cikin tsarkakakken zuri’a ta ba. Haka kawai, muna da ‘ya’ya ba rasawa muka yi ba, daidai har goma, ka dauko mana dan tsuntuwa? Wa ya sani ma ko uwarsa shegensa ta yi ta yar don gudun abin kunya shi nemu za ka kwaso mana?�
A lokuta da dama Hajiya Nafi kan mance zuciya irin ta tsohon sojan, tsawa ya daka mata mai gigitarwa ya ce, ‘Get out! Stupid, idiot.�
Kafin ta farga kuma har ya rigata fita daga dakin, shi da ya ce ta fita, ta yi tsaki ta yarfar da hannuwa cikin kakabin yau ita Brigadier ke kira idiot abin da bai taba yi ba, shekaru daidai har ashirin da biyar sai yau a kan wannan tsintattar magen, wannan ya kara mata tsana da tsangwamar jaririn da ba ta ma san ko wane jinsi ba ne a rai.
Lallai in ta bar jaririn nan tare da shi tana shirin ganin wulakanci da tashin hankali, don shi in ya so abu ya so shi kenan, haka in ya ki shi ko duniya za ta taru a kan shi ba zai so shi ba.
“Haka kawai ina zaman � zamana a kwaso min jidali, ai sai ka kaiwa munafukar matar ka tunda dama da ita ku ke kulle-kullen munafurcin ku, sai yau don rana ta baci za a kira ni? In ma kai ka yi shegensa aka kawo ma ai in ta yi wari ma ji.� Ta yi waje fuuuu! Kamar guguwa tana kwalawa ‘yar koren ta Asbi kira.
Kishingide take cikin (3 seater) tana nazarin jaridar TIME takun shi kadai ta ji bisa marble din da ke shimfide a gidan ta san cewa shi ne, kasancewar shi, maigidan ta, Brigadier Bello Makarfi, mutum ne mai takin kansa. Duk da ya kwana biyu, kakkarfan mutum ne mai tsari, ga masifar saukin kai, musamman a cikin iyalinsa.
Ta aje numfashi da jaridar gaba daya ta maida hankalin ta ga kofar shigowa, Sanye take cikin jajayen English wears riga da siket na zaman gida, a kunnen ta jan dankunne ne na barima dan mitsitsi, ta matse gashin kanta cikin jan hair-bound sai kamshin turaren ta Sandara ke tashi a falon. Saratu Sani Makarfi kenan.
Ta mike cikin zumudi ta amshi babyn,
“Ikon Allah, Baban su Khalil baby daga ina?�
Ta kai duban ta gare shi, kyawawan idanun ta na masu bidar bayani, ‘yan bakaken lebban ta makale da lallausan murmushi.
“Allah ne Ya ba ki, short and simple.� Ta fadada murmushin ta zuwa dariya-dariya.
“Kada ka zolaye ni da abinda har abada ba zan samu ba.�
Ta rungume babin a kirjinta idanunta suka ciko da kwallah, ya janyo ta gare shi ya ce,
‘Na taba yi miki wasa kwatankwacin wannan?� Ta girgiza kai da sauri.
‘To I mean what I said (Ina nufin abin da na ce).
“In kuwa haka ne sai in ce Allah ya biya ka da Aljannar Firdausi Baban su Khalil, very cute baby girl, (kyakkyawar jaririya). Don Allah Daddyn daga ina?�
“Daddy ko Darling?�
Ta yi murmushi ta ce, “To Darling din, Allah ji nake kaunar ta na karuwa a raina, har bana jin zan iya baiwa uwar ta, ka taimaka ka karba min riko baban su Khalil.�
Ta kwantar da kanta bisa kafadun shi kamar ta saki kuka, ya janye zuwa ga kan wayarsa da ke ta faman tsuwwa ya amsa ya ce,
“Hello.�
‘Wato Daddy ka mance da mu a school ko ka ce da Sam ya zo ya dauko mu ko?� Faisal ya ce.
