baki kara dariya ba, sai ranar da kika gan ni ko Daddy?�
Yayi dariya ya ce, “Kwarai Intisar, in na ce zan baki labarin irin suman da ta…� Hajiya Hadiza ta mike tana harhada tangarayen da suka ci abincin a kufule ta ce,
“Bari in bar maku wajen, sai ka ji dadin sawa ta kara raina nin tunda ita dama ba kunya ce ta ishe ta ba.�
Suka yi mata dariya dukkansu. Ba ta bi ta kan su ba ta dauki kwandon kayan abinci ta yi gaba, yayinda Amabassador Basheer ya shiga bata labarin rayuwar su tun daga ruga zuwa kauyen Shanono, har zuwa tahowar su kasar Faransa. Ba shakka ta ji tausayin maman ta sosai ta kuma kara jin kaunar ta a ranta.
Sun yi shirin barci ya lura Hadiza dai fushi take da shi, tana tsaye jikin mudubi tana sharce kanta data wanke cikin kumfar pert plus ya zagaya ta baya, kyawawan fuskokin su suka koma cikin mudubin ya ce,
“Wayyo ni Bishir ina zan sa kaina? Haddizana na fushi da ni a kan laifin da ban san na yi ba ta ce ba wani nan, kome kake yi mun kana sane, tunda ai na nuna maka bana so. Yarinyar nan fa kana mancewa diyar fari ce baa sakar masu baki haka�
Ya tuntsire da dariya ya juyo ta gaba daya ya ce “Don Allah Dijangala, yaushe zaki shigo gari ne?�
Babu inda wadannan kyawawan kafafun na Dije na basu taka cikin duniya ba, amma har yau tana abu tamkar tana cikin ruga ko kaugyen Shanono?
Ta kara kumbura amma sai tayi murmushi, don yadda ya kirata da Dije rabon shi da hakan tun dawowar shi daga Jamiar Nsukka dake kudu, ta ce,
“Ai ko Annabi (SAW) ma ya ce dan kauye sai yayi shekaru arbain a birni sannan ne zai zama dan birni. Ni ko yau shekaru na ashirin da takwas a birni, ka ga kenan har yau da saurana.� Ya yi dariya ya ce,
“Naji-naji ni dai hakanan nake son Dije na, ko ta zama yar birni ko bata zama ba. Bana fatan abinda zai bata mata rai balle ya raba ni da ita. Neman alfarmar Dije na nake ta dinga sassautawa Intisar tana nuna mata kulawar ta tamkar sauran yayan ta, domin ba shakka ita din abin tausayi ne. Har yau bata kai ga samun cikakken farin ciki a rayuwar ta ba.�
Washegari tun wajen karfe tara na safe Hajiya Hadiza ta shigo dakin da suke, a lokacin duk sunyi wanka suna shiryawa ta ce, “Me kuke shiri game da zuwan bakin?�
Intisar ta ce, “Wai su waye?� Hajiyan ta juya tana ce wa,
“Nima ban sani ba, amma tunda har Daddyn da kansa ya fadi zuwan su ai kin san masu muhimmanci ne.
Akwai komi a kitchen in da abinda baku samu ba sai ku yi magana a tura direba kasuwar yan kaba don ni bana jin shiga kitchen din nan a yau.�
Intisar ta ce a ranta ‘shiga kitchen ai sai mu manyan kuku.� Ta dauki mayafin Pakistan ruwan bula da ke jikinta ta yafa ta zura silipas ta fita tana cewa da Hunainah,
“Yi kwanciyarki ki huta, ni nan da kike gani ingarma ce a wannan fanning.�
Ta tuntsire da dariya ta ce, “Ah ah zan taya ki, ai in Allah ya ce ce ka huta sai ka huta, kuma tunda gani a yanzun ko mutuwa ce na ji na gani muyi ta tare.�
Tayi murmushin da ya tuna mata da wasu alamura da dama da suka gabata ta yi gaba tana cewa, “nagode sister, balle Insha Allah sai na riga ki mutuwa, ko ba komi zaki dage wurin ganin kullum ranar Allah kin yi min addua, kin taya ni yiwa Alameen kin kuma taya ni ganar da Ya Faisal abinda yake tunani game da ni ba hakan ya ke ba, illa dai ba zai taba saurara ta ba, da ya gane wasu abubuwa da kowa bai gane ba. Kwalla ta ciko idon ta, ta yi saurin fita don bata son Hunainah ta gani, ta san halinta yanzun sai ta fita damuwa, Hunainah ta yi dan jim, can kuma tayi tagumi tace
“Oh Allah! Ka dubi wannan baiwa taka, ka bata soyayyar nan da take nema mai barazanar raba ta da duk wani farin-cikin da take ciki.�
Wayar ta da ke kasan pillow ta shiga kida cikin daddadan sauti, kamar ta kyale ta bi bayan yar uwar ta sai kuma dai ta daga, ganin bakuwar lambar mai layin glo kuma ta nan cikin gida Nigeria ta sha mamaki, ta san dai dawowar ta kenan bata hadu da kowa ba balle ta bashi nambarta, gashi ba lambar Hidaya ba bata su Najib ba.
