Share this page
ya jarrabe ta da ita, in banda wannan yarinya a duniya wa zai kuma kallona da mutunci bayan irin rayuwar kuncin da na jefa su itada uwar ta, amma bata kullace ni ba, ta yafe mun dunguma dunguman hakkokinta da ke kaina ba tare da wani tashin tashina ko bin baa si ba. Uwar ta da yan uwan ta basu taba kallona da abinda na yi mata ba, sun sani ba wai basu sani ba. Ka sani, ba don ta rasa masoya ne har yanzu ta ke zaune a hakan ba sai don ku da ta kallafa soyayyar ta a kan ku, har bata jin zata iya kaunar wani bayan jinin mahaifin ku. Alameen ya yi kokarin ganin ya jefa yarinyar nan cikin rayuwar farin-ciki iyaka iyawarsa, amma hakan bai yiwu ba, mutuwa ta katse masa duk wani hanzari. Na rantse da Allah da a ce yana raye. Da tuni yarinyar nan ta daina kuka a rayuwar ta, ta daina bakin cikin da har yau zuciyarta bata rabu da shi ba, ta samu madawwamin farin ciki haka a rayuwar ta. Ashe idan baa tausaya mata ba bazaa kulla gaba da ita ba. Ni na san wallahi ba don kai ta yafe mun ba, illa kawai tana girmama ku, tana ganin kima da mutuncin ku fiye dana kowa a duniya, tana darajja ku tana kaunarku kaunar da bata yiwa yan uwan ta na jinni. Da ace bata kaunar ku, da wallahi har duniya ta nade bazata kuma kallon ku ba sabida abinda na ce da ita a can baya balle har ta so hada rayuwa da ku. Ina mai tabbatar maka ko bayan raina Intisar ta sake kuka a domin ka, Allah zai bi min hakkina na haifar ka da na yi da kokari na wajen ganin na inganta maka rayuwa da abinda kake so kake kuma gudu da gangan. Ta sa habar zaninta ta share hawayen da suka cika mata ido.� Faisal ko motsi ya kasa, durkushe kawai yake tamkar mai neman gafara. Zuciyar sa ta cunkushe da tunaninnika daban-daban. Ya rasa abinda ke masa dadi, ya rasa abinda ke sanyashi tsanar duniyar da abinda ke cikin ta, ya rasa abinda ke sanyashi nadama a kan Intisar. A ganinshi ai shi ya dace a tausayawa ba ita ba, shi da bashi da saa, shi da yake son maso wani? Shi da bai ci riba ba ko kankani a soyayyar daya wanzar da rayuwarsa a yi mata? Amma wai har shine uwarsa zatayi masa baki a kanta, bayan ita din nan ba abun tausayi ba ce; muguwa ce, mayaudariya ce, azzaluma ce kuma mai son kanta da farin cikin ta kadai? Ya girgiza kai wasu zafafan hawaye suka zubo bisa lallausar kumatun sa, ya ce cikin matsanancin takaici, “Yanzu Hajiya me kike so in yi?� Ta ce, “Ban sani ba, shashashan banza kawai. Kana zaune har wani zai aure ta baka cikawa kanka kowanne buri ba, baka cimma wani farin ciki a rayuwar ka ba, ka zo a banza zaka koma a hofi, kana ta kunci da dacin rai kai daya babu wanda ya san kana yi sakarai kawai. Yanzu yanzun nan ba sai anjima ba ka nemeta ku sasanta, ai na san son ta ke lalata ka ba wai ban sani ba, zuba maka ido nayi in ga iya gudun ruwan ka, amma naga abin naka bana kare bane, wanda bai san abinda ke masa ciwo ba. Ya yi murmushin takaici ya ce, “Hajiya, tunda muke a duniya, na taba ce miki ina son Intisar, so na soyayyah, da har kike cewa in aure ta?