*UMMULYOODAH*, domin kuwa taka ce, Mahaifinka numfashinsa na ƙarshe shi ne........
Daga nan tin be kai ƙarshen rubutun ba jikin sa ya shiga wani kalan ɓari, har yana jin kamar ana dafa namomin jikin sa ne, kafin yayi wani aune, har jikin sa ya kwaranye da wani kalan zuba na tashin hankali. Wani kalan soma jijjiga kansa yayi yana ja baya da baya kafin kuma ya saki wani irin ihu, wanda ya sanya baki ɗaya ɗakin amsawa.
A wani irin mugun zuciye yakai maaaaaaaa.....
_★ Tofa wai ya masu karatu suke tunani ne a cikin wannan tafiyar? 😂 😂 😂 😂_
_Tako ta ina fa gwaramace sabuwa a cikin tafiyar!_
_To nikam ma na rasa ta yacce zanyi in ganar daku, kawai mu ci gaba da kutsawa cikin tafiyar kai tsaye_
_Shin me kuke tunanin CAPTAIN AA ɗin mu zai aikata?, kuna tunanin ze tafi can UMMULYOODAH Ne?, ko kuwa ze tsaya seya kammala abinda ke gaban sa.....?_
08104493215
*BY AMMEY LAYLERH 💐*
༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻
# 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ
~Na Maryam Naseer Mirrah~
𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️
Book One paid
♡
Page 37&38
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
# HE WILL FIGHT
# WAR
```O Allah, grant us the strength to overcome our weaknesses and the wisdom to make the right decisions in life. Bless us with Your mercy and forgiveness .May your prayers be answered, and may you always be guided towards the path of righteousness and goodness
AMEEN 🤍🤲 JUMMAH MUBARAK 🕋📿```
♡♡♡♡♡♡♡♡
ꨄYana kaima mirror'n dake ɗakin wani irin bugu, yana zube gwiwwowinsa ƙasa, yana me sake fasa wani uban ihun da yafi na farko, domin kuwa irin uban abinda yaji ana masa a tsakar kansa inba ihun ya fasa, ya san ba zai taɓa samun sauƙi ba. Se dai me makon yaji sauƙin hakan, Sema ji da yayi zuciyar sa na sake ɗaukar wani irin raɗaɗin ɗaci da ƙuna da tayi. A wani irin zabure ya miƙe tino da waccen paper ɗin da yayi, wacce take cikin envelope ɗin nan, don haka take ya isa ga bag laptop nashi yana zugeta gaba ɗayanta, wawuro envelope ɗin yayi yana runbumota zuwa jikinsa, har lokacin jikinsa be dena wannan rawar tashin hankalin da yake a ciki ba, envelope ɗin ya kama yana yageta, tare da saurin warware fara tass ɗin takardar da take ɗauke da ja ko ma ɓakin rubutu ya kamaci ace ya ƙira shi da shi ohon masa.
```Wannan ZUCIYAR me ɗauke da TAURARI ta TAURARO ce!, Idan akace TAURARO ana nufin abinda kyalli ko tarihin sa basa taɓa gushewa ata ko wacce fuska. Kallon gajimare daga sararin samaniya, tamkar zanen wata ne akan tsaƙiyar ruwa, ada na zaci wannan JARIRIYAR ZUCIYAR ta TAURARO ce wanda hasken sa baya taɓa gushewa, sedai kash wannan kalmar ta ƘADDARA da kuma DA ɗinmu ta riga da ta wuce, shi ke nufin rugujewar kowacce iriyar ƙaunar dana jima yima, Na so ka a loƙacin da nayi tunanin mu ɗin tsatso ɗaya ne ya haife mu. Wanda gaggawa da rashin jure hakan daga gare ni ya sanya ni fidda wani a madadin kai, a Matsayin ABOKIN RAYUWA TA LOLLY, Sai dai kash a wannan lokacin kalma ɗaya tak itace tayi sanadiyyar kulluwar komai, Kamar a yanzu ma wannan kalma ɗayar itace ta zama sanadiyyar buɗewar mafarin Lamarin, ƙofar da sannu a hankali surrukan dake danƙare a cikin ta za su dinga silalewa har su bayyana a daidai lokacini da ba a buƙace su ba.
