amma a bayan idon sa.
Karfe daya da rabi na sulusin dare ta fito daga maboyar ta, wato cikin store, ta san dai duk nacin sa zuwa yanzun ya hakura ya tafi amma me? Ta zauna gefen gadon ta kenan ya murdo kofar ya shigo.
Ba karamar razana ta yi ba amma sai ta cije, ta yi kamar bata gan shi ba. Ta cigaba da kokarin gyara wajen da zata kwanta. Hakikah zuciyar ta ta girgiza da ganin muguwar ramar da yayi fiye da sanda ya kwanta ciwo, ga sumar da ta cika kyakkyawar fuskar sa kamar ba Al’ameen din da ta sani ba, mai tsananin kwarjini, gayu da kwalisa, ilhama da cikar zati. Fuskar shi ba annuri sam kamar yadda zuciyar sa ke wani irin zazzafan bugu da sauri da sauri.
Ya dubeta da lumsassasun idanun sa cikin fidda rai da al’amarinta, ya karisa har gaban mudubin ta ya ja (stool) ya zauna yana fuskantar ta, cikin raunanniyar muryar da bata taba ji daga gare shi ba yace
“Inteesar!�
Ta dago ta dube shi, amma ta kasa magana, sabida zuciyarta dake neman bayar da ita. Ji ta ke kamar ta ruga ta rungume shi tayi kukanta mai isar ta, ta gaya mishi tayi kewarsa ita ma fiye da yadda harshe zai iya furtawa, fiye da yadda kwakwalwa zata iya fassarawa kuma fiye da yadda tunani zai iya kintatawa.
Ta ji ta a marainiya, duk kuwa da tarin iyayen da suka zagayeta a yanzun. Ta fi jin ta a mai cikakken gata, a sanda suke tare a (kitchen) fiye da yanzun da take da Daddy da mamar ta. Ta azabtu da rashin ganinsa fiye da yadda shi yake tunani.
Ya dubeta ya gani, ta fi shi ramewa da lalacewa, ta fi shi ciwon zuciya illa ita mai iya ‘controlling� zuciyanta ne ba kamar shi da zuciya ke juyawa ba.
Ta fishi jin ciwon abinda take masa da hukuncin da ta yanke masu, kuma ta fishi azabtuwa daga hukuncin. Ta fi shi tunanin yaya rayuwarta zata karasa batare da shi ba? Ya fiye mata duk wannan gayyar dangin da suka zagayeta! To amma wannan alkawari ne, alkawari ne tsakanin ta da zuciyar ta da Ubangijin da ya halicceta ta yaya bazai gane ba ya taimaka mata wajen cikar alkawarinta da burin da ta dade tana ciwa zuciyarta�.
Sheshekar kukan Al’ameen ya katseta da digar zafafan hawayenshi bisa tafin kafarta, dubawar nan da zatayi sai taga Al’ameen ne durkushe a gabanta, yama rasa kalmar da zai yi amfani da ita wajen rarrashinta da nuna mata muhimmancinta a gareshi.
Me zai gaya mata ta yarda bazai iya jinyar zuciyar nan ba� me zai gaya mata ta san ya manta komi, ya manta kowa, ya manta ko shi wanene saboda rashin soyayyar ta?
To itama kukan take mai tsima zuciya an rasa wanda zai rarrashi wani a tsakanin su.
Ta ga dai inta biye masa zasu kwana ne a hakan, wanda ita bata fatan hakan. Ita kadai ta san yakin da take yi da zuciyarta a duk sanda take tare da Al’ameen, balle a irin wannan halin da zuciyoyinsu ke gab da narkewa saboda azababben son da fada ma bata baki ne.
