wannan ilimin mai matukar wuya. Idan kika sameshi samun Aminu ba zai maki wuya ba haka in kika barshi ke da banza a cikin su daya kuke, don sai kin raina kan ki a cikinsu.
Ni in son raina ne ma Allah bana son ki auri mai mata irin Ihsan, ki dubi yadda take hauka akan mijinta fa, ke ‘yar nan, mind yourself (ki shiga taitayinki)�. Ahaf! Ai kamar Antin ta shiga ranta taga abinda take shiri komawa makaranta, tayi murmushi tare da saurin rufe ido, maganganun Antin take aunawa abisa sikeli daya bayan daya, wanda dama duk tayi tunaninsu, babu wanda bata ga gaskiya a ciki ba, ta ce a raunane.
“Na gode Aunty.�
Ta rufe wayar, sai yanzu ya fuskanci da wa take magana, bata ko dubeshi ba ta murda kofar da zata hadaka da dakin ta daga falon Anti, yayi hamzarin murda keys ya zare ya tura aljihun bayan wandon ‘basachi� dake jikinsa ya ce.
“Me Anti Hajjo ke gaya maki a waya, kike godewa kina kuma kara yi mun asaran hawayen da nake ganin daraja da kimar su fiye da na kowa?�
Wasu ubansu harara da ta watso mai ya bashi mamaki don bai taba ganin tayi ba, ga idanun sunyi jawur sai ta kara kyau a idon shi, ko da yake so ne hana ganin aibi, ya ce, “Inteesar� da muryar nan da ke karya lagonta, ta kassara kuzarin ta, amma a yau ko gezau, har yanzu hararar shi ta ke ba kakkautawa.
Ya soma taki har inda take tsaye tamkar sassakakken gunki, ta soma ja da baya kamar wadda taga abin tsoro da kyama, ta san ba karamin aikin shi ba ne ya kamata da kokawa kawai don ya sata yin magana, cikin tsiwa da yatsina ta bude dan bakinta tana mai nunashi da dan manuninta ta ce,
“Wallahi Al’ameen ka sake ka tabani yau zan fasa ma kaine, in bar inyamurar matarka da jiyyar da baka taba yi ba.� Bai fasa dosarta ba ya ce,
“Jinya kuma wacce ce ba’ayi ba? Sai dai kar a kuma, idan jinya ta ciwon son halimah ce, to ayi ta yi kar a tashi. Kar ki kara kira mun mata inyamura, yadda kike musulma diyar musulmi, haka itama take.� dai-dai lokacin da ta dangana da bangon karshe na falon, shi kuma bai fasa bin ta ba, ta ce,
“Wallahi zan kirawo Anti, tayi ma kashedin shiga harkana, ka nemo Halimar ka can amma ni Intisar ce, ka manta ka taba sanina a rayuwarka, ina gaya maka, ina kara gaya maka� ya toshe mata baki. Ya ja hannunta na dama da karfi har bisa seater dake tsakiyar falon, ta karfin tsiya ya zaunarta ya ce,
“Ke in ma Daddy zaki kirawo babu laifi. Amma sai na gama maganar da zan yi. Kin san me ya kawo ni?
Zuwa nayi in gaya maki ranar da duk wannan maganannen bakin ya kara kuskuren cewa bazai aureni ba don uwata, wallahi sai na kakkarya ki.�
Cikin tsiwar da bai san ta iya ba ta ce,
‘Ka karya ni? To ka ji ka sani ko da can da ka makantani, don ban da wayo ne, amma yanzu wallahi sai dai ayi ‘yar bibbiyu� saura kadan da dariya ta kwace masa, to amma shi kansa yasan bai kyauta ba, jiya ya mareta yau ya gaya mata kakkausar magana, shi da ke neman wanke dattin da Hajiya ta yayyaba masu daga idanunta.
Ya dire gwiwoyinsa bisa carpet abinda bai taba yiwa wata ‘ya mace a rayuwarsa ba, a yayinda ita kuma take zaune cikin kujera ta cika fam, kiris take jira ta fashe.
