Share this page
ne kana masa wani aikin ta ƙarƙashin ƙasa, in banda haka ta ya kake tununin cewa AA ɗin bashi da laifi?, kada fa ka manta cewar ƙiri ƙiri aka kama shi da kisan Kanal Musa Bappa Babayo!!!...." Juyowa shima Nassar ɗin yayi yana sake fuskantar MG fawaz ɗin, kafin cikin yaƙi ni yace. "Dama can kai haka kake MG Fawaz, Idan baka son mutum zai iya siyar da borkono kace ba zafi, haka zalika kuma zai iya wucewa ta cikin ruwa kuce ya tada ƙura koba haka ba?, nd ina son ka tuna cewar kowanne mutum kan gwada zafin wuta ne sau ɗaya a cikin rayuwar sa, amma shi wannan sojan shi da kansa yake ta famar fafutukar shiga wutar, taya har kuke tunanin mutum mai tsananin gaskiya da kuma sadaukar da rayuwarsa domin ƙasar da kuma aiki da zuciya kamar CAPTAIN ALIYU ABDULLAHI zai iya zama ɗan Ta'adda, haka nan kuma ba tare da an tsaya anji dalilinsa ba, ni nasan dole akwai dalilinsa da yin hakan, da kuma manufar sa, amma ba ɗan ta'adda bane kamar yadda kuke ƙiransa da shi, dole Akwai dalili ko nace dalilan da suka sanya shi zare kansa daga cikin mu......" yay maganar yana furta a gafarce shi tare da barin room ɗin Jamaal na mara masa baya. Aka bar tarin mazan famar riƙe da kawuna, wasu kuma riƙe da zuciyoyin su..... *MAMAN NUWAIRAH* "Ummih tin da nake ko a karatun littatafan hausa novels, ban taɓa jin labarin da ya sanyani zubar hawaye ba kamar nawa ba, domin kuwa a nawa labarin cike yake da tarin sarƙaƙiya masu cike da wasu manya-manyan tasgaro na rayuwa, ehhh lallai dole ni Nafisa naji cewar wasu lokutan har kamar da gayya ƙaddara ke kwankwasa min ƙofa Ummih Naaaaaa, bayan ga wasu can suna ta dariya da shagulgula, wasu ma sai ka rantse ba su taɓa ɗanɗanar ƙuncin rayuwa ba, ba kuma su san da ire iren waɗan nan bakamantan rayuwar irin tamu ba, bare susan ya zafi da raɗaɗin dake danfare cikin ta yake ba, To amma kamar yadda nasha jin manya na yawan cewa dama amintattu yardaddu masu imani sune suka fi fuskantar ƙuncin rayuwa, masu tafe da tarin ƙaddarori wanda suke kewaye da manyan guma guman ƙalubale marasa yanke wa, A cikin wannan duniyar mutanen cikin ta sun nuna min cewar, azzaluman cikinta sunfi masu adalcin cikinta yawa, shin a ina ne zan sama wata gwanar MARUBUCIYA ƳAR BAIWAR DATA SHAHARA A DUNIYAR RUBUTUN TA IN BATA LABARINA?, Wanda na san ze sanya sanya zukata su girgiza, kamar yanda ze sanya wasu zubar hawayen da babu matararsu sede Ikon ALLAH!, A yau naji tabbas zan iya bata tahiri da labarin rayuwa ta kaf tin daga yarinta har zuwa aurena da Auwal, da kuma kutsowar Jiddah cikin rayuwar auren mu sune mata kan farko na jarrabawar rayuwa ta Ni NAFISATU, dawowar Husna ƙanwar Jiddah gidan shine FARKO da kuma ƘARSHEN LABARINA, Yau gani a Matsayin sakakkiya, wacce AUWAL ya saka akan Husna ƙan Jiddah matarsa, ya sake ni akan yadda na gano kowacce iriyar alaƙa ke tsakanin sa da ƙanwar Matar sa Jiddah, ya sake ni ya zaɓeta ita da Yayarta da nake da tabbacin duk lokacin da KWAN ze FASHE, Itama za ayi ta ta ƙare ne, duk da kasancewar ita ne wacce ta fara bama Husna LASISIN fara shiga sabgar mijin ta. Ummih Naaaaaa ina me baki tabbacin se sunyi nadama su duka, zasu yi nadama, suy ta yin nadamar da babu iyaka, AUWAL se kafi kowa yin nadama, domin nadamar ka ta farko da zaka fara itace ta rabuwa dani, ita kuwa Jiddah nadamar ta ta farko da zata fara itace........ Se kuma ta dakata sakamon kukan daya kufce mata irin me kamar ze fasa ƙirjin nan ya fito. Mahaifiyar ta da take kwance akan ƙafafunta ne ta furta. "NAFISATU komai da kike fuskanta a cikin wannan rayuwar lokaci ne kawai, domin farin ciki ba ya taɓa zama har abada, haka ma baƙin ciki baya taɓa dawwama. Dan a lokacin da rayuwa ta yi miki kyau, ta yi miki daɗi, abu na farko da zaki fara yi, shine ki gode wa ALLAH sosai, ki kuma more kowanne lokacin, ki cika zuciyarki da farin ciki da wadata, Domin wata rana waɗannan lokutan za su zama abin tunawa ne kawai a gare ki, haka za Idan kuma abubuwa suka rikice, rayuwa ta yi zafi ko ta cika da ƙalubale, ta juya baya bata ko waywayarki, abubuwa suka yi nauyi, hawaye suka zama abokanki, ki tuna cewa wannan ma na lokaci ne kawai, kuma zai wuce kamar yadda sauran lokuta suka wuce to shima haka wannan ɗin zai wuce. Kamar yadda wahala take da ƙarshe, to haka shima kowanne irin ciwo yake da iyaka ba madawwami bane. Ki dage da hakuri! Saki da ciwo amma goben Ƴaƴanki nake son ki duba Nafisa, ki ci gaba da tafiya wata rana se labari, ki riƙa fatan alheri. Domin ranar farin ciki na nan zuwa, tabbas zata zo, za ta zama fiye da yadda kike zato, kuma za ta sa ki manta da dukkan hawayen da kika jima zubarwa..... Kana ison ki sani cewar, Zuciya bata taɓa samun nutsuwa har se bawa ya lazumci wannan kalmar ta. _Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakeel_ Domin kuwa wannan kalma ba kawai magana ba ce, tana da asali ne ɗauke a cikin Alkur'ani. A cikin Suratul Āl-Imrān (3:173) Allah ya ce: وَالَّذِينَ قَالَ لَهُمْ النَّاسُ إِنَّ النَّاسَ قَدْ جَمَعُوا لَكُمْ فَاخْشَوْهُمْ فَزَادَهُمْ إِيمَانًا وَقَالُوا حَسَبْنَا اللَّهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ Haka nan Annabi Ibrahim (A.S) lokacin da aka jefa shi cikin wuta saboda bai bauta wa gumaka ba, shi ma da ya ambaci _Hasbiyallahu Wa Ni'imal Wakeel_ Sai Allah ya ce, Ya wuta, ki zama sanyi da aminci a gare shi. Wannan shi ne ikon tawakkali ga ALLAH... Annabi Muhammad (S.A.W) shi ma ya koyar da mu amfani da wannan kalma. A hadisi ya ce, _Duk wanda ya ce, _Hasbiyallahu La ilaha illa Huwa 'alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul 'Arshil 'Azim_ sau bakwai safe da maraice, to kuwa lallai Allah zai wadatar masa daga duk abin da yake da bukata na duniya da lahira... Don haka nake son idan kika ji damuwa, tsoro ko rashin mafita, ki tuna wannan kalmar. Kiyi ta maimaita ta a cikin zuciyarki, da zuciya ɗaya, domin duk wanda ya dogara da ALLAH, ya isar masa daga duk wata buƙata tashi, Domin duk wanda ya dogara ga ALLAH!, ALLAH ba ya taɓa barin sa Nafisa.... " Ɗago kanta tayi a karo na farko tana kallar ummin nata, tare da