Ta sauka daga gadon itama tayi tsugunne bisa carpet a gabansa tamkar yadda yayi, don tana ganin it’s a disgrace agareshi ya durkusa mata, cikin muryar kuka da nadama tace
“Ni, ni� dama cewa nayi sai in har Hajiya ta rokeni gafarar abinda tayi mun, ta kuma furta amincewa da ni a matsayin matar ka, sannan ne zan yarda.�
Ya dago a hankali ya dubeta, yayi tsai da ransa yana nazarin zancenta. Tamkar kuma wanda aka yiwa allurar kuzari kuma sai ya mike tsaye, ya zauna a gefenta yace
“Har ga Allah Saratu wanan shine uzrin ki?� Ta gyada kai tana hadiyar zuciya. Yayi murmushi, ya ce,
“Intisar, idan na kawo Hajiya na gaban ki da Daddy da Aunty, ta nemi gafararki, ta kuma ce ta amince muyi aure, shikenan?�
Ta kara gyada kai da sauri. Ya sake yin murmushi ya mike, jikinsa ba inda baya rawa ya ce,
“Keep your promise.�
Ya soma ja da baya-da-baya har ya tadda kofar fita idon shi na kanta, yana mata murmushin da har abada ba zai gushe daga zuciyarta ba, cikin karfin hali itama ta mayar masa, sai kuma duk suka kyalkyale da dariya ga hawaye sosai a fuskar kowannen su. Ya daga hannunshi ya sumbata kana ya huro mata iskar. Da haka ya bar dakin gudu-gudu sauri-sauri, zuwa inda ya adana motarsa. Akan idon Daddy dake kallonshi ta taga ya ja motar ya bar gidan.
Daddy da Aunty Saratu suka yi ajiyar zuciya a tare. Duk kawaici irin nasa a yau ya yanke shawarar dosar Intisar a washegari don jin inda ta sa gaba, abin ya isa.
Washegari ta je gaida Daddyn da safe kamar yadda ta saba a ‘main� falonshi, yana rigingine cikin kujera da ‘yar karamar rediyon shi inda yake sauraren ‘Voice of America� shigowar ta yasa ya kashe rediyon kwata-kwata ya bata hankalinshi yana murmushi tun kamin ta zauna ya ce,
“Saratu, gobe fa in Allah ya kaimu tare da su Hunainah zaku tashi, daga Korea zasu rakaki makaranta don duk wasu shirye-shiryen komawar taki ban san sanda Al’ameen yayi ba. Dama abinda yasa aka daga tasu tafiyar kenan nima ban sani ba sai jiya yake gaya mun. Sai dai kuma naga alamar bakya son sakin jiki da Haj. Hadiza, Why?�
Ta yi shiru, yayi zaton bata ji ba sai ya sake maimaita tambayarshi. Ta dan kada kafadu alamun zancen bai dameta ba ta ce, “ba komi� ya ce,
“Ba komi, na nufin komi. Duk inda kika ji ance ba komi, to anan koman take�.
Ta ce, “To Daddy itama bata kula ni sai ‘ya’yanta (Su Hidayah) to ni ma ba sai in zauna inda na fi wayau ba?� Ya girgiza kai cikin murmushi “a’ah, ba zaki zauna inda kika fi wayau kadai ba. Uwa-uwa ce, matsayinta ya wuce duk yadda kike tsammani, ko ita bata kula ki tilas kuma wajibi ne ke ki kulata, ki dinga nuna mata kauna.
Above all, Hadizah bafillatana ce usul fillanci take maki, wannan kunyan na dan fari na nan tattare da ita ga kuma rashin shakuwarku, wanda wannan sai a hankali. Ke zaki taimaka ku shaku. Idan bakya kusantarta yanzun ba zaku taba sabawa da juna ba tunda yake ke mace ce, gidan aurenki zaki cikin dan lokaci, ki daure kiyi hutun karshen wannan shekarar tare da su. Don ba mamaki kamin ku dawo an daura auren ku duka.�
Ta cira kai a hanzarce tana yi mai duban mamaki kana tayi saurin sadda kai, cikin siyasa irin tasu ta manya ya ce,
“Wai yayane? Ke da mutumin me kuke ciki ne, na ganshi yana ta mana zarya kamar marayan da ya rasa uwa, me kuka yanke ne? Su Najib fa ku suke jira don tuni sun gabatar da bukatarsu suna son asa masu rana da wuri.�
Yayi shiru yana nazarin irin karbar da tayi wa zancensa.
