Share this page
jini ya nuna su, yana me furta. *** "Ku sani sarkin ku na gaba wato KAMAALA ƊAN ASHFUD JIKAN KAMAALA RAHEEM DAWOOD dashen ALLAH NE, hadari ne shi malafar duniya duk wanda yace zaiyi dashi yaja da ikon ALLAH. Dole wannan karon dan zaki ya bayyana akan miƙiyansa kuma maha'intan iyayen sa, ku ji rayi lokacin Dawowar SARKI ASHFUD a karo na biyu, inda masu gudu su gudu ma domin kowa ya shirya ma bayyanuwarsa a karo na biyu.... " Ya ƙarasa faɗar maganan nashi a fusace, "An ce Mara dabara shi ne yake barin ruwan sama ya jiƙa shi, mai hikima kuwa tun kafin ruwan ya fara sauƙa ya riga ya gama samo wa kansa mafaka. Idan ya kasance har a tsayin wannan shekaru mahaifinsa ya kasa ja damu, don me kake tunanin jaririn da yake baida mafaka ko wata majingina ko tsira da rayuwa shi ze rayu har ya bamu ciwon kai?. Bare ya ƙalubalencemu. Ka sani kana da zaɓi biyu ne kawai a cikin wannan duniyar, zaɓinka na farko ko dai ka bamu wannan jaririn ko kuwa kaida shi duk ku zama sheƙaƙƙu." Sake riƙe jaririn dake maƙale a hannun sa da kyau yayi, tare da furta." Se dai ku sani kun makaro, kun kuma zo a mummunan loƙaci, domin ƙaddarar itace da kanta ta zaɓeni bawai ni ne na zaɓeta ba, Wannan jaririn seya rayu, seya zame muku ƙadan garen bakin tulu, seya zame muku alaƙaƙai a cikin rayuwarku, seya sanya kowannenku gudun ceton rai.... " Wata shegiyar dariya mutanen uku suka saki waɗanda fuskar su take ɓoye cikin rawani da shiramin da suka ɓoye dasu. Kafin ɗaya daga cikin su ya furta."Sai na tuna da maganar Malamin Falsafa Freud da yake cewa, Ko wanne mutum yana da zaɓi biyu! Na farko ya zaɓi wahalar aiki ko dai wahalar nadama. Frued yana nufin ko dai ka zaɓi wahalar jajircewa yanzu wajen gina gobenka ta hanyar yin watsi da daɗin kwanciya da kake yi a katufu, ko dai bayan fitowar rana, ko kuma loƙacin da dama ta wuce maka kasha wahalar nadama na ƙin huɓbasa da jajircewa da kaƙi yi wajen gina kanka a rayuwa, ta hanyar zaɓi da son gina rayuwar waninka ba wa kai ba" Ƙafarsa ɗaya da take tsiyayar da jini ya ɗan dogara tare da numfashi yana me furta. "Na farkon wanda tun kafin zafin rana ya keto, tuni ya fara shirin neman inuwar da zai sha inuwa, na biyun kuwa cewa yay wanda yake jiran rana ta fito sannan ya fara tunanin yadda zai samu inuwa. Manyanmu na cewa ba' a shuka a rana guda, kuma a yi fatan samun inuwa a wannan ranar.Idan kana da shekaru 25 zuwa 35, bai kamata ka zauna kana jira sai wani ya baka dama ba. Idan har a wannan shekaru ba ka kafa tushen kanka ba, to ta yaya zaka yi tunanin lokacin da kake mataki na girmantakarka, Sarki ashfud yana yawan cewa, Dole mutum ya ɗauki nauyin kansa. Idan ba ka yi hakan ba, sai wani ya ɗauka maka, amma ba yadda kake so ba. Idan har kuna da tunanin cewar zan tsaya inci gaba da dogara daku to kunyi kuskure, ku sani cewa rayuwa ba ta jiran mai dogaro da wasu. Dole ƙwaƙwalwarka tayi aiki, dole in shiga cikin mutane kala-kala don koyon dabarun zama da mutane, Idan ka gaza yin hakan, za ka kasance cikin jerin mutanen da za a