Cikin sassanyar muryar ta mai zaki da taushi ta ce,
“Yello! Hunainah Bashir ce a kan layin?�
Daga daya bangaren Hashim ya yi wata irin ajiyar zuciya, ya ce
“Don Allah Hunnainah, ki saurare ni kar ki katse, Hashim ne da kuka gamu da shi a filin jirgi, pls Hunainah help me, zuciyar zata narke in kika ki sauraron ta?�
Ta yi murmushi, muryar shi da yanayin maganar shi cikin nutsuwa su suka fi daukar hankalin ta, cikin kwantar da murya da ita kanta bata san ta yi ba, ta ce,
“To Hashim, mai ka ke so?�
Da sauri ya ce,
“Hunainah! Hunainah na ke so don Allah!! Ta kyalkyale da siririyar dariyar ta da tafi zakin sarewa a kunnuwan shi, ya kara kwanciya sosai a doguwar kujerar da ya ke kwance, ya kankame wayar gam kamar mai tsoron kada wani ya fizge, ya cigaba da magana cikin shauki da bege.
“Allah Hunnainah tun a Air-port din Cairo kika kwance mun kai, baki bar ni da wani tunani ba ko kankani sai naki, don Allah ki amshi kokon barana ki sammun gurbi a zuciyar ki ko yaya ne zan ji dadi in tsugunna a nan har zuwa sanda zaki bani babban gurbin.
Na yi maki alkawarin Insha-Allah ba zaki yi dana sani a kaina ba, ba za kiyi da na sani da zamowa na uban yayan ki ba, zan yi kokarin zama masoyi mai amana. Ki bar hadani da sauran mazan da aka ce kina tsoro don wallahi ni ke na ke tsoro Hunainah, sai yadda kika yi da ni. Cikin kwana dayan nan rak ba ki barni da tunanin komai ba sai na kyakkyawar fuskarki da fushin ki da kame mutuncin kanki. Ki yarda ba duk mazan ne muka taru muka zama daya ba, akwai masu soyayyar tsakani da Allah, wadanda zasu iya bada rayuwar su da komi da suka mallaka a domin ki Hunainah. Ki yarda da ni you are very special (ke ta musamman ce) ko zaayi yaudara ba zaa yaudare ki ba.�
Gaba daya ya kashe duk wata laka dake tare da ita, ta zamo pale duk wani kuduri da tunani da take da shi a kan maza, Hashim ya warware shi a yau.
A tsaye take a da, amma bata san sanda ta kai ga kwanciya bisa rug-carpet dake gaban gadon ta ba. Tana murmushi rungume da wayar kamkam ta kasa cewa komi yayinda shi kuma Hashim ya cigaba da ragargaza mata zuciya da dadadan kalaman shi har ta yarda ta amince ta kuma tabbatar wannan dai na daban ne, kuma shine Mr. Right din da ta ke nema. Muryar shi ta yi kasa sosai ya ce cikin matsananciyar damuwa.