Tayi lamo da wuyanta a masangalin kujera abin tausayi. Idonta ya kawo ruwa raw-raw cike da nadamar hukuncin da ta yanke akan Al’ameen, wanda tasan abinda bazai taba yiwuwa bane. Tayi kokarin maida hawayen don bata son Daddy ya gani.
To amma shi Daddyn duk tsawon lokacin idanunshi na kanta, tsoron shi Allah, tsoranshi kada Intisar tace bata son Aminu. Da ina zai sa kansa da rigimar Al’ameen yadda jiya ya sashi gaba da magiyar a daura musu aure koda tace bata son shi!
Abinda shi kuma ba zai taba Iyawa ba wato danne mata hakki don farin cikin nashi? To amma shi kansa yakan so kasancewar al’amarin ba don komi ba sai don cigaban zumuncin bangarorin guda biyu, hakannan zuri’arshi kadai ya taba yiwa sha’awar auren kamilallar mace irin Intisar! Balle gudan jinin sa Ameenu?
Kwata-kwata tarbiyar Ihsan bai mishi ba, tun haduwar su na farko. Hakannan banda mutuncin Dr. Argungu da yake gani da tun zagin da Ann Hathaway taje ta yi mishi har ‘office� kan wai Al’ameen ya ci mutuncin Addininta don kawai ta bashi shawara kan zaman shi da Ihsan gaba daya suka sire mishi.
Haka shigowa da Ihsan ke yi rungume da Al’ameen har cikin dakinsa abin na damun sa kwarai, don dai ba yadda zai yi ne. Cikin murya mai sanyi ya ce,
“Saratu, ki gaya min saboda Allah ba kya son Al’ameen ko?�
Ta shiga girgiza kai da sauri alamun ba haka bane, hawaye suka soma biyo kumatun ta. Tsohon Brigedier Bello Makarfi, ya mike zaune daga kishingiden da yayi, ya daura hanunshi na dama a kanta, ya ce,
“Wannan hawayen da kike kwarararwa a kullum yana damuna, sai in ga ni ban kai ga taka rawar uba har yau a gareki ba. Bayan ukubar da na sanya ki cikin gidana, still na kasa share miki hawaye a shekarun farin � cikin ki, na kasa tsayawa in gina maki rayuwa ta kwarai tamkar yadda na gina ta ‘ya’yana, na zalunce ki, na bautar dake, ban baki kwakkwaran ilimi ba har yau, ban idasa da zaba maki miji na gari a girman ki ba.
Idan bakya son Al’ameen kada ki ji nauyi na, ki kawo ko waye ni kuma mai share hawayen ki ne, in har ya cancanci ya amsheki daga hannuna, zan bashi.
Ki bar la’akari da kasancewar Aminu da a gareni, ni duk daya kuke, sai ma in ce kin fi shi. Domin ke ‘ya ce da ban taba ganin mai biyayyar ta da son iyayenta tamkar ke ba. Na rantse, a cikin ’ya’yan da na haifa bakidaya babu wanda ya ji kai na ya ke kuma kaunata tamkar ki.
Don haka don baki son Aminu baya nufin bakya son Daddyn Aminu, Illa shi Aminu ne ba kya so saboda wani aibinsa ko wani kuskure daya aikata miki kika kasa yafewa!
Ni dai hakannan nake son ki da Al’ameen, ba don komi ba sai don masifaffen son dana lura yana yi miki mai gigigatarwa, mai neman fitar da shi daga hayyacinsa, mai neman raba shi da rayuwarsa.
Duk kuma bakomi ba ne face sakayyar Allah garemu a kan ki. Ina son inda za’a so ki ne, har illa masha Allahu, ba inda za’ayi miki son wanin ki ba. Abin nufi, masu aurenki domin wani naki, kyawu ko dukiyarki.
