A yau zai fadiwa Aminu “Intisar ba ‘yar saratu ba ce balle shi.�
A sannan ne kuma su Hajiya Hadiza suka fito daga mota suka yi wa harabar asibitin tsinke. Hidayah rungume da ‘yar uwarta Hunainah da fargabar halin da zasu sami ‘yar uwarsu ciki ke neman kayaswa, bata ko iya daga kafa sai jan kafa.
Hassan da yake ya san Daddy shi ya nunawa Haj. Hadiza shi zai shiga wani daki na musamman wanda a ka’ida ba’a barin kowa ya shiga sai likitoci da malaman asibiti, ya ce “nake jin itace a can dakin Hajiya, don ga Makarfi can zai shigaâ€? this is Brigadier Bello Makarfi…â€sai kawai ta kwasa a guje tun basu ankara ba.
Kusan a tare suka shiga da Daddyn tana haki kamar ran ta zai fita. Daddy bai kula da ita ba don shi kansa ba’a hayyacin sa ya ke ba, ya ji dai wani ya shigo tsammaninsa Hajiyarsu Aminun ce, ya dubi fuskar Al’amin cikin (Oxygen) wato abin janwo numfashi yayi mamakin yadda Allah ya mayas da halittar shi cikin dan lokaci kalilan, ya kara imani da mulki da ikon sa kodayake ba’a mamaki da ikon Allah, wannan wace irin masifa ce? Ya soma sheshshekar kuka kasa-kasa kafin ya tuno da abinda ya shigo da shi. Ya karisa dai-dai kunnen Al’ameen ya ja kujera ya zauna, ya kai hannu bisa sumar kanshi yana shafawa a hankali ya fara magana, muryarshi na rawa da karkarwa�
Hajiya Hadiza bazata ce ga wanda ke kwance a wannan gadon ba, don ko gani bata yi sosai, ita dai kawai tunaninta ya bata diyarta ce ‘Fatima� fakat, za kuma tayi ko menene don tserar da rayuwarta in dai zata iya koda hakan na nufin a zuke jinin jikinta ne bakidaya a sanya wa Fatima.
To sai kuma maganganun Bello Makarfi, suka dauki hankalin ta kwarai, suka kuma warware duk wani taraddadi dake zuciyar kowannen su.
“Al’ameen ka gafarce ni, na san mun yi kuskure ni da Saratu wajen boye maku ainahin kowacece Intisar, ba mu yi hakan domin mugunta ko wata manufa ta daban ba, illa domin tserar da ita daga kuncin da zata iya fadawa a girmanta inta fahimci ita ‘yar tsintuwa ce, sanin kanka ne ba abinda ya kai rashin asali ciwo. Aminu ka taimake ni ka mike ni kum in aura ma Saratu-Intisar!
Wallahi ba ‘yata bace, tsintar ta nayi a daji na kawowa Saratu. Hajiyar ka zata tabbatar maka da hakan. Al’ameen don Allah ka mike! Ka mike!! Ba abinda ya hadaka da Saratu da zai hanaku aure�
Kuka yaci karfinsa da ya ga Aminu ko gizau. Ya kifa kai jikin karfen gadon yana ta yi kamar ba tsohon soja ba. Tausayi da dadi ne ya rufe Haj. Haddizah, wasu siraran hawaye suka ziraro mata, hawayen farin-ciki da tausayi duk a lokaci daya.
Ta dibi yadda Allah Al-mussawwiru ke juya masu al’amuran cikin ruwan sanyi, ta kara amincewa lallai shi buwaya ne, gagara mithali. Sai ta matsa jikin gadon Al’ameen ta dubshi sosai. Tausayin shi da kaunar shi babu inda bai bi jini da tsokar jikin ta ba.
Wai fa wannan kaunar diyarta ne ya kayar dashi haka? Ta russuna ta barin hagu, kanta jikin gadon a kife tace.
