zai yi? Tunda gashi har Goggon su na cewa (da su abokanen wasa ne da an musu aure), kenan ta fahimci duk fadan da suke takalar junan su duk cikin sigar SO ne? Son ma irin wanda ya fi karfin boyuwa a zuciya aka rasa yadda za’ayi da shi ya fiddo kansa kowa ya gani.
A take ya amince da shawarar da zuciyar shi ta bijiro na tafiya (Birmingham) zurfafa ilmin sa (Masters) amma shi ba zai je soja kamar yadda Daddy ke so ba, ba don komi ba sai don kada ya mutu, ko a harbe shi bai ganewa idon sa wane irin (lucky man) ne zai sami Intisar a matsayin matar aure ba.
Shi kam ina ma ba’a gidan su yake ba? Ina ma shi ba dan Daddy Makarfi ne ba? Ina ma shi dan Wa, ko kanin Daddy ne?
Tunaninnikan da yake tayi kenan marasa kai da gindi har aka yi kiran assalatu a kunnuwansa, ya mike yana layi tamkar bugagge ya sako alwalla ya shiga nafilfilin da bai san iyakar su ba yana rokon mai canza al’amura daya canza mishi da mafi kyau.
Karfe shidda dai-dai na safiyar ranar wadda ta kasance Talata, ya dauki diary din shi yayi wasu rubututtuka masu matukar muhimmanci a gareshi da Saratu, yana yi yana zubar da kwalla tamkar ba Faisal ba, ya hade duk wani abin amfanin shi da yake bukata cikin katuwar trolly ruwan bula mai duhu, ya shirya cikin suit baka da ratsin toka-toka sunyi masifar amsar shi, ya matse wuyan shi da bakin tie ya barwa al’ummar gidan (note) cewa yayi sammakon tafiya ya kama hanyar Ilorin inda yake hidimar kasa.
Tunda Faisal ya tafi Ilorin ko waya bai yiwa kowa ba har tsayin watanni ukku cif, Daddyn na yi mai cuku-cukun tafiya Unibersity of Birmingham dake UK inda zai hado MSc dinsa wata kila ma har Ph D. Admission din bai fito ba sai a watan Mayu daga can ya tafi ko sallama bai zowa kowa ba, alhalin su Najib duk suna zuwa gida a duk karshen wata.
Hajiya ta damu sosai. A watan Najib, Bello, Yasir. Nasir da Faruk suka sami aiki a garin Enugu inda suka yi bautar kasa, aiyuka kuwa masu gwabi (tsoka), shi Najib a (Petroleum Refinery) na Enugu, Bello (mai sunan Daddy) a kanfanin Inshora, Yasir da Nasir a NITEL sai Faruk a bankin (Inland) da gidajen zama da motocin hawa da komi.
Sai gidan ya dade sai su Idris kananan dake makaranta suma basu faya zuwa ba sabida suna shekarar karshe karatun yayi masu zafi sosai.
Haka kawai Intisar ta rika jin ranta na baci kamar koyaushe wani bakon al’amari zai faru da ita mai dadi ne ko mara dadi? Sai da Faisal ya cika watanni ukku cif yana karatu a Birmingham Daddy ya kira Hajiya yace da ita Faisal fa ya zarce UK yin M Sc din sa, in ya ga dama bayan shekaru biyun ya dawo, in yaso kuma ya zarce har Ph D ba zai takura mishi ba.
Brigadier na girmama Faisal duk cikin ‘ya’yan sa a sabili da abubuwa guda biyu: juriya da karfin zuciya.
Faisal ne a duk cikin ‘ya’yan sa zai ce mai yayi abu yayi koda ransa baya so, sannan duk cikin ‘ya’yan sa ba mai hakuri, nutsuwa da sanyin ran Faisal, yana da daukan komi na rayuwa da sauki, (sabanin Ameenu mai zafafawa akan al’amuransa).