“Plz Hunainah say something mana? Shin am I accepted? Ta ce cikin shagwabarta da ta saba yiwa kowa,
“To ai kai ne dadin bakin naka yayi yawa, bayan nasan matarka ma duk hakan kake fada mata?�
Ya kyalkyale da dariya ya ce,
“Eh mana, matata ma Hunainah duk haka nake gaya mata, amma nafi son Hunainah akan Hunainah.�
Ta ce, “Itama sunanta Hunainah?�
Yadda furucin ya fito daga bakin ta cike da kishi abin tausayi bai san sanda ya kankame fillon kujerar ba, tamkar ita din ne ya kankame ya ce,
“Sunan ta kenan Hunainah Bashir, I love her very- very much!.�
Ta ja wata irin kakakarfar ajiyar zuciya, wani dadi ya ratsa shi cikin murmushi ya ce,
“To ya, Hunny na, in zo Kano domin ki? Ba zaki haramta mun ganin wannan kyakkyawar fuskar ba, ba zaki yi mun rowar wanan daddadar muryar ba?�
Ta yi dariyar ta mai ban shaawa duk da baya ganin ta ya ji ta har cikin ran sa, ya ji ta har cikin jinni da jijiyoyi, tsuma kawai yake cike da bege saida ta ja aji ta ce,
“You are welcome.�
Ya ce, “gobe-goben nan fa?�
Ta ce, “Ahah sai dai next week ban gama hutawa ba tukunnah.�
Yayi shiru kusan minti uku bai ce uffan ba, ta yi zaton ajewa yayi har zata kashe itama sai ta ji ya ce,
“Kada ki yi mamaki kamin kwana bakwan da kika ambata kin ji labarin mutuwa na, kuma ke ce sanadi Hunainah.� Ta ce,
“Me yayi zafi Hashim ko yau ne ka zo, am sorry.�
Ya ji dadin saukin kanta da saurin amsa kuskuren ta, ya na son mace mai saukin kai da rashin amfani da soyayyar da ake mata tana azabtar da mai kaunarta, ya ce,
“Na gode Hunainah, ki gayar mun da Yayar mu kamin in zo mata gaisuwar surukai, wai don Allah ya sunan ta ne?�
Ta ce, “Saratu Intisar take, zata ji sakon ka yanzun nan, don ma ta fita ne da kun gaisa, zan je tana jira na.�
Ta lura in don ta shi ne su kwana suna yi ba zai gaji ba. Ya yi murmushi ya ce,
“Wai ke mai wayo, to ai ban gaji da jin sassanyar muryar nan ba Hunainah, ni ya za ki yi da ni to?�
Ta yi muramushi ta ce, “Zan kira ka in na gama Hashim ka yi hakuri, baki ne zamu yi� Ya ce,
“Shikenan Hunainah, sai me zaki dan ce mun da zan rinka tunawa kamin bakin su tafi?�
Ta yi dariya sosai tace,
“Wohoho Hashim! Me kake ci na baka na zuba? In dai Hunainah ce ka samu, Im only yours!�
Ya cillar da wayar ya rungume filon kujerar yana na gode, na gode Hunainah and Ill forever be yours too!�
How much do you like this story?
5/16/22, 07:35 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book four
*@Takori*
Page8ï¸âƒ£
Da gudu ta fada kitchen din ta kankame yar uwar ta, ta daga ta cancaras tana juyi da ita a kitchen din ta ce,
“Aunty Intisar sunan ki daga yau, kin yi mun abinda har abada bazan manta ba, me kike so in miki nima in faranta miki don Allah?� Ta ce,
“To aje ni in gaya miki, kada kirjin ki ya bude?� Ta dire ta tana dariya ta ce,
“Wallahi baki da nauyi, shafal kamar na dauki bokitin ruwa.� Ta bita da kallon mamaki ta ce,
“Hunainah, dama kina da karfi haka?� Ta juya mata baya cikin jin kunyar abinda ta yi, ita kanta bata san inda karfin nan ya fito ba, karfin soyayya kenan?
Ta dafa kafadarta ta ce, “Me ya faru ne sister, you look so happy than ever, whats the matter? (Da alama kina cikin, farin ciki fiye da koyaushe, me ya faru?) Ta juyo ta koma cikin nutsuwarta ta ce,
“Ke share kawai, nayi passing papers dina in ji Saajid Marwan (abokin karatun ta).� Ta san halin Intisar sarai, yanzu idan ta ji zancen nan sai kowa a gidan ya ji, tsiya kuwa da zasu yi mata ita da Hidaya, sai ta kasa kurbar ruwa a gidan don ta sha ce musu ba wanda ya isa ta bata muhimmin lokacin ta a kansa, sabida duk mazan mayaudara ne balle Hidaya da tayi saurin yarda da Najib bata ko tunanin karatun ta, gata nan har yau ta kasa komawa karatun, Najib sama- Najib-kasa bata da wani aiki sai nasa ga tsohon ciki tun bata cimma komi a rayuwa ba (a tunanin ta fa).
