Share this page
kanta da yawa, mai biyewa sharrin shaidan da rudin zuciya, abinda Allah ya hore mata bai sa ta gode masa ta fuskanci abinda zai anfaneta ba, aah, ta wanzar da muhimmin lokacin ta wajen nuna tsana da kyara ga wata kankanuwar halittar Ubangiji da bata tare mata komi a rayuwa ba, ta biyewa sharrin kawaye da dukiyar da Allah ya hore mata, maimakon tayi aikin lada da su ko sadakatul jariyah, aah, sai ta bata su ga tsafe-tsafen banza, wanda aka ce gaskiyar mai shi ne domin a yau, babu ya wargaje! Ba abinda hakan ya kare su da shi, Allah ma kadai ya san irin farin cikin da Saratu da Saratu da Bello Makarfi suke ciki a yanzun. Ga dai gidan tana gani, ta sha wucewa ba sau daya ba ba sau biyu ba ta gabansa, amma ya gagareta shiga. Bai sake ta ba. Ta tabbata a zahiri ba kishi ko zafin ranta ne ya hanata komawa gidan ba, illa ita din ji ta ke ta kaskanta, ta wulakanta, hakannan bata da idon da zata dubesu, ko ma tace kwata-kwata ji take gidan yafi karfinta. (To tun a duniya kenan wata shariar, sai a lahira)! Shin ma anya ba hakkin su ne ya rikide ya dawo kan yayanta ba? Wannan soyayyah da Faisal da Ameenu ke wa Intisar, ta tabbata ba kadan ba ce, kwayar idanun su ya nuna, komai na jikin su ya nuna, ta tuna Almeen magana yake amma a zahiri fatar bakin shi ce kawai ke motsi, a sanda ya ke cewa zai daina sonta zai daina kaunarta, in har hakan zai sa ta yafe masa Wasu hawaye suka kara zubo mata, wannan shi ake kira nadama mara amfani. Inama ba tayi ba, inama bata aikata duk wannan ba! Wani bangare na zuciyarta ne ya tunatar da ita cewa ai akwai sauran lokaci, lokaci bai kure ba, da zaki gyara bayan ki, ki nemi gafarar kowannen su, dukkanninsu masu sanyi ne (musamman Alameen) tabbas zasu yafe miki, ba tare da wani jan rai ko bata lokaci ba, kuma hakika zasu yi farinciki dukkanin su, idan kika nemi afuwar Intisar din nasa zai yi farin ciki da hakan. Wannan tunanin ne ya dan sanyaya mata, ta mike domin dauko wayar ta, ba wanda tayi tunanin fara kira sai Almeen tana mai saka irin tausasan kalaman da zata yi amfani dasu wajen bashi hakuri, tare da tabbatar masa da amincewarta 100% kan bukatarsa. Kuma tace da shi a washagari yazo ya dauke ta ya maida ta dakin ta, ya danganata ga Intisar ta nemi gafararta ta sa mata albarka, ta nemi gafarar mijinta da abokiyar zamanta su koma zama na amana da aminci kamar yadda tun farko Saratu babba ke so su yi. A yayinda ta kai hannunta ga wayar, a yayin ne zuciyarta ta yi wani irin mummunan bugu irin wanda bata taba yi ba a rayuwar ta. Lokaci guda yawun bakinta ya tsinke, hakannan tsigar jikin ta ya tashi yarrr! Dai-dai sanda agogon dake makale a bango ya ke kada karfe biyu na rana, cikin daddadan sautin da yafi mata kama da wakar Bankwana! A Gidan Bello Makarfi Dawowarsa kenan daga sallar Jumaa da sassarfar shi, cikin takun sa mai karfi ya doshi sassansa, to amma tun safe yau haka yake sukuku ba kuzari. Aunty Saratu ta karaso ta amshi brief-case daga hannun shi da bakar suit da ya ratayo a kafadun shi, lokaci guda kuma tana loosing tie din shi tare da yi mai sannu