rubuta tarihi a kansu da kalmomin. _Ya rayu amma bai yi tasiri ba_ Domin duniya kamar motar haya haka take, idan ba ka hau ba, za ta tafi ta bar ka. Idan kana tunanin da akwai wani lokaci mafi dacewa da gyara rayuwarka, ku sani shekara mai zuwa ba ta taɓa bada tabbacin cewa za ka samu tikitin hawa wannan motar. To yanzu ne lokacin. Ko ka tashi ka ɗauki ragamar rayuwarka, ko kuma ka zauna har duniya ta manta da kai, ni kuma bana da fatan hakan!... Ka na da wani mutum ƙwaya dal da ya haskaka rayuwarka? Daure ka yaba, ka kuma kyautata masa gwargwadon iko. Kada ka jira har sai bayan ya mutum a barka da dogon sharhin da ba shi da wata Alfanu, sedai ni na kuskurema hakan, amma zan gyara abinda na ɓata ɗin ta hanyar inganta rayuwa, Domin kuwa ita kanta rayuwar tamkar hanya ce mai cike da tsaunuka da kwari da tudu, mai cike da duhun dare da hasken rana. Daga shekaru ashirin da biyar 25 zuwa talatin da biyar 35, matashi yana cin karo da gagarumar jarabta, ba daga komai yake samun wannan jarabta ba sai da zuciyarsa. Wannan ne lokacin da rayuwa take tantance ko zai haye tudun nasara, ko kuma ya ci gaba da rayuwa na bayansa suna tattaka shi suna kaiwa ga Nasara, kun sami wannan damar tawa ne a baya ku sani wannan ba shi ke nufin zakuci gaba da zuba min zaɓa ina caka ba, Tabbas duk wanda ka gani yau to yabiyo ta jiya. Haka zalika duk wanda ka gani a matakin nasara, to kuwa tabbas acikin nasarar nashi akwai tarin ƙalubalen daya fuskanta kafin haka, SADAUKARWA 💪 ....... ꨄ Bata dakata da tafiyar da take yi ba har seda ta danganka kanta da inda hasken aci balbal ɗin da take hangowa, Sema sake ƙaimi da tayi wajen ci gaba da sassarfa har ta isa inda take gano hasken aci balbal ɗin. Yadda take saurin kaɗai kamar zata kifa domin burin ta ta isa wajan, shi ne zai baka tabbacin lallai ko meke tafe da matar me girma ne haka, dutse ne babba a wurin sai yadi kalar ja da aka yanke saman dutsen dashi da kawunan skeletons sassaƙale a ko ina anyi ado dasu. Tin kafin ka isa wurin zaka fara jin wani gurnani da gunji gunji kamar bana mutane ba. Tana isa deda daf da dutsen wani katoton boka ya bayyana gabanta, bakiƙirin dashi katoton gaske wanke yake ɗauke da kan jakanya. Zubewa tayi a ƙasa gabansa, bayan ta gama dalalo masa wasu dalasiman da duk wacce take zuwa wurin sa dolene ta iya shi. Cikin ruɗu da kuma alhini da take a cikin sa ta furta "Ta haihu! Ta haifi yaro namiji, sedai an sama matsal....... "Da ka ta domin anan bansan kalmar matsala ba Maddiyya, Domin kuwa dama can mun riga mun ga hakan zata faru. OUMMEEY zata haihu kuma ɗan zo girma. Me kike so a yiwa jaririn?, A kashe sa kamar yacce aka kawar da ubansa,? Ko kuwa a haukatar dashi tamkar yanda muka haukata uwar?, Ko kuwa so kike a lalata rayuwar sa ta gobe?, A juyar da tunanin sa?, a cikin waɗan nan jerin abubuwan dana lissafo sai ki zaɓa wanne kike so ayi ma yaron a ciki? Ko wanne kike so zamu taimaka miki."" Ya faɗi cikin murya mara daɗin sauraro mai bada tsoro da firgita wanda yake sauraron ta. Sai dai wani