tafi bai bar zancenta ba, bai daina tuna ta ba a kowanne dakika, harshensa bai bar ambaton sunan ta ba.
Abu kadan sai ya ce, “Allah Sarki Baby na ana can, ko me ake yi yanzun?�
Antyn sai ta yi dariya ta ce, “Ai sai ka bar naka karatun ka bi ta can ku yi tare.�
Sai ya ce,
“Bari in samu hutu ki gani, Aunty nima Riyadh zan tafi.�
Ta kamo hannun ta suka zauna cikin kujera ta ce, ‘Saratu wai ke ba kya girma ne? Faisal da gaske yake jarrabawa yake yi, kuma ba a barin jarrabawa a jami’a a fito. Ke in kina taki jarrabawar kin taba tahowa baki gama ba? Idan kin kwantar da hankalin ki da kafafun shi za ki gan shi da zarar kun koma, don ba ki san yadda ya damu da ke ba ne.�
Sai tayi murmushin da ba ta shirya ba. Antin ta kara da cewa “‘Taso ma ki ga wani abu.� Tana lalube cikin shafin yahoo-mail wani katon zanen zuciya kalar shi ja mai haske ya bayyana a jikin screen din kwamfutar, a kasan ta wani boyayyen rubutu ne da aka dunkule sa cikin tsari mai kyau da daukar hakali,
Saratu-Intisa!
Drop my picture into your mind Sis, allow it to dissolve in consciousness, and it will spread a healing balm over your entire soul. This is one of the simplest processes to feel me beside you.
Read hard and make us proud.
Faisal Bello Makarfi.
Ba ta san sanda ta yi dariya ba kamar ba ita ce mai kuka wiwi yanzun ba. “Shin Mamana ta yaya zan sa hoton Ya Faisal a raina?�
“Shi ne sai ki dauko fuskar shi a zuciyarki, ki sama ranki cewa wannan Faisal ne ku ke tare, yana kallon ki yana miki hira, yana kuma yi miki wannan kyakkyawan murmushin nan nasa. In kin yi hakan ba za ki ji haushi ba don ba ki gan shi a wannan shekarar ba.�
To Saratu ta koma makaranta cike da farin cikin kaunar da Mamar ta da ya Faisal ke mata.
Ba karamin bakin ciki ta taras a makaranta ba da ta ga ta shafe sati daya, biyu har uku su Hunainah ba su dawo hutu ba. A sati na hudu ne ta kasa daurewa ta je ta tambayi malamin da ke kula da shige da ficen hutun dalibai da suke kira Sayyid Ridhwan game da su. Ya dade yana bincike kafin ya samo mata detail din su, cewa ya yi da ita dama aikin jakadanci mahaifin su yake yi, inda kuma duk ya tashi nan suke komawa da karatu, yanzu kuma an yi posting dinsu kasar Korea.
Ta samu wani kututturen icce ta zauna ta yi kukan ta mai isar ta; kukan sabo da kewa, kukan rashin amini, (to lose a friend is the greatest loss of all losses). Sai ta ji rayuwar makarantar ya zamo mata wani irin salam, musamman in ta tuna hirarraki da ban dariya irin na Hunainah masu cike da hikima a ciki, da kuma tonon fada irin na Hidaya da a kullum ke sanya su zama busy wato dai ba za su zauna shiru ba.
Ta yi kuka har idanun ta suka shiga zafi da radadi. Daga baya ta rugnumi kaddara ta sanya wa ranta salama, don malamin Islamiyya ya sha gaya masu imanin mutum ba ya cika har sai ya yarda da kaddara mai dadi ce ko mara dadi?
Kenan Allah ya kaddara iyakacin rayuwar da za ta yi da su kenan, shi yasa har ya nufe ta da zuwa gidansu, ta watsar da komai ta rungumi karatun ta kamar da, barin ma da ta yi sabuwar kawa Raadhah, mutuniyar Jeruslaam, tana fatan wata rana Allah ya kara hada ta da su ko da a mafarki ne.
Sun ci gaba da karatu sosai Saratu Bello na kara yin fice. A wannan shekarar sau biyu ta fita debate a kan lissafi har Abudhabee (Dubai), dayar a Oman dukkansu UAE ne wato United Arab Emirate, ana kuma nunawa a tauraron dan-adam, ta kuma daukowa makarantar su kofin zinare, wannan ya kara bata damar zama ‘yar lelen malamai da hukumar makarantar gaba daya. Kingston College, na hangen bata shugabar dalibai in ta iso ajin karhse, wai ‘yar Africa! Africar ma kasar da suka fi gani da kaskanci, Nigeria ce?
