Share this page
yi shawara da matar shi tunda mahaifiyar shi bata da lafiya. An zauna da Ihsan a ranar wadda kanta ke sunkuye cikin abaya. Daddy ya shaida mata abinda kenan ya kuma danka mata komi na Alameen ya ce ya bar mata duniya da lahira ita da abinda zata Haifa, illa kason mahaifiyar shi da za a cire. Ihsan na hawaye tace ta amsa, amma itama ta barwa abinda zata haifan, bata son komi na Alameen domin bata taba tunanin ta ci gadon Alameen ba. Burin ta har kullum shine shi ya bizne ta. Don haka in an cire na Hajiyar Daddy ya cigaba da kulawa da jikarsa ko jikansa dukiyarshi a hannunshi. Alfarma daya take nema su yi mata shine Rehab yayi kokarin maido Meritime cikin Nigeria kamar yadda Alameen ya dade da wannan burin kuma har ya mutu da burin a zuciyar shi. Tace ya riga ya nemi iznin assasa asibitin daga federal ministry of health tun dawowar su, takardun komi suna nan a gidan su, tuni ginin yayi nisa, haka ko bayan rasuwar shi maaikatan basu daina ba, domin ya riga ya biya su kudin su. Tana so Rehab ya taimaka mata ya cigaba da jagorantar asibitin koda yana can Miami ne. Akwai karatu da zata karo na tsawon shekaru ukku kacal idan ta dawo zata cigaba da jagorantar Asibitin kamar yadda Alameen ke son yayi Allah bai bashi iko ba. Abinda zata haifa tana da burin in mace ne ko namiji? To zai yi karatu irin na Baban sa, ya jagoraci Meritime, tana fatan ko bayan ran ta Daddy ya taimaka mata wajen cikar barin ta, wanda Alameen ya dade da yiwa rayuwar sa amma rayuwar tayi mishi gaggawa. Rehab ya daga ido ta cikin farin mudubin idon sa ya dubeta. Yayi mamakin yadda cikin bakar fata aka samu irin wannan soyayya ta tsakani da Allah tsakanin mace da mijinta tamkar a kasar haihuwarshi (India). A da, ya dauki matan bakar fata a matsayin masu kwadayi da son abin duniya kadai; basu san mecece soyayya ta gaskiya ba. Amma a yau Ihsan Abubakar, ta shayar da shi mamaki. Ba shakka rayuwa ta kada Ihsan ta shigar da ita taitayin ta, ta yarda ita din ba komi bace face kyal-kyal banza, da zaka tafi ka barta ka shirya ko baka shirya ba. Ta zama mai tsoron Allah da gudun duniya abinda Alameen ya dade yana nusar da ita bata gane ba sai da ta faru a kanta. A karshen satin Faisal ya iso daga Lagos, sanye yake da kufta da wando na bakar lallausar shadda getzner. To tabbattaccen kamshinsa na (5,000 Doller) kadai daya gauraye ilahirin gidan ya sanar da mutanen gidan isowarsa as usual. Ya saya kwayar idanuwan shi cikin bakin dark glasses ta yadda baka iya ganin halin da kwayar idon shi ke ciki. Babu shakka mutuwar dan uwansa ta dokeshi inda duk ya dauki laifin ya daura akan baiwar Allah da bata ji-ba-bata gani ba, itama ta kanta ta ke Intisar. Inda abinda ya tsana da gani a rayuwarshi a yau to Saratu Intisar ce. Yana ganin ta as a wicked lover kuma har abada baya jin zai yafe mata. Baya ga tagayyara tashi zuciyar tare da daidaita farin cikinsa, ba kuma tare data kara waiwayar shi a rayuwarta ba don sanin shi din a mace yake ko a raye? Ta koma ga zuciyar dan uwan sa, ta illata ta gabadaya da ciwon da har abada bazai warke ba. Duk hakan bai ishe ta ba, sai da ta yi sandaiyyar danganar shi da karkashin kasa, inda baa dawowa. A yanzu kam ya na mai tantama da alamarin ta, tare da furucin da nahaifiyar su ta dade ta nayi a kanta na cewa, shin ko ita din, mayya ce? Ya samu Daddy zaune bisa kujera yana nazarin labarun da ake watsowa daga tashar CNN a akwatin talbijin din jikin bango (plasma) dake falon. Yar lelen na gefe rike da karamin