tarin abin mamaki amma matar nan bata ko yi ɗar ba, saima sake gyara zaman ta da tayi tare da fesar da wani mayen numfashi ta furta, "Na tsani jinin Razeenerh, bana son jinin OUMMEEY yayi wani kwakwkwaran motsi a cikin wannan masarautar har se naso, bana son jinin OUMMEEY ya ɗaukaka a cikin wannan duniyar, A kuma ko ina ze rayu, duk wannan maganar babu ita, domin kuwa Qasim bafaden sarki yaci amanar mutanen da suka aikesa game martaba sarki ashfud ya tsira tare da yaron, bayan ya kashe me martaba. Se dai ka sani wutar bata fara aiki ba, buyagin hayaƙinta ne kawai ke aikin cunkushe kwakwalan wasu tsirari na kaɗan daga cikin mutanen fada" wata kafurar dariya bokan ya kuma saki me kama da kukan jaki ya furta. "Shegiyar uwa, uwar la'anannu, Shegiyar uwa, uwar tsinannu...... Ki an yanzune muka fara wannan yaƙin, wanda bashi da ƙarshe, ki jira girman sa, kowacce duniya zaki ga da kalar ɗabi'ar da zai tashi, ni ne nace zanyi in na faɗa kuma bana fasawa sai na tabbatar hakan, sedai da sharaɗin cewa..... Muryanta na wani irin rawa ta taryi numfashinsa ta hanyar furta, "Meye shi sharaɗin?." wata kafurar dariya ya sake bushewa da ita yana me furta. "Kome ze faru daga baya babu ruwan mu, karkiga laifin mu, aikin mu mun riga munyi in kika ga wani canji ko saɓanin hakan daga baya, domin kuwa ƙaddarar yaron me ƙarfi ce, tin kafin yazo duniyar yake nuna min hakan. Jeki la'ananniya karkiyi kuka dani, Jeki akwai sakamako, akwai sakamako...... Miƙewa tayi tamkar zata bar wurin, Se kuma zaram ta zare ƙahon dake jikin ta ɗaure ta gefen jikin ta tana lumawa bokan a ƙahon zuciyar sa ta tsakiyar ƙirjinsa. Tare da furta. "Sai dai ka sani kayi babban kuskure boka na ambatar kuskure da sakamako bayan aikina, ina so ka sani Mardiyayya bame tsoro bace, domin shi matsoraci baya taɓa zama gwani, ni kuma gwanar nake da buƙatar zama. Ka sani duk wahalar aiki, duk ƙalubalen da zan fuskanta ba a bakin komai suke ba, sedai bana taɓa ɗaukar faɗuwa a cikin wasa da kasada ta, duk tashin hankalin sa na amince zanyi babu wani sakamako Se wanda na zaɓarwa kaina da ƴaƴayena boka a sauƙa lafiya....... " ta ƙarasa maganar tana fisge ƙahon daga tsaƙiyar ƙirjin nashi. Wanda yayi saurin dafewa yana kuma fashewa da wata mahaukaci yar dariya, wanda gaba ɗaya dajin ya ɗauki." Ki sani dole akwai sakamakon! Dole ranar zata riskeki, dole zaki girbi abinda kika jima shukawa mardiyya, za ki yi nadama, zakiy nadama, fatan nasara da kuma rashin nasara anan gaba, sena dawo ɗaukar fansa ta tare da miki dariya wata rana, dole nima zan rayu akwai bukatar na dawo wata ranaaaaa" daga haka wata Guguwa ta baybaye dajin kafin kuma ɓatttt ta ɓace tare da bokan...... ꨄ Hhhhhh Na ce Idan ana dara fidda uwa ake, ina gwanar wata ga tawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin dake cikin suger da kuma zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da wani ɗanɗano, yayin da ita kuma zuma ta kasance tana wanke ƙwaƙwalwa ne tasss, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, kuma ƴar baiwar