sa tare ba, tun auren su, ko ofis tana like da kayan ta saboda nurses masu yi masa kallon da bai gamsar da ita ba. Ihsan kenan.
Takalmi flat fari sol dan Thailand ta zura kafafun ta dan dagwas, turare mai suna turare ita kan ta ba ta san kala nawa ta fesa ba, musamman collection na Calvin Klein da Dior, ta yadda har ba za ka tantance kamshin wane turare take ba, wannan duk yana daga cikin koyarwar Al’ameen Bello, domin shi mutum ne mai masifar son kamshi, baya jin kyashin saya masu turare ko na nawa ne.
Musamman zai je Paris don kurum ya sayo masu turare, wadannan na daga cikin dalilan da suka sa har kullum take son shi, take kuma kara kaunarsa a kowanne dakika, domin hakika shi din special ne, haka komai nasa na musamman din ne.
Tun haduwar su bata kara duban wani da namiji a duniya da sunan so ba, shi kadai take so, shi kadai take sha’awa, shi kadai ke burge ta, hakan nan shi kadai ne namijin da zai iya yi mata kowanne irin wulakanci ta shanye. Dr. Ihsan kenan.
Cikin takun kasaita ta wuce Ann ta ce,
“Ba za ki je ku gaisa ba Ann?�
Ann din ta dube ta sama zuwa kasa ta ga yadda ta wani hade kamr mai shirin zuwa dinar babbar aminiya, wani haushi ya kama ta don ita so take ta kashe auren kowa ya huta, don ba ta ga yaron da ya isa ya wulakanta gudan jinin ta ta kyale ba komai tashen nairarsa kuwa, kuma ko dan uban waye shi balle wani shirmen banza likitan kwakwalwa, amma ba ta son ta bata farin cikin Ihsan, don ta lura still tana son mijinta sai ta bi ta da siyasa.
Ta juyar da kai kawai ta ce,
“Ki je kawai ki ji wadda ya zo da ita, zan zo in raina ya yi sanyi, don har yanzu raina a bace yake. Kin kuma sanni ban iya boye bacin raina ba.�
Ta kadai kai ta fita fuskar nan ba annuri sam, ta shiga taka matattakalar da za ta sada ta da falon, kasancewar ainahin ginin falon bakin Dr. Argungu a kasan gidan yake tamkar ka shiga rijiya ne ka tadda sabuwar duniya. Ta sa kai ba ko sallama.
Aminun shima daman ya cika fam, da shanya shin da aka yi fiye da awa biyu kamar wani mai neman aiki a bankin su?
How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ___________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book one
*@Takori*
Page6ï¸âƒ£
Tsaye yake kikam, ya hade hannuwan shi a kirji yana kallon tangama-tangaman hotunan ta kamar ta fito ta yi magana da aka manna a kusurwa biyu na falon tabbacin ana ji da Ihsan kenan, kuma ita daya kenan a gidan tamfar rai ga iyayenta. Ko bude abubuwan da aka jera masa bai yi ba balle ya kai ga ci.
Ta samu kujera can nesa da shi ta harde, ta dauki remote control ta karo karfin A.C ko sannu da zuwa ba ta ce masa ba balle ci kan ka. Shi ne ya gaji da shirun ya bara, ya dubi agogon hannun shi Jovial ya ce,
“Saboda Allah Ihsan haka ake karbar baki ku a gidan ku?�
Ta sake tunzura ta ce, ‘Da aka yi me?�
Ya ce, “Kin san awanni biyu kenan kwarara, ina zaman jiran fitowar wani a cikin ku, amma shi ne sai yanzu ki ka ga damar fitowa?�
Ta yamutsa fuska ta ce a zafafe,
“Aminu, har kana da bakin gaya min haka? For God’s sake, yau kwanakin mu nawa a garin nan amma ka nuna wa iyayena ba ni da wata daraja a idon ka ba ka kuma damu da ni ba, shi ne kuma har za ka nemi gayan magana? Wai haka muke karbar baki, to ni ko iyayena da wa ka ke?� Ta tsatstsare shi da ido.
