Share this page
Kuma ta sani tin da har taji bala'in Baba Asaben to kuwa ta sani abincin dare ne umman nasu ta hana ta. A haka ta ƙaraso cikin gidan rai ɓace duk da kasancewar uban gajiyan data kwaso a wurin aikin nata. Shigowarta gidan ne ya dakatar da bala'in Baba Asaben, don tanayin Hannah ɗin duk cikin yaran umman sunfi shiri da ita, "Yauwa Ƴar Albarka ƙara da ALLAH ya kawo min ke, zo maza ki bani ko na shan shayi ne, da awarar bakin layi in naci sena ɗumama cikina da ruwan sha yin tin da yau uwar ki tayi halin." ta san me take nufi da tayi halin, abincin data hana take nufi. Don haka ta buɗe wallet nata tana zaro mata ƴan ɗari biyar biyar guda biyu, a cikinu irin kuɗin da Apc Malek ya bata. Nan ta shiga mata godiya kuwa tana sake damƙe kuɗin a hannun ta sosai, gudun ma kada umman ta kawo musu wurta, don halinta ne tsaf zata iya. Daga nan Baba Asaben ta tafi zuciyar ta fall cike da farin cikin samu jika ta gari, tini ta gama lissafe kuɗinka tsafff, Ta sai awarar ɗari da Hamsin, ruwan bunu na hamsin ta ɓoye ɗarinta bakwai da kaɗan kaɗan ta ringa cin dadi abun ta. Aikuwa haka aka yi tana fita ta sama me awararta, Ƴar biyu hamsin manya wacce ake so yawa da filawa ta sayi a barta kamar yacce ta tsara, tana yin gaba ta sai ruwan bununta se gida. Ita kuwa Hannah kai tsaye ɗakin da ya zama mallakinta ita kaɗai a yanzu ta nufa, kayan aikinta ta fara zare wa tare da ɗaura fallen zani tana fitowa waje bayan ta rufa kanta zuwa ƙirjinta da ɗan kwali, ruwan ɗumin data gani akan wuta tayi wuf ta kwashe rabin sa, tana faɗa wa bayi bayan ta sirka da ruwan sanyi. Bata wani jima ba ta fito a ba yin kasancewarta bame nauyin wanka ba. Kai tsaye nafilar data saba tayi, kafin mahaifiyarta ta shigo ɗauke da kwano a hannun ta tana dire mata dambun shinkafar da tayi tin na rana, kanta ta girgiza mata tana ce da ita ta ƙoshi, tare da miƙa mata baƙar ledar data shigo da ita. Kwanciyar ta tayi daga haka tana kunna datar wayar ta, shi ta fara dubawa ta kuwa ci sa'a ta ganshi online. _Hi Assalamu alaikum da kyakkyawan da babu kamar sa a duk faɗin NIGERIA _ alamar riƙe haɓa ya turo mata da kuma ta zaro ido waje yana rubuta _Ki rufa min asiri bama iya Kano ba duk Nigerian gaba ɗaba, kuma tsaya ma ranar fa kika gama ce dani ba bu yabo babu fallasa ne niɗin._ Alamar dariya me rugujewar haƙora guda biyu ta tura masa ɗauke da Rubutun. _A ranar kafin na kware maka ne yallaɓoi, se daga baya na gane ashe ƙatoton kuskure na kusa tafkawa, ALLAH a yanzu gani nake ji nake kai kaɗai ne kafi kowa kyau a cikin wannan duniyar. _ da kyau ya ƙara gyara kwanciyar sa a cikin ransa yana furta anzo wajen. Cikin tarin pisc na goods guys ɗin da yake sauƙewa a wayar sa ya shiga, hannunsa be sauƙa kan kowa ba se akan pisc na Captain AA da aka turo masa, ba tare daya lura sosai ba hannun nasa ya taɓa yana tura mata tare da rubuta _Ciki harda wannan? _ Rasss haka taji gabanta ya ɗan faɗi zuciyar ta tana bugawa, tare da soma ƙarewa pisc ɗin kallo. Wata ijiyar zuciya ta sauƙe tare da rubuta. _Ni ai banga komai ba tattare dashi ba sabo da ni kai zuciya ta da idanu wana Sir Maleek kaɗai suka sani a cikin mafi kyawawan duniya_ ★ wani alamar zaro ido ya tura mata yana me rubuta. _Ki rufa min asiri kada kyawawan duniya su jiki kina wannan saɓon_ sticker na dariya ta tura masa tare da rubutun. _Yabon gwani ai ya zama dole oga, kamar yacce masu iya magana suke cewa wai habaicin kura ai