kika kusa salwantar da rayuwar ki akan tunanin bazaku iya auren juna ba.
Amma abinda na ke so ki gane shine, ki yi tunani, ke yarinya ce karama har yanzu cikin shekarun (teenage), wannan gigin son duk na dan lokaci ne, da anyi auren an haihu shikenan ya zama tarihi sai zaman hakuri da juna.
Abinda nake so da ke shine ki tsaya ki gina rayuwarki a bisa tubala na kwarai, in ba hakaba ba mamaki bada jimawa ba soyayya ta ruguzata. Al’ameen ya fiki wayo, daga shi har matarshi ba tsaranki bane a budewar kai da ilmi.
Don haka ki tsaya ki nemawa kanki madogara mai kyau tukunna, wanda shine wannan ilimin mai matukar wuya. Idan kika sameshi samun Aminu ba zai maki wuya ba haka in kika barshi ke da banza a cikin su daya kuke, don sai kin raina kan ki a cikinsu.
Ni in son raina ne ma Allah bana son ki auri mai mata irin Ihsan, ki dubi yadda take hauka akan mijinta fa, ke ‘yar nan, mind yourself (ki shiga taitayinki)�. Ahaf! Ai kamar Antin ta shiga ranta taga abinda take shiri komawa makaranta, tayi murmushi tare da saurin rufe ido, maganganun Antin take aunawa abisa sikeli daya bayan daya, wanda dama duk tayi tunaninsu, babu wanda bata ga gaskiya a ciki ba, ta ce a raunane.
“Na gode Aunty.�
Ta rufe wayar, sai yanzu ya fuskanci da wa take magana, bata ko dubeshi ba ta murda kofar da zata hadaka da dakin ta daga falon Anti, yayi hamzarin murda keys ya zare ya tura aljihun bayan wandon ‘basachi� dake jikinsa ya ce.
“Me Anti Hajjo ke gaya maki a waya, kike godewa kina kuma kara yi mun asaran hawayen da nake ganin daraja da kimar su fiye da na kowa?�
Wasu ubansu harara da ta watso mai ya bashi mamaki don bai taba ganin tayi ba, ga idanun sunyi jawur sai ta kara kyau a idon shi, ko da yake so ne hana ganin aibi, ya ce, “Inteesar� da muryar nan da ke karya lagonta, ta kassara kuzarin ta, amma a yau ko gezau, har yanzu hararar shi ta ke ba kakkautawa.
Ya soma taki har inda take tsaye tamkar sassakakken gunki, ta soma ja da baya kamar wadda taga abin tsoro da kyama, ta san ba karamin aikin shi ba ne ya kamata da kokawa kawai don ya sata yin magana, cikin tsiwa da yatsina ta bude dan bakinta tana mai nunashi da dan manuninta ta ce,
“Wallahi Al’ameen ka sake ka tabani yau zan fasa ma kaine, in bar inyamurar matarka da jiyyar da baka taba yi ba.� Bai fasa dosarta ba ya ce,
“Jinya kuma wacce ce ba’ayi ba? Sai dai kar a kuma, idan jinya ta ciwon son halimah ce, to ayi ta yi kar a tashi. Kar ki kara kira mun mata inyamura, yadda kike musulma diyar musulmi, haka itama take.� dai-dai lokacin da ta dangana da bangon karshe na falon, shi kuma bai fasa bin ta ba, ta ce,
“Wallahi zan kirawo Anti, tayi ma kashedin shiga harkana, ka nemo Halimar ka can amma ni Intisar ce, ka manta ka taba sanina a rayuwarka, ina gaya maka, ina kara gaya maka� ya toshe mata baki. Ya ja hannunta na dama da karfi har bisa seater dake tsakiyar falon, ta karfin tsiya ya zaunarta ya ce,
“Ke in ma Daddy zaki kirawo babu laifi. Amma sai na gama maganar da zan yi. Kin san me ya kawo ni?