Don haka duk abinda Faisal din ke so yana kokarin yaga yayi mishi, in har bai fi karfin sa ba, baya son ya bata masa ko kadan kamar yadda shima yake mai biyayya da zuciya, gangar jiki da duk abinda ya mallaka yaron baya da kwaramniya ko kadan kwatankwacin su Najib, hakannan kome zai yi in ka auna sai kaga hikima a ciki, baya yin abu kai tsaye sai ya tabbatar yana da hujja na yin hakan.
Don haka ko kadan bai damu da makudan kudaden da ya narkarwa Faisal yayi M. Sc a turai ba, shi dai burin sa ya sanya shi farin ciki kamar yadda yake sanya shi a kullum
Hajiya ta gunduma ashar ji kake abu kazan uban nan…don me Daddyn bai gaya mata ba sai bayan ya tafi, kan me ba’a shawara da ita kan harkokin ‘ya’yan ta sai kace ba ita ta haife su ba?
Ta tsuguna ta haifo dan a cikin ta a ce Saratu ce mai tsara mishi yadda take so? Yace tayi hakuri kada ta dauki hakki, Saratu bata ma sani ba balle ‘yar ta.
Faisal dai dan sa ne, kuma shi ya roke shi alfarmar baya son kowa yasan zai tafi, sai bayan ya tafin, tace ai don ya san zata hana ne shi yasa ya hana a gaya mata, duk an tarwatsa mata ‘ya’ya cikin duniya an hana mata jin dumin su, alhalin ba’a san yadda tayi ta haifo kayan ta ba, ba komi yasa Daddyn yake barin su suna tafiyar ba sai don bai son ta ji dumin abinta, yana bakin ciki don matar sa bata da su a fake da karatu, to wane irin karatu ne da bai isa a yi shi a nan cikin kasarmu da manyan jami’o’in da mu ke da su ba?
Ko su da basu yi ba karatun ba wani abu ya ragu a jikin su? Daddy Makarfi sai yayi dariya ya kamo hannun ‘yar rigimar yace
“bai ragu ba kam, amma ai gaki nan kina abu kamar rudaddiyar tsohuwa ko ni nan na fiki wayewa.â€a kara kuluwa ta fige hannunta ta nufi kofa tana kunkunin Daddy ya gaya mata magana don ya nuna mata matar shi na aikin banki, har ita za’a gayawa wayewa, ita da take fita kasashen duniya saro zinarai take ciniki da matan manyan kasa bakidaya aikin kawai, ta sani dai baya shawara da ita kan harkar ‘ya’yan ta, to dai ita ce uwar su, wanna sunan (Nafi Uwar su Aminu) ba zai taba canzawa ba, kuma da tsohuwar zuma ake magani haka duk warin daddawar, ita ta gyara miyar (tana nufin ita da bata yi karatun ba, ita ce ta tallafi gidan a sanda aka garkame shi a kurkuku ba masu karatun bokon ba), fiye da wannan ma matsayin ta na mahaifiyar su ya dace a dinga neman yardarta kamin zartar da komi a kan su koda karatun ne.
Shi kansa Daddy ya san ya bata mata kuma tana da ‘yar gaskiyar ta sai yayi ta lallashin ta, yana nuna mata menene don Faisal ya tafi Turai? Ita da kullum take hantara da kyarar shi ai jin dadin ta ne, sai tayi murmushi ta huce, ta fi kowa farin ciki.
Tafiyar Faisal� na nufin al’amura masu muhimmanci a gareta, tafiyar Faisal� na nufin farin cikin ta, farin ciki ba daya ba, ba biyu ba hakannan ba uku ba, tafiyar Faisal� na nufin cikar dadadden burin ta.
Ko ba komi, Intisar za tayi bakin ciki, watakila har yayi sanadiyyar katse duk wani farin cikin rayuwar da take ciki a yanzu. Ita ko mai farin ciki ce da duk wani bakin cikin su Saratu a rayuwa.
Saratu da Saratu zasu daina amfana da dan ta, zasu daina morar sa wanda wannan ba karamin nakasu bane ga rayuwar Intisar kuma cigaba ga wani specific (kayyadaddden) kudurin ta a gaba, wanda bai wuce na raba Saratu Da Saratu da duk wani farin ciki dake cikin rayuwar duniya.