“Kwarai Al’ameen Saratu, Intissar kuma Fatima ba kanwar ka bace kamar yadda kake tunani, ka tashi don Allah ka tausayawa Intisar da Babanka bisa halin da zai shiga in ya rasaka. Ni ce mahaifiyar Intisar. Mahaifin ta ya rasu ne tun tana Jaririya a dalilin bakin-cikin sace mana ita da a kayi aka kai daji, shine Babanka ya tsinta. Wannan shine gaskiyar al’amarin.
Idan ka mike Al’amin ko a gobe sai mu daura maku aure, in ce ko shikenan? Ba fa abinda ya hadaku da Intissar!� Ta fadi da dan karfi cikin gunjin kuka.
Maganganun har tsakar kwakwalwarsa amon su ke yawo, ya motsa kadan alamar sun dameshi, Alfered ya janyesu yace “ya isa hakanan�.
To Hadiza da Daddy sai aka koma kallon-kallo. Kallo daya yayi wa Haj. Hadiza yasan yaga mahaifiyar Saratu a yau, in banda nauyin shekaru ba zai yarda ba Saratu-Intisar din su ce wannan tsaye a gabansa ba.
Kwanaki goma abinda iyaye da ‘yan uwa ke ta gayawa Al’ameen da Intisar kenan. Har ita kanta Anti Saratu ta gigice rannan da Intisar tayi wani dogon suma kamar bata dawo ba ta shiga fada mata ba abinda zai hanasu aure don babu alakar jini a tsakaninsu. Malam Sani da Goggo Jummai ma ba’a barsu a baya ba wurin nunawa ‘yan gatannan kauna.
Haka Hidayah da Hunainah dake kwana rungume da ‘yar uwarsu a cinya, suna rokonta ta tashi ta auri Yaya Al’ameen, ta basu kulawar da yayye ke baiwa kanne, ta ji dumin Mamarsu itama. Su nuna mata kulawa da kaunar da bata samu ba na kanne mata.
Fatan Anti Saratu kawai samuwar lafiyar Intisar da likita ya ce, ‘Shock� ne kadai ya gigitata ya wargaza mata tunani. Amma a hankali tunaninta yana saisaita kuma tunda ga komi yazo da sauki, danginta sun bayyana a sanda ake tsananin bukatar su.
Ita da Hajiya Hadiza kwana suke bakin su bai yi shiru ba kullum dai zancen kenan. Cikin wannan halin Najib ya kira mahaifiyarsu a waya ya ce,
“Hajiya, kin ce zaki dawo har yanzu kaman an aiki bawa garinsu, amma yanzu ina jin ya dace ki dawo, tunda ga Aminun ki kwance a gadon asibiti ba yadda yake, bai kuma san wanda ke kansa ba?�
Ta ce cikin shesshekar kuka
“Idan ka gan ni a Nigeria to na zo ganin ku ne, amma ni da gidan ubanku har abada! Sai dai ya zaba ko ni ko Saratu da tsinanniyar ‘yar sa. Idan nazo zan baiwa Aminu lafiya ne? Allah ya bashi sauki.�
Najib ya so yayi mata bayani yaga ma bayanin baya da amfani, shin yaya zata ji idan ta ji cewa ‘yar da tafi tsana a duniya ce Dan da tafi so fiye da kowa ke so har ya kamu da ciwon zuciya? Ashe dalilinta na kin Intisar shine don tsinto ta aka yi, kuma tana tsammanin shegiya ce? Wane bayani zai mata ta fahimta a waya? Sai yace “Hajiya ki daina illata Intisar hakannan, don zaki sha mamaki. Don Allah ki gyara halin ki, ki dawo ki ji me ke faruwa cikin rayuwar ‘ya’yan ki?�
Faisal tunda ya fahimci abinda ke faruwa ya bar asibitin, bai kara waiwayar kowa ba, babu kuma wanda ya kara jin duriyar shi cikin asibitin. A lokacin da ake tsammanin shine mutumin da zai fi kusantar Saratun fiye da kowa.
Iyayen na mamakin irin wannan masifaffen so na Intisar da Aminu, gashi ba wani dogon lokaci suka dauka tare ba. So mai neman salwantar da rayuwa kamar a birnin Hindu ai abin mamaki ne.
