fara cin abincin ba ta ji yajin ba sai yanzu da ta koshi?�
Ba wanda ya tanka mata sai Anti da ta mike ta bi bayan Intisar din ta, Faisal ya janyo plate din Saratu ya dibi kadan ya kai bakin shi, ba shiri shi ma ya furzar ya ce,
‘Wuh! Allah masifar yaji, ci ka ji Daddy?�
Aminu ya harare shi ya ce,
‘Wa ya sa ta ta zuba? Ina kallonta tana ta zazzagawa kamar ‘yar kauyen da bata san mene ne a ciki ba�
Daddy ya dago a hankali ya dube shi na dan lokaci, kamar mai son fahimtar wani abu a tare da yaron, bai ga komai ba illa tarin kuruciya fal a cikin kan shi. A yau kam ya nuna masa bacin ran shi a fili ya ce,
“Ko kadan bana jin dadin yadda ka ke mu’amala da kanwar ka Aminu, kai ba ka ganin Saratu karamar yarinya ce ne? Kai da ka ke babba da ya dace a ce ka hada kan dukkan kannen ka ka rungume su, sai ya zamo kai ne ka ke nuna bambanci? To su kuma kannnen na ka su koyi me kenan daga gare ka?
Jiya ina ji fa kana tsula mata carbi wai ba ta iya karatu ba, to ba haka ake koyar da karatu da azaba ba, idan har ba za ka koya mata yadda ka ke koya wa sauran ba, ka bari na gode.
Amma daga yau sai yau, kada ka sake taba lafiyar Saratu da sunan duka, don uwar ta na maku kawaici ba zan zuba maku ido ku illa ta yarinya ba, once and for all, ka kiyayi Saratu Ameenu!.�
Hajiya ta aje cokalin da yake hannunta ta dubi Daddy a yatsine kamar za ta yi magana, ko me ta tuna? Oho! Ta maida bakin ta ta tsuke, can kuma ta ja wani dogon tsaki tsuuu! Ta ce,
‘‘Tashi mu bar wurin nan Aminu, maigida ya zo mai tabarma a bakin kofa ai sai ya nade kayarsa, mu nan ba wurin zaman mu ba ne na masu uban ne.�
Ta fada cikin yi wa Daddyn gatse, amma shi din bai tashin ba, kwantar da kai ya yi ya yi ta bai wa Daddyn hakuri har da kwallah. Sai da ya tabbatar masa ya yafe masa tukunna.
Wannan na daga cikin halayyar yaron da har kullum take sayo masa mafificiyar kauna a zuciyar mahaifin shi. Zai yi komai, zai bata wa kowa, amma ban da wadannan mutanen guda biyu; Daddy da Hajiya.
Mutum ne da ya iya takun rayuwar shi, da wuya ka fahimci abinda yake ciki. Yana da taka-tsantsan cikin dukkan al’amuran shi mawuya ci ne ka ce yau ga ta inda ya kuskuro ka, sai dai da yake an ce wai zuciyar mutum birnin sa.
Haka ne Al’ameen mugun mutum ne na karshe ga wanda ya tsana, sai dai muguntar sa tafi yawa a kan Intisar.
In kin san wata kalma wai ita ‘yan-ubanci, to Al’ameen Bello ne shugabanta. Yana son uwarsa, yana son kannensa, baya son kowa ya rabe su saboda matsananciyar kaunar da yake wa Daddyn shi. Yana da ra’ayin rikau na Malam Bature kan single nuclear family life, bai ga dalilin da Daddy zai bata masu family ba ta hanyar kawo wasu can.
A da, kafin Dady ya auri Saratu yana matukar shiri da ita, haka ko san da take karatu a Edeter musamman ya kai mata ziyara har sau biyu a matsayin ta na kanwar ubansa, yana jin dadin mu’amala da ita, kasancewarta mace mai ilimi irin yadda yake so, kuma wadda ta rage masu cikin dangin ubansu kaf, sai Baffa da Goggo.
Amma tunda ta zabi zaman kishi da mahaifiyar shi shi ma ya ce to mu buga, in ya so mai sa’a ya kwaci Daddyn.