Intisar ta yi murmushi don ta sunsuno yar uwarta ta amma sai itama ta bagarar ta ce,
“Shine kuma sai ka ce yau kika fara cin jarrabawa, idiot� Ta sa hannu ta lakace mata hanci ta cigaba da kwabin da ta ke cikin mider, ta ce,
“Je ki daki ki cigaba da hirar ki da Saajid Marwan din naki, ko dai da shi zaa yi ne?�
Ta kyalkyale da dariya tace amman kin yanke ni, wannan abu dan kutuf ya kuttun tofa miyau? Ta ce,
“Yi a hankali dai ke mace ce, kada ki haifo irin sa ko wanda ya fi shi muni.�
Ta dubi yawan aikin da Intisar ta yi cikin dan lokaci tana can tana soyayya, ta jinjina kai ta ce,
“Amma ni a ganina Hajiyar su Najib ba karamin taimakon rayuwar ki tayi ba, tayi miki horo na ya mace, abinda kike yi ni ko rabin rabin sa bazan iya ba, ke ko cake wannan wallahi ganin wahalar in zauna in kwaba na ke.�
Ta yi murmushi ta ce,
“Nima na sha tunanin haka, in banda dukan da take mun da kebur, da shocking din da take jona mini kamar wata barauniya, da zagin da take mun na fitar hankali da ni da Anti Saratu, da gorin da take mun a kan son yayanta, wallahi da na gode mata.�
Hunainah ta fiddo ido ta ce, “Shocking fa kika ce? Ta girgiza kai cikin tuno tsohon bakin ciki ta ce,
“Shi fa, ke dai kawai a share, ban taba gayawa kowa ba ko Antina sai Alamin, na barwa raina, na barwa Allah ya saka min abinda matar nan ta wanzar da rayuwanta a yi mun, na barta da fitowar rana da faduwarta, na bar ta da duniya da abinda ke cikinta, na bar ta da Allah!�
Hawaye suka ciko idon ta, Hunainah ta ce, “Menene kebur? Ta ce,
“Wani siririn karfe ne da ake daure itace da shi, yafi bulala zafi, ya fi kututturen ice shiga jikin dan adam, kada Allah yasa a doke ki da shi Hunainah. Ta janye rigar ta sama ta nuna mata gadon bayan ta ta ce,
“Duba nan ki ga, wannan tabon har abada ba zai goge daga kafafuna da gadon baya na ba, kamar yadda har abada bazan yafe mata ba.�
Hunainah ta dubi zanen da ke gadon bayan ta wani a kan wani, sai dai yabi lafiyar jikin ta ya fara bacewa, ta share kwallar idon ta tace ido na idon matar nan Unh! Intisar ta yi murmushi ta ce,
“Kada ma ki fara wannan tunanin, don a yanzu ta zame maki dole, kakar dan ki da Hidayah zata Haifa, ni kuwa ta gama mun komi tunda ta haifa mun Alameen ta shayar da shi, ta so shi, ta kauna ce shi fiye da komai a rayuwar ta, ta haifa mun Faisal daya zamo ginshiki kuma tushen duk wani mataki da na taka a rayuwa.
Ya so ni, ya kaunace ni yayi duk iya kokarin sa wurin gina mun rayuwa mai inganci. Ina tabbatar miki duk wani hakilon Faisal na rayuwa domina ne, ni yake nemawa, bai damu da kansa ba tunda yana daga tsatson Hajiya, bana jin ko jikokin jikokin su zasu taba wahala a rayuwa.
Tana da arzikin da hankalin ki ba zai taba baki ba don haka ni yakema tanadin rayuwa amma ba shi ba. To don ta ki ni bata yi laifi ba, don ita zuciya an halicce ta da kishi a kan abinda ta ke so, ta na son yayan ta, su kuma suna so na, dole ta yi kishi dani.�
Hunainah ta yi ajiyar zuciya ta ce,
“Allah ya saka miki.�
Ta ce, “Wannan kawai itace magana Hunainah, A bar wa Allah ya fi a ja Yasin. Yanzu me ta isa ta yi mun a duniya sai dai in mata in kwana lafiya, to amma ba zan yin ba, ko gobe na gan ta durkusawa zan yi har kasa in gaishe ta, don na san Alameen ko a ina ya ga Mamata ba zai yi mata kallon banza ba, zai tsuguna da guiwoyin sa ya gaisheta cike da girmamawa. Ya gaya mun cewa kiyayyar da take min bata da dalili Allah ne ya daura mata, ba don kuma wani aibu na ta ke ki na ba, illa kawai ta samu kanta a mai ki na. Sai in fidda ta cikin masoyana in rungumi masu so na.