furta,"Ummih to ina zan sama wata MARUBUCIYAR da zan bata labarin rayuwa ta ta RUBUTA MIN SHI, Ta yanda ire iren mata waɗan da idon su suka jima rufe wa kamar JIDDAH???...." Kafaɗunta Mahaifiyar nata ta riƙo tare da ɗan jijjigata tana me furta. "Idan kin bata labarin taya zata rubuta shi NAFISATU, domin kuwa ai labarin be ƙare ba, domin kuwa ciki babu girban abinda aka shuka ɗin, kinga kuwa a kwai buƙatar dakatawa domin samun cikakken labarin, ta yadda ze bata ma'ana me kyau ta hanyar sakamon abinda aka shuka...... Kinga kuwa Ken a babu buƙatar gaggawa a cikin LABARIN NAKI!!!..... Kanta take gyaɗawa tana fahimta tare da na zartar kalaman Mahaifiyar nata, tabbas tana da gaskiya, tana da gaskiya anan, dole akwai buƙatar jinkirtawar, sedai wacce take son bama labarin ne bata son ta kufce mata, dan haka ta ɗan sake dubar Ummin nata tana me furta. "Ummih bana son in rasa dama tace nima, wajen bama wannan baiwar ALLAH'r MARUBUCIYAR nan labarin nawa..." "WACECE?" Ummin kai tsaye ta cillamata mata da tambayar. "AMMEY LAYLERH ce UMMIH..." "to fa wacece ita kuma haka?" Ɗan sobbing kanta tayi a jikin mahaifiyar nata tana me furta. "Wata ƴar baiwa aka samu a cikin DUNIYAR MARUBUTA, Nima na fara sanin tane ata sanadiyyar wani littafi nata me suna *DUNIYARMU* _ME CIKE DA TARIN ƘALUBALE_ da ta taɓa rubuta wa, wanda naji yayi kamanceceniya da nawa labarin sak, don haka nake son bata nawa labarin koda kuwa ba zai sama tushe nashi na kansa ba ta rubuta shi a cikin wani sabon Novel nata da naga ta fitar wanda zata rubuta a wannan ƙarshen shekarar, Me suna *RAMIN KURA* Ummih tana da wata irin baiwa da fikira na na daban, tana da wani irin edentity da qualities wajen rubuta labarai makamantan nawan nan, izini da kuma amincewar ki kawai nake da buƙata Ummih Naaaaaa....." tayi maganar da sake fuskantar mahaifiyar nata, ta buɗe baki da niyar bata amsa kenan Mijinta Mahaifi ga NAFISAN ya doka sallama, wacce shine ya katse ummin a bama Nafisar amsar da tay niyar. Fita tayi tsakar gidan domin tasan cewar ya shigo ne cin abincin sa, tin da dama kamar hakan yake dawowa, sedai maganar daya faɗa mata ce ta kusan ɗiba ta kayar da ita. "Ka kuwa san abinda kake faɗi Babansu Waleedah? Magana fa kamar naji kana yi wai Mijin Nafisa ya dawo da ita, bi ma'ana ya meda sakin daya mata kwana shida yau cif da cif?" Ƙasa da muryarsa yayi yana me furta. "Haba AISHA ban fa sanki da wannan halin ba na riƙo, Wllh ² nima kunyar waɗan da suka zo min da maganar ne ya sani amincewa, domin kuwa AUWAL be kyautata rayuwar Nafisa ba, ni kaina idan na zauna ni kaɗai na nakanyi mamakin wai miye harya shiga kan AUWAL ɗin ne daya rabu da Nafisar, ya kuma sanya ta cikin irin wannan uku ba da tarin damuyoyi irin haka, Ina tarin Soyayyar da yake mata a da ta tafi ne wai?.... " wani zubar daya ketoma Ummin ne ta sanya bayan hannun ta tana gogewa, tare da furta,"Abu na ƙarshe da yake bani mamakin kenan nima Baban su Waleedah, ka tuna yadda muka sha fama dashi kansa AUWAL ɗin kan Nafisa ta amince da auren