To sai naga Al’ameen ne irin mijin da ya dace da ke, irin mijin da na dade ina yi miki burin samu, zai kuma rike mana ke da dukkan kauna irin wadda muke so ki samu a gidan aurenki.
Na kuma dade ina sha’awar yiwuwar hakan a raina tun kamin shi ya furta, tun a sanda yake cin zalinki naga abubuwa dayawa cikin kwayan idanun sa, na kuma san ko ba dade ko ba jima Allah na nufin wani babban al’amari a tsakanin ku. Amma in kina ganin na so kaina ne Saratu fada mini?�
A gaggauce ta rarrafa gareshi ta gurfana a gabansa, ta girgiza kai da karfi ta ce,
“A’ah! Har abada Daddy nasan babu mai kaunata a duniya tamkar kai, har kuma iyayen da suka haife ni. Ba kuma zaka taba yin wani abu da sunan son kai a gareni ba. Kuma ni baka taba bata min ba, dai-dai da rana daya balle ka sa ni cikin ukuba.
Bana kuka domin kiyayyar Al’amin, kuka nake don so da kaunarsa, da suka yiwa zuciyata katutu. Allah Daddy, ban taba fada ba, amma Aminu na taba ji har ruhi da bargon jikina, nake kuma azabtuwa a zuci da gangar jiki domin kaunar sa!
Kuka nake domin nadamar tsatstsauran hukuncin da na yanke a gareshi wanda na zauna nayi tunani akai na tabbatar ba zai taba yiwuwa ba, domin kiyayyarta gareni ba karama bace, da kiyayyata aka halicceta baza ta taba yin abinda na kudurta ba.
Kuka nake domin sanin cewa na jefa Al’ameen dina cikin halin kaka-ni-kayi, halin da bazan iya fitar da shi ba, halinda zai iya janyo muguwar gaba tsakanin sa da wadda ta haifesa, ta shayar da shi mamanta, ta raine shi har ya girma ya kai munzalin da har na gani na ke bege, take kuma son sa fiye da kowa a duniya.
Dama tace ni din mayya ce, yanzu zata kara tabbatar da zarginta cewa na mayancewa ‘ya’yanta, bayan ni kullum kokarina shine in nisance su, in yakice su daga cikin rayuwata amma na kasa!
Ko nayi kokarin hakan bana cin nasara, ba don kaunar jini ba sai don cewa su wani bangare ne daga jikin Daddy Makarfi. Jinin da yafi karfin wulakanci da tozarci a gareni. Ina tsoron hukuncin da zata yanke masa, wanda ko menene ni ce zan zamo sanadi.�
Daddy ya yi murmushi, yace “Gaya mun hukuncin da ki ka yankewa Al’ameen din ki?� Cikin hawayen dai tace
“Cewa nayi yaje yazo da Hajiyar sa, ta nemi gafara ta kan kiyayyar da ta wanzar da rayuwarta nuna mini, ta kuma furta amincewa da auren mu da bakinta, sannan ne zan maido soyayya ta, in rungume shi matsayin miji na uban ‘ya’yan da nake burin samu daga tsatson Daddy Makarfi.� Ta cigaba da kuka sosai, ta ce,
“Daddy daga baya nasan ban kyauta ba, nayi nadama, hukuncin yayi masa tsauri, don bazata taba amincewa ba, shi kuma ba zai dawo gareni ba sai da amincewar ta, tunda hakan muka yi alkawari. Ni kuma ba don komi nayi hakan ba sai don kwatarwa kaina da ‘ya’yan da zan haifa a gaba ‘yanci daga gareta.
Ina guje masu halin da zasu iya fadawa a gaba daga ukubar ta. Ni kadai nasan ita ko wacece? Ku bar ganin wai don iyayena sun bayyana zata daina ki na, a’ah, kiyayyar ta gareni a cikin jinin jikinta take, bazata taba dainawa ba. Koda kuwa a ce ni ce mafi rinjayen iyaye a duniya.
To amma ai shi Al’ameen na zalunceshi, na hukuntashi da laifin da ba na shi ba ko Daddy?� Tayi shiru tana maida lumfashi cikin zargin kanta.
