aure! Karatu dai karatu kadai Faisal kaman alhuda huda?
Duba kaga kanin bayanka matar sa tsohon ciki gareta, haihuwa yau ko gobe. Dubi Alameen ya tafi, amma ga Alameen Alameen nan na yawo cikin gidan nan yana tuna mana da shi muna yi mishi addua, ko ba zaka yi aure domin bukatar kanka da cikar mutuncika ba, kayi domin shi kansa ibada ce mai zaman kanta.
Ban san me kake nufi da rayuwar ka ba, ban san meye planning dinka a rayuwar nan ba. Ina jiye maka tsoron kazo duniyar a banza ka koma a hofi. In kana ganin bani iya yi maka maganin matsalarka to a kalla zan baka shawara wadda kai a shekarun ka bazaka hangosu ba. Ko kuma mutuwar Alameen ce ta ke nukurkusar ka har yanzun? Take neman kayar da kai tun karfin ka bai kare ba?�
Yasa hankici ya share idonsa ya share dogon karan hancinsa ya ce,
“Aah Daddy, na riga nayi tawakkalin cewa ya tafi, ba kuma zai kara dawowa ba.� Ya ce,
“Madallah, ni dai da zaka bi son raina da ka hakura da tafiyar nan ka rungumi aikin ka an kuma daura maku aure da matar marigayi Ihsan da ka faranta mini, ko ba komai yarinyar ta nuna mana ita mai kaunar mu ce ba wai abinda muka mallaka ba. na dade ina kissima yiwuwar hakan a zuciyata ba tun yau ba..�
Ya dago cikin wani irin yanayi na firgici da tashin hankali ya dubi mahaifinsa, kana cikin nutsuwa yace
“Daddy! Na rokeka alfarma, don girman Allah koda wasa kada ka kara tunanin zancen nan balle ka fada wani ya ji. Kada ka bari alamarin yayi tasiri a zuciyarka don Allah? Yaya ma zaayi ka yi wannan tunanin? Zaka karasani kwanana bai kare ba.
Ka bar ni in ji da ciwon da zuciyata ke yi. Ba matar da Alameen ya aura akan yana so ya tafi ya bari ba don ba ya so ba, ko yarinyar da ya taba nema bazan iya aure ba balle matar sa. Kayi min uziri ka karbi hanzari na, in dai tafiya ce na fasa amma don Allah, kada ka kara ce min wani abu makamancin wannan.
Daddy ya yi murmushi ya ce yaro dai yaro ne. To kaje ka kawo min yarinyar da kake so cikin kwanaki goma rak! Amma in ba haka ba zan daura aurenka da Ihsan a ranar da kwanakin nan suka cika. Na gaya maka na kara gaya maka babu wasa cikin magana ta.
Cikin matsananciyar damuwa ya ce ni bani da wata yarinya da na ke so. Ban taba son wata ya mace a duniya ba. Alameen kadai na ke so!!! Don haka na baka wuka da nama ka zartar da duk hukuncin da ka ga dama a kaina, ka zabamin ko wacece amma ka taimake ni Daddy kada ka aura min matar Alameen. Wallahi zan gudu in bar garin, don ni Ihsan Yaya ta nake ganinta.
Saura kadan dariya ta kwace masa amma ya cije ya daure yace shikenan, tashi je ka sai na neme ka. Sai dai ina mai gargadinka ka cire abinda ke damunka daga zuciyar ka domin tsira da lafiyarka. Babu wata cuta da Allah ya saukar a doron kasa da bai saukar da maganin ta ba. Ka kaiwa Sarki Allah kukan ka amma ba wannan damuwar da ka sawa ran ka ba babu gaira babu dalili.
Ya mike kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya doshi sassan Anti Saratu. Tun daga hangoshi Alameen karami ya watsar da kayan wasan shi ya rarrafo da hamzari ya kama kafafun shi, shi kuma yayi gaggawar russunawa ya daukeshi ya rungume a kirjin shi.
