Share this page
abincin ya ce, “Yanzu duk ke ki ka sarrafa wannan Halimah, a ina ki ka san Shartoum?� Ta wani irin juyo ta dube shi a ranta ko cewa take, “har ni za a tambaya abincin Larabawa?� Ta ce, “Allah ka rage kallo, domin haramun ne.� Ya sake murmusawa a karo na biyu ya ce, “In banda Halima ba mutumin da ya ishe ni kallo.� Ta dan juya kadan ta ce, ‘Ah! Matarka fa?� Ya ce, ‘Ihsan sunanta.� Ta ce, “Ni ai ba sunan ta na ce ka gaya min ba, cewa na yi ita ma haka ka ke takura mata da kallo?� Ya kai lomar farko na macaroni cikin bakinsa, dandanon girkin da komai ya yi masa dadi har kunnuwansa sai da suka motsa ya ce, “To wai ke, ina gamin ki da matata ne, are u jealous?� Ma’ana kina kishi? Ta juye kubewar da ta kammala yankawa cikin tafasasshen ruwan miya mai rai da motsi da ta hada ta ce, “Wa, ni?� Ya ce, “Yes, ke Halimah.� “A kan me ka ce haka?� “A kan na ga kin damu da ita, ita ba ta ma san ki ba.� Ta zobara baki gaba yadda takema Faisal in ya ba ta haushi ta ce, “Na yi zaton sai ana son mutum ake kishin sa?� Al’ameen ko ya nuna damuwa da shaguben ta, sai zuba abincin shi yake cikin tumbinsa santin dadi na dibar kununwansa, ya ce, “Oho! Haka nima na ji?� Su duka ba su san sanda suka sa dariya ba. Ya ce, ‘Zan tafi Niger yanzun nan sai wurin jibi zan dawo, na zo miki sallama ne, ga kaya ki yi amfani da su kafin in dawo in gayawa mutanen gidan nan bukata ta ta auren ki halimah. Ina fata ko me za a yi miki, Halima za ki kasance a baya na?� Ya kafe ta da ido, ta yi shiru ba tare da ta juyo ba, amma ta yi sanyi da juya miyar da take yi. Anya za ta iya aure ba da yardar iyayenta ba? Duk ko da yadda take jin Al’ameen a zuciyarta, ruhin ta da kasusuwa, bargo da gangar jikin ta gaba daya? Ba ta jin za ta iya zartar da wani al’amari ga rayuwar ta ba tare da sani ko amincewar wadannan iyayen nata biyu ba, ina! Balle aure dungurungum, tukunna ma shi Al’ameen waye ne? Bata da wani sani a kan shi, dabi’a, sana’a da uwa-uba asali. Ba ta san komai a kan shi ba, in ban da so makaho ne. Haka kawai fa rana daya suka ga juna, guguwar mahaukacin so ta fyade kowannensu, duk da bata jin ko barawo ne za ta fasa son shi da kaunar shi, amma aure? Sai ta kada hafizin harshenta ta ce, “Idan har Daddy ya amince ba?� Ya ce, “Idan kuma aka samu akasin haka?� Ta girgiza kai da sauri, ‘Nima ba zan amince ba!� Ji ya yi kirjin shi yayi wani irin bugawa da karfi! Ya hadiyi wani makalallen miyau da ya tokare a makoshin sa da kyar, ya zuki iska ya fesar cikin takaici ya ce, “Kenan you don’t love me Halimahhh?� (Ba ki so na Halima?). Ta ce, “Sam, ba haka ba ne Al’ameen…� Ya riko hannuwan ta duka biyu cikin zafin nama a zafafe ya ce, “To yaya ne?� Ta daga lumsassun abnormal idanunta ta dube shi, shi ma duban ta yake impatiently (A kagauce) ta ce cikin raunannar murya. ‘You said so many things to make me happy, and try your best to make things work out okey for me. If I could describe your kindness, I would be describing an angel. If I should describe your love, I would be describing my whole heart. U are a gift Al’Ameen, from Glorious God to me, you are an angel! How could I say I don’t luv U (Ta yaya zan ce ba na son ka?) Illa iyaka ana son duk abinda dan adam zai gabatar, ya yi kokari kada ya saurari ra’ayin shi, ya saurari ra’ayin na gaba da shi. Ka ga kaman shi Daddy ya girma har ya kusa tsufa, ya yi edperiencing wasu al’amura na rayuwa, musamman auren da aka gina a kan soyayya, wanda mu da muke kasa da shi ba mu yi ba.