Share this page
_"Ba kowa bane"_ yay maganan cikin rashin tsoro da fargaba. Wani ɗan iskan kallo Gen ɗin ya cillo ma AA ɗin cikin yanayin fusatar zuciya yana dakar dest table ɗin dake gaban sa. Tare da furta _"To ne yasa kayi hakan, kodan kana kwaɗayin ka gaje kujera da matsayin sane?....." ya sake watsa AA ɗin tambayar cikin hasalar zuciya. Shi kuwa Captain AA Folding hannuwansa kawai yayi akan ƙirjinsa tare da furta."Guess the old man left a furtune behind, da dukkan alamu tsohon nan ya mutu ya bar kaddarar sa..." ya furta cikin rashin shakkun a gaban Wanda yake ɗin. _"Re show some respect, ka nuna mutum tawa Captain_" chief of army daya miƙe a matuƙar fusace ya faɗi yana wani kalan dakar table ɗin dake gabansa.... Wata shegiyar dariya ya sake sheƙewa da ita tare da furta. "The old man's dead and' gone, tsoho dai ya riga daya sheƙe, He live and died for himself, ya gama shantakewarsa, domin shi ɗin ba ƙaramin yaro ko matashi bane kamar Sameer Tafida....." yayi maganar yana wani saƙalo wuyan sa da hannunsa idanhwansa na yawo a kansu..."Hey idiot...... Have you lost your mind? Ka rasa tunanin kane mahaukaci?..." "Not my mind, ban rasa kwakwalwata ba, my heart zuciya ta, ƙasata rayuwata abokan aiki na, su nake ta rasawa......" Kai shashasha ba maganar shirme bace ta taramu anan wurin ba, kawai ka faɗa mana uban me yasa ka sheƙe Kanal???." ɗaya daga cikin manyan sojojin da tin da aka fara maganar be ko tanka su ne yayi maganar cikin mugun ɓacin rai.... "Matsayi! Kujera!! Duka biyun nake so shine dalilin daya sanya na sheƙe shiiiii...... cikin tsananin ɓacin rai da gajiyawa da rainin yawon da AA ɗin ke kawo musu chief of army ya miƙe tsaye tare damƙar wuyar rigar Captain ɗin, ya sake tambayar sa akan uban me ya kashe Kanal ɗin. Wani kalan zame hannun chief ɗin yayi tare da furta. _"Sabo dani jirgin ƙasa ne duk Wanda ya bi ta hanyata markaɗeshi na ke yi, domin kuwa matsayi da ikon sa nake da buƙata wannan shine..... " wani wanke fuskar Captain ɗin chief yayi da mari, tare da furta."Har abada kuwa ba zaka taɓa kaiwa wannan Matsayin ba ALIYU ABDULLAHI...." Idanunsa jajir ya kalla Chief ɗin tare da furta. "Sir kada ka bari mu fara buga wannan wasar da kasan bazaka iya kaiwa ƙarashen sa ba" "Idan naƙi fa?" Chief ɗin ya tambayeshi cikin takaici da jin haushi" Bayansa ya juya "Mu zuba ni da kai to sir" yay maganan yana juyawa a fusace ga duk sauran manyan soldier ɗin, tare da fatali da table ɗin da suke shaƙe da takardu, Yana zame rigar sa ta kake dake jikin sa yana cilla ma chief ɗin a saman fuska haɗi da hular pcarp nasu na soldiers. da suka masa saura a jiki, dan dama wandon combat ne a jikinsa Ash. Haka yasa kansa yana ficewa a ɗakin taron. "A ahhh Captain ka dawooooo" Nassar Bunza yayi maganar da ƙarfin bala'i, amma ina duk yadda Nassar ɗin yake kiransa da son dakatar da shi, haka ya fice abinsa. Wannan shine mafari silar komai da komai...... Cikin ƙanƙanin lokaci seka pisc na Captain