“Kuma ka san yunwa ta matsa min amma ba ka damu ba ko�.� Cewar Najib.
“To da ka je Kanon, ka sayo min Gurasar?� Yasir ya tambaya.
“Wai me ya same ka ne Daddyn mu? Muna ta Magana ka yi shiru. Ko Hajiyar mu ta sake bata maka rai? Faruk ya dora na shi tambaya.
“U keep silent Daddy, what’s the matter (Ka yi shiru me ke faruwa)? Inji Furkan.
“Wai ma tukunna ka bawa bindigata bullets din da na ce ka sa mata kafin in dawo?� Bello (Daddy) ya ce.
Ya yi murmushi cikin rashin gajiyawa da jerin gwanon tambayoyin su, don in akwai abin da ya saba da shi to wannan ne.
“To shin nawa zan fara amsawa ne my cuties, irin wannan tambaya haka, yaushe ku ka koma ‘yan jarida daga sojojin da na sani?�
Gaba daya suka rude, kasancewar duk suna jin sa a tare, shi ma hakan handsfree.
“Nawa-nawa za ka fara amsawa Daddy.�
“To ku yi mun uzuri my dear soldiers, Antin ku ce ‘in labour�, so ku bari in ji da zuwan our newly born baby.�
“Eho!!! Daddy Anti amarya haihuwa za ta yi? Amman mace za a haifo mana ko?�
“Ga Sam nan na turo shi ya dawo da ku in kun zo kun gani.�
Ya rufe wayar ya dubi Saratu da ke ta faman lallashin baby ya bude mata hannuwan shi duka, ta tafi da sassarfa sai kuma ta kara da gudu-gudu ta shige, ya maida ya rufe su ruf, ita da babin ya shiga rada mata cikin kunnuwanta.
“A kullum shi yasa nake dada son ki Saratu, duk abin da ni ke so kina so. In an batamin sai ki shayar da ni farin cikin da ke mantar da ni ni tsoho ne. Allah ya yi miki albarka ya kuma sakawa Baffa Sani da ya yi tunanin hada mu aure da alkhairin duniya da lahira. Wannan yarinya Allah ne ya ba mu.�
Ya kwashe duk yadda ya tsinto babin gaba daya ya fada mata har yadda su ka yi da Hajiya kafin ya shigo sashin ta ya fada mata bai rage komai ba. Ta yi salati ta kara kankame jaririyar gaba daya ta ce, “Amman Hajiya ta yi wauta, da ai na kowa ne, kuma ba ka san wanne ne zai ji kan ka ba. Ni kam Allah bai nufe ni da haihuwa ba da kai Baban su Khalil, amma na gode masa da ya kawon ta inda ban tsammani ba.
Na yi alkawarin rike yarinayr nan tsakanina da Mahaliccina ba kuma zan taba nuna mata ba ni na haife ta ba.
Abin yi yanzu shi ne ka je ka rufe bakin wanda duk ya san al’amarin don gujewa bacin rai a gaba, sai in ce Ubangiji Allah ya taya mu riko da amana.�
Ya yi mata kyakkyawar sumba ta nuna kauna da yarda, hadi da godiya mai tarin yawa. Ko a yanzu kimar amaryar shi Saratu ya dadu a idanun shi, hakan nan ya kara ba ta wani matsayi na musamman a zuciyar shi.
