Share this page
mata ne, su da suke nema. Ta kai hannu ta dafa kan yarinyar tana share mata hawaye da hannunta, ta kuma sauko daga kujerar da take zaune ta zube gwiwoyinta a gaban Intisar din kamar yadda ta yi, ta ce, “Ki yafe min don Allah Saratu, ki yafe ni Saratu, bani da kalaman da zan yi amfani da su wajen nuna miki dimbin nadamata kan abinda na yi miki. Abinda zan iya cewa kawai shine kiyi hakuri ki yafe min hakika nayi nadama, na yi nadama mara amfani a kan ki Intisar. Kada ki dubi tsakanin ki da yaya na ko abinda suke miki, wannan hakkin ki ne. Ki dubi girman Allah da manzon sa ki yafe mini. Kuskure ne nayi, nasan kuma babu wanda yake sama da shi. Kiyi hakuri da abinda Faisal ya ce da ke, ban san me ye ke damun sa ba. Hajiya Hadiza ta shigo, tana tura troller kwandon kayan abinci zuwa dining da ke gefe guda a falon ta ce wane irin abu ne haka Hajiya? Don Allah ki koma ki zauna. Ta ce, “Aah Hadiza, ki bar ni in roki gafarar Intisar kawai, ko kwanta mata ne sai in yi, in ba haka ba hakkin ta ba zai bar ni kwanciyar kabari ba. Intisar ta kama hannun ta ta maida ta bisa kijerar ta ce shikenan Hajiya, Allah ya yafe mana gaba daya.� Shiru ta yi tana mamakin sanyin zuciya irin na yarinyar, tana mamakin kaunar da take wa yayanta. Ta na mamakin hakuri da yakanar ta da daukar alamuran duniya da sauki. Bata zaci ko a mafarkin ta yarinyar zata taba yafe mata ba. Ta tabbata ko don wannan halayyar tata dole kowa ya sota, dole alumma su kaunace ta, dole ta zamo a bar so ga duk wani da muamala ta hadata da shi koda na second guda ne, hakika a yau ta kara tabbatar wa da cewa da a ke ita din yar baiwa ce. Ita kuwa Intisar ta yi laakari ne da fadar Ubangiji (SWA) mai cewa hakikah Ubangiji mai afuwa ne, kuma ya na son bayin sa masu afuwa. Bata duba Alameen ko Faisal ba, ta yafe mata saboda Allah. Ta yi tunanin to me ya sameta bayan kiyayyar da ta ke nuna matan? Babu komi sai alheri. Ita ce dai har ta dangana da asibitin masu hankali. Amma ita ai gata da lafiyar ta sumul kalau a gaban iyayen da aka tsaneta don bata da su. Sun hadu suna cin abinci gaba dayan su har Abban Hunainah, Najib da Hidayah da kuma Khalil da suka zo tare da shi. Hajiya Hadiza tace wai ina Faisal ne a gidannan? Hajiya tace rabu da shi mutumin banza, na rasa inda ya dauko wannan bakar zuciyar kamar tsohon kuturu, ni wallahi har fargaba nake Jumaar sa ta zo ya zo garin Abuja, ya zama wani masifaffen karfi da yaji, abu kadan su Furkan zasu yi ya rufe su da fada in banda Alameen karami babu wanda ya ke ragamawa a gidannan, ban sani ba ko gamo yayi cikin kabilun nan na Lagos don ba kyau ne da su ba. Hidayah ta tuntsire da dariya har tana kwarewa, Najib yayi saurin cika ruwa a kofi ya mika mata yace kin gani ko? Hajiya shiyasa baa son magana in ana cin abinci. Baban Hidayah ya dago ya dube shi yayi murmushi ya ce Najib ka na ji da matar nan ta ka, baka san tafi kowa fitina a gidan nan ba. Ka rage rawar kan nan da kake a kan mace, in ba haka ba zata raina ka. Daga shi har Hidayan sun ji matukar kunya Hajiya ta ce, “Umh-umh, kyale sa ya kula da matar sa, dubi halin da ta ke ciki fa ai dole a kula da lafiyar ta.� Hajiya Hadiza da bata san tsamar da ke tsakanin. Faisal da Intisar ba ta dube ta ta ce, “Ke tashi maza ki je waje ki nemo man Faisal, ya zo ya ci abinci.� Hajiya ta ce, “Ba zai wuce bencinnan na wurin masu gadi ba, ki ce da shi ya zo ina kira yanzun nan.