To haka Aminu ke ta azabtar da baby Intisar kullu nau’in azabar yau daban ta gobe daban. Har sai da ya zamanto Baby in ta hango Aminu a bakin gate a guje take komawa dakin Mamarta tana haki kamar ranta zai fito, ko kuma wadda ta ga dodo, sai dai ta bude baki ta ce ga abin da yake mata ina! Tana masifar tsoron sa, tun Anti Saratu ba ta ganewa har ta fahimci baby na gigicewa in ta ga Aminu, haka ko muryar shi ta ji daga waje ta nutsu kenan, tun kuma ranar da ya hana ta shan majina ba ta kara ba, majinar ma kanta tsoron ta take ji, bini-bini tana yawo da tissue tana cewa da ‘yan uwan su goge mata, kada Ya Aminu ya yanke mata hanci ko ya ba ta fitsarin Bombino.
Shi ko in ya ga Anti Saratu a wuri ya soma yi mata wakar come on beautiful baby kenan ko taso tambayar baby sai ta fasa, ta kan dauka don yana matsanta mata wurin karatu ne.
Ranar wata Asabar ba aiki daga Aunty har Daddy suna gida ba su je ko’ina ba. Hajiya ce dai ta tafi Cape-Town can South Africa harkar gwala-gwalan su, kafin ta tafi sun shirya a nakasta Intisar yadda mutane za su daina sha’awar ta ta hanyar gurgunta wadannan kafafun nata ta zama gurguwa ta daina wannan tafiyar tata kamar ta mage, ita kuma za ta taho mai da mota End of Discussion (da ‘ya’yan gata ke yayi a lokacin) da ta yi masa alkawari. Aminu yana matukar tsoron Babansu yana kuma masifar son Hajiyar shi ta yadda duk abin da ta nuna ba ta so shi ma daga ranar ya tsane shi kenan.
Rashin imanin da yake ganawa diyar Aunty Saratu ba wai halin shi ba ne domin dai shi mutum ne mai son kananan yara da son wasa da su shi yasa yake son Khalil.
Komai yake yi yana yi ne don farin cikin Hajiya, don Hajiyar shi ta ji dadi, domin ta ce da shi ba irin wulakanci da tozarcin da Daddy bai mata ba a kan Intisar lokacin yana makarantar kwana shi yasa shi ma ya tsane ta, don komai yake so ita ma Hajiyar naso, komai yake so ta na yi masa, ko damuwa ya shiga Hajiya ba ta kuma samun kwanciyar hankali ba kuma za ta huta ba sai ta ga ta gusar masa da wannan damuwar.
Abu daya ne har zuwa yanzun ta ki mara masa baya wato ra’ayin shi na son tafiya karatu Miami (Miami gari ne na ‘yan hutu cikin U.S.A) don tana ganin duk cikin ‘ya’yanta ya fi sonta, ya fi su kaunar ta, ya fi kaunar abin da take so. Idan ya tafi wa zai taya ta kiyayyar su Saratu?
Tsaye yake jikin Volvos 6 din Hajiyar shi, yana ta faman murza ‘yar karamar kwamfutar aljihu pocket computer, sanye yake cikin Kaftani na wata jikakkiyar shadda-rini ‘yar Mali. Sai ga Intisar da Khalil tana rungume da ribdediyar teddin ta, daga inda yake tsaye yana iya jiyo muryar Khalil na cewa, “Baby ki je ki kwantar da ita a karkashin mota zan je in dauko mata filon ta.�
Ya juya ya koma cikin gida yayin da ita kuma ta nufi karkashin motar da Al’ameen ke tsaye ba tare da ta lura da shi ba, domin ya ba su baya ne. Sojojin da ke gadi a harabar gidan ba wanda ya ba su hankalin shi kasancewar sun riga sun saba wasansu a wurin kullum ta Allah.
Ta sunkuya za ta shimfide teddin kenan, sai ya sa kafa iya karfin shi ya yi (bull) da ita, ta hantsila ta wulwula har sau uku, kafin idanunta da goshinta su hadu da wani karfen pipe ta gigice ta dimauce ta saki wata irin razananniyar kara da amsa kuwwar ta ya ratsa illahirin gidan, gaba daya ma’aikatan gidan har shi Aminun suka yi kanta a guje.
Jikinsa ya yi sanyi da ganin jini na gudu daga idanun yarinyar hade da wani irin ruwa. Ya saki Computer da ke hanun shi ya dauke ta a gigice yana.
‘Emma bude mini mota, wayyo Allah na shiga uku! Na yi kisan kai!�
Abin da yake ta nanatawa kenan, har suka isa asibiti. Mummunan labarin ya riski Aunty Saratu ne tana cin abinci, ta saki cokalin ta ce, ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un�.� Don Khalil da ke bayar da labarin cewa ya yi idanun Baby sun tsiyaye.