AA ya gama zagaye media, tare da manyan jami'an da aka baza duk wanda ya ganshi ya harbe shi kawai, domin shi ba jami'i bane yanzun. Wannan lamari shine ya sake baje media ta ko ta ina, duk inda ka gilma kuwa maganar sane a keyi. Haka dai al'amurra sukaci gaba da wakana mafi rinjayen kuma akan captain AA ɗin... Ɓangaren Hannah kuwa sosai abubuwa ke tafiyar musu akan duk yacce suka tsara ita da Asp Maleek ɗin ta. Yau gidan Baba Asabe ta wuni tin safe dake bata da aiki yau ɗin. Manyan fararen idonta ta zaro tana ƙarema wanda ke jikin photon kallo. Tabbas wannan pisc ɗin ta san shi, idan har kintacenta gaskiya ya bata to wannan mutumin shi ne wanda Sir Maleek ya taɓa tura mata,yana tambayar ta ko da ace zata haɗu dashi, ganin yacce aka buga masa alamar *WANTED* Ne ya sanya hankalin Hannah tashi, wanda har hakan ya sata shiga media, don ita ba ma'abociyar social media bace, nan take kuwa sega pisc nasa sun gama karaɗe fuskan wayar nata, ɗaya bayan ɗaya haka ta shiga bin Pics ɗin nasa da kallo tare da nazari akan su, wannan beyi kama da me laifin da ake tuhumar saba, domin kuwa kana kallon sa kaga tsayayye kafaffe akan aikinsa. Wayar ta ta sanya tare da dokama Maleek ƙira, bugu ɗaya kuwa ana biyu ya ɗauka, yana me furta "ALLAH ya taimaki AMARYAR GOBE" Murmushi tayi wanda sautin sa ya fita har yana iya jin ta. "Ammmm Yallaɓoi muje ta online ina son damu yi wata magana ne dama!" "Girmanki ne kin wuce haka ƴen matana...." daga haka suka datse ƙirar suna komawa ta online ɗin. _Me yasa ake nemar wannan a matsayin babban Criminal ɗin da ƙasa dama duniyar ke nema ruwa a jallo, tsakankanin kwanaki uku kawai da suka wuce? _ haka ta tura masa tare da pisc na AA da aka dokama tambarin me laifi. _ Sabo da shi hadari ne malafar duniya babyyy..... _ 'Ohhhh god' ta furta a ranta a bayyana kuma tana dafe goshinta tare da ɗan jijjiga kanta. Bata dawo hayyacinta ba kuma sega domin typing nashi ya sake faɗo mata. _Zaki iya tunawa da Makwanni uku da suka wuce rana Monday lokaci yamma wurin haɗu wa kuma. *THICKSAKE FACTORY* ɓangaren *Coffees & Restaurant*...... _ haka ya turo mata. Tin kamin ta gama karantawa ya sake turo mata da. _A koda yaushe A ta sayen wasan kan iya farawa Hannah, kai tsaye yana ganin duk wani motsin ki da duk mutanen da zasu fara bibiyan rayuwanki muddin agogon na tare dake.... Zaki iya tuna ranar?_ ɗan dafe kanta tayi domin tsafff ta gama tuno wa wanda take a wurin ma wani chako mako ya mata magana. Tabbas ta tuna se kuma ta ɗan juya agogo dake ɗaure a tsintsiyar hannunta. Tare da rubuta masa _Na tuna_ cikin abinda be wuce kiftar ido ba sega reply nasa. _To shi ne, shi ne CAPTAIN AA, domin yayi gwagwarmaya aka haife sa, domin farauto masu laifi aka haife sa HANNAH, tin da nake ɓan taɓa ganin mutum kishi da son ƙasar sa ba sama dashi, shi ne madubi na, shi ne abin koyi da alfaharina..... _ Yana gama turo mata ya kashe waya tare da datan sa yana komawa kan wani case na wata yarinya Ƴar