irin hannun da zamu fada a gaba? Kada ki guji mutanen da kika taras da farko domin irin su ne zaki taras a gaba�.
Shekarun mu biyu a gidan Hakimi muna bauta. Ba zan taba mancewa da ranar da Basheer kanin Hakimi ya dawo daga jami’ar Nsukka inda ya ke karatu ba.
Basheer shakikin Hakimi ne da Hakimi ya rike tun yana karami bayan rasuwar iyayen su. A nan garin yayi firamare ya ci makarantar kwana ta FGC da ke Kano ya je ya kammala da sakamako mai ban mamaki. Hakimi ya danka mai gadon iyayen su da ke hannun shi ya ce ya je yayi ta karatun har ya gaji sabida hazakar shi. Tun da Basheer ya wulwula kudu ba’a kara jin duriyar shi ba sai ranar nan. Gabadayan karatun Basheer yayi shi ne a kan (Diplomacy), tun da ya bar Shanono bai dawo ba sai ranar da ya hado digirin shi na biyu, ya watsa takardun neman aiki a (Nigerian–Embassy) na kasashe har ukku sabida International Studies ya danganci aiki da kasashen ketare ne.
Ranar kwatsam sai ga Bashir, ‘ya’yan Hakimi da matan shi duka suka debi murna babu babba ba yaro kowa baki a washe har muma da ba’a san da mu ba muna ta dariya, kasancewar Bashir mai faram-faram da barkwanci kowa son shi ya ke a gidan. Ban taba ganin Hakimi na far’a, irin wadda ya rika yi a ranar da Bashir ya dawo ba.
Rannan ina shara Bashir ya zo wucewa dakin amaryar Hakimi, ban ga tahowarsa ba na sharo mai sharar da na sharo a kafa cikin wasa yace,
“ke ‘yar fillo, ba kya gani ne? Koda yake na gane wayonki, don in rasa mata ne, to ai ni kyakkyawa ne a Nsukka kar kiso kiga yadda ‘yammata ke bibiya na, ni nan da kike gani ‘yammata jaka-jaka gare ni�.
Hajjo da ke gefe tana wanke-wanke ta ce
“ka yi hankuri, bata sani ba ne�. Ya kai duban shi gareta domin da fari bai lura da kasancewarta wurin ba, sannan ya dube ni, a kidime yace
“ikon Allah, ke Hussainarta ce ko, koko ‘identical twins� kuke?� Duk sai muka yi murmushi a tare, kumatunan mu suka lollotsa gwanin sha’awa. Bishir ya bushe a tsaye, yace “ku ‘ya’yan makota ne?�
Hajjo da ya ke Allah ya zuba mata magana, a komai ma da ba’a tambaye ta ba balle wannan mai dalili? Wani zubin surutu har tsunkulin ta yake, ko ni aka tambaya abu in har tana wurin ita ke aran baki na ta ci mun albasa, tayi narai-narai da ido ta rausayar da kai gefe ta ce ,
“ai mu marayu ne, Uwa da Uban mu duk sun mutu, ruwa ya tafi da Yafendon mu, Baffan mu kuwa garin gudu yumbu ya kayar shi ko shurawa bai yi ba…� sai ta koma kukan da ta ke kwana da wuni ta na yi.
Bashir ya matsa gare ta ya russuna a gaban ta cike da tausayi yace “ayya kanwata! Duk wani mai rai mamaci ne, muma nan duk zaman jiran ta muke.
Nima Bashir tamkar ku din nake, har gara ku kun san Innar ku har kun yi rayuwa mai dadi tare da ita, ni ko tana haifana ko fuskana bata gani ba ta tafi ta bar ni. Bani da kowa a fadin duniyar nan sai Allah, sai Yaya na, amma ba na kuka, don haka kema ki daina kuka. Daga yau na zame maku Yaya, kin ji?�
Hajjo ta gyada kai alamun ta ji abinda ya ce. Ya sanya hannu cikin aljihu ya fiddo hankici fari sol da shi ya mika mata yace � share hawayen ki maza-maza, zani cikin gida yanzu zan dawo�.
