Share this page
tafiyar naka, to zaka kai inda baka yi tsammani ba ma, sedai aikin yana da matuƙar wahala, dan haka a gobe zan gabatar da duk wani tsarin da muka gama shiryawa..... " Rungume shi chief ɗin yayi yana me furta. " Zaka iya kuwa Captain?, Wannan aikin yana da matuƙar wahala da sanya kai a haɗari, wanda hakan ze iya zama silar rasa rayuwar ka...... "Zan iya sir harma fiye da hakan indai akan ƙasata ne, raina fansa ne wa ƙasata, zubar hawayen ta tafasa zuciya ta yake, tsananin cikin ta kuma kan narka zuciya ta dan me ba zan kawo mata ɗauki ba ta hanyar sa daukar mata da rayuwa ta ba...." daga haka su ka rabu da juna, Rabuwar da basa da tabbacin zasu sake haɗuwa har ƙarshen abada. Wannan rabuwar itace sanadiyyar faruwar komai, domin kuwa daga nan sabon babin wasar ta fara me cike da sarƙaƙiya.......... ♡ Suna zaune a department nasu su uku ita ne da Janan se Nasma. Janan ce ta kallesu su duka, tare da furta. "Guy's na manta ban baku wani zazzafan news ba...." se kuma ta ɗan dakata tare da tallafar haɓarta tana wani lumshe idanunta tana me sake furta. "Mafarkin Captain nayi...." ta furta wanda ya sanya Nufy zaro Idanu cike da mamaki tace. "Captain? wanne Captain in?." Wata katuwar hararan wasa Janan ɗin ta mata tare da gyara zaman ta, cikin ƙaunar abin da takeson faɗi ta gyara zamanta, tare da ɗan sake lumshe idanunta. "Captain dai, Yaya AA ya yanki, wai sau nawa kika son kullum sena tuna miki da hakan. MR PERFECT MAN dai nawa CAPTAIN AA...." Idanu Nufyn ta sake warowa cike da matsanancin mamaki tace. "Kina nufin Yaya dai Yaya na wai?........" kai Janan in ta jinjina mata tare da cewa "Eh shi dai, ko ban kai ya so ni bane?, ko kuwa bana da abinda zai so nin ne?, Don ni tin kallon farko dana masa zuciyana ta kamu da son sa, domin tin da nake ban taɓa ganin wani mutum irinsa ba, ya haɗu Nufy cute handsome ne bana wasa ba, don ALLAH ki sa ya soni baby.... " tayi maganar tana me rolling idanunta don ita kaɗai kawai tasan irin son da take ma wannan bawan ALLAH....... Ɓangaren Nufyn kuwa mutuwar zaune tayi, tunda Janan ɗin ta soma maganar nata, kafin a wahalce ta haɗiyi wani wahalallen saliva ɗin da taji ya tsaya mata a maƙoshi ta haɗiye, ahankali ta ɗan lumshe idanunta tana ƙoƙarin shanye abinda ke son taso mata akullum a kuma ko da yaushe, indai wani ze yabi yayan nata ko zance so ya shiga.... Jin tayi shiru ne ya sanya Janan ɗin dafa shoulder nata, cike da son jin bayani akan Mr perfect man ɗin nata tace. "Why kikayi shiru haka beb?" Buɗe idanunta tayi jin yanda Janan ɗin ta dafa shoulder nata, tare da sauƙesu akanta, kallon cikin idanun Janan ɗin tayi sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa, don hango wani abu acikin idanun Janan ɗin da tayi, wanda ya sanya taji wani abu me kama da fargaba na neman kamata, ita kuwa Janan ganin Still tayi shiru ne yasa ta kamo hannun Nufyn, ba tare da ta lura da yanayin da take ciki ba tace. "wannan alfarmar kawai nake nema daga gare ki baby, ki taimaka min kisan duk yacce zaki yi ki shanyo min kan Mr perfect ɗina pls naci wannan arziƙin..." nan ma shirun Nufy ta sake yi kamar ruwa ya shanye ta. "Kunga guys ku zo muje muyi sallan la'asar naga lokaci yayi, kuma anata fita no need mu zauna a anan karma a raba sallamar bamu nan." Nasma ta katse musu zaman kuramen da kallo cikin kallon da suke bin juna dashi. bata iya cewa komai ba sai bin bayan Nasma ɗin da tayi suka fita daga cikin inda suke zaunen. Kai tsaye inda aka tanada donyin awala