Al’ameen ya san ba shi da gaskiya, kuma ko a wurin Allah ne ba shi da ita. Dole ya sauke nashi temper n ya samu masangalin kujera ya rage tsawo, ya sanya hannu cikin aljihu ya zaro wayar shi da ke ta tsuwwa a cikin aljihun kaftanin shi, ya dade yana magana da aminin shi Rehab wato babban likitan Meritime yana gaya masa irin muhimman ayyukan da suka gabatar ne a kwanakin, ya ce ya yi kyau ya kuma yaba komai, ya gaya masa akwai motocin sa har yanzu suna port bai san ba a auno su ba, sai jiya ya je da kansa ya auno masa ta jirgin ruwa, amma ta Nijar za su biyo don ba jirgin kaya tun bayan da suka taso, don haka ya je ya fiddo su a Yamai. Suka yi sallama ya maida wayar shi aljihu.
Ya dubi Ihsan da sassanyan kallo ya ga ko kallon shi bata yi, ta maida fuskar ta can wani gefen daban bayan ta daure ta iya daurewa kamar bata san Allah ya yi ruwan tsirar shi ba ma, ransa ya sosu, amma sai ya yi murmushi ya ce,
“Ihsan kenan, dadi na da ke ba kya tsayawa ki ji uzurin mutum sai kawai ki kama fushi, amma ai ke ma dai kin san I missed you very-very much…�
Ya kira kalaman cikin tattausar muryar da ta kusa sa ta gyangyadi, amma da yake tana son ta nuna fushin nata sai ta cije ta kyabe baki a lokaci guda kuma tana girgiza kafa daya kan daya ita ala dole fushi take, duk sai ta ba shi dariya, ya mike har inda take ya mika mata hannuwan shi masu matukar taushi alamar ta tashi su yi sulhu, amman sai ta noke cikin jan aji irin nata, sai ya russuna ya kama hannayen ta duka biyun ya mikar da ita tsaye, suka fuskanci juna cikin ido, ita kallon haushi take masa shi kuma kallon I beg your pardon.
Ta ce, “Me ye haka?�
Amman can karkashin zuciyar ta hucewa take yi, tana kuma kara son mijinta a kowanne dakika, duk wata hanya da ya san zai bi ya wanke laifin shi a zuciyar ta ya san shi, duk da ta san kaunar da ita take masa ta rinjayi wadda yake mata, amma yana kokari a koyaushe ya nuna shi din mai son ta ne, mai gudun bacin ran ta ne.
Bare yanzun da ta yi kewarsa, fiye da yadda bakin ta zai iya fassarawa, sai ta bada kai bori ya hau. Sun dade cikin farantawa junansu tamkar suna gidan su koko bakin beaches na Miami, kafin su zauna su fuskanci juna, jikin ta a barin kafadun shi na dama, ta soma share hawaye da bayan hannu duk ya bi ya rikice ya ce,
“Me ye kuma?�
Ta ce, “Anya Al’ameen ba ka gamu da wata kana so ba a dawowar mu? Wace ce Halimah da ka ke kirana da sunan ta yanzun?�
Ya ji gabansa ya fadi damm! Kwata-kwata ya manta da wa yake tare, ya mance a inda yake, ya mance abin da yake yi, ita kadai ke yawo a ransa, ita kadai ke yi masa gizo a kowanne kiftawar ido. Amma ai namiji ne, tuni ya waske ya sha kunu ya ce, “Da aka yi me fa?�
Ta yi tsaki ta ce, “Nufin ka ba na ji sosai ko me? You ‘ve both changed, u ren’t my real Ameenu (Gaba daya ka canza kai ba Aminuna da na sani ba ne).
Ya ce, ‘Ashe? Baki na yi ko fari?�
Ta ga yana neman ya raina mata hankali, sai ta yi murmusin takaici ta ce, “Man, kada ka yi fooling dina man? Be frank, duk ka canza, ka yarda ko kada ka yarda, na ji ka ba a yadda na saba jin ka ba, na rantse I’m smelling something trouble (Ina sunsunar wani abu mara dadi a tare da kai).