A wurin uwar gida Kwaire ya nemi jin labarin mu tace “haka kawai ya je ya kwaso mana masifa rana tsaka, don sun gudo daga daji, ka gansu nan in ban da bauta ba abinda suke mana, kaima in kayan ka sun yi datti, ka dinga dankara masu har gugar takalmi daga yau kar ka kara yi, tsuntsu ne Allah ya kawo mana daga sama gasashshe�.
Da Hakimi ya shigo gidan bayan sallar lisha Bishir ya ke tambaye shi labarin mu. Hakimi ya kwashe komi ya gaya mishi har ciwon da nayi kamar ba zan rayu ba. Ya kare da cewa “ni kam don Allah ni ke rike da yaran nan, na kuma san sakamako na na gareshi. Duk ma mai cutar su cikin mata na ai ita da Allah, Allah yana kyale hakkin maraya ne?�
Sai da Bashir ya fiddo hawaye don tausayin mu ya kuma ce da Hakimi zai aure ni koda bamu da iyaye balle muna da su. Hakimi ya sa mai albarka mai yawa amma sai ya ce tunda shi saurayi ne ya auri Hajjo ita ce budurwa, amma ni na gaya mishi na taba aure har na haihu mijin ne ya mutu aka kuma sace diyar. Bishir yace shi ba budurwa ta dame shi ba, hakannan tun da ya ganni ya ji bai iya rayuwa ba tare da ni ba, Hajjo kuwa zai rike yadda zai rike diyar cikin shi har zuwa sanda itama Allah zai bata miji ya yi mata aure.
Ya roki Hakimi da ya bar sirrin nan a tsakanin su ko muma kada ya bari mu ji bare matan shi da ke kin mu tamkar mutuwar su, har zuwa sanda takardun shi na aiki zasu fito, kamin nan yana so ya ja ra’ayinmu mu saba da shi musamman ni da ya ga ko magana bana yi da kowa.
Shima Hakimin tunanin shi yayi dai-dai da na dan uwan shi, ya kara karfafa shi da cewa abin da yayi jihadi yayi, da sannu zai ga budi da nasara cikin rayuwar shi. Don duk wanda ya taimaki wani babu shakka Allah zai taimakeshi. Yayi masa Addu’ar samun aiki mai tsoka wanda zai tallafe mu har mutuwa ba tare da gazawa ba, ya kuma kara tunatar da shi hakika yayi riko da sunnah, domin Manzo mai tsira da aminci ma ya fara ne da auren Nana Khadijah a lokacin tana bazawara, ta ma girme mishi nesa ba kusa ba. Kuma mata irin Dije sai wanda Allah ya nufa da samun rahmar aure domin daga halaye, dabi’u zuwa surar ta duka babu mummuna, ta kowanne fanni ma na fi ‘yar uwata nutsuwa.
Tun daga ranar Bashir bai barin mu mu yi wani aiki mai wuya sai ya amsa ya yi. In wanke-wanke ne sai dai ya wanke mu dauraye haka in surfe ne sai dai ya surfa mu tankade, in kuwa wankin kayan su ne sai dai ya saba mu dauraye mu shanya.
Ga shi da raha kullum cikin sa Hajjo dariya ya ke don ni da wuya duk ban dariyar sa ya ga hakorana. Rannan ya ce da Hajjo mai yasa ni bana dariya ne?