� Al’ameen duk da cewa maganar ta ta farko ta yi mai dadi, ta kuma wanke shakkun da ke zuciyarsa, amma ya kasa fahimtar ko me take nufi da wannan murdaddiyar magana? Bai san san da ya ce, ‘Shin me ye tsakanin ki da Daddyn gidan nan?� Anan ne ta fuskanci shirmen da take shirin tafkawa, da sauri ta ce “Babu, sam babu, illa a dan zamana tare da su na fahimci cewa shi mutum ne irin sauran mazan jiya masu kaifin tunani da hangen nesa.� Ya ce, “To magananniya, kina ganin wrong choice (Zaben tumun dare) za ki yi wa rayuwarki kenan a hada rayuwa da Aminu?� Ta ce, “Kash! Ana baka kana kin amsa, na riga na amince da Al’ameen-Al’ameen ne100%, illa just what my sociology told me, ka yi hakuri a bar maganar sai ka dawo din?� To Al’ameen ya tafi Niamey da kwarin gwiwa da dukkan goyon baya na zuciyarsa kan amincewa da yarinyar da ko sunan ta bai sani ba, dari bisa dari zuciyarsa ta amince da ita. Ya lura bayan nutsuwa, yarinyar mai hankali ce da sanin abinda take yi uwa-uba kyakkyawan tunani da hangen nesa she leave no stone unturned tamkar ba karamar yarinya da ba ta kai shekaru ashirin ba. Hakan nan akwai wannan kalmar ‘class� a tare da ita ba daya take da sauran matan da ya sani ba wannan daban ce, ta san mutuncin kanta, ta san baiwar da Allah ya yi mata na ‘ya mace mai darajjah. Duk rudewar da mata ke yi a kan shi a Miami, ita ba ta yi surprised! (Don Allah mata mu dinga jan mutuncin mu a komai). Ya yi duk abin da zai yi a Yamai cikin kwanaki uku rak ya turo kayan shi ta jirgin ruwa. Ranar da zai dawo ya shiga kasuwa a Yamai don bude ido kawai, ba abinda ya dauki hankalin shi irin kayayyakin matan su da ya tabbatar za su yi kyau da Halimar shi tun da itama tana yanayi da su, ya ciko akwatuna masu kyau da kayan matan Zindar, Niamey, Maradi da Damagaram da niyyar in sun yi aure da Halimar shi zai bata ta dinga yi mai kwalliya yana ganin ta kamar ‘yanmatan Niger. Hatta necklaces da duwarwatsun adon su ya saya mata, su wannan da niyyar su zai ba ta a matsayin tsaraba da zarar ya koma. Ya tsaya a wani kantin turare ya saya wa Hajiyar shi saitin Givenchy (for women) da take amfani. A ranar ya sauka a Abuja. Masu aikin fenti ya tarar suna ta yi a kowanne sako a gidan. Khaleel ke gaya masa wai Aunty Saratu ce za ta dawo sati mai zuwa. Har ran shi ya ji dadi, amma sai me? Ya shiga sashin Hajiyar domin ya sanar da ita dawowarsa, ya kuma bata tsarabar ‘givenchy’n da yayo mata, ya ji shi a kulle gam da mukulli. Ya kwalawa Furkan kira ya ce, “Kai Hajiya ta je anguwa ne?� Furkan ya ce cikin rashin jin dadin al’amarin “Ya Aminu rabu da Hajiyar mu kawai, wallahi tana bin shawarar su Anty Suwaiba ne kawai, suna kai ta su baro. Yanzun wai ta koma Kaduna saboda Daddy ya ce da ita Maman Intisar za ta dawo, ba ka ga irin zagin da ta yi wa Daddy ba a gabanmu har mu da muka goya masa baya.