da zuwa. Bai amsa ba hakannan dai ya wuce zuwa toilet, tayi zugudiii a falo da taguni da hannuwa bibbiyu, cike da tunanin me ke damun Daddy a yau ne? Daga can gefe wayar shi dake cikin aljihun suit din shi da ta aje ke ta tsuwwa, ta fiddota da nufin mika masa toilet amma ganin sunan mutumin da ke kiran ya dan kadata, Commissioner of Police Adams Stacy, kawai sai ta amsa ba tare da wani tunani ba. Ya fara ne da magana cikin nutsuwa cewa ta sada shi da Markarfi direct wato kai tsaye inda ita kuma ta nuna baya kusa, ya fada mata ko minene in ya fito zata fada masa, shi kuma ya dage kawai ta bashi Makarfi har ranta ya baci ta kashe wayar, ta cillata bisa kujera. A dai-dai lokacin daya fito daga toilet din, ba kuma tare da ya tambaye ta ita da wa take magana a waya ba kawai ya hau darduma ya zauna, can kuma ya mike ya fuskanci gabas ya tada sallah da ba zata ce azahar ce ko laasar ce ba, don kuwa dawowarshi kenan daga sallahr jumaa, kai da alama bama ya son magana kwata-kwata kuma baya cikin hayyacin sa, ta tambayi kanta ko rashin nutsuwar sa na da alaka da kiran da aka yi masa yanzun? Oho! A irin wadannan lokutan itama bata faya takura masa ba, baya-baya take da shi har zuwa lokacin da shi da kansa zai ware ya kulata, sai ta maida hankali bisa jera abinci bisa tebur. A sannan ne wayar ta cigaba da kara ba kakkautawa amma bata ko dube ta ba, ta tabbata mutumin dazu ne, ta tsani mutum mara yarda da kafiya. Sai da ya sallame sallar a lokacin wayar tayi burarin ta har ta gaji ta katse ta kama wani, ya mika hannu ya dauki wayar ya ce, Hello? Daga can bangaren mutumin ya ce, Your excellency, Stacy Adams ke magana daga ofishin yan sanda da ke Minna yace na gane ai, akwai lambar ka a waje na, ina fatan dai lafiya? Yayi dan jim, yayinda zuciyar Daddyn ta shiga harbawa da sauri da-sauri, ya tabbatar wannan shine sakamakon mugayen mafarke mafarken sa a dan tsukin, sai dai ya ambaci (Innalillahi) a zuciyar sa yafi sau talatin tun ma kafin ya ji mabbabin kiran. Yayi karfin hali ya ce ina sauraronka. Mutumin ya ce cikin tattausar murya Your edcellency, muna tare da gawar dan ka Dr. Alameen Bello Makarfi, ya yi mummunan accident akan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna, wanda bincike ya nuna yafi minti talatin da sakin sityarin motar shi wanda hakan ya janyo hatsarin motoci fiye da goma akan titin, babu wanda ya tsira a cikinsu. So ku zo babban asibitin Minna ku karbe shi da kayayyakin da ke cikin motarsa da ke tare damu. Ina mai yi maka taaziyya, hakika rasa mutane irin su M.A.B, ba karamar asara ba ce, ba ga iyayen su kadai ba har ma ga alummar Nigeria bakidaya. Hawaye na kwarara daga idanunsa, irin wadanda bai taba zubarwa ba, har kuwa lokacin da aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai da san da ya rasa iyayen sa! Ya ce, “Daga Allah muke, kuma gareshi zamu koma. Alameen Allah ya ji kan ka, ya sa mutuwar ta zamo hutu a gareka, ya baka Aljannar Firdausi madaukakiya, ya yafe maka kurakuranka, ya inganta aiyukan ka na kwarai, ya shafe zunubanka, ya sa ka zamo Da mai ceto ga iyayen sa.