sa, amma dubi fa daga ƙarshe da irin mummunar sakayyar daya saka mata, Tabbas ƙarin Aure ba laifi bane ga kowanne namiji, tin da Annabinmu Annabin Rahama shi ne ya mana nuni da hakan, cewar ko wanne Namiji yana da damar aurar mataye ɗaɗɗai har guda huɗu cif, sedai ya haramta hakan ga duk wani namijin da ya san ba zai iya adalci wa tsakanin matayen nasa ba,kuma abinda muke fama dashi kenan a wannan zamanin, Kaga Namiji ya ƙara aure amma babu adalci a tsakanin matayen nasa, wasu shiga suke su fita, wasu kuwa dama can haka halinsu yake, Kaga an auro amarya amma buƙatarta na farko shi ne ta ya data shiga gidan wanda ya auro ta iyo waje da uwar ƴaƴansa, wacce bata san irin gumurzun da taci ba wajen gina shi wannan mijin nata, wasu kuwa iyayen gidan nan zasu ce amarya bata isa ta shigo musu gidan auren suba, ta hanyar biye biyen Malaman banza da bokaye, Se kaga ganan anyi auren amma babu adalci a tsakani, domin kuwa an riga da an raba tsakanin, ni dai da kayi shawari dani, da wllh Nafisa ta gama Aure kuma kenan da Auwal, ko da ace kuma shi ne ƙarshen namiji a duniyar nan, sai dai me afkuwar ta gama afkuwa, tin da har ya riga da ya maida auren sa da nafisan...... Babu abinda zance se mata fatan alkhairi, da bin ta da addaana a duk inda take, ubangiji ya jiɓanci lamuranta, ya shige mata gaba, ya zama gatanta a wannan komawar da zata yi, ubangiji ya ɗora ta akan nasara tare da maƙiyanta..... Kukan Nafisa ɗin ne ya dawo dasu daga hayyacinsu, domin kuwa tsaff take jin duk tattaunawar nasu, cikin wani irin kuka ta zube gaban iyayen nata, tana me furta. "Baffa! Ummih don ALLAH ku min rai! Ku min afwa ku sashi janye wannan auren nasa daya mayar dani a karo na biyu, domin kuwa wlh zanci gaba da cutu wa ne kawai da kuma zaman ƙunci kamar baya... *UMMULYOODAH* Cikin wani irin mugun mawuyacin hali yake ɗan jujjuya kan sa , wanda da dukkan alamu wani mummunar mafarki ne yake yi, tin daga kan yadda wata uban zufar dake keto masa, a cikin mafarkin nasa kuwa sosai yake gudu a cikin tsakiyar fadar, yana ihun nemar ɗauki, shi kuma wannan mutumin da gaba ɗaya jikin sa ke lulluɓe yana sake binsa. Haka har seda ya dangana da bakin wata ƙofa, cikin gigicewar yanayi ya sanya hannayensa biyu da nufin fara dukar ƙofar, wani kalan waro idanunsa yayi sakamakon tozali da wannan baƙar ƙofar da yayi, wacce shi ne da kansa ya sanya aka garƙame wata gawurtacciyar mahaukaciya a cikin ta. Sake waywaya bayan sa yayi daidai wannan Bad Man ɗin na shirin kawowa inda yake ɗin. Cikin wani irin mugun tashin hankali ya dage iyaka ƙarfin sa ya fara dukar wannan ƙofar, yana cewa "ADEENERH ki mini rai ki ceceni ki ceci rayuwa ta, ki taimake ni ki buɗe man wannan ƙofar!, na sani kina jina kina kuma saurarata, dan ALLAH. Don ALLAH ADEENERH....." Daidai nan wannan me ɓoyayyar fuska da jikin ya iso garesa kuma yana me furta. "Taya kake tunanin Mahaukaciyar data shekara talatin da biyu, ba'a cikin hayyacinta ba zata iya taimakarka daga gare ni SARKI AFUUD?..... Yay maganar ne kuma yana ciro