� Ta dube sa a lalace ta ce “Ai fa, shine naga ka bar kasar baki daya saboda tsoron, kada son daka ke yi matan ya fito kowa ya gane, sabida bakin cikin bazaka iya aurenta ba alhalin tana kanwar ka da kuke uba daya? Shi ne kake bata min domin ta, kake yin fito-na-fito da ni duk a kanta. Tun a lokacin na dago ka Faisal, kawai na godewa Allah daya bani ikon cika alkawarin da nayi wa Babanku na cewa bazaa taba ji daga baki na ba ita din ba yar sa bace, na tabbata a lokacin da sai ka aure ta, koda ni din zan ki amincewa. Wannan shine babban dalilina na kara boye maku maganar, don ina ganin bakin ciki na na karshe a rayuwa kuma wanda zai kayar dani a lokacin shine ka aure ta. To amma dubi yadda Allah ke juya alamuran rayuwarmu gaba daya ta yadda mu din bamu tsammana ba, bamu taba zato ba. Ina mai tabbatar maka idan ka bijirewa magana ta a yau Faisal zaka yi nadama mara amfani a gaba dayan ragowar rayuwar ka, irin wadda na yi, danuwan ka ya yi. Ka yi amfani da sauran damar da Allah ya baka a lokacin daya dace, domin in ta wuce, ba zata taba dawowa ba!� Ta fada tana kada yatsanta Ibham, lokaci guda kuma ta mike ta bar masa dakin idanun ta cike da hawaye. Ji yayi zaciyar sa ta karye, duk wani sauran kuzari da ke tare da shi ya kare. Ya mike ya fito daga dakin, shi kansa bai san inda ya ke jefa kafar sa ba, kawai ya tsinci kansa a tsakiyar falon gidan. To ina zai dosa cikin gidan nutane karfe goma sha biyu da rabi na dare? Ban da dai uwa-uwa ce kuma dole a bita da yadda ta ke so. Banda ma rigima irin ta Hajiya to ya je yace mata me? Shi fa ko nambar wayarta baya da ita. Above all ma yana ganin magana da ita ma bata lokaci ne tunda ba wani amfani ke gareshi ba. Na farko Intisar-Intisar ce har kullum a gare shi, the past memories will forever remain fresh in him, sai dai ai shi bata son shi, Alameen kadai take so. Shi ba komi bane face yayan da ta ke kauna. Me yasa Hajiya ba zata dubi wannan ba? Me yasa bazai cigaba da zama a matsayin da ta bashi ba ko don tsira da daraja da mutuncin sa da take gani? Tunanin hakan ya sanyashi juyawa, tare da kokarin maida kwallar da ke neman bayar da shi. Amma sai Najib ya tokare masa hanya da kafar shi ta dama. Ya daga ido ya dube shi fuskarsa babu alamun wasa hakan nan bacin ransa ya ninka na koyaushe, ya fito baro-baro cikin idanun sa. Najib din bai kalleshi ba don shi kansa ya razana da tension din da yaga Faisal din a ciki, wayar sa kawai yake latsawa cikin murmushi, cikin saa kuwa bugun farko ta shiga, ita din ce kuwa ta dauka da alama dai cikin magagin barci ta ke, cikin rarraunar muryarta kamar koyaushe tace Yello! Ya Najib ya aka yi? Ya ce ki yi mun afuwa, na katse maki barci. Ki sakko yanzu nan falo ina son ganin ki personally, is vital ki zo da sauri. Da haka ya katse wayar ya maida aljihu. Ya dubi dan uwan shi yai murmushi ya ce, “Gata nan zuwa, kayi hakuri da shishshigi na, I just dont want to loss you, as I lose Ameenu! (Bana son rasa ka, kamar yadda na rasa Aminu) kuma na rantse idan ka cigaba da azabtar da kanka kai ne da wahala, in ma dukanta ne ka yi, amma ka ke tunawa a kullum duk laifin da kake tuhumar ta da shi, bata aikata ko daya ba, zargi kawai kake kuma wallahi in baka yi wasa ba zaka yi nadama mara amfani. How much do you like this story? 5/16/22, 20:23 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *✍� SIRADIN RAYUWA✍�* Book four *@Takori* Page🔟 Shikam ya shiga uku, wai meyasa kowa ya budi baki sai yace zai yi nadama a kan Intisar? Bai taba yin nadama a rayuwar sa ba, kuma har abada ba zai yi ba! Ita ce dai ya kamata a gayawa wannan. Intisar din wace ce? Wannan daya rike a hannun shi tun tana jaririyar ta? Wannan da ya ci kashin ta ya ci fitsarin ta, yasa mata feeder ya cire mata pampers itace wata mutum da zai yi nadama a kan ta? Yayi murmushi cikin takaici mara misaltuwa ya bude baki don baiwa Najib amsar da ta dace da shi, babu shi babu alamar sa. Nitsatstsen