Hajjo yadda suka saba da Bishir komi fada mai take bata boye mishi komi da ya shafe mu, haka kawai zan ji tana bashi labarin yadda muke rayuwa a ruga tare da Innar mu. Rannan ma ji nayi tana koya mai yadda ake tatsa harda cewa “Kawu na, Saniya fa sai da shafa a ke tatsar ta.�
Ya tintsire da dariya ya ce,
“kenan nima Hajjo sai da sannu zan samu So daga Yayar ki?�
Ta ce “meye so kuma Kawu na?�
Ya daura hannun sa bisa kirjin sa ya lumshe ido yace “So, is a feeling for deep affection, a bery strong feeling of affection…� ta yi sukutiii…� tana sauraron shi da dukkan hankalinta da iyakar fahimtar ta, tace “magana kake ko yare?� Yace “tunda baki ji ba shikenan�.
To a yau ma sai ta gyara zama, ta kalmashe ‘yan kafafunta kyawawan idanuwanta cikin na Bashir, na tabbatar wani babban sirrin zata kwaye masa, da haushi ya isheni sai na kai mata mangara da hauri da kafa, Bashir ya yi hamzarin rike hannuwana duk sai naji jikina ya yi sanyi, yayi saurin saki na ya dube ni cikin ido, wata irin kunya ta lillibe ni, wani abu ya daki kahon zuciya ta irin wanda ban taba ji ba nayi saurin sadda kai, yace
“ko da wasa, kada ki sake dakar min kanwa ko bana nan ban yafe ba, Hajjo na gaya mun, mai yasa Hadizah bata dariya?�(Don shi bai taba cewa Dije ba, ita ma Hajjo ya hana ta har ta saba da fadin Haddizar), ta dube ni tayi murmushi kana ta maida duban ta ga Bashir, ta kalmashe ‘yan idanun ta tace.
“Kana ji ba?
Can-can an mata aure, an sata a lalle ta je gidan miji, ta haifo sankaceciyar jaririya, hancin ta irin wannan (sai ta ja nata), bakin ta irin wannan (sai ta ja nawa), gashin ta curi guda. Sai barayi suka lalabo cikin dare suka dauke ta suka ranta a na kare…� (tana yi tana gwada irin gudun da barayin suka rika yi da ‘yan yatsunta). “Tun daga ranar bata kara yin dariya ba, sai ciwo, ta yi ta ciwo kaman ta mutu, ka san kowa yana son dan sa Kawu na, kamar yadda Innar mu ke son mu, tamkar yadda Addar nan gidan ta ke son Salisun ta muku ta ke zagin mu. Rannan tace mun watakila ‘yar ta ta mutu yanzu tunda ba wanda zai ke bata nono…�.
Bashir yayi shiru ya juyar da kai, bai son su ga hawaye ya ke fitaswa. Ya sa hankici ya dauke hawayen idanun shi da suka kada suka yi jazur kamar gauta, shi kan sa bai san ya akai ya baro wannan maganar ba.
“Hadizah, Insha Allah za mu ga ‘yar ki Fatimah, mu hada da wadanda zamu haifa a gaba mu sa su a makaranta, suyi karatu irin nawa. Mu mun rasa soyayyar iyaye tun muna kankana, amma su Insha Allah zamu rungume su da dukkan so da dukkan kauna har zuwa ran da muka daina numfashi�. Sai ya tashi ya fice.
Matan Hakimi fa suka maida idanun su kan Bashir da duk wani takun shi cikin gidan. Wasu cikin su suka ce dakin mu yake zuwa cikin dare yana lalata da mu shiyasa ya tare a gindin mu, wasu suka ce a’ah, ai har da ranar ma abinda muke yi kenan cikin daki.
Rannan har yana gayawa Inna Kwaire magana don ta ce da Hajjo tsintacciyar mage, yace da ita sanda Yayan shi ya aureta, aka dauko farin kyallen da ake shimfidawa amare fari kwal aka same shi, don haka gara Hajjo da aka tsinto daga daji ta san mutuncin kanta, itako da aka tsinto gaban iyayen nata ai basu ga mutuncin ba.
Ai kuwa a ranar data kama Hajjo da duka sai da ta targada ta.