shekara 7 da aka ma fyaiɗe, shi ne yake kan aikinsa. *After One week* National Police Headquarters. _Criminal Investigation Department (CID)_ Cikin tsananin sanin darajar ayyuka biyun dake gabansa masu zafi wanda yake dap da cimma gaci ya sake dubar POLICE OF COMMISSIONER tare da furta. "Sir waɗan nan al'amurran ba abinda za'aji ai shiru bane, tun da har yake iya cutar da daruruwan mutane ta hanyar amfani da karfin iko hakan babban zunubi ne yallabai!. Be kamata ace tantirin ɗan ta'adda irerensu ace suci gaba da shaƙar ƴantacciyar iskar duniya ba. Domin kuwa kamata yayi ace zuwa yanzu numfashinsu baya tare da gangar jikkunansu, ko ace suna cen prison suna girbar abinda suka jima shukawa domin su girbi kayansu ba!...." Se kuma ya ɗan fesar da wata iskar ɓacin rai tare da dafa hannuwansa biyu saman desk ɗin dake gaban Cmmsner ɗin tare da furta...." Tabbas zuwa yanzun na gama fahimtar komai sir....... Yay maganar yana ɗan jujjuya wa a cikin office ɗin hannun sa ɗaya riƙe da ƙugunsa."Shi yasa ma aka kutso min da zancen case na yarinyar ba? se bayan na gama tattara duk wasu bayanai da hujjojina kana ace an soƙe case ɗin, tabbas akwai kullalliya a ƙasa, Na gama ganewa....." ya sake faɗi yana shafar sumarsa daga ƙasar ƙeyarsa tare da fesar da wani zazzafan numfashi. Tsaye commissioner ɗin shima ya miƙe tare da fara zagaye maleek ɗin se kuma ya shiga tafa hannayensa yana me furta...." Da kyau, da kyau Acp Maleek lallai kana da kwanya me kyau, shi yasa kake birgeni gaskiyane kana da brain me kyau.... Tin da har ka iya gano shirina cikin sauƙi haka amma duk da haka, hakan ba shi ke tabbatar da kawo ƙarshen wasar ba, domin kuwa yanzu ma aka fara...... " "Dansa batu akan a janye batun case ɗin yarinyar ba, wacce ma bata raye bare ayi shari'an har gaskiya tai halinta ba ba haka kake nufi ba?.... "Da kyau *ACP MALEEK* nima ayau ɗaya dai kam na sara maka" yay maganar yana sarawar gabansa kamar yacce yayi alƙawarin. "Se dai kuma duk inda aka ce yaro, to kuwa yaron ne, Salin Alin cikin ruwan sanyi kada ka sake taso da wata magana dangane da GREEN SNAKE, domin kuwa sake tono maganar daidai yake da rabuwar numfashi da gangar jikinka kenan, ko kuma sena fara tarwatsa rayuwar ka ta hanyar lalata maka ita a gidan kaso..... BOOMMMMM FIRE🔥 🔥 🔥 🔥 🔥 ....... " Yay maganar yana wata shegiyar dariya tare da zagaye Maleek ɗin kafin kuma ya koma mazauninsa ya zauna. "Kai a tinaninka kenan ba, domin ni barazana wa mutuwa ta ba wani baƙon abu bane a wurina sir!, Don haka tunda har na riga na fara aikin nan, nake ga babu wata barazanar data isa dakatar dani ko sa ni na janye batuna akan wannan case ɗin sena kai ƙarshensa, se ko in mutuwa nayi, bi ma'ana kuka sanya aka raba gangar jikina da numfashina!" se kuma ya ɗan dakata tare da fesar numfashi me zafi. "Se dai kashe ni a cikin tafiyar ba shike nufin kawo ƙarshen case ɗin ba, da kuma azzaluman mutane da gurɓatattun jami'ai irinku ba sir, na gaba da kuma ya gama