A lokacin ita Ihsan ta tafi asibitin Alameen Memorial da ake canzawa suna maimakon MERITIME. Ko ba don haka bama a dan tsukin bata samun zama sabida shirye shiryen bude asibitin da ya gabato, tana sa ran yaye Alameen karami ne ma cikin wannan watan mai kamawa domin hidimomin sun mata yawa, ga tafiyar ta karin karatu saura watanni (3) kacal.
A kan Alameen bata da kaico ta san Anti Saratu na iya kokarin ta a kan sa, haka Hajiyar Alameen duk wani buri da tattalinta ya taallaka ne a kan dan yaron da bai ma san ko shi wane ne ba. Motsi kadan zata shigo sassan Antin tana ina maigidana ne? Ban ji duriyar sa ba tun dazu, wane shagalin yake yi ne?
Kayan wasa kuwa na dubban nairori bata jin kyashin saya masa ko na nawa ne har ma wanda yafi karfin shekarun shi irnsu automatic motorbike da kekunan yara musamman take yo odar su daga Germany duk don Maigidannata. Inda shi kuma Daddy bashi da wani aboki kaman wannan Alameen Alameen Bello. In kaji shi yana bashi labari sai ka rantse da wani cikakken mai hankali ne yake magana ba da yaro dan shekaru biyu ba.
Faisal ya zauna ya kifa fuska cikin tafukan sa, yayinda Alameen ke dabdalarsa a dokin wuyansa. Antin ta karaso rike da tambulan cikke da sassanyar madarar shanu fresh ta mika masa. Ba tare da yayi musu ba ya amsa ya shanye wata niima da sanyi suka sauka a zuciyarsa. Jijiyoyin kansa duk sun mike rada-rada a kansa haka tsigar jikinshi sai tashi yake, tabbacin zazzabi ke neman kama shi.
Ba ta katse shi ba har saida ya samu nutsuwa don kansa, kana cikin sanyin murya ya ce,
“Aunty, kin ji abinda Daddy ya yanke a kaina?�
Ta ce, “Ya hanaka tafiyar ba? Ni ma ban ga dalilin tafiyar ba�
Ya ce, “Tafiya ni na fasa da kaina, cewa yayi in kawo matar aure cikin kwanaki goma ko ya aura min maman Alameen karami. Sabida Allah Anti yaya ma Daddy zai yi wannan bahagon tunanin? Sabida Allah an yi mun adalci kenan? Cikin mu wa aka taba zabawa matar aure? Yaya zaayi in iya hada rayuwa da matar da Alameen ya mutu ya bari ba don baya so ba, sai don mutuwa da tayi mishi yankan kauna? Wannan ai cin amana ne da tozartawa.
Wallahi ko yarinyar da Alameen ya furta ya na so, bazan iya aure ba balle matar sa. Komi son da nake mata kuwa zan iya jurewa. Don na tabbata in shine ya san ina son mace, da ko itace autar mata daga ranar bai kara sonta. Zai hakura ya bar mini domin shi dan uwa ne mai dimbin karimci da sadaukarwa.
Na zo ne in roke ki alafarma ki hana Daddy wannan kudurin nasa, ni kuma nayi alkawarin yin biyayya ga duk matar da ya zaba mini matsayin abokiyar rayuwata ta har abada, amma ni ba zan auri Ihsan ba.�
Ta yi murmuishi ta ce, “Na ji uzurinka Faisal, kuma da yardan Allah zanyi kokarin in ganar da shi. Amma da sharadin zaka amsa min wata tambaya guda daya da zan yi maka. Kayi min alkawarin zaka fada min gaskiya ni kuma na yi maka alkawarin ba zaka auri Ihsan ba!�
Cikin sauri ya ce, “Wace tambaya ce Anti? Wallahi zan amsa miki iyakar abinda na sani.�
Ta ce, “Shhhh, ka daina saurin rantsuwa akan abinda baka da tabbas.�
Ya ce, “Wallahi Anti zan gaya miki.�
Rantsuwar da yazo yana dana sanin yinta kamar yadda ta gargadeshi a farko.