� Al’ameen ya rasa me ma zai ce? Ba tun yau ba wasu halayen na Hajiyar shi ke ba shi kunya da takaici ba, yanzu da girman ta a ce ta yi yaji ai ba karamin abin kunya ba ne a garesu, bai taba ganin mace mai kishin kishiya irin ta ba, wanda a shekarun ta ya isa a ce ta bari, ta kame girman ta, amma ashe wasa farin girki? Ko zama bai yi ba a lokacin ya zari mota ya nufo Kaduna cikin unguwar Kabala Custain, ainahin gidan kakanin su na wajen uwa. Tun daga get maigadi yake sanar da shi duk gidan babu kowa sun tafi hutu Dubai har Hajiyar. Ya girgiza kai a daren ya dawo Abuja, amma bai koma gidan su ba, gidan sa da Daddy ya ara masa wanda cikin ‘yan kwanakin babu abin da ba a zuba a ciki ba na jin dadin rayuwa, sai su da suka ki zaman gidan, anan ya kwana. Ya kira Hajiyarsa a washe gari, yana ba ta hakuri ta dawo ko don darajar su, amma sai ta sa masa kuka wai su da uban su so suke su taru su kashe ta. Ya ce, “Amma dai Hajiya ko za ki Dubai ba yanzu ne ya dace ba, sai a ce bakin ciki ya kore ki, ai kamata ya yi ki bari sai ta dawo tukun duk in da za ki sai ki je. Ya ya za ai mu kashe ki da bakin cikin mu bayan ke ce wadda ba mu da ya ita a duniya? Ki yi hakuri ki dawo don Allah.� Ta ce, “In dai ni ce uwar ka Aminu, to ba kai ba Saratu ko ta shigo gidan, in har kana son in dawo.� Ya ce ya amince, amma fa in har ta dawo din. Ban da abin Hajiya shi ina ma ya zauna a gidan balle ya shiga harkar su (sai ka ce wani lokacin kuruciya). Shi dai har ga Allah lallaba ta yake yadda take so don kar ta zubar da kimar ta a idon mutane, tunda kowa ya ji ba ta gidan ya san me ta yi wa tafiyar, shi kuma ba zai so zubewar mutuncin uwarsa a idon kowa ba duk lalacewar ta kuwa, duk da cewa ita din halin ta sai ita. Karfe goma na safe, ya shirya cikin danyen boyel navy green, haka motar da ya hau a yau ‘Kia� ce, lemon green, koren takalmin fata ne a kafar shi kirar Italy. Daman Al’ameen ba dai iya cool dressing ba, ya yi amfani da farin mudubin ido don ado kawai, ya nufo gidan su cike da nishadi. Ya saki kan motar a shararren titin Atiku Abubakar, har ya tadda katafaren gidan su yana bin sautin Alicia Keys, iskar damuna na kara armasa masa hantsin tare da gudanar masa da wani bakon nishadi, in da duk ya motsa kamshin turarrukan sa Ultraviolet da Vanderbilt da yake yawan amfani ke tashi. Al’ameen kenan. Ya duba kicin bai gan ta ba, ya leka dakin da suke kwana nan ma ba ta nan, ya leka dakin Dela babu alamar ta, gabansa yayi mugun faduwa, sai ya tsaya a kofar kicin din cikin zakuwa rike da ‘yan makullan shi yana zuba idon ganin ta inda za ta bullo. Zuciyarsa fes, take a yau domin hakika ta azabtu da rashin ganin Halimarsa for long four days (Tsayin kwanaki hudu). Daga can lambun gidan ta bullo rike da ribdediyar goba koriya shar da za ta hadawa Daddy guava juice sai ta ga bakon da bata zata ba, tsaye kofar ofishin ta. Ta saki baki galala! Da gani na jin dadi ne ta ce, “Lah! Al’ameen saukar yaushe?� Idanun su ke kallon juna tamkar sun hadiye junan su don so da kauna. Ita kanta ta yi kyau a yau, domin ta yi wanka kenan ta sanya daya cikinr iguna da skirt din da ya sayo mata kalar su black and pure white, sai doka kamshin brut (body spray) take, hakan nan curarren gashin ta mai kama da gammo yau ya sha wanki ya ga mayuka kala-kala da ya shekara bai gani ba sai sheki yake a cikin sassanyan hantsin na Litinin. Ta yi mai tufka daya kwal murtukekiya jelar sai yawo take a gadon bayan ta, she look so cute kwarai cikin kayan. Ita kanta ba ta san nishadin me ta tashi da shi a yau ba? Haka kawai tun da Dela ta ce da ita Hajiya ta yi balaguro Kaduna ta tashi ta fetse kwalliya, ashe rabon gwarzon masoya Al’ameen ce. Ya bude mata dukkan hannuwan shi amma sai ta noke ta cilla mai katuwar gobar da ke hannun ta, ya mika dogon hannunsa ya janyo jelar gashinta da karfi, don zafi