takunta ya jiyo tana saukowa daga saman bene, bai san daliliba kuma ya samu kansa cikin gigicewa da dimaucewa. Wannan tsohon son, wannan tsohuwar kaunar da an ka ce bata taba gushewa sai dai masoyan su gushe, to balle su da suke ras, a bisa ganiyar kuruciyar su. Wai wannan Intisar din Aunty Amarya ce yau ake lika mai yana cewa baya so! Intisar din shi da baya hada kaunar ta data kowa a rayuwar shi. Intisar din da ke zuwa cikin mafarkin sa, tsayuwar sa, zaman sa, tafiyarsa da duk wani alamari da yake gabatarwa. Intisar din da zuciya ke kuka domin son ta, gangar jikin ke azabtuwa domin kaunar ta, yawun baki ke kafewa, gudun jinin jiki ke daskarewa, tunanin shi da hankalin shi gabadaya ke gushewa a duk lokacin da yaji sassanyar muryar ta. Wannan murmushin, wadannan abnormal lumsassun idanun, wannan takun mai kamar na mage catwalk, wannan da wancan, kai everything about her that drives him crazy idan ya bar su a yau, shikenan? Sai ya juyo cikin wani irin slow motion da yafi kama da umarnin zuciya zuwa abinda take matukar so. To itama din kallonshi take, cikin wani yanayi na mamaki da rashin abin cewa. Suka yiwa juna kuri da ido, kowanne na kokarin gano boyayyen sirrin da ke cikin zuciyar dan uwansa. Ba shakka ta ga abubuwa da dama cikin kwayan idanun shi; bayan ciwon so da ya illata su, akwai rashin yarda, tuhuma, zargi da yanayin nan na yaya zan yi da son ki? Ta dai tabbatar bazata iya jure ganin irin wannan kallon na zargi da yake mata ba sai ta juya masa baya, a yayinda hawayen da take tattali suka samu yanchin kan su. Ta daga kafa da niyyar hawa bene domin komawa inda ta fito amma ina! Kafar tace bata san wannan ba, bata amince ba. Wannan Ya Faisal ne fa? Har yau, har gobe wannan Yayan ne da babu kamar sa, Yayan da zata iya sacrificing (sadaukarda) komi nata domin farin cikin sa including rayuwar ta. Shine yau cikin wani tsohon burin daya dade da shi, amma ta kasa taimakawa wurin samar da shi a gare shiashe kenan ita ta cika butulu, dan adam mai manta alkhairi, kaza ci ki goge bakin ki.. ta sake girgiza kai da karfi kamin ta samu kanta zube a gaban shi da dukkan guiwoyin ta. Kuka take na fitar hankali, kuka irin mai gigita duk wani mai imani, kuka take irin mai motsa zuciyar duk wani mai sauraron ta balle Faisal? Ya dira hannuwan shi duka biyu a bangon da ya ke jingine cikin muryar da ta razanata, ya ce, “Enough .. is enough Intisar! Ba tun yau ba ai nasan so kike ki kashe ni, kamar yadda kika kashe min Ya Ameenu? To amman wallahi ko zan mutu bata dalilin ki ba; baki isa ba, kin yi kadan ba a haife ki ba har yau ko wacece ke! Uwa ta ta ce idan kika sake zubar da hawaye domi na bata yafe mun ba, wato tunda kin kasa kashe ni shine zaki sa bakin uwa ya lalatani? Abinda bata taba gani ba sune suka zubo a yau. Yayi kokarin kau da fuskar sa don kar ta gani, don a ganin sa ba karamin ci baya bane Intisar taga hawayensa, hawayen ma domin ta. Kenan ta yi galaba a kansa, kenan shima ba zai iya controlling zuciyarsa ba kaman Alameen in dai a kan Intisar ne? Sai yayi saurin juya mata baya tare da saurin sanya hankici ya share idon sa amma ita din bata fasa kukan ta ba har da sheshshekar da ke kara kona masa zuciya. Ta kama kafarshi ta dama, wani irin karaya, da ya ji zuciyarsa tayi shi kansa yayi mamaki, hakannan kalma ko daya ta kasa fita bakinta, yace sakar min kafa da wata murya tamkar ba tashi ba. Ta ce in na sake ka ai ban gama cin ribar rayuwata ba, ni fa mayya ce, ko ba haka