To Al’ameen da ‘feeling hopes� din da Daddy da Hadiza ke ta bashi ya soma shaida mutane. Ga Addu’o’in da su Baffa ke tayi har Mallam Sidi ya zo Abuja ya kwana yi masu addu’o’in samun saukin Ubangiji. Ranar wata Juma’a ya mike zaune yace zai sha (tea), farin-cikin mikewar sa wurin Daddy da suaran ‘yan uwa kema kin san ba sai an fada ba, jiki na rawa Haj. Hadiza ta hada shayi mai kauri ta mika mishi. Kai ciwon Aminu harda na shagwaba don ya dade da samun sauki ko don Allurai da magungunan da ake dirka mishi kadai masu tsadar gaske, sai ya rufe ido yana jinsu kurum.
Ba abinda yake son ji irin ya ji Daddy na yi masa ‘yar murya yana rokon sa don Allah ya tashi shi kuma ya aura mai Saratu a gobe. Har president da sauran abokan aiki da abokan arzikan Daddy sun zo duba Al’ameen, haka Dr. Argungu da sauran abokan Daddy na (aikin soja).
Daga Miami, Florida, da duk inda Al’ameen yai aiki ko karatu abokanshi likitoci sun barko don nuna mishi kauna, duk kuma sun ji to bakin Rehab ne da ya kira wayar Aminu Najib ya dauka yace yana kwance a babban asibitin birnin tarayya ba lafiya, kai wannan Asibiti yaga taron jar fata da bai taba gani ba, haka ta bangaren Daddy kusoshin Nigeria sai barkowa suke daga ko’ina cikin kasar mu mai dimbin albarka.
Wani abin dariya sai suyi ta cewa M.A.B na ciwon kirji ne. Idan an fadi haka Haj. Hadiza tayi ta dariya.
A ranar Ihsan tazo a gigice, Babanta ne ya gaya mata Aminu na kwance Asibiti. Ko gayawa Ann bata tsaya yi ba ta zari mota ta taho. Tana sanye da atamfa Holland koriya dinkin Niger, kanta yane da dan mayafi.
Ta isa ga gadon Al’ameen bata ko kula da tarin iyayenshi balle ‘yan uwa ba ta janyoshi ta soma kuka a lokacin yana barci. Haj. Hadiza ta tambayi su Nasir ko wacece? Suka ce suke jin itace Ihsan matarshi, don suma basu taba ganinta ba.
Tayi ta bata baki tace Aminu yaji sauki sosai a hakan ma sai karfin jiki kawai.
A can Asibitin da Intisar take, su Hunainah na tare da ‘yar uwarsu suna jiyya har ta soma taka kafafunta, kar kiso ki ga farin ciki a wurinsu da Anti Saratu.
Maganar farko da Al’ameen yayi shine akan me Haj. Hadiza ta bari aka sace Intisar? Haj. Hadizah tace “kai da baka da lafiya ina kai ina tone-tone? Amma kasan dai babu uwar da zata dauki Da na halal ta kai Daji, duk wahala, duk talauci balle babu daya kanwar biyu�. Sai yayi murmushi.
Ranar Asabar aka sallami Intisar, ita, Anti Saratu, Hunainah da Hidayah suka zarce gida, shi Al’ameen Alfered ya rikeshi yace bai gama farfadowa daga ‘Luv-sick� din nashi ba, kullum tsiyar da yake tayi mai kenan sai yayi biris ya kyaleshi kamar bai san yanayi ba.
Washegari ya mike da safe ya zare masu ledar ruwan ‘drip� da suka makala mishi ya aje bisan gado. Ya dubi inda Ihsan ke ta sharar barci ita da Haj. Hadiza (‘yan jinyar shi kenan kowa na tare da Intisar) a ranshi yace “mun hadu a gaba�. Kafarshi ko takalmi babu ya fita wajen asibitin ya tari machine yace ya kaishi Addis Ababa Crescent.
Masu gadi zuwa ma’aikatan gidan kadan ya rage dariya ta kufce masu ganin Oga ko takalmi babu dare a bayan achaba, ya sauka kuma sai yasa kai zai shige, mai babur yace “Sir, kudina fa?� Gabadaya ya juyo ya shafa aljihunan wandonshi zuwa na gaban riga bai ji ko sisi ba, Major mai baiwa shukokin gidan ruwa bai san sanda ya tintsire da dariya ba, a nashi aljihun ya biya mai machine.