Zuwa nayi in gaya maki ranar da duk wannan maganannen bakin ya kara kuskuren cewa bazai aureni ba don uwata, wallahi sai na kakkarya ki.�
Cikin tsiwar da bai san ta iya ba ta ce,
‘Ka karya ni? To ka ji ka sani ko da can da ka makantani, don ban da wayo ne, amma yanzu wallahi sai dai ayi ‘yar bibbiyu� saura kadan da dariya ta kwace masa, to amma shi kansa yasan bai kyauta ba, jiya ya mareta yau ya gaya mata kakkausar magana, shi da ke neman wanke dattin da Hajiya ta yayyaba masu daga idanunta.
Ya dire gwiwoyinsa bisa carpet abinda bai taba yiwa wata ‘ya mace a rayuwarsa ba, a yayinda ita kuma take zaune cikin kujera ta cika fam, kiris take jira ta fashe.
Ya langabe kai gefe guda gwanin ban tausayi, yayi kamar ya share mata hawayen da suka soma surtu, sai kuma yafasa. Ya ce,
“Inteesarr!�
Yadda ya kira sunan cikin murya mai karkarwa da kauri (husky) kadai ya birkita Saratun, bata jin ko dan yatsanta zata iya motsawa. Ya ce,
“I ‘am sorry, terribly sorry! Wallahi ni, wasa nake maki, in karya ki in ce na karya wa kenan?
Jiya kuma zuciya ce ta debe ni, kin san bata da kashi, abinda kika fadi cikin mutane ya bata mun kwarai. Ni kaina ban san ya akai ba, Pls, 4 give me…� Ya karasa a raunane, kana ya matso ‘yar kwallah, ya maida ta bisa kujerar ya ce,
“Wallahi Intisar nasan Hajiya ta bata miki, to amma ni meye laifina? Ni ban ji tsoron abinda hakan zai janyo man ba daga gareta na furta ina sonki? Sannan kuma bakya tausaya mun halinda zan shiga in na rasa ki kwata-kwata, ki tuna baya?�
Ta sadda kai kawai, bata son jin wannan abun da take ji game da Aminu, bata son wadannan ‘feelings� din da take ji game da shi masu tada tsigogin jikinta a duk lokacin da suke tare, to amma Al’ameen din kamar wani mayen karfe ne, wuyarta yayi mata magana da wannan muryan nashi mai jan mutum uwa lantarki duk wani ‘weakness� din ta ya gama samunshi.
Ta tabbata nisa da shi shine abu mafi a’ala a gareta in har tana son cimma kudurirrikanta akan Haj. Nafi, wadanda daga ita sai zuciyarta sai mahaliccinta suka san na mene, amma ba don bata son shi ba.
Karya ne ko fatar bakinta ta fada, to bacin rai ne. Shi kadai take so har cikin tsokar zuciyarta, har gangar jiki zuwa kwakwalwarta babu inda baya girgiza da kaunar Al’ameen da sha’awar komi nashi, ita kadai ta san me take ji da yakin da take yi da zuciyarvta a duk lokacin da yai kuskuren kai hannunshi gareta koda yatsar hannunta ne kuwa amma ta rantse, ta kuma ta rantse ko son sa zai kasheta, ko duk duniya zata taru a kanta, bazata aure shi ba!
A ganinta ta hakanne kadai zata rama abinda sukai mata shi da mahaifiyarsa wanda har abada bazata manta ba, ba zata yafe mata ba kuma ba zata daina tunawa ba.
Bata san wannan hukuncin da ta yanke yai tsauri ba, domin son da Al’ameen ke mata Allah kadai ya san iyakarsa; ba na wasa bane, ya wuce ayi ramuwar gayya akansa yayi masa tsauri bazai iya dauka ba. Da kyar in bata yi kuskure ba, da kyar in hukuncinta ba zai zamo nadama mara amfani a gareta ba.