� Na yafe maka duniya da lahira. Ina rokon Allah yayi maka rahmah da gafara!. Wasu hawayen suka zubo, irin wadanda basa saukaka kunci da radadin mutuwar da a zuciyar mahaifansa! Balle da irin Alameen Bello! Ba iyayen sa kadai ba, duk ma wanda wata muamala ta taba hada shi da shi koda sau daya ne, dole ya girgiza da gushewar sa a doron kasa. A lokacin ne ye tuna wannan ba lokacin kuka bane, lokaci ne na karfafa zuciya, lokaci ne na nunawa Alameen din sa gata na karshe a rayuwarsa, wanda ba komi bane illa Addua da nema masa rahmar Ubangiji. Wani Imani ya zo masa. Ya yunkura ya mike ya doshi kofa ya manta babu ko kwakkwarar suttura a jikin sa. Aunty Saratu ta mike bata ko ganin abinda yake gabanta illa ta mika masa babbar riga da takalmi, suka fito harabar gidan a tare. Har zuwa sanda Daddy da mukarrabansa suka shiga mota suka bar gidan, bata ko motsa daga inda take tsaye ba, hakannan hawaye ko digo daya bai fito daga idanuwan ta ba. Ta kasa gasgata alamarin, ta kasa gaskata abinda kunnuwan ta suka jiyo mata, ta kasa amincewa da wai Alameen ya rasu! Ta dauki alamarin a matsayin irin mugayen mafarke mafarken nan da dan adam ke yi ya farka cikin dan lokaci. Allah kadai yasan tsawon awonnin da ta yi a tsaye a wajen tamkar sassakakken gunki ko gungumen itace. Har zuwa lokacin da motar da ke dauke da gawar Alameen tare da motocin da ke biye da ita suka cika harabar gidan. Ta daga ido taga wai yau Alameen ne ake fiddowa da sunan babu wata gaba dake motsi a jikinsa kuma babu numfashi. Abin mamaki, babu ko kwarzane a jikin sa, babu ko digon jinni a jikinsa tamkar mai barci kai baka ce accident yayi ba. Fuskarsa da a kullum ke cike da ilhama da cikar zati, tare da kwarjini na musamman a yau ma hakan ta ke, baya ga wani haske da annuri da ya kara tamkar a ce Alameen ya bude kyawawan idanuwan sa ya amsa. Ta dai tabbatar wannan zahiri ne ba mafarki ba ne sai ta yanke jiki ta fadi, yayin da jinni ya soma bin kafafunta ba kakkautawa. Babu ko tantama dan yaron cikin da take dauke da shi ne ya bi dan uwan sa nan take. How much do you like this story? 5/14/22, 09:27 - Ummi Tandama😇: ____________________________ *✍� SIRADIN RAYUWA✍�* Book four *@Takori* Page3️⃣ Kamin wani dan lokaci labarin mutuwar Alameen Bello yayi tambari a cikin Abuja da wajenta ta kafofin yada labarai, haka gidan redion BBC tuni sun watsa labarin zuwa Jackson Memorial dake (Florida), da Meritime dake birnin Miami, haka sashen Hausa, redion Nigeria Kaduna, suma labarinsu a dan tsukin kenan. Kamin kace meye wannan gidan Bello Makarfi babu masaka tsinke balle dai-dai da isowar shugaban kasa da yan majalisar sa, gami da babban limamin masallacin Abuja wanda zai jagoranci sallar. Daya bayan daya samarin Brigedier ke isowa, wani ya samu sallar wani bai samu ba, (irin su Faisal da Najib da ke garuruwa masu nisa). Cikin wannan halin ne direbanta ya karaso da ita gidan cikin motarta (Volvos6) ko inda zasu tusa kan motar babu a layin, don haka tace da shi ya ajiye ta a nan farkon layin. Ta fito duk jikinta nade cikin laffaya koriya shar, idanuwan