ba ta san sanda ta fada jikin shi ta yi maza kuma ta ture shi ta ce (Dela da ke makale jikin kofar dakin ta, tana leken su, ta daura hannuwan ta a ka ta ce, “Na shiga uku ni Dela, kar dai yarinyar nan ba ta san Aminu ba? Za a aikata da na sani! Ko da yake duk laifin uwarsa ne…ikin ta babu inda baya rawa saboda kaduwa, yau kam ta yi dana sanin sa masu idon da ta yi, da bata ganowa kanta wannan kayan takaici ba, wai an ce ka bar abin da ba ruwanka izuwa abinda bai shafe ka ba, sa-ido sana’ar banza). Sai ta ja bargo har kanta ta kudunduna tana rawar dari. Ta ce cikin fushi, “Aminu, ba na so, kada ka sake, wannan haramun ne, idan kuma ka ki zan gaya wa matar ka ta ja ma kunne.� Ya tuntsire da dariya ya ce, ‘Ita har ta isa?� Ta gyada kai, ‘Har ta yi yawa.� Ya tura hannun shi a aljihun shi ya ce, ‘Zo ki ji?� Ta harare shi cikin haushi ta ce, “Ba’a zuwa.� Ya mannawa wani gefen daban ido ya ce (ba tareda ya dauke idonsa daga gefen da ya mannawa idon ba), “Ashe kadangaru ma na son kafar fararen mata? Dubi yadda yake lasar farar kafar ki cike da so da kauna.� Haba! Da ta daka wani tsalle, sai gata makalkale jikin Al’ameen tana ihun rokon sa, “Don Allah cire min shi, don girman Allah! Sai hawaye sharrr! Jikinta na kyarma. Ya fiddo hannun shi daga aljihu rike da necklaces da zobba, abin hannu da kafa na duwarwatsun matan Niger da ya sayo a Niamey, ya russuna ya daura mata a kafa, ya daura mata a hannu, ya mike ya daura mata a wuya. Ya bula hancin ta da kwambalelen abin hancin su mai kama da awarwaro, sai da ta feso wasu hawaye don azaba, amma ta yi kyau! Ta yi kyan har ta gaji!! Ta bishi da ido galala! Kana hannayen ta da ke cikin nashi. Da jikin sa data makale. Ta sauke idon ta ga kafafun ta, wani hawayen ya zubo. Ya kai hannun ya shafo hawayen yana murmushi ya ce, “Haba Halimah! Ya ya ki ke min asarar hawaye a kan kadangare? Ba kadangare ba, ko Zaki bai isa ya taba ki ina gani in kyale shi ba, sai dai ko ni ko shi. I luv u Halimah!� How much do you like this story? 5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *✍� SIRADIN RAYUWA✍�* Book one *@Takori* Page8️⃣ 1 Rabi Al-Thani (Hijriyyah) Wata Biyu Bayan Dawowarsa Al’ameen da Halimar shi (Kamar yadda ya nace da kiranta) sai aka soma shimfida ingantacciyar soyayya mai ban mamaki da ban sha’awa. Barin yanzu da ba su da shamaki, Hajiya kishi ya kore ta don har kwanaki suka shura tana Dubai ta ki dawowa. Su Khalil tun safe in sun tafi makaranta sai karfe shida na yamma suke dawowa don haka ba su ma san me Al’ameen ke yi a gidan ba, kai ko a mafarkin su ba su kawo ya ma san hanyar kitchen din gidan ba, to ya je ya yi me? Ita kuwa Dela tsoron shi take, da ta gan shi za ta soma bare-baren jiki ta gaishe shi ta wuce ta bar su. Tana kakabin abin a zuciyarta ita kadai amma ba ta ce da yarinyar komai ba. To ta ce mata me? Me ke tsakanin ki da Aminu ko me? Ta gaya masa ya ce tasa mai ido a yi mata asarar abincin ta yadda duniyar nan ta zama uhm-uhm, ba ruwanta su karata. Daga ita har Al’amin sun dauka da ba son juna suke ba, sai yanzun. Tun tana jin kunyar sa har ta gaji ta bari, domin ban dariya irin na Al’amin Allah ya yi yawa da shi. So, shakuwa da yarda da junansu su ne muhimman tubalan da suka gina soyayyar su a kai. Haka amincewa da junan su kullum sai kara karfi yake a zuciyar kowannensu. Ji suke, daya bai iya rayuwa ba tare da dan uwansa ba. Ba ta