Inda Allah ya cece shi shi ne kafin ya motsa bakin shi don shirya amsar da zai ba ta, Ann ta yaye labule ta shigo, shi ne ya matsa gefe cike da haushi, me ake da kafiri? Babu ko sallama balle neman aminci ga wanda ka taras? Ita ko Ihsan ba ta ko motsa daga yadda ta ke ba don ita kanta ba ta ji dadin abin da mahaifiyarta ta yi ba, ai ko bature yana kwankwasa kofa, ta san halin Al’ameen din ta sarai daga yau baya kara girmama ta, don ya sha ce mata babu dabba kamar mai shiga waje babu sallama.
Ann ta dade tana kallon su cike da haushi kaman ta rufe Ihsan da duka ta ce, ‘Get out stupid.� Sum-sum-sum ta fice tana sharar hawaye, ita fa tana son Aminu, ba kuma za ta yarda a kashe mata aure ba, ita kadai ta san wahalar da ta sha kafin ta same shi. Sai dai a yau ma kamar kullum tana shakkar kaunarsa gare ta, amma na yau ya fi na kullum.
Duk da cewa bai nuna mata wani abu ba ita dai zuciyar ta na ba ta yakinin a lokacin da suke tare hankalin shi baya tare da ita, musamman saboda sunan da ta ji ya fito cikin kuskure daga bakinsa, da kyar in ba wata ya gano yana so ba, sai ta kara barkewa da kuka.
Ta samu kujerar da ke fuskantar shi ta zauna ta ce, “I’m sorry, na dauka wajena ka zo da babanta?�
Ya ce, ‘Oh yes, Ma’ama, me too, am sorry, ni da Ihsan mun yi missing juna ne sosai.�
Ta dube shi a lalace, sai dai fa ita kanta na mamakin wai wannan tsalelen ne mijin Ihsan din ta? Ko ita ta samu miji kamar shi ba haukan da ba za ta yi ba a kansa, sai ba ta ga laifin Ihsan ba ko kadan, amma Addinin shi ne ba ta ra’ayi, kuma tana son Ihsan da auren manyan mutane ne irin baban ta ba wai yara professionals irin su Aminu ba, yo me na sama ya ci bare ya bai wa na kasa?
Ta zuki iska ta fesar ta ce, ‘Haka ne? Ni ko sai na dauka ba ka son ta ne.�
Ya ce, “Ki yi hakuri Ma’ama, na dade ne rabona da gida, shekaru goma sha biyar, na dawo na tarar da uzururruka da yawa da suka sha gaban kaina, in kin duba fa kwata-kwata ko sati biyu kwarara ba mu hada ba a kasar, ita kan ta Ihsan ta sani ni ne babba a gidanmu, so kin ga ko family dina bai isa a ce na gama da su within a week ba, ku yi mun uzuri, rashin zuwana baya nufin tozarci ko izgili a gare ku don ko jiya babana ya samu Dr. A ofis, so ki yi hakuri.�
Ta gyada kai cikin gamsuwa da wannan ta ce, “Na lura dai kana son ci gaba da zama da Ihsan bayan wanda ku ka yi a Miami bai isa ba, to ina da wasu sharudda da zan gindaya maka a gaba, idan har ka amince da su to ko a yanzu sai in kira Ihsan ku tafi.�
Ya ce, ‘Ina jin ki Ma’ama.�
Aminu fa daurewa kawai yake yana bin ta da yadda take so, ba don komai ba sai don nuna yes, yana son Ihsan, ya kuma san bai kyauta masu ba, amma shi ne za su gara shi kamar wata taya don kurum ya ce yana son ‘yarsu, su din banza?
Ya dai kanne bai nuna ba a fuska. Ann ta gyara zama ta dube shi sosai ta ce,
“Da farko dai ni Christian ce, karewa ma Babana Pastor (priest) ne babba a sanda yake raye. To a bisa tsarin mu tun Ihsan na karama tana bina church kuma har ta tafi America ba ta daina ba, ba zan ce Ihsan Kirista ba ce tun da kuwa baban ta ya dage ta yi Addininku, kuma nima na ga tana so sosai, don haka ba ruwana da wannan.
To yanzu da ta dawo ma lallai ne duk Lahadi kabar ta ta je chochi ta ji wa’azi, ba zan ce kada ta yi sallar ku ba, wannan bai shafe ni ba, amma chochi dole ne ta je duk ranar Sunday.