dasu kuma ya zauna lafiya, domin shi an haife shi ne domin kawo ƙarshen zalumci da azzalumai.... wannan Maleek ɗin dake tsaye gabanka har abada shi kaifi ɗayane, kamar yadda zafin kansa be taɓa barin ya aikata ba daidai ba. Kashe Maleek a cikin tafiyar kuma na nufin kun gayyatoma kanku da kanku goran gayyatar tonuwar asirinku da mutuwar kune wa BOSS!!!" "Tabbas se a yanzun nima na gama fuskantar komai Acp Maleek, kace ashe linkin ba linkin ɗin maƙudan kudaɗen da muke amsa daga hannun mutane maban banta, kaima shi kake amsa daga wasu wuraren, tin da ashe ma gashi har uban kake da" commissioner ya faɗi yana wani shafar munafukin ƙasimbarsa da katon cikinsa dake rawa shima, se kuma ya kece da wata kalan dariya yana furta "Ashe dai masu fatar akuyan yawa garemu, to me zai hana kawai ka faɗo cikinmu kai ma sunanka yay shura da ƙauri a baki ɗaya jahar kano harma da kewayenta Acp Maleek " Idanunsa ya ɗan rumtse da ƙarfin bala'i tare da bugar teburin gaban commissioner ɗin cikin ƙarajin murya ya furta. "Har abada In banyi adalci wa ƙasata da kuma aikina a matsayina na jami'a ba, zuciyata bazata taɓa samun nutsuwa ba, a yayin dana buɗi ido na kalla ana aikata wata ɓarna a cikin ƙasata, to kasa cin abinci nake, haka kuma kasa barci nake yi, don haka ni banyi kama da jami'i ɗan rufa ido ba ni ɗin *KAIFI ƊAYA NE* wanda baya lankwasuwa ta daɗi se anci kashi. Domin taurin kan dake jikina, na rantse ko baban babanka baya da, dan haka ka kula sir, ohhh ba buƙata ma se in har ka taɓa ni a daidai lokacin ne shi kuma zai bayyana a gareka.... domin bada kariya daga gurɓatattun ƙasa irin ku, da suke lalata aikin goben matasansu ta hanyar musu barazana da mutuwar su akan aikinsu!!!" "Waye shi?" commissioner ya tambaya. "*MALAFAR DUNIYA, JEJI WANDA BA'A YI MASA KYAURE, DOMIN SHI KAMAR HADARI HAKA YAKE, GABANSA YAKE SAWA DUK INDA YASO, baya da tsoro bare kace shima zaka bashi tsoron, domin shi kansa tsoron AA firgitashi yake"* "stop here" Ɗaya daga cikin mahaintan da suke bashi goyon baya ya faɗi. Tare da furta. "zamu gani...." Wallahi oho shi dai kansa kawai yasa yana barin ɗakin binciken. _Daga wannan sa'in sar komai ya faru, rubutacciyar ƙaddarar da bata ƙarya ta faɗa kan Acp maleek, Se wayar gari yay ya ganshi a cikin destination prisoners, sedai akwai sanadi!!! Ehhhhh tabbas akwai sanadin hakan mujeeeee_ Kafin hakan. A daren ranar ya ziyarci Hannah. Cike da tsoro take kallon sa cikin karye war zuciya. "tsoro na ke Sir.!, ina jin tsoron rasa ka sosai Yallaɓoi, kawai ka janye komai da suke buƙata ɗin don ALLAH bana son na rasa ka....." Sake dubanta da kyau sosai yayi tare faɗin. "Mrs Maleek ina son ki sanya wannan yaƙinin a ranki cewar har gaban abada matsoraci baya taɓa zama gwani, don haka zan tsaya akan gaskiya da gaskiya ta, su yi tayi har zuwa lokacin da gaskiyar zata rayu" Kuka ta fashe dashi a loƙacin tana me sake furta. "Nidai kawai ka janye ka kyale musu komai ɗin da suke bukata haka nan