Saratu, babu nau’in kayan kwalliyar da babu. Bayan haka na ganki da ‘kit� mai cikke da kayan kwalliya ‘wet-lips� kala-kala. Wai meyasa ‘ya’ya na suke firgita ‘yan mata ne?
Saratu ta taba sharce dan yatsa da wuka tana firan dankali saboda firgitar ganin Aminu na, to ke, karki zare don Allah.�
Ta bude baki galala! Tana kallon Antin kamar wawuya, Anti ta fita da gudu-gudunta amma bata motsa daga inda take ba. Hunainah ta shigo tana mata dariyar shegantaka ta ce,
“Yaya Najib yace ya soke ‘seniority� dinki daga yau, in kika sake takuramin zamu taru muyi miki dan banzan dukan da zaki kasa motsi.� Ta kyabe baki tana zira doguwar rigarta tana cewa,
“In seniority ne yanzu na fara, ki je ki gaya masa.�
Ba yadda bai yi ba ta fito taki, duk Anti Saratu na jin su, da ya gaji da magiyar har dakin ya bita ya tarkatota falon yana cewa,
“Nima balaraben ne da za ai mun gaye ko na miki kama da shasahashun samarin Faransa, wadanda mata ke masu yanga koko donni ba fari bane, da dai ba’a san asalin balbelar bane sai tace daga Makkah ta zo, da wasu idanun ki fiki-fiki kina wani lallankwasa harshe wai ke balarabiya nan ko fillo mai tallen nonon shanono ce.�
Dukkansu har ita basu san sanda suka tintsire da dariya ba har Intisar da ke ji da abinda ya ishe ta ta murmusa iya fatar baki, da suka dameta sai ta tashi tsam ta bar masu falon, daga baya Anti taji su sun sarke da hira ana ta darawa, tayi murmushi a zuciyarta tayi fatan abinda take zargi yazan tabbatacce.
An hadu har Daddy washegarin ranar ana karya kumallo kamar yadda yake a al’adar gidan, amma Najib da Hidayah sai aikawa juna kallo ake ana murmusawa duka Antin na hankalce da su tana dariyarsu, ta tabo Intisar ta nuna mata Najib da Hidayah na magana da ka, kamar kadangaru, da alama Hidayah rokonshi take ya daina kallonta Daddy na kusa da shi, shi kuma ya dage kai tare da dage gira alamar sai me in Daddy na kusa da shi?
Haushi ta shake Hidayah, sai kuma ta ga to me yayi mata zafi? In dai ‘ya’yan Hajiya ne gata nan gasu, wadda ba’a Haifa ba ma suna nan suna jiranta, ta harareta ta gyada kai ta cigaba da cin abincinta.
Daddy ya aje kofi ckin natsuwa yana walainiya da idanunsa bisa makeken teburin cin abincinshi da Iyalinshi da yake ji incomplete har sai da yayi nasarar gano wanda bayanan, ya ce,
gasu, wadda ba’a haifa ba ma suna nan suna jiran ta, ta harareta ta gyada kai ta cigaba da cin abincinta.
“Wai ina Faisal ne a gidannan?� Nasir ne ya amsa ya ce, “Na ke jin bai fito ba, kwanannan na rasa meke damun Ya Faisal Daddy, duk ya zama wani calm, cool and introvert (Shiru-shiru, sanyi-sanyi kuma mara son magana) ko murna ba yayi da samun aikin sa, har matsayin mataimakin D.G, kasan ba wai don qualification din shi ya kai bane illa kasancewarsa trained din England kuma ya nema a dai lokacin da shugaban NNPC yai retire mataimakin shi ya hau kujerar shi kuma aka bashi (Ass.Director) amma banga alamar yayi farin-ciki ba.�
Daddy yai dan nazarin maganan Nasir kana ya maida dubanshi ga Intisar data sunkui da kai, ita kadai ta san yadda take ji, ita kadai tasan halin da zuciyar ta ke ciki kan sauyawar rayuwar Faisal. Ai ita zata gayawa kowa Faisal ya canza, mutum mai far’a, raha, da hada-hadar jama’a (cheerful and passionate) shine a yanzu ya maida kansa bare a gidan ba tare da shiga harkar kowa ba.