suka nufa, Ita tafarayin alwalan kana Nasman tare da Janan su kayi a tare, Gefen masallaci suka nufa, wajen da aka tanadawa matan hospital ɗin musamman dan yin sallah, atare sukayi sallan bayan sun idar da sallan ne suka koma nufa inda ofishin uban gidansu yake, wanda yake ta famar yankwanasu wajen kwanansu biyar kenan akan sallamar da aka yi, Se yau sukaci tiyya ze basu sallamar. Ƙarfe 6 daidai aka basu sallamar tare sakamakonsu kuma se daga baya. Ita ne ta ɗebesu da kanta kasancewar duk basu zo da nasu motan ba. Janan ta fara sauƙewa kafin Nasma, zuwa lokacin 7 tayi. Ita kaɗai ne a cikin motar don haka ta ɗan kwantar da jikinta ajikin kujeran motar, ahankali tare da ɗan lumshe idanunta tana sakin ajiyar zuciya. Kalaman Janan ɗin na taso mata amma tana famar dannewa, don hana ɓacin ranta bayyanuwa. hakanan taji gaba ɗaya duniyar ta daina yi mata daɗi, tun da ba tasan me yasa take jefa ta cikin masifa da bala'i ba, Me yasa a duk lokacin da wata zata bayyana soyayya ta ga yayan nata take jin tamkar ruguza mata wani abu daga cikin rayuwar ta ake yi ne?, wanda ita kanta batasan ko menene shi ba, starring motar ta soma murzawa, ahankali takejin wani irin sanyi me daɗi na ratsa jikinta, sake lafewa jikin kujeran motar tayi tana sakin numfashi ahankali, idanunta naga titi data buɗe su wanda suka jima alumshe, Haka har ta kai gida. A compound na gidan tayi parking car nata tana Fitowa a natse, ta fara tafiya. Yana tsaye jingine da jikin car nashi da be jima da shigowa ba shima, buɗe idon sa a kanta sosai yayi, a ranshi yana me raya _the girl is beautiful not just beautiful but extremely beautiful, she’s got this flawless shining skin that looks like fresh and creamy milk, that are put together to give her this perfect and flawless skin, idanunta are so white shines which made her look intimidating, she’ thin and tall the girl is almost perfect with nothing left for people to criticize_ don shi dai ita kaɗai ce macen da ya taɓa gani me aji da kyau da zallar cikar zati, tafiya takeyi a natse yana me sake bita da mayun idanunsa. Lokacin da ta shiga babu kowa don haka ta haye samarta wanka tare da sallah tayi, ta faɗa kitchen da zimmar taya Ammey kirki, sedai harta kammala, Sakwara da miyar dage dage tayi ta jar miya, sannu da gida ta mata tana me tambayar ta ba zata ɗan haɗa musu da lemu haka ko ɗan kunu ba?. Hanya ta bata tana ce da ita bismillahi don ita kam ta gama nata, saboda haka ta shige tana buɗe fridge ta ɗebi gyadarta da already ba'a rabasu da ita, lafiyayyen kunun markaɗaɗɗiyar gyada soyayyiya ta dama musu.wacce ya sha ubar madara se ɗan sugar ba da yawa ba gudun kada ta sane gar ɗin gyaɗar nata... Take kitchen ɗin ya sake kacamewa da ƙamshin kunun da tayi. Se after isha'i kana kowa ya hallara a dining ɗin, shima anan ta fito ta same shi dan taje watsa ruwa ne, kowa abincin yake ci a natse duk se taji ta kasa sake wa, dan kamar idanu taji yana yawo a jikinta. Seda yaci sakwaran kana ya tsiyanya kunun, wani kalan lumshe kyawawan idanunsa yayi, don a duniya idan da abinda yafi so to shine kunur gyadar nan daya tabbata ita ne tayi, haka yake sipping abin sa a natse cikin gently nutsuwansa. Babu jimawa da kammala diner ɗin ya tashi, wanda ya saka Nufyn sakin wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, tabbas yana da kwarjini mai tarin yawa, wanda shi yake sawa duk takejin kanta wata iri, bata da wani kwarin guiwa a gaban sa duk haka take ji, ɗan lumshe idanunta tayi tare da haɗiye