Ta wanzu domin ta tabbatar da rufewar rayuwar da ita kaɗai ta san ya mafarinta yake, Ta wanzu ne na tsayin lokuta a bayan duhuwar da take jin za ta zame mata shamaki wajan bayyanar da sirrin dake bisne cikin ta, wanda take da tabbacin zai iya taɓa kowa ciki har da ita kanta,
Sai dai kash! Nayi ala wadai da wannan kalmar ta ƙaddara, da ita ba ayi mata wayau. Kamar yadda ba a yi mata dabara, haka kuma tana iya shammatar kowa da komai yayin da za ta bayyanar da kanta. Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya, da sukace gajen haƙuri kan iya sanya mutum ya gaza ganin Alheri ALLAH. Mutane da yawa suna gaggawa su yanke HUKUNCI kamar yadda ni nayi LOLLY, suna kuka da kaddara suna manta cewar sune SUKA JAWO hakan, suna mantawa cewa jarrabawa ɓangare ce ta rayuwa. Kamar yadda ni manta hakan, ashe akwai dalili, akwai DALILI na wanzuwar hakan, tabbas se a yau ni NUFAISA na sake yarda da cewar ALLAH yana tare da masu haƙuri, kuma yana basu lada ta hanyar hakan, ba tare da iyaka ba indai ka iya jurema duk abinda ya gagara, domin tabbas shi ne yace bayan tsanani akwai sauƙi, kuma wanda ya jima yana yaƙi da haƙuri da kuma juriyarsa, tabbas zai bashi abinda ya jima FATA da kuma BURI harma zarta abinda bai zata bai tsammata ba. Da ace nayi haƙuri da jurewa da WANNAN ZUCIYAR TA TAURARO CE, Sedai naji tsoro ne a lokacin da gudun jefa kai wa halaka, har ƙarshen abadan abada, MY JEAN-CLAUDE... IF YOU'RE NOT MINE.... I'LL HAVE NO REASON TO LIVE.....```
Tin kamin ya kai ƙarshen Rubutun yaji zuciyar sa ta wani irin harba mishi, wani kalan miƙewa tsaye yayi tare da nufar ƙofar wani ɓangaren na daban,yana shiga parlourn ya maida ƙofar ya rufe, kana ya zame tare da zama aƙasan tiles ɗin daɓas, tare da jingina bayan sa da jikin ƙofan parlourn. lokaci guda kuma ya shiga kokuwa da numfashinsa dake barazanar ɗauke wa. Cikin wani irin murya da tsantsar tashin hankali ya shiga furta.