ta shabe-shabe da hawayen da ta ke jin har abada bazata daina zubar da su ba, illa a yau ta ji wani sabon imani ya shige ta, tsoron Allah da takwah ya karu a zuciyarta. Ta yi iya kokarinta don ganin hawayenta ko daya bai diga a kasa ba, kokari take wajen ganin ta maida su, Allah Sarki! Wai Aminun ta ya tafi, Aminun ta mai sonta, mai yi mata biyayyar da cikin yayanta kaf, babu mai yi mata kwatankwacin ta. Ya tafi, cike da bakin-cikinta na rashin kyautayi da tausayi a gareshi, ya tafi, cike da buri na karshe a rayuwarsa wanda bata taimaka masa ya cikashi ba, ya tafi, ba tare da samun wata daddadar kalma ko daya daga bakinta ba a lokacin da yake tsananin bukatar hakan. Ya tafi, yana mai rokonta wata alfarma wadda bai taba nema daga gareta ba. Dama ya ce rashin amincewarki na nufin alamura da dama ckin rayuwa ta. Da ma yace in kin so, zan iya murmurewa kamar ban taba yi ba, haka in kin so zai iya zama ajalina! Wasu hawayen suka shararo mata. A yau Aminun da take so fiye da kowa da komai a duniya, hada da rayuwarta kuwa, ya tafi, akan buri da soyayyar wadda ta ki jini, ta tsana ta ke kuma gaba da ita fiye da mutuwar ta. In haka ne ita dame tayi riba a kiyayyar da ta ke wa yarinyar? Ta na raye a doron kasa, za kuma tacigaba da rayuwarta tamkar kowa har zuwa lokacinda ita ma nata ajalin zai zo. Ashe duniyar ba komi ba ce? Ashe duniyar ba madawwama ba ce? Duk wata daukaka, soyayya, dukiya, ilmi, gami da gata basa hana mu komawa ga mai kowa mai komi? Ta ci burirrika da yawa a rayuwar ta a kan Alameen dinta, taci burin ganin jikokinta daga gareshi, ta ci burin ya mallake komi na Daddy Makarfi, ta ci burin ya biye mata su sake korar Saratu su gina kansu, su tsere ma saa, suyi wa kowa fintinkau. Bata so ya hada rayuwa da tsintacciya mara asali, bata so ya hada rayuwa da wadda ba kowa bace baa kuma san ko yar waye ba, bata so Saratu ta more shi, ba ta so Saratu ta rabe shi. To a yau ya tafi ya bar mata duniyar bakidaya. Cike da kuncin da soyayyarta ta uwa, bata yi kokarin yaye mishi ba. Cike da kucin da soyyar da take ikirarin yi mishi bata taimaka ba ko kankani wurin fidda shi daga halin ukubar da zuciyarshi ke ciki ba. Ta sa habar zaninta ta share hawaye da majina a tare, zuciyarta na suya da kuna, gangar jikinta na kaduwa. Ta russuna ta kai hannunta na dama ta yaye farin kyallen da yai mata shamaki da kyakkyawar fuskar sa. Fuskar shi fes, tamkar bai taba dandanar wani bakin ciki a rayuwarsa ba. Babu ko kwarzane a jikinsa. Karfin imanin da ya kara ratsata shi ya bata damar bude Alkurani mai tsarki ta shiga karanta masa tare da sauran yan uwansa da mahaifinsa. A lokacin Ado direba ya sauke Ihsan a gidan, ta soma dara mutane tana shigowa cikin falon, sai ta tsaya sororo idanuwan ta a kan Aminun ta, nannade cikin farin kyallen da idonta ke ganinshi bakkirin. Wata juwa da ta shiga kwasarta ta soma ganin mutanen sun zama bibbiyu uku-uku, har zuwa lokacin ta kasa gasgata abinda ake ankarar da ita. Hajiya ce ta mike ta kamo hannunta, ta mika mata wani bangare na Alkurani da a ke karantawa, a lokacin ne kowa ya