har yanzu kai yaro ne Maleek in ban da abin ka miye na saurin, sannu sannu dai ko tin da har na bika ta lalami ta lumana kaki amincewa duk abin da ya faru da kai kai kuka da kanka ba wa kowa ba, idan har kace zakaci gaba da wannan binciken tabbas a kowanne taku da kake ƙara wa, to ina son ka sani kana sake kusanta kanka ga mutuwar kane" Cikin fusatacciyar murya ya furta. "Ban taɓa sa wani binciken da ban kai ƙarshen saba, ka ma wani daina bama kanka wahala sir, domin ka na mance cewa ko da waye kake tare, Ina son ka sani komai daka sani a duniya yana da farkon faruwarsa na farko. Nine na farkon da zan fara gagararka kaji, kana ina son sena gama wajiga rayuwar ka ne kafin tonuwar sirrinka, domin na nuna maka cewar ni ɗin in the best ne". "_HHHHHHHHH_ mutuwar ka zaɓa kenan Ɗan sanda Maleek me aiki a kan gaskiya da amana, Ɗan gidan ƙasar sa NIGERIA?..... To shi ke nan babu komai ƙasar taka kuwa ita da kanta ne za tayi silar mutuwarka, bayan tayi ALLAH wadai da kai"
Wani shegen murmushin gefen baki yayi tare da furta "Kai a tunaninka kenan ba, ni barazana wa mutuwata ba baƙon abu bane a wurina!, tin da ba jiya ba, ba yau ba ka sabar dani da fuskantan barazanar wa mutuwar, bama daga wurin ka kai ɗaya ba daga wurin mutane maban banta!. Don haka tun da har na riga na fara aikin nan nake ga babu barazanar data isa sawa na janye batuna akan wannan case ɗin, se ko in mutuwa nayi bi ma'ana kuka sanya aka raba numfashin nawa da gangar jikina kamar yadda kuka jima ikirarin yimin!" se kuma ya ɗan dakata tare da fesar numfashi.
"Se dai ina son ka sani kashe ni a tafiyar ba shike nufin kawo ƙarshen azzaluman mutane da gurɓatattun jami'ai irinku ba sir' akwaisu akwaisu akwai dubinsu masu zuciyar lu'u lu'u da ɗanyen gwal, duk da shi baya da runduna ko ayari domin kawar da magauta azzalumai, amma a ko ina bila adadin wannan MALEEK ɗin dake tsaye gabanka har gaban abada shi kaifi ɗayane, kamar yadda zafin kansa be taɓa barin ya aikata ba daidai ba. Kashe Maleek kuma na nufin kun gayyatoma kanku da kanku goran gayyatar tonuwar asirinku da mutuwar kune wa me zuciyar da babu irinta!!!"
Daga haka kit kit kit ya datse ƙiran nashi.....
ꨄ
_Captain AA_
Tin da ya shigo barrack ɗin ya nufi *SPACE RESEARCH* nashi, domin sake faɗaɗa bincikensa dangane da wata ƙungiyar ta addanci data dama ƙasa, daga yau kaji sun kai sumame can garin, se kaji komai sunkai hari can gari, don haka baki ɗaya ma hankalinsa yake akan binkicen tushen hasalin ƙungiyar, sedai tashin farko daya binciko se yaga ashe duk ƙungiyar su Fata ce, Wato Fata Abdul_phata Omer tare da ƙasusuwan bayansa irin su green snake, Mustoupha die, duk babu wanda bezan su green snake sune Jiga jigan da suka gama damun ƙasar ba. Yana tsaka da binciken nashi ne kuma General Murtala na goma na son ganin sa a _Criminal Investigation Department (CID)_
Kai tsaye ya nufi department ɗin yana bi ta ƙofar OUT OF SERVICE. Gaba ɗaya wadan da suka kamata ne a wurin, don haka yana shiga ya sara musu General murtala na gona na masa nuni da wurin. Be zauna ba yake a tsaye yana jin yanda manyan sojojin ke gwabza musu akan ba tin kararsu ya kamaci ace sunyi ba, shi dai duk yana jin su don haka yace shi kaɗaima ze jagoranci tafiyar, domin wannan ɗin wata babbar dama ce da suka same ta a hannun su, Sam karsu bari su yi amfani da wannan damar. Nan masu ruwa da tsaki a cikin tafiyar ya munafukar ɓoyayyar hanya suka ƙi tafiyar nashi. Don haka ya miƙe a ɗan zafafe yana me furta.