Sai tayi murmushi ta sawa abun albarka, tace da Daddy Allah yasa kada shi ya mancesu, ya guje su ya nisancesu tamkar Al’ameen.
Daga Intisar har Antin ta sun ji tafiyar Faisal ne kamar daga sama. A falo Anti Saratu tayi ta kakabin abin Intisar na jin ta bata ce komi ba, hakannan bata juyo ba domin a lokacin tana wasa ne da kwamfutar antin tana ‘game� din ‘Mabis Beacon�. Ashe wannan shine trauma din da take sunsune tun watannin baya; Rabuwa Da Ya Faisal!
Idon ta suka yi rau-rau sai kwalla suka zubo masu zafin gaske, tasa bayan hannun ta ta share da sauri don kar Anti ta gani. Antin ta zauna shirim, cikin ‘leather seat� din da suka yiwa falon kawanya tace
“Saratu shine ko ki gaya mun Yayan naki zai tafi Birmingham?�
Da Antin ta san kunci da tukukin dake nukurkusar zuciyar wannan baiwar Allah, hakika da bata yi mata wannan tambayar ba, amma Anti ce, bai yiwuwa ta kyaleta duk yadda taso yin hakan, duk kuma irin rashin son maganarta a lokacin, tace
“Mamar mu babu abinda zan iya boye miki, in da ya gaya min zai tafi, abinda na sani kawai shine brother is in love (yana cikin soyayya) amma yace wai ba zai taba iya auren yarinyar ba, nake jin abinda yasa ya bar gida kenan.
Amma ni ce shaidar cewa Ya Faisal ya tsani karatu ‘abroad (kasar waje)�.
Anti tayi jugum, kallo daya zaka yi mata ka tabbatar tafiyar Faisal ya taba zuciyar ta, fiye da zaton Hajiya, ya takaita farin cikinta, fiye da yadda Hajiyar ta kintata a zuciyar ta, ta ce,
“Oh ni Saratu! Ban da abun Faisal maiyasa ba zai fadi ba, sai ya bar kasar? Bana jin ko diyar wanene a garin nan da Babanku ba zai iya aura mishi ba. Allah to ya sa hakan shine mafi alkhairi.�
Da daddare tayi shirin kwanciyar barci kamar yadda ta saba amma me? Idanuwanta sun ce basu san wannan ba. Tayi kukan ta mai isar ta, da ta kasa gane musabbabin sa.
Ba zata ce son Faisal take ba, don bata san ma hakikanin menene son ba. Amma da tayi tsam da ranta ta fahimci kishin yarinyar da ta sa Faisal barin Nijeriya ne!
Haushin tafiyar sa ya shafe kewar sa, mafi rinjaye shine irin matukar sabon da su kai da juna.
Akwai wani kebantaccen al’amari game da Faisal a tare da ita, da ita kanta bata san menene ba. Abinda zata iya cewa shine Faisal, wani mutum ne precious wato (mai darajja) da kima agareta da muhimmancin sa da kimar sa ya zarta na kowa in ka dauke Daddy da Mamarta. Kenan mancewa da shi a tarihin rayuwar ta ko barin tunanin sa, wani abu ne da ba zai taba kasancewa ba!!!
Mu karasa a littafi na uku, Takorin ku ce.
Wa billahi taufeek!
How much do you like this story?
5/9/22, 21:00 - Ummi Tandama😇: ____________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book three
*@Takori*
Page1ï¸âƒ£
Lahadi/Jumada-Awwal
Watanni Biyu Bayan Barin Faisal
Satin Daddyn kwata-kwata biyu da fitowa ya shiga sabon ofis din sa a gidan shugaban kasa. Cikin watanni biyu rak arziki ya ci uban nada, rayuwa a gidan Brigadier Makarfi ta dawo sabuwa ful arziki wane shekarun baya.