Wata ranar Litinin ta fito daga library tare da wata yarinya Rabikha, aka ce da ita principal na kiranta. Ta zo shiga kenan suka ci karo da Khalil, tsoro ya kama su, don wannan shi ne karo na farko da wani kira makamancin wannan ya ratsa da su a tare. Tsoron ta Allah, tsoron ta kada ta yi laifin da zai sosa ran Daddy a rayuwar ta. To amma me?
Ta dade da sanin wani kamshi da ba ta jin shi a jikin kowa a duniya sai mutum daya, ba ta jin shi jikin kowa in ba� Ji ta yi an sure ta an yi sama da ita ana juyi da ita tamkar a hadiye ta, sai kuma dariyar mamar ta, ta dubi mai rike da itan, Ya Faisal ne.
Tuni ta saki ihu, ta rukunkume shi tamkar ta sume don dadi ba ta ko ta Mamar ta. Kaunar Faisal da Intisar wannan cikin jininsu ne, kuma daga Indallahi take. A duk san da suke tare da juna, mantawa suke da kowa a duniyar sai junan su.
Da Principle ta ga ofishin ta ya kacame da hayaniyar wannan family masu matukar kaunar junan su sai ta fita ta bar masu ofishin. An yi hira an yi dariya, amma baby magana daya, biyu za ta ce ina Daddy na? Sai Faisal ya ce,
“Ba ki san Daddy ya tsaya takarar President ba?� Ba su tafi ba sai yamma lis. Washe gari suka zo suka yi masu sallama suka tafi. Dama sun zo aikin Umrah ne.
To haka karatun ya kasance masu, duk shekara suna zuwa gida su yi wata guda suma kuma mutanen gidan na zuwa masu a kai akai, musamman Faisal, ka’ida ne duk karshen semester Daddy ya biya mai kujerar dubo Intisar.
Wannan wani alkawari ne da ya yi wa rayuwar shi cewa ko Daddyn ba zai biya ba, zai san duk yadda ya yi ya kai wa Intisar ziyara ko da hakan na nufin ya ciyo bashi ne.
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah, yau ga Saratu Bello ta kammala ajinta biyar na secondary a shekarun ta goma sha biyar a duniya. Shi kuma Khalil ya kammala, don ma sun maida shi baya ne saboda faduwa darasin lissafi da ya yi, amma da tun shekarar baya ya gama, daga wannan hutun shi ba zai koma ba, ita ce dai za ta koma ta yi final year din ta.
An danka mata dankwalin shugabar dalibai. Wayyo! Ashe daga wannan hutun, mafarkai da burirrika ba za su taba zama reality ba.
Saratu ta dawo hutu cike da farin cikin abu biyu, first of all, alkawarin da ta yi wa Daddy na kwato (1st Position) din ta daga hannun Amra Rushd abokiyar takarar ta mutuniyar Katar, da ta kwace mata a zangon baya ta cika shi, ta kwato (1st position) din ta as usual. Sai na biyu za ta ga farin cikin Mamar ta a fili, watakila ma har ta goya ta da zani duk da girman ta kuwa. A wurin Mamar har abada ita BABY ce, ta kan ce, har sai ranar da ta samu kani.
Haka take yi mata duk san da ta yi na daya, wato ta goyata tayi ta zagaye daki da ita, in kuwa na biyu ne ta shiga korafi kenan.
“Saratu kina wasa, Saratu alkawarin mu da ke kenan? Saratu where is your delegence (Ina kwazon ki), I dare you!�
To yau dai duk ba ko daya, ga na dayan ta ta dauko, saura tukuicin Anty da Daddy.
Ashe labarin bakin ciki da tashin hakali ke nan yana tsimayen su su fito daga jirgi, wanda daga jin sa Saratu sulalewa ta yi nan take a kasa sumammiya.
*****
Cyril Stober ne tare da sabuwar Newscaster Hawwawu Gebi, ke karanto kanun labarun yau daga gidan talbijin na kasa (NTA Abuja), inda ya ce,
“An kama wadanda suka shiryawa kasa juyin mulki a ranar 5/5 wanda Benga Delsu da Bello Makarfi ke jagoranta. A yayin da aka shiga hasko fuskokin su daya bayan daya, kafafuwan su da hannaye duka daure cikin ankwa abin babu kyawun gani.