Bata kai karshen tuninta ba ta tsinkayi muryar Daddy can tsakar kanta na cewa “Saratu-karama maza–maza kirawomun Faisal, ki gaya mai na ce kada a kara zama cin abinci a gidannan yana cikin gidan bai zo ba, ba na so!�
Ta mike tsam tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, tamkar mai tafiya bisan kaya kafafunta na harhardewa don sanin duk jama’ar falon ita suka zubowa na mujiya, haka kawai taji gabanta na faduwa fat-fat tana dosar sassan su bugun kirjinta na kara tsananta tamkar koyaushe wani bakon al’amari zai faru da ita mai dadi ne ko mara dadi?
Hakan dai ta daure ta tsaya kofar dakin tai sallama ta yane labulen ta leka kanta kadan, don tunda take bata taba shiga dakin Faisal ba tun bayan tafiyar ta Riyadh, kuma koyaushe ta zo hutu yana makaranta, sadda ta same shi agarin kuma ana cikin tashin hankalin rashin Daddy wama yake ta wani neman dan’uwansa.
Da hankali ya natsa kuma ta dauki buhun fushi ta aza masa shida ‘yan uwansa kaf bakikkirin take ganinsu, bata kula su tunda kan su kadai suka sani sai Hajiyarsu, bayan fitowar Daddyn kuma ga abinda ya faru, inda Faisal ya bar kasar, to sai yau, don haka tana ta kissima me zata gani a dakin Faisal?
Karar zubar ruwa a toilet ya tabbatar mata Faisal na wanka ne, a hankali ta karasa shigowa da gangar jikin ta har tsakiyar dakin, sai kuma ta juya zata koma har ta kai bakin kofa kawai ta juyo ta karewa dakin kallo tsaf, haka kawai taji tana son yi mai kwa-kwa.
Tangamemen hotonta (window-size) tun tana shekaru takwas cikin ‘snow� wato kankarar Switzerland irin wanda ke dakinta na kuruciya, shine abinda zaka fara tozali dashi a gabas maso kudu na dakin.
Dakin babu wani shirgi komi tsaf cikin tsari da burgewa, dan matsakaici ne shimfide da marbles sai dan karamin chinese-carpet siriri a gaban gado (medium Italian-bed), da centre table na ‘row-glass� a gefe. Ba kujeru ko daya sai wadda ke jikin tebirin karatu da tulin takardu da jaridu zuwa magazines. Ilahirin dakin gauraye yake da parmanent watau tabbataccen kamshinsa na 5,000 dollar perfume tamkar kwalba guda aka rotse a dakin, nan ko tsabar kama komi nashi ne da turaren yayi, ma’adanar sanya kaya ta jikin bango da labulaye shara-shara farare sol sai sanyin raba ke kwarara harda kankara-kankara, don son sanyi irin na Faisal split biyu ce a dakin ta sama da ta kasa, ba wani kayan kallo sai allon kwamfuta har (Desktop, Mini, da Laptop) dake can wani corridor akan tebur na musamman makale da ‘yar kujerar kushin mai juyawa.
Cikin tafiyar nutsuwa ta iso jikin gadon inda ta hangi DIARY din shi da ya aza biro a tsakiya, da alama yanzun yai rubutu, sai ta zauna bisa (centre-table) ta soma bude shafukan cikin zakuwa.
Shafin farko wani dan karamin hotonta ne (pass-port size) shima tun tana kankanuwa, aji daya a makarantarsu ta Riyadh. Shafi na biyu maganganun da sukayi ne can baya kan Ronke Adeyemi. A kasan su yayi wasu maganganu da suka gigita ta inda ya rubuta;
Ya bar gida domin kar abinda ke ranshi game da ita Saratu ya tonu. Itace hakikanin yarinyar da yake so, yake kauna, take burgeshi yake kuma son ya aura da dukkan ruhi da zuciyarsa amma ba zai taba iya aure ba tana matsayin kanwar shi da suke uba daya?