ku AMMEY LAYLERH, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na tsaya bashi labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha,LITTAFIN RAMIN KURA ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, zalunci, sarƙaƙiya, gami da Izza, *RAMIN KURA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yazo, gashi da kaifin gaske kaifin yankan domin zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa?, Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *AMMEY LAYLERH* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da tsantsar mugunta Zanba cikin aminci, labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa, kun san dai alƙalamina baya taɓa rubuta shirme, ku dai kawai ku biyo ni *AMMEY LAYLERH* taku cikin wannan zazzafan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake, da kuma yadda zata kaya, haɗi da warwarar wannan ƙullaliyar zare da abawar dake chakuɗe cike da sarƙaƙiya....... Waɗanda suka karanta littatafanta irin su. *MIKIYA, DUNIYARMU, TA DABAN, KAREN BANA, JALAAL AREEF, ƘAUNA BIYU, SO DAN Rayuwa DUHU na DUKAN duhu,* Sune kaɗai zasu san ya ɗanɗanonsa yakeeee.... Hajiya karki bari ayi tafiyarnan babu ke. Domin kuwa ta manya ce, ta kuma musammance... Chart mee or call🤙 08104493215 Hhhhhhhhhh to ai shikenan 😅🥰 A gimtse 🫰 🙃♥️✅ *BY AMMEY LAYLERH ✍️ ✅* *༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻* # 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Book One paid ♡ Page 3&4 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. _NA'EEMA SULAIMAN SARAUTA *NIMCY LUV* har abada ƙaunarki ɗaya ce a gareni my Role model, me zuciyar lu'ulu'u da Zinare domin duk inda akaje aka zo ke ce AMMEY LAYLERH 💐. Na sadaukar miki da wanan littafin, this novel is for you my humy darling princess tawa, my support system, my Role Model I love you_ *Zuciyarki fara Aniyarki fara, kyautatawa Halinkine, Mutunci da karamci duk a tare suke dake,MAMAN IHSAN tawa har gaban abada ke kaunar AMMEY LAYLERH ce, Ina Sonki da yawa da yawa ina matuƙar godiya gareki tare da sake jaddada ƙaunarki gareni* _Special Thanks to Masoya masu bibiyana, ina alfahari daku a ko ina a kowacce duniya kuke Love you all 💞💖💘💗_ ♡_Capricorn season_ # THE POWER IN ROCKET 💪~ # DEEP ASSUMING FOV # Boms squad # A TAITOR's # ROMANCE # BLOCKBUSTER # A SOLDIER's # Courage # Hop0 # Is Crime # Destiny # Betray # HotLove # His love towards ♡♡♡♡♡♡♡♡ Mai martaba Sarki *ASHFUD KAMAALA RAHEEM DAWOOD* shi ne sarki na goma sha biyar a masarautar *UMMUL YOODA* dake cikin garin _Adafan ta tsakiya dake Nahiyar Chadi da Sudan maso Arewa cin Sudan ɗin_ jika ne wajan Mai martaba sarkin Ummulyooda RAMEEM DAWOOD. Sarki na goma sha huɗu a wancan zamanin, wan Mahaifin sa Sarki Ashud wanda mahaifinsa ya masa takwara dashi a yankin Chadi ta tsakiya. shi ne sarki na goma sha uku, Mahaifinsa KAMAALA RAHEEM DAWOOD Yana da tarin ƴan uwa da dama wanda suka haɗa da uwa ɗaya uba da ɗaya, da kuma wanda suke uba ɗaya, shi kaɗai ALLAH ya zaɓa a cikin su ya baima sarautar Ummulyooda duk