Shi kan shi Daddy jikin shi babu inda baya rawa, da kyar ya kulle Aunty Saratu yabi bayan su saboda yadda ta fita daga hayyacinta cewa kawai take, ‘Yanzu baby shi kenan idon ki ya tsiyaye?�
Likitocin ido kwararru uku ne a kan Intisar suna kokarin ceton ‘eye-bulls� dinta (kwayar idonta). Sai bayan awanni uku babban likitan ya nemi ganin Daddyn a ofis din shi, ya fara da kwantar masa da hankali, don ganin yadda duk ya fidda rai ya kuma ba shi shawarar a kai baby asibitin kwararrun ido na Kaduna, in an yi sa’a a ceci lafiyar idonta, amma he’s sorry to say, ko da Saratu ta warke ba za ta ci gaba da gani da naked-eyes dinta ba.
Inda duk hankalin Daddy yake in ya yi dubu to ya tashi, bai tausayin Baby kamar Aunty Saratu, da ta ci duk wani buri da fatan ta a kan Inteesar! Amman a yau a ce ta makance! Duk kwazon ta, duk himmar ta da ke sawa ana yi mata hangen zama wani abu a gaba. Bai san san da wasu zafafan hawaye suka shiga yi masa lugulgude a fuska ba tamkar ba Brigadier na soja ba.
Yasa habar babbar rigar a ya share kafin ya sa hannu a tura su Kadunan.
A jirgin (bell-view) da suke ciki, Aminu Bello, tafukansa yasa ya rufe kyakkyawar fuskarsa. Ya sha jin Malamin su na Islamiyya na cewa, ‘Ku roki Allah ya kare ku daga nadama mara amfani.�
Bai taba sanin mene ne nadama mara amfani ba sai yau. Tausayin mahaifin su kadai ya ishe shi na wahalar da ya jawo masa. Ya san Daddyn na son shi, amma a yau yana shakkar, idan son da Daddy ke wa Inteesar diyar Aunty Amarya bai dame wanda Daddyn ke masa ba.
A asibitin Kadunar ma sun ce ne idan Daddyn na da hali to ya gaggauta fitar da diyar sa asibitin kwararrun ido da ke Jiddah, nan suka bar Intisar karkashin matsananciyar kulawar likitoci su suka tafi neman visa. Masu abu da abin su nan da nan suka samu. Karfe tara na dare an shigar da Baby tiyatar ido.
Mu karasa a littafi na biyu.
Taku
Takori
How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two
*@Takori*
Page1ï¸âƒ£
Ameenu kishingide cikin lallausar kujerar asibitin Saudi-German, nadama goma da ashirin ji yake kamar ya farkewa Daddyn shi komai, in ya so ya nemi gafarar shi, ko ya samu saukin wannan dumbin hakki da ya dauka na rayukan al’umma da dama, na kuma yarinyar da ba ta ji ba ba ta gani ba, ba ta kuma tsare masa komai a rayuwa ba.
Lokaci daya ya ji ya tsani kan sa kai da duk ‘ya’ya masu irin halin shi na taya iyayensu mata kishi. Amma tsoron hukuncin da Daddyn zai dauka a kan shi ya hana shi, gani yake kamar ma ya san shi ne sanadiyyar shigar diyar shi cikin wannan azaba shiru kawai ya yi masa, watakila ma kuma idan ya fada masa shi din ne ya tsane shi, hakan kuma ya yi sanadiyyar jawo masa bacin ran Hajiyar shi.
Ya yi tunani iyaka tunani, ya rasa mafita cikin al’amarinsa, tunda kuwa ya zama fitina kenan ga iyayen shi? Daga karshe ya yanke abinda yake ganin shi ne mafi dacewa a gareshi shi ne ya bar su kwata-kwata ya fita daga tsakanin su, ya yi nisa da rayuwar su, ya bar masu kasar baki daya ya je ya ginawa kansa sabuwar rayuwa mai amfani. Me ye amfanin ‘ya’ya irin sa masu sanya iyayensu cikin halin ha’u’la’i? Babu.
Kada ma ya je Hajiya ta angiza shi ga kisan kai, don ma abin ya zo da sauki? Da ta mutu fa me zai ce da Ubangijinsa? A kan wani kishin su na mata wanda shi bai shafe shi ba.