Bayan wannan abubuwan da ya gamu da su ne a Birmingham, nasarorinsa da matsalolin da ya gamu dasu. Mu’amalarshi da wata yarinya Jean, saboda kamanninta da Saratun na sawa ya so ta.
Duk ta wuce wannan a gurguje jikin ta ba inda baya rawa zuwa inda ya rubuta matsalar karatunta, inda ya rasa kudin maidata Riyadh! Irin mawuyacin halin da ya shiga har Allah yasa Haj. Ta bashi kudi ya kai mata banki, yadda ya samo visa da su da yadda sukayi da Anti Saratu. Tun daga lokacin ya kudurce wa ran shi neman nashi: (neman na kan sa) don Saratu ta huta, don Saratu tayi karatu mai kyau irin wanda Mamar ta ke so tayi, don Saratu ta samu ingantacciyar rayuwa tamkar tasu, don Saratu ta samu rayuwa mai kyau koda mijin da ta aura baya da shi, shi ya zame masu komi. Ya alkawartama ranshi rashin dogaro da dukiyar Hajiya, dukiyar da Saratu bazata amfana da ita ba, bai ga amfaninta ba.
Akwai inda ya rubuta wahalhalun daya sha a Birmingham domin kokari da son fidda son ta. Amma abu kullun sai karuwa. Abinda ya kai shi ga kurba ‘giya� domin neman ‘relief�. Tuni hawaye ya wanke mata fuska. Ya cigaba da rubuta yadda giya tayi masa wata illa a huhu, babu wanda ya kula da shi sai Jean. Hakan dai a daddafe yayi-baya-yi-ba ya kammala karatun M. Sc bai ma tsaya yin Ph D din ba. Dawowarsa babu abinda ya fara karo da shi sai maganganun Anti Saratu masu kama da saukar mashi a kahon zuci. Cewa da ta yi,
“Insha Allahu duk wani jininsu sai ya ga tozarci a duniya.�
Tun daga lokacin ya yanke shawarar yayi baya da ita, don ya san Hajiya ta riga ta gama illata mutuncinsu a idanunsu. Idan ya cigaba da nuna mata kauna ba mamaki tsohon gyambon ya bare.
Abin mamaki, Yadda yayi nadamar dawowashi Nigeria ranar da Inteesar da Aminu suka fadi suka suma akan idonshi wai a matsayin suna son juna unknowingly ba tare da sani ba, yadda labarin ya gigitashi, tun daga lokacin ya ji ya tsani dan uwansa Al’ameen don yana ganin yaci amanarsa. A ganinsa shine mutum na farko da zai bada shedar so da kaunar da yakewa Intisar tun tana jaririya.
Ashe shima kansa Aminun bai san wacece yarinyar ba, bai san Intisar ce diyar Anti Amarya ba! Bai san yarinyar da yafi tsana fiye da kowa ce ba. Sai ya ta’allaka suman Aminu da cewa ‘shock� ne ba ‘so� ne ba, kuma daga ranar bai kara son ta.
Da zance ya bayyana cewa Saratu ba kanwarsu bace ya gigice, a lokacin ne kuma ya lura maimakon Aminu yayi dana sani sai ma warkewa da ya soma, wannan ya tabbtar masa da cewa Al’ameen na “love-sick� ne ‘rather than shock� kamar yadda ya tsammana, farin cikin ganin cewa zai mallaki Intissar din sa, daya shekara yana jiyyar soyayyar ta, (kura da shan bugu, gardi da amshe kudi), sai ya gwammace yin nisa da asibitin kada bakin ciki ya kasheshi kwanan shi bai kare ba.