� Sai da kirjinta ya harba kamar ta ce wayyo Allah! Ta mike talau! Juwa ta kwasheta saura kadan ta kai kas, Hunainah ta tallafe ta tace yi a hankali, kujerar nan zata tade ki Najib ya dago ya dubesu yayi murmushi kawai ya dauke ido a kan su. Ta fita cikin kasala da rashin kuzari amma sai ta labe a hanyar zuwa wajen bata je din ba, a ranta cewa take lallai ma ya Faisal! Har yau bai gama sani na ba, ba dai ni ce baya son gani ba, ni mujiyar sa ajalin sa to nima bana son ganin sa ko hanyar daya bi nima na daina bi. Hawayan da basa wuya a idanunta suka zubo. Ta sa gefen rigar ta ta share ta dawo falon ta zauna a mazaunin ta tace yace ya na zuwa. Shiru shiru babu shi babu alamar sa har suka kare cin abincin. Abinda kunnuwanta suke jiyo mata Hajiya na baiwa mamarta labari ta kasa gasgata shi, hakan nan ta kasa amincewa da abinda ta ke jin. Wai Faisal ya kawo wa Baban shi mata Bayarabiya kuma bazawara mai yaya uku da suke aiki tare a NNPC wai ita Ronke yace nan duniya ita ya ke so, su kuma sun ce wannan auren sai bayan ran su. Hajiya Hadiza ta yi dariya ta ce, “Ina ruwan kurucci dangin hauka. Kin san idan Allah yayi ma wata baiwa baka gani, sai dai wani ya gane maka. Amma ina mutum kaman Faisal ina auren bayerabiya?� Najib ya ce, “To yaya zai yi Hajiya? Wadda ya ke so bata son shi, ba sai ya je inda ake son shi ba?� Ya fada ne kamar da biyu, idanun shi a kan Intisar, wadda cikin sanyin jiki ta aje cokalin da ke hannunta ta tashi ta yi dakin su da ke saman bene. Ta sa mukulli ta rufe kofa ta tafi gaban taga ta tsaya kawai, hannayenta sarke a bayanta, wasu irin zafafan hawaye suka zubo a kumatun ta. Kamar an ce da ita juya nan; ta kalli harabar gidan ta tagar. Daga can ta hango shi cikin motar sa porsche kafarsa daya a motar daya a waje, sanye cikin lallausar shadda yar Indonesia ruwan kasa-kasa dinkin Tazarce, fatar agogon roled da ke hannunshi ma ruwan kasa kasar ce haka takalmin fata na kasar Italy dake kafarsa ruwan kasa ne mai duhu. Ya rame ainun hakannan kyawawan idanunshi masu narkar da zuciyar ta sunyi ciki sosai ya kara fari, haka lallausan fatar shi ta kara gogewa sosai fiye da sanin da ta yi masa a baya. Waya ce yake amsawa cikin lumshe ido, da gani zaka san kalaman da a ke gaya mai cikin wayar ba karamin dadi su ke mai ba, don har kwantar da kujerar motar yayi da alama dai cikin matsanancin nishadi yake. Zuciyar ta ce ta shiga harbawa da sauri da sauri don tuni ta fassarawa kanta koda wa yake maganar kawai Ronke Adeyemi. Ta ja murfin tagar da karfi ta rufe garam, tare da zuge labulen gaba daya, ta durkushe a nan ta yi kukan ta mai isar ta. Ta tabbata a yanzun kam Faisal ya daina son ta! Duk wani so, duk wata kauna daya ke mata ya zagwanye sakamakon rashin maida mishi martanin dimbin soyyayar da ya shekara yi mata. Ronke yake so tun-tuni har yanzu kuma bai daina ba, har ta zama bazawara uwar yaya uku still ya na son kayar sa. Ita kuma haka Allah ya so da rayuwar ta? Ba zata taba cin riba a soyayya ba. Allah Sarki! Wai yau ita Intisar ce Faisal ya ke neman maraba da ita. Ita din da a da, baya da abin so da gani tamkar ta. Ita din da a da, in bai gani ba baya iya nutsuwa amma a yau rashin ganin ta shine nutsuwar sa, kwanciyar hankalin sa kuma abinda yake matukar so. How much do you like this story? 