lura da jinin daya yanke yake malala a kasa kamar da bakin kwarya, kana ta fada jikin makarar ta kankeme shi jikinta na wani irin kyarma ta ce yaya za kai min haka? Yaya zanyi da babyn ni kadai Alameen bayan kace tare za muke rainon sa? Yaya zanyi da rayuwar bayan na sha gaya maka in ka bar ni bazan kara rayuwa mai kyau ba? Bazan iya amfanawa kaina komi ba? Kai da kace min Kaduna zaka ka dawo, muje nemon auren Intisar din ka, na riga na gama yi muku shirin tafiya honey moon Miami! A cikin gidanmu na da Alameen yaya zakayi mana haka? A yayinne idnnuwanta suke shiga lunshewa da kansu, kamin ta bingire a jikin shi kamar mai barki. Babu wanda bata baiwa tausayi a wajen ba. Dr. Hajjo ce da Goggo Jummai suka kinkime ta suka sa a motan Hajjon suka yi asibiti da ita. Jinin da ke fita jikinta ya balain gigita Aunty Hajjo, rokon ta Allah, rokon ta kada Ihsan ciki gareta yake ficewa kaman Anti Saratu, don haka ta ke kwarara gudu kamar ta tashi sama bata damu da zagin da motocin da ke gabanta da bayanta ke aiko mata ba, yayinda Goggo Jummai ke rungume da ita a bayan motar zuwa National Hospital inda akayi admittin din Aunty Saratu. Yafiya ta uwa da uba, albarka ta uwa da uba tare da adduar neman Rahamar Ubangiji daga bakin da baya da kaico, bakin uwa, Alameen ya same shi daga bakin mahaifansa. Yo me yafi wannan dadi? Hajiya bata tashi tsinkewa gabadaya da alamarin Sarki Allah ba, sai da aka zo fita da Alameen dinta zuwa gidan sa na gaskiya. A nan ne ta ce bata san wannan ba. Ta ruga ta rike shi tamau da karfin da kowa ya tabbatar ba nata bane. Daga Najib, Yasir, Bello har Faisal, watsar dasu tayi bakidaya da sukayi kokarin rabata da makarar dake dauke da Alameen dinta. Ta shiga surutu wadanda kowa ya tabbata baa hankalinta take yin su ba. “Kana fitowa na dauki waya in gaya maka cewa na amince, kazo ka daukeni muje gaban mahaifin ka in nema maka aurenta. Shine ban samu layin ba. Na zauna da niyyar gobe in taho da kaina, sai kawai na ji a radio wai kayi hatsari. Don Allah ka dawo, wallahi da albarka ta da kake nema kaje ka auri Intisar. Na yarda, na kuma amince da abinda a da, naki amincewa da gan-gan cewa ita din yar baiwa ce, ba duk yayane irin ta ba, ba duk yaya ne Allah yayi wa nasibobin da yayi mata ba, ba duk yaya mata ne masu hakurin ta ba. Na yarda, na amince ta zamo uwar yayanka, na tabbata suma yayan zasu zamo nagari, kuma masu biyayya da yakanah tamkar ku. Ko asirin da nayi mata a baya, ba da son raina ne ba, illa Hajiya Suwaiba da ta tursasani wai in ba hakaba watarana akan ta Babanku zai rabu da ni. Yayana, zan daina jin diminku duk Saratu zata kwace ku da kinibibinta. Kuma ni bance ayi mata na mujiya ba cewa nayi kawai a farraka tsakaninta da ku da Daddy Makarfi Jin irin batutuwan da take na tozarta kai, wadanda tabbas bana mai cikakken hankali bane yayanta suka sake yunkuri cike da karfin zuciya suka bambareta daga jikin makarar aka fita da shi. Duk abinnan da ake, Daddy Makarfi, rike yake da tazbaha idanunshi babu ko digon hawaye, a sahun gaba, wurin raka Alameen gidanshi na gaskiya. Hakika