Da Bashir yaga abin nasu bana kare bane sai ya zuciya, ya sami Yayan shi yace ya ja ma matan shi kunne ko dukkansu yayi masu dan banzan duka. Hakimi yayi murmushi yace yanzu kai Bashir, in aka kyale ka sai ka daki matan aure da ‘ya’yan su da jikoki da surukan su suna kallon ka?�
Ya ce “to sabida Allah ina ruwan su da yaran nan ne don Allah tun da dai ba zaman su suke ba koko akan su suke zanne?� Hakimi yace
“in kana son komi ya zo karshe, gobe a daura auren ku da Dije, ku zauna anan dakin da suke har zuwa ranar da Allah zai yiwa aikin fitowa�. Bashir ya amince.
A ranar ne kuma ya samu sakon kiran (Intrebiew) daga Abuja ana kiran su a safiyar washegari, ya gayawa Hakimi kar a fasa daurin aure amma shi za shi Abuja ya san maganar aikin ne.
Karfe goma na safe Hakimi da Liman suka daura aure na da Bashir akan sadaki naira dubu biyar. Duk wasu kayan lefe da ke yiwa ‘yar gata a garin Shanono Hakimi yayi mun ni da ‘yar uwata. Har gobe, bani da abinda zan ce da Kawun nan naku Hunainah, domin yayi mun abinda ko mahaifana da suka haife ni iyakacin abinda za su yi mun kenan.
Babban alkhairin sa gare ni shine da ya hada ni da miji irin Bashir, daya zamo jigo ga rayuwata, bango abin jingina ta kuma abin alfahari na.
Don haka har kullum bana tashi daga inda nai Sallah ban nema masa rahma da gafarar Ubangiji ba.
Sati na zagayowa sai ga Bashir cikin farin cikin da ba zai misaltu ba tare da wani abokin sa Hassan cikin motar Hassan din.
Yana gaida kowa shi da Hassan suka shigo dakin mu, Bashir ko kulawa da su Hajjo da Hassan bai yi ba ya sure ni ya shiga juyi da ni a tsakar dakin. Hajjo ta ja mayafinta ta rufe ido tana laluben bango tana cewa “bako-bako boye ni, kada Kawu na yace na yi rashin kunya� ta shige cikin babbar rigar Hassan gabadaya suka sa dariya.
Bashir yace “Khadijah tabbas ke alkhairi ce a gare ni, kamar yadda takwarar ki Nanah Khadijah ta zamo alkhairi ga Manzon mu?�
Bashir bai taba tsayawa tambaya na ina son shi ko bana son shi? Abin da ya sani shine in har sai ya san wannnan za mu yi aure, ashe kuwa zamu mutu ba mu yi ba. Tunda dai ina bashi girma ina kuma tsananin jin kunyar sa, yasan alamun so kenan a wancan zamanin.
Ya samu Hakimi ya gaya mishi sati mai zuwa zamu tashi zuwa kasar Faransa in da zai fara aiki da ofishin jakadancin mu na kasar. A ranar da aka kira su Abuja aka danka mai takardun shi na daukar aiki shi da Hassan babban aminin shi da wasu abokan karatun su da dama.
Ya tsaya ne shirin ‘pass-port� da bisar mu ne ni da shi da Hajjo. Hakimi ya sa wa abun albarka, ya kuma kara dankawa Bashir amanar mu, yace ya ke tunawa a kullum bamu da kowa, Allah shine gatan mu sai ko shi, Basheer.
How much do you like this story?
5/8/22, 09:59 - Ummi Tandama😇: ______________________________
*âœðŸ? SIRADIN RAYUWAâœðŸ?*
Book two
*@Takori*
Page8ï¸âƒ£
Da ranar tafiyar mu tazo ni kam sabanin ‘ya’yan gata da ake rakasu da nasiha da Addu’a ni da zagi da gori da habaici ‘ya’yan Hakimi da matan shi suka raka ni wai mu mayu ne, mun lashe kurwar Bashir da ta Hakimi to su kurwarsu ta fi karfin kankarar mu. Hajjo yarinyace ba hankali ga maida martani inda duk aka tsokalo ta sai ta yi masu gwalo da zata shiga motar Hassan ta ce,
“Alalalo! Zamu shiga jirgi dai ba ke Inna Kwaire�.