a ke ce muku ba? Don haka in kaga na sake ka Ya Faisal to nima bana numfashi. Kisa kuma tunda na rigaya na fara akan me zan bari? Bayan barin ba zai shafen wannan dattin na baya ba? Ya yi murmushin da bai shirya ba, ya ce haka ne? To ki je ki kama kurwar wasu man, dole sai tamu? Ta share hawayen da suke zubo mata tace ai baka sani ba, takun ce tafi ta kowa gardi. Kuma abinda baka sani ba shine mu mayu in muka fara cin daya a gida, bama hakura sai mun cinye sauran duk. Don haka kai ne babba a yanzu, ta kanka zan fara kenan? Sannan in gangaro Nasir, in iso Daddy karami, in gangaro in dawo Faruk sannan Yasir. Sai in koma kan Idris da Furkan. Shima Najib din ba don na koshi ba, sai don yar uwata da ke samu tana lasa sannu a hankali kamin shima ta kayar da shi gaba daya. Mutun daya kawai zan bari shine Khaleel shima a bisa dalilai biyu; Na farko kurwar sa ta mun kankanta, makale mun za tayi a makogaro. Na biyu kuma ina da burin saka masa abokantakar kurucciya; shi abokina ne, dan uwa na ne, abokin shawara na ne. Cikin halin kunci, dadi, farin ciki da ukuba da na kasance a raynwa, bai taba juyan baya ba, bai taba goranta mun ba. Bai taba daina so na ba kuma bai taba nunan ni bare ce a gare shi ba. Ta cika mishi kafar ta mike da gudu ta yi sama da hawayenta da basu bar ambaliya ba. Amma sabida zurfin ciki irin nata sai ta rakabe tayi kukanta mai isar ta ta share idonta, kana ta lallaba ta je ta kwanta a gadon ta. Idan tace barci ya ziyarci idanunta a yau ita kanta ta san karya ta ke. Wani irin masifar son Faisal da bata taba ji ba ke yagalgala zuciyar ta. Ta kudundune a cikin bargonta tamkar curin alkaki. Gaba daya jikinta kyarma yake kamar ana kada mata gangi, haka a take wani irin sanyi mai huda bargo ya shiga keta tattausar fatar ta zuwa cikin jikin ta, kamin dan lokaci wani zazzafan zazzabi ya rufe ta. Don haka koda tayi sallar Asubahi bata iya ta cigaba da lazimin da take yi ba har zuwa wayewar gari ba; lallabawa tayi ta koma cikin bargonta da take jin da shi da babu duk daya ne a gareta, domin bai taimaka ba ko kankani wajen rabata da wannan azababben sanyin da take ji. Wajen karfe bakwai na safe Hidayah ta shiga jan kafarta wai ta tashi suyi mata rakiya bakin mota zasu tafi. Cikin kankanuwar murya ta ce ki yi hakuri, akwai barci mai yawa a kaina Allah ya kai ku lafiya. Muma nan da next week na ke jin zamu taho Abujan, safe journey. Hidayah tayi murnushi kawai ta juya tana sauka daga matattakalar bene, tana ta korafin zurfin ciki irin na yar uwarta, ga dai damuwa fal a bakinta amma ba zata taba bude baki ta fadi ba. *** A Lagos A birnin Ikko, cikin maaikatar matatar mai ta kasa (NNPC) Engr. Faisal Bello Makarfi ne jingine jikin tagar ofishin sa yana kallon alumma cikin motocin da ke yawo bisa titi, freely, babu abinda ya dame su. Har yau ya rasa sukunin zuciyarsa ya kuma kasa yankewa kan sa hukunci. Babu abinda yake tunani kamar kalamun Intisar gareshi a daren jiya, da irin kukan da ta dinga yi a gabansa. Ya ji zuciyarsa a karo na farko tana mai kalubalantar sa musanman in ya tuna abubuwanda Hajiya, Aunty Saratu da Najib suka ce da shi. Ya dace ya yiwa Intisar uzuri cikin alamarin ta, me zata iya yi akai? Me ta yi na hakika wanda ya zamanto cin amana, ko yaudara? Na farko dai ta so Alameen a sanda bata da kowa, ya nuna kulawa da damuwa da rayuwar ta a zuwan dukkanin su basu san junansu ba. Baya da haka ma wace diya mace ce zata yi arba da Alameen Bello, har ya furta yana son ta tace bata son shi? “Babu! Wannan karya ne!