name kare ne, to nima yau ɗaya dai na ɗana yabon abin da yake mallakina_ _Inye wato ma har na zama mallakin naki_ ya rubuta mata tare da alamar tambaya da kuma irin ta tagumin nan, _Ehhh mana ko kana tantama ne yallaɓoi? _ ta tura masa tare da sake rubuta masa _Ba fahari ba nake babu irin ka a sashena, ina son mu riƙe juna da amana har bayan rai in mun yi macewa_ stickers ya turo mata irin ta ratsa zuciyar nan, haka dai suka ci gaba da firarsu, wanda daga ƙarshe suka koma voice. Ita ne ta fara masa sallama sakamakon baccin daya ci ya gama cinye idanunta ..... ☆ ABUJA ꨄ Yamma ci ne mai matuƙar daɗi me tafe da wani irin yanayi na musamman, haka kuma yau ɗin babbar rana ce data kasance ta musamman, wato Jumma'a ranar da take ɗauke da albarka da kuma rahamar Ubangiji kala daban daban. Wannan dalilin ya sanya sassanyar iskar data kasance ta hadarin da yama samaniya ado yake bada wata kalan iska mai cike da tsananin daɗi, da kuma sanya shauƙi ke. Wanda a hankali a hankali wannan iskar ta fara fita da yayyafin ruwa me dadi, kafin sannu a hankali ruwan ya soma yin ƙarfi sosai. Ruwan ake yi sosai inda yanayin yayi wani irin daɗin gaske, ga wata irin ni'imtacciyar iska wadatacciyar da akaci gaba da yi tana sake gauraye ko ina, lokacin wuraren ƙarfe 5 ne na yamma amma sai kayi tunanin dare ne sosai, saboda duhun sauƙar ruwan. Tsaye yake gaban wani photo frames irin na da ɗin nan, ya tsura masa kyawawan fararen idonuwansa, yana jin kallar pisc ɗin na haifar masa da tafasa namomin jikin sa, ci gaba da kallar photon yayi wanda ya sanya jikinsa fara wani irin tsuma,Sosai ya sake kurema photon kallo kyakkyawar balarabiyar mata ce da mijinta, duk kan su fuskokinsu ɗauke da kyayataccen murmushi wanda ya bayyana hasalin martaba da kuma daraja shi.Yau kwanan pisc ɗin uku da a wurin sa daya binkito a kayan bappansa, ba tare daya san yayi hakan ba. Domin bame sauƙi bane a wurin sa, don hanyar warware wannan kullin bame sauƙi bane a gare shi cikin sauƙi har haka ba. Wani wahallen numfashi fesar domin tin ranar farko daya fara ganin pisc ɗin jikinsa ya ɗauki wani kalan tsuma, har zuwa yanzun haka ma da yake tsayen. Ahankali take tafiyar slowly hannun ta ɗauke da ɗan madaidaicin basket wanda yake ƙauke Pepper meat se kunun gyaɗar da yaji madara. Duk wani taku da zata yi jinsa take har tsakar kanta. Bata ganshi a parlourn saba, don haka ta nufa master room nashi. Tsayen da taganshi ne yasa ta tsurawa bayan nashi ido, tana mejin zuciyarta na bugawa tightly. Sake faɗuwa mai tsanani gaban ta yayi don ganin yadda kamar jikin sa ne yake rawa. Ƙirjinta ne ya sake bugawa da ƙarfin daya sanya ta ajje basket ɗin dake ɗauke a hannunuta, tana me nufar inda yake kai tsaye kafin ahankali ta buɗe bakin ta cike da nutsuwar muryanta a bayyane tana me ambatar sunansa. "lolly?" Ɗin data ambata ne ya dake shi har tsaƙiyar kansa tare da saurin maida pisc ɗin ma'ajin daya masa na musamman. Yana juyowa gaba ɗayansa inda har zuwa lokacin jikin nasa be dena rawar yake yi ba, ƙasa ta ɗanyi da kanta tana damƙe hannuwanta dake ɗan rawar daya fara itama, Kafin cikin nutsuwarta ta sake ce dashi "Lolly kana lafiya kuwa?" ta furta tana sauƙe numfashi mai sanyi, da kulawa sosai ya dube ta tare riƙo hannuwanta yana nufar sofar da ke gaban gadonsa da ita, zaunar da ita yayi saman sofar shi kuma yana zama bakin bed. Se kuma ya gaza furta mata komai yana riƙe kansa da hannuwa biyu zafin kansa nemar tashi. "Kayi haƙuri yaya ita rayuwa dama haka take ta kan zo da sauyi a ko wanne yanayi, koma dai miye ke damunka duk da kasancewar bansan ko miye ba, idan kayi haƙuri wajen jure ƙaddarar hakan tare da adda'o'i se kaga komai yazo mana da sauƙi domin adda'o'i kan sassauta kaifin ƙaddara........ Suna zaune a hakan har duhun magrib ya kawo kai, inda shi kuma yana can ya tafi duniyar tunani, Kiraye kirayen sallan magribar da ake tayi ne, ya soma ratsa cikin kunnuwansa yana dawo dashi hayyacinsa, tsammm ya miƙe yana yana fita kai tsaye daga room ɗin. Kanta ta dafe da duka hannuwanta biyu idon ta na ci kowa da wasu ruwan hawayen tausayin kanta da kanta. Tare da ɗaga hannuwanta biyu tana me furta. "Ya Allah ka kawo min mafita ni ɗin na kasance bai wace agareka mai ƙasƙantar da kanta, ya rabbi ka kawo min mafita cikin wannan mugun abin dake ƙoƙarin ɓalle min tsayin shekara da shekaru!, kawai zan cema Mohan ya fito dana faɗa cikin wata halakar" Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un ɗin da ta furta shima ya shiga nanatawa yana daga tsaye bakin ƙofar shigowan da dawowansa kenan daga masallacin. Kunnuwansa sukayi masa wannan mummunan jin, kenan itama wai tana nufin tana jin abin da yake ji akanta kenan kome?, Cikin zuciyar sa ya furta _Ya ilahi me hakan ke nufi dasu ne to?, son juna suke, son kasance a ƙarƙashin inuwa ɗaya su ke shi da ƙanwarsa, da a gaban idon sa Ammeynsa ta reni cikin ta tare ma dashi, a kuma gaban idon sa Ammeyn shi ta haifa masa ƙanwar tashi amma ALLAH ya jarabcesu da son junansu.?. Don haka yay hanzarin komawa da baya yana fasa shiga room ɗin zuciyar sa na bugun uku uku. Be dawo gidan ba tin da ya fita se bayan sallar isha'i, Kota ɓangaren iyayen nasa bai bibi gudun kada ma ya haɗu da ita. Sedai me yana shiga ya ganta kwance saman carpet ɗin ɗakin, wanda da dukkan alamu gangarowa ma tayi ta faɗo. Cikin rashin kwarin gwiwa ya nufa inda take kwancen, gani yayi shijjabin jikin ta kamar ya shaƙe ne, don haka ya kai hannunsa saitin wuyar nata, kallon yacce ta duƙunƙune a cikin shimar ɗin yayi, haka yayi kaman zai gyara mata amma kuma sai ya fasa, tare da saurin ɗauke kansa daga gareta. lokaci ɗaya ya haɗe fuska tamkar bashi ba,tino zancenta na ɗazun da yayi ne ya sashi rumtse idanunsa tare da ɗan cizan jajayen lips nashi, a hankali ya soma girgiza kansa, yana jin zuciyarsa babu daɗi,wani irin abu yaji yana yi masa yawo acikin jikinsa. NUFAISA kuwa da tin farkon shigowarsa ta ji shi ne ya sanya ta kasa buɗe idanunta, har zuwa ɗurkusawan da yayi gabanta bugun zuciyarta na sake tsananta, yayinda ƙirjinta ke harbawa da sauri. Ahankali kuma taɗan buɗe idanunta wanda cikinsu ya cika da ruwan hawaye, ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, tare da ƙoƙarin shanye ruwan hawayen nata, dan batajin zata iya barinsu sukai ga sauƙa akan fuskar ta, ɗan satan kallon sa tayi wanda har ya miƙe tsaye yana barin wajen. gefe guda kuwa zuciyarta ne ke saƙa mata abubuwa da yawa, azahirance kuwa so take ta ɗan ƙara satan kallon nasa, amma kuma kwata kwata tsoro da fargaban da takeji sun hana ta hakan. A jikin sa yaji farkawan nata, be juwo ya kalle ta ba ya furta "Idan kin fita ki kulle min ƙofar" wanda hakan ya cilastata miƙewa jiki a sanyaye tana fita gaba ɗaya. ☆ ꨄTabbas SOYAYYA wata irin ƙaddarace da take ɗauke akan kowanne bawa, sannan kuma wata abace da ba'a iya ganin launinta da ido, hakanne