Bai yiwuwa mu samu soyyaya daga kowa don ko Annabin rahma Allah bai bar shi ba makiya ba. Kenan ya dace na yi mata uzuri. Uwa- uba tana auren mutuminda bani da kamar sa a duniya, tana auren Daddy Makarfi, da dadi ba dadi ta yi hakuri ta zauna da shi cikin kowanne hali. Ni kuma duk mai kaunar sa abin girmamawa ne a gareni.
Don haka a ranar da kika yiwa Babar Alameen rashn kunya, a ranar zan lakada miki dukan da baa taba yi miki ba!�
Ta rungumeta tana dariya ta ce, “Allah ya sauwake ki doke ni dukan haushi sai dai ki yi mini dukan kauna.�
Ta ce, “To ko ke fa?�
Cikin dan lokaci sun kammala aikin su mai ban shaawa, abinci kala-kala har kala bakwai Intisar ta shiryawa bakin ta da bata san ko su wanene ba, abin sha kala hudu, (snacks) kuwa baa maganar su kala-daban daban mai ban shaawa. Gabadaya abincin ta babu irin namu daga na Masar sai na Korea. Sai da kasusuwan bayanta suka amsa kas! Kana ta shiga wanka.
Ta dade tana gyaran fatar jikinta da mayuka masu gyara fata da sanya taushin fata, irin su aveeno E45 da norwegian formula kamin ta shirya cikin wani tattausan lesi (cotton) baki mai kananan duwarwatsu, ta killace gashin kanta cikin hair bound ta mulke siraran labbanta da lip-balm mai sanyin kamshi, ta kuma feshe jikin ta da turaren cKIn2U. Iyakacin kwaliyar ta kenan a kullum cool don ko kwalli bata damu da ta sanya ba sai Anti Saratu ta matsa mata.
Hunainah na gefen gado can a makure tana amsa waya cikin yar karamar murya don bata son Intisar din ta ji, da ganin yadda take kashe murya kasan da masoyin da a ke matukar so ake magana. Intisar ta yi biris da ita kaman bata san me take ba amma a ranta tayi dariya tayi har ta gaji.
Ta na zaune a gaban mudubin bata mike ba tana fesa turare wani dan yaro da bai fi shekaru biyu ba ya yane labulen dakin ya shigo yana zare kyawawan idanun shi alamun bakunta, yatsun shi biyu duka a baki yana tsotso, sanye yake cikin caftan na purple shadda rini me tsadar, kafar sa daure cikin farin kambas.
Da farko dai zuciyar ta ce tayi wani irin mummunan bugu kafin hawaye su biyo baya su bata mata kwalliyar fuskar ta, kirjin ta yana harbawa da sauri da sauri ta karasa ga yaron, ta zube ragwaf a gaban sa ta kama hannuwan shi da ke cikin bakin sa ta rungume shi sosai a kirjin ta, hawayen ta na zuba a gadon bayan sa.
Ganin babba tana kuka shima sai yasa kuka, ta yi saurin share idon ta tana dariya ta cira shi zuwa gefen gado ta zaunar da shi a kan cinyoyinta ta jawo jakar Hunainah da bata rabo da choculate ta dauko kit-kat ta bare ta bashi, ta ce,
Alameen Alameen Bello, suna na Aunty Intisar, ka na so na? Ya gyada mata ka kawai cikin halin ko in kula, ta ce wa ya kawo ka? Yace Uncle dina da Baba na.
To ai uncle din nashi da Babannin nashi suna da yawa, don haka bazata ce wanne ne ba wanne ne ba. Ta ce ka ga shi wancan Alameen din yana sona, yana yi mun murmushi, kaima kayi mun murmushi don Allah?
Gaba daya ya bude bakin yana yi mata dariya da kyawawan hakoran shi, beauty point din da cleave suka lotsa a tare, tayi saurin juyawa tana share hawaye.
Hunainah ta kashe wayarta ta dauki yaron a cinyar ta, itama kwalla ta cika idonta tace Allah da girma yake, Intisar ashe akwai irin wannan kama ta da da uban sa? Intisar ba baki, tace Alameen ka ga ka sa Aunty Intisar kuka, ka bata hakuri ya kai dan hannunshi ya shafo hawayen ta, ya sauka daga cinyar Hunainah da gudunsa yayi waje, a hausar shi wai Baban shi zai je ya nunawa Antin tana kuka.