Ya langabe kai gefe guda gwanin ban tausayi, yayi kamar ya share mata hawayen da suka soma surtu, sai kuma yafasa. Ya ce,
“Inteesarr!�
Yadda ya kira sunan cikin murya mai karkarwa da kauri (husky) kadai ya birkita Saratun, bata jin ko dan yatsanta zata iya motsawa. Ya ce,
“I ‘am sorry, terribly sorry! Wallahi ni, wasa nake maki, in karya ki in ce na karya wa kenan?
Jiya kuma zuciya ce ta debe ni, kin san bata da kashi, abinda kika fadi cikin mutane ya bata mun kwarai. Ni kaina ban san ya akai ba, Pls, 4 give me…� Ya karasa a raunane, kana ya matso ‘yar kwallah, ya maida ta bisa kujerar ya ce,
“Wallahi Intisar nasan Hajiya ta bata miki, to amma ni meye laifina? Ni ban ji tsoron abinda hakan zai janyo man ba daga gareta na furta ina sonki? Sannan kuma bakya tausaya mun halinda zan shiga in na rasa ki kwata-kwata, ki tuna baya?�
Ta sadda kai kawai, bata son jin wannan abun da take ji game da Aminu, bata son wadannan ‘feelings� din da take ji game da shi masu tada tsigogin jikinta a duk lokacin da suke tare, to amma Al’ameen din kamar wani mayen karfe ne, wuyarta yayi mata magana da wannan muryan nashi mai jan mutum uwa lantarki duk wani ‘weakness� din ta ya gama samunshi.
Ta tabbata nisa da shi shine abu mafi a’ala a gareta in har tana son cimma kudurirrikanta akan Haj. Nafi, wadanda daga ita sai zuciyarta sai mahaliccinta suka san na mene, amma ba don bata son shi ba.
Karya ne ko fatar bakinta ta fada, to bacin rai ne. Shi kadai take so har cikin tsokar zuciyarta, har gangar jiki zuwa kwakwalwarta babu inda baya girgiza da kaunar Al’ameen da sha’awar komi nashi, ita kadai ta san me take ji da yakin da take yi da zuciyarvta a duk lokacin da yai kuskuren kai hannunshi gareta koda yatsar hannunta ne kuwa amma ta rantse, ta kuma ta rantse ko son sa zai kasheta, ko duk duniya zata taru a kanta, bazata aure shi ba!
A ganinta ta hakanne kadai zata rama abinda sukai mata shi da mahaifiyarsa wanda har abada bazata manta ba, ba zata yafe mata ba kuma ba zata daina tunawa ba.
Bata san wannan hukuncin da ta yanke yai tsauri ba, domin son da Al’ameen ke mata Allah kadai ya san iyakarsa; ba na wasa bane, ya wuce ayi ramuwar gayya akansa yayi masa tsauri bazai iya dauka ba. Da kyar in bata yi kuskure ba, da kyar in hukuncinta ba zai zamo nadama mara amfani a gareta ba.
Ya cira hannunta ya aza bisa kirjinshi, tana iya jin nannauyan bugun da zuciyarsa ke yi akai-akai, jikinta ya soma sanyi, ya ce,
“Ki ji Intisar, kiji irin bugun da zuciyar nan ke yi a domin ki, saboda ke ne take ciwon da har abada bazata daina ba, ba kya tausayi na Intisar ba kya sona yanzun? Allah na rantse, in muka cigaba da tafiya a haka wata rana�. Wata rana bugawa zatayi gabadaya ta fashe kowa ya huta, ki taimake ni ki agaje ni, ki daina la’akari da laifin da ba nawa ba kina hukunta ni dashi don Allah?�
Ita dai ta zamo ‘pale� ko motsi ta kasa balle tayi kokarin yin wani abu, ta rasa abinda ke mata dadi shi kuma bakinshi bai yi shiru ba da gaya mata irin halin da zai shiga in ya rasata. Har ya kai ga kwantar da kansa bisa kafadunta.