ma yasa ba'a iya sauyata, saidai idan taso takan tashi daga sunanta na SO ta koma ƘIYAYYA. Acikin kowani rayuwar ɗan Adam akwai salon ƙaddarori masu tarin yawa, akowacce duniya a kuma koda yaushe ƙaddara tana tafiya ne daidai da rayuwa, haka kuma tana rayuwa da mu ne cikin farin ciki ko akasin hakan, abu ɗaya ne yake tafiya acikin zuciyar kowanne bawa, shi ne MURADI, FATA, da kuma son samun ABINDA ZUCIYA KESO. Sannan kuma babu wani bawa wanda ke iya gujewa tarin ƙaddarorin dake bibiye da shi, da kullum suke binmu tamkar inuwar mu, Lallai ƙaddararmu tana gudana ajikinmu tamkar jini, a kowacce rana a kuma koda yaushe abubuwa ma ban banta suna faruwa, to haka itama ƙaddara takan iya sauyawa ako da yaushe. Shin su kuma tinda ya fahimci tasu ƙaddarar ne salonta yazo da hakan, don haka ya sanya yaƙinin yaƙar tasu ƙaddarar koda kuwa da ƙarfin adda'a ne. Don haka tin daga wannan rana ya ma rage zaman gidan, ya rage amsa ƙiranta a waya da ta kan yi masa a kai a kai. ꨄ kwance take saman ƙayataccen bed nata, tana sanye cikin English wears na riga da wando, inda sosai kayan suka amshi yanayin jikin ta. kasancewan ta ba mai jiki sosai ba, sannan sun zauna ɗas a jikin ta tare da baiyana ƙuruciyan ta fili. Kunnenta saƙale da headphone. Kallo ɗaya zaka mata ka gane cewar hankalin ta na kan wayan ta ne me ƙirar Samsung. Kana kallon ta zaka gane cewan hankalin ta gaba ɗaya na'a kan wayan ne, domin ko kwakkwaran motsi bata yi, sema jifa-jifa takan yi ɗan murmushi, wani lokacin kuma takan lumshe manyan fararen idanuwanta ne tare da runtse su na ƴan wasu daƙiƙu, sannan ta buɗe tare da sake mai da hankalin ta kan screen na wayan. Tin ɗazu ammey ke faman maka mata ƙira amma kuma babu alaman motsin ta, ballantana ma tasa ran za ta ji ƙiran har ma ta amsa mata. "Nuafaisa!!!" a wannan karon kammmm Ammeyn nata ta ƙirayi sunan a ɗan tsawace. Wanda yasa nufaisan saurin zaburo wa tare da miƙewa tsaye tana nufo inda taji ƙiran. Sai faman kwaɓe fuska take tana yatsineta, bata ganta a parlourn ba don haka kai tsaye kitchen ta wuce, wani kallo Ammeyn ta wurga mata tare da cewa. "Me yasa ke wani lokacin wai baki iya abu da lissafi ba Nuafaisa?, ke yanzu kina cikin gidan nan a zaune har se na miki maganar kamamin aiki?" tana ƙara sa maganar ta fice ta barta a wurin duk da hakurin da Nufaisan ke bata. Cikin nutsuwa taci gaba da haɗa abubuwan da zata buƙata wajen haɗa musu dinner ɗin, se da ta kammala soya musu yambol ɗin da Ammeyn ta riga da ta haɗa kana ta apple drinks. Haka ta gudanar da aikinta cikin nutsuwa harta kammala, koda ta gama tuni an soma kiraye kirayen sallan Magariba, don haka tayi saurin jere abincin saman dining table, sannan ta wuce room nata. wanka tayi tare da ɗauro alwala, koda ta fito daga toilet wata ash doguwan riga iran turkish ɗin nan ta saka sosai rigan ta mata kyau. hijab ta san ya sannan ta tada sallahn. Hijab ɗin dake jikinta da tayi salla dashi ta zare, sannan ta saka wani ash hula akanta,tana fitowa Bappansu tare da ammey har sun fito, don haka kai tsaye serving nasu ta soma tana tunaninsa a ranta, ganin yanzun kwata kwata ya dena dinner tare dasu. Tana cikin wannan tunanin kuma Bappansu ya zaro wayarsa daga aljihu, tare da dannawa lambar Yaya AA ɗin ƙira, wanda fitowarsa daga wanka kenan ganin ƙiran Bappan ne ya sashi ɗagawa. "Kazo dining kayi dinner." shi ke nan abinda ya faɗi a takaice, tare da katse ƙiran.Jin Bappan ya datse