Dear, ka hakura ka zo muyi auren mu, laifi babba fa suka ɗora maka Ya Maleek, Waifa laifin Raping yarinyar suka mayar kanka. Mai yasa a koda yaushe manyan gari sune suke zama maubuɗin aikata ko wanne irin tarin zunubai, a ban ƙasa zunubai kuma mafi MUNI, shin ta yaya za'a samu ƙwanciyar hankali a ƙasa?,Mai kuɗi ya wulaƙanta talaka,masu mulki suma kuma su wulaƙanta talakawan dai,shugabanninmu kuma suna tauye haƙƙunan matasanmu, wala jami'ai ko ma'aitansu na ƙasa dasu, wasu mazajen kuma su tauye haƙƙunan matayensu dake kansu, malamai suci zarafin ɗalibansu,ƴan siyasa su lalata yaran mutane ta hanyar basu manyan drug wa fyaiɗe ga ƴan mataye mu, harma da ƙananun yara,ya rabbi wannan wacce kalan lukutan masiface,wannan girmamman abun yafi tunanin dukkan mai tunani, shin wai sai yaushe za'a samu sauyi a ƙasar nan?, taya za ayi ƙasa ta dai²ta a samu nutsuwa,ya rabbil izzatu ka kawo mana mafita, Na ɓata lokacina domin yin aiki tuƙuru da rai da rayuwa ta akan aikina, sedai ashe ba haka hasalin tafiyar yake ba, ashe cikin ta tattare take da tarin wasu gima giman tarin ƙalubalai masu tarin yawa ina dana sani, ina dana sanin sanin fara wannan mayaudarin aikin nan nawa, akan aikin nan babu kalan abubuwan da ban fuskantaba kama tin daga kan iyaye ƴan uwa ƙawayena, sedai tin banyi nisa a cikin tafiyar ba na raina fata. Don ALLAH ka janye wannan case ɗin Ya Maleek, mutanen ma da kake yi sabo dasu ganan yanzu sune suke aikin aibantaka a tasashen yaɗa labaransu na ƙarya, shin Ya Maleek se yaushe zaka gane cewar wannan rayuwar da duniyar ba irin ta da bace!, Se yaushe zaka gane cewan Ɗan Adam ba'a taɓa iya masa, me yasa ba zaka haƙura da har aikin naka ba iyeeee?........ Tay maganar tana kai hannun ta tana dukan tsaƙiyar ƙirjinsa, hannuwanta duka biyun ya kama yana ɗorawa a saman fuskarshi, tare da sumbatarsu. riƙe hannun tai ta maƙalƙaleshi tana kuka sosae "Don Allah karka min haka ya Maleek tsoron rasaka nake yi" rungumota kawai a jikinsa yayi yana lallashinta tare da furta. "Ina son ki sanya a ranki cewar an haifeni ne badon naji tsoron mutuwa ba HANNAH!. An haifenine domin kawo ƙarshen baragurbin cikin al'umma, ki sani kowanne zaki mafaraucine a dawa yayinda aka shigo gonarsa, ki ɗauka kamar haka ne, gona ta suka shiga!, iyakar daba tasu ba suka tsallaka, ki sani wannan ɗin shi ne mafarin wasar. inason ko wanne irin tsoron dake cikin ranki ki kawar dashi domin *ABDULMALEEK MUSTAPHA WAZEER * ba matsoraci bane, samm ban ma haɗa hanya da tsoro ba bare nasan ya kalansa ko kamanninsa suke, har gaban abada inason ki kasance jarumar mace ko bayan babu raina ki zama jajirtacciya tsaye akan aikinta kiyi alfahari da kakin aikinta na ƳAR SANDA!!!" Yana faɗim hakan ya sake rungumota jikinsa da ƙarfi. ijiyar zuciya dukkaninsu suka sauƙe zuciyoyinsu na bugawa, A hankali kuma ya zare ta daga jikinsa, tare da kamo hannunta yana ajje mata car key na motar shi, peck ya mata a goshi yana cewa zeyi ke warta, daga