“Ni za ni in biyewa shirmen su Furkan, sai ku je Mother’s Delight ki hado mata duk abin da za ta bukata. Daga naira daya zuwa million na yarje miki Saratu ki je ki hado a kawo min bill din.�
Ta yi murmushin da ya fidda siririyar wushiryar ta,
“Har yanzu ban ji sunan Baby na ba?�
“Ai yanka za ai Saratu sati mai zuwa idan Allah ya kai mu, haihuwa fa muka yi, kuma haihuwar ma na ‘ya mace da muke mafarkin samu a gidan nan, kenan dole a yi shagali ko don rufe bakin mutane?�
Ta yi ‘yar dariyar ta mai ban sha’awa ta ce,
“To ai kowa ya san ba ni da ciki, the worst part din ma yadda ku kai da Hajiyar su Aminu, yi tunani?�
Ya yi dan jim,
“Idan har za ta dagawa mutane hankali ne kan abin da aka yi domin neman mafificin lada a wurin Ubangiji, wallahi sai dai ta bar gidan nan, don ba ta isa ta sani ko ta hana ni ba.�
Ta girgiza kai ta yi daki rungume da babyn ta da ta samu barci.
*****
“Magana ce nake so mu yi?�
‘Ba ni da lokaci.�
“To ki aro, ki karkade kunnuwan ki ki ji ni. Dukkanin mu ba yaro a nan, kuma na yi zaton shekarun ki da tunanin ki ya isa ki zama mutum, amma kina halin dabbobi.�
Ta gwalo ido cikin mamaki, “Yau ni ka ke kira dabba Baban su Khalil, a kan tsintacciyar ‘yar ka?�
‘Ni ban ce miki dabba ba, na ce ne kina irin halin su na rashin tunani. To ki ji ba da wai ba, ranar da duk ki ka bude baki ki ka furtawa wani yarinyar nan ba ‘yata ba ce, tsinto ta na yi, babu igiyar aure ko daya a tsakanin mu.�
Ta fashe da kuka,
“Au! Ci min mutunci za a yi saboda ka je ta tsafe ka shi ne za a tozarta ni? Ba ka cewa ka sake nin kai tsaye?�
Ya juya zai fita ta sha gaban sa fuskar nan jage-jage da hawaye, “Na ji ba zan fada ba, amma ina fada ma gaskiya, ba ruwana da yarinyar nan, na tsane ta, Allah tun ranar da ka kawo ta, na fada na kara.�
‘Wannan kuma matsalar ki ce, gafara nan ban hanya in wuce tun ban babballa ki ba.�
‘Ai ban gama ba ne, mijin karuwa, kada shegiyar ‘yar ku ta sake ta shiga sabgar halatattun ‘ya’yana.� Ya nuna ta da dan manunin sa ya ce,
“Nafisa, ke Nafisa ki fitar min a ido in rufe. In ki ka kara kira min mata karuwa, za ki dandana kudar ki, karuwanci har aka fi ki? Ko ba kina karuwancin na aure ki ba?
‘Ya’ya kuwa ‘ya’yana ne babu fitinanniyar da ta isa ta raba mini kan su. Kin san tsintsiya ko? To haka zan maida su. Ki kiyaye zugugun bakin nan naki.�
To kwana biyu dai suna badakala da yin ta ba dadi da maigidan. Ta dai tabbatar Brigadier gab yake da ya guntile tsohon auren su a kan shegiyar jaririyar shi. Yinin ranar zungur kukan bakin ciki ta wuni yi musamman da ya kori ‘yar koren ta Asbi ya ce kuma ko gaisuwa ta sake yi da matar shi sai ya harbe ta ya ba ungulu naman ta, don ya lura sun kukkulla munafurcin su da suka saba. Sam direba da sauran sojojin da ke aiki a karkashin sa duk ya tura su Lagos ya dauko wasu sababbi daga Porthacourt. Brigadier Bello Makarfi kenan, namiji saura mazan jiya, hadari sa gaban ka, guguwa mai fyade wanda ta so, sojan arewa mai watsa shashashai. Wannan ne kirarin sa.
How much do you like this story?
5/7/22, 13:10 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book one
*@Takori*
Page1ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
Wane Ne Brigadier Bello Makarfi?