ƙiranne yasa shi cilla wayartasa kan gado, ba don ya so ba yaci gaba da shirya kansa cikin nutsuwa, wasu irin tarin tunanninka kwance ƙasan zuciyarsa. Haka ya fito se baza uban ƙamshinsa yake, tin farkowan fitowarsa cikin takunsa na isa. zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun parlourn da suka ƙarawa parlourn kyau, sannan kuma suka sake ƙawata shi, facing cap ɗin dake kansa ya cire, wanda kai tsaye hakanne ya bawa asalin kyakkyawar fuskarsa bayyana. Asalin kyau da kuma zatinsa na sake zagaye shi, yayin da yake da wasu irin fitinannun eyes masu kyau da ɗaukar hankali,inda wannan tsananin kwarjinin nasa na naban mamaki ke sake bayyanuwa. Tin da ya ajje p cap ɗin take kallon sa har zuwa saman lafiyayyen tulin gashin kansa dake kyalkyali tana fidda shining na kyau. Inda gaba ɗaya ganinsa ya so birkita mata lissafi, hakanan taji zuciyarta na tsananta bugawa, idanunta da suka sanja launi ta lumshe gudun kada wani cikin iyayen su ya lura da yanayin da take cike. Aikenta da Ammey tayi zuwa ɗakin tane ya sanyata sakin wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, tana miƙewa tabbas idan taci gaba da ganinsa irin haka wata ran kowa ze fuskanta halin da take a ciki wata rana. A bayyane ta sauƙe ajiyar zuciya tana ɗaukan wayan Ammeyn nata ta fito, a lokacin harma ya bar wurin keyarsa kawai ta gani yana ficewa hanunsa ɗauke da jug na drink ɗin data haɗa. Tana ba Ammeyn wayar itama ta bar wurin bayan ta ɗebi yambol ɗin tare da juice tana ma iyayen nasu seda safe, don bata jin zata iya sake fitowa kuma se idan ALLAH ya tashe mu lafiya. To ai shikenan🤗 😅🥰 semu gimtse 🫰 haka nan da wani sabon salon nasu kuma🙃 😊.... 08104493215 *BY AMMEY LAYLERH ✍️* ༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻ # 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Book One paid ♡ Page 15&16 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. *Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank* ♡♡♡♡♡♡♡♡ HANNAH ꨄ "Wannan na jikin photon da kike gani Green snake sunan shi, aikine ya biyo ta kan sa duba da cewar ke mace ce zaki fi iya saurin jawo mana hankalinsa ta ruwan sanyi, kana ganan waɗan nan sune file na criminal ɗin, sauran takardu tare da bayani kuma se daga baya zamu ci gaba da sanar dake komai, Daga ƙarshe kuma ina mai gargaɗinki da ki bi abun a hankali!, kana kibi a sannu domin kafff ƙasar nan a yanzu bana tunanin akwai mutumin da ya kai wannan mutumin haɗari, Wani gwauron numfashi ta sauƙe tare da tarkata takardun tare da hotunan tana solute na IG Moussa, tare da ficewa daga office ɗin. Tana barin office ɗin ta sauƙe wani bahagon numfashi me tafe da abu biyu duk a lokaci guda. Kai tsaye daga nan gida ta nufa kasancewar dama yau dama bata da aikin komai. Tunanin Acp Malek fal ranta, tabbas ta sake gasgatashi akwai mutanen da suke son ganin bayan sa. Akwai masu bibiyar rayuwar sa bayan *Officer Khabeer Mashi Dikko....