Daga Bashir har Hassan dariya su ka yi, ni ko har muka zo Abuja kuka na ke na tunanin iyayen mu da batacciyar jaririya ta.
A filin jirgin saman Abuja muka kwana tsimayen jirgi mai zuwa France ana ta cike-ciken takardu, da asuba muka bi jirgi ‘direct� (kai tsaye) zuwa babban birnin Paris. Gidan da muka zauna yana nan a jerin gidajen ma’aikatan jakadanci na kasar.
Ba anguwa daya muke da Hassan ba don shi yana cikin gidajen ma’aikatarsu ne amma kullum ya taso aiki gidan mu zai yada zango su ci abincin rana tare da Bashir har dare.
Shakuwa mai tsanani ke shigar su shi da Hajjo. Da girman Hajjo da komi Bashir ya dauketa ya dankara a aji daya.
Hajjo ta sha tsiya wurin ‘ya’yan Faransawannan don tace mun har kungiya-kungiya suke yi zuwa kallon ta (katuwa a aji daya) ga wani sunan shakiyanci da suka lika mata (Mère) watau Mamar su kenan.
A rayuwata ban taba halartar makarantar boko ba, amma na yi karatun Addini mai yawa a wurin Baffan mu sanda ya ke da rai. Sai Bashir ya kashe muhimmin lokacin sa yana koyar da ni karatu da rubutu haka Hajjo komi ta koyo haka zata zo ta yi ta koya mun Bashir na aiki ya koma karo karatu (PhD) babbar Jami’ar Faransa yana kara zurfafa ilimin sa.
Shekara na zagayowa na haife ki Hidayah, asalin sunan ki Rahmah, sunan mahaifiyar Bashir ne kika ci, Hajjo ne ta sa maki Hidayah to sai muma din muka kama.
A shekarar Bashir ya halarci kwasa-kwasai da dama a kasashe daban-daban, da ta kai har a ka yi mai karin girma daga matsayin da ya ke da shi a wajen aikin su zuwa (Consultant) na kasar Nijeriya a Faransa.
Hassan bai taba furta mana son Hajjo yake ba har ta kare makaranta, kwazon ta da basirar ta yasa Bashir yayi cuku-cukun da ya nema mata aji biyu na karamar sakandire ta kuma lashe gwajin duk da suka yi mata tas. Sai da ta kai aji hudu a sakandire ne Hassan ya fito karara ya gaya mana shi fa kamun Hajjo ya ke.
Daga ni har Bashir mun yi matukar farin-ciki ko da yake dama tuni mun dago shi, bini-bini kaji shi yana “kanwata, me ya hada ki da wancan karmasashshen Bafaranshen? Ke fa yarinya ce har yanzu, baki isa yin abuta da maza ba. Babban farin-ciki na shine na kasancewar Hassan 100% ya cika kamilin mutum dan babban gida a jihar Borno, don mahaifin shi sanannen malamin Addini ne, duk da zaman shegiyar kasa irin France, ya canza wasu daga kyawawan dabi’un shi duk da hakan ni da Bashir ba mu ji ko dar na wanke Hajjo mu ba shi auren ta ba tun kamin kammala karatun ta na sakandire don mun san Hajjo na da wayo dole ta canza Hassan, barin ma yanzun da kanta ya bude da rayuwar turai.
Idan kin gan mu a lokacin zaki rantse bamu san wata aba miyar kuka da kalkashi ba don gabadaya sajewa muke da mutanen kasar, duka harshen mu ya juye da Faransanci zallah sai ma Bashir da ya ke baki shi ke tona mu, amma ko Hassan fari ne sol.