Bello Isyaku Makarfi, mutumin garin Makarfi ne ta jihar Kaduna, Bello ya tashi maraya gaba da baya hannun Baffan shi Mal. Sani ya girma. Lokacin da aka tura shi NDA garin Jos, shekarun shi ba su fi ashirin da biyar ba. Kwazo, himma da sadaukar da kai irin nasa ya kai shi matsayi iri-iri a soja cikin ‘yan shekaru kalilan.
Ya auri Nafisa diyar wani shahararren dan siyasa mai neman kujerar gwamnatin Kaduna na lokacin wai shi Magaji Doller ne tun auren saurayi da budurwa, don dukkansu so ne ya hada su lokacin tana ajin karshe a sakandire, sai bayan auren ne ya fahimci Nafi watsatstsiya ce, irin ‘ya’yan nan da iyaye suka jika da naira, babu kwaba babu hantara kasancewar ita kadai suka Haifa, sai daga baya ne Allah ya nufa ta zauna gidan auren, da taimakon kaunar da take masa.
Gidan iyayen ta yana nan a unguwar Kabala Cutain, cikin garin Kaduna wanda a halin yanzu mahaifiyar ta ce kadai a ciki (shekarun baya ne mahaifin ta ya rasu a hatsarin jirgin sama a kan hanyarsa ta zuwa birnin New York).
Wannan ya ba ta damar zama millionnaire domin daga ita sai mahaifiyar ta kadai suka gaje mahaukaciyar dukiyar da ya bari. Kusan Nafisa ta fi mijin ta kudi don shi ma’aikacin gwamnati ne na kasa, sai dai za a kira irin su top-millitary a yayin da ita kuma ke harkar cinikayyar gwalagwalai daga kasashen Africa daban-ban da sauran kasashen da ke ketaren mu.
Akwai babban shagon sayar da gwalagwalai nata na kashin kanta da ta bude a babbar kasuwar Kaduna, wanda ta sanya wa sunan first born din ta Al’ameen Jewellaries.
Akwai matsananciyar kauna tsakanin ta da babban danta Al’ameen wanda ya ci sunan marigayin mahaifinta ne. Hakan nan sun bude wani a Lagos sai dai na hadin gwiwa ne tsakanin ta da aminan ta Haj. Suwaiba matar gwamnan Kaduna na lokacin da Haj. Badi’a ministar kudi ta lokacin. Sun yi aure yana matsayin Laftanal-kanal a shekarar da suka haifi Mohd. Al’ameen, yana major din shi ta haifi Najib, Faisal da Yasir. Shekarar da mahaifin ta ya rasu ne ta haifi Nasir da Bello mai sunan Daddy da suke kira (Daddy Karami).
Daga Bello ta haifi Faruk sai ‘yan biyu duk maza Idris da Furkan. Dan ta na karshe shi ne Ibrahim Khalil da bai fi shekaru uku ba a lokacin. Kusan duk yaran sun fi shakuwa da Hajiya Saratu fiye da ita ba don komai ba sai don ba ta da lokacin su, harkar kasuwancin ta ya fiye mata komai muhimmanci, ke dai bar ta masifar son ‘ya’ya da kashe masu kudi, amma babu lokacin kula da tarbiyyantar da su.
Duk wata kulawa da ta dace uwa ta kwarai ta bai wa ‘ya’yanta yaran nan sun same ta ne daga Aunty Saratu, tana iya kokarin ta kwarai wajen ba su kulawa ta musamman da ingantacciyar tarbiyya, kai ba ka ce ba ita ta haife su ba, ba ta ko damuwa da habaicin da Hajiyar ke yada mata na “a ci a yi kashi kadai.�
Ita ko rurrutsa ma take wato kwanika, don duk shekara take haihuwa, sai daga kan Khalil ne haihuwar ta yanke mata, don haka kusan gaba daya yaran dukkansu daya, ba za ka iya bambance wa ko kani ba in har ba su suka gaya ma ba da bakin su.