san me ye so ba a rayuwar ta amman Al’ameen ya koyar da ita wata irin soyayya mai shiga rai a lokaci daya, ya koyar da ita yadda za ta so shi, ta kaunace shi shi kadai a zuciyarta. Ba ta taba jin son wani da namiji a duniya irin yadda take ji yanzun a kan Ala’meen ba. To haka shi ma, tuni ya mance da Ihsan kwata-kwata a babin rayuwar shi watakila ta zama tarihi. Wadda a lokacin ta rasa nutsuwa kwata-kwata na rashin sanin makomar ta; ‘yar rakiya? Ko matar Al’ameen? Ita kam da ta san cin amanar da kasar haihuwar ta abin tunkahon ta, Nigeria, za ta yi mata kenan da tun farko ba ta takura su dawo ba. Haka Ann ta ce da ita muddin ta name shi bai kawo kansa ba ta bar ta da Jesus ya bi mata hakkinta na haifar ta da ta yi da wahalar da ta yi ta yi da ita. Ya tabbatar mata da amaryar Daddy ta tare zai kai masa bukatar su, kasancewar sa gwarzon uba, mai son duk abin da ‘ya’yan shi ke so ko da shi ba ya so in har bai sabawa tarbiyya da Addini ba, ya tabbata ba za a samu wani mushkila daga gare shi ba, sai dai ko daga gare ta, don ya lura son shi take amman auren baya gaban ta sam. Duk lokacin da ya yi zancen aure ya kan lura ta shiga wani zuzzurfan tunani, sai ya ta’allaka hakan da tunanin mahaifiyar ta da ta ce ta rabu da ita tun tana karama ba ta san inda take ba. A irin wadannan lokutan ya kan gaya mata zai zamo mata Uwa�, zai zamo Uba a gare ta. ‘Yan uwan shi za su maye mata gurbin nata ‘yan uwan, su nuna mata kauna ta jini da bata samu ba a rayuwar ta. Zai zamo mata miji kuma aboki, zai zama komai nata, zai kauna ce ta muddin ransa�, zai nesanta ta da Hajiyar da ke kin ta�, zai bude mata duk wasu kofofin farin ciki da dan adam ke burin samu! Ta kasance cike da tunanin wa Daddy zai aura? Ta je daki ta kwanta a dandaryar kasa ta yi ta kuka. Ta tabbata ta rabu da mahaifiyarta kenan har abada! To amma kauna da kulawa irin wanda Al’ameen ke nuna mata, wani abu ne dake rage bakin ciki da takaicin da zuciyar ta ke ciki. Ta kan tambayi kan ta yaushe ne wannan daukin da Najib ya kwadaitar da ita zai zo ne? Ko ko Al’ameen ne? Shi yasa ya dage su yi aure? Allah Sarki! Tana matukar tausaya masa, bata taba ganin mai son ta bayan Faisal, irin Al’ameen ba, ai ko ita shegiya ce ya kyautu ta aure shi hakan nan. To amma a matsayin da take kai a yanzu wa zai mata auren? ***** 12 Jumada Akhir (Hijriyya) Rana Mai Dimbin Tarihi A Gare Ta Faisal Bello Makarfi ne ke saukowa daga jirgin MEA International, ranar sha biyu ga watan Jumada-Akhir. Gaba daya Engineer Faisal B. ya canza tamkar ba shi ba, yana sanye cikin bakaken suit ya kuma daura thick coat saboda matsanancin sanyin da ake tsugawa, bakin takalmi sau ciki ne a kafarsa kirar Italy, hannun shi na hagu daure da agogon Rado yayin da na daman ke rataye da matsakaiciyar jaka irin wadda matafiya kan zuba passort da sauran kayan amfani na gaggawa. Bai fara tozali da kowa ba sai Ya Ameenu da rabonsa da shi shekaru goma sha biyar. Ya karasa da gudu suka rungume juna suna juyi kafin su soma hawaye. Abubuwa da dama sun faru, na farin ciki da na bakin ciki, na bakin cikin shi ya fi yawa. Bai taba zaton zai kara ganin Al’ameen ba a rayuwar shi, har suka iso gida kuka suke wiwi. Ya rasa mai yasa bai kullaci Aminu ba? Amsar shi ne don yana son shi, ko a cikin ‘yan uwansa Aminu daban ne. Kuma tunda har Daddy ya yafe masa shi a kan me ba zai yafe masa ba? Bai fara tambayar kowa ba sai Inteesar dinsa, Aminu ya ce, “An ce tana makaranta amma daman kwanan nan za mu kai mata ziyara tunda ga ka ma ka dawo shi kenan.