Cikin wannan halin Faisal ya turo kofar falon ya shigo, fes idon shi a kan su, ya juya da sauri yana cewa, “Excuse me plz. Ya Aminu ban sani ba!�.
Ta mike a gigice ta banka dakin Anti, ta kifa kai bisa gado ta soma rera kuka sabo fil. Ina rowan mai neman kuka an jefeshi da dunkulen kashi.
Gabadaya suka zubo mata ido Anti da Ihsan suka yo kanta Anti ta ce,
“To kin gani Ihsan mijinki kullum sai yasa min ‘ya kuka, don haka ki je ki ja kayan ki ku tafi.� Ta sake kuluwa ta shaka ance Al’amin mijin Ihsan, ta sake tsugewa da kuka.
Ihsan ta matsa jikin gadon ta dago kanta ta aza bisa cinyarta tana murmushi tace “Haba little sister na, kin hana mun miji sakat ko tausayinshi ba kya ji, jiya saura kadan ya sakeni, don Allah kiyi hakuri ki bamu hadin kai ko na samu kan Al’ameen nima…�
Ta soma fidda kwalla itama, wani tukuki na cinta a rai, wai yau itace da kanta ke rokon wata ‘yar ficikar yarinya ta so mijin ta, Aminunta data gama shan bakar wahala a kansa, ta sadaukar da komi nata dominsa, take son sa tamkar ta fidda zuciyarta, ayya rayuwa!
Ta daure ta share wasu azababbun hawaye da suka biyo kumatun ta a guje ta ce, “Intisar, Al’ameen ya gaya mun bazamu taba samun kwanciyar hankali ba in har baki yarda da maganar auren ku ba. Don Allah Intisar ki taimake ni.�
Aunty ta juya ta fita, bata iya jure ganin wannan abin tausayi. Ita Ihsan din ce ta ke bata tausayi, ta tabbata ba karamin so takewa mijinta ba, abinda tayi mata da yawa baza su iya ba, dazu akan idonta Aminu ya turo kofa ya rufesu har da mukulli amma sai cewa tayi.
“Allah dai yasa ya shawo kanta. Don na lura Intissar akwai zucciya.�
Intisar ta dago don babatun Ihsan ya isheta, fuskar nan jike sharab da hawaye ta dubeta sosai ta ce,
“Ina ganin mutuncin ki, don haka don Allah don Annabi Anti Ihsan ba ruwan ki, ki rabu da Al’ameen kawai, shi bai ji tausayi na ba sadda yake kwallo dani har na zamo nakasashshiya? Hajiyarsa bata ji tausayi na ba a sadda Daddy ke kwallo da ni ba a gabanta, da sadda take fyaula mun kebur? Take sa min shocking? Ke har da kan ki kike son in auri mijin ki ashe karya kike ba son shi kike ba.
Baki sani ba, ni fa tunda fari ba son mijinki nake ba, kaddarar Allah ta hada mu a kichin kuma kaddarar ta raba, don haka ki tafi don Allah ina bukatar hutu, ina maku addu’a Allah ya baku kwanciyar hankalin ba sai tare da ni ba, ke ni ba wani aure da zan yi, da din ma dana amsa masa rashin galihu ne da rashin abin yi, yanzu kuwa ina da abinyi ina da galihu, ba wanda ya isa yayi kwallo da ni ban yi karar sa an fitar mun hakki na ba, ki je ki lallashi abinki ke daya ko ke ba mace bace baki ishe shi ba?�
Ta fiddo mata ido cikin barazana kamar gaske, bayan a zahiri ji take kamar ta makureta ta huce.
Ihsan tayi murmushi ta mike, a ranta ko cewa take lallai wannan yarinyace, danya (fresh), kalaminta kadai zaka ji ka tabbatar kurucci dangin hauka na dawainiya da ita, har akwai wata ‘ya mace mai cikakken hankali ta kuma san abinda takeyi da zata budi baki tace wai bata son Al’ameen Bello?