5/16/22, 20:23 - Ummi Tandama😇: ______________________________ *✍� SIRADIN RAYUWA✍�* Book four *@Takori* Page9️⃣ Hunainah ta dafa kafadun ta, ta dago a hankali ta dube ta, sai ta rungume ta da karfi tayi kukan ta mai isar ta a kafadun yar uwar ta. Ta ce, “Hunainah ni kuma haka Allah ya so da ni? Soyayyar yayan Daddy ne zata kai ni kabari na. Hunainah ya Faizal ya daina so na, leka ki ga da Ronke yake magana, ni kuwa ko gani na baya son yi.� Ta ci gaba da kuka sosai yayin da Hunainar ta shiga taya ta suka yi tayi kamar wasu yaran goye. Ta ce, “Ni wallahi zan je yanzu in bawa Ya Faisal hakuri, in gaya mishi hakikanin abin da ke zuciya ta. Idan ya auri Ronke din nan Allah Hunainah mutuwa zan yi nima in bi Alameen sai mu yi auren mu a can.� Hunainah ta yi murmushi duk da hawayen da ke zuba mata, ta tabbata yar uwar ta bata cikin hayyacin ta, soyayyah na neman zautar da ita ta ce, “Aah, baza ki je ki bashi hakurin ba, me ki kayi masa? Laifin da kasan kayi shine kake bada hakuri a kai amma ba wanda baka san ka aikata ba. Ai ko Allah baya kamamu da laifin da muka yi a bisa kuskure. Mutun mai laifi, shi yake kama kansa da kansa ta nuna cewa ya san da wannan laifin. Ki bar shi ya je ya aure tan mana, sai me? Sai aka ce daga kansu babu sauran mazan aure?� Ta share idonta tana murmushi ta ce, “Akwai maza da yawa a duniya. Amma a zuciya ta babu kaman Faisal! Ni kadai nasan shi ko wanene? Alkhairin sa da karimcin sa masu yawa ne a gare ni. Yafi karfin komi a waje na. Ina tabbatar miki Faisal ya fi so na da komi na duniya. Duk wannan son da kika ga Alameen ya yi mini, wallahi wallahi Faisal yafi shi so na. Illa cewa shi Alameen baya iya boye abinda ke zuciyar sa kuma baya iya controlling din ta akan abinda yake so. Sabanin Faisal da ya kasance mai juriya da karfin zuciya, ta yadda ko da a ce son zai kashe shi zai iya jurewa ba tare daya nuna ba. Ki taimake ni Hunainah in ganar da shi irin asalin kaunar da nake mishi yafi gaban duk wasu kananun zargi daya ke yi a kaina. Ko me zan fada niki game da ni da ya Faisal ba zaki gane ba, da dai a ce kinsan irin rayuwar damu kai a baya ne. Abinda nake so kawai ki gane shine Faisal, wani mutun ne precious wato mai darajja da kima a zuciyata da girman sa da darajar sa da na ke gani ya zarta na kowa in kika dauke Daddy da Antina. Ronken nan da kika da kika ji ana ambato ba son ta ya ke ba, zai aure ta ne kawai don ya rama tozarci da cin amanar kaunar da yake tunanin nayi mishi� Ta sa gefen dankwalinta ta share idon ta, ta fyace hancinta ta yi murmushi cikin takaici ta ce, “Hunainah, a lokuta da dama wasu alamura na rayuwa kan zo wa mutum ba a yadda ya tsammana ba. Na so Faisal tun yana a yaya na jini haka a gaba dayan rayuwata son shi nake ni din ban sani ba. Soyayyar Alameen irin soyayyar nan ce da ke shigar mutum farat daya, ta rugurguza duk wani tunanin hankali da ya mallaka, kasancewarsa wani irin mutum na daban a cikin alumma, komi na shi ya kasance in style yadda babu zuciyarda ba zata kwadaitu da kasancewar sa abokin rayuwarta na har abada ba. To haka ta ragargaza min zuciya ba tare da tsammani na ba, wanda a lokacin ban taba tunanin zan so wani da namiji a duniya bayan wannan ingantaccen son zumuncin da na ke wa Ya Faisal wanda a wani bangaren ba haka ba ne; so ne na soyayyah, na shaawar komi na shi. Sabanin kaunar Alameen mai shigar mutun farat daya, soyayyar Faisal a hankali ta shige ni, ta bi jinni da tsoka, kasuwa da bargon jikina tun ban san kaina ba, ta yadda