Al’ameen ya juya yace da mai babur ya jira shi, mintuna goma a tsakani ya dawo da mukullan mota (Peugeot 505 Station Wagon) ya dankawa Major yace ya fitar da ita a rumfar adana motoci ya bashi, ya katse dimbin godiya da fatar alkhairin da mutumin ke ta kwarara mishi da cewa, “kayi mun Addu’a, Allah ya bani Halimahh!
Malam Sani Daddy ya umarta da ya bude taron da Addu’a. Bayan an shafa ya dubi Haj. Hadiza yace in Ambasada yayi izni ta fadi labarinta da yadda ta rabu da ‘yarta Fatima har ya tsinta. Ambasada yace ta fada.
Tiryan-tiryan ta fadi tun aurenta da Sarkin Noman Shanono, yadda kishiyar ta Shatu tasa aka sace Saratu suka kai daji. Abinda ya faru da ita bayan wannan har zuwa sanda su Hidayah suka kawo ta gidansu na Riyadh, wahalar da suka sha kan nemanta da ciwon data kwanta kamar bata rayuba har zuwansu Bashir Lagos a lokacin Daddyn yana kulle, sun kuma baro Lagos zuwa Abuja shida iyalinsa fiye da shekaru biyu, su kuma basu san inda suka koma ba har zuwa sanda Hajjo ta sami labarin cewa shi Makarfi ya yi bikin cikar shekarun haihuwarshi sittin a jarida, ta matsawa Hassan ya bincika suka je Korea suka taho da su.
Zuwan su can gidan Daddy da shaida musu da akayi suna Asibiti. Shigowar ta dakin da Daddy ya shiga da kuma abubuwan da ta ji yana fade.
Shima Daddy ya kwashe duk yadda ya tsinto Saratun a dokar daji a kan hanyarsa ta zuwa Kano daga Kaduna domin halartar (Seminar) ya kawowa Saratu, rokon shi da tayi su rufe sirrin a ce ‘yar ta ce har illa Masha-Allahu.
Yadda suka gayawa ‘ya’yan shi cewa haihuwa tayi haka uwar su saida suka yi alkawarin cewa duk rintsi ba zata fada ba. Brigedier yai shiru na ‘yan dakikai kana ya cigaba.
“Bayan wannan ban san komai ba. Na yi zaton Saratu karama na Riyadh, ashe wai tana gidan tana aiki a sassan masu aiki. Allah ya gani ban taba sani ba har zuwa dawowar Saratu gidana, da yake mun sami sabani na lokaci mai tsawo hakannan ni ba mazauni bane kwata-kwata.
Na dawo daga tafiya muna hirar fahimtar juna da iyalina kamar yadda muka saba, a lokacin Saratu ce min tayi Intisar tazo hutu ne daga makarantar da muka kaita a can Riyadh, inda har kika ce kin ganta Haj. Hadiza. Aminu ya shigo, yadda ya nuna kwata-kwata bai taba sanin Intisar ‘yar gidan bace.
Ita ta rika fadar wasu maganganu da dukkanmu bamu gane ba amma…sai ya dubi Intisar da murmushi, ta kau da kai ta sunne fuskarta da karfi jikin Antinta. Shi ko gogan sai ya kara lumshe ido yana dubarta da dukkan so da duk wata kauna da da namiji ke iya mallakawa diya mace, ba abinda ya dameshi da iyayen su dake zazzaune, suruki zuwa matar shi ta aure.
Daddy ya cigaba da cewa “amma ke Intisar na ji kin ce ne wai ashe Al’ameen ne nawa na Miami? Amma har kuke shirin aure? Sauran duk ban ji ba don haka daina jin kunya. Kai kuma Al’ameen kace Saratu ta maka karya, daga nan kuma duk kuka susuce kuka susuta mu. To kuma bayan kun ji ana cewa duka babu alakar Jini akwai aure shine ko kunya babu kuka karkade riguna kuka taso daga gadon asibiti, wato mu zo muyi muku auren ko?