Alkurani izfi sittin bugun Misra tana karantawa. Kallo daya ya yi mata ya kawar da kanshi haka itama, da ganin mugun ramar da kowannen su yayi. Zuciyar ta ne ya bata wani irin bugu, don sai ya zamo mata Alameen sak a ranar bankwanar su illa shi din yafi Alameen haske da kauri kadan. Tamkar bai taba sanin ta ba, bashi kuma da masaniyar kasancewar ta a wajen ya doshi Daddy suka gaisa, suka shiga hira ta abinda ya shafe su. Cikin karfin hali ta juyo tace ina wuni Ya Faisal? Da sauri ya amsa sabida dukan da zazzakar muryarta ta yiwa zuciyarsa, ba tare daya dubeta ba ya ce lafiya, yaya gida? Da haka ya maida hankalin shi kan zancen da suke da Daddy cewa ranar litinin zai tafi da Hajiya asibtin Meritime da ke Miami domin har zuwa lokacin babu wani cigaba akan alamarinta a asibitin kwakwalwa na Kaduna. A lokacin Daddy ya ji matukar kunyar dan nasa kan biris din da yayi da alamarin mahaifiyarsu, ko ya ta ke bai taba tambayar wani a cikinsu ba. Ya sadda kai ya ce kun yi maganar da Dr. Rehab ne? Ya ce Eh, shi da kansa mun je ya ganta, shi ya kawo shawarar mu tafi da ita can din in Allah ya yarda zasu yi iyaka kokarinsu. Daddy ya ce Allah ya taimaka, in akwai wani matsala sai kayi gaggawar sanar dani, ya ce babu wata matsala don shi Rehab din ne ya dau nauyin komi daga aljihunsa. Ta tashi ta bar masu falon cike da tukuki da kunar da zuciyar ta ta shiga yi kan irin wulakancin da Ya Faisal ya tsiri yi mata ba tun yau ba. A washegari takardun ta na karatu suka fito suka tadda Daddyn a ofis, sabida kyawun sakamakonta hade yake da gurbin karatu daga Jamioi har ukku sai wanda ta zaba. Jamiar (Ummul-Kura) da ke Madinah sun bata gurbi a fanning pure and applied chemistry yayin da (King Abdul-Aziz University) da ke Riyadh suka bata biochemistry inda (Al-Azhar) da ke Egypt suka bata (doctorate) gurbi a medicine and surgery. Duka cikin ukun nan babu na yarwa babu kuma wanda ba raayin ta ba. Don haka da Daddyn ya bata zabi tace ta bar mishi wuka da nama ya zaba mata wanda duk ya ga ya dace da ita. Ranar da Faisal ya daga da mahaifiyarsa kasar Amurka nema mata maganin tabin kwakwalwa data samu. Ranar ne itama ta daga Egypt tare da Najib da Hidayah da Daddyn ya wakilta suyi mata rakiya, bayan sun kammala duk wani shige da fice da ya kamata aka bata lokacin da zata fara shiga aji, wato daya ga watan Junairu na sabuwar shekara mai kamawa, kimanin watanni biyu kenan kamin lokacin. Sun hadu da Hunainah a can wadda tuni ta zama yar gari, don haka ita ta nuna musu garin suka ci shi. Najib da Hidayah kam wani sabon honey moon din aka bude. Yayinda ita kuma ke tare da Hunainah kodayaushe, tana koka mata rayuwar ta da ta ishe ta, komi bakikkirin take ganinsa, bata jin dadin komi. Ta gaya mata ita ta yanke rai da samun farin-ciki a rayuwarta, komi da ta ke yi tana yi ne cikin karfin hali da inganta Imani. Babban abin da ya dameta ya kuma kara dagula lissafinta da jin dadin ta shine gabar da Faisal ya daura da ita, ita ba yarinya ba ce, ta tabbata Faisal ya daura alhakin mutuwar dan uwansa da baya da kamar shi a duniya ne a wuyan ta. Ta ce cikin karyayyar zuciya da radadin zuci mara misaltuwa. “Hunainah a da na so Faisal, na so shi a cikin rashin sanin shi din ko me nene a gareni. Hakannan dai nike son shi sabida shi mai kyautayi ne da tausayi, kuma gwani wajen nuna kulawa da nuna kauna a gareni. To kin san zuciya an halicce ta ne a bisa kaunar mai kyautatawa a gareta, to hakan ne ya faru da ni a lokacin. Na so shi a sailin da ban san ma menene