Ya cira hannunta ya aza bisa kirjinshi, tana iya jin nannauyan bugun da zuciyarsa ke yi akai-akai, jikinta ya soma sanyi, ya ce,
“Ki ji Intisar, kiji irin bugun da zuciyar nan ke yi a domin ki, saboda ke ne take ciwon da har abada bazata daina ba, ba kya tausayi na Intisar ba kya sona yanzun? Allah na rantse, in muka cigaba da tafiya a haka wata rana�. Wata rana bugawa zatayi gabadaya ta fashe kowa ya huta, ki taimake ni ki agaje ni, ki daina la’akari da laifin da ba nawa ba kina hukunta ni dashi don Allah?�
Ita dai ta zamo ‘pale� ko motsi ta kasa balle tayi kokarin yin wani abu, ta rasa abinda ke mata dadi shi kuma bakinshi bai yi shiru ba da gaya mata irin halin da zai shiga in ya rasata. Har ya kai ga kwantar da kansa bisa kafadunta.
Cikin wannan halin Faisal ya turo kofar falon ya shigo, fes idon shi a kan su, ya juya da sauri yana cewa, “Excuse me plz. Ya Aminu ban sani ba!�.
Ta mike a gigice ta banka dakin Anti, ta kifa kai bisa gado ta soma rera kuka sabo fil. Ina rowan mai neman kuka an jefeshi da dunkulen kashi.
Gabadaya suka zubo mata ido Anti da Ihsan suka yo kanta Anti ta ce,
“To kin gani Ihsan mijinki kullum sai yasa min ‘ya kuka, don haka ki je ki ja kayan ki ku tafi.� Ta sake kuluwa ta shaka ance Al’amin mijin Ihsan, ta sake tsugewa da kuka.
Ihsan ta matsa jikin gadon ta dago kanta ta aza bisa cinyarta tana murmushi tace “Haba little sister na, kin hana mun miji sakat ko tausayinshi ba kya ji, jiya saura kadan ya sakeni, don Allah kiyi hakuri ki bamu hadin kai ko na samu kan Al’ameen nima…�
Ta soma fidda kwalla itama, wani tukuki na cinta a rai, wai yau itace da kanta ke rokon wata ‘yar ficikar yarinya ta so mijin ta, Aminunta data gama shan bakar wahala a kansa, ta sadaukar da komi nata dominsa, take son sa tamkar ta fidda zuciyarta, ayya rayuwa!
Ta daure ta share wasu azababbun hawaye da suka biyo kumatun ta a guje ta ce, “Intisar, Al’ameen ya gaya mun bazamu taba samun kwanciyar hankali ba in har baki yarda da maganar auren ku ba. Don Allah Intisar ki taimake ni.�
Aunty ta juya ta fita, bata iya jure ganin wannan abin tausayi. Ita Ihsan din ce ta ke bata tausayi, ta tabbata ba karamin so takewa mijinta ba, abinda tayi mata da yawa baza su iya ba, dazu akan idonta Aminu ya turo kofa ya rufesu har da mukulli amma sai cewa tayi.
“Allah dai yasa ya shawo kanta. Don na lura Intissar akwai zucciya.�
Intisar ta dago don babatun Ihsan ya isheta, fuskar nan jike sharab da hawaye ta dubeta sosai ta ce,
“Ina ganin mutuncin ki, don haka don Allah don Annabi Anti Ihsan ba ruwan ki, ki rabu da Al’ameen kawai, shi bai ji tausayi na ba sadda yake kwallo dani har na zamo nakasashshiya? Hajiyarsa bata ji tausayi na ba a sadda Daddy ke kwallo da ni ba a gabanta, da sadda take fyaula mun kebur? Take sa min shocking? Ke har da kan ki kike son in auri mijin ki ashe karya kike ba son shi kike ba.
Baki sani ba, ni fa tunda fari ba son mijinki nake ba, kaddarar Allah ta hada mu a kichin kuma kaddarar ta raba, don haka ki tafi don Allah ina bukatar hutu, ina maku addu’a Allah ya baku kwanciyar hankalin ba sai tare da ni ba, ke ni ba wani aure da zan yi, da din ma dana amsa masa rashin galihu ne da rashin abin yi, yanzu kuwa ina da abinyi ina da galihu, ba wanda ya isa yayi kwallo da ni ban yi karar sa an fitar mun hakki na ba, ki je ki lallashi abinki ke daya ko ke ba mace bace baki ishe shi ba?�
Ta fiddo mata ido cikin barazana kamar gaske, bayan a zahiri ji take kamar ta makureta ta huce.