Sannan kai Aminu karyar me Saratu ta yi maka?�
Gaba daya falon aka sa dariya, Hunainah har da hawayenta jage-jage inka dauke Faisal da ‘yar Argungu. Shi kansa Dr. Argungu yayi murmushi kuma hakika labarin ya tsuma shi. Baya shakkar wadannan mutane masu cikar mutunci nada nufin cutar ko cin zarafin ‘yarshi illah al’amarin Intisar da Aminu Allah ne ya tsarashi.
Aminu ya dubi Haj. Hadiza da girmamawar da bata kwatantuwa yace
“Maman su Hidayah karyar da yarinyar nan ta shirya min har ta wuce hankali. Wai Babanta ne ya siyarwa Haj. Ita tayi mata ayyuka, nace yana ina? Wai yana fita ranar da ya kawota mota ta bigeshi ya mutu, uwar ta kuma bata san inda take ba wai dama foreigner ce, wai talauci ne ya ishesu suka sayar da ita.
A hakan kuma sai gata tana min karatun kimiyya mai inganci, tun daga nan na sinsino karya take, na dai bita ne kawai da yadda take so don a zauna lafiya.
Akwai sanda haka kawai na yi tunanin ko gudowa ta yi daga garin su akan maza? Don ko sallama nayi mata bata amsawa amma in mai aikin Hajiya ce (Dela) sai ta amsa�. Nan ma aka sake yin dariya. Ya ce
“Na taba ganin hoton Hidayah da Hunainah a hannun ta, ina gani nace wadannan kannen ta ne, domin kamar ta isa. Amma a rashin sanin dukkanmu, tace da ni makaranta kurum ta hadasu amma ko Mamar su kamar an tsaga kara suke�. A nan kuma murmushi aka yi.
Al’ameen ya yi shiru na dan lokaci cikin wani tunani, a lokacin sautin muryar shi ya karye gabadaya. Ya dubi Anti Saratu yayi murmushi ya sadda kanshi kasa cikin jin nauyi ya ce,
“Na taso da kiyayyar Intisar diyar Anti Amarya, a dalilin son da Daddy ke mata, ban ga wanda akaiwa hakan ba cikin su baki daya bayan ni, amma wannan son ya zarce nawa.
A da, Daddy na sona fiye da kowa a gidan, amma tunda aka ce an haifi Intisar a kuruciyata sai nayi tsammanin Daddy ya daina sona.
Babu wani nau’in azaba da ya zo min a rai da ban gana mata ba, amma Intisar so na take bata kuma guje ni ba, kullum sai ta yi ta leke na. Idan na juyo muka hada ido sai ta zura da gudu dakin Mamarta.
Nayi ball da ita domin ta karye, ko ta targade ta daina wannan tafiyan nata kaman ta mage tun tana mitsitsiyar ta amma ba don ta makance ba. A kuruciyata, ban taba tsanar kaina irin ranar ba. Na bar gida a dalilin bakin-cikin abinda nayiwa Intisar haka agabadayan tsayin rayuwata 15 years a Miami, Intisar nake tunawa da halin da na barta ciki.
Yana daga abinda ya dugunzumo zuciyata ga son dawowa, don kawai in ga Intisar in nemi gafarar ta. Abin haushin, Hajiyata ta boye min gaskiyar inda take, don kar inje ko don kar ince tayi ba dai-dai ba? Haka su Najib ban san dalilinsu na boye min ba, kodayake ban tambayesu ba, suma kuma basu ce min ba.
Hajiya ce tayi sanadin da naje kitchen (Madafi) kamar yadda tayi sanadin da na nakasta ta. Zuwan da yayi sanadiyyar kasancewana dumu-dumu a kaunar yarinyar da ban sani ba, kawai na sa mata suna halimah, ashe intisar ce kanwar Faisal diyar Anti Amarya, kuma ‘yar wasu? Kai abin da mamaki�. Kowa sai murmushi.
Dr. Argungu ya dan zamo daga cikin kujerarsa yayi gyaran murya duk hankali ya koma kansa aka nutsu ana sauraron sa yace.