_"Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha, Ya wadud³ ya zul'arshil Majeed, ya fu'alillima yurid, As'aluka bi izzatil lati layuram, wa mulki kallazi la yurad, Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n_" haka cikin wani irin tashin hankali yaci gaba da karanta duk wata addu'a da tazo bakinsa, har zuwa lokacin kuma jikinsa bai daina masa rawan da yake masa ba, sakamakon wasu shuɗaɗɗun abubuwan daya saba gani cikin mafarkinsa, lokaci guda yaji wani ɗan iskan masifaffen zazzaɓi na rufe sa cikin kiɗima ya fara zantukan zuci. Sakamakon tunowa da yayi yanzun fa shikenan wani na daf da mallakar FAISAH ɗin sa, Innalillahi Wa'inna ilahi rajiu'n. Ya sake ambata a can cikin tsaƙiyar ƙirjinsa, Shin wannan wace iriyar ƙaddara ce me zafi har haka?, shin me ya sa ta ne san tashi da abu mafi soyuwa a cikin duniyar sa?, me yasa seda komai ya gama kwace musu kana mabuɗin lamarin ya fara, me yasa ƙaddara zata masa?, me yasa zata ƙi tausaya mata a daidai wannan halin da yake a ciki?, Me ya sa ƙaddara zata banzatar dashi tamkar tana mancewa dashi ne, cikin DUHUN DAREN DA YAƘI TAUSAYAWA, tsaye ya miƙe daga yacce yaken yana me sake wawuro takardar daya gama cukuwkuye abarsa, yana ci gaba da karantawar, nan take jikinsa ya sake ɗaukan wani irin masifaffen rawa tamkar mazari, yana wani irin tsuma ji yake tamkar ana tsikara masa allurai ne a gaba ɗaya ilahirin jikinsa, lokaci ɗaya kawai yaji wani irin baƙon yanayi ya ziyarcesa na fargaban RASHI; cikin wani irin yanayin daya kasa tantance shin mafarki yake ne, ko kuma azahirance ne duk abubuwan ke faruwa amma ya kasa tantance hakan, don haka cikin rashin sanin madafa ya ci gaba da karanto duk wata addu'a da tazo bakin sa. Yayin da yaji numfasa naci gaba da fusga,
adduo'i ya cigaba dayi cikin ikon ALLAHA albarkacin Adduo'i kuwa da yake da kuma zuciyar namiji dake da dakiya yasa yafara dawowa hayyacinsa.
Cikin wani irin yanayi mara misalta, ya ɗago eyes ɗinsa da suke a lumshe yana sake sauƙe ganinsa akan farar takardar, don haka ya ja wata iriyar ajiyar zuciyar da seda ya sanya ƙirjinsa motsawa, wanda hakan har ya bama six packs ɗinsa dake kwance damar motsawar shima, yatsun hannuwansa biyu ya sanya yana tura su cikin sumar kan shi ya fesar da numfashi. Cikin wani irin slow ya sake buɗe lulu eyes nashi, tare da sauƙe idanuwansa kan fuskar ta da yake kallonta saman screen na woyar shi kamar ba gobe, kafin a wani irin hankali ya motsa bakinsa wanda ni kaina banji ko miye yace ba. Ya shafa fuskanta ta saman screen na woyar, wani irin rolling idanunsa yay da suke a mugun miskile ya furta. "Wyh? Me yasa who *SHONERH* (Shona) ?" ya faɗa in a wisfa. Domin jin yay duk wani emotion's nashi da suke jima shuɗewa within all this years, be taɓa tsintar kansa cikin tsaka me wuya irin yau ba. All daren ranar be runtsa ba se wajajen ƙarfe ukun dare bacci ya ɗan sace shi, dan haka ƙirar sallahn farko a cikin kunnen AA ya dira dake kwance, saman lallausar italian bed ɗin sa, da yaji off white cotton bedsheets me tsananin taushi ya rufe daga jikin shi har izuwa kan kyakkyawar fuskansa, da adda'ar bacci ɗauke a bakin sa ya farka daga ɗan baccin daya sama surar cikin ɗaki kun, ɗan ware sleeping eyes nashi yay cikin kasala, bai motsa ba sai after like 5 scnds, lokacin ya idda adda'arsa kana ya zubo da ƙafafunsa da bisimillah akan lallausan carpet na room ɗin, a natse ya miƙa hannunsa ya kunna wuta,wata tsaftatacciyar farar riga ce ta bacci kuma mara nauyi ajikinsa da dogon wando shima mara nauyi lallausa, goran ruwan dake bedside drower nashi ya ɗauka yasha sau biyu kana ya mayar ya ajiye, adan hanzarce ya miƙe ya shiga bathrum yay alwala ya dawo tare da cire rigar sa, yana ɗora wata nevy blue jallabiya me tashin kamilallen ƙamshin mayen tularensa na kylian love, kai tsaye masjid ya nufa, duk da kasan cewar tsakanin inda yake da masjid ɗin, akwai ƴar tafiya, amma hakan baya taɓa hana shi zuwa kowacce salla, ciki kuwa harda ta asuba. Koda ya dawo be sake fitowa ba dan ko breakfast baiyi ba, duk kuwa da yadda guards nashi dake tare dashi su kayi ta zaryar sanar masa. Amma haka ɗan bawan ALLAH'n nan yay ƙememe Yaƙi ya fito, ganin hakan ya sanya guards ɗin sa cewa akai masa side nashi, sedai kuma suna cikin tafka mahawarar wanda zai je sai gashi ya saƙƙo.