Suka kafawa Daddyn su ido kuriiii, abin tausayi tamkar sa zuko shi daga akwatin talbijin din. Cikin kwanaki biyu kacal ya rame, ya yi baki, ga wata kasumba ta tashin hankali da ta baibaye fuskar shi mai zati da kamala, kan shi a sunkuye, tun suna kuka kasa-kasa har suka rikice gaba daya da kakkarfa, Faisal ne ya mike ya finciko wayar T.B din ya hada ta da garu.
“Allah Daddy ba zai yi haka ba, wannan sharri ne, sharrin..�
Ya ma kasa karasawa saboda takaici da kunar zuci. Duk gidan ya koma tamkar gidan mutuwa, Inteesar tun zuwan ta da ta riski labarin, ta fadi ta sume, aka samu ta farfado har lokacin kudundune take cikin bargo tana rawar dari, zazzabi da masassara suka rufe ta, hakoranta sai karo suke da juna kawai ji ka ke kaf-kaf-kaf.
A ranar Najib da Bello suka iso, washe gari sai ga Nasir da Yasir su ma a gigice, Nasir mai raguwar zuciya nan falon Hajiya ya zube yana kuka riris shi da kananan kannen shi, ita kanta Anti ta fita hayyacin ta ba kadan ba, bata ko iya rarrashin su.
Najib ya ce,
‘Me zai sa Daddy ya sanya kan shi cikin wannan bala’i?�
Shi ko Faisal rantsewa ya yi da Allah ya tabbata Daddy ba zai taba aikata abinda ake zarginsa da shi ba, saboda president aminin Daddy ne na kut da kut tun suna NDA a Jos suke tare har girman su har tsufan su ba a taba jin kan su ba balle a same su da wani sabanin ra’ayi, ya ya za a ce an hada baki da shi a kashe shi? Sun rasa ya za su yi? Sun rasa wa za su kai wa kukan su a yanzu ya dube su, yadda kasa take cike da su Daddy a wannan lokacin.
Sai Saratu ta share hawaye ta ce,
“Ya Najib, ni ina ganin mu taru mu yi ta addu’a da kan mu kawai, in Daddy ba laifn shi sai ka ga sun sako shi da kansu a lokacin da ba mu tsammana ba, amma duk inda za ku je a halin yanzun ba wanda zai saurare ku.�
Sai a yau Hajiya Nafi ta taba daga ido ta dubi Intisar a rayuwar ta, duba na mutum dan adam, ta ce, “Yarinya karama ta fi ku tunani, amma kun tsaya kuna ta koke-koken banza amfanin me ke gare shi?�
Washegari Najib ya nemo bisa din mutum biyar da shi da Faisal, Yasir da Hajiya sai Anti, suka dunguma kasa mai tsarki domin yin dawafi na musamman kan Allah ya fiddo mijin su/mahaifinsu cikin ruwan sanyi, suna addu’a fuskokin su jike da hawaye, tuni an manta da wani kishi, to ina wanda ake yin kishin domin shi?
Gidan farin ciki gidan Brigadier Bello Makarfi, komawa ya yi tamkar gidan makoki, dukkan harkoki da walwalar su sun karkatse. A satin Saratu da Nasir suka kamo hanyar kauyen Makarfi. Kallon fuskokin su kawai Baffa Sani ya yi ya tabbatar babu lafiya haka goggo Jimmai.
Nasir ba ya ko iya magana sai Saratu ce ta yi mai bayanin halin da ake ciki hawaye na bulbular mata a guje. Malam ya shiga rarrashin su yana tunatar da su duk wani soja haka ya gada, shiga hadarurruka ba yanzu Babansu ya fara ba, ya ma fi na wannan a baya lokacin da rikicin sojojin Amurka da Saddam Hussaini ya ritsa da shi a Baghdaza, da lokacin da aka kashe Major-General Aguiyi Ironsy ya kuma fito sumul kalau.
Tun a ranar ya tara malamai bila adadin ya raba masu abin sadaka suka dukufa rokon Allah. Duk wani shahararren malami da ya kwana ya tashi a garin Makarfi da wajen ta Malam Sani ya kai abin sadaka a taya su rokon Allah ya fiddo Bello, gudan jinin shi kuma bango abin jinginar su.