Ta tattara hankalinta gabadaya gareshi cikin murryar manyantaka da bada umarni tace menene hakikanin abinda ke damunka, tsakaninka da mahaliccin ka?
Cikin juyayi da dana sanin alkawarinsa ya ce,
“Anti soyayyah ce ta ke azabtar dani. Shekaru dai-dai har goma sha daya. Amma alhamdulillahi a yanzu ta kusa karasani nima in bi dan uwana in huta da azabar ta.
To amma matsalata shine bana so tayi galaba a kaina, kamar yadda tayi galaba akan dan uwana.
So nake in nuna mata banbancin mu na cewa ni mai iya controlling zuciyata ne sabanin shi da zuciyar ke juya alamuransa.
Idan na barta ta yi galaba a kaina sauran yan uwana ma bazata kyalesu ba, haka zatayi ta bin mu daya bayan daya tana kashewa har sai ta karar damu. Don haka bazan barta tayi galaba a kai na ba.�
Murmushi tayi ta ce,
“Wace yarinya ce kake so shekarun da suka wuce, ba kuma zaka taba iya aure ba har ka bar mu domin ta?�
Cikin kaduwa da matsanancin mamaki ya ce, “Anti wa ya gaya miki wannan maganar?�
Ta ce, “Bai zama dole ka sani ba, ka yi alkawarin amsa min tambayata ne kawai amma ba kai ka dinga tambayata ba. Sabida haka ka ji tsoron Allah ka idasa cika alkawarin ka.�
Ya sunkuyar da kansa kasa, in banda zufa ba abinda ke ketowa daga koina a sassan jikin shi, duk kuwa da A/C da fanka da ke ta aiki a falon. Ya yi dana sanin saurin rantsuwar sa. Nauyi da kunyar idanunta duka sun masa mayafi. Muryar sa can kasan makoshin sa tamkar ba tashi ba, ya ce,
“Anti Inteesar din ki ce!�
Ba tare da alamun wani mamaki ko girgiza da furucinsa ba ta ce,
“To yanzun ka daina son nata ne?�
Ya girgiza kai har yanzu bai dago ba, ji yake har abada bazai iya kara hada idanu da ita ba, a sanyaye ya ce,
“Ya zaai na daina sonta? Ita din ce dai har yau bata bar ni na huta ba kuma har gobe ba zan taba iya auren ta ba!�
Ta ce, “Hujjah?�
Ya ce, “Hujjata a da shine kasancewar mu uba daya. Hujjata a yanzu kuwa Alameen ya so ta. Ni kuma bazan taba yin tarayya da shi a son komi ba ban hakura na bar mishi ba. Don na san da a ce ya san ina sonta, da tuni ya hakura ya bar mini.�
Saura kadan dariya ta kwace mata amma ta cije,
“Ta girgiza kai tana murmushi�
Ta ce, “Wannan ba hujja ba ce ba Faisal. Don haka tashi je ka. Cikin kwanaki goma ka yi tunanin abinda ya dace da kai. Ko dai samawa zuciyarka abinda ta dade tana so don dorewa rayuwa mai inganci ko kuma auren matar yayan ka.
Ina mai tabbatar maka har yau, har gobe Saratu na son ka. Soyayyarta da Alameen wata kaddara ce daga Allah amma kai kadai take so tun tana mitsitsiyar ta. Ta damu da kai sosai, zata iya yin komi a domin ka. Gareta duk yadda rayuwa ta zo, a karbeta. Don haka ne ta karbi soyayyar Alameen.�
Sau da dama tana yiwa komi na rayuwarta uzuri da Faisal da Daddy Makarfi. Ta baka wata daraja da muhimmanci a rayuwarta irin wanda bata baiwa kowa a duniya ba. Duk halin da kake ikrarin ka shiga a wancan lokacin, ina mai tabbatar ma itama ta shiga kwatankwacin sa koma fiye da naka. Ta damu da kai sosai. Ta na matukar kishinka fiye da yadda baka zato.