Kaman kullum haka ya fito su kuma cikin girmamawa sukà ringa gaidashi, yana amsa masu a takaice kamar koda yaushe, zaune ya kai kan couch fuskarnan kada ran kada han. A yadda su kayi zata da tsammani se kuma suka ga kishiyar hakan, domin kuwa sun zata breakfast nashi zayyi, Sema laptop nashi dake gaban sa, wanda gaba ɗaya ya gama maida hankali da rayuwarsa akan aikin daya duka fa yi, wine yace su bashi kawai, kafin kiftar idanu kuwa se gashi sun ɗauko mishi daga cikin deep fridge ɗin dake floor ɗin.
*NIGERIA*
_★NUFAISAH_
Ata ɓangaren Nufaisah kuwa wasa wasa data fara jinya, bayan kawo akwatunanta da gidan su Mohan sukayi, har seda abun ya kai ta kwance, abu kamar wasa har ya fara zame mata kamar wani strange ciwon ODD wato _oppressive defiant disoder_ ganin dai yadda iyayenta suke nemar tada hankalinsu akan sabon sabbin bhvrs ɗin ta yasa ka ta ɗan fara jurewa hakan, sedai haƙarta be cimma ruwa ba, domin kuwa har hakan seda ya kai ta ga kwanciya jinya a wata private hospital. Dan haka koda suka dawo se iyayen suke tsaye aka ta, harma aka sake ɗage zancen bikin nata aka ƙara sati biyu. Sosai ta ɗan ji sauƙi², amma dai koma yaya ne kawai tana taɓa rayuwar ne.
Ko a yanzu ma tsaye take a cikin babban parlourn gidansu, hannunta rike da wani mug, me ɗauke da zazzafan shayin ɓaure da yaji kayan ƙamshi, jikinta sanye da 3q jeans black sai wata armless brown, tana daga tsayen da take inda take facing da ƙofar shigowa parlourn, kafin a hankali kuma ta nufa saman cushion dake ƙawace da parlourn, babu motsin kowa se nata ita kaɗai, ita ɗin ma kuma ba wani kyakkyawar motsin kirki take yi ba, cikin wani irin sanyin daya jima kama jikinta, ahankali ta soma tafiya tana nufar garden na ƙayataccen gidan nasu.
gida ne da ya mugun tsaru, sam sam baya da wani tarkace sema wani irin tsarin da yake da, dan kusan kominsa a kiyasce yake tun daga kan tsarin ginin gidan, har zuwa komai da komai da yake da. A kan wata farar sofa ta kai zaune tare da wayarta, gaba ɗaya ta gama yankemawa kanta abinda ya kamaci ace tayi a karo na biyu kamar yadda ita ne ta yankema kanta a karo na farko. Don haka cike da yaƙini da kuma yarda da kai ta soma rubutun ta, Rubutu bame yawa tayi ba, amma kuma me kama zuciya ne rubutun.