Ihsan tayi murmushi ta mike, a ranta ko cewa take lallai wannan yarinyace, danya (fresh), kalaminta kadai zaka ji ka tabbatar kurucci dangin hauka na dawainiya da ita, har akwai wata ‘ya mace mai cikakken hankali ta kuma san abinda takeyi da zata budi baki tace wai bata son Al’ameen Bello?
Ta mike ta na rataya jakarta ta nufi kofa ta ce,
“Ki dai kara baiwa zuciyar ki shawara Intisar, Al’ameen mai matukar son ki ne tsakani da Allah. Ba fata nake miki ba, amma ba zaki samu miji da ke son ki tamkar yadda ya ke son ki ba.�
Intisar ta bita da hararar haushi, kar ta samu din, wannan dan iskan mijin nata? Yau kam kunya da tozarci tagama jin shi a rayuwar ta. Da wane ido zata dubi Faisal?
Wane kalami gareta na wanke kanta daga sunan mayaudariya, maciyiya amana, butulu kuma mai manta alkhairi a idon Faisal? Sai ta kara jin tsanar Al’ameen ninkin baninkin na da, dubi yadda yake wa matarshi don wai kurum tana sonshi. Itama idan ya aureta wata rana ya sami wadda ya fiso fiye da ita ba mamaki ya turota lallasar yarinyar da yake son, tab! In ita ce ai za’a yi kata’i. Bata san wannan duk yana cikin wayewar Ihsan da duniya ne ba, ko ba komi zata sayo ma kanta daraja da soyayya a zuciyar mijinta, gaskiyar Hajjo ne Ihsan da Aminu sun fita wayo, ba kuma tsaranta bane a budewar kai da Ilmi.
How much do you like this story?
5/14/22, 09:25 - Ummi Tandama😇: _____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book three
*@Takori*
Page9ï¸âƒ£
A lokacin ne hankalin ta ya kai ga Hidayah da Hunainah wadanda ke hada komatsansu cikin ‘trollies� din su basa ko dubarta. Hankalinta ya tashi, ta ji babu dadi ta ce,
“Ku kuma ina za ku?�
In jakunkunan su sun amsa, to suma sun tsinka mata. Ta ja jiki ta sakko daga gadon fuskarta jike da hawaye taje ga Hidayah da Hunainah, ta kama kowacce da hannu daya ta rungume a jikinta ta cigaba da kuka mai tsuma rai su kansu basu san sanda hawaye ya cika idon su ba. Tace cikin kuka
“Don Allah ‘yan kanne na ba sai jibi zaku tafi ba?� Hidayah ta tureta tana share hawayen ta da bayan hannu.
“Ai zaman mu baya da amfani, tunda ke ba kya jin shawarar kowa kuma ba’ajin damuwarki. Yaya zaki sa Ya Aminu kuka akan idon matar sa?
Mu bazamu iya jurar ganin wannan wulakancin ba, so hauka ne? Kuma idan yanzu ba kya sonsa ba zaki aure shi ba ai ba haka ake abun da wulakanci ba.�
Ta ce, “Hidayah, Kome zan gaya miki a yanzu bazaki gane ba�. Baki san Babar Al’ameen ba ne�.� Ta katseta,
“Ba bu abinda na tambayeki, ban kuma ce ki gaya mun ba, ban santa ba ba kuma na so in santa, to amma ta yaya zaki hukunta shi da laifin uwar sa wanda ba nashi ba ai har ga Allah kin dau hakkin shi…� Ta ce,
“Hidayah, ba wannan ne kadai ba�.� sai kuma ta kara sa kuka, to tace mata me?