Brigadier Bello kakkarfan mutum ne na sosai, wankan tarwada mai kyakkyawar sura. Da wuya ka yi masa kallo daya ba ka maimaita ba saboda cikar zati da kamala. Mutum ne mai tausayi da jin kai, ya sha fadawa hadarurruka iri-iri a zamanin kuruciyarsa irin dai na kowanne soja, amma juriya da maida kai irin nasa yasa har kullum cikin promotion kan promotion yake.
Bai damu ba don ya sadaukar da ransa kan cigaban kasar shi, Nigeria. Jaridu da mujallun Kaduna kan so buga abin da ya shafe shi saboda yadda jama’ar Kaduna da kewayen ta ke son shi. Ba shi Kaduna, ba shi a Lagos, kuma ba shi Abuja inda duk aiki ya wulla shi anan yake shi da iyalin sa, ayi ta famabn canjin makarantar yara.
Rayuwar su abin sha’awa ce ga kowa barin ‘yan mazan ‘ya’yansu masu tsabar kama da juna. Duk da kasancewarsa ba mazauni ba baya sake da tarbiyyar ‘ya’yan shi. Islamiyya dole ne su je ta da yamma haka da dare ya aje masu malamin Addini da ke karantar da su littattafan Addini irin su Kawa’idi, Ishmawi, Sirah, Arba’una Hadith, Nurul-Mubeen da sauran su. Idan kuma sun tafi makarantar boko ba su dawowa sai karfe hudu na yamma, domin akwai special edtra lesson da yasa ake masu after school hours. Don haka duk cikin yaran Hajiya Nafi kaf babu dakiki kowanne kwaro ne wajen karatu, idan har ka ji su suna tafka musu to a kan karatun su ne, don kowanne ji yake ya doke dan uwansa a hazaka. Haka lafazin da ke fita bakin su a shekarun su zai ya ba ka mamaki, babu wanda ba za ka ji shi da ma’ana ba. Ga hadin kai, ga baiwa babba girmansa koda shi ke binsa a haihuwa.
‘Ya’yan Brigadier ba su san wani abu wai shi yawo ba ko raini ga na gaba. Basu iya zagi ba, basu iya karya ba, basu san yaya ake yin su ba. Haka idan sun dawo daga lesson din dare, kafin su kwanta karatun su ya koma wuyan Anti Saratu.
Saratu, diyar Baffan Brigadier ce, auren zumunci ne a tsakanin su, zumuncin ma irin wanda aka zama daya din nan kamar wa da kanwa na ciki daya.
Ta kammala digirin ta na farko daga Jami’ar (Edeter) da ke U.K, inda ta karanci Insurance zallah. Wannan kuwa daurin gindi ta samu daga murdadden dan boko dan uwan ta Bello, wanda ya dauki nauyin komai na karatun ta shekaru hudu cif a matsayinta na kanwarsa wadda nauyin komi nata ke kansa tunda ba’a yi mata aure ba.
Ta dawo gida tana da shekaru ashirin da hudu da haihuwa. Rikicin auren ta da Alhazai biyu shi ya yi sanadiyar auren ta da yayanta, ko ko in ce daga gatse.
Da fari Baffan su ya kira Brigadier ne ya ce,
‘Ka ga karatun nan dai kai ka daurewa Saratu gindin yinsa, ga shi ta dawo kowa ya zo ta ce ba ta so ga illar shi, kana nufin auren ma ka daure mata gindi ta ki yi?�
Ya ce, ‘A’a Baffa, Saratu na son yin aure, ba ta samu wanda ya kwanta mata ba ne har yanzu. A yi hakuri a kara mata lokaci.�
Baffan ya yi salati ya ce, “Shekaru ashirin da hudun za a karawa lokaci? To wallahi ba a gidana ba sai dai ka dauke ta ka kai can gabanka ta zauna. Duk kun ja min surutu a gari, ban isa in je wajen daurin aure ba sai an nuna ni ana zundena ga wanda ya aje uwar mata a gida wai boko. Idan ba kya son shi Alhaji Saminu saboda mata uku, shi wannan ministan fa mai mata daya saboda Alah me ye laifin sa?�
‘Yar auta Saratu sai ta kwabe fuska, ‘Gaskiya Baffa ya fiya tumbi, rundumi, ina zan kai wannan kayan jigida?�
Brigadier ya yi dariya shi ko Baffan sandarsa ya dauka zai buge ta Bello ya tare, ya ce,
“Ni za ki kawowa fitsara don ki nuna min ke kin je turai kin fetsare? In gaya miki Mungo-Park ma kakan-kakan ku mun ga iyakar sa balle ke, kuma tunda ba kya son Alh. Aliyu sai ki tattara ki bar min gida ko a daina ganin ki a garin nan ana nuna ni a wajen daurin aure.� Ya soma kuka.