abincin dake maƙale ama maƙoshinta. tashinsa shi ya sa ta ɗan saki jikinta sosai. Abbu wanda ya kammala cin abincin shima ne, idanunsa ya sauƙa akan wayan AA ɗin, wanda ke aje nan kan saman table ɗin da dukkan alamu ya manta tane, inda sauƙe idon nasa akan wayar kuwa yayi daidai da soma ƙiran wayar da akayi, kallon sa ya kai kan Nufaisah da ke goge bakin ta da tissue Abbu yayi, cikin kulawa yace. "Nufaisah ɗauki wayar yayanki ki miƙa mishi ana ƙira, ya manta yana barinta anan." Jin maganan da Abbun ya faɗa ne yasa lokaci ɗaya ta fara tari ba tare da ta shiryawa hakan ba, da sauri ta ɗauki ruwa tasha, tare da soma mutsustsuka idanunta, kallon da Ammeyn ta ta mata ne yasa asanyaye ta ɗauka wayar nashi dake ta faman ring har zuwa lokacin. Miƙewa tsaye tayi tare da barin dining area'n, koda ta ƙarasa cikin parlournsa da kai tsaye ze sadaka da sashin sa tayi, Hakanan take jin ƙirjinta na bugawa da ƙarfi da kuma faɗuwar gaba. Gaba ɗaya seta tsinta jikinta da fara rawa, ahanakali ta ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar, tare da murɗawa ta tura ƙofar ciki, asanyaye ta ɗan kutsa kai cikin babban parlournsa, takun farko ta jefa ƙafanta akan wani lallausan carpet me taushin gaske, ga kuma wani irin daddaɗan sanyi me tafiya da ƙamshin dake tashi a ɗakin, ɗan lumshe idanunta tayi, tare da maida ƙofar ta rufe, idanunta ta baza wajen ƙarewa parlourn kallo ko zatyi nasarar ganinsa, sedai baya parlourn amma komai na cikin parlourn a tsare yake, dan da dukkan alama mamallakin parlourn baya son yawan tarkace da hayaniya, domin daga yanayin tsarin parlourn nasa zaka fahimci haka, inda aka zuba wasu haɗaɗɗun cushions masu kyaun gaske a tsakiyar parlourn, sai kuma royal blue and ash curtains in da aka saka ajikin kowacce ƙofar windows dake cikin parlourn, kasancewar kujerun nada kalan ash shiyasa curtains ɗinma suka kasance kalan ash ɗin. Parlourn taci gaba da kallo tamkar wani baƙonta. Kafin tayi kundubalar nufar ƙofar tare da turawa, wani zaro idanunta waje tayi, domin sam bata yi tunanin ƙofar abuɗe take ba shiyasa ta tura, a ɗan tsorace ba tare da ta ƙarasa shiga ciki ba, da ƴar siririyar muryarta tayi sallama. Sai dai shiru haka taji babu amsa, ba ko motsin mutum bare tasa ran za'a amsa mata ma, sake kwala wani sallaman tayi, still babu amsa. Jin shiru ne yasa tayi tunanin cewa ko baya cikin ɗakin ne ma, mebi ba yana can yana wani aikin ne a wani lungun na daban, hakan ne ya bata damar sauƙe ajiyar zuciya tare da ƙarasa shigewa cikin ɗakin. ♡ Wannan mayataccen daddaɗan ƙamshin nasa ne daya gama kama ɗakin ne ya daki hancinta, wanda hakan ya sata jan fararen idanunta ta lumshe tare da jan wani dogon numfashi,domin tana wani kalan masifa masifan son ƙamshin yayan nata, ɗan buɗe idanunta tayi ahankali jin kamar ana kallonta, inda ta sauƙe su a kansa. Zaune yake agaban dressing mirror yayin da ya bama ƙofar shigowa ɗakin baya, sanye yake da white trouser yayin da ya cire rigar gata nan a gefensa, yanayin yanda ya juya baya ne yasa gaba ɗaya surar bayansa ta bayyana, inda wasu ƙananan hairs suke kwance lub akan white skin ɗinsa, yayinda fatar tasa ke wani irin shining na kyau, yanayin yanda ya juya baya ya kuma duƙar da kansa ƙasa shiya sanya ba'a iya ganin ko me ne yakeyi, kuma shima ba lallai yasan anshigo ɗakin ba. Idanunta masu kyau ta zubama fatar bayan nasa bata ko ƙiftawa, ba komai ya ɗau hankalin nata ba kuwa face zanen zanen tattoo ɗin dake gefen cikin sa, Se na gefen wuyarsa ƙasar