“To a madadin kawun Al’ameen ina nemawa dana Al’ameen alfarmar auren Intisar a hannun ka Daddyn Intisar koko a hanun su Bashir Sambo ne?� Hajjo ta yi karaf tace
“Ina! A hannun Daddy Makarfi ne, har yanzu wannan sunan “Saratu Bello Makarfi� babu mai kankareshi. Mu kam Ameenu shine namu, don haka mun bayan alfarmar Dr. Argungu.�
Daddy ya sunkuyar da kai tabbas nauyin Argungu yake ji, amma a zahiri yafi kowa farin-ciki. Ya dade da wannan burin a rayuwar sa don dai ba yadda zai yi ne. Kamin ya sani abin furtawa Ihsan ta fasa kara mai firgitarwa ta soma yiwa Babanta kuka tana masifar baya kaunar ta ita dama Ann ce kadai mahaifiyarta. Kuka take wurjanjan tana neman fita daga falon amma Anti Saratu da Hajjo suka riketa tamau.
Intissar ta mike sauran kannenta suka mara mata baya kamar wasu ‘body-guards� dinta, harta kai bakin kofar fita falon ta juyo Idanunta sun kada tamkar an watsa masu dakakken barkono, wani tukuki yazo ya tokareta a kahon zuci, kallon da tabi kowa dashi tamkar ba ita ba, ba kowa take tunani ba a wannan lokacin face kuruciyarta da al’ameen dan Haj. Nafi.
How much do you like this story?
5/10/22, 21:33 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book three
*@Takori*
Page6ï¸âƒ£
Ta zargi kanta ta tsani kanta duk a lokaci daya ta kuma kalubalanci zuciyarta da so da kaunar Al’ameen. Idanunta gab suke dasu tsiyayo da kwallar da ta kasa kwarara balle taji sanyi-sanyin azabtuwar da kirjinta keyi¸duk da haka tayi murmushi ta girgiza kai ta koma ta russunawa Dr. Abubakar Argungu ta ce,
“Don Allah Baban Anti Ihsan kada ka kara fadin wannan maganan. Alkawarine na riga na yi tuntuni ba abinda zai kara hadani da Jinin Haj. Nafi ko a Lahira balle aure? Da nasan ma Al’ameen dan ta ne wallahi ko gaisuwa…� sai ta rushe musu da matsanancin kuka.
Duk falon yayi tsit sai da tayi mai isarta tukunna ta nayi tana share hawaye da majina da gefen mayafinta.
Tamkar anyi masa allurar karfi, Al’ameen wanda ke sauraronta cikin rashin fahimtar me take cewa, ya isa gareta tamkar wanda aka fizgo daga kujerar da yake zaune, ya figi hannayenta duka biyu ya mikar da ita daga durkuson da tayi kamar na mai neman gafara sukayi facing (fuskanci) juna tamkar zakarun dake shirin dambacewa, yace cikin karyayyar murya
“Kika ce mene Intisar? Say it again!�
Ta dube shi cikin ido, babu tsoro ba fargaba balle kallon nan nata cikin kunya dake gigita shi, babu komi cikin kwayar idon dake birgeshi face kallon tsana da tsabar kiyayya tsagwaro, da karfi ta ce,
“Nace ko zan mutu ba aure, bazan aureka ba! Ka je ka tambayi mamarka ya mukai da ita? Tunda dan ta shine ‘da� to taje ta nemo masa ‘ya� ba bayi irin mu ba (slaves). Aure nace ba zanyi ba, Al’ameen ko ana dole�.?� Kamin ta kare ya falla mata kyakkyawan marin da ya gigitata, in batayi kuskure ba ta ce har ta ga wuta. Aunty Saratu ta saki Ihsan ta ce,
“Ah ah! Al’ameen, bayan lahanta mata idanun kuma again za’a kurumtata? Wallahi bazai yiwu ba. Ta ce batayi din ko tilas ne? Ga matarka nan ta dawo dakinta ita kuma a bar mana ita haka ta sarara. Wanda uwarku tayi mata bai isa ba sai ka kara mata? Al’ameen akan idona? Ke Saratu shige mu tafi� Ta juya ga Ihsan ta ce,
“Ihsan kiyi hakuri ki zauna a dakin ki, indai a kan Intisar ne kin ji tace bata yi, in ce ko shikenan?� Gaba daya suka fice.