son ba, son shi nake, amma ban san son shin na ke ba, kawai na san ni mai tsananin kishi ce a kanshi ta yadda bana son ko da wasa in ji ko in ga wata mace ta rabe shi. Babu ranar da ta fiye min tashin hankali tamkar ranar da ya ke yi mun hirar budurwar sa Ronke Adeyemi. A ranar na tabbatarwa kaina ina son Faisal, so na soyayya a matsayin yana yayana da muke uba daya? Don haka na kalubalanci zuciyata na gargadeta da kakkausar murya a kan haramci da rashin dacewar abinda ta ke so! Haka na samu taimakon kiyayyar da mahaifiyarsu ke mun ya zagwanyar da 50% na soyayyar, kawai dai na bashi matsayin wani mutun precious a zuciyata (wato mai darajjah) kuma har yau, har gobe hakan ne ba abinda ya canza. Domin in har zan manta Faisal wanene a gare ni? To kuwa zan manta wane ne Daddy Makarfi. Yayi min dimbin alheri kwatankwacin na Daddy na, tun ban san kaina ba. Kawai na budi ido na gan shi tare dani, cikin karimci da ingantacciyar kulawa. Ko a sanda uwarsu ta yi min shamaki da su, na kuma alkawarta ma raina na rabu dasu har abada, na tambayi kaina a lokacin anya zan iya rabuwa da Faisal? Na bawa zuciyata amsa nan take da cewa, aah! Faisal wani mutum ne mai muhimmanci, kima da daraja a zuciyata da bazan taba iya rabuwa da shi ba. Haka lokacin da ya bar ni ba zato ba tsammani, na yi kuka nayi kewa na shiga kunci mara misaltuwa. A hankali na dinga sanyawa zuciyata salama tare da kokarin yakice shi a raina amma na kasa, sabida wata ingantacciyar kauna ce nake yi masa ta daban a zuciyata. A sailin ne kuma Alameen ya shigo cikin rayuwata. A lokacin da zuciyata ta rasa aboki, take cikin kadaici. Lokacin da nake mai tsananin bukatar taimako. Sai ya zo da wata irin soyayyah mai shiga rai ya shimfidata a zuciyata, irin wadda ban taba ji ba. Irin wadda ko a mafarki ban taba yin na tsintar kaina cikin ta ba. Soyayya ce irin wadda ko muryar sa na ji, sai na ji gabban jikina, zuciya zuwa kwakwalwata gabadaya sun amsa! Idan dosowa yayi inda na ke, babu inda baya girgiza da kadawa a jiki na. Na tambayi kaina ashe dai wannan itace soyyar ta hakika, waccan da nayi duk a cikin gigin kuruciya ne kuma sabo da shakuwa sune tubalan da suka ginata a birnin zuciyata. Wannan ita ce natural love kuma love at first sight wadda daya bazai iya rayuwa mai dadi ba tare da soyayyar dan uwansa ba, wadda kobo ko sisi ba zai iya sayen ta ba; saukakka ce daga indallahi! Kwatsam, kaddara da mutuwa suka yi mun yankan kauna, a lokacin da muke gab da cikar burin zuciyoyin mu. Duk da cewa ta wani bangaren zan iya cewa ni na jawo amma na amince kaddara gaba take da komi. Na ji ciwon rasa Alameen yadda harshena bazai iya furtawa ba, zuciyata bazata iya kwatantawa ba, ba don na yi imani da Allah da duk abinda ya saukar a gareni, mai dadi ne ko mara dadi? Da na tabbata babu abin da zai hana ni fita daga hankalina, sai dai komai ina dangantashi daga Allah ne. A duk sanda na tuna Alameen ina yi masa adduar neman rahma kuma na tabbata wannan ita ce kauna ta karshe da zan nuna masa. Ni kadai na san ciwon da zuciyar nan ke mun Hunainah, ni kadai na san kadaici da maraicin da nake jin ya sameni. Na dauka wannan ne lokacin da Faisal zai tausaya mun, ya waiwaye ni ya rungumeni, ya bani soyayyar da na rasa ta dan uwan sa mu debewa juna kewar Alameen, to amma abinda na fahimta shi a yanzu kiyayyar da yake mini da da hali, da ya koreni daga gidansu, da da hali, da ya dauki fansar dan uwansa a kaina. Yana gani na muguwa mayaudariya kuma maciyiya amanar soyayya. Na rasa yanda zanyi da zuciyata Hunainah, na rasa wanda zan fadi wa abinda ke damuna idan ba ke ba. Na san ke kadai kika san irin ciwon da nake ji ke kuma ce kawai zan iya gayamawa na ji sanyi a zuciyata Hunainah.