Abu na biyu kuma shi ne na san ku Hausawa ba ku dauki mace da wata daraja ba, da kun yi ‘yan shekaru da ita shi kenan ta gama amfani, sai a auro wata a wulakanta ta, to Ihsan ita kadai ce da mu, ba mu da wani kwai a duniya sai ita, kenan ba za mu zuba ido mu bari a wulakanta ta ba a ko’ina, dole mu kula da farin cikin ta, don sai tana farin ciki ne mu ma za mu kasance cikin dawwamammen farin ciki da kwanciyar hankali.
Don haka in har kana son ci gaba da zama da Ihsan sai ka rubuta min a rubuce ka yi alkawari tsakaninka da Allahn ka daya cewa ba za ka kara auren wata mace bayan ita ba, ban hana ka harka da mata ba don na san matashi kamar ka ga sura uwa-uba naira, ba za ka lamunci rayuwa da mace guda ba.
Sharadi na karshe shi ne ban yarda ka hana Ihsan yin duk abin da take so ba, don tana son ka, tunda mu ma ba ma hana ta yin son ranta, idan har ka amince yanzu rubuta min in kira ta ku tafi. Ganin baban ta bai zama lallai ba, don bai isa komai ba.�
Al’ameen na zaune tamkar sassakakken gunki yana sauraron yadda ake tsara mai rayuwar kafirci ziryan a gidan auren shi. Tab, ba zai taba amincewa ba, don bai tashi ya ga ana hakan a gidansu ba, bai ga inda Daddy bai isa komai ba a gidansu, au shi ne shi ma za a nuna mai bai isa komen ba don kawai ya ce yana son ‘yar su?
Niyyar shi da kawai ya mike ya tafi ya kyale ta sai sun neme shi don kan su, sai kuma ya yi tunanin ai kunyar marar kunya asara ce.
Ya ce, “Am, Ma’ma, bana nufin izgili, raini ko kaskanci ga maganarku, illa ina son in miki bayanin da maybe, ita Ihsan ba ta yi miki ba.
Da ni da Ihsan, duk mun hadu a Jami’ar Miami ne ko kuma na hadu da Ihsan na karuwancin ta ne ko ko in ce, dukkanin mu watsewar rayuwar turai ta hada mu, ba wai cikin mutunci na aure ta ba a hannun iyayenta da za’a kafa min wasu sharudda marassa madafa bayan auren da muka yi ba da sanin ku ba ko wasu specific hujjoji, da abin mu ku ka gan mu.
Zan iya cewa ma na taimaki Ihsan ne daga gurbatacciyar rayuwar da ta jefa kanta a Florida, ashe in ba a gode min ba, ba za a wulakanta ni ba, a kan me yanzu don mun dawo cikin ku za a nunan iko da matar da na biya sadaki, a gaban shaidu?
Maganar zuwa church ma kwata-kwata ban amince ba, yaya tana sallah za a ce min ta je chochi yin wa’azi, sai dai in itama Ihsan Kiristar ce short and simple, amma ba a hada Addinin mu da kowanne addini sai dai in completely ta koma addinin ki ne?
Sai maganar aure. Ni dai Aminu Bello Makarfi, Musulmi ne gaba da baya, Addinin mu ya ba mu damar auren mata daidai har hudu in har muna da hali za kuma mu iya adalci a tsakanin su, domin kare kan mu daga dattin zina.
Don haka ba zan iya wannan alkawarin ba, idan na yi niyyar in kara aure zan yi.
Na ji kina cewa wai ina da chance na neman mata a waje alhalin ina da aure, to a Addininmu babu wannan damar, ko na Kiristan ba san inda ya baku wannan damar ba. Na karanta bible din ku ciki da bai din sa ban ji wannan nassin ba, (adultery)?
Wancan ma da muka yi a turai mun tuba, duk rudin kuruciya ne da rudin shaitan, amma a yanzu dube ni am a perfect gentleman (cikakken mutum ne) na wuce stage na wannan shedanar.