da tarin ƴan uwa manya da yake da. Duk kuwa da kasancewar masarautar, Babbar Masarauta ce ta asalin larabawa, Masarautar ta samu asali ne tun iyaye da kuma kakan ni, Wanda a kowanne ƙarni ake sake gyareta haɗi da sanja wasu tsarin abubuwan ma na daga gine ginen ta.... Tamkar a yanzu da take hannun margayi ASHFUD KAMAALA RAHEEM DAWOOD. Wanda masarautar ta samu haɗaɗɗen gini irin na masarautun nan da sukayi zarra sukayi fice a cikin manyan masarautu. Yana yin tsarin ginin kawai abin a tsaya a kalla ne, domin kuwa tsaf zaka ɗauka hotel ne ma saboda tsananin yadda yake da kyawu, da kuma passes daban daban dake cikin emirated ɗin, banda wasu shegun benaye iyaka ganinka wanda aka tsarasu da iyaka zallar gilashi. Masarautar Ummulyooda kenan! Masarautace me cikakken iko wacce take taƙama da Al'adarta da kuma Addininta. Masarautar _UMMULYOODA_ ginanniyar masarautace wacce take tsaye da ƙafafunta tun iyaye da kakanni, tun a wajen masarautar zaka fahimci ba ƙaramin Mutum ne ke mulkar Masarautar ta UMMULYOODA ba cikin cikakken iko da kuma ginshira haɗi da wani irin kwarjinin daya ma duk wani family daya dangaci duk wani family dake cikin masarautar Ummulyooda. Bare kuma azo kan uwa uba me mulkartar baki ɗaya kaima me karatu ai kasan babu ƙarin bayani domin ɓatama kai loƙacine domin magana ake ta sarkin sarakan masarautun duniya. Sarki ASHFUD KAMAALA sarki ne mai cikakke ilimi da kuma wayewa, Inda a matakin boko yana da matakin PHD. A ɓangaren ilimin addini kuwa ba'a cewa komai domin yafi zurfi a wannan ɓangaren ma fiye da komai, shugaba ne shi me tarin ilimi da kuma adalci da sanin ya kamata da tausayin talakawan sa ta ko wacce fuska, baya lamuntar zalunci ta ko wanne ɓangaren ko waye kai ko kuma ɗan waye yayi ba dai-dai ba masarauta zata hukunta. Yana da yawan taimako da sadaka musmaman ga wanda basu dashi, baya jurar ganin talaka wan ƙasar sa cikin ƙunci da ƙasƙanci, don haka ya tamkar waliyyi a gare su. Wannan tarin alkhairan nashi ya sanya kowa dake cikin fada ya tsane shi, ciki kuwa harda iyaye da kakanni, domin anyi yaƙinin cewa tinda ake sarakuna a masarautar ba'a taɓa adalin shugaba irin sa ba, duk da kasancewar mahaifinsa ba haka ya taka irin wannan muhimmi yar rawar a nasa lokacin. Sedai daya tashi nashi mulkin seya zarce na mahaifin nashi, sunan shi kuwa ya jima da cika da timbatsa ta kowacce kusurwa da kewayen duniyar ma. Sarki ASHFUD yana Matan sa uku. Yayin da da babbar cikin su itace Fulani RUMAANA, itace uwar gidan sa auren saurayi da BUDURWA suna da yara biyar duk mata ne. Mace ce makira a ɓoye, a bayyane kuwa zata nuna maka duk duniya babu wanda take so sama dakai amma a ɓoye tafi kowa cin dunduniyar ka. haka zata yi ruwa ruwa mayi mayi gabanka ita nan game ƙaunar ka, Se Matar sa ta biyu itace Fulani Mardiyya itama ƴar sarkin Junayna ce wacce ta gaji duk wani irin makirci da kulla kulla irin na mahaifiyarta, bayan nan ita Mace ce mai izza da ƙasaita da nuna zallar iko a kan komai, itama tana da yara shida domin haihuwar kwanika take