Ranar da nayi haihuwata ta uku a duniya wato ke Hunainah, ranar ne Bashir ya kammala Ph D din sa in da muka kara samun ‘promotion�. Mun dawo gida anyi gagarumin auren Hassan da Hajjo a garin Biu ta jihar Borno da Shanono ta jihar Kano, biki irin wanda ba’a taba yi a Shanono ba. Bashir Uban amarya kuma babban aminin ango an ba Naira kashi haka Hassan, sun nuna basu da abin so da kauna kamar kanwar su Hajjo.
To ni ma komawa na yi kamar sarauniya wurin matan Hakimi ko numfashi ji suke kaman su min. ‘Ya’ya na kuwa ko makota basa bari su dauke su wai kar su shafa masu datti, ni ko na balle bakin jaka na kara jike su da ‘yan yanzu, ai sai na kara zama kamar kwan da kaza ta nasa yanzu-yanzunnan, ko motsi nayi a ce “Hajiya Hadiza, me kike so?�
An sa Hajjo a lalle akayi sunan Baby, inda Bashir ya wanken dattin rai na ya mayar mun da sunan Innar mu (Hannatu), ke Hannatu Baban ki ke kiran ki Hunainah har yau din da ta bi ki. Bakar fatar Bashir da farar fata na ya mai da ku kalar coffee mai haske da har ake maku kallon ruwa-biyu, ya kuma sanya ‘nationality� din ku ‘in doubt� (cikin shakku) bayan a zahiri gaba da baya ku Fulfulde ne ziryan.
Da Hajjo ta kare sakandire suka zo Borno gaida Abban su Hassan da baya da lafiya, ai kuwa fir ya hana Hassan komawa aiki France kasancewar shi babba a gidan su kuma shi kadai ne da namiji. Duk kannin shi mata ne a gidan auren su ga tsufa mai wahala da ya kamashi.
To Hassan da Hajjo ke ma kin san takaici ba sai an fada ba wai an katse masu rayuwa. A nan Maiduguri Hassan ya sayi kankareren gida na garari suka tare, inda Hajjo aka rufe bakin mahaifa kif aka afka Unimaid inda ta ke karatun (linguistic) harshen Faransa da Barbarci ziryan. Daga baya ne aiki ya cilla su Lagos inda Hassan ke aiki da ma’aikatar ilmi ta kasa wato Federal Ministry of Education.
Shekarun ki Hidayah shidda, Hunainah biyar aka yi wa Baban ku Ambasada a kasar Russia, bamu dade ba aka canza shi zuwa Jordan inda a nan ne kuka kare firamare. Muna da shekaru uku a nan Allah ya yi wa Ambasadan kasar Nigeria a Saudiyyah rasuwa, aka sake yi mana (transfer) na wucin gadi zuwa Saudi-Arabia kafin a fidda sabon Ambassada, inda muka zauna a birnin Riyadh. Aka kai ku makarantar sakandire ta kwana.
Ba zan manta ba, ba kuma zan taba mancewa ba, a dan tsukin na yi ta mafarke-mafarken wai na ga jaririya ta da aka sace. Kuka zo hutun ku na farko a aji daya da kawar ku idan baku mantaba, yau shekaru biyar kenan da faruwar al’amarin da har yau yake damuna a rai domin na tabbata wallahi Fatimah diyata na gani�.