Maganar in bar Ihsan ta yi son ran ta? Like how? (Ta yaya?) Ban gane ba! Kada ki manta ina auren Ihsan ne fa ba fa ita ke aurena ba, don haka tilas in ta yi ba daidai ba in gyara mata. Mu a Musulince namiji ke ruling matar shi ba wai matar ke ruling din shi ba.�
Ya yi shiru idon sa ya kada ya yi jazur alamun bacin rai. Ta ce, “To who ‘re you telling all these rubbish? (Wa ka ke gayawa wannan maganar banzar?).�
Cikin bacin rai ya ce, “Am not talking rubbish, I only told you the fact (Ba maganar banza nake ba, gaskiya kawai na gaya miki).�
Ta ce, ‘Sai ka sake ta kuwa, yanzun nan kafin ka bar falon nan, ana aure dole ne?�
Ya yi murmushin takaici ya ce,
“Bana jin kaina sai ‘yar ki, idan na sake ta sai kin gwammace mutuwar ta da rayuwar ta.�
Ta ce, ‘Then divorce her and see (ka sake ta ka gani), me zai same ta?�
Ya ce, a yayin da yake mikewa tsaye,
“The worst thing you‘ve never imagine.� Wato abin da ba ta taba tsamamni ba. Ita ma ta mike ta ce, “Tun da na ce ka sake ta ta ruwan sanyi ka ki, to ka je, amma Ihsan ba za ta gidan ka ba.�
Har ya kai bakin kofa sai ya juyo,
“Kada ki kara cewa in sake ta, ba zan taba sakin mace ba a rayuwata. Ba don komai ba sai don daraja da girmanta da nake gani da tausayinta, amma ba wai don son ‘yarki ba.
Da wannan nake cewa, in za ku iya ci gaba da ba ni auren Ihsan, idan na dawo daga tafiyar da zan yi a gobe zan zo in tafi da ita, in kuma kuna ganin akwai cutarwa ko takura a gare ta, duk ya rage na ku, sai in ce da ku, Salam!�
Sai ya russuna mata da hannuwan shi biyu tamkar wani Ba’indiye, alamar girmamawa kenan da ake yi wa iyaye a Miami, ya juya ya yi ficewarsa.
How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book one
*@Takori*
Page7ï¸âƒ£
Tafe yake a mota zuciyarsa na faman tafasa da kuna, tunda yake ba a taba humiliating (Cin mutuncin) shi irin yau ba, ba a taba yi masa wulakanci irin na yau ba. Don haka maimakon sautin Khusairi kira’ar Mahmood Khaleel yake bi cikin Suratul Ma’idah. A ran shi kamar ya yi zagi, sai dai dadin kira’ar da yake sauraro na sanyaya masa zuciya, ya ce,
‘Ihsan din me har da za a daga wa mutum hankali kan auren ta? Ita nan har wata mace ce da za a tada hakarkari a dagawa mutum murya a kan ta mts! In da sun san a yanzu babu wani gurbi da yake jin zai iya jogana son wata diya mace a zuciyarsa, bayan HA-LI-MAH, da ba su yi masa wannan jan ran ba, da ba su yi masa wannan wulakancin ba, in ba don ma Hajiya da ta hankado shi ba zai zo ne? Ya yi kwafa shi daya ya ce,
“Allah za su sha mamaki.�
Daga nan harkokin sa ya wuce, ya duba ginunnukan shi ya ga yadda ake aiki tukuru cikin fasaha da kwarewa irin ta Malam Bature, abin ya burge sa, haka tsakanin shi da hukumar lafiya komai na tafiya daidai, ya biya ‘Sahad Stores� da ke kan titin Benghazi Street ya yi wa Halimarshi sayayya masu firgitarwa duk na kayan ciye-ciye da lashe-lashe, mayukan gyaran kai da shampoos, dryer zuwa sauran tarkacen kayan gyaran gashi, haka ya ciko mata kit da kayan shafa duk set din neutrogena collection kamar wani mai hada lefe, ya san da kyar ne za ta yi amfani da su, ba burinsa kenan ba, illa ya ga dan murmushin ta mai gigita shi.
Haka ya koma boutikue na kayan kanti ya saya mata riguna da skirt zuwa dogayen riguna (Designers) masu karshen tsadar. Gaban sa baya ko dar na za a iya tambayarta ina ta samu? Idanuwan shi sun makance cikin wata irin soyayya mai gigitarwa, tunanin shi ya gushe, ita kawai yake gani a gabansa.