Bata da abinda zata ce da ita ta fahimta game da Faisal Bello Makarfi, daga Anti sai Daddy ne zasu fahimce ta akan hukuncinta amma su Hidayah baki ne basu san komi ba.
Dai-dai lokacin da Anti ta shigo tana rike da Zarah, tun kan ta zauna Zarah ke mikawa mutuniyar ta Hunainah hannu tana zillo daga jikin Antin, ta amsheta yayinda Antin ta samu gefen gado ta zauna ta dibesu dukkansu tace “duk mi ya janyo wannan?�
Hunainah ta ce,
“Tafiya zamu yi Anti� ta ce, “Ina?�
Su duka suka hada baki suka ce “Can inda aka sauki su Maman mu.� Ta ce,
“Akan me?� Duk suka yi shiru ta ce,
“Nasan sai jibi zaku tafi Korea, mun yi da Hajiya sai zasu tafi zasu biyo ku tafi, to a kan me yanzu zaku ce zaku tafi, ku bar ‘yar uwarku cikin irin wannan halin da ta jefa kanta don bana ce wani ya jefa ta ba.�
Hunainah ta ce, “To Aunty yaya zamuji dadin zama alhalin tana kuntatawa kanta? A ce mutum bashi da aiki sai kuka kamar wanda ya rasa iyaye da dangi, mu bamu da amfani a gareta kenan. Muna iya kokarin mu don kawo ma Saratu canjin rayuwa amma bata gani. Damuwar ta bamu isa mu ji ba, bamu san hakikanin kuma me ke damun ta ba. Ni ban ga meye abin bakin ciki duk a cikin maganar nan ba, tace ta fasa auren Yaya Al’ameen waye yace dole ta aure shi?
Sai kuma tasa mutane gaba tayi ta kuka in ta canja shawarane ba sai taje ta sameshi ta bashi hakuri ba?�
Ta share hawayenta da yatsunta biyu ta ja ‘tissue� ta fyace hanci ba tare da ta lura da hararar da Intisar din ta wurgo mata ba, dai-dai lokacin da Najib ya yi sallama ya shigo.
Da ganin yanayin da suke ciki duk ya bi ya rikice, ya zube a gabanta bai ma kula da Anti dake zaune ba ya ce,
“Hidayah, tafiya, why?� Sai ta sake barkewa da kuka.
Ya fiddo ‘handkerchief� a aljihun don share mata hawayen da ke zuba ya na tambayar su me ya faru? Aunty ta ce,
“Najib ya zan yi in san damuwan Saratu ne don Allah?�
Ya kai dubanshi ga Intisar, cikin kwanaki kalilan rak wai har tafi can baya sanda take cin bakar wuya lalacewa, yayi murmushi ya ce,
“Aunty, wait a minute� (jira ni minti daya).�
Ya juya ya fita da sassarfarshi, ya fi rabin awa kamin ya dawo Faisal na biye da shi. Idanun shi jazur da gani shi din ma yana cikin tsananin tashin hankali kwatankwacin koma fiye da na Intisar din, don dai shi namiji ne, sannan akwai juriya.
Kallon kyama kawai yake bin kowa da shi da tsanar duk wani al’amari dake cikin duniyar. Najib ya ce,
“Zauna� ya ce,
“Bana bukata.�
Ya tsaya kikam a bakin kofa ya harde hannuwanshi bisa kirji, idanunshi akan Inteesar tamkar mijin da ya kama matarshi da kwarto.
Najib ya zauna jikin Hidayarshi, cikin kwanciyar hankali ya dibi Anti cikin basira ya ce,
“Dibe su Anti.�
A mamakance Anti ta dubi Faisal, kana ta maida dubanta ga Intisar ya ce,
“Anti me kika fuskanta?� Ta ce,
“Dukkanin su, suna cikin yanayi daya.� Ya kuma cewa,
“Anti ba ki tuno can baya?� Cikin rashin fahimta ta ce,
“Ban gane ba�.