� Ya yi shiru cikin tunani, shekarun da suka gabata suna da yawa, ya ci a ce yanzu ta yi nisa a jami’a in har lissafin da yake daidai ne. To ko a jami’ar take? Ya so kwarai ya tambayi Al’ameen sai ya share, ko da can Al’ameen na shiri da Intisar ne balle yanzun? Ya sauke shi a kofar gidansu ya juya ya tafi gidansa don yana da abin da zai yi da yawa. Haka kuma a ranar ne motar Daddy ta sauke Aunty Saratu, Zarah, Goggo Jumami da aminiyar ta Jami a harabar gidan, sabanin da su kai da motar Al’ameen na mintuna uku ne kacal, Aunty Saratu again a matsayin matar Daddy Makarfi. Ta kara kiba, ta kuma yi haske sosai na samun hutu da kwanciyar hankali. Baben ta Zarah na kwance a kafadun Jami tana barci suka shiga sabon sashin Aunty Saratun wanda da farko sun dauka ba a Nigeria suke ba, babu abin da Daddy bai zuba mata ba na jin dadin rayuwar duniya irin abin nan dai da ake kira Aljannar Duniya. Dakin Inteesar kadai abin kallo ne don a naira miliyan biyu cif Daddy ya sa kamfanin edcel interior decoration suka yi wa Intisar da yake tsammanin tana makarantarsu a Riyadh. Tun kafin ta zauna ta ke kwalawa Intisar kira tun karfin ta, sai Khalil ya shigo yana toshe kunnensa haka su Goggo suna “Kar ki lahanta mana dodon kunne.� Khalil ya ce, ‘Anty ki yi hakuri, ba jiyo ki za ta yi ba, don tana can sassan ‘yan aiki, bari in je in dauko miki ita kawai aka, don in na ce ta zo ko kallo na ba za ta yi ba.� Hawaye suka fitowa Saratu sharr! Wai Saratun ta ce a sassan ‘yan aiki? Ta daura hannuwa aka ta fasa kururuwa ta ce, “Amma Allah ya isa tsakanina da ke Haj. Nafi.� Da haka ta kwasa da gudu babu ko dankwali tuni ya yi nasa waje, ta bi hanyar da zai sada ta da sashin ‘yan aikin. Khalil na bin ta yana kira shi ma kukan yake, a daidai lokacin da Faisal shi ma ya fito daga cikin gidan bangaren Hajiyarsu ko jakar hannunsa bai aje ba saboda kururuwar da ya ji ta gigita shi na muryar da ya tabbatar Antinsu ne, ganin Antin tana gudu babu ko mayafi bai san san da ya yar da jakar hannunsa ba ya rufa mata baya, yana “Aunty Saratu ki tsaya!� Ta ce, ‘In tsaya, uwarku ta karasa kashe min ‘yar? Ban san me Saratu ta tsarewa Hajiyarku ba haka Faisal, wannan karon ba zan taba amincewa ba!� Bata kuma tsaya da gudun da take ba, hakan nan hawayen ta ba su bar ambaliya ba. Tana tsaye tana farke buhun semovita don zubawa cikin ruwan zafi tafasashshe, Aunty Saratu ta rungumeta ta baya, yayin da hawayen ta da ke ta kwarara suka dinga sauka a kirjin Inteesar! A fusace ta juyo, a zaton ta Al’ameen ne ta ce, ‘What a nuisance, Aminu?� To amma sai ta ga mamarta, da ko a mafarki ba ta zaci sake gani nan kusa ba. Idanuwanta suka bubbude gaba daya tamkar sa fado. Ta kai hannu ta shiga tattaba ta a gigice ta dai tabbatar ita din ce hanci, ido, baki fuska, babu abinda ya canza a jikinta. Ta bude baki kamar mai son yin magana amma sautin ya kakare ya ki fitowa sai dai labban ta da ke motsi yanayin motsin na nufin, “Mamana?� Aunty Saratu ta janyo ta ta rungume tsan-tsan a kirjin ta cikin yanayin fita hayyaci ta soma cewa. ‘Saratu? Haka Nafi ta maida ke? Allah ya isa tsakanina da Hajiya Nafi, ba zan taba yafe mata ba haka duk jinin ta, in Allah ya yarda sai ya ga tozarci a rayuwa…� Faisal ya yi saurin

Chapter 6 of 38