mutuwar Alameen ta girgizasu, ta wargaza tunaninsu, ta takaita farin-cikinsu, ta azabtar da ruhinsu, ta dai-daita tunanin su, ta girgiza zuciyoyin su ta kuma nutsar da su ga kara kadaita Allah! A wani bangaren mutuwa ce wadda baa taba yi masu ba. Sun shiga yanayi na kewa, kunci da alhini irin wanda basu taba shiga a tarihin rayuwarsu ba, ninkin ba ninkin halin da suka shiga a sailin da aka kulle Daddyn su. Wai ance ba mutuwa ake wa kuka ba, sabo ne, to sun saba da Alameen. Yaya ne mai kyautayi da son jinin sa, da iya takun rayuwar shi. Mutun ne da ko hanya ce ta hadaku da shi a wuni daya, zaka so ka zauna da shi shekara daya. Idan zama ne na shekara ya hadaka da shi, zaka so cigaba da zama da shi muddin rayuwarka. Yana da dimbin kirki da dimbin alkhairi. Yana da tsananin kulawa kan abinda yake so musamman iyaye da yanuwan sa, yana kuma nuna hakan a fuska, aljihun sa da zuciyar sa. To balle kuma matar shi abokiyar rayuwar shi. Mutuwar Alameen sai ya zamanto tamkar wani girgijen gini na gidan ne ya fadi, ya ruguje. Walwala ta karanta haka zuciyoyi sun azabtu, babu mai iya yiwa dan uwan sa taaziyyah sai kallon-kallo. Ba abinda kunnuwan su suka tsana da ji kamar wani ya ce da su, “Ya hakuri?� Allah ya sani, da ka ce musu wannan gara kawai ka ce, “Allah Ya Ji kan sa!� Anan ne za ka ga wasu hawayen kauna sun zubo. Irin kaunar nan da har abada, bazata taba gushewa ba. Makarfi yaga kauna daga alummar Nigeria da wajenta kwarai da gaske. Daga shugaban kasa zuwa gwamnonin jihohinsa duka, kusoshi na mulkin soja zuwa na farar hula, likitocin Florida musamman daga birnin Miami da duk wani sako ko loko da Alameen yayi karatu ko wani aiki na wucin gadi sun barko domin jajanta masa wannan babban gibi da yayi a rayuwarsa, da cike shi abu ne da har abada ba zai yiwu ba! Yaya goma suka saura masa amma ji yake a yanzun kam bashi da ko daya a duniya. Ko dama can kaunar Alameen daban ce data kowa a zuciyarsa, baya hada son da yake masa da na kowa cikin yayansa. Yana son shi, ya na kaunar shi tun yana tsumman goyon sa, ta yadda har yake kiran sa BURI NA. Sai dai har kullum yana mai farin-ciki da irin mutuwar da Alameen yayi; ranar Jumaa, cikin watan Ramadhan, da azumi a bakin sa.Wani irin hatsari amma kamar Baben dake goye a bayan mamarsa. Albarka ta uwa da uba. Kykkyawar shaida daga duk wanda ke tare da shi. Dr Rehab gurfane yayi gaban shi yana kuka da hawayensa marassa launi yana cewa Na dade ban samu mutun mai kyakkyawar zuciya irin M.A.B (Mohammed Alameen Bello) ba! Na dade ban ga Musulmin da ya san shi Musulmi ne a turai irin M.A.B ba, na dade ban ga mutumin da ke tara halal batare da digon haram a ciki irin M.A.B ba, na dade banga mutum mai alkhairi da duk abinda ya mallaka a duniya irin M.A.B ba, ban taba samun aboki nagari mai amana kwatankwacin sa ba. Hakika kun yi rashi babba, amma wannan ba rashin ku bane ku kadai na alummah ne. Nafi kowa sanin dimbin alherinsa. Tabbas shi ya tafi, amma aiyukan sa na alkhairi ba zasu taba yankewa ba! Hajiya kam, daga baya saida aka dangana ga psychiatric Hospital na Kaduna