Ta mike ta na rataya jakarta ta nufi kofa ta ce,
“Ki dai kara baiwa zuciyar ki shawara Intisar, Al’ameen mai matukar son ki ne tsakani da Allah. Ba fata nake miki ba, amma ba zaki samu miji da ke son ki tamkar yadda ya ke son ki ba.�
Intisar ta bita da hararar haushi, kar ta samu din, wannan dan iskan mijin nata? Yau kam kunya da tozarci tagama jin shi a rayuwar ta. Da wane ido zata dubi Faisal?
Wane kalami gareta na wanke kanta daga sunan mayaudariya, maciyiya amana, butulu kuma mai manta alkhairi a idon Faisal? Sai ta kara jin tsanar Al’ameen ninkin baninkin na da, dubi yadda yake wa matarshi don wai kurum tana sonshi. Itama idan ya aureta wata rana ya sami wadda ya fiso fiye da ita ba mamaki ya turota lallasar yarinyar da yake son, tab! In ita ce ai za’a yi kata’i. Bata san wannan duk yana cikin wayewar Ihsan da duniya ne ba, ko ba komi zata sayo ma kanta daraja da soyayya a zuciyar mijinta, gaskiyar Hajjo ne Ihsan da Aminu sun fita wayo, ba kuma tsaranta bane a budewar kai da Ilmi.
How much do you like this story?
5/11/22, 08:13 - Ummi Tandama😇: ______________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
*@Takori*
Page7ï¸âƒ£
Su Inteesar bayan sun baro gidan Al’ameen da aka tashi taron har suka zo gida kuka take. Ba kukan komi ba ne face na nadama da tsanar kanta! Amma su ‘yan uwan basu san haka ba, sai tausarta suke da kalami masu dadi. Wai ashe Al’ameen din Hajiya ne take ta wannan hakilon akansa, amma Al’ameen ya yaudareta kuma har abada bazata taba yafe masa ba! In ya ce tayi masa karya itama ai yayi mata karyar.
Hajjo da ba’a rabata da abin dariya tace “kai ni Haj. Saratu Al’ameen ya burgeni. Fau, gaskiya jan kumatu yau yaga wuta. Ai ko ni ce Aminu abinda zanyi miki kenan.
Ciwon zuciya ya kamani akan ki, in samu kaina da kyar kice bazaki aureni ba kan wani shirmenki da bai shafeni ba.�
A ranta ta ce, “Allah sarki! Baki san ko wace uwar sa ba, da ba zaki ga laifi na ba! Baki san ya nake da uwar sa ba, da in banda zuciyar muslunci ba zaki ce in gaishe shi ba balle aure.�
Hajiya Hadiza ta ce, “Ai wannan ma bazata sabu ba, wannan irin butulci dame yayi kama? Anti Saratu ta juyo ta dubesu sannu a hankali kana Intissar din ta dake ta rasgar kuka. Ita kadai tasan kukan me Intisar take, halinda zuciyarta ke ciki da nadamar da ke tattare da ita. Tayi kwafa ta ce,
“Tunda dai tace batayi don Allah a bar zancen nan, wai Haj. Hadiza da me Instisar zata ji ne? Sabon sauyin zuciyarta ko maganar Aminu? Ba ciwon zuciya ba in ma ciwon mutuwa ne Aminu yasa Intisar fiye da wannan kuma sun cancanci dubun wannan daga gareta, duk da ba laifinsu bane.
Kar ki manta Aminu ne ya makantar da Intisar da hannunsa, da Allah ya tashi saka mata sai ya saka mata ta hanyar daura mai masifar sonta, don haka mu kyale Intisar taji da abinda ya dameta� Har suka kawo gida zancen kenan. Haj. Hadiza ta ce,
“Haba Mamar Intisar, maimakon ki lallasheta sai ki dada tunzurata? Ai babu ramuwar gayya tsakanin wa da kaninsa kuma abinda Allah ya kaddara to sai ya faru.