Tunaninikan da yake ta yi kenan har aka fiddo Intisar daga dakin tiyatar da karfe biyu da rabi na sulusin dare agogon su na can. Ya tsaya a kan ta yana ta muzurai ganin yadda aka nannade dukkan idanunta da bandeji, jikinsa ya saki gaba daya.
Washe gari likita Doctor Khair ya tabbatar wa Daddy Saratu za ta gani da taimakon medical glasses kanana da za su yi mata. Bayan sati biyu da yin aikin aka cire bandejin da addu’o’i na musamman a bakunansu don Daddy har Dawafi na musamman ya yi a kan lafiyar Intisar kadai.
To Alhamdulillahi Saratu na gani daga kusa-kusa, sai dai ba ta iya gane abin da ke nesa da ita tangaran abinda a turance suke kira short eye-sight.
A ranar Dr. Khair ya manna mata farin siririn medical glasses tamkar gidan biro don siranta garai-garai da shi kamar na ado, wallahi kada ki so ki ga yadda ya karawa yarinyar nan wani irin kyau da kwarjini, da aka sa mata sai ta kama dariya.
Daddy ya kashe kudi ba kadan ba, amma wannan ba shi ne damuwarsa ba shi dai burinsa kada a ce Saratu ta rasa ganin ta kwata-kwata. Don haka da ya tabbatar tana gani tar da gilashin in an cire ne take gani dusu-dusu sai ya gode Allah.
A ranar da suka cika sati na biyar suka dawo. Anti Saratu duk ta rame ta yi duhu saboda zullumi. A guje Intisar ta rungume Mamarta suka shiga juyi a tsakar gidan har suka bai wa kowa da ke wajen tausayi.
Tana gaya mata labarin Daddy ya saya mata gilas mai kyau, za ta ke ba ta aro tana danawa, yaya Aminu yana ba ta abinci a baki baya tsula mata carbi a unguwar da suka je. Yayin da Ameenun ya yi tsaye harde da hannunsa bisa kirji yana kallon su cike da jin nauyi ko kadan bai bari sun hada idanu da Antin ba, tunda suka dawo. Antin ta dube si ta watsar ta ce, ‘Al’ameen kenan. Kai ma sannu da kokari.�
Yanayin yadda ta fadi maganar cikin gatse, dole ta sa shi ya yi murmushin dole har cleft din ya lotsa, ya kuma sha jinin jikin sa, ji yake kamar ya ce da kasar ta tsage ya shige, ji yake kamar Anti Saratu ta san shi ne sanadiyyar nakasar diyar ta.
Haka kurum Daddy ya aika takardun retire (murabus daga soja) Abuja. Ko kadan Al’ameen bai so ba, domin yana tunanin Daddyn ya yi hakan ne domin ya yi joining su Benga Delsu da ke son yin juyin mulki cikin ‘yan shekaru kalilan. Bakin ciki biyu kenan ya hadu ya tarar masa. Ga nadamar abin da ya aikata, wadda ta sa har ya tsani kansa da kasar haihuwar shi baki daya, ga kuma bakin cikin Daddyn su zai zubar da mutuncin su a idon duniya.
Ran shi a masifar bace ya sake bijiro da bukatar shi na tuntuni, wato na son tafiya karatu Miami, ba tare da ya tambayi Daddyn dalilin shi na yin ritaya ba. Daddyn ya ce ya je duk abin da suka shawarta da mahaifiyarsa shi ba shi da ta cewa. Da kyar Al’ameen ya shawo kan Hajiyar ta amince da tafiyar shi sai dai ba ta amince mai zuwa America ba, duk wani Musulmi na kwarai yana neman tsari daga sharrin wannan kasa, amma ba wai ya yi marmarin kai kansa ba, ba mamamki ya mance kasar haihuwar shi Nigeria ce, birni irin Miami?
Birni ne na hutu zallah, yana daya daga cikin biranen da kasar Amurka ke takama da su, saboda kasancewar shi wani bangare na kara bunkasar tattalin arzikinta (tourist attraction) sabida yadda al’ummar duniya suka zabeshi a matsayin wajen hutun su (Miami resort) ga kuma kashe Musulmi da kasar Amurka ke yi a lokacin.
Ta ce ko dai (ELT Banbury) wato Ealing Tertiary da ke England ko Hull Unibersity (duka Britain ne), hankalinta zai fi kwanciya, in kuma duk ba su yi masa ba to ya tafi jami’ar Abuja. Ya amince zai tafi Hull ne kawai a fatar baki amma can a karkashin zuciyar shi ya kudurce a Miami zai karaci gaba dayan sauran rayuwar shi har mutuwa, ba don jin dadin da ke cikin birnin ba sai don wani specific reason (kayyadadden kuduri) nashi na daban.