haka ya fara janyewa domin jiniyar ƴan sandan data soma karaɗe ila irin anguwar, yana dab da fita ta sake faɗawa jikin sa, itama tana cewa zata yi kewarsa, za kuma tayi ta dokan jira yin dawowarsa koda hakan na nufin zata MUTU BABU AURE. Hannuwansa na rawa ya sake rungume ta ƙam, yana ce da ita wannan ba alƙawari bane kada tay masa haka, Kanta ta ɗago dake malale da ruwan hawaye, tana cilla mishi wani kallo me kama da harara, Se kawai ta haɗe bakin ta da nashi wuri guda, tana me furta. "Wannan ɗin tabbaci nake baka, babu wanda ya isa keta gonar daba tashi ba, zaka dawo!, zamu rayu!!, zamu rayu damu da yaran da zan ta haifa maka ABDULMALEEK MUSTAPHA WAZEER, ina jin hakan a duk wata magudanar jinin dake gudana a jikina....." da sauri ya janyeta a jikinsa ya na fita a motan, sabo da wani kalan kukan da yaji ya taho masa. Numfashi me ƙarfi ya saki loƙacin daya fice motan, daidai da ana sama hannuwarsa onka a shige dashi cikin motar. "I LOVE YOU MIJINAAAAAA......." Haka yaji sauƙar muryanta da shine abu na ƙarshe da kunnuwansa suka gama saurara. Daga nan komai ya faraaaa........ *To ai shi kenan semu gimtse haka nan ko?, yau duk Page ɗin yazo min a wani kalan bahagon yanayi wllh, I'm so sorry 🙏 my edentity people sorry 🙏 for ɓata muku rayukan da nayi....... * _Wayyo soyayya_ _Shin wai ma ya kuke tunanin wasar zata kaya?, wai dan ALLAH ma kuwa Kuna jiyo wani ƙamshi ƙamshin AA ɗin mu ne anan kusa? _ *Ku na tunanin cewar Captain AA a yanzu daya koma babban Criminal ze iya ziyartar Maleek ɗin mu kuwa?, kuje duk na baku assignment..... * _Wasar fa me zafi ce, kamar yadda littafin yake me zafi kuma na musamman.... _ 08104493215 *BY AMMEY LAYLERH ✍️ * ༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻ # 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Book One paid ♡ Page 31&32 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. # HE WILL FIGHT # WAR *Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number nawa. 3206656358, Maryam Nasiru first bank* ♡♡♡♡♡♡♡♡ ꨄ Daga nan bata sake ji daga gareshi ba ita ma, tayi duk iyaka shige da ficenta a matsayinta na yar sanda amma abin yaci tura. Ta inda ma zaka san cewar abin bana Allah bana kawai prison aka wuce da Maleek, duk kuwa wanda ya je da niyar ziyartar shi ba'a taɓa barin sa ya gan shi, iyayen sa kuwa da kuma babban yayansa da yake costom shima duk sunƙi bara su ganshi, sunce laifin da ake tuhumarsa dashi ba ƙara mi ba ne, Se a wani dare babban yayan nasa me suna Yusuf ya sama ganawa da ƙanin nasa, sun yi magana me tsayi kafin yayan ya fito daga inda yake yana matsar hawaye. Hannah kuwa tin da taga abin bana wasa bane, ta dena fita ko can da nan, Se zuwan da yaya Yusuf ɗin yayi kana ya samu da kyar ya shanyo kan ta, inda suka fara wani aiki tare da ƙarƙashin ƙasa ba tare da kowa ya sani ba. Kawai se gani a kai ta dawo bakin aiki, kowa bece da ita komai ba dan haka itama se bata ce da kowan komai ba, Commissioner kuwa dake dama