Ba Aminu ne ya jawo mata laluran ido ba illah Allah ya kaddara zata gamu da laluran ido ta dalilinsa, kuma Allah ya haramta rumuwar gayya, sannan abinda ya wuce shekara goma sha biyar ba’a tada shi ba sai yanzu don Aminu yana son ta?
Kome Babarsa tayi mata ai ba sa’ar ta bace da zata ce zata rama! Da ita mai hankali da halarci ce bazata bude baki a gaban Brigadier tace bazata auri jininsa ba, koda kuwa ace yankar naman jikinta Hajiyar Aminu ke yi a kalla yaci darajar mahaifinsa da ‘yan uwansa dake sonta.
Mutamin da ya daukota a daji bai san ko ‘yar waye ba. Ya hada da nashi ya rike bai kyamaceta ba duk da cewa bai sani bama ko shegiya ce, ya sota ya kaunaceta ya kula da dawiniyar rayuwarta shekaru goma sha takwas! Sai don wani dan gajeren sabani ya faru da bai taka kara ya karya ba tace bata son jininsa balle dansa na cikinsa, don ta tabbata shegiyar!
Ai idan ni na haifeki, na shayar dake mamana to baki da miji sai Jinin Bello Makarfi sai ko in sune sukace basa so to wannan kuwa. Ni dama ba kowa bace ke ‘yarsu ce, sai yadda suka ga dama da ke.
Wata rana irin ta yau bazaki ganmu ba sai ki san inda kuma zaki je tunda in kina da kunya bazaki cigaba da zama a gidan ubansa ba!�
Anti Saratu ta ce, “A’aaah! Ya isa haka nan, sai ko in ikon haihuwa da shayarwa zaki nuna min Haj. Hadiza, amma in ba hakaba ni Saratu na rantse in har Intisar bata so bazata auri Aminu ba.� Inteesar ta kara fashewa da kuka a ranta cewa take
“Ni Saratu na shiga uku, tsakanina da Al’ameen Allah Ya isa, yau ina zansa kaina gashi ya janyo su Mama suna fada a kaina?�
Hidayah da Hunainah kuwa rungume suke da ‘yar uwarsu suna tayata koka abinda take kokamawa, da baza su ce ga hakikaninsa ba, ba suce ko uffan ba don baya daga cikin tarbiyyarsu tsoma baki a maganar manya in har ba an nemi jin ta bakinsu ba, amma kam da sunbi bayan Mamarsu da Antin su Hajjo don a duniya ba su ga wanda ya dace da Yayar su kamar Al’ameen ba.
A ranar mutanen Makarfi suka koma, Daddy yayiwa Minister Hassan da Ambasada masauki a gidan saukar bakin gidan shugaban kasa su da matan su. Ba yadda Anti Saratu bata yi da Intisar ta bi Hajiya Hadiza masaukinsu ba amma ta kiya, gani take kamar zasu gudu da ita su rabata da Mamarta, gani take in ta yi hakan ta yiwa Antin butulci, ba don bata son uwarta ba illa a yanzu da komi ya bayyana gareta take tausayin Anti Saratu, wai ashe ba itace mahaifiyarta ba amma tayi mata irin wannan rikon da wata uwar bazata yiwa dan cikinta ba, take jin ciwonta, ciwon da uwa mahaifiya zata jiwa dan ta. Matsayin data riki Anti Saratu na uwa, bai ragu ba ko kadan a zuciyarta sai ma karuwa da yayi, haka matsayin uwarta shima daban.
Ba wani sakar mata fuska Haj. Hadiza takeyi can ba shiyasa tafi shakuwa da Hajjo cikin dan lokaci, su dama su Hunainah ba bakinta bane, haka Baban su yadda yake janta a jiki, sai take kwatantashi da Daddy.