Ya riga ya shirya tunkarar kowa da maganarta, auren ta zai yi cikin watannan da son ran wani ko babu he did not care (Bai dame shi ba).
A dai kamfanin ta kicin ya same ta tana yankan danyar kubewa da Hajiya ta ce a yi wa Daddy da busasshen kifi da daddare, ‘yar zulunbuwar rigarta ta sha wanki da omon Aerial ta yi fes. Nadadden gashin kanta a cure wuri guda kamar gammo as usual (kamar kullum), duk da wahala da ta tsotse ta ta kuma kwalmade ta still ita kyakkyawa ce kullum kuma kamar ana kara mata kyau ne.
Ya hade hannuwan shi bisa kirjin shi bayan ya aje ledojin da ke hannunsa bisa marbles, duk wani acting din ta cikin yauki na halitta sha’awa yake ba shi, haka duk wani motsin ta burge shi yake, ya ce, “Ha-li-mah.� Da muryar da ke dauke da sakonni da dama.
Ba shakka gangar jiki da ruhin ta duka sun amshi sakon da ke tattare cikin muryar Al’ameen, sai ta yi murmushin da yake son gani, ba kuma tare da ta dube shi ba ta ce,
“Ni fa na gaya ma Al’ameen ba sunana Halimah ba, ka daina ce min Halimah.�
Ta kasan idanun ta ta dube shi don ita yanzun wata masifar kunyar shi take ji, tun maganr su ta daren jiya. Aminu ya kasa magana, tuni ya bushe a tsaye, ji yake kamar ya jawo ta ya rungume, amma ya yaki zuciyarsa da aikata hakan. Tunda yake, bai taba jin wanda ya furta kalmomin nan uku sak, Al-A-Min, ya yi mai dadi ya kuma iya fadi tamkar ita ba.
Sai ya zari mayafin daya cikin dogayen rigunan da ya saya mata ya karasa ya nannada mata aka, still ba ta dube shi ba ta ce, ‘Shukran.� Wato na gode.
Ya ce, ‘Yunwa nake ji sosai, tun safe ban ci komai ba, na fito bikon matata ga shi ba su ba ni ba, ni kuma don haushi na ki cin abincin su, don Allah ko kin yi ragowar na rana ki sammun?�
Ba ta san san da ta tuntsire da dariya ba, yadda ya karya murya ya rausayar da kai sai ya tuna mata da Patch Adams, jarumin fim din America na fim din (Brilliant) sai ta girgiza kai ta ce,
“Ko ka san Patch Adams?�
Ya ce, “Humour is the best medicine, shin ke kin amince cewa humor is the best medicine? (Ban dariya shi ne babban maganina kowacce cuta).�
Suka koma tattaunawa a kan fim din inda ya lura ita dai tana son fim din sosai. Ta ce,
“Me yasa suka hana ka matarka?�
Ya zuba uban tagumi abin dariya hannuwan sa a kan freezer ya ce,
“Oho! Masu, Kiristoci ne sai ana hakuri.�
Da haka ta ja bakinta ta tsuke, ta jawo babban food flask na Daddy ne da ta je daukowa domin wankewa ta taras ko budawa ba a yi ba, niyyar ta in anjima ta ci idan Hajiya ba ta nema ba, a nutse ta dauki babban plate ta juye abin da ke ciki, farfesun kayan cikin rago ne irin mai sa yawun mutum tsinkewar nan tun bai sa a bakinsa ba, sai farar macaroni a babban flask din, ta bude wani fadi ka mutu, wani abincin Larabawa ne shartoum da ake yi da naman kaza, kwai da waken gongoni, ga kuma farfesun kifi ragon ruwa fari sol da shi, ta hada duk a katon tray ta dora mai akan freezer inda yake jingine a jiki ta ce,
“Ko za ka iya cin wannan Al’ameen kafin in kammala tuwon dare?�
Ya dube ta cikin ido da idanun shi masu kama da an diga masu silver saboda sheki, ta kawar da kanta da sauri domin ba ta iya jure kallon nan nasa ta ce, “Ka ci kafin in kammala wannan, Al’ameen ka fiya kallon mutum Allah.�
Ya yi murmushi mai fidda sauti, ya dubi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 38