"Yallaɓoi taya kuke iya bacci cikin salama?, bayan alhalin kune kuke tauye haƙƙin rayukan da kuke ikirarin kuna karewa!, Shin wai jinin al'ummar da kune kuke yin sanadiyyar mutuwar su baya hantarar ku ne?" se kuma ya ɗan dakata zuciyar sa naci gaba da tafarfasa da ire iren waɗan nan zalincin na manyan nasu, wani kalan ɗauke kansa gefe yayi tare kuma da juye kamar wani kububuwa yana me tire hannuwansa guda biyu kan table ɗin general murtala ɗin tare da ci gaba da furta. "Kwarai wannan abu ne da duk wani me hankali ze iya gane hakan, gaba ɗaya ma nawa ƴan ta addar Ƙasar nan suke? Taya za a ce wai sun gagari wannan ƙasar ina mamaki yallabai!, A Kowacce lokaci idan suka so suna kashe mana maliyoyin mutane ta hanyar tada bama bamai, kuma mafi akasarin duk harin da ake kaima talaka wane, me ye yasa se iyaka talakawan wai suke bi suna kashewa? Shin basu san inda manyan Kasar suke bane ba? Ko Kuwa zutonku ba zasu iya zuwa inda suken ba? To ba haka bane. Ainihin abinda ke faruwa su ne masu daukar nauyin su, suna amfana dasu domin biyar bukatar kansu. Zahirin abinda ke faruwa shi ne SON ZUCIYA, KWADAYIN ABIN DUNIYA DA KUMA Son ITA DUNIYAR Kanta...... " ya furta idon sa na sanja launinsu sosai.
" Meye kalamanka suke nufi Malam Aliyu? " general ya tambayeshi a ɗan ƙausashe yana jona FLAS HABER tare da hasko masa irin jam'i an da suka rasa. Yana me furta." Dufa da kyau ka gani AA yanzu so kake muci gaba da rasa jam'i an mu masu kwazo ne ko kuwa?, a har kullum duk kwanan duniya waɗan nan ƴan ta addar kashe mana rayukan adalan sojojinmu suke yi, ko a hakan kake son muci gaba da rasa manyan jam'i an mu irin haka? "Jinin jikin sa har wani kalan tafarfasan ɓacin rai yake tare da gyara tsaiwarsa, hasalin gwarjini da haibarsa na cike wurin duka ya musu rufa, tare da furta.
" Seda muka sadaukar da rayukanmu kamin mu karɓi wannan aikin, don me zamu ci amanar Ƙasar data kasance mahaifiya a gare mu? Yallaɓoi, dama dan mu sadaukar ga rayukan namu a ƙasar aka haife mu, shi yasa muje sanya a ran mu a
duk lokacin da muka fita fafatawa domin gwabza wa da ƴan ta adda, mu ke sanya a ran mu zamu kashe ne ko a kashe ka. A yanzu wannan Ƙasar tamu yanzu haka ba iyaka ta addanci ba ne yafi damun mu ba, babban abinda yafi damun mu shi ne SON ZUCIYA..... "
""SON ZUCIYA?"
Kanal bappa babayo ya tambaye shi.
"Kwarai kuwa sir son zuciya ne yallabai Kanal, son zuciyar da da yawan manyan Kasar mu kai har ma da wasu daga cikin jam'i an mu suke nunawa, da yarda da suke wajen haɗa kai da ƴan ta adda domin samun wasu manyan kuɗaɗe, wannan shi ne babbar damuwar Yallaɓoi. Idan zamu iyawa kanmu adalci, mun san cewa ba shugabanin bane suke juya Kasar nan tamu ba, su wa annan masu son zuciyar su ne. Domin duk kannin komai na Kasar yana a karkashin ikon su ne, hatta dashi kan shi shugaban da zai yi mulkin. Suna zaɓar wanda suka ga dama ne su ɗora akan mulkin, saboda su ne da kuɗaɗen ƙasar se kuma yanda suka so haka za ayi, sun lafe gefe suna kallon yanda suke azabtar damu suna mana dariya, shin wannan ba abin kunya bane a Ƙasar nan?, ƙasar mu ta jima da zamo wa koma baya akan sauran ƙasashen duniya, saboda masu zarmiyar cikin su sun fi mu yawa tirrrrr da wannan ɗabi'ar mara kan gado......" daga haka ya sanya kansa yana ficewa a wurin domin shi be ga amfanin ƙiran da aka masa ba, ohhh se yanzu ne ma yake ganewa, wato sun ƙiran shi ne domin su dakatar dashi?...