abinda ya kawo shi Kanon kenan, yana kammalawa ya koma Kaduna. Cikin sirri ta ziyarci iyayen yarinyar nan ta ɓatta kama harta sama ganawa da su, inda take tambayar ko miye dalilinsu na ɗorawa mutumin da ya yarda daya sadaukar da tashi rayuwar sabo da tasu wannan mummunar ƙazafin?. Nan take uwar yarinyar nan ta shiga kuka tana warwarema Hannah ɗin komai, kan cewar baraza aka musu da rayuwar su muddin basu fito sun bayyana cewar Maleek ɗin shine yama Ƴar nasu fyaɗen ba harta rasa rayuwar su. Nan take ta musu sallama bayan ta naɗi komai a cikin wayar ta ba tare da iyayen sun sani ba, haka suka ci gaba da shige da fice har zuwa kan case na green snake ɗin da shine silar faruwar komai. A gefe guda kuwa sabuwa dal ɗin waya suke amfani da ita, ita da yaya Yusuf tare da sabbin sim card suka buɗe sha fuka ɗaya da sunar white snake, ɗaya kuma da sunan blockbuster suna ɗora wasu miyagun ayyukan da cikin sauƙi suka gama ɗana tarkonsu, ai kuwa ya ɗanu ɗin. Dan haka suka fara buga wani shegen wasa. Iyayen Hannah kuwa ganin ta gama zubar da komi ne ya sanya hankulan su kwanciya, don dama Malam ayoub harda taimakon Rubutu ya haɗa mata dashi........ ♡ AA. Duk wata kafar sada zumunta har zuwa lokacin magana take a kansa, kan tawayen da yayi daga jami'a zuwa tantirin, dan haka ma aka ne masa aka rasa, ya kwashe iyayen sa ya gudu ma ƙasar da ba'a san inda yake ba. Dan haka jami'ai suka tsare gidansu dake nan cikin Abujan, sedai duk wasu bincike sunyi sun gama amma sun rasa gane kan komai. Sedai abinda basu sani ba shi ne cewar iyayen AA ɗin na nan a cikin garin Abuja. Cikin wani kalan mugun tsaron sa, duk da cewar shi baya ƙasar, amma komai dake faruwa a NIGERIA ɗin tamkar a kan idon sa ne ake aikata komai ɗin. Domin ta ko ta ina idonsa yana nan kewaye da duk wasu muhimman abubuwan da suka shafi rayuwar sa, ciki kuwa harda Lamarin Maleek.......... *GOA* Cikin sanyin safiyar yake ɗan running kaɗan kaɗan a cikin kewayen anguwar ta *DARK ROOM* gefensa kuma wani kare ne irin me cikin kurar nan, da gani ba ƙaramin hatsabibin kare aka yi a wurin ba, *CURSED PRINCE* Kenan. Kare ne na musamman da yake ji da shi, tin farkon zuwansa ƙasar shi ne ya zama tamkar babban amininsa, wanda yaje ya sayo shi a cikin zakuna, cikin ƙanƙanin lokaci kuma ya saba dashi, tafiya suke suna ɗan running ɗin tare. Wata ɓakar *AUDI Q3* tasha gabansu, wanda Cursed prince yay tsalle yana shan gaban uban gidan nasa, ya tare gaban car ɗin. Wani fari tasss ɗin bature ne ya diro daga cikin motar, riga ce a jikinsa mara hannu, Se tree quieter ɗin wando, gaba ɗaya tin daga kan baturen nan zane yake da tattoo har zuwa Saman jikinsa, "Wow! Wow!! Wow!!!" yay maganar domin karen ba ƙaramin birge shi yayi ba, da tsallen da yayi yana tare uban gidan nasa. Wai ya kai hannu da niyar taɓa karen, ai kuwa da yayi wani tsalle yaje se daki ƙirjin mutumin AA yay hanzarin dakatar dashi, ta hanyar ɗaga masa hannu. Wani tafin wannan baturen

Chapter 17 of 23