da ita, domin a cewa gamu da abinda suka kira mental disorder. Iyaka kokari likitan Alameen wato Dr. Alfred yayi wajen ganin cikin wata ukku da wasu yan kwanaki da Ihsan ke tare da shi bai zube ba. Amma na Anti Saratu ya fita, sai dai fatan Allah ya bada musanye da alheri. Kwanan Ihsan goma kwance a gadon asibiti bata san wanda ke kanta ba. An yi mata karin jinni fiye da leda uku hakannan karin ruwa baya yankewa. A binciken kwararren likita Alfred ta gamu da ciwon hawan jinni. Don haka suka cigaba da rikonta a asibitin yayinda suka sallami Aunty Saratu tun a ranar sadakar bakwai, kuma a ranar ne Haj. Hadiza da Ambasada Bashir da diyarsu Zarah da ta zama buleliya jazur da ita suka sauka a birnin Ikko inda daga nan suka biyo jirgi zuwa Abuja cikin tsananin dimauta da gigicewa, suna masu mika taaziyya mai girma ga Bello Makarfi. Sai ya ce mu gode masa, mu godewa Allah, Allah na gode maka! Hakikah karfin imani irin na wannan bawan Allah na baiwa kowa mamaki. Shukrah yake tare da hamdalah ga Allah a koyaushe akayi masa taaziyyar gudan jinin sa Ameenu. Ya kama hannun Ambassada yana murmushi ya ce, Basheer? Don me ba zan gode masa ba? Sanda ya halicceni nikadai ya halitta, ban san kowa ba, bansan komi ba. A hankali ya koyar da ni in mike in taka kafafuna a doron kasa. Ya bani ikon yin aure, na haife su, amma ba nawa bane, amana ce ya danka mini ya ce in kula masa da su zuwa lokacin da zai karbi abinsa. A duk tsawon lokacin nan daga niimarsa nake ci, nake sha, nake numfashi, na ke neman abinda zan kula da su. In ciyar dasu in tufatar dasu. Yayi min falala da niima daga duk wani jin dadi na rayuwa. Babban niimarsa gareni shine yayo ni Musulmi, yayi nufin karbe Alameen daga gareni domin ya jarraba imani na, yaga cewa shin ni mai godiya ne ga dimbin rahmominsa da fadhalolinsa a gareni ko ko zan butulce? Sabida wannan jarrabawa kankanuwa da ya yi mini? Don haka har kullum nake gode masa, na tabbata ban fi shi son Alameen ba, kauna ta da shi shine in yi masa addua, na nema masa Rahman Allah, kuma ina rokonku ku taya ni nema masa gafara domin hakikah yana daga cikin nagartattun yaya masu shiga zuciyar iyayen su! Satin su daya a Nigeria suke juya kasar Korea, Aunty Saratu ta gargade su ta kuma gargadi kowa da kada a sake Intisar ta ji wannan labari, wadda a lokacin take zana jarrabawarta ta karshe a secondary. Gargadinta yafi zafi a kan Hidayah, wadda ke tare da mijinta a nan Nigeria tare da su. Ita Hunainah dama tana Jamiar Al-Azhar da ke Cairo inda take karanta physiothearaphy. Suma kan su, sun tabbatar babu mai iya dosar ta da wannan labari illa tazo ta gani da idanun ta, taji abinda kowa ya ji, koda yake ita din mai jin fiye da abinda kowa ya ji ne! Ranar kwanaki na arbain da rasuwar Alameen an yi adduoi na musanman da sadaka mara iyaka, a yayin ne kafafuwa suka fara daukewa, sai su isu, wayyo! Ashe wanda ya mutu shine ya mutu, rayuwar sai wanda ke raye? Jarrabawa ta karshe da ta zana ta kama ranar litinin. Bata farin ciki ba kuma ta bakin ciki duk da cewa kusan rabin burinta na rayuwa,

Chapter 30 of 38