wani ƙaho daga bayan hannunsa, ya cira ze luma masa kenan se kuma ya dakata. Tare da sakin wata sheɗaniyar dariya, ya soma magana cikin amsa kuwwa. "Ba yanzu ba!, Ba tin daga yanzun zaka fara girbar abinda ka jima shukawa ba PA'PAAH!, dole kana buƙata ƙarin lokaci kafin hakan......" yayi maganar yana cilli da wannan ƙahon dake hannunsa, yana soma ja da baya da baya, yana kauce wa a wurin sega *PRINCE SHAMEER ASHFUUD* tsaye daga bayan wannan Bad Man ɗin, yana sakar ma da Mahaifin nasa wani irin shegen murmushi, tare da masa wata alama da yatsunsa biyu shima ya fara ja da baya da bayar yana tafiya, kamar daga sama kuma yaji ya furta..... "Ita ƙarya fure take ba iya fidda ɗa take ba, lokacin wasan ka ya kusa ƙare wa, domin ɗan zakin ya gama girma, kayi mamaki ba?,to lokacin be ƙara so ba, Se lokacin da My identity twin nawa ya gama bayyana, wato *KAMAALA ASHFUUD RAMIN DAWOOD kenan, Kaga dai kenan duk inda aka je aka zo *RAMIN KURA* _SE ƳAƳANTA_ kenan........... Firgigit kuwa daidai nan ya farka daga wannan mummunar mafarkin da yayi, wanda ke neman wargaza brain nashi. Wata shegiyar ajiyar zuciya yake sauƙewa, ga wannan gumin naci gaba da tsatstsafo masa, dan haka ya shiga sauƙe numfashi akai-akai, yana me jingina da jikin gadonsa, tare da kai kallonsa kan matarsa mafi soyuwa a cikin matansa, uwar gidan sa wato fulani Hudayya da ta jima da daɗewa gudaliya a gare sa. Dan haka ya miƙe jikin sa na mazari ya faɗa wani special room, yana shiga ya fara zare kayan jikin sa, tare da isa gaban madubi, da isar nasa kuwa gaban madubin, wata baƙar guguwa ta bayyana, Se kuma aka fara magana a rarrabe wannan baƙar guguwar na riƙe ta koma wata halitta, wacce bata da suffa ko kyan gani. "Kayi kuskure AFUDDDD......" Wata hargitsatstsiyar murya ta faɗa me amsa amo, kuma babu daɗin saurare. Ba tare da an bar shi ya iya furta ko A bane, wannan muryar taci gaba da faɗin. "Haƙiƙa kayi kuskure AFUD kuskuren mafi muni a ciki, kayi kuskure da har kabar ƳAƳAN yayanka ASHFUD suka rayu doron ƙasa, sabo da su ɗin masifa da bala'i ne a cikin rayuwarka AFUD!!!..... Domin tabbas wanzuwarsu a doron ƙasa akwai sanadi ba seda na taɓa faɗa maka ba shin? , ban san wacce kalar baiwa da matsayi ruhinsu ke ɗauke da su ba. Domin kuwa ba iyaka yaron da QASEEM ya gudu dashi bane akwai wani, wanda yana nan yana rayuwa a cikin wannan masarautar, Sai dai duk iyaka bincikena akan gano ainihin ko wanene wannan yaron, na garara gano taƙamaimai ko wane ne shi?, Abu guda ɗaya shine kullum yake sake maimaita Kansa shine cewar lallai ƙaddararsu me girma ce, to ka sani wannan ɗin ba komai bane face cew, lallai shima ɗayan ya tsira, wanda wannan naka yana nufin cewar shima yana nan dab da bayyanuwane, wanda bayyanar sa shi ne babbanr masifarka AFUD, Amma akwai abu guda inhar zaka iya gano mana shi wannan na jikin masarautar, to kuwa zamu sama duk wasu goyon baya da taimakon ruhin da ke lulluɓe da fatarsa....." Wani irin zufane ya shiga keto ma AFUD ɗin, dukkanin zuciyarsa kuwa jinta yake kamar zata