Duk da haka ya zauna ‘in hope� ma’ana cike da burin sauyawar al’amuran, kaman yadda yake tsammanin shi kadai yafi kowa so da sanin ciwon Intisar diyar Anti Amarya. Amma a kwayar idon Al’ameen ya ga so tsantsa, ninkin-ba-ninkin na shi. Ya san Aminu Mai-nasara ne, ba kuma abinda ya taba sawa a rai bai samu ba. Ya san Saratu ta furta kin amincewa da auren Al’ameen ne only in frustration din (cikin bacin ran) kiyayyar mahaifiyarsu a kanta. Amma duba daya yayi mata ya gano babu inda bai amsa son Al’ameen a zuci da gangar jikinta!
How much do you like this story?
5/14/22, 09:25 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book three
*@Takori*
Page8ï¸âƒ£
A kalaminshi na karshe, wadanda kuma suke kalmomi na karshe a littafin da alama ma yanzun ya rubuta;
‘To in haka ne shi meye ribar sa a rayuwa? Da me ya yi riba da me ya tsira? Bai gani ba! Bai ci riba da son Intisar ba, bai ga amfanin ilmin daya nema don ta huta da shi ba, tunda Al’ameen billonnaire ne, baya bukatar a agaza masa, bai ga ranar da son da ya shekara yi mata yai masa ba. He is but a real loser! To amma tunda don ita ya nema, shi mai mallaka mata duk abinda ya mallaka a duniya ne koda kuwa ta auri Aminu ne ko waninsa, tunda dama tunda fari ya alkawartawa ransa hakan.� Ragowar bata iya ta karasa ba, saboda kwakwalwar ba zata iya ganewa ba…�.balle ta fassarawa zuciyar ta!
Inteesar ta daga ido sama tamkar mai kididdiga adadin juyawar fanka, wasu irin hawaye ne marasa dandano bare launi ke tsere ‘one after the other� (bi-da-bi) kan kyakkyawar farar fuskar ta. Abubuwa da dama ta tuna a wannan lokacin, wato kuruciyarsu da Faisal can baya.
Ashe dama abinda take ji game da shi a lokacin itama ‘son� ne? Gaba daya jikinta ba inda bai diba ba cikin kaduwa, dimuwa da razana, a take zazzabi mai zafi ya soma kokarin rufeta, saboda karkarwa da ilahirin jikin ta ke yi littafin ya zame ya fadi kan kafarta, dai-dai lokacin da Faisal ya murda kofar bandakin ya fito gabadayan sa.
Daure da towel faffada iya kungushi yana ‘combing� sumar kanshi sai ya daskare cikin matsanancin mamaki, suka dubi juna a gaggauce idanunta face-face da hawaye, tayi saurin juya mai baya, kana ta doshi kofa tana cewa.
“Dama Daddy ne yace in kirawo ka, kada a kara zama cin abinci kana gida baka zo ba� ta sheka da gudu zata bar dakin abin tsautsayi, sai gilashin ya fado ta kuma taka shi da kafarta hannun ya lankwashe amma saboda quality (karkon) gilashin bai fashe ba, kamin ta russuna ya isa gareshi sai suka russuna a tare, hannunshi ya riga isa bisa gilashin don haka natan sai ya sauka akan nashin, shi yai nasarar daukowa, yasa karfi wajen gyara lankwashewar da yayi, a yayin da ta jingina da bango idanunta a runtse, hakannan hawayen basu fasa kwarara ba kamar an sunce fanfo.
Ba komi take tunawa ba a lokacin face ranar da ya cire mata gilashi ta baya, lokacin ana shirye-shiryen tafiyarsu Riyadh ita da Khaleel, ta dinga bin inuwarsa a hasale tana “bani gilas dina Ya Faisal, kaga bana so� haka dukan da ya sha da filo da wakokin da ya kanyi mata na “come on beautiful Babe, Maman?�
Cikin nutsuwa ya maida mata gilashinta, suka sake dubar juna a susuce sai ta kara da gudu.
Ya dade anan tsaye yana tunanin me ta gani ya sata kuka? Me ta gani ya gigita ta haka? Bai yi tsammanin zata sake kulawa da al’amarinsa ba a yanzun dai da ta ke cikin son Yayan shi Ameenu?