� Hunainah kuka yar uwar ta Intisar ma kuka. An rasa mai rarrashin dan uwansa. Ita Hunainar da aka gayawa labarin don neman kwarin gwiwa da shawararta sai tafi victim din ma karaya da zub da hawaye. An rasa mai lallashin wani. Hakika tafi yar uwarta jin ciwon wahalolin da take fuskanta a rayuwarta. Tunda uwarsu ta haifeta kawo girmanta bata taba hutawa ba. Bata taba ganin mai SIRADI iri-iri a rayuwa irin Saratu-Inteesar ba. Daga wannan bakin-ciki ya gushe sai wannan ya bullo. Gaskiyarta ne tabbas ba don ta kasance yarinya mai karfin imani ba da ta fita a hankalinta. Kalaman Hunainah ga yar uwarta shine; “Ni na tabbata Ya Faisal na son ki. Wannan son da yake miki tun kina tsumman goyo ba abinda ya canza domin soyayya ta gaskiya bata taba gushewa kamar yadda bata tsufa, saidai masoyan su tsufa. Balle ku da yanzu nema kuke kan ganiyar kuruciyarku. Kawai dai zan iya cewa yana jin zafin ki wanda na san as time goes on zai daina ne, ki fidda damuwar komi a ranki, domin karatun ki bana wasa bane in bah aka ba zaki sha mamakin mugun kayen da zaa dinga yi miki. Ki bar komi a hannun Jallah mai kowa mai komai, wanda Ya halicci Faisal, Ya halicci Alameen, Ya halicci Inteesar ya sanya soyayyar juna a zukatan su. Ki bashi ikon zaba miki abinda ya san shi ne mafi alkhairi a rayuwarki.� Hakika nasihar yar uwarta ta nutsar mata da zuciya. Tayi damarar karfafa zuciyarta da kokarin yakice duk wata damuwa da ke damunta, tareda daura aniyar fuskantar karatun ta da dukkan iyawarta. Gabadaya daga Alameen har Faisal ta sanyasu cikin wani fai-fai na tarihin rayuwarta ta baya inda ta budewa kanta sabuwar rayuwar data tarar a gaba. Duk dai a lokacinne kuma tabi jirgi zuwa kasar Korea domin gano mahaifiyarta kamin lokacin da aka diba musu na fara karatun ya cika. Inda ita Hunainah hutu ne zata je na karshen semester wanda daga shi in ta koma zata shiga mataki na uku. Hidayah da maigidanta Najib sun koma gida Nigeria inda Hidayar zata fara karatu a jamiar Enugu inda mijin ta ke aiki kenan. Daddy ya zaba mata Al azhar dake Egypt ne sabida dadadden burin da ya dade dashi kan son Saratun ta zamo mai amfani ga dumbin alummah da fasahar da Allah Ya bata, wannan shine dalilinsa na zabar mata Medicine and Surgery. Hakika sun ji dadin hutunsu a Korea tareda mamarsu. Duk wani daddaurewa da takewa Inteesar a da, yanzu ta daina jan ta take a jiki fiye dasu Hunainah. Ita kadai tasan dimbin tausayin da yarinyar ke bata wanda ita din bazata iya maganta mata matsalolin da Allah Ya daura mata a rayuwarta ba. Gabadaya ta kare, sai tsayinta da farin kadai dama jikin ba wani jiki na azo a gani ba. Ta kan yi mata nasiha da ta kara dayanta Allah a alamuranta yana sane da ita, ba wai mancewa yayi da ita ba. Da sannu zata samu madawwamin farin-ciki a rayuwarta kamar kowa. Hakurin ta da kudurin ta na alkhairi a kan kowa, ba zai tashi a banza ba. A lokacin Haj. Hadiza cikin ta ya tsufa sosai, haihuwa yau ko gobe. Zahrah an sanyata a nursery tayi wayo sosai ba abinda bata cewa. Ta gaya musu Daddyn su Hunainah yayi retire suna jiran kwanakin da aka deba musu su cika su koma gida bakidaya. Su Inteesar sun ji dadin hakan sosai. Daya ga watan Junaiuru na sabuwar shekarar suka koma makaranta. Inteesar ta samu sauyin rayuwa ta fannnoni da dama, haka tsarin karatun Al-azhar yana burgeta komai cikin nutsuwa babu takurawa. Suka durfafi karatu babu kama hannun yaro, balle data fahimci abin na yi ne, mai wasa sai ya kwashi kashinsa a hannu sai ta kara dagewa tareda bada himma sosai. How much do you like this story? 