yi, shekarar data haife ka shekarar zata dire maka ƙanwa ko ƙani. Maza huɗu ne yaran nata babban shi ne Zayed su kuma sauran duka ƙananune, inda daga nan tasa aka cire mata mahaifarta gaba ɗaya domin a ganin ta da tunanin ta haihuwar ƴaƴa maza a gidan sarauta shi ne riba. Kuma ta haifa don haka ta cire duka mahaifar nata. Tin da yaran nata sune dai mazan, kuma sune manyan maza a kaf gidan sarautar kasancewar sune kan gaba a komai za'a yi na sarauta tabbas dasu ake damawa. Babban burin Fulani Mardiyya a duniya shi ne yaranta su gaji sarautar UMMUL YOODA, data kasance tsarkakkiyar masarauta. Se matarsa ta uku wato ADEENEERH EL_ HASSAN KUWAIT. Ita ɗin cikakkiyar Ƴar sarki al_hassan ce Babbar yaya ga AK EAGLE, tana da wani irin kwarjinin data gata daga mahaifin nata, kai da ganin yanayin maganar ta da yanayin takun ta kaɗai kasan cewar yeah ita ɗin jinin sarauta ce gaba da baya, domin kuwa shi ne yake yawo a jikin ta gaba da baya. Fara ce tass kyakykyawa domin ta ɓangaren mahaifiyar kyawawa ne sosai. Ta jima bata Haihu ba ku san shekarar ta goma sha biyar da aure kenan tare da sarki ashfud, se a wannan lokacin ALLAH ya bata cikin data kusan haife sa bata cikakken hayyacinta. Kusan lokaci ɗaya Fulani RUMAANA tare da QUEEN OUMMEY (ADEENEERH) Suka fara laulayin ciki. Inda ita ta haihu lafiya yaranta biyu mace da namiji, Sedai macen bata zo da rai ba, a yanzun haka tana nan tare da kyakkyawaan yaronta, wanda kowa yake mamakin kyawun nashi, domin kuwa kyan harya zarce misali da tunanin me karatu..... Duniyarta ta mata ƙunci a sanda ta buɗi ido ta ganta se ita kaɗai ɗinta, wani kalar nauyi da ƙunci ne suka haɗu suka daskarar mata da zuciyar ta nan take, Ta nemi adalin mijin ta ta rasa, ta nemi Abinda ta haifa shima ta rasa walau mace ce ko namiji ne, wanda hakan shi ne yay sanadiyyar bar bata wani ƙatoton tabon da take jin har ƙarshen numfashi da wahala ta manta da hakan,Lallai tabbas da ace ƙarfin iko a hanun kowanne ruhi yake a zahirin rayuwa, da ita ce zata zama mace ta farko a duniya mai ƙarfin ikon da zai girgiza zukatan kowaɗanne irin azzalumai. Kafin shuɗewar wannan al'amari ma su ɗauke da kundun baƙin ciki rayuwar rayuwar da aka jefa ta, ita da adalin mijin ta, jinsu suke tamkar dutsen lu'u-lu'u ne su a cikin tsakiyar zinarai. Domin magana ake ta laylerh da majnun. Don matuƙar ƙaunar juna zunzurutu mara algus ɗin da suke ma juna, mara gauraye da suke ma junansu. Masu kuka a yayin zubar hawayen ɗayansu, masu dariya a yayin farin cikin ɗayansu, masu jinya a yayin da ɗayansu ya kwanta jinya. Masu shiga matuƙar damuwa a yayin da suka kalla wani nasu yana cikin damuwa, Sarki ashdud kenan me zuciyar lu'ulu'u da zinare. Wanda zuciyar sa take a wanke tsafff domin UBANGIJI madaukaki ya riga da ya gyare mishi ita tsafff, yana son ƙasar sa da mutanen dake cikin ta, yana son masarautarsa da mutanen dake kewaye da ita. Yana ƙaunar duk wani abu daze kawo ci gaba wa ƙasar sa, yana ɗauke damuwar wasu koda hakan yana nufin shi ze kwana cikin damuwar yana ɗaukar