ƙeyarsa wanda dama shi tasan da shi, sedai na gefen cikin ne bata taɓa gani ba, Ahankali ta ɗan lumshe idanunta, tare da buɗesu a lokaci guda, gaba ɗaya ta gama shagala da kallon zanen dake kwance daga gefen cikin nasa, hakanan taji shauƙin taɓa zanen na fusgarta, cikin nutsuwa ta soma takawa zuwa inda yake, wanda har zuwa lokacin bai ɗago kansa ba, bai kuma yi wani kwakkwaran motsi ba, da dukkan alamu dai baisan da wanzuwar nata cikin ɗakin nasa ba. Taku kaɗan ya rage mata ta ƙarasa garesa, ƙiran wayansa da aka kuma yi ya katse ta, wani sabon tsoro ne da faduwar gaba taji ya lulluɓeta dan gaba ɗaya tamanta me ya kawota ma ɗakin nasa, ɗagowa tayi ta kallesa, still har yanzu bai ɗago kansa ba, bai kuma nuna ya san da wanzuwarta ba har zuwa lokacin, murza ɗan yatsun hannunta ta soma yi ahankali dan batasan ta ina zata fara yi masa magana ba. Akaro na barkatai kenan dayay closing very beautyful eyes akan ta,Kafin ahankali ya ɗan juyo da kansa, batare daya ɗago ya kalleta ba, ya miƙa mata hannunsa alaman ta bashi wa yan. Kamar dama jiran hakan take nan take da sauri kuwa ta sakar masa wayar a tafin hannunsa, saidai tasha mamaki kwarai dan batayi tunanin yasan da zuwanta ɗakin ba, bare kuma tsai warta gabansa. Ɗan satan kallon sa ta sake yi, saidai bata iya hango full face nashi ba kamar farko, dan bawai ya juyo gareta bane, amma tana iya ganin rabin fuskarsa, da kuma gefen kumatu'nsa wanda ƙawataccen sajen dake wajen ya kwanta lub gwanin ban sha'awa. Dan har wani kalan blue blue yake fidsawa. Juyawa tayi cikin sauri ta nufi hanyar fita daga ɗakin, Tana fita daga cikin ɗakin ta saki wata ƙatuwar ajiyar zuciya, Bata sama kowa ba zuwa lokacin a parlourn, dan haka kai tsaye ɗakinta ta wuce tana kwanciya cike da wani kalan masifan zazzafar ƙaunar yayan nata, da taji kamar ta faɗa jikin sa ta rungume sa, kai inda hali ma ta masa fyaide, don yanzu a wannan zamanin tsaff ta gama yarda tsaf mace zata ma Namiji fyaiden..... Sake sakin wata sabuwar ajiyar zuciyan tayi akaro na barkatai, ahankali kuma ta sake matse pillown dake hannunta tare da lumshe idanunta tana cusa kanta ciki. "Komai nashi gwanin birge wa so cutie!." ta faɗi a abayyane ba tare da ta sani ba, wannan naked skin ɗin gadon bayan nasa da kuma tambarin zanen tattoo ɗin da ta gani agefen cikin sa ne keta yiwa idanunta gizo. Sannu ahankali ta fara jin wani baƙon tunani na shigar ta yana ratsa cikin kwakwalwarta, wanda asanadinsa ne zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi, saurin sanya hannayenta duka biyu tayi ta toshe kunnuwanta tare da rumtse idanunta. Tana shiga soma ambaton sunayen ALLAH kan ya sassauta mata wannan al'amari, dan sosai zuciyarta ke bugawa da wani irin abun dake mata yawo acikin kai da zuciyarta, idanunta da suke a lumshe ne suka ciko da wata kwalla, kafin ahankali ta soma sakin shashsheƙan kuka mara sauti, tana me roƙon ubangijinta gafarar laifin data masa, don ya yaye mata wannan masifa da bala'in da take cikinsa....... ♡ ♡ ♡ AA kuwa yana amsan wayar picking call nata kawai yayi, tare da kara wayar akan kunnensa, har wanda ke kan wayan ya gama bayanin da zaiyi baice ƙala ba, yana gama jin bayanin da akeyi masa a cikin wayar ya datse ƙirar tare da cilla wayar kan bed, kafin a hankali ya ɗago da kansa tare da lumshe tsumammun idanunsa, numfashi ya ɗan fesar kana ya miƙe tsaye daga zaunen da yake. cikin takunsa na isa da kuma yanayin da ya saba ya nufi haɗaɗɗen gadonsa, hannunsa yakai jikin bango, inda ya