ko muryarsa na jiyo daga waje jikina ya fara tsuma kenan, haka zuciyata zata fara rawa ina dai kokari ne ina boyewa saboda Anti, da sanin cewa hakan ba dai-dai bane haramun ne, haramun din ma wanda Allah ya yi kakkausan hani a kai. Shima kamar ya san hakan, sai ya tafi. A lokacin ne na samu nayi jinyar zuciyata har ta warke. Sai kuma Alameen ya zo, shi kuma da wata irin masiffafar soyayya mai shiga rai a lokaci daya. Duk da haka ina kokarin in tuno Faisal da dinbin karimcin sa. Ko a sanda na shiga wannan daumuwar da kukan zuci, bayan fitowar mu daga asibiti, kuka kasa gane hakikanin me ke damuna har kuka yi fushi kuka ce zaku tafi? Wallahi ba komi bane damuwa da halin da Faisal ke ciki ne, damuwa da alamarin sa ne da ganewa da nayi ashe shima irin son nan da nake masa ya ke yi mun. A hakan sai na samu kaina cikin halin dimuwa da rashin abin yi. Duk da cewa kaunar Alameen ta fi rinjaya na alokacin amma na tuna Faisal, na tuna alkhairinsa, na tuna karimcinsa, na tuna kyautayin sa da jin kansa a gare ni. Babu abinda mahaifiyar sa bata ce da shi a kaina ba, babu irin wulakacin da bata yi masa a kaina ba amma yace ya ji ya gani shi mai kaunar mu ne da ni da Anti na. Sanda ya tambayi Hidayah cewa wai ko zata iya aurensa, baki ji yadda na ji a raina ba. Na ji tsoron in tace eh, to ni ya zanyi da rayuwata, yaya zan ji a raina? Sai na gode Allah da tace aah duk da nasan ni din bazan hada yanuwa biyu in aura ba. Ke Hunainah in nace zan gaya maki matsayin Faisal a zuciyata sai mu kwana mu wuni ban gama ba. To don Allah meye laifi na a nan? Ta ina naci amana? Yaya yake so in yi da raina? In banda ke ba wanda zan iya budar baki in gayawa zuciyata Hunainah, ki taimakeni in ganar da shi abinda ba zai taba ganewa ba, ba tare daya saurare ni ba. Ta cigaba da kuka mai motsa zuciyar duk wani mai sauraron ta. Hunaiah ta ce, “Duk na ji, amma wallahi baza ki je ki wulakanta kanki a gabansa ba. Idan kika gaya masa hakan a yanzu cewa zai yi don kin rasa Alameen ne ba zai taba yarda da ke ba. Ki barwa Allah alamarin ki roke shi zabin alkhairi cikin rayuwar ki.� Hakika nasihar yar uwarta tayi tasiri a gare ta, ta samar da nutsuwa a zuciyar ta. Ta ce Allah gani gare ka, na baka zabi ka zaba mun da mafi kyau. To a gaba daya kwanaki biyun da su Hajiya suka yi a gidan bata kara ganin Faisal ba. Akwai wani abokin sa Tajudden mutumin Kano a unguwar Yan kaba can wajen sa ya ke wuni, tun safe yake ficewa bai taba cin abincin gidan ba. In banda Najib, Hidaya da hunainah babu wanda ya san me su ke ciki. Haka Najib ya yi iyaka kokarinsa don ganin Faisal din ya zauna ko na awa daya ne a gidan don su dai-dai ta da Intisar din amma ya nuna baya bakata kai ko son ganin ta ma ba ya yi, ya matsu lahadin ta zo su tafi don dai baya son iyayen su tuhume shi ne amma da tun jiya ya yi tafiyarsa. Hidayah ta tabo Intisar da kafarta tana nuna mata Hunainah data rakube a gefe tana amsa waya sai kwasar dariya take cikin nishadi, ta ce cikin rada, “Wai wannan saurayi ta yi ne?� Ta yi murmushi ta ce, “Ke sai yanzu kika lura? Ai jiya abinda ta kwana yi kenan sai da na sa tissue na toshe kunnuwa na don dariyar ta ta hanani barci kamar wata shashashar madina� Hidayah ta ce, “Ina ruwan farin shiga� Suka yi dariya suka tafa. Ta sha jinin jikinta, ta dan juyo ta kalle su suka juyar da kai suna wata hirar daban, ta juya ta cigaba da hirar ta. Intisar ta ce, “Tunda bata ce miki ba, kyaleta ki bita da hakan ita da kanta zata fada miki, ko ina zaa kai karatun likitan kuma oho! Wannan soyayar ta irin mai sawa mutum ya shiriri ce din nan ce, kwata kwata fa ko wani kwakkwaran kallo batai masa ba, a waya kawai ya wargaza mata planning to ina ga suna tare?