� Shi kan sa ya sani wannan a cikin jinin Alameen ne, yana daga cikin baiwarwakin da Allah yayi masa watau farin jinin mata, tun yana sakandire babu irin damben da yammata basa yi a kan shi, balle a lokacin da yake cikakken mutum? Hakannan ya san Intisar tana da wani hali na girmama duk mai kaunar ta, da kaunar duk mai kaunar ta. Ta so Alameen a cikakkun shakarunta na teenage a lokacin da ta san menene so na hakika kuma mece ce kauna? Tana kaunar sa matsayinsa na Yayan ta mai sonta, mai kulawa da ita da alamarin ta, a matsayin sa na Yayan da suke uba daya. Sabanin Alameen da ya zo mata a matsayin wani bako da bata sani ba. Mutuwa dai guda daya ce, sai dai hanyoyin ta yawa garesu. To hanyar mutuwar Alameen ta kasance hakan, akan turbar cika burin zuciyar shi na so da kaunar Intisar amma ba Intisar ce ta kashe shi ba. To ta kashe shi a kan me? Bayan shine kadai wanda zuciyarta ke so da kauna? Wani kishi kuma ya zo ya tokareshi a kahon zucci. Dai-dai lokacin da Tajuddeen ya bankado kofar shi ya shigo. Ya juyo da sauri ya dube shi yayinda shi kuma ya watsa mai katunan da ke hannun shi a fuska, ya ce meye haka na ke shirin gani? Faisal are you in your full-sense? (Kana cikin cikakken hankalin ka) Ya russuna ya dau daya cikin katinan daya watso mishi, katin gayyatar auren su ne Ronke ta bugo take rabawa cikin maaikatar inda itama nan take aiki. Yayi murmushi cikin bagararwa yace to meye abin mamaki? Ba ni na ce ina sonta ba? Ya bishi da kallon ya ga mahaukaci ya ce ko ka san Ronke ita ta kashe mijinta da hannun ta, don kawai ta samu damar auren ka? Yayi dariyar shi mai ban shaawa data kara kular da Tajon ya ce to ai ka ji shi bata son sa, shi yasa ta kashe shi, ni ko akan me zata kashe ni? Ni da ta ke so shekaru dai-dai har takwas? Tajuddeen ya mike yasa hannun shi cikin aljihu yana girgiza kai yace alright, Allah ya baka saa Faisal ya fita bayan ya bugo masa kofar ji kake garam. Yayi tsaki a ransa yace kaga mun mutum da daukar dala ba gammo. A karshen satin ya iso gida cike da zullumi, ya kara ramewa, ya kara lalacewa alamun rashin cikakkar nutsuwa ya game koina a tare da shi. Babban zullumin sa yau ne rana ta karshe da Daddyn ya deba mishi don jin amsa ta karshe daga gareshi tun bayan fatattakar zancen Ronke da ya yi. Ya tabbatar mai daga ranar in bai zo mai da wata kwakkwarar madafa ba auren shi da Ihsan karshen satin ya tabbata, zai daura, duk da ita Ihsan din bata nan ya jirata ta dawo. Idan har akwai abinda yafi daga masa hankali a rayuwa to wannan maganar da Daddy ke ikrari ne. Yana zaune falon Aunty Saratu wadda ke ta fama da fitinar Alameen karami dake ta fatali da komi na falon wai shi a kai shi gidan Baba Najib, ko kallon inda yake bata yi ba, balle ta bashi lemu ko madarar da ta saba bashi idan yana cikin bacin rai don ita yanzu Faisal ya daina bata tausayi haushi kawai yake bata. Wai Intisar din ta, ita ce ake lallamin Faisal ya aura yana bijirewa kamar an ce da shi rasa masoyi ta yi? Tayi kwafa ta ce sai ka isa falon ya fito, tun dazu dama ya ke tambayar isowar ka. Ya mike tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, ya nufi sassan Daddyn zuciyar shi na harbawa. Gwarzon Uba, namiji sauran mazan jiya, na zaune cikin lallausar carpet din karamin falon hutawar shi yana sauraron labarum duniya daga muryar Amurka (Voice of America), a gefen shi Hajiya Nafi ce tana ninke wasu kayan Daddyn da aka