Daddy ya ce, “Ku dai mata duk shekarun ku tumaki ne.� Dr. Argungu ya ce “Hakane, yanzu kuma da kansu zakaji sun dawo maka da maganar, kaga Ihsan don Allah. Daga cewa an fasa aure ta shige daki ko kunyar idanun mutane, koda yake duk Amerikar ce ta kwashe masu albarka� Dukkansu suka sa dariya.
Wannan ta wuce.
*****
Ihsan kwana tayi kuka Al’ameen kuma kwanan takaicin da bazai fadu ba. Kin dai san Aminun Halimar, Halimar ta ce bata auren? Ya rasa ma takamaimai takaicin me yake? Sai da yayi tsam da ransa ya fahimci takaicin abin da ya aikata ne.
Yaya za’ayi ya bugi ‘yar mutane a idon mutanen da basu da ya ita a duniya a lokacin da suke cike da doki da farin cikin ganinta suna lailayarta tamkar kwai? Kuma bayan tana da gaskiya. Abinda Hajiya tayi mata in yayi tunani kome tace dasu daidainta ne, ba kuma abinda ba zata ce dasu ba, don ma dai tana da dimbin hakuri, to amma for God’s sake su ina ruwansu kuma meye nasu a ciki? Ina laifin wani ya taba shafar wani?
Shi bai guji tashin hankalin da zai gani daga Hajiyar ba ya furta yana sonta? Koda yake yana tsammanin tsoro ne ko tausayin Ihsan ya sata furta hakan. Bai sani ba, ta fadi ne heart and soul (baka da zuci).
Ya juya ya dubi barin da Ihsan ke kwance, shi din ma tausayinta ya kamashi. Rana daya tak tashin hankalin daya jefata ciki ya ramar da ita. Barci take amma ga busassun hawaye nan a gefen fuskarta.
Tun safe bakinta ko ruwa bai gani ba balle abinci, gara shi ya samu yayi karin kumallo mai kyau. Ya nemi zuciyarsa shawarar abinyi? Ya tabbata in har za su cigaba da rayuwar aure da Ihsan dole hakkinta ya kamashi, domin zuciyar bazata taba iya wannan adalcin ba, na son wata diya mace a yanzu bayan Halimah, (Intisar diyar Anti Amarya).
Shawara ta karshe da ya yanke da zuciyarshi shine na ya rabu da Ihsan taje ko Allah zai hadata da mai sonta fiye da shi, ta kuma zauna da uwarta lafiya, shima ya sami saukin matsalolinshi.
Ya zuro kafafunshi kasa a hankali ya janyo lokar gilashin da ke jikin gadon ya fiddo wani dan (memo) da yake amfani don kananan rubuce-rubuce, ya zari biro ya daura bisa.
Kamar an ce da Ihsan ta bude idonta, a hankali ta bude ido ta dubeshi ta mike taga rubutu yake cikin wannan talatainin dare, ya rubuta sallama kenan ta fizge biron tasa kuka.
Ta san ba abinda zai rubuta a dai-dai wannan lokacin in banda saki agareta, don yana ganin hakan shine kadai hanyar samuwar kwanciyar hankalinsa ya samu ya auri wadda yake so. Ta kifa kai bisa cinyoyinsa to shiga rera kuka mai karya zuciya.
Yayi shiru yana kallon ‘ceiling� shi kadai yasan me yake sakawa a zuciyar nan tashi mai cike taf da rudani. Ihsan ta san Aminunta, ta san tausayinshi da jin kai. Yana iya fasa komi don tausayi da jin kai. Ta sauka daga gadon gaba daya ta durkusa a gaban shi tana kuka hawayenta masu dumi na diga bisa farar kafarshi, tace a cikin muryar kuka
“Wallahi Aminu in ka sake ni na gwammace in kashe kaina
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 38