Intisar dakinta ta nufa agigicenta ta maida kofar ta rufe ta murza key. Ta jigina da kofar ta sake runtse idonta da karfi, tamkar mai son farkawa daga mafarki. Abubuwanne ke tariyo mata can baya tamkar a majigi. Ta tabbatar Faisal shine mutumin da ta fara so a rayuwarta kuma mutumin da bazata taba samun mai kaunarta a duniya tamkar shi ba. Tausayinshi, yagama narkar da duk wani tunani da ta mallaka. Ta zargi kanta da cin amana ta kuma kirayi kanta da ‘butulu� dan adam mai manta alkhairi.
To amma wani bangare na zuciyarta ya kalubalanci hakan da hujjar cewa, a lokacinta da Faisal tsammani suke su ‘yan uwan junane sabanin haduwarta da Al’ameen. Hakannan Al’ameen shi ya koyar dai ta son shi, shi ya kimsa mata son shi karfi da yaji, bata san so na soyayya ba sai akan shi, don haka bata jin Allah zai kamata da wannan hakkin na Faisal sai dai kaso mafi rinjaye na zuciyarta na karfafata da cewa, yanzu ne ya dace tayi wani abu, yanzu ne ya dace ta sadaukar da kanta da soyayyarta (son da takewa Al’ameen) don nunawa Faisal wannan kaunar da ya wanzar da rayuwarshi nuna mata, tun tana a tsumman goyo. To wai ma ya akai ta so Al’ameen? Bata sani ba, illa may be because he is unikue (watakila don shi din na daban ne).
Ta yaya? Ta yaya zata nunawa Faisal din kauna bayan a yanzun ya nuna baya da lokacinta ma? Ta tambayi kanta, lokaci guda ta bawa kanta amsa da cewa ta hanyar auren shi mana Intisar? Amsar tayi mata nauyi a baka da zuci, wai Intisar matar Faisal in banda Allah mai juya al’amura ina wannan abu zai taba zuwa masu a rai?
A lokacin ne kuma ta tuna shima fa Faisal dan Hajiya ne! Wannan zuri’ar da tayi alkawarin ba zata sake kulawa ba! Wannan zuri’ar data nuna mata kiyayyar da ba wani mahaluki a doron kasa da ya taba nuna mata! Wannan zuri’ar da idan ta aura, ta sake jefa kanta cikin bala’I da masifa ne watakila ma fiye da na baya. Bayan yanzun da cikakken gatanta, ga Aunty, Daddy, uwa-uba dangi da uwa mahaifiya masu so da kaunarta. Zuri’ar Haj. Nafi? Ta girgiza kai da karfi, ire-iren maganganun Haj. kadai ke dawo mata wasu na bin wasu.
“Wai me yasa kike son ‘ya’yana ne, bayan ni na tsaneki? Har kullum mutum kanyi nisa ne da jinin makiyin shi, Saratu banda ke! Don naji ance komi Faisal kike ambato, har kuka kika yi da ya bar kasar, yayi maki kama da ‘ya’yan mutsiyatan kauye ne?
So nake bandakin nan ya fiki fari, ya kuma fi Faisal di na kamshi� Faisal ne ya sa miki suna Intisar, kuma da na ne, mallakina ne, don haka daga yau na kwace�. Ke Jikar Jummai ce, Jummai uwar Saratu�. Daga yau kika sake koda kallar min ‘ya’ya, sai na sa wuka na tsokale wadanna makafin idanun munafurcin, kina jina? Ta tuna amsar da ta baiwa Hajiyar a lokacin. A yau ma sai ta samu kanta da nanata su, sai dai sabanin sunayen da ta kira a wancen lokacin a yau cewa tayi…ba Faisal ba, ba Aminu ba� duk wani jininki ma idan na sake daga ido na dubeshi ba da kiyayya ba, ki ce ni shegiya ce na amince!
Ta kudurce a ranta daga yau dukkansu ko gaisuwar dayansu bata so. Aure kuma in har sai da ‘ya’yan Haj. Nafi ne, to ita Saratu ta yafe!