Brigadier ya ce, “Baffa duk abin bai yi kamarin haka ba, kash…�
‘To, to na ji bai yi zafin haka ba, ai sai ka gaya min me kuma ku ke nufi? Ka ce karatu, an kare, sai kuma me? A sani a bakin duniya ko me? Ba kwa auren junan ku kowa ya huta? In kuma shi ma tumbin gare shi to don uban ki zo ki fice min a gida ki koma can turan ki auro bature sardidi sannan ne ki ka burge ni.�
Dariya ce ta kama su dukkan su, ya yi murmushi ya tausasa murya cikin rarrashi, ‘Allah ya ba Baffa hakuri, abin bai yi zafin haka ba sam, Saratu kin ji me Baffa ya ce? Me zai hana ni ki aure ni?�
Kunya ta kama ta, ta sunkuyar da kai ba ta ce komai ba. Sai dai a ranta hakika ta yi na’am da auren Yayan ta, don dama tuni ta dade tana sha’awar yiwuwar hakan, don duk duniya ba ta ga namijin da ke burge ta kamar shi ba. Sai dai me? Tana masifar tsoron Hajiya Nafi, don ta san ta kwarai kamar yunwar cikin ta kan azababben kishi a kan mijinta da suma da suke dangin sa balle sun aure shi? Baffan ya ce,
“Za ki amsa ko sai na yi kwallo da ke?�
Ta zabura ta fake a bayan Yayanta, cikin tsoro ta ce, “Baffa to Hajiyar su Aminu fa?�
Brigadier ya yi murmushi, “Ke manta da ita, ba abin da za ta yi miki, kin amince ko Saratuna?�
Duka suka yi wa juna lallausan murmushi har suka bai wa Baffan kunya, ya mike yana karkade buzun shi ya yi cikin gida.
Ba karamar badakala aka kwasa da Hajiya Nafi ba kan auren Saratu, don cewa ta yi munafurci ne su Baffan suka kulla mata don dama sun tsane ta, amma in ban da haka a rasa wadda za a kakaba masa duk cikin dangin nashi sai yarinyar da suka tashi gida daya?
Kwanan ta goma a yaji babu wanda ya je bikonta da ta ga abin ba na wasa ba ne, dolen ta ta dawo ta tadda amarya a rufaffen sashin da ba kowa, kamar ta yi hauka, ta hana kanta ta hana kowa a gidan nan sakat da bala’i.
Da ta ga wannan ba zai mata ba, domin kamar tana zuga su ne su kara likewa juna sai ta koma bin malamai da ‘yan tsibbu, ta mance Saratu kanta ‘yar malam ce, ba kowanne karabitin asiri ke kama su ba.
‘Ya’yanta ke ta tausar ta da cewa ta kwantar da hankalin ta har Najib na cewa,
“Maman mu in ta zo me za ta yi miki? Maman mu ba a kan ki za ta zauna ba.�
Shi ko Faisal cewa ya yi, ‘In dukan ki ta yi Ya Aminu zai rama miki.�
To sai ya kasance ita Saratun mace ce mai ilmi na zaman duniya ta san yadda take tafi da abokiyar zaman ta cikin lumana. Amma har inda nan ke motsi, Hajiya Nafi kafarta ba ta bar gidan ‘yan tsibbu ba da ‘yan bori ba a hana Saratu haihuwa.