* tabbas. Dama a wancan ranar yayi alƙawarin jefo ta cikin wasan, kuma Acp Malek ɗin ta shi ya sake tabbatar mata da hakan, se gashi ma tun ba'a je ko ina ba harta faɗo cikin jerin masu buga wasan, kwarai kuwa zata bashi mamaki ko ta ce zata basu mamaki don zuwa yanzun itama ta san ba iyaka su kaɗai bane a cikin tafiyar dole akwai ƙasusuwan bayansu. Kamar yadda IG Moussa yace ita mace ce tabbas zata nuna masa irin tarin baywa da ubangiji yama mata, seta ruguza tunanin wasu mazan da suke ɗaukar cewa babu abin da mata zasu iya, idan ba bautar aure ba, seta nuna musu mata ta kowanne fannin sune jigo da kuma ginshiƙin duniyar baki ɗaya ma, tabbas zata nuna musu se tayi hakan, se hakan ta tabbata. Da waɗan nan tarin tunaninnikan fal ranta harta suka iso zuwa anguwar ba tare sata lura ba. "Hajiya mun ƙara so" mai keke napep ɗin ya faɗi, wanda maganar daya mata a karo na babu adadi shi ne ya dawo da ita cikin hankali da tunaninta. Wani bushashshen yawu ta haɗiye tana bashi kuɗinsa, a ranta tana ayyana _Tabbas sun taro match domin kuwa *AKWAI KURA*, Tabbas dole in shirya yin wannan wasan_ da haka ta sanya kanta zuwa cikin gidan nasu. ☆ Jan gida. "Abban Nuwairah kamar wanka fa naga kayi ?", Maman Nuwairah ta faɗi alhalin ta san ita dai babu abin da ya shiga tsakanin ta dashi, hasali ma fashin sallah ta ke yi. Fuskarsa ya ɗan yamutse sosai daidai yana ɗaukar sallaya ya shimfiɗa murya can ciki ya furta. "Mafarki nayi" daga haka ya sanya gaban sa gabas yana kallon alƙibla, Ita kuwa Maman Nuwairah da wani kalan kallon na gaji da renin hankalinka ta bishi don ba yau ya saba mata irin wannan renin hankalin ba. Don dama ba yau yake mata irin hakan ba idan ta tambayeshi se yace mata mafarki yayi. Dake ta san halin kayanta ciki da bai se kawai ta ɗauke kanta zuciyarta na mata suya sosái, domin sau da dama ta tamkar zamanta da Abban Nuwairah ya ƙare, sedai idan ta waywaya baya Yaranta! Yaranta su ne abin duban ta. idan ta tsallake ta tafi ta barsu kenan me gari ya waya? Ta tsallake ta barsu domin halin mahaifinsu to su ɗin kuma fa?, Idan ta tuna ire iren waɗan nan abubuwan se duk taji gwiwanta yayi sanyi, da ganin laifin kanta tun farko da bata tsaya da kyau tama yaranta zaɓin uba na gari ba. Sedai ya zata yi? a haka allon ƙaddara ta yazo mata babu kuma yacce zata iya sauya ƙaddararta daga mummmuna zuwa kyakkyawa har se ranar da ALLAH ya so... Sau da tari ta kanji ladamar haihuwa tare da Mijin nata, sedai ta kan yi gaggawar tuba. Domin IN SHA ALLAHU ba za ta taɓa danasanin haihuwar ɗaya daga cikin yaran taba, domin tana Son su sune *DUNIYARTA*gaba da baya ALLAH. A kullum kwanan wannan duniyar adda'arta a kansu bata taɓa yanke wa daga bakinta. Domin ubangiji ya albarkaci rayuwar su dukansu ya raya mata su cikin aminci da buwayarsa, ya kare mata su daga sharrin masu sharri, tana Róƙon ALLAH da buwayarsa wanda wani baya kwaɗayinsa. Tana Roƙonsa da ƙarfin mulkinsa da wani ba ya iya rusashi, tana Roƙonsa da al'arshinsa me girma me ɗaukaka. Daya tseratar da yaranta daga sharrin mahaifinsu, tana me Róƙon ALLAH da kar ya jarrabcesu da laifin da ba nasu bane ba su suka aikata ba, sanda ake aikatawarma suna bacci wasu kuwa tun kamin su zo Duniyar. "ALLAH IN SHA ALLAHU bazai jarrabe mu da wannan ba ko dan halin Rayuwar da muke ciki na tsanani nida yarana. Zeji tausayinmu, yay riƙo da Hannayenmu da tsarkin mulkinsa..." ta furta a bayyane idanunta na zubo da wasu ruwan hawaye masu zafi da ciwo, domin a kaf duniyar idan da abinda yafi faɗar mata da gaba to shi ne laifin Mahaifinsu ya faɗa kansu wata rana, ko ba yanzu ba. Lallai ta sake yarda da ake cewa babu halittar dake saurin ruguza dukkan buri mafarkai yadda da aminci na ɗiya mace irin halittar ɗa Namiji,Inda idan ta dace da abokin rayuwa na gari, sai taga tana yiwa maza dukka kallon abu ɗaya wato adalai su, kamar a yanzu yadda ta haɗa duka maza tana musu kuɗin goro da suna

Chapter 7 of 23