� Suka kara kwashewa da dariya. Ta dai tabbatar da ita su ke, sai ta fita ta bar musu dakin. Baa jima ba kuma suka ga ta yi kitchen shiru-shiru bata dawo ba ashe girki take delicious, kamshi ya cika hancinan su a take yawun mai cikin ya fara tsinkewa ta ce, “Aa ah, wannan yarinya wa take wa girki? Don Allah zo muje tsurku� Intisar ta koma ta kwanta tana cewa, “Ni ba irin ki ba ce, kina abu babu jan girma shiyasa ta rainaki� Ta ce “Ai wallahi sai na je, kuma sai na ci� Tana taku da kyar da kyar ta nufi kofar fita sai taba Intisar dariya. Hunainah a kichin tare da Lami mai aikin su tana taimaka mata, ta hada abinci kala-kala irin su (Badadis, ruzz wa dajaj, ful wa tamis, mabkabkah, firakh, shawarmah da pizza) ta killace a cikin wermers. Hidayah ta shiga bubbude wermers din tana sa cokali tana kai loma, da gudu Hunainah ta zo tana rufewa, ta ce, “Me kike nufi? Ni bani da kwano a gidan ko me?� Ta ce “To dama ina kwanon yake? Na dauka tunda anyi miki kayan aure an sallame ki daga gidannan?� Ta ce “To wallahi sai naci abincin nan tunda ba ke kika yi ba, solobiyar banza ba fuss ba ass rakiyar mata duniya.� Intisar dake shigowa tayi dariya, ba tun yau ba fadan Hunainah da Hidayah na bata dariya, idan suka fara kamar sa cinye junan su fada dai irin na sakonnin juna da baya karewa. Ta zo ta shiga tsakani ta ce, “Ke Hidayah rabu da wannan ki debi wancan na cikin tukunya tace a kan me? Ga na saman tukunya zaa ce inci dandakakke? Shi wannan din na wanene na san dai Daddy baya cin abincin larabawa� Ta ce, “To neman rigima kike, zan kai karar ki wajen mijin ki, haka kawai kizo gidanmu zaki fitine mu a wane dalili?� Hadayah dai ta rantse sai ta debi abincin nan don bata ga amfanin sa ba, kuma miyanta ya tsinke dan cikinta yana ta motsi yana tsunkulinta shima yana so ya ci. Ita kuma Hunainar kaman tayi kuka ta rantse baza ta diba ba. Rigima har kunnen Maman da Hajiya da ke zaune a falo, Najib bai yi magana ba kar ya yi a ce yayi rashin kunya, amma shi ma a ransa ya rantse sai matar shi ta ci abinda ta ke so. Dan haka suna falon ana ta mayarwa da maman zance ya zare jiki ya je ya kwashe warmers din duka ya yi dakin da aka sauke su shi da Faisal, kana ya fiddo waya ya kira matarsa ya ce ta ci son ranta. A can falo Hajiya Nafi ta ce “Don me ba zaa bata ba? Ku baku san rigima irin ta ta mai juna biyu ba ko tausayin ta bakwa ji?� Intisar ta ce, “Ai an ce taci na tukunya ta ki.� Maman ta ce, “To ku me za kuyi da abincin in kun hana ta ci? Ita da zata tafi gobe ta bar maku gidan?� Intisar zata yi magana Hunainah ta kyafta mata ido ta ce “Ai abincin ba namu ba ne, bako muka yi wa.� Hunainah tana ta kyafta mata ido da take yatsun kafarta alamar tace bakon nata ne, bata kalleta ba. Hajiya ta ce tana murmushi, “Suruki muka yi? To na waye a cikin ku?