A duk halin da take ciki, na farin-ciki ne ko na bakin ciki kai take tunawa tace Allah Sarki Ya Faisal! Da yana nan da kaza-da kaza, da kaza bata faru ba, da kaza ta faru. Ta fi kowa bakin ciki da tafiyar ka ni nasan wannan, amma ita tsammani ta ke ban gane ba.
Ya girgiza kai har yanzu kan shi a sadde, ya ce,
“Anti wannan kauna ce ba soyayyah ba. Intisar kauna ta kawai take, amma bata so na!�
Ta ce, “Babban jigon soyayya shine kauna. Kai ba namiji bane? Baka san yadda zaka yi ka gina soyayyar ka a zuciyar matar da kake so ba? Sai ka zuba ido ka zama dan kallo kana muku-muku cikin daki? To zauna nan kallon ruwa har sai kwado yayi maka kafa.
Ina mai tabbatar maka Intisar ta shigo wani matakin da take tsananin bukatar soyayyar da namiji a yanzu, komai na iya faruwa da rayuwar ta balle a inda su ke da babu kowa a tare da su sai Allah da ya halicce su. Bar ganin ta yarinya mai kamun kai, da yawan yaya mata basa iya tsallake wannan stage din (adolcence). A jiya da na lissafa jibi ne zata cika shekaru ashirin da haihuwa. Faisal me kaka jira da rayuwar ka? Ina ganin lokaci yayi da ya kamata ku fuskanci alkibla sahihiya.�
Kwana yayi yana nazarin zantuttukan da suka yi da Anti a daren jiya. Sai dai har zuwa lokacin ya kasa tsayarwa da kansa wata sahihiyar shawara. Ya kasa daina ganin Saratu a matsayin mai dimbin laifi a gare shi. Laifin da yake jin har abada ba zai iya yafe mata ba!
Hakan nan zuciyar ta ki bada goyon baya, ta ki daina bugawa a kowanne second da so da kaunar Inteesar, shi kam ya rasa inda zai tsoma rayuwarshi ya ji sanyi.
Ya kasa zabarwa kansa komi cikin zabin da aka bashi. Abinda yake da tabbaci kawai shine ko zai mutu ba aure, ba zai auri matar Alameen ba, kamar yanda ba zai iya auren yarinyar da Alameen ya furta yana so ba kome zaayi da shi kuwa, balle Intisar din da har abada ba zai daina ganinta a matsayin azzaluma ba a cikin soyayya, mayaudariya mai son kanta da yawa kuma maciyiya amanar kauna.
Laifuffukan ta gareshi basu da iyaka kuma tananinsu ma bata lokaci ne. Ya dai barta da duniya da abinda ke cikin ta kadai sun isa su koya mata hankali.
How much do you like this story?
5/16/22, 07:35 - Ummi Tandama😇: ______________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book four
*@Takori*
Page7ï¸âƒ£
Ranar litinin Ihsan ta tashi zuwa Miami inda zata halarci kwas na tsawon shekaru uku madadin karatun ta, yaronta Alameen karami ta bar shi ne karkashin kulawar kakanninsa. Duk wasu shirye shiryen tafiyar Ihsan Dr. Rehab ne yayi mata Allah kadai ya san kudurin shi na alkhairi kan wannan mace mai kyakkyawar zuciya ta marigayin amininshi.