hakan ba a bakin komai ba, muddin mutum ze samu farin ciki a cikin tashi duniyar ☆ Ɗagowa tayi ta kalli Afud Kamaal da idanuwanta da suka canza zuwa kalar ja sosai ta zuba masa jajayen idanunta. Kafin idnonta su zubo da wasu kwallar zafin da zuciyarta ke mata, na tsananin tausayin kanta da kanta, yau ina yaran ta biyu data haifa?, domin kuwa ta san yara biyu ta haifa duk da kasancewar bata wani cikakken hayyacinta. Amma tasan da cewar yara biyu ta haifa, tin da watan haihuwarta ya kama dama take a cikin zullumi, domin kuwa duk wata kulla kulla ta gidan sarauta babu wacce bata sani ba. Don haka kullum take cikin faɗuwar gaba, domin ita tata uwar tin ba tafi shekara 7 da haibarta ba aka kashe ta, aka kuma kashe musu kakan su ASHAAN A MASARAUTAR SU TA EMAAR's. Babu kalan kulla kullar da bata kalla ba. Maganar Afud ne ya dawo da ita daga duniyar data ɗan Lula. "Duba da idanuwanki ki kalla ADEENERH yadda daraja da Martaba da kima yanda take ƙaruwa da kuma dukiya" Kanta ta sake ɗagowa a karo na biyu tana kallarshi da jajayen idanuwanta. Dakatar dashi tayi ta hanyar furta. "Ai ita kwaryar kirki a ragaya take, darajar kanwa kuma se cikin miya..... Numfashinta ya tarya shima, wanda ya sanya oummey buga masa wata uwar tsawa, domin ita ɗin dakakkiyar mace ce da sam bata da tsoro ko shakkun wani abu. " Ka gimtse min bakin ka anan Afud!, idan ina yiwa mutum bayani baya gimtseni. Ko kana nufin harka manta da wannan ƙa'idar da nake da?, ka sani cewar tarin dukiya ba shi ne karfin ikon mutum ko kuma kima da darajarsa ba, ka gina zuciyar ka akan gaskiya tsayayya shi ake kira da hasalin ƙarfin zuciya afu......" Wata kafurar dariya yayi yana me furta." To yanzu shi mijin ki da yay gaskiyar yana ina?, Matsalar shi ne tausayin da yake da yayi sanadiyyar wargajewarsa tare da daular sa a cikin wannan masarauta..... A yanzun wannan masarauta ta wace!, kuma zataci gaba da tafiya ne bisa ƙarfin ikon da nake da A kuma tsarina ADEENERH, Idan kuma zaki iya Dakatar dani Bismillahhhhhhhhh....... Ni kuwa ina nan zaman tsimayinki....... " Dubanshi tayi duba irin na kai ɗin zuciyar ka baƙa ce bame kyau bace, tare da furta. " Ka tuna cewar duk abin da ka aikata cin amana ne Afud!, kuma shi addininmu be ko yar damu cin amanar kowa ba, duk kuma wanda yaci amana to kuwa tabbas yana haɗuwa ne, Da mummunar ƙarshe bame kyau ba, kuma kana ƙarfin ikon da kake jin kana da UBANGIJI se ya kawo wanda zai yi maganin ka, Ka da kayi tunanin wannan tsoratarwace, ƙa'idace ta wannan rayuwa, domin UBANGIJI ya daɗe da ƙadarta hakan. Domin Kuwa duk abinda ka shuka to ka tabbatar da cewar shi ne wanda zaka girba ko ba jima Afud.... " wata mahaukaciyar dariya ya fashe da ita tare da sanya ƙafarsa ɗaya ya to kare inda take zaune, kafin ya dubeta tare da furta. "To yanzu faɗamin abinda mijin ki ya shuka ya kuma girba?, To ni neeeeee, Ni ne wanda ya shuka ya kuma ni ne wanda ya girba ADEENERH AL_HASSAN EMAAR's KUWAIT....." Wani kyakkyawan mari ta sauƙe masa wanda ya zo masa a bazata,

Chapter 2 of 23