♡
Tin daga ranar da Acp Maleek yayi musayar yawu da K mashi tare da ɗan san dan, be sake bi ta kan kowa ba, kwatsam se ji yayi wai commissioner ya dawo nan da aiki a tsakan kanin kwanaki uku kacal. Tin da ya dawo ma se shi ne sake bi ta kan shiga sabgar kowa ba ya dukufa ne kawai akan aikin sa, wanda yake tsaff da cika burinsa. Se a yanzu da shigowarsa kenan ko office nashi be shiga ba akace sabon commissioner na neman sa. Harɗe ya tarar dashi zaune ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, shegiyar munafukar fuskar san nan ɗauke da murmushin mugunta da cin nasara. Solute nashi yayi tare da furta. "Sir" Tin daga sama har ƙasa ya ƙare masa kallo, tare da furta. "Ni da na matsu da case ɗin nazo amsar shi da kaina, ko dai ta ruwan sanyi ko kuwa ta ƙarfin tuwa...." wani murmushi me kyau Acp Maleek ɗin yayi tare da furta, "Se dai kuwa ko ta ƙarfin tuwan sir, kuma ka sani ko da ace ka amshe ta ƙarfin tuwan ALHAMDULILLAHI saƙon ya isa inda ya kamata...." Da kallon wannan wasan kwaikwayon yaran fa commissioner ya shiga binsa dashi. In da shi kuwa ya juya ze fi ce daga cikin office ɗin. "Dakata ai baka karɓi saƙon naka ba me gaskiyar ɗan sanda." ya faɗa yana miƙewa a kan kujerar ganin yana ƙoƙarin barin offishin, tsayawa yayi kuwa harya iso inda yake tsayen ya miƙa mishi farar takarda tare da cewa....
"Wannan takarda ce ta dakatar da kai daga kan aiki har na tsawon lokacin da zan gama ƙaddamar da bincikena akanka, domin ina zarginka da haɗin kai wa wasu mutanen da basu dace ba. Kamar yanda yanzun ka faɗi da bakinka, tare da barazana da maida martani wa na sama da kai..... "
Tsaye kawai yay yana kallonshi har ya gama maganar shi, kafin ya sa hannu ya amshi takardar tare da furta. "Kamar yadda muka saba a kowanne lokaci mai girma commissioner, wannan ɗin ma zai wuce" yana gama faɗar hakan yasa hannu yana raba takardar gida huɗu yana me furta. "Ka fuskance ni gaba da gaba nida kai mu gwabza kawai. Kai harka manta da sharaɗina?, to ka sani ba kallon shugaba nake maka ba a yanzun haka kallon abokin gaba nake maka, wanda nake da yaƙinin sena kawo ƙarshenka, idan har kana ɗaya daga cikin maciya amanar ƙasa da kuma aikinsu. dan haka baka da hurumin da zaka dakatar da ABDUL_MALEEK MUSTAPHA a aikinsa ko da na second ɗaya ne, na barka lafiya." daga haka yasa kansa yana ficewa a office ɗin ya barshi tsaye sororo kamar wawan da yaga mace na wanka.....
♡ 2 days ago
THE THICKSAKE FACTORY
Coffees & Restaurant
*Hannah*
Zaune take a ɗaya daga cikin ƙayatattun kujerun wurin. Inda take zaune kusan na 50 minutes tana zaman zuba idon ta inda ze ɓillo. Haka tana zaune har idanuwanta suka kai kansa. Inda yake sanye da Ash balmains na wata crazy shirt me shegiyar tsada da straight wando sai tsadaddun cover shoes ɗin dake ƙafarnsa na ballies, wanda kodan yawan sanyasu ɗin da yake ne ya sa kai tsaye zaka gane cewan shi ɗin tsayayyen jami'i ne. ɗauke kanta take son yi daga face nashi, sedai ta gaza hakan, don wani irin sabon kyaun da take daɗa iya kalla me kyau daga gareshi, wanda kyaun yafi yanayi da irin morning beauty ɗin nan ko ko dai muce morning freshness. Duk yacce taso ɗauke kanta daga kallonsa gaza hakan tayi, domin kuwa fin ƙarfinta zuciyarta tai ta kasa ɗauke fararen idanuwanta akansa tana masa wani irin kallan da ita kanta bama tasan tana masa ba. Shi kuwa tunda yay tozali da kyakkyawan face nata tsananin azabtuwan da zuciyarsa yay akan sonta da yaƙi barin Heart nashi ne ya sa ya kasa ɗauke idanuwansa daga gareta....
Se da ya kai zaune gabanta kana seta iya janye kanta daga gareshi tana sauƙe ijiyar zuciya, tana tunanin ko kwana biyun da tayi bata sanya shi a idon ta bane ya sanya hakan kuma oho?.....
"GREEN SNAKE......
_Su Oum Areef se a sakar min mara nayi fitsari, don gudun kar su Ummu jannah,& masheer sumin dariya nd others da kuka hana kanku bacci jiya toh ga nan kusha karatu lafiya😅😅 A daina hana kai bacci hilis dan nima bana hana kaina a to 🤦♀️ a da dai anyi amma banda yanzu uhummm_
To ai shikenan🤗 😅🥰 semu gimtse 🫰 haka nan da wani sabon salon nasu kuma🙃 😊....
08104493215
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻
# 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Book One paid
♡
Page 19&20
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
# HE WILL FIGHT
*Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank*
♡♡♡♡♡♡♡♡
ꨄ
♡
♡ ♡
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 23