Zaman lafiya da a ke a gidan Makarfi tsakanin Hajiya Nafi da Anti Saratu abin sai ya burge ka, ya kuma baka mamaki tamkar ba wani sabani da ya taba shiga tsakanin su. Lallai duniya makaranta, ta koyar da Hajiya Nafi darussan rayuwa kala daban-daban. Hakannan harkokin kasuwancin ta daya fara durkushewa sabida rashin kwanciyar hankali a yanzun ya fara farfadowa. Yayinda Aunty Saratu ta a je aiki kwata-kwata ta rungumi auren ta da hannu bibbiyu, da fatan cikawa da imani kadai.
Ambasada Bashir Sambo, sun dawo gida bayan ritayar sa a embassy. Katafaren gidan da ya kwashe shekaru biyar yana ginawa yana nan cikin anguwan Lamido Crescent dake cikin birnin Kano. Gida ne na gani a bada labari da duk fadin anguwar babu wanda ya kama kafar sa, tamkar an dauko shi ne kacokam daga kasar France an aza a filin wajen.
A lokacin tagwayen data haifa duk maza suna da shekaru biyu da haihuwa sai Zarah da ke da shekaru hudu, wadda daga yaye dai ta za ma yar su kwata kwata, don daga Daddy har Aunty Saratu babu wanda ya kara magana a kan zaman yarinyar tare dasu.
Tsarin rayawar gidan dole ya baka shaawa, babu hayaniya sam-sam, rayuwa ce kawai suke kamar a turai. Lokaci-lokaci suna zuwa Shanono duk da cewa dangin sun kare. Matan Hakimi tun bayan rasuwar sa duk sun kama gabansu, manyan yayansa maza kuwa duk Bashir ya dauki nauyin karatun su a manyan jamio’in mu, matan duk shi ya aurar da su tare da basu jari mai tsoka domin dogaro da kai. Haka duk matsalolinsu yana kokari a kai domin tabbatar da cikin su babu mai kukan rashi.
Ba tare da yin shawara da kowa ba Hajiyar su Faisal ta shiga yi masu cuku cuka ita da Faisal, Najib da Hidayah domin tafiya Al-kahira, saida ta kammala tsaf aka sanya masu date din tashi kana ta samu Daddy ranar girkin ta a wani dare, ta sadda kai cikin matsananciyar kunya ta ce,
“Babansu Khaleel, ina neman izninku zuwa wajen Intisar, ina matukar kwadayin afuwarta da yafiyar ta gare ni, har yau ji nake ban sauke wani nannauyan dutse daga kaina ba. Idan ka amince zan nemi rakiyar su Najib ko albarkacinsu ta dube ni ta yafe mani.�
Tasa habar zaninta ta share idonta ta fyace majina ta ce,
“Idan yarinyar nan bata yafe mun ba, bana jin Alameen ma zai taba yafe mini. Haka ubangiji na ma ba zai yafe mun ba, iznin ka kawai nake nema domin nagama komi, jibi ne zamu tashi.�
Ya daga ido ya dube ta kawai ya ce, “Me yasa bakya shawara kafin gabatar da alamuran ki? Sai in ce kin yi asarar kudin ki domin kuwa jibin ne zata dawo hutun karshen shekara.�
Ji ta yi kamar anyi mata bushara da Aljannah. Ta ce,
“Ba komi ai, Allah ya kawo su lafiya.�
A Egypt
Saratu da yar uwar ta Hunainah, cikin wani boutikue dake cikin jerin kantunan Shaam-El-Sheikh da ke cikin birnin Al-Kahirah, dukkansu suna sanye da riga da skirt iri daya samfurin Dolce&Gabbana, sun kuma daura after dress bisa dressing din nasu kala daban-daban, na Intisar grey ne wato ruwan toka-toka yayin da ta Hunainah ta kasance baka sidik. Hunainar rike da kwando da suka cika taf da kayan shafa, (shopping) suke domin dawowa gida hutu a washegarin gobe in Allah ya kai mu.
Ga dukkan alamu ita Hunainan cike take da farin-cikin dawowa hutun ko ba komi ta dade rabon ta da gida fiye da yadda ta saba yayin da a daya bangaren Intissar gata nan ne dai kawai. Kwata-kwata ta rasa me yasa bata farin ciki da wannan hutun duk da cewa kuwa rabon ta da gida shekaru biyu kenan cif.