Sai da hankali ya natsa aka mance komi Aunty Saratu ta farkewa Daddyn gaskiyar Saratu bata kammala karatu ba.
Daddy yayi ta fada har yana haki kan don me tuntuni bata gaya masa ba, da yanzu bata yi zangon karatun ta na farko a aji shidda ba, gashi shekara ta zo tsakiya tilas abarwa sabuwar shekara mai kamawa in Allah yayi tsawon rai. Amma kam ran shi ya matukar baci inda ya dauki duk laifin ya daura akan Anti Saratu.
Ranar Lahadi, cikin sabon watan Jumada Awwal, ta shirya cikin wani lallausar material baki wuluk mai yarfen jajayen furanni. Curarraren gashin kanta ta nade shi tsaf cikin dankwalin kayan ta yadda baka ganin ko sili daya, kafar ta sanye cikin (bed-shoe) watau takalmin bakin gado, sannu a hankali take sauka daga benen sassansu tana bin matattakala cikin nutsuwa da yaukin ta na musamman da Allah ya hore mata.
Tayi amfani da sassanyan turare (Week-End Burberry) sanyin kamshin na tashi daga jikin ta kadan-kadan inda duk ta gifta har ta iso falon hutawar Daddyn, da yake ranar Lahadi ce, ya kan kasance ne a falon yana ‘browsing� tun safe har bayan karfe hudu na yamma baya zuwa ko’ina.
Ta sakko ne musamman da niyyar bashi labarin Hidayah da Hunainah Bashir Sambo, kawayen ta na makaranta da suka shaku, bata taba yi mai zancen su ba, shi ko Daddyn komi nashi ita yake fara gayamawa kafin kowa a gidan har matan sa kuwa, tana ganin Daddyn zai taimaka ya binciko mata inda suka koma a Korea da adireshin su, kullum da tunanin da take kwana take tashi kenan, don dai hankalin su bai kwanta bane sai ko yanzun da take ganin ya dace Daddyn ya san da su Hidayah, har abada bazata taba mancewa da su ba.
Yaran Sun zauna cikin kwakwalwar ta (like the screen saver of her imagination) Musamman Hunainah, kauna ce mai karfi take masu da har ta kan tambayi kanta, da su da Ya Faisal, wa ta fi kauna?
Ta same shi da ‘laptop� din shi ne kamar yadda tayi tsammani, sai ta ja kujerar da ke fuskantar shi ta zauna, suka dubi juna suka yi murmushi ta ce,
“Daddy an tashi lafiya?�
Ya ce, “Tunda ki ka ganni a nan ai zance ya kare, kin san tambayarki itace amsarki Saratu�.�
Magana yake amman hankalinta baya tare da shi, yana ga allon kwamfutar. Wani kayataccen rubutu ne Daddyn yayi, yayi mai ‘design� mai kyau, da gani yayi ne don ado kawai cikin kwanfutar ba don ya aikawa wani ba, kalolin da aka kawata rubutun da su masu daukar ido ya dubesu ne koda bai yi niyya ba.
A gurguje ta shiga bin rubutun bata sani ba ma a fili takeyi ba.
“Although he refused to assist me when I needed his assistance most, I should, however, forgive him wholeheartedly.�
Ma’ana “Duk da cewa ya ki taimakamin a sanda nake tsananin bukatar taimakon sa, duk da haka zan yafe mai da zuciya daya�.
Cikin ‘yar karamar muryar ta ta ce, “Daddy waye wannan?�
Yace “Yayan ku Al’ameen ko kin manta shi?�
Ta kai hannu ta zare gilashin ta a hankali ta ce, “Al’amin kuma? Waye haka?� Cikin tsananin mamaki, zaka iya karantar hakan karara cikin abnormal (marassa lafiyan) idanun ta.