Tin da ta gama rubutun nata ta tasa wayar nata a gaba ta zuba mata fararen idanuwanta, wanda a zahirin gaskiya bawai kallon nata take ba ta tafi ne duniya irin ta tunanin *Ruhinta* wato ALIYU ABDULLAHI (lolly), tana jin tana son tayi faɗa da yaƙin wannan mara karar ƙaddarar data lulluɓe tsakanin su tin farko, kafin kuma ta yaye shijjabin data jima lulluɓa musu ta musu shinge, a daidai lokacin da bai kamata ba, a kuma daidai lokacin daya gama ƙure musu, don me yasa ita ƙaddarar bata san daidai ba? Kuma bata san kara ba?. Ita kaɗai take yaƙin a zuciyarta, tana jin kamar rayuwarta na gab da faɗuwa ƙasa ne, domin kuwa ji take yi kamar daga yau bugun numfashinta ze tsaya da aiki ne. Tana tsaka da wanann tunanin ƙiran woya ya shigo cikin woyartan. A natse ta waiwaya don duban me ƙiran,zuciyarta ce taji ta sake mata nauyi ganin me ƙiran, sunan *M*h*n _MOHAN_ data gani ne ya sanya jin zuciyar na ƙarasa cin kushewa da tarin abubuwa ma ban banta. Domin kuwa haka yake mata a ƴan kwanakin da take son kaɗaice kanta, amma kuma shi kusan kullum seya ƙirata, kuma hakan baya sanya wa ta ɗaga woyar nashi, ga kwanakin bikin kullum ƙara kusanto ta suke. Wanda ata ɓangaren mahaifiyar nata take amsar wani irin gyara me rai da lafiya na musamman, Wani runtse idanunta ta sake a karo na biyu lokacin da wayar nasa yake sake shigowa cikin wayar ta, ji tayi zuciyarta na woni kalan tafasa wai me yasa a wannan gaɓar kam Mohan ke son ƙarasa halaka rayuwarta da shegen ƙiransa na azaba ne?. Hannunta ta kai da niyar katse ƙiran, sedai bisa kuskura tayi answering na call ɗin. Yana jin anyi answering call nashi cikin ɗan yanayin fusatuwa da kuma kaushin dake cikin muryansa ya furta. "Ki gama duk wani kauce² da guje gujenki, daga ƙarshe dai dole mallakina zaki zama Nufaisah, ke tawa ce har abada ba zaki iya guje min ba, kamar yadda baki isa kaucema aure na ba koda kuwa na dare ɗaya ne, dole sena ɗanɗani zumarki Nufaisah, tin da dai kin hana min mallakar jikin naki Ata sauƙi, har seda na kashe kuɗaɗe na aure ki, don haka maza² ma ki shirya ma kanki cewar wannan aure na kauda sha'awa, kuma ki sani daga inda na gama gusar da wutar ƙishin dake raina, sena lalata rayuwarki Nufaisah, kuma a tsarin aure na babu saki, amma ki sani sena gama lalata rayuwarki, kwatankwacin yadda kika wulaƙanta tawa rayuwar a lokacin baya, ki saka wannan a ranki, you're forever mine har gaban abada, inyi kuma yacce nake so dake Nuf.......
Tin kan ya gaza ƙai ƙarshen maganar nashi ta taryi numfashinsa ta hanyar. "Idan har kasama damar hakan kenan Mohan?, domin dama wannan zuciyar bawai ta amsheka a Matsayin ABOKIN RAYUWARTA bane na har abada, kawai ta zaɓeka ne don gudun faɗawa daga halaka, kuma yanzu anyi walƙiya gaskiyar ɓoye ta fito fili, don haka seka shirya yaƙi, domin kuwa a daidai wannan lokacin ZUCIYAR tana ga wanda ya dace ne, idan kuma ka shirya yaƙar wanda aka yi ZUCIYAR domin shi dama seka shirya yaƙar hakan..... Tana kammala maganar nata ta wani irin datse ƙirar tare da cilli da woyar, fuskar nan da daman murmushi da far'a abu ne da suka jima yi ma fuskar nata tazara, domin kuwa kuwa cikin ƴan tsakanin nan samm ganin koda farin haƙorinta, abu ne daya jim yin kaura a tata duniyar dai. So take ta karfafa kanta cewar, a yanzun da da ba abu ɗaya suke ba, domin kuwa dai yau ɗin ka ta banbanta da ƙaddarar jiyanka, goben ka ce kaɗai zata tabbatar maka da hakan, kuma itama ta jima yarda da hakan tabbas, cikin zuciyarta take furta. _You can do this Nufaisah, you have to do this, ke ɗin a yanzun ba NUFAISAH ce ba wacan Nufaisar ta baya bace, ke ɗin a yanzun wata sabuwar Nufaisar ce, ba NUFAISAH ta lokutan baya ba, wannan ɗin wata sabuwar jaruma ce...