Duk wasu shirye-shirye na tafiyar Al’ameen, shugaban kasa na lokacin wanda aminin Daddy ne na kut da kut tun suna NDA shi ya yi wa Al’ameen, ga inda Daddy ya ce a kai shi, amma Al’ameen ya zage ya ce da shugaban Miami ne. Akwai kudi na musamman da kasa za ta ke tura masu duk shekara a matsayin su na ‘yan kasa masu karatu a waje da alkawarin dawowa su yi wa kasar su aiki.
Ran Al’ameen a masifar bace ya bar Nigeria zuwa U.S inda daga nan ya nemi hanyar birnin Florida, a inda ya sami gurbi a babbar jami’ar Miami inda aka yi admitting din shi into lebel 1 Medicine.
A shekarar shi ta biyu a Miami rannan ya ji a tashar BBC cewa an yi juyin mulki a Nigeria. Tunanin Al’ameen kawai shi ne har da Daddy din shi wanda yana ganin wannan karshe zubar masu da martaba da daraja ne Daddyn ya yi tunda har abada ya bar masu abin fadi, ba kuma ya cikin tsari na abin da ya koyar da su.
Aminu ya yi kuka ya yi kuka har ya gode Allah, kukan da bai taba tsamamnin zai taba yi ba a rayuwarshi. Ya alkawartawa ransa shi da gida Nigeria har abada! Ko ya gama karatun shi nan zai nemi aiki ya yi aure ya yi zamansa.
Ya manta Allahu shi ne mai juya al’amura yadda ya so. Ya je ga kwamfuta ya zanowa mahaifin shi sako yana fitar da zafafan hawaye (sanda na rubuta wannan littafi ilmin yanar gizo bai yi sauki da yaduwar da yayi a yanzu ba haka sadarwa ta kwamfuta ba kowa ke yin ta ba) na dalilin da yasa ya bar Europe zuwa U.S shine don kar suke samun koda labarinsa, a ganin sa ba shi da sauran amfani a gare su. Ya yi matukar nadamar wani gagarumin laifi da ya yi wa Daddyn shi ne zamowar shi sanadiyar nakasar Inteesar diyar Anti amarya.
Ya kuma nuna karin dalilin shi na yin nisa da su saboda bakin cikin abin kunyar da yake tunanin Daddyn ya jawo masu. (Kaico! ‘Ya’yan yanzu har mun fi iyayen mu tunani da sanin abin da ya dace su yi? Mun fi su sanin abin da yake mai kyau a gare su? Anya Aminu bai yi kuskure ba?) A karshen sakon sa ga abin da ya ce duk dai mai nuna tsantsar nadamar sa kan abin da ya aikatawa Intisar ko ko nadamar shi da ya kira mara amfani.
“Now, plz, don’t think I feel I’ve overcome all these regrets, I’ve not. I am one of those people that have to-day-to-day job on myself. But gradually, by trying to follow your teachings, I’m learning to control myself and be less critical of my fellow human being. And, it’s like being released from a prison. I just never dream that life could be so full and wonderful as earlier. Sincerely. (Sai ya yi signing din shi a kasan signing din ne ya rubuta).
Mohammad Al’ameen Bello.
Ma’ana: A yanzun haka kada ku dauka ko na yi nasara ne a kan dumbin nadamar da na yi, ban yi ba. Ina daya daga cikin mutanen da ke duba rayuwar su ta yau da kullum a kan-kan su. Amma a hankali, nan gaba ina kokarin in bi koyarwarka, ina koyon yadda zan ke sarrafa rayuwata in kuma zamo mara kushe da hassada ga kowanne dan adam dan uwana. Sai kuma hakan ya zamto tamkar fita ne daga kurkuku. Na san dai rayuwa ba za ta taba zama cikakka kuma mai dadi ba kamar da.
A ranar Anti ke da Daddy, yana bisa kwamfuta yana duba sakonnin shi, yawanci abokan aikin shi ne ke yi masa korafi da nuna rashin jin dadin su na ritaya da ya yi da wurwuri, da sauran karfin sa da komai ga wadatacciyar lafiya. A kuma lokacin da ake mai hangen isowa matakin General, cikin ‘yan shekaru kalilan.