Nasir ya bude account din shi ya karowa Baffa kudi masu yawa.
Watan su Hajiya guda a Saudiyyah kafin su dawo. Gidan ya kuma komawa tamkar gidan mutuwa harkokin su suka kara katsewa, na makaranta sun kasa komawa, masu aiki su kasa komawa bakin aikin su, kowa na ji da yadda ya ke ji a zuciyarsa. Najib ya yi trying wayar Aminu, kwata-kwata ya daina amfani da layin, ya aika mai ta e-mail babu amsa. Da yamma ya shiga dakin Hajiya sai ya tarar da ita tafukan ta cikin fuska tana ta razgar kuka. A sanyaye ya zauna ya sunkuyar da kai ya ce.
‘Hajiya duk fa abin da ya yi zafi maganin sa Allah ne.�
Hajiya Nafi ta ce, “Na san da haka Najibullahi. Tunanin Al’ameen ke damuna, baya ko tunawa da mu balle halin da muke ciki. Mun yi da za shi Hull Unibersity, cikin ajiyana na banki na tattara na tura Ali dan kanin mahaifina ya binciko min Aminu a England, address din da ya bar mini ka san me ye? An ce kwata-kwata babu mai irin sunan shi a cikin shekarun da muka ambata da ya zo daga Nigeria.
Na rasa inda zan sa kaina in ji sanyi. Idan na rasa Aminu na rasa ubansa ina zan sa kaina?� Sai ta kara tsanannta kukanta.
Najib ya lankwashe kai abin tausayi ya ce, “Amma dai Hajiya kin san dai cikin kowanne hali Ya Aminu zai iya kula da kansa a ko’ina.
A ganina bai dace kisa damuwar inda yake a ranki ba har ya zo ya dame ki, hakan yana iya zamo miki illa, kuma a cikin wannan halin da muke ciki na kewar mahaifin mu ke ma mu rasa farin cikin ki akan ya Aminu shi kadai ransa? Tunda dai kin san ko ba dade ko ba jima zai dawo ne?�
Ta ce, “Ya kuwa bazan damu da inda Al’ameen yake ba, alhalin duk cikin ku babu mai kauna ta tamkar shi? Babu mai gudun bacin raina tamkar shi? Babu mai son abin da nake so tamkar shi? Ba mai damuwa da bakin cikina tamkar shi? Ya ya kuwa ba zan damu da inda yake ba?� Najib dai ya yi ta lallashin ta har ya samu ta yi shiru.
Washe gari ya zauna ya zanawa Aminu duk halin da suke ciki ta cikin yanar gizo internet yana rokon shi ya zo su taru su san hanyar da za su kubutar da mahaifinsu da ya tabbatar da ba ya da laifi. Ya tunasar da Aminu yanzu ne fa ya dace su nunawa ubansu kaunar da ya wanzar da rayuwar shi a nuna masu. Ya tabbata ya kammala koma wane irin karatu yake yi cikin wadannan dumbin shekaru amsu yawa da suka gabata. To amma me?
Daga Ameenu no reply har tsayin sati guda, wannan ya kara tunzura ‘yan uwan. Sai a kwana na takwas ne ya cillo wani matsiyacin rubutu don a ganin sa ai abin da ya jiyewa Daddyn kenan tun farko da ya yi ritaya amma shi bai jiyewa kansa ba.
Rubutun Al’ameen Bello, ya nuna bai damu ba, bai kuma da ranar barin inda yake, domin America, ta zama wani ginshiki na farin ciki da kwanciyar hankali a gare sa, ta yadda har bai jin wani abu da ya shafi gidansu zai sa ya baro ta. A takaice dai ga abinda Ameenu ya rubutowa dan uwansa Najib.
America teaches the cultivation of peace of mind to me, not as an escape from life into protected quiescence, but as a power center of which comes driving energy for constructing personal and social living. One is responsible for the outcome of what would be sealed.
Al’ameen Bello
How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: _____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two
*@Takori*
Page4ï¸âƒ£
Najib ya fashe da kuka, ‘Faisal, anya wannan Yayan mu ne da na sani mai so da kaunar Daddy?�
Shi ko Al’ameen ba su san a halin bakin cikin abin da ya ke tunanin mahaifin su ya aikata ne ya furta wadannan kalaman ba, a ganinsa me Daddy ya rasa a rayuwa da zai tsunduma kan shi cikin irin wannan masifa in ban da rashin godiyar Allah? Har nawa duniyar take da zai bari neman mulkin duniya ya rinjayi imanin shi?