In ka ganta cikin kannen ta kamar ‘yan uku, sun zamo tamkar wasu tsoka daya kowanne ji yake da dan uwan sa, motsi kadan daya zai yi ta tambayeshi menene? Su su Hajia Hadiza ma sun ce nan da kwanan uku zasu tafi saboda shirye-shiryen tafiyar su Hunainah makaranta. Sun sami (admission) a Jami’ar Al-Azhar dake Cairo ba kuma sun zo ne don su tafi da ita ba, ta ce da Aunty Saratu har abada Intisar tana nan a diyarta wannan shi yasa Anti Saratu kukan dadi.
Zarah kuwa ta zamo ‘yar Haj. Hadiza don ko nono Zahra taki amsa koyaushe tana jikin ta tun kwanakin da Antin tayi tana jinyar Intisar bata kula da ita ba Haj. Hadiza ke bata madara suka saba, da hankali ya natsa ne ta bata kememe ta ki amsa, sai ta lafe jikin Haj. Hadiza.
Anti ta ce, “Tunda kin yaye kanki ai shikenan� suma su Hunainah na matukar son Zahra da kula da ita, har fada suke akan daukanta da girmansu da komi.
A daren ranar Intisar na kwancea falon Anti duk yatsun Al’ameen sun fito rada-rada a farar fuskarta, haushi da takaici duk ba wanda babu a zuciyar nan, ga tunanin Ya Faisal, ta rasa abinda yasa yanzu ko gaisuwa bayaso ta hadasu, hakannan duk inda ya san zasu hadu a gidan to yana kokarin yaga cewa ya kaucewa wannan hanyar, in kuma guri ya kure sun hadun to ba dai ya daga ido ya dubeta ba, ya kuma bi ya daure wannan lallausar fuskar da a kullum ke tarairaya da sata nishadi tamkar bai taba sanin ta ba dadai duniyar.
Sa’annan bayan sun shigo su Najib duk sun shigo sun mata sannu da jiki anyi raha da ‘yan dararraku na abinda ya faru tsakaninsu dasu Hidayah amma banda shi.
Ta rasa wane irin laifi ne tayi mishi haka da zafi, ta dauka a yanzu ne ya dace dangantakar su ta fi ta da. Ko zata ki kula ‘ya’yan Haj. Nafi don Babarsu, ta kula su darajar kaunar da su ke nuna mata, amma ba don uwarsu ba.
Don Ko da suka ji gaskiyar dangantakar su a yanzun sai ma suka kara dagewa wajen jan ta a jiki, basa hada son ta da na kowa cikin kannensu maza, banda Ya FAISAL din ta kadai.
Shi a ranar ma ya fara zuwa aikin da ya samu a NNPC na nan Abuja kasancewar shi trained din kasar Ingila don haka bai sha wahalar samun aikin ba. Don haka ne bai zama sam, in ya fita tun safe sai dare. In ranta yayi dubu to a dugunzume yake da damuwa.
Hakikah ta damu da Faisal can baya fiye da kowa a duniya. Wannan dadaddar kaunaar mara algus tana nan har inda yau ke motsi, illa sauya matan da yayi farat daya ke damunta.
Zarah ta rarrafo ta kama kafafunta tana kallonta, bata kula taba sai Hunainah ce ta miko hannu zata dauketa tana cewa
“My sweat Zarah, share wannan kada ta make ki.�
Dai � dai lokacin da Hidayah ta fito daga toilet din dake makale da falon, da alama wanka tayi, kanta cikin “shower-cap� tana daure da faffadan towel, fatar nan lub-lub tamkar masu shiga wankan inji ga dogon wuya tubarkallah kamar barewa sak Yayarsu.
Ta fannin kirar jiki kam basu da maraba illa fasalin fuska kowa da zubin tashi, haka complexion ya banbanta.