“Muna da wani Yaya ne Aminu Daddy ko dai cikin dangi ne ta Makarfi?� Mamaki ya kama Daddy, ya ce,
“Sanda Aminu ya bar kasar nan bakiyi wayau ba, Aminu ne ya janyo maki laluran ido, har da shi muka kaiki asibiti a Jeddah ba mamaki da baki san shi ba, abin mamakin shine ko sunan shi baki sani ba?�
Ta ce, “Kwata-kwata ban taba ji a bakin kowa ba, ba wanda yake zancen shi daga Ya Faisal, Ya Najib har su Mamar mu ban taba ji ba.�
Yayi murmushi ya ce,
“Su Najib ai haushin sa suke ji, sunce sun fidda shi a layin ‘yan gidannan.� Abinda ta lura da shi shine idanun Daddynsu cike suke da kaunar dan shi Al’ameen da bege mai tsanani. Ta gyara zama ta ce,
“Daddy a bani labarin Ya Ameenu?� Ai kamar mai jira ta tambaye shi, ya shiga bata labarin Al’ameen tun daga rayuwar shi ta kwaleji, hazakar shi irin nata, da yanayin mu’amalar shi da mutane. Ya ce,
“Mutane da dama na mai mummunar fahimtar girman kai da wulakanci, amma ni nasan Al’ameen dina (gentle) ne kawai. A ‘ya’ya na ba mutun irin Al’ameen Saratu, domin shi din genius ne (mai madaukakiyar iyawa).
Al’ameen nawa, yana kaunata sosai Intisar, ban taba zaton jin dadin turai da kyale-kyalen ta zasu sa ya mance ni ba balle…� Bai iya ya karasa ba sakamakon hawaye da suka shimfido mai a guje.
Ya juyar da kai don bai son Sartun ta gani amma ta ganin. Tuni itama nata idanun suka cika da kwallah, tayi azamar mai da gilashinta tasa tissue tana share hawaye ta kasan gilashin. Tsana da haushin wannan Yaya Al’ameen ya dirammata tunda kuwa har zai sa Daddy kuka da azabar kewar shi, bata san sanda bakin ta yayi subul da cewa
“Daddy maiyasa kake son Al’amin har haka?�
Yayi murmushi ya ce, “biyayyar sa.
Ban taba ganin yaro mai gudun bacin ran iyaye a duniya irin Al’ameen ba. Yana jin maganata yana yi mun biyayya, ban taba cewa ya bar abu yaki bari ba sai a kanki.
Ya gaya mun sabida nadamar abinda ya aikata gareki ne ya bar mu kwata-kwata don aganin shi bashi da amfani a gareni…�
Ya kwashe labarin komi ya gaya mata, bata yi wani mamaki ba, tunda kuwa dan Hajiya Nafi ne, ba illata ta ba, ta tabbata ko konata ne Hajiya zata iya sawa a yi.
To amma albarkacin wannan son da ta ga Daddy na yiwa Al’ameen sai taji itama tana son shi, bata kullace shi ba ko kadan.
Tabbas a lokacin zai kasance yana yaro ne cikin gigin kuruciya, tana da tabbacin da zai zo a yanzun he’ll be a caring brother (dan uwa mai nuna kulawa). Tace
“Kaayi hakuri Daddy, ni na tabbata Al’amin zai dawo a lokacin da bamu zata ba.� Ya ce, “Kayya Intisar, Aminu fa har gaya mai akai an kulle ni, akan laifin da ya tabbatar ba zan taba iya aikatawa ba, amman yace wai zaman Amurka ya fiye mai kwanciyar hankali bazai dawo ba.
Koma menene laifi na ne da tun farko na amince mai ya tafi.
Ban taba kuka akan son dan da na haifa ba sai a kan Al’ameen. Ameenu yaro ne mai matukar shiga rai don haka fidda tunanin shi a lokaci guda, abu ne da bazai yiwu ba.
Tunanin sa na azabtar da ni Saratu Ina kokari ina dannewa ne kawai don bana son kuma ku shiga damuwa�.
Inteesar tayi zuruuu tana sauraren Daddyn duk tausayin sa ya nannadeta, amma a ranta cewa take Allah ya isa tsakanin ta da wannan Ameenun, kuma wannan Al’ameen anyi tsinanne, tunda kuwa har zai iya sanya rayuwar Daddyn su a wani hali bayan wanda ya fito, kuma akan sanin kansa, suna murna duk wata matsala ta kare?