Ga Mamakin ta sai yayi murmushi, ya dora hannu bisa kafadarta, ya ce,
“A’ah, ba ki zalinceshi ba, kin yi dai-dai. Ban taba ganin yarinya mai tunani, hazaka da hangen nesa irin ki ba Intisar! Ina ma a ce sauran yara mata zasu yi koyi da dabi’un ki da an daina wulakanta su a gidan aure.
Soyayyar dake zuciyar ki bata rufe maki ido ga hango gaba ba, da abinda gobe zata iya haifarwa ba. Sadaukarwar ki da sanin ciwon kan ki bazasu tashi a banza ba!!!
Abu ne da bazan iya gaya miki ba, Illa ni ma Haj. Nafi ta cuce ni ba kadan ba, wanda hakki ya koma mata. Ban saketa ba, amma ga gidan, ga ‘ya’yan nata kiri-kiri ta kasa zama a cikinsa, to tun a duniya kenan wata shari’ar sai a Lahira!
Komi za kiyi Saratu ki sa Allah a gabanki, bayanki, hagunki da damanki. Kar ki ji tsoron mutum domin shi ba komi bane face abin halitta daga yunbu, mai yin komi daga kudirah da Iradar Ubangiji kuma bisa nufi da yardar sa.
Magana ta karshe shine ina bayanki akan kudurinki na cewa sai Aminu ya kawo mahaifiyar shi nan a gabana ta nemi a fuwarki, bisa dimbin azabobin data gana miki, wanda ko Allah baya yafe hakkin wani kan wani. In kuma har baki yafe mata ba ai Allah ma bazai yafe mata ba.
Ta kuma furta da bakinta cewa ta amince ki zamo mata a gareshi wannan tunani ne mai kyau. Ni kuma alkawari daya nake so ki min shine, daga yau bazaki sake zubda hawayennan haka kawai bada kwakkwaran dalili ba muddin ina raye�
Ta sa hannuwanta duka biyu tana sharewa tace
“Na daina Daddy, kuma in har hakan ta faru ni kuma na amince da auren Al’ameen koda a gobe ne, kuyi duk abinda kuke ganin ya dace.� Ya ce,
“Ubangiji yayi miki albarka Saratu, ya zama jagoranki a rayuwa, ya baki aljannah mafificiya sakamakon biyayyar nan da kike yi mun a gidan duniya. Kada Allah ya nuna min ranar da Ameenu zai tozarta ni a idonki.�
Ta sunkuyar da kai cike da kunya, a ranta ko cewa take ai ko Aminu kullum yankar tsokar jikinta zai ke yi yasa a miya, zata daure ba tare data gayawa Daddyn ba. Ya ce,
“Abinda nake so dake a karshe shine ki ji abinda na ce da ke, ki bi mahaifiyarki su rakaki makaranta, ki maida hankali kan abinda ya kai ki, muma insha Allah zamu ke zuwa dibaku a kai-akai, in kun samu hutu ki zauna tare da su har mu ji me Al’ameen da Mamar sa suke ciki a san abin yi.
Da dai za’a hada auren ku da na su Najib ne amma ina ga yanzu za’a fara yin nasun, har sai tazo tukun (Hajiyar), kuma ki saki jiki da ‘yan uwanki don Allah.�
Cike da murmushi tace ‘I can do anything for your sake, Dad (zan iya yin komi domin ka Babana)� ya ce,
“To Allah yayi miki albarka.�
Mu karasa a littafi na hudu kuma na karshe insha Allahu. Taku har abada,
� Sumayyah Abdulkadir.
How much do you like this story?
5/14/22, 09:26 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book four
*@Takori*
Page1ï¸âƒ£
Alkawarin da ta yiwa Daddy bata karya ba. Ranakun da suka biyo baya, ta karesu ne cikin farin cikin da walwala ga kowa. Kowa a gidan yayi mamakin canzawarta haka farat daya sai dai babu wanda ya tambayi dalilin canzawar tata.