To sun ci nasarar wannan kam, tunda ance abin gaskiyar mai shi ne. Amma kullum mijin su kara son ta yake saboda hankalin ta da tunani.
Rashin haihuwar ta ba su danganta shi da kowa ba face Allah. Su kan ce lokaci ne har yanzu bai zo ba. Shekarun ta biyar a gidan wadanda in kin dube ta ba za ki ce ta hada ashirin da taran ba. Tana aiki da Insurance Company na Kaduna.
Haj. Saratu baka ce bakin da akan kira black beauty. Mace ce da ta lakanci kalmar ‘gayu� duk da shekarun ta still ita ‘yar gayu ce komai kuma cikin gayun da bokon take yin sa. Rakiyar Brigadier aiki duk ita ce haka in za shi abroad domin hutu ko aiki duka Aunty Saratu ce mai rakiya. Ita Hajiya son ‘ya’yanta ta sani sai maida kobo ya koma dari.
*****
Ta sanya baby a ruwa ta yi mata kyakkyawan wanka, tana mai tazbihi ga Al-Khaliku Sarkin kaga halitta ta yadda ya suranta wannan yarinya tamkar diyar Larabawan Masar. Wani irin so ne ke huda bargo da tsokar jikin ta na ‘yar da ba ta san ko ta wa ye ba!
Ta ciro bebin daga ruwan tana nannadewa a tawul kenan su Khalil suka shigo, wani na ture wani, kowannensu na cewa shi zai fara goyon bebin da Daddy ya ce ta haifa suna makaranta. Dadi ne ya kamata ta ce, Najib ne zai fara goyawa tunda duk ya fi su karfi.
Najib shi ne da na uku a ‘ya’yan Hajiya, yaro ne mai kunya sai ya sadda kai a ransa yana cewa yaya ma za ai ya goya mace? Ya ce, ‘A’a Anti ai mace ce, da dai namiji ne sai in goya.�
Faisal da tun shigowar su yana durkushe gaban jaririyar ya yi farat ya ce, ‘Gafaracan da Allah malam ni in goya, anti ni za ki na goyawa baby kullum.�
Ta sa masa bebin a baya tasa zani ta kulle masa. Najib da yake duk ya fi su wayo har Faisal din da ya girme shi ya dubi bebin sosai ya ce,
“Antin mu a haka wani sai ya ce bebin nan ta yi wata uku?�
Gaban Antin ya bada dam! Sai kuma ta yi dan jim, kafin ta ce,
“Ai su dama lafiyayyun babies haka ake haifan su da girman su.�
A ranar kwata-kwata Faisal bai bar Anti da raino ba, shi ya zabi kaya overall na babies masu kyau cikin kayan da Daddy ya jibge mata ya sanya mata ya shafe mata jiki da olive oil.
Haka Antin ta ce da su nonon ta ba ya da lafiya don haka doctor ya ce a dinga shayar da baby da madarar NAN. Faisal shi ya sanyawa babyn feeder a baki yana ta zuga ta wai ta yi sauri ta shanye ko ta yi saurin girma su dinga tafiya makaranta tare.
In sun dawo ta bi su Islamiyya kafin su kwanta ya koya mata ABCD. Su kuwa sauran sun zagaye ta in ka dauke Al’ameen da ke makarantar kwana, suna ta yaba kyawun kanwar su, a cewar su ba su taba ganin baby mai kyawu kamar ta ba, ji suke tamkar su lashe ta don so, babu kamar Faisal, da kyar suka bar ta gun uwarta, don sun dage sashin su za ta kwana ko sauro ba za su bari ya taba ta ba, sai da Antin ta ce da su cikin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 38