Shin shi Ya Al’amin din nan bai tsoron hakkin Daddy ya hana shi kwanciyar kabari?�
Ta tausasa halshen ta ta dukar da kai cikin matsanancin takaici ta ce,
“Ba dai biyayya Al’ameen yake maka ba Daddyn mu? To na yi alkawari tsakanina da Sarki Allah zanyi ma biyayya Daddy irin wadda Al’ameen bai taba yi maka ba! Zan maye maka gurbin Al’ameen.
Zan wanzar da rayuwa ta a biyayyar ka, zan dauwama a cikin umarnin ka in har bai sabawa mahalicci ba, bazaka taba sani abu in ki yi ba koda ya fi karfin lafiya, rai da abinda na `mallaka; sai dai in mutu a cikin umarnin ka Daddy!�
Kalamun ta sun matukar bashi mamaki, hakannan sun girgiza shi amma bai nuna ba, sai yai murmushi ya shafi kanta da hannun shi na dama. Shi kansa ya san hakan a tun ranar da ya daukota cikin tsumman goyonta a dokar daji. Ya ga alamun hakuri, biyayya, kyautayi da jin kai tattare da ita.
Yana kaunar ta, kaunar da baya yiwa daya cikin ‘ya’yan sa bayan Al’ameen. Ta ce “Wai shin ba’a bin sawun Yaya Aminu ne?�
Ya girgiza kai, “Ba wai kudin ne babu ba Saratu. America kasa ce mai girman gaske, (It’s the greatest country of the world). Abin takaicin shine yana birnin Miami yana buya a cikin Florida kar mu gan shi ko kar mu san inda yake. In banda adireshin sa na e-mail ban san komi game da shi ba a yanzu.
Kuma ke a tunanin ki yaron da ya watsar da iyayen sa akan kansa, bai son ganin su kina ganin ya dace iyayen su zubar da darajar da Allah yai masu ta iyaye su nemeshi?
Ai har kullum da ke neman albarkar iyaye ba iyaye ke neman albarkar da ba.
Yaran yanzu ne ka haife su amma baka haifi halin su ba. Duk in da uba ya kai ga gwada masu kauna da nema masu farin ciki su sai sun sashi kuka. Ba zan nemi Al’amin ba koda zan mutu ne ban gan shi ba, koda na mutu, Saratu ki gayawa Yayanku Aminu, son nan da nake mishi tun yana gudan jininsa, ina zumudin a haife shi in samu magaji, da kasancewar shi buri na ba abin da ya canza har gobe sai ma abinda ya karu.
Kuma har cikin raina na yafe mashi kuncin daya dasa mani na shekara da shekaru.�
Sai ta rufe bakin Baban su da tafukan hannun ta, kamar tace wayyo Allah! Sabida bakin cikin Al’ameen da mutuwa da Daddyn ke ambatawa kansa.
Ta ce, “Insha Allahu Daddy ni da kai, zamu gayawa Ya Ameenu wannan. Daga yau zan fara Addu’a duk inda Al’ameen yake, Allah ya karkato da hankalin shi gida Daddy.�
*****
Wani muhimmin abin farin ciki daya samesu bayan kubutar Daddy da ‘yan watanni shine bayyanar matashin ciki jikin Anty Saratu, farin cikin Inteesar a wannan dan tsukin kema kin san ba sai an fada ba. Daddy don farin-ciki makullin mota KIA ya danka mata fara sol ta fara zuwa sabon aikin da ta samu da (Afri-Bank). Gabadaya sun kirayi shekarar da watan Jumada-Awwal; ‘Cikar Burin Shekara Da Shekaru.�
Dukkan Farin-Ciki Na Tafiya Ne Da Bakin-Ciki
Laraba/Ashirin Ga Watan Jumada-Thani
Ranar wata laraba, da saratu ta kira LARABGANA a gareta, ya kama ranar girkin Antinne don haka tayi mata sallama ta nufi sassan Daddy, duk ranar girkin ta haka suke wa juna, babu zancen kunya tsakanin Saratu da diyarta Saratu.