wanke. Faisal yayi sallama cikin muryar shi mai cike da ladabi da rashin kuzari, gaba daya suka amsa mai sallamar tare da kai duban su gare shi. Cikin su babu wanda zuciyar shi bata motsa ba da ganin karin ramar da yaron ke tayi a kullum, ya kasa hutar da zuciyar shi, ya tsayar da ita wuri daya ta samu abinda ta ke so. Cikin yayan su baki daya basu taba ganin jarumi kuma mai fin karfin zuciya irin Faisal ba. Ga mamakin sa, abinda bai zata ba Daddyn murmushi ya sakar mishi mai kwantar da hankali ya ce bakin Ikko ne, sai yanzu aka iso? Ya dan ji dadi shima ya yi murmushin, kansa a sadde ya ce eh wallahi, an samu delay ne na isowar jirgi mai zuwa Abuja, da nace zan bari sai gobe to kuma sai naji duk hankalina yayo nan din suka cigaba da hirar su kan aikin shi da karin girma da ya samu, wanda Daddyn ya gani a (television) daren jiya cikin labarun NTA na kasa. Ko kadan bai sako zancen da Faisal din kewa dari-dari ba. Sai da Faisal din yace kwanannan Nigeria zata yi exporting crude oil (fitar da man fetur) zuwa Belgium kuma shine wanda alamarin ke hannun sa, don haka cikin sati na sama yake sa ran tafiya Belgium din zai yi a kalla sati biyu domin yin wasu bincike. Daddy ya maida fuskar shi ta koma ta manyantaka kamar yadda yake yi a duk lokacinda zai masu magana mai muhimmanci ya ce Faisal cikin babbar muryar da ta kada yayan hanjin sa ina maganar mu ta kwana? Ya kara sunkuyar da kai ya rasa bakin magana sai zufa da ke ketowa takoina a sassan jikin shi. Hajiya ta yi tsaki ta ce kaima da laifinka Baban su Khalil. Har yaushe zakayi ta biye mishi yana yi ma yawo da hankali sai kace shi din karamin yaro ne? Ya daga mata hannu yace babu ruwan ki, ai hakkin shi nake son in bashi kuma Allah shine shaida na Faisal ko a lahira bani da hakkin ka. Maganar wannan Bayerabiya na soke ta kwata kwata har abada, koda wasa kuma ko bayan raina kada ka sake tada ita. Dr. Rehab ya aiko neman auren Ihsan a hannu na don haka rana irin ta yau, Jumaa, Insha Allah zan daura auren ka da Saratu Intisar, Ihsan da Rahab, Hunainah da Hashim kamar yadda iyayen su suka danka mini. Don haka tashi je ka. Bana bukatar wata kalma daga gare ka, ba lallashin ka nake ba umarni ne, its order! Saratu nada watanni ukku dazata yi kamin ta koma makaranta don haka ba Belgium ba, in ma birnin Sin ne zaka tafi, amma kafarka kafarta. Duk abinda kuke ciki tun-tun-tuni na sani ba ban sani ba, illa bana so nake shiga personal life din ku ne. Na dauka kai da kanka watarana zaka kawo mun maganar kana son auren Intisar komai daren-dadewa? Ban sani ba, ashe kai tuni ka canza soyayyar da kiyayyah? To don Allah karewar kiyayyah Faisal idan na baka auren Saratu ka yanko min ita gunduwa gunduwa ka kawo min gabana, sannan ne zan san baka son ta! Ka gane ko? Yallah! Kana iya tafiya ka fara shirye-shiryen ka daga yau ko kwandalar ka bana nema. Bai ce komi ba, ya taso ya fito ko ganin gabansa baya yi, bai kuma kara kula kowa ba a gidan, washegari karfe sha daya na rana a Lagos tayi mishi, week-end da yazo da niyya ma ya fasa yi musu Intisar din tazo ta yi masu. To ai kuwa kamar ya sani, a ranar yar halak din ta dira a gidan ita da yar uwarta, murna wajen jamaar gidan abin baa magana. Ta kankame Mamanta tana dariya ta ce ke Baby na sai yaushe zaki girma ne? Dube ki kin zama cikakkar lady abin alfaharin kowacce uwa, shin me Maman Hunainah take baku ne haka? Ta kyalkyale da dariya ta ce, “Kin san Allah Mamar mu ba abinda take

Chapter 36 of 38