Ba irin bugun da su Hunainah da Anti ba suyi ba amma Intisar bata bude ba. Wuni tayi cin kuka da nadama mara amfani. Ta rasa meyasa rayuwar ta ke da matsaloli iri-iri tun tana jaririyarta. Dagabaya kuma tayi tunanin akan me zata bari soyayyar ‘ya’yan Hajiya ya wargaza mata rayuwa? Komi fa mutum ke daurama kansa don Allah baya daurawa rai sai abinda zata iya.
Ta yankewa kanta ‘solution� na karshe tayi murmushi ita kadai. Ta san cikin Iyayenta kakaf, babu mai matsa mata akan wannan kudurin nata. Sai ko Mamarsu Hunainah ita ko bata jin ta don ta tabbata Daddynta zai bata goyon baya dari bisa dari.
Ba ita ta fito ba sai karfe hudu na yamma, shi din ma azababbiyar yunwa ta fiddota. Su Hunainah na magana da Anti Hajjo a waya ta ce,
“Gata nan ma ta fito� ta mika mata wayan ta ce,
‘Hello Aunty� Hajjo ta ce,
“Ba wani Yello Aunty, nikan baki dauke ni Antin ba, da ko menene ke damunki da kin kira ni kin gaya mini, Saratu shin me yayi zafi ne haka? Na ji an ce tun safe kin rufe kanki a daki kina kuka.
Na dauka kasancewar mu kusa da ke, da tabbacin da kike da shi na iyayen kwarai ya isa ya sanyaya maki zuciya? Wannan kuntata duk na menene?�
Tayi shiru, Idanuwan ta sunyi rau-rau kaman ta saki kuka. In da Anti Hajjo ta san yadda take jin zuciyar nan tata, da bata zargeta da kuntatawa kanta ba.
Ita ba sauyin Iyaye ya dameta ba, damuwarta daban ne, daga ita sai Ubangijin ta suka santa. Hajjo ta ce,
“Koda bakya kaunar mu Saratu, mu ne dai iyayenki, kuma ba’a sake iyaye sai iyayen daki. Wannan rashin sakin jikin da kike damu ban sani ba ko don ki na ganin bamu isa mu zamo iyayen ki ne ba?� (Aunty Saratu ce ta koya mata, ba’a jin damuwan ta sai da dabara) Ta sa kuka da karfi tace “Aunty Hajjo me ya kawo wannan maganar?
Na rantse da Allah ba haka bane, ni abinda ke damuna daban ne.�
Hajjo ta ce, “Don kin ce kin fasa auren Al’ameen? Ke, yarinyar ki da ke kar ki bari ciwon hawan jini ya kamaki akan soyayya. Shi Al’ameen din yace dake ya damu? Yana can tare da matarshi Allah kadai yasan farin-cikin da suke ciki sai ke ki bi ki kuntatawa ranki?�
Ta share hawayen da ke zuba mata da bayan hannu, dai-dai sanda dan halak din ya yiwa falon tsinke, matarsa na biye da shi tamkar ta shige jikinshi don tsatsiba, ya zarce kai tsaye har inda take, ya ja tebur inda take ya daura kafa daya, dayar kuwa na kasa tamkar mai son jin kwakkwafin abinda ke sata kuka a waya.
Ihsan ta bisu da kallo kana tabi bayan su Hunainah da sukayi cikin dakin Anti. Intisar ta bude baki domin ta bawa Antinta amsar da tai niyya amma kwarjinin Al’ameen ya katse komi. So ta ke tace har wata tsiyace Al’ameen din da zata kuntatawa kanta akansa? Ita ba shine damuwanta ba.
Hajjo ta ji tayi shiru ta cigaba da cewa, “Ni dai shawarata a gareki Intisar, ki fidda damuwar komi a ranki, ki koma makaranta. A shirye muke damu nuna maki kauna ta kowanne fanni. Na san kina son Al’ameen, so bana wasa ba. Tunda har
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 38