Hakanan dai take ji a ranta wani bakon alamari na shirin faruwa da ita a wannan tafiyar kamar yadda yake a aladarta, komi zai faru da ita mai dadi ne ko akasi takan ji bacin rai ne wanda ke kasancewa zane baro-baro a kyakkyawar fuskarta, duk rabin hirar da Hunainan ke mata kan tsohon cikin da Hidayah ke tare da shi, da bidirin da zaa sha wajen haife shi kasancewar Hidayar mai rakin tsiya ko kadan hankalin ta baya tare da ita.
Gane hakan da Hunainan tayi sai itama ta ja bakinta ta tsuke, har suka koma makaranta basu kara ce da juna komi ba.
Karfe tare na safe jirgin Egypt-Air ya dire su a birnin Kano. Kai da ganin su kaga yayan hutu na garari kuma yammata na kasaita, wadanda gabansu da bayansu, gata da hutu kadai ke magana. Zai yi wuya ka yarda haifaffun kasar Nigeria ne, sun fi kama da santala-santalan matan Mouritania ko kuma irin half-cast din nan da suka tashi a kasar sanyi. Akwai wata nutsuwa ta musamman da zuzzurfan ilmi ya kara ma fuskokin su. To haka makallalen saurayin da Hunainah ta yi tun a cikin jirgi ke biye dasu har zuwa reception inda duk suka a je kafa nan yake mayar da tasa.
Ya kare ganin basu da niyyar kulawa ya sha gabansu, kyakkyawar fuskarshi dauke da kayataccen murmushi ya dubi Intisar ya ce Assalamu Alaikum Yayata, zuciya ce ta ga wani koren fure tana so shine take ta faman bibiyar sa, kada iska ta dauke shi ko kuma ya bace mata tana ji tana gani.
Suna na Hashimu Ingawa, ki taimaka kar ki bari furen nen ya bace mani, don Allah? Yana magana ne cikin accent na Katsina, ya rausayar da kai gefan da Hunainah ta ke, ta cika ta yi fan har tana neman fashewa. Idan da abinda ta tsana a duniya to wani namiji ya ce yana sonta, duk dangantakar dake tsakaninsu daga ranar zata wargazata da rashin mutuncin da ko inuwar ta ya gain sai ya sauya hanya.
Ta tura akwatin ta fuuuu! Tayi gaba kaman guguwa. Intisar ta yi murmishi, haka kawai ta ji gayen ya burge ta, tana son mutum mai fallasa asirin zuciyar sa da fidda zahirin kaunarsa gaban kowa ba tare da shayi ko haufin komi ba tamkar Alameen din ta.
Ta dube shi tsaf yake baya da makusa, da ganin shi ka ga wanda ilmi da naira suka ratsa sai dai baki ne, amma bakin sa mai kyau ne tunda kuwa ya hadu da hutu da gogewa. Sanye yake cikin makubar suit da ratsin fari sol ya daura jibgegiyar rigar sanyi fara sol wadda tsawon ta yake har guiwar sa, ya zuba dukkan hannayen shi cikin aljihun rigar amma hakan bai boye hasken agogon diamond da ke walkiya cikin lafiyayyar fatar hannun shi ba.
Ta ce mun gode Hashim, amma in gaya maka gaskiya wannan furen da kyar zaka same shi ya fiddo ido abin tausayi duk sai ya bata dariya, da gani maabocin raha ne shima kaman Alameen ya ce is she married (maana tana da aure?) ta girgiza kai tana murmushi tace uhm-uhm, tukunna dai, karewa ma dai wannan furen naka tsoron maza yake, da kyar zata tsaya ta saurare ka.