Ya bugi Jakar Hidayah da kafarsa ya ce,
“To cut the long story short! Na fahimci daga Faisal har Intisar suna son junansu ne tunda dadewa, duk wani da ya san kuruciyarsu zai gane hakan sai dai in baya da lura.
Na dade da sanin Intisar kishin Faisal take har zazzabi sai da nayi na kwana bakwai don mamaki. Intisar na cikin damuwar yaya zata bar Faisal akan Al’ameen? Ko da taso Al’ameen ta so shi ne a rashin Faisal, ta so shi ne domin ya mallaki wasu ‘qualities� da ‘appearances� na Faisal kaman murya, taku, da sauran su, yayin da Faisal ke jin haushin jinkirin shi na kin fara furtawa cewa…�
A fusace Faisal ya katse shi,
“Dakata don Allah Malam abin naka ya koma sharri, for God’s sake, yaushe na taba ce ma ina son Intessar, irin son da kake nufi? Yaushe ka zama predictor? Zuciyar wa ka shi ga a tsakanin mu har ka gano hakan?�
Najib ya dubeshi a lalace ya ce,
“To canzawa juna da kuka yi na mene ne?�
Kamin ya rufe bakinsa kawai sai suka ji Faisal ya ce,
“Hidayah zaki iya aurena?�
Hidayah ta dago a razane, ta girgiza kai da karfi tace “A’ah, wallahi ba ruwana, ni ina da wanda nake so kada a kara sani a ciki.�
Yadda ta fada da sauri da gigita saida ta ba Najib matsiyaciyar dariya, ya kuma ji nadamar abinda ya jangwalo ga abin na shirin juyewa kansa, shi ko Faisal wani dogon tsaki tsuuu� yaja ya juya ya fita har yana tuntube da dokin kofa.
Hunainah ta sunkuyar da kai cikin alhinin wannan cukurkudadden al’amari. Anti ta dubi Najib ta mike tsaye ta ce,
“Ni dai ina ganin Saratu ki sassautama ranki hakannan, Allah ya zaba abinda yafi alheri gaba daya.� In banda Najib ba wanda ya ce, “Amin.�
Ta fita ta ja masu kofa yayin da Najib ya cigaba dayi mata nasiha mai sanyaya rai. Ya ce,
“In da nine ke, Saratu ba kuma wani abu da zai sake sa ni bakin-ciki. Kamar yau ne nake gaya maki cikin wasikata sanda akai mana katanga dake cewa; ni na tabbata wani babban al’amari ne zai faru dake anan gaba, kuma hakika ke din wata ce a cikinmu.
Ga shi a yau kin zamo mabudi kuma sityari mai juya zuciyoyin ‘ya’yan Hajiya, sai inda ki ka garasu. Duba ki ga nima shakikiyarki bata barni ba. Kun zamo mana barin jiki, bango abin jinginar mu mu ji sanyi sai yadda kuka yi da mu. Don a yau Hidayah tace bata so na, ina jin haukacewa zanyi.
To haka daga Ya Aminu har Ya Faisal na tabbata babu mai tsira daga takobin kaunarki, duk da nasan Al’ameen bai san Faisal na sonki ba da duk matsalar ta warware.
Duka wannan matter bai yi kamari yadda kika daukeshi ba, don Allah, ki maida walwalarki ki, ki bude sabon shafin rayuwar farin-ciki da ‘yanci tamkar kowa, ina kara gaya miki ba fa mai yi miki dole kan abinda ba kya so.�
Tasa gefen dankwalinta ta share idon ta tas, eh, gaskiya Najib ya fada, yanzune ya dace ta budewa kanta sabuwar rayuwa mai ‘yanci, tamkar sauran ‘ya’yan gata, ciki kuwa har da neman ‘yancin kanta na rama abinda uwar su ta shekara yi mata!