faso rufin fata bakwai ɗin dake kirjinsa ta faɗo, saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki, yayi munin daya zarta tunanin duk wani me hasashe. Cikin duhun daren daya gama dalme ɗakin, AFUD ɗin ya ɗago Idanuwansa da sukai jajir, tare da juyowa kansa ya kalli gaban dogon yaron, zuciyarta na kasa jurewa, duk da ya san cewar a ƙa'idar aikin nasu babu juyo, amma haka ya sake ɗagowa a karo na biyu yana sake kallan Bokan nasa, cike da wani irin tsananin tashin hankali mummunan da yaji kamar bazai iya ɗaukar nauyin sa bane ya furta... "Don me se iyaka JININ DEENERH tare ASHFUD ne zasu zamo barana wa rayuwa ta!?, me ya sa se iyaka su....... Ya furta idanunsa jajajir," Saboda da sune wanzuwarsu a doron ƙasa sanadi ne, haka kuma an haifesu ne domin su yi yaƙi da Masarautar Ummulyoodah, amma idan har zakaci gaba da yin imani da ni AFUD, To kuwa tabbas matuƙar ina numfashi ba za ka taɓa tozarta ba , kamar yacce ka fara seka kai ƙarshen wasan AFUD wannan ɗin alkwarinane.!!!....." take Sarki Afud yaji wani sanyi har cikin ransa, tare da furta. "Da kai ɗaya kawai na dogara ya shugabana, haka za kuma da kai ɗaya ne na yi imani a kaf cikin rayuwa ta, don haka nake son samun afwa da sauƙi daga gareka" wani uban ihu bokan ya kwarara tare da furta. "Seni Malafar duniya, domin kuwa ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka, dalilin haka ya sanya masallacin kura ba'a bama kare limanci, shi yasa a koda yaushe kwarin gwiwwarka ke burgeni AFUD, ta yanda kake nuna ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, koda kuwa menene zai faru ya faru, shi yasa nake ƙiranka da *dakan ɗaka shiƙar ɗaka...* koma kayi baccinka cikin salama ɓatacce, domin kuwa nasarar taka ce, idan har zakaci gaba da min biyayya da kuma amsar umarni daga gare ni..... " daga haka ya ɓace ɓattt inda shi kuma ya maida kayan jikin sa yana komawa Saman bed nashi... Â daidai wannan lokacin kuwa tana zaune ta fuskanta alƙibla, duk da kasancewar tsaƙiyar dare ne lokacin, amma hakan be tame ta, sema hannun ɗaya data dafe saman ƙirjinta, ɗayan kuma ta ɗaga shi sama, tana me furta.... "Ya ALLAH cikin wannan duhun daren da Yaƙi tausayawa, daren daya raba tsakanin ruhi da ruhi, da kuma alaƙa mai cike da ruɗani, ka kawo min ɗaukinka, tin kafin wannan rikitacciyar duniyar ta ƙarasa rushe komai kafin gaskiya ta bayyana?, cikin wannan ginanniyar ƙiyayyar tasu maras tushe da amfani, wanda son zuciyar da ya wuce kima ya janyo na rasa haske da kuma majinginata, ta hanyar nuna wariyar da ake nunawa cikin jinin dangi. Tabbas a cikin wannan duniyar akwai ƴan uwan da suke jefar da amana cikin wuta saboda hassada, akwai abokan da suke lalata dangantaka saboda ƙeta da mugun buri. A duniyar da Mulki tare da kuɗi suka fi mutunci daraja, cikin wasu ɓoyayyun zuciyoyin da son zuciyarsu ya rinjayi adalcinsu, waɗan da suka rikiɗar da alaƙa me ƙarfi ta zama jarrabawa, Mutanen da son zuciyoyin su ya sanya suka yi wa junansu wariya, suka raba soyayya da dariya, suka kuma haifar da rauni da