Hajiya Hadizah ta yi shiru hawaye na bulbular mata, jikin ta ya hau rawa. Hidayah da Hunainah, da suka yi jigum suna sauraron ta da dukkan hankalin su, suka juya suka dubi juna a gigice, cikin tsananin mamaki da ta’ajjibi mara misaltuwa suka hada baki, wanda su kan su basu san su yi ba suka ce
“Saratu Bello Makarfi???�
Dubawar nan da za su yi Mamarsu numfashi dai-dai ta ke fitar wa ba kuma ta ko iya shaida wanda ke kanta alamun hawan jinin ta ya tashi kenan. Hidayah ta fashe da kuka tace “Mamar mu don Allah kar ki mutu ki bar mu, Mamar in kin mutu ya za mu yi?�
Karamar wato Hunainah ita ta yi hankalin kiran mahaifin su, masu aikin gidan mata suka taimaka wurin sanya ta a mota aka nufi asibitin da suke zuwa da ita.
A daren nan Ambasada da yaran shi ba su rintsa ba, suka kwashe labarin data basu kaf suka gaya mishi, shi kansa ba karamin girgiza yayi ba yace idan yarinyar na makarantar ku ta Riyadh har yanzu, mai zai hana mu je mu neme ta? Idan har hakan zai dawon da farin-cikin Hadizah?
Kawanaki uku bayan nan jirgin safe ne ya sauke su a birnin Riyadh, garin da rabon su da shi shekaru biyar kenan cif. Motar musamman aka tura ma Ambasadan daga Saudi-Embassy ta kwashe su zuwa Kingston College.
Su Hidayah sun ga makarantar su ta da ta samu sauye-sauye ta fannoni da dama musamman ta fuskar cigaba, hatta ‘principal� din da suka sani a da ba ita bace yanzun an canza a an kawo wata daga Asia maimakon Ayyush Siddiky da suka sani mutuniyar Madina.
Ita bata san ma yarinyar da su ke nema ba ta dai hada su da wani tsohon malami, malamin shine Sayyid-Ridhwan mai kula da shige da ficen dalibai ya kuma dade yana aiki a nan. Ga abinda yace da su,
“ayya! Yarinya mai hazaka irin Sarah, ban san maiyasa iyayaenta suka katse mata karatu ba a shekararta ta karshe. Inda duk kuka ganta ku baiwa iyayenta shawara su maido mana ita koda basu da ko sisin kobo ne, domin Saratou ‘yar baiwa ce�.
Daga Ambasadan har ‘ya’yan shi ji suka yi kamar su daura hannu a ka su rafsa ihu, Hunainah bata san sanda hawaye ya ziraro mata ba tasa hannu ta share. Su kanyi tunanin kaunar da sukewa Saratu Bello, a sanda suke makaranta, sun dauka kauna ce kurum ta haduwar jini daga Indallahi, da kuma ‘kualities� na ita Saratun da ke sawa kowa ke sonta a (Kingston), to ashe Saratu jinin su ke gauraye dana juna shiyasa suke jinta har kasusuwa da bargon jikin su, barin yanzun kuma da suka ji wai ashe diyar Maman su ce?
Ba abinda ke damun su kamar lafiyar mahaifiyar su da ke ta walagigi, tayi-bata yi ba Allah masani. A gidan saukar bakin da aka yiwa ambasadan masauki cikin su ba wanda ya rintsa, kowanne abinda ya ke sakawa daban ne dana dan uwansa, zuciyar kowannen su cike take da alhini da taraddadi.
Hidayah dake kwance cikin kilishi tana kallon sama sai ta mike a gaggauce ta takarkare kamar gyare ta shiga jerawa ‘yar uwarta kira, duk ta rude sai rawa jikin ta yake kamar mazari.
A gigice uban da ‘yar suka sauko daga bene inda garin sauka Hunainah ta sulmiyo daga matakala ta biyar amma bata kula ba ta gyagije ta mike, don sun dauka wani mugun abu ne ya faru da ita, a tare suke tambayar ta “lafiya?� Tayi wata irin ajiyar zuciya kamar an ce ga Saratu a gaban su ta rungume ‘yar uwar ta tace “na tuna ne Daddy, Saratu ta taba gaya mana ita da iyayenta suna zaune ne a Lagos, kuma nan anguwar su Aunty Hajjo�
Hunainah
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 38