A lokacin cikin ta ya shiga watanni uku duk wasu alamomin mace mai juna biyu sun gama bayyana a jikin ta. To bayan fitar Antin har goma na dare Inteesar na falo kwance cikin (rest-chair) dake falon tana sauraron labarun ‘network� daga gwanin ta Cyril Stober da Hawwa Baba Ahmed bata san sanda barci mai nauyi ya dauke ta ba, sabida a yau wuni sukai girke-girken Daddy ita da Mamarta ko na minti biyu ba su huta ba.
Ba ita ta farka ba sai karfe ukku na sulusin dare shima sakamakon masifafffen sanyin da taji yana hurata ne, ta yayibi bargo ta ji wayam. Ta mike taga yadda ta bar komi a kunne ta kashe talbijin da ke ta shuuu! Da sauran kayan wutar da ke falon.
Ta daga labule da niyyar kashe fitilun falon ta je ta kwanta kenan taji motsin ana taba kofa. Cikin ta ya hautsina ji kake kulululuuuu! Musamman data tuna bata rufe ko kofa daya ba bayan fitar anti, a guje ta shige bayan labule ta sandare ko kwakkwaran numfashi ta kasa shaka balle ta fesar.
Ba abinda ta kawo wa ranta a lokacin face gaggan ‘yan fashi ne suka kawo masu ziyara, amma wannan ba karamin abin mamaki bane in akayi la’akari da irin sojojin da ke gadin gidan Bello Makarfi tuni ta soma hawaye, a lokaci guda kuma fitsari ya kulle mata mara.
Bata san sanda ta sakeshi daga tsayen ba.Tsoron ta Allah, tsoron ta kada su taba lafiyar Daddyn ta. Ko wannan shine dalilin yin zancen mutuwa da Daddyn yayi mata a kwanakin baya?
Daga inda take rakube a bayan labule, tana iya hangen kofar shigowa falon su kasancewar labulen shara-shara, kuma dakin gauraye yake da hasken da Allah bai bata ikon kashewa ba.
Tana ganin sanda aka turo kofar falon cikin nutsuwa da sanda, ba abinda ‘yan idanun ta basu gane mata ba kasancewar akwai wadatar hasken kyandir kamar safiya. Sanye da bakar zulumbuwar riga, kanta a tsefe, tana rike da bakar kwarya a hannun ta na dama, wata bakar tsuntsuwa ce da ake kira mujiya matacciya rike a hannunta na hagu; Hajiya Nafi ce.
Kanta tsaye ta murda kofar dakin barcin Antin ta shiga, tafi karfin awa daya kamin ta fito, tuni numfashin Intisar ya dauke. Ashe bata gama razana da mamaki ba?
Da ta fito daga dakin Antin dakin Intisar din ta afka gaba-gadi. Ji tayi kamar tayi ihu amma sautin ya dauke kakaf.
Me wannan baiwar Allah ke yi masu haka a dakuna cikin irin wannan talatainin dare?
Nan ma tafi awa biyu kamin ta fito. Ta diba gabas, yamma, kudu da arewa bata ga kowa ba, sai kurum ta fice ta jawo kofar. Daga kwaryar har tsuntsuwar, sun bace bat.
Wai a wauta irin tata, sai ta sheko da gudu ta lelleka dakunan ko zata ga in da ta aje masu kwaryar da mujiyar? Tunaninnika iri-iri ke shigar ta. Mafi rinjaye shine Hajiya na bakin ciki da cikin da Anty Saratu ke dauke da shi, shine tazo tayi mata wani mugun abu?
Ta sha jin ana cewa Anti Suwaiba aminiyar Hajiya matsafiya ce ta kuma dade tana son sanya Hajiya a turbar tsafe-tsafe Hajiyar na ki, don ita Hajiya na daga cikin irin matan nan da basu yarda cewa asiri shi zai kwato masu miji ba sai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 38