Haka ta shiga ƙarfafama kanta domin karfafawa kanta guiwa, daman waye zai karfafa matan?, amsar itace babu, don idan ba ita ɗin kanta ba, babu me ƙarfafa matan, Mikewa tayi ta soma takawa sannan ta ɗauke kanta daga kallon wayar ta da take yi, wata ajiyar zuciya ta sauƙe bayan ta ɗauka wayar ta nufi ƙofar fita daga garden ɗin,tana jin wani irin so da ƙaunar da bata taɓa yima wani mahaluki ba take masa,wanda ba za a iya ɗora shi a kalan kowanne mizanin awo ba, don ya girmi hakan. _I will call you Back_ Haka taji kamar gilmawar fitar maganar shi, amma kuma tana rasa ta inane maganar ya fita, saurin kallar wayar ta tayi dake hannunta sedai kuma taci screen, basar da hakan tayi tana koma hanyar komawa cikin gidan nasu.
Cikin wani irin ƙuncin da take sake jin kanta a ciki haka take tafiyar, sedai na yau ɗin ya zama daban da sauran kwanakin don gaba ɗaya ta gama zama so silent, maganganun Mohan ɗin gaba ɗaya sun gama kassara mata jiki, samm babu wani abu me kama da ƙarsashi ko kaɗan a tattare da ita. Duk kuwa da cewar yadda Ammeyn ta ke tsaye a kanta,amma zuciyarta taƙi yarda tare da aminta da hakan, Se ma ji da take yi kamar ta tafka wani ƙato ton kuskure ne mara iyaka, Har a ranta take jin wannan ɗan yen hukuncin nata data yankamar kanta a da be gama yankuwa ba, don haka ma tinda ta wuce samanta bata sake leƙowa ko ina ba har zuwa dare, domin bata gama dawowa daidai ɗin taba, gashi kuma bata san bata son tayarma da iyayen nata hankali akan ire iren banza yen maganganun da Mohan ke jifarta dasu a ƴan sati kan nan, don har barazana yake mata cewar, tsaf wllh ze bayyanasu ga hukumar da suke neman iyayen AA, bawai tsoron hakan take jiba, don a ranta bata ji ba akan daidai ɗin sa yayan nata ya yanke wancan hukuncinba....
♡
A ɓangaren AA kuwa shi kaɗai yasan abinda ya gama tsarama ransa, akan matakin da yake son ɗaukarma kansa. Ɗan lumshe janyayyun idanunsa da dama suke a janyen yayi rubutunta daya gama karantawa ɗazun na dawo masa daki daki a tsakar kansa....
_My heart I'II always stay by your side_
```Can't live a moment without you swear I'II fall apart```
_Can't stop thinking about you as long as I breath _
♡My Nie!, can't love anyone like I love you♡
_you're my word!, MY reason to be alive, MY Nie for you can never end....._
*You're My Destination!!!.....*
*You're the journey......*
*You the one that dweeds in mee my mine!!! *
Wata iriyar kyakkyawar iska ya fesar, yana ƙoƙarin hana kansa abinda yake son aikatawa, tamkar gilmawar tsawa haka yaga gilmi da kuma sauƙar maganar ya yanki tsaƙiyar ƙirjinsa. "Karka sare da wuri haka KAMAALAH ƊAN ASHFUD JIKAN KAMAALA RAHEEM DAWOOD, A cikin wannan rayuwar a yanzu dole seka zama JARUMI a rayuwar wasu, sannan kuma dole ne seka zama UBAN DABA ata wasunsu, Yanzun ne lokacin yaƙinka ze faraaaaa...."