Wasa farin girki! Tun kowa na tsammanin Intisar wasa take maganar rashin amincewar ta kan aurenta da Al’ameen har suka tabbatar da gaske take. Duk wasu hanyoyin sadarwa tsakanin su ta toshe su, bata daukar wayar shi hakannan in zai wuni cikin gidan bazata bari ya ganta ba, ko dai ta kulle kanta a (toilet) ko ta shige cikin (store) har ya gaji ya tafi haka Anti tace ba ruwan ta, ta tsame hannun ta a al’amarin duk abinda Intisar din ta zabawa rayuwar ta tayi dai-dai.
Al’ameen duk ya sukurkuce ya rasa inda zai tsoma ransa, bashi gaban Daddy bashi gaban Anti, wurin Hajiya Hadiza kadai yake samun sanyi to ita din ma mijin ta daga baya ya gargadeta ta fita harkar su, tunda tare ta gan su, bata da wata (power) in dai akan Intisar ne.
Su Hidayah kam bakin-cikin da suke ji kan Yayar su da hukuncin ta har kuka suke tausayin Al’amen kadai ya ishe su, duk ya rame ga wata kasimba ta babu gaira babu dalili ta cika kyakkyawar fuskar sa, duk son gayu da kwalisa irin na Al’ameen Bello, a yanzu babu ya kau. Babu komi gaban sa kamar Intisar din da ke neman kufce masa karfi da yaji yana ji yana gani.
Babban abinda yafi damun sa shine wani kululu ko katutu dake tokare shi a kahon zucci, in ya tuna wai yau Halimar sa ce ke gudun sa sabida Hajiyar sa? Yayi dakacen kasancewar sa Al’ameen dan Hajiya Nafi, ba tun yau ba, a yau ma yana karawa.
Ya kuma tabbata wannan tabon data yaba masu har abada bazai gogu a zuciyar yarinyar ba. Yayi ban hakurin, yayi ban bakin yayi lallashin duk a banza. Yo ina ya ganta ma?
Ta haramta masa ganin kyakkyawar fuskarta da ke sa shi nutsuwa balle dan murmushin ta dake gigita shi, duk sun zama tarihi, na wani zamani can daya shude, zamanin da yake ganin ba zamanin da ya samu gata a cikin sa kamar sa, wato zamanin rayuwar ta a Kitchin.
Ya kan zauna yayi tunani, iya kokarin sa ya rasa mafita cikin al’aamarin sa, karewa ma, bai san me take nufi da shi ba; tana son sa ko ta daina son sa?
Kai bashi kadai ba babu wanda ya san nufin da ke kunshe cikin zuciyarta a gidan. Cikin wannan halin Faisal ya samu Daddy ya gaya masa ‘transfer� da ya dade yana nema zuwa NNPC na Lagos ya fito. Daddy ya nemi dalilin ‘transfer� din yace hakanan yake son yanayin garin Legas, ya kuma dade da burin aiki a nan to sai ga yadda al’amarin ya kasance, wato samun aikin da yayi da wurwuri anan Abj.
Daddy yace ya je Allah ya sanya albarka amma yayi kokarin zuwa ya ga lafiyar gida duk karshen sati ko bayan sati bibbiyu. Ba kuma tare da ya kara bi ta kan kowa ba ya yai tafiyar sa, inda ya rungumi aikin sa cike da karfin zuciya.
Yau kam Al’ameen ya kudurce bai barin gidan sai yaga Intisar ko da hakan na nufin ya kwana a gidan ne. Yana ta zarya falon Anti zuwa sassan Daddy har dare bata ba alamarta. Shi kam duk ya fi daura laifin komi akan Anti don a tsammanin sa da sanin Antin Intisar ke yi masa duk abinda ta ke yi.
Bai sani ba, Antin ta fishi takaicin abinda Intisar ta yanke a kansa, don dai bata son matsanta mata ne. Ta tabbata ita yarinya ce, amma mai sahihin tunani da hangen nesa, tabbas tana da kwakkwarar hujjar ta ta yin hakan. Ita kadai tasan azabar da ta kwankwada a hannun Hajiya, sai dai tana matukar tausayin Al’ameen har hawaye take masa kamar su Hidayah
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 38