kashe hasken wutan ɗakin, bedside lamp ya kunna wanda yake bada blue light, hayewa saman gadon yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, gaba ɗaya jin kansa yake a mugun wani iri... Haka har wani shegen bacci yazo yayi awon gaba dashi, Duk sanyin A/C'n dake tashi acikin ɗakin, amma hakan bai hana murɗaɗɗiyar surar jikinsa fidda gumi ba, ahankali yake ɗan jujjuya kansa, wanda kai da gani kasan baccin da yake bayayi masa daɗi ne, acikin baccin nasa ne kuwa ya samu kansa cikin wata duniya ta daban, wanda ke neman juya masa tunani da kuma lissafi, duk da cewa hakan ba baƙon yanayi bane awajensa amma bayajin zai iya jurewa. Gata nan yauma kamar kullum tana durƙushe ta juya masa baya, gaba ɗaya jikin ta ɗaɗɗaure a wata mahaukaciyar waje. Jikin sa har na wani kalan kerma da tsucmar da a kullum kwanan duniya yake yi ta cikin duniyar mafarkin nasa, ya tunkari matar, sedai taku ɗaya ana biyun kamar koda yaushe wani kalan baƙin guguwan hadari yazo ya baje wurin. "Shin lokacin baiyi bane KAMAALAH?, Lokacin bayyanuwar taka ba tay bane?, har zuwa yaushe zanci gaba da zaman jira. Ba zaka fito ka nuna musu cewar ajiyar ALLAHr nan ya gama girma ba!, Ka sani UMMUL-YOODAH tare da jama'ar garin ka suna nan dakon tsumayin zuwar ka ƙasar ka ta haihuwa take, kazo ka ruguza wancan mulkin ƙarya da zalincin KAMAAAAA...... " Se kuma ya farka daidai nan a wani irin zabure, bakin sa ɗauke da manyan adda'o'i, zaune yake a tsaƙiyar bed ɗin ya dafe kansa da duka hannuwansa biyu, jikin sa na wani irin ɓarin da yake zubar da gumin da yake kwaran ya kamar ruwa. Shin wai minene yake faruwa a cikin duniyar sane?, me yasa yake yawan mafarkai ire - iren waɗan nan, sedai na yau ɗin ya sha ban ban da sauran daya saba yi, dan kuwa a yau wannan matar tayi magana, ta kuma ƙirashi da sunan daya sanya tsigar jikin sa tashi.... Ahankali ya zuro da ƙafafunsa ƙasa daga kan gadon, tare da ɗan cijer red lips nashi saboda yanda jikinsa ke ɗaukar wani mugun zafi... Luff yay a tsakiyar bed ɗin, ƙwaƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ne kawai ke faman aiki a lokaci ɗaya, hakan yasa shi barin duniyar mutane ya koma zuwa wata duniyar ta daban.... 10:10am 🕙 Ahankali ya ke ware idanunsa wanda sukayi jajur dasu, hannu yasa yaɗan dafe kansa dake sarawa kaɗan kaɗan, hakanan gaba ɗaya duk bayajin ƙarfin jikinsa, wanda hakan kuma baya rasa nasaba da barcin dabe samu damar yi ba a daren jiya, Cije jajayen laɓɓansa yayi, cikin ɗan kuzarin daya saura masa ya sauƙo daga kan gadon. Kai tsaye ya nufa hanyar toilet, tun daga bakin toilet in ya soma rage kayan dake jikinsa, saida ya zama naked sannan ya ƙarasa gaban shower, hannunsa yasa ya kunna makunnin shower'n, take ruwa ya soma sauƙa ajikinsa, ahankali yaɗan lumshe idanunsa yana mejin sanyin ruwan na ratsa duk jikinsa, wanda hakanne kuma yasa shi ɗan jin relief. Sama da 30 minute yana tsaye ruwan na dukan jikinsa, ahaka dai yayi wankan kana ya fito daga toilet ɗin, towel ne ɗaure a waist nasa, gaba ɗaya jikinsa ɗauke yake da damshin ruwan da yay wankan, yayinda lafiyayyar suman kansa ta kwanta tayi lub, itama ahankali take ɗan ɗigar da ruwa. Wani mini towel ya ɗauka wanda dashi ya goge kai da kuma jikinsa, lumsassun idanunsa da launinsu ya gushe da ga farare zuwa ɗan jaa ya buɗe a hankali yana furzar da ruwa tare da nannauyar numfashin da yake nemar sake sarƙe shi...... Kai tsaye yana gama shirin nasa ya nufi garden nashi, dake nan gari guda ga wasu irin bishiyu masu masifar