Wani irin dakar kansa da hannunsa yayi yana jin wani special emotions na kama shi, waya yayi da bata wuce 50 second ba, yana datse ƙiran bayan an gama tabbatar masa dacewan flight nashi ze tashi ne da biyar na yammacin gobe idan ALLAH ya kai mu. Ajje wayar a gefen sa yayi yana kishingiɗa, wasu abubuwa na tsumma namonin jikinsa, don ko iyakar ambatar sunan ƙasar aka yi wani irin abu yake ji na musamman. Kamar kuma wanda ya tina wani abu, yay hanzarin sake ɗaukan wayar sa, tare da shiga chart nashi da Abbunsa, saƙo ya ajje masa yana fita a WhatsApp ɗin....
JAN GIDA
ALHAMDULILLAHI Maman Nuwairah ta koma gidanta, bayan fama da aka sha, har zuwa lokacin kuma babu wani abu daya sanja a gidan, Sema wasu sabbin abubuwan da suke sake bullowa a kowacce safiyar duniya da zata waye. Mafi sauƙin da taji wanda kuma take sake godema ALLAH akan hakan shi ne, dena sanya damuwarsu ranta, bayan ta dawo ɗin nan, haka ƙawaye wasu daga cikin ƴan uwa suke zuwa mata da zance akan itama ta miƙe tsaye akan kafafunta, ta nemarwa kanta mafita, amma kuma se take basu amsa da cewar.
"Da naso kama gidana a tin farko, da ban bar Abban Nuwairah ya ƙara wani auren ba, bare har a ɗebo tarkace su zo su cika min gida, harya kwace min Miji ana juya shi yadda ake so ba, abu ɗaya da zan ci gaba da bama mutane amsa shi ne cewar. _Bazan taɓa bin malamaiba, Akan Auwal, domin nie don ALLAH nake son sa, kamar yacce na aure shi domin ALLAH, zanci gaba da addaar ALLAH Ubangiji ya kawomin mafitarsa, don wannan HUKUNCI ba nawa bane nashi ne, bana gaggawa akan lamura na, domin idan nace zan ɗaukarwa kaina wani matakin daban, wala ALLAH kuma nie tawa Rayuwar tazo ƙarshe, kunga kenan me aka yi?, wannan haƙurin da nasha na baya zaman shekara da shekaru na ɓata su a banza, sun tashi a wofi, don haka na zubama SARAUTAR ALLAH idonu, don shi ne zai kawo mafitar a loƙacin da zata be tsammataba....._ duk kuma wanda ta faɗama wannan maganar se jikinsa yayi sanyi, yaji In sha Allahu ze tayata ta addaa, ko a wannan komen da tayi wayar dubu ɗari da hamsin Auwal ɗin ya sema Husna ƙanwar Jidderh. Basu nuna mata ba, Sema kame kamen da suka dingayi da kuma ɓoye ɓoyen wayar, ALLAH sarki ita kuma bata san yanzun sam duk wani almin dahanarsu ba damar ta yake yiba, ta jima da jinginar da hakan, harde kuma dan kansu suka dawo mata magana, a da ne ta damu da ire iren rashin mutunci da idan Husna ɗin tayi yake damunta, amma tin da ta sanya wa ranta salama hakan ya dena damunta, to ma don me ze dame ta?, ta tabbatar banbancin yarinyar dasu a gurin mijin nasu kaɗan ta, yadda zasu ganshi da gajeren wando Haka zata ganshi, yadda zasu gyara masa bedroom nashi haka yayarta zata sanya ta gyara masa, kai in banda wata toshe war kai da kuma rashin lissafi da basira wai ke sa kike a Matsayin matar mutum, amma kene a kitchen, ita kuma ƙanwar naki ko nace ƴar uwar nata ita ne me kula mata da mijin, tana can gaban wuta, ita kuma tana nan a A/C da A/C wurin mijin ta duk ranar girkin ta tana kula da mijin. Ke in banda ma jakanta da ko a cikin matan ma ke rako su duniya kika yi har ki sakarma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 23