hawayen da babu ranar dena su, Mutanen da suka sanya hassada ta zamo gubar da ta tsaga zukatan su ta sama wurin zama daram, Son zuciyarsu ya zama tamkar makami me linzamin daya gama yin raga raga da kyakkyawar alaƙar dake tsakanin mu, Ta yanda nuna ƴan ubanci ya zama sanadiyyar haifar da wariyar cikin gida harta samar da rarrabuwar kawuna, ta kuma jima lalata ƙarfin soyayya mu, ta yanda ina ji ina gani, na zama kamar *MOTA UWAR GLASHI* Ina Gani na faɗa Rami. Tabbas ne Adeenerh na sake yarda SANIYAR DA BA TA DA JELA... ALLAH ke kore mata Ƙuda don ina jin lokacin hakan na daf da dumfaroni, wai shin shi wannan lokacin na bayyanuwar komai be gama yi bane kitheart!???..... Domin ina jin hakan a jikina na daf da faruwa" wata uwa walkiya aka watsa, tare da tsawa ba lokacin damuna ba a lokacin, wani irin dariyar farin ciki da kuma kuka ta saki a lokaci guda, tana me furta. "Na sani, dama nasan lokacin yayi MAZAJEN FAMA, KITHEART LOKACIN KUNE WANNAN BA NASU BA..... *Nigerian Abuja* "Haba Junayna, ki tuna cewar fa kece kika raini Aliyu tamkar ɗan da kika haifa a cikin cikin ki, kin bashi cikakkiyar tarbiyyarki, kin kuma soshi fiye da ƴar da kika haifa, kin nuna masa ƙauna, baki taɓa barin sa koda de da sau ɗaya a zuciyar sa yaji ba mu ne hasalin mahaifansa ba, Don me kike son fitowa ki nuna ma duniyar cewar ba mu ne iyayen Aliyu ba?, don kawai fifita rayuwar taki ƴar eyeee, naji Nufaisa Son Aliyu take, so kuma irin na aure, don ALLAH kimin wannan alfarmar kada ki bari Nufaisa ta fahimci komai, bare ma har ta san da wannan maganar, ina son ta tsaya iyaka nan ni dake...." "Wllh ni kaina na rasa me ke son hawan kaina Qaseem, amma tabbas koma miye tausayin ta ke kamani Qaseem, amma zanci gaba da roƙon ALLAH ya magance mana wannan matsalar dake son kunno mana kai, ga dai shi ma bikin nata befi nan da 1 months ba, idan na tuna hakan ina jin daɗi sosai Qaseem..... Da baya da baya Nufaisan data gama jin komai ta shiga komawa, domin kuwa dama tazo wurin iyayen nata ne dangane da maganar kawo lefen da Mohan yake son yi, kasancewar su yanzun kamar a tsare ne suke, don haka komai ba a buɗe suke yin saba.... Wani kuka ne ya kusan kowace mata amma ta sanya tafinan hannayenta biyu tana toshe bakinta, tare da komawa a guje.... *BY AMMEY LAYLERH 💐* 08104493215 ༺❥𝙍𝘼𝙈𝙄𝙉 𝙆𝙐𝙍𝘼༻ # 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ ~Na Maryam Naseer Mirrah~ 𝘼𝙈𝙈𝙀𝙔 𝙇𝘼𝙔𝙇𝙀𝙍𝙃 ✍️ Book One paid ♡ Page 35&36 𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎. # HE WILL FIGHT # WAR *Littafin RAMIN KURA na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da an biyani haƙƙina ba. Idan kinji kinason cigaba da karanta wannan littafin toh ki biya kuɗin ki akan 1k kacal domin karantashi cikin salama da kwanciyar hankali, idan kuma kinsan zaki fitar min da littafi dan Allah kada ki saya ki riƙe ku ɗin ki banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntuɓeni ta wannan number ɗin 08104493215, idan kuma kai tsaye kike son biya ganan no na account number

Chapter 19 of 23