kyau da suka ƙawata gurin, an kuma kewaye gurin da kujerun glass da aka yiwa, tafiya yake a natse waya manne a kunnensa, inda ya rigar dake jikin sa ta gama bayyana wannan faffaɗan ƙirjin nasa. kasancewar rigar armless ce a jikin sa, yanayin zubin halittar sa ya nuna shi ɗin maji karfi ne. Wata irin tsaiwa ya yi a wurin, tare da riƙe ƙugunsa da hannu ɗaya yana me furta. "Taurin kan dake a jikina, na rantse ko baban babanka baya da dan haka ka kula....." Yayi maganar dole yana kaiwa zaune kan wata royal blue gothic chair dake garden ɗin. Idanunsa lumshe ya sake furta. "Ni ban yarda da faduwa ba......" daga nan suka shiga maida maganganu da shi da wanda yake yin wayar....... ♡ *KOMAI YA NA DA SANADI * Tabbas haka ne komai na rayuwa akwai sanadinsa.... Kamar yadda faifan videon kisan Kanal a hannun CAPTAIN AA ya fita...... _Hhhhhhhh na san dai se gindayar daku nake tayi ba?, to yanzu ne ma hasalin wasar zata fara_ _Don kuwa bamu ko tsoma ƙafa a cikin duniyar labarin mu na RAMIN KURA ba, domin kuwa akwai kulla kulla rikita rikita da yawa a cikin littafin RAMIN KURA _ *Hope dai normally yana maku dadi dai ko??? 😂 😜... * _Don ina son ya zarce MIKIYA Kwamacala, gwagwarmaya da ma komai da komai.... _ Chart mee or call🤙 08104493215 Hhhhhhhhhh to ai shikenan 😅🥰 A gimtse 🫰 🙃♥️✅ *BY AMMEY LAYLERH ✍️ ✅* ༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻ # 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Book One paid ♡ Page 29&30 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. # HE WILL FIGHT # WAR *Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank* ♡♡♡♡♡♡♡♡ ꨄ *KOMAI YA NA DA SANADI * A ranar a kuma lokacin babu wani baƙon rai mai numfashi a cikin sansanin sojojin da suka runtsa, a daren *CAPTAIN AA* ya sama ƙira daga sama kuma. Kafin wayewar garin ranar kuwa tuni wannan videon ya gama karaɗe duniyar baki ɗaya kan cewa wani jajirtaccen jami'in soja ya sheƙe ogansa a wurin aiki, su Abbu basu san da iri yar wainar da ake toyawa ba se a washe garin ranar da safe, suke samar labaran. Zuwa lokacin kuma tuni AA ɗin ma ya jima da barin gidan, yana can Headquarters na sojoji. Dan haka hankalin Abbu idan yayi dubu to a lokacin a tashe yake, dandanan sega wani shegen zazzaɓi yayi ciki da shi. ♡ *NIGERIAN ARMY HEADQUARTERS ABUJA* Tun daga farkon shiga headquarters ɗin zaka fahimci cewar lallai ba lafiya ba, domin kuwa ta ko ta ina ta ko wanne saƙo da longo kewaye suke da manyan sojoji masu jini a jika. A babban ɗakin taron dake cikin headquarters ɗin kuwa, duk wani army dake da babban matsayi ne kewaye a cikin ƙaton hall ɗin, suna Zazzaune saman kujerun da kowanne ke pacing ɗan uwansa, a matuƙar fusace General ya doka saman table ɗin dake gabansa, cike da ƙonar da zuciyarsa ke masa, da kuma takaicin wannan abu ya ɗago rinannun idanunsa yana zuba su akan Captain AA dake tsaye akan ƙafafunsa babu ko alamar tsoro tattare dashi, ko shakkar komai Sema cikin fushi da yake kallar kowa daga cikin ɗakin taron. _Akan me zaka harbe shi Captain?, Tambayarka nake me yasa ka harbeshi?.... Gen ɗin ya faɗi yana kallar AA dake tsaye akan digadigansa cikin tsana me kyau mara algus. "Harbe shi nayi...." AA ɗin ya faɗi babu alamar tsoron komai a ransa. _"To ka gaya min uban wa ye yace ka harbe shin? Ka gaya min uban waye ya baka umarnin kai harbin ma, kuma akan miye ka harbe shin?" General Toufiq Ali wada ya faɗa a matuƙar tsawace ba tare daya bari ko kyakkyawar numfashi me kyau ya shaƙa ba.

Chapter 16 of 23