Ko babu komi ta samu courage da relief daga rudanin da zuciyarta ke ciki. Alameen bai zo ba a washegari, ta tabbatar duk inda yake yana bisa hanyar neman Hajiyar sa, a Dubai ne ko a Kadunan ne oho su suka sani!
Ta tabbatarwa kanta lallai wanda ya rasa abokin shawara abin tausayi ne, ita dama tun fil azal Daddy ne abokin shawararta sai ko Ya Faisal wanda a yanzu baya yi da ita, da wuya su bata shawarar da in tabi bata ganin yakini a ciki. Hankalin kowa ya kwanta musamman yan uwanta da basu san wainar da suke soyawa ita da Babanta ba, wadanda a yanzu sabon shafin soyayya ne mai karfi aka bude koko in ce ake kara kullawa tsakanin Najib da Hidayah.
Wayewar garin litinin sukayi sallama da kowa har da Daddy da kansa a rakiyarsu (Airport) din Abuja, Najib da Hidayah dai kamar bazaa rabu ba illa sun yi alkawarin kasancewa a waya a kullum kamin a mallaka masu juna, hakannan shi Najib din za suke zuwa da Daddy.
Zahra taki barin Haj. Hadiza kememe har shidewa ta shiga yi da Khaleel ya dage sai ya amsheta, kawai sai aka ji Anti Saratu ta ce,
sai ku tafi da ita a yayeta, in ma zaku rike na baku halak malak. Ban sani ba dai ko Daddin Ameenu na da uzuri? Daddy yayi murmushi yace umh-uhm, Allah ya kiyaye hanya Zahrah, Zahrah Allah ya kai ku lafiya!
Haj. Hadiza ta rungume Zahra tsam-tsam har da hawayenta, ta rasa bakin godiya bisa dimbin karamcin wadannan mutane, bata san me zata yi ta saka musu ba itama banda mallakawa yayansu tsala-tsalan yan matan ta, sai Ambassador ne kema Daddyn matukar godiya, su kadai suka san me suka kukkula kan auren yayan su ba tare da sanin yayan bama.
Kwanan Intisar kwata-kwata ukku a gidan mahaifiyarta a kasar Korea, Abbansu ya maida ta Riyadh. Makarantar da fi so a rayuwarta, makarantarta ta baya, makarnatar da ta zamo silar warwarewar alamuran ta da gajarta bakin-cikin rayuwarta, tunda kuwa anan ne ta hadu da su Hidayah, har suka dangana ta ga mahaifiyarta.
Makarantar da ko a mafarki bata kara yin na dawowa cikinta ba, don tana ganin bazata kuma samun irin wannan gatan ba. To haka alamarin Ubangiji yake, don haka yake cewa La Taknadu min Rahmatullah (Wato kada ku fidda rai da rahmar Allah) domin buwayar shi ta wuce mithali. Hakannan duk wani SIRADI a rayuwa da sannu in an yi hakuri zaa tsallakeshi, ba kuma inda hakuri da fawwalawa Allah alamura baya kai dan adam.
Ta daga kanta sama a cikin ajinsu, kana ta sunkuyar. Ta yi duba ga rayuwarta mai juyawa tamkar a majigi. Ta kara jin tsoron Allah, tsigar jikinta ya tashi yarrrr! Ta kara tsarkake shi a zuciyarta, kadaitaccen sarki mai juya alamura yadda yaso. Tayi duba izuwa wahalolin da ta sha a rayuwa, wai yanzu duk sun zama tarihi. Ita kanta duniyar haka take, no condition is parmanent (ba wani yanayi da yake tabbatacce). Saratu ta watsar da tunanin komi ta rungumi karatun ta bil-hakki. Har yanzu burinta yana nan kan son gyara rayuwar alummah!
Ta girgiza da labarin mutuwar mutuminta Dr.Alhassan, bayan auren sa da kawarta Rabikha. Ta jima tana yi mai Addu’ar Rahma da gafara wurin Ubangiji. An kai ta aji shidda ne, don haka bata wasa. Da yawan Malaman da ta sani a da, basu bane a yanzu, wasu an canza su, wasu an kara masu girma.