Hidayah ce ta shigo Najib na biye da ita kaman jela, kafin ka ganta sai ka fara ganin tulelen cikin ta sabida girman sa, kafafunta sun kunbura haka ita kanta ta zama katuwa basu san sanda suka fashe da dariya ba. Ta juya cikin shagwaba, hannunta a ido tana kai karar su ga Najib. Ya ce,
“Kyale su honey, shekara mai zuwa duk haka zasu koma suma, gara ke tare zamu yi nakudar mu mu biyu mu haife kayan mu.�
Hunainah ta ce, “Tab! Allah ya nuna mun wannan rana, wallahi bayan taga zai koma ya na leken ki, ki na wayyo Allah Najib, ba ka ce tare zamu yi nakudar ba, ya zaka tafi ka barni ni daya? Tana yi tana gwada irin rike kwankwason da Hidayar zata yi gaba daya suka sa dariya har ita.�
Najib ya ce, “A bar zancen wasa, ke Intisar bakuwa kika yi tana falo, Maman Hunainah ta ce ku je dukkan ku. Kin ga dan ki ko? Ta sukuyar da kai a hankali ta ce, “Eh, Alameen ya girma fiye da yadda na zace shi, kamannun shi da Baban shi har sun yi yawa.�
Ya yi murmushi ya ce, “Kowa haka ya ke cewa.�
Duk sai suka yi shiru dukkansu, babu shakka kowa Alameen din ya tuna. Najib ya bagarar ya dubi Hidayah yace zani cikin gari honey, take kia of yourself, pls, me kike son in taho miki da shi? Ta yamutsa fuska tace kafafunnan sun matsa mun Najib, ko asibitin zamu koma? Ya ce yana karasowa inda take kwance a gafen Hunainah,
“Aah bari in gani, I can deal with them, messaging din su zan cigaba da yi zasu sace yanzun nan.�
Gaba daya ya manta da su Intisar da ke wajen, ya debi kafafun ya aza a cinyar shi yana matsawa sannu a hankali. Cikin matsananciyar kunya suka zame daya bayan daya suka bar masu dakin zuciyar su cike fal da shaawar su, barin Hunainah da a take ta rinka kissima wai inama ita ce da Hashim din ta, ita kuwa Intisar tunanin ta shine Allah ya bata mai son ta kamar yadda Najib ke son Hidayah, har baya iya jurewa a gaban kowa nunawa yake bashi da abu mafi muhimmanci kamarta.
Ta shiga falon da sallama, amma sai tayi turus, a bakin kofar bata karasa ba. Zuciyar ta na harbawa, kafafuwanta suka sage, jikin ta yayi sanyi; Hajiya Nafi ce, a zaune a falon mahaifiyar ta sai Khaleel da ke shan lemun Ribena. Ta juya da niyyar komawa cikin gigicewa amma muryar da ta ji daga can kofar shigowa ta katse gudun jinni a cikin jikin ta, ta warware tunanin ta kaf ta kasa koda motsa kafar ta balle ta idasa yunkurinta na komawa inda ta fito, muryar Faisal.
Ya ce Intisar! Bata amsa ba, amma ta dakata kuma bata juyo ba, shima bai shigo cikin falon ba, daga can bakin kofa yake maganar kamar baya so, da gani don ta zame masa dole ne amma da ba zai yi ba.
Ba kuma tare da ya kalli sashen da take ba ya ce (cikin murya ta girma da bada umarni).
A matsayin Yayan ki, baa matsayin dan ta ba, ina ganin ya dace ki saurareta. Ba lallai ne ki yarda da abinda zata ce da ke ba, amma a kalla tunda gaba take da ke, ta kuma taso gari-ya-gari domin ki, ta kashe muhimmin lokacin ta tazo gareki, duk da kike kasa da ita, ta zo neman wata alfarma a gareki.
Ashe kenan ta san cewa ke wata aba ce mai daraja da zata nemi wani abu daga gareki. Bai dace ki wulakantata ba tunda Manzon Allah (SAW) ya ce bakon ka annabin ka ne. Kuma ko a lahira wani kan ci albarkacin wani.
Da haka ya juya yayi ficewar sa. Ya bar mata permanent (tabbataccen) kamshinsa na (5,000 Doller perfume) da har a mafarkin ta jinsa take yi. Hawayen suka idasa zubowa bisa kundukukinta.
Cikin dauriya da jarumtaka ta juya ta isa gabanta, ta zube guiwoyinta a kasa hawaye na zuba a idon ta tace Hajiya ina wuni?
Ita kanta Hajiyar kuka take yi, haka bata ji dadin kalaman da Faisal yayi amfani da su wajen yi mata magana ba, tamkar ya goranta mata kaunar da suke
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 38