5/14/22, 09:27 - Ummi Tandama😇: _____________________________ *✍� SIRADIN RAYUWA✍�* Book four *@Takori* Page6️⃣ Bayan Watanni Uku Lallai babu cutar da Allah ya saukar a doron kasa ba tare da ya saukar da ita tare da maganinta ba. A yau Hajiya Nafisatu Bello Makarfi, ke sauka daga matattakalar jirgin KLM cikin filin jiragen saman da ke garin Kaduna. Dr. Rehab Mohammed tare wasu daga likitocin asibitin meritime su biyu sune suka yo mata rakiya daga Birnin Miami da lafiyarta da hankalin ta sumul kalau, inda yayan ta Faisal da Nasir suka zo taryenta, kar kaso ka tona zuciyar su mai cikke da godiya ga sarki Allah da ya baiwa mahaifiyar su lafiyarta sumul kamar ba ita ce ta tafi bata san abinda take yi ba. Suka rungume juna daya bayan daya cike da kewa da farin ciki, a yayin ne wasu hawaye marassa dandano suka zubo mata. Ba komi ta tuna a lokacin ba face ranar da Alameen ya zo ya dauketa a air-port zuwa gidan iyayen ta ranar da ta dawo Dubai, kuma ranar da ta kasance ta karshe a tsakanin su. Ashe wani bakin cikin na nan yana jiran ta, shine rasuwar mahaifiyar ta Hajiya Iyami. A nan kuka ya zamo mata sabo. Yayan ta sunyi nufin tafiya da ita gidan mahaifinsu inda ita kuma ta nuna aah, suje su fara rokar mata gafararsa tukunna, bazata koma masa gida ba da yawunsa ba, kuma ta san har ga Allah ta zahince shi kwarai da gaske, in bai yafe mata ba ta san hakkin sa kadai bazai barta ba. Baa maganar hakkin Saratu da Saratu da ke kanta. Ta roke su su nema mata gafarar wadannan bayin Allah kafin ta zo da kanta neman gafarar su. Ta tabbata hakkinsu ke ta dawainiya da rayuwar ta. Komawarsu gida suka tadda labarin duk suna asibiti, Ihsan ce ke nakuda tun shekaran jiya haihawar ta zo da tangarda, daga karshe dole mahaifinta ya sa hannu aka shiga da ita dakin tiyata bakunan su cike da adduoin samun saa domin hakika ta jigata, duk wani mai imani dole ya tausaya mata. To alhamdullahi an yi nasarar fiddo jariri katoto da shi lafiyyaye. Daddy ya amshi Babe da niyyar yi mishi addua da lankaya mishi kalmar shahada amma sai zuciyarsa ta buga da karfin gaske! Yayi tazbihi ga Allah ya tsarkake shi a zuciyar sa, ya kara imani da buwayarsa da isar mulkinsa akan komi. Babu ko tantama wannan Alameen Bello ne yake rike da shi a sanda mahaifiyar shi ta haife shi. In kasan photocophy na Alameen to wannan jaririn ne. A take ya lankaya mai sunan shi cikin kunnuwan shi wato Alameen Alameen Bello. Sai dare aka fito da Ihsan zuwa dakin hutu, duk tayi wani fiyat ta zabge sabida wahala. A wannan dan tsukin ne kuma taga kauna da karimci daga lyaye da yan uwan Alameen irin wadda bata taba tsammanin zata samu ba. Ta tabbata ita yar gata ce amma Alameen ya fita gata gaba da baya, kuma kaunar da iyaye da yan uwan shi ke mishi, duk dimbin arzikin iyayenta ita bata samu koda kwatankwacin ta ba. Ashe ba dimbin arziki da dukiya ne gata ba, aah, matsayin da kake da shi a zuciyar iyaye da yan uwan ka. Har aka basu sallama suka dawo gida bata san kukan Baby Alameen ba, koyaushe yana jikin Aunty Saratu da kannen mahaifin sa, iyakacin ta da shi shan nono kadai. Gaba daya sun dauki kaunar duniya sun aza bisan Alameen karami musamman Faisal da Najib da shiga goma fita goma sai sun ce a kawo masu yayansu. Bayan sunan