Kudi dai na gwamnati albarkacin aikin soja bai san wane iri yake so kuma ya yi ba. Ya manta cewa, “Kalmomi da alkawarirrikan da aka yi su cikin fushi, kamar cin wuta suke, ba za ka taba iya maida barnar su ba.�
Daga Faisal har Najib sun ce a kyale Ya Aminu ya yi yadda yake so. Allah zai fidda Daddy ne ba sai da taimakon sa ba.
Ranar Asabar Baffa na Makarfi ya zo da malamai kimanin guda goma aka bude masu nan sashen baki, sati guda suka share suna saukar Alkur’ani mai tsarki, an yanka raguna har ba iyaka an yi sadaka haka sauran abubuwan sadaka iri-iri iyalin Brigadier ba mai jin kyanshin bada ko mene ne.
Sai da Aunty Saratu ta zamo babu ko sisi a account din ta ta hada da saida bungles din ta na danyar gold. Haka samarin nan na Brigadier ba sa barcin kirki kowannensu kamar bai taba mallakar kwandalar kansa ba, duk sun jeme abin gwanin ban tausayi.
Hakika Bello Makarfi ya gina iyalin shi a bisa tubala na so da shakuwa da shi, ta yadda rashin sa ya zamo masu tamkar rasa rayuwar ne dungurungum. Mutum ne da ya iya zaman duniya kuma mutum mai nuna wa ‘ya’yan shi da matan shi kauna da kobo, lafiya da karfin shi.
Ya tsaya tsayin daka domin iganta rayuwar su ta yadda har sun fi kaunar shi a kan-kan su, dama duk wani abu da suka mallaka a duniya.
Malamai iri-iri na karya da na gaskiya haka suke zuwa suna cin kudin su da sunan wai kafin sati an sako shi, amma shiru ka ke ji wai malam ya ci shirwa, sai ma sabon bakin mummunan labarin an dauke su daga Kiri-kiri Prison zuwa South Africa.
Intisar, dama gwana ce wurin kai wa Sarki Allah kukanta a komai, to balle wannan matsala da ta shafi rabin ranta ‘Daddy Makarfi�. Yarinyar nan ‘Halwa� ta shiga, idan ka ganta a wancan lokacin sai ka amince ta fi kowa damuwa da Daddynsu.
Jar fatarta ta yi duhu ainun, idanun ta sun fada ciki, sai kwayar idanuwan nan da karan hancin kadai. Ba a zancen komawa makaranta, aljihun kowa ya masifar girgiza, hatta Hajiya Nafi ba karamin faduwa ta yi ba a wannan shekarar, sabida cin kudin kawai ake ba’a inbesting din su, sai da ta kai ta kawo abinci wannan ya soma karanci a gidan Makarfi.
Wani abin mamaki duk wasu abokan arzuka na Brigadier da abokan aiki wadanda cikinsu babu wanda ya taka matsayin da yake kai a soja ba tare da taimakon Makarfin ba, babu wanda ya yi tunanin ya taimaka masu ko da da kwayar shinkafa ne sai jelen jaje da ake ta yi masu ana Allah ya kiyaye gaba amma naira daya wannan babu wanda ya dauka ya ba su da sunan wai yana amintaka da Daddyn su. Ganin haka Faisal ya tara ‘yan uwansa kaf a falo ya ce.
“To Assalamu Alaikum ‘yan uwa. Ku sani fa (La yukallifullahu nafsan illa wus’aha) Ma’ana: Allah baya dorawa wata rai abin da ya san ba za ta iya dauka ba. Saboda haka a abar komai a hannun Allah, mun yi addu’a daidai karfi daidai iko da gwargwado, we’be to wait for the outcome, wato mu jira ijaba a barwa Allah komai, mu koma makaranta masu aiki su koma bakin ayyukan su.
A yau ku duba ku gani yadda aminan Daddy suka watsar da tallafin mu da shiga al’amuran mu bayan cikin su babu wanda ya taka matakin da yake kai ba tare da taimakon Daddyn mu ba. Wannan bai ishe mu ishara ba?