Yayi wata ajiyar zuciya mai karfi duk sai ya kara burgeta, da gani ba kankanin so ya kamu da shi a lokaci daya ba. Ya ce ni dai Yayata, pls help me, ni na san yadda zan yi, kuma zaki yi mamaki Allah, bata samu Mr Right dinta bane yet, amma ni tunda na ganta a Cairo nasan we are meant for each other kuma naga matar aure, shin zaki iya ba Bakatsine auren yar uwar ki?
Ta yi murmushi mai sauti har kyawawan hakoranta suka bayyana tace why not? Katsinawa sun dade suna burge ni. Don an ce akwai su da rikon aure da muhimmanci fiye da Kadawa da Kanawa. In har ya cancanci in bashi kuma tana son sa everything is possible wato komi mai yuwuwa ne.
Ta fiddo katin Babansu mai dauke da adires na gida ta kuma fiddo biro cikin jikar ta ta rubuta mai nambar Hunainah a bayan katin, yayi mata godiya sosai, ya ce har abada ba zan mance da wannan taimakon da kika yi mun ba Yayar mu, na gode. Da haka suka rabu, ta doshi Hanainah da ke ta faman cikka, kiris ta ke jira ta fashe.
Bata bi ta kanta ba ta fiddo waya ta cire layin ta na Cairo ta sanya MTN tayi lodin recharge da ta saya a gefe tana kiran Babansu, cikin minti goma sha biyar sai ga mota ya turo masu da direba, ya kwasheu zuwa Lamido Crescent.
A cikin motar Hunainah ta kara cika ganin Mamar da Baban ba wanda yazo taryon su ga bakin-cikin da Saratu ta kunsa mata kuma ta ki bata hakuri sai hawaye sharrr! Intisar tayi kokarin maida dariyar ta don kar ta fito ta rufe ta da duka.
Sai da suka shiga gidan ta sunkuya ta kwashi dariyar ta mai isarta tana bawa Maman labarin yadda aka yi da sabon saurayin Hunainah, ita ko tunda ta watsar da trolly din ta tayi sama bata kara saukowa ba, saida matsiyaciyar yunwa ta hullo ta.
Sun hadu a dining karfe hudu na yamma suna cin abinci tare da Baban su, yan biyu a cinyar Intisar hagu da dama tana sanya masu friso cream a baki da dan kankanin cokali yayinda Zarah ke zaune bisa tata kujerar kusa da ta Babanta Bashir tana cin vicorian sandwitch suna bashi labarin makaranta da yanayin karatun su, ya ce nikam ban so kika dauki surgery ba, naso ne ki dauki gynaecology domin muna da karancin likitocin mata kuma mata yan uwan su a nan Arewa tace lah Daddy, ai Hidayah ce tace zata dauka bayan ta haihu, sai na ga da mu taru duk a abu guda, ai gara a rarraba kafa ya ce wannan shirmammiyar ce zata koma wani karatu, ba ki ji ba tun yaushe take wakar zata koman kin kara jin sun tayar da zancen, ki daina sata a layin karatu bar ta dai da mijin da giringidishin ta, amma ba wani karatu da zata koma balle idan ta soma zubo yaya. Gaba daya aka sa dariya.
Yace Daddynki yace ki yi zaman ki sai ya neme ki, kuma kiyi shirin tarbar wasu muhimman baki gobe da zasu zo specially don ke ta yi murmushi ta ce,
Daddy kenan, shi gani yake har yau bana son zama da mama ne bai san alkunya nakewa Aunty na ba ta fada tana kallon mamar cikin ido cikin sigar tsokana.
Da ganin fuskar maman ka san ta ji dadin maganar ta amma sai ta daure fuska ta ce ke bana son rashin mutunci, Hajiya Saratun kike yiwa alkunya?
Don ta kara bata kunya sai ta shagwargwabe fuska ta ce to
“Mama ai so-so ne, amma son kai ya fi ko? Ni ma ina son jin dumin mamana da ta haife ni, don Anti Hajjo tace mun tunda aka sace miki ni
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 38