Ita kanta shugabar makarantar da ta sani a da Ayyush Siddik ba ita bace a yanzu. Tace ashe ko ina ma haka abubuwa ke juyawa ba a kanta kadai ba! Bata kuma kara bi ta kan komi ba sai karatunta, ga wayar yan uwanta tana samu akai-akai, sai dai Alameen ko sau daya bai kira ta ba.
Ranar da suka fara jarrabawar gwaji Haj. Hadiza da Ambassada suka je mata, ba karamin farin ciki tayi ba, don rabonta da ganin wani nata watanni bakwai kenan. Anan ne suke gaya mata Hunainah ta wuce Jamiar Alazhar Hidayah kuma an daura auren su da Najib suna honey-moon a can Al-kahiran, tayi mamaki kwarai da Hidayah bata gaya mata ba, gashi kuma suna waya.
Daga baya ne ta tuna cewa Hidayah ta sha gaya mata bata son ta rigata yin aure, so take ayi komi nasu tare. In kuma hakan bata samu ba ita kam bazata ji dadin yin auren ba.
Auren Hidayah da Najib ya tabbaar mata har yanzu Alameen bai dawo daga gun Mamarsa ba! Ko dai ta ja rayin sa kan nata, ko kuma wani mummunan alamari zai faru, wanda take gudu, take guje masa. Ko kuma kwata-kwata bata amince ba shi ya sa ya rabu da ita? Bata sani ba. Ba irin tunanin da baya zuwa mata a rai amman ta ki gasgata kowanne, kowanne tana yi mai uzuri ne da cewa Alamin zai dawo gareta komi rintsi ba zai bari Hajiya ta rabasu ba.
Ramadhan 20/10 Hijriyyah
Allah Sarki! Alameen Bello ne ke tafe cikin motarshi (ash colour Rio), sanye da Jamfa da wando na bakin yadin Filted. Ya saya raunnanar kwayar idonshi cikin bakin dark glasses akan hanyarshi ta zuwa air-port din garin Abuja domin dauko mahaifiyarsa da jirgin data shigo daga Dubai zai sauketa a yau.
Yayi parking a inda aka tanada domin adana motoci ya karasa reception ya samu gefen wata kujera ya rage tsawo. Kada kaso ka tona zuciyar sa da ke bugu da sauri-da-sauri mai cikke da kunci, fargaba gami da igiyar so da ta yi mata dabaibayi.
Idan har ka san Dr. Alameen Bello a da, to a yanzu sai ka wuceshi ba tare da ka shaida shi ba; gaba daya ya kare, sai tsayin da karan hancin gami da fararen idanun kadai.
Yayi zaman akalla mintuna talatin kamin a fara shelar landing din jirgin. Tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ya mike yana mai dauriya da karfafa kansa da cewa akwai jin kai na uwa, akwai kauna ta Uwa ga dan ta. In ta kalleni ai zata tausaya mini, ita kanta tasan ba haka na dawo ba, tasan na zamo mara amfani, zan kuma kare rayuwa ta a hakan muddin bata bani abinda zuciyata ke muradi ba, zan gaya mata zuciya na ciwo, duk wani bugu da take yi Intisar ne a ciki, zan fadi, zata rasa ni muddin tayi min shamaki da Halimanaaa.
Bai sani ba, ta dade a tsaye gaban sa, sanye da koriyar atamfa sufa, ta yane jikinta da yalwataccen mayafi, ta dade tana nazarin mugun zabgewar da yayi, kai da alama baya ganin abinda yake gabansa ma, baya jin taku balle gane abinda ke faruwa a gabansa. Ta mika hannuwa ta rungume shi ta soma kuka ta ce,
“Ameenu mutuwa zaka yi ne?�
A sannan ne ya dawo hayyacinsa, ya runtse ido cike da farin cikin saukar ta lafiya, ya russuna ya dauki Jakarta ya rataya yajata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 38