Shi ko Brigadier Makarfi ko kadan ba su san tsarinsa ba, baya da wani nufi illa ya samu lokacin kula da iyalin shi da sa ido sosai a kan tarbiyyar su, tare da fantsamawa mahaukacin kasuwanci don neman abinci, wannan shi ne kadai dalilin shi na yin ritaya, amma ba wai don wani dalili na daban ba.
Kwatsam sakon Al’ameen ya bayyana jikin screen , ya karanta ya maimaita fiye da cikin carbi amma bai fahimci abin da yaron ke shirin bayyana masa ba.
Ba inda suka ce ya je ba ya je, kuma shi ya yi sanadiyyar nakasar idanun Saratu? Ya kai duban sa ga sashen da Aunty ke kwance tana karatun littafin addu’o’i na Al’ma’asurat da take karantawa duk dare kafin kwanciyar barci, ta kare tana kishingide jikin tuntu da alama cikin dogon tunani take, ya ce, ‘Saratu kin yi barci ne?�
Ta muskuta kadan don ta gyara jin dadin kwanciyar ta ta ce, “No, ina tunanin secondary din da ya dace a kai Saratu ne. Sanin kan ku ne Brigadier dole Saratu ta ci gaba da samun ingantaccen ilimin da ta faro da shi, to makarantun nan na Lagos duka babu na yarwa, amma tarbiyyar Saratu nake ji.
Duka makarantun cakude suke maza da mata kenan hakan nan za ta tashi girman Lagos? Abin nufi, ba tarbiyyar Musulunci ba tsarin Addini balle al’adun mu na Hausa?�
Ta yi shiru kadan ba tare da ta dube shi ba, can kuma ta ce,
“Brigadier, ni dai don Allah ina neman alfarma, ina da account mai nauyi, amma dole sai da taimakon ku. So nake in kai Saratu makarantar kimiyyah ta harshen Larabci da ke Riydh ne.�
Daddy ya yi shiru bai amsa ba, tsawon lokaci yana nazarin zancenta, ya kama kan shi da ke faman sarawa tamkar ya rabe gida biyu ya ce, ‘Zo nan Saratu, ki karanta min abin da Al’ameen ke cewa da kan ki watakila na fi fahimta.�
Jikinta ya yi mugun sanyi da ganin Brigadier hawaye yake fitarwa, ita ma ta karanta sakon Ameenu a fili cikin nau’in turancinta (British accent) da ta samu a shekarunta hudu a Edeter, ita ma ta kasa cewa komai, sai dai bata dimauta ba kamar mijinta. Daddy ya share hawayen da ke bin kwarmin idon shi, tausayin Intisar ne kurum da karin kaunar ta tattare da shi.
Tun da yake da ‘yar yarinyar nan babu abinda ba ta gaya masa, amma ko sau daya ba ta taba budar baki ta ce da shi Aminu ya ko dungure mata kai ba. A tun ranar da ya dauko ta, ya ga alamun hakuri a tare da ita, yatsun hannayenta duka cikin bakinta tana tsotso, irin su ne ake kira ‘damo sarkin hakuri.� Hakuri ne da ita tun tana tsumman goyon ta.
‘Anya zan taba yafewa Aminu? Mene ne dalilin kashe Saratu da ya so ya yi? Me yake nufi da kin bin umarnin mu ya tafi inda ransa yake so? Anya Al’ameen jini na ne kuwa? Yau dan cikina ke zargina da abin da ya san ko a mafarki ba zan taba aikatawa ba?
Duk kaunar da nake masa a yau sakayyata kenan, ai shi kenan in dai duniya ce ya je ga shi nan ga ta, wanda bai zo ba ma tana nan tana jiran shi. Allah idan har akwai hakkina akan Al�.�
Aunty Saratu ta yi sulu ta rufe mai baki da tausasan yatsun ta, ‘Kada ka yi haka Baban su Khalil, kada kai ma ka yi abin nadamar. Ni dama tuni na san Ameemnu ne ya yi kwallo da Saratu a bakin Emma, lokacin Aminun bai san yana durkushe yana wanke tayoyin mota ba, amman ban ce komai ba.
Ba don komai ba sai don na san komai Al’ameen ya yi sa shi aka yi, kome ya yi, ya yi ne a dalilin son Mamarsa, a kuma cikin taya mamarsa kishi, amma ba halin shi ba ne.
Ba tun yau ba na san Al’ameen shi kadai ne ya gado Babansa a wurin tausayi da jin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 38