Intisar doguwace siririya, fara tas, tamkar kirar larabawan Muritania ko ko mutanen Sirreleon. Shape din fuskarta oval mai kayatattun idanu da wadatar gassun gira, ido da sumar kai. Komi nata tamkar ita ta zaba caras-cas, kuma zam-zam ya dace da ita, tana da labba jazur sirara tamkar yankar reza, wanda in tai murmushi sai ta zama tamkar ‘yar flower (rose) yayinda Hunainah take doguwa kakkaura, kalar coffee, irinsu ne ake kira doguwar mace alkyabbar mata, ga tsayi, ga zati, duk tafi Yayun habewa da cika ido kai sai kace itace Yayar, nan ko girman kasar larabawa ce kawai kunfi shekarun ku buloras, kwata-kwata bana zata cika shekaru goma sha shidda, tana da kyawun da kai tsaye za’a kira manyan kyau, komi a waje, idanduna dara-dara farare kal, in tana kallon ka sai ka dauka hawaye zatai saboda wani sheki da kyalli da kwayar idonta keyi tamkar an diga masu mai me maiko.
Sabanin Intisar shiru-shiru mai sanyi, ita Hunainah ‘yar yi ce zakakuwa, da ba’a takalanta ta kyale, duk gemun mutun baya bata tsoro haka duk rawanin sa in ya shiga hancin ta zata fyato shi, ko da suke makaranta itace mai tare masu fada idan Hidayah ta tsokalo, da bakin rashin mutunci wa ‘ya’yan larabawan da duk suka kawo masu wargi.
Tafi Hidayah son Intisar kuma jinin su yafi gamuwa ko sanda suke makarantar ma sun fi jituwa, duk da halin su ya babanta.
Hidayah dabance a cikinsu, domin dai ita yarinya ce mai jin kanta, ‘yar gayu kuma wayayya mai son hulda da kawaye masu ilmi, don ita takan ce bata a layin kucaki (su Hunainah), ko larabawa da turawan ma da suke tare dasu sai masu aji take kawance, akwai kuma son yawon bude ido garuruwan kawayenta dai-dai ne bata jefa kafarta ba, don haka duk ta fisu budadden ido, idan ta juya harshe zuwa larabci sai ka rantse tsatson King Abdul-Azeez ce, haka in ta murda turanci bazaka ce ba Afro-America bace, haka in ta juya Faransanci, yaren manyan kasashe dai-dai ne bata iya ba. Hidayah Bashir kenan.
Tana da matsakaicin tsaho da dogon wuya kuma tafi Hunainah haske, amma bata kai Intisar ba, gatanan dai mai sheki kamar tarwada.
Ta zazzarewa kanwar ido “kawota nan, ko in make ki wallahi, ban ce da ke in ta tashi ki gayamin ba, ina jin ki wani ‘your sweat Zarah� banza mummuna, bakauya.
Kamin Hunainah ta mayar da martani Najib ya shigo cikin takunshi na kasaita na ‘ya’yan Daddy ya coge jikin kofar shigowa, ya zuba hannuwa cikin aljihun shudin Jeans dake jikinshi yayi dariya a cikin kallon Hidayah ya ce,
“Uh, su seniority manya� ai da ta daga ido taga shine sai ta saki Zarah jikin Hunainar ta falla da gudu dakin Anti.
A yadda ta fado mata dakin sai data firgita ta mike a hanzarce sukai cirko-cirko, ta ce, “Ke lafiya, sai kace wadda aka jeho ko sallama kamar wadda ta ga dodo?�
Ta cira kai ta dubi Anti Saratu ta mayar wani gefen bata san me zata ce mata ba, ta sauke sassanyan numfashi ta ce da ita me? Najib ya ganta cikin kayan wanka bayan dama can ya takura mata da kallo tun a asibiti da shigar mata hanci da kudundune?
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Barshi ma dai kawai Anti� cikin murya mai kwantar da hankali da sassauci Anti ta ce,
“Hidayah, wani abin tsoro kika gani?� Tace� Lalah, actually nothing. Tambayar ki zanyi ki bani wet-lips.�
Anti ta saki dariya ta juya mata baya tana cewa.
“In kin duba kan mudubin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 38