� Intisar ta yi murmushi kawai, cike da kunya ta mike ta yi dakinsu, wannan ya tabbatar masu cewa bakon nata ne kenan. Hajiya ta mike jiki babu lakka, kamar anyi mata duka ta nufi dakin da su Najib su ke, tayi sallama ya bata izinin shigowa, sunyi rashe rashe bisa carpet suna kwasar gara, fuskarta kawai ya kalla ya san wani abu mara dadi na damun ta, amma ganin Hidayah sai ta yi kokarin maida damuwarta ta ce Faisal nake nema, ina yake? Yace yana can cikin gari wajen Tajudden Alhaji tace kirawo min shi a wayar ka ya nuna mata wani gefe can bisa centre table ga wayar shi can, anan ya ke barin ta, baya fita da waya. Tace duk sanda ya shigo ka sanar dani, ko karfe nawa ne. Ta juya zata fita, har ta kai bakin kofa ta juyo tace amman baku kyauta ba, wannan abincin Intisar bako zata yi, ta zauna ta shirya masa. Don son kai irin naka shine ka satowa matar ka. Wannan ba dai-dai bane sukayi murmushi su duka, don sun dago abinda ke damun Hajiyar, (ta dauka bakon na Intisar ne) ya ce, “Hajiya kada ki damu, bari in je in yo masu take-away in kuma basu hakuri tace kayya! Ba dai kamar anyi a gida ba, kuma ka san wahalar da ta sha wajen yin abin ta? Kai dai ka daina son kai a alamuranka, domin yana jawo nadama mara amfani.� Jikin sa yayi laasar da kalamun Hajiyar. Tsam, ya tsame hannun sa daga plate din ya dauki mukullin mota yace da Hidayah yana zuwa. Ya nufi pounded yam da ke kan titin Audu Bako yayo wa Hunainah take-away na sakwara da miyar egusi da naman kaza mai rai da lafiya, ya biya Mr. Biggs na Beirut Road ya sayo snacks kala kala ya kuma je captano ya sayo dankwala dankwalan kaji gasassu ya dawo gidan. Da kansa ya je ya wanke warmers din data shirya abinta ya shirya mata kayanta yanda ta bar shi ba tare da su din sun sani ba ma, don su a tsammaninsu tunda aka yowa Hidayah waya ta manta da zancen abincin. Sai karfe sha daya da rabi na dare Faisal ya shigo gidan, ya soma hada kayan sa cikin jaka don karfe shidda na safiyar washegari zasu hau jirgi mai tafiya Abuja. Najib ya zare jiki ya je ya sanar da Hajiyar dawowar sa. Bai zata ba bai tsammana ba kawai ya ji gyaran muryar Hajiyar akan sa ta sallame a dakin ta samu gefen gadon dake dakin ta zauna, fuskarta babu alamun wasa ko kankani, ta fuskance sa sosai tai ce, “To Ba-Kano, wurin ka na zo.� Ya yi murmushi ya ce, “Ka ji Hajiya, har wani dadewa nayi a Kanon da zan zama Ba-Kano? Tace oh oh, naga wai kai kullun zaga Kanon ka ke ciki da bai din ta, ko gaishe mu baa yi.� Ya ce, “Wallahi wurin Tajudden nake zuwa, ai kin san shi wannan abokin aikin nawa da ya zo ya gaishe ku a sallar bara?� Ta ce, “Allah sarki! Ashe wajen sa kazo, ba wajen mutanen da kake kwana a cikin gidansu ba, ai da ka sani can wajenshi ka sauka, da masu gidan baza su san da kai bama balle har su dinga tambayar laifin da suka yi maka kake gudunsu ko maigidan baka gaisarwa, bayan kana kwana cikin gidan sa?� Ya yi shiru, kan sa a sadde ya ce, “Kuyi hakuri Hajiya, wallahi ni ba abinda sukai min, hakannan dai yanzu nake jin bana raayin hayaniya� Ta sakar mai dakuwa da duk yatsunta goma ta ce, “Su waye masu hayaniyar, ni Uwar ka ko Uwar su Hidayah, ko ko Uban da ya haife su?� Ya yi shiru bai ce komi ba. Ta ce, “To magana ta karshe data kawo ni shine bazaka har gidan nan ba sai ka nemi masu gidan ka gaya masu dalilinka na gudunsu kamar makiyan ka, ka kuma nemi Intisar ka bata hakurin gabar da kake da ita sai kace wadda ta dauki bindiga ta harbe danuwan naka, bayan ni uwar sa ni nayi sanadiyyar ajalinsa. Yau da a ce Alameen yana raye, zai so ganin wannan yarinya kullum cikin bakin ciki da baya karewa? Kullum idanun ta kamar na mai takaba, ba don komi ba sai don kaunar ku da Allah

Chapter 35 of 38