A yau in cewa akai Daddy ya fadi ya mutu, ba za su taimake mu da komai ba haka za su bar mu mu tagayyara, da kyar su ce
‘Allah ya jikan rai.�
Ashe kenan wannan karatun nan namu da ayyukan mu su ne madogarar mu sai kuma Allah gatan kowa? Karatun nan shi ne gatanmu, da shi za mu rufawa iyayenmu da kannin mu asiri. Ga shi kowannen mu ya yi asarar shekara guda wadda da tuni wasu cikinmu sun kammala har sun fara aiki. A gobe kowa ya koma inda ya fito, mu ci gaba da addu’a hakika ita addu’a ba ta faduwa kasa banza, kuma wanda ya fawwalawa Allah lamarinsa ba zai taba tabewa ba.�
To nasihar dan uwansu ta ratsa su dukkan su. Saratu kam sharban kuka kurum take kashirban. Hajiya ta ba kowannen su isassun kudi ya koma makaranta. Ka ji ‘ya’yan Hajiya, to Saratu da diyar ta Saratu fa?
A ranar baby kwana ta yi lallashin Mamar ta ta koma aiki ita ma, don Hajiya tuni ta koma harkokin ta, da yake ba ta son ganin bacin ran Saratun shi yasa kawai a wayewar garin Litinin ta shirya ta tafi. Allah Sarki! Wani ta taras a mazaunin ta, Insurance Company, ba su san wasa da aiki ba.
To su sai abun duniyar ya taru ya yi masu yawa. Ta dai aika da takardun neman aiki kamfanoni da bankuna da dama a nan cikin Abuja, to amma aiki a Abuja sai ga masu uwaye a gindin murhun. Ba abin da ya dame ta kamar yankewar karatun Saratu a shekarar ta ta karshe, dama ta kammala ne da da sauki sai ta nema mata public unibersity wato ta gwamnati, ta tafi.
Yadda Hajiya ta yi komai nata-ya-nata ta tabbatar ta nuna mata ranar NAIRA ne. Khalil din ta ya gama, to ita yanzun ina za ta nemo makudan kudaden da za ta maida Saratu Kingston College?
Sai ta hada dukkanin gwalgwalan ta na ado gaba daya ta tattara ta sa a kasuwa, an yi masu sayen daraja kuwa. Ta dade da amsar mota cibic hannun Daddy wadda take zuwa aiki a ciki, ita ma ta yi gwanjon ta wani makocin su ya saya a wulakance. Ranar Laraba suka biyo motar haya zuwa Makarfi abin da ba su taba yi ba a rayuwarsu, don direban gidan tuni ya kama gaban sa tunda ya ga an yi watanni har shida ba wanda ya tuna ya ba shi ko sisi, ba shi kadai ba duk ma’aikatan wajen sun gudu in ka dauke maigadi, shi ma tabbas don ba shi da wajen kwana ne in ya tafi watakila shi yasa ya zauna amma hatta ‘yan aikin Anti Saratu sun yi tafiyar su tuntuni, sai ko ma’aikatan cikin gida su Dela da ke bangaren Hajiya da yake ita tana biyan su amma na Anti Saratu ko wata ba a yi ba da kulle Daddyn suka kama gabansu.
Wannan bai damu Hajiya Saratu ba abinda ya dame ta ya dame ta.
Sun iso Makarfi karfe uku da minti ashirin na rana lokacin Malam yana cikin gari, Goggo Jummai ta yi masu kyakkyawar tarba, bayan sun ci abinci sun yi kat, sannan Saratu da Saratu duka suka hada kai da gwiwa suka yi shiru. Goggo, ta ce,
“Ku yaran nan, da kuruciyar ku za ku sanyawa rayukan ku cututtukan zamani masu wuyar magani? Mu ma tsofai-tsofai da mu rashin Bello bai hana mana rayuwa mai kyau ba sai ku? NI na san Bello na sarai tun yana a tsumman goyon sa babu abinda zai sa ya aikata abin da ake tuhumar sa da shi. Kuma ko don albarkacin addu’ar da ake ta yi gaskiya za ta bayyana, ko ba dade ko ba jima.�
Aunty Saratu ta ja numfashi, Intissar kuwa kuri ta yi da jajeyn idanun ta kan tururuwan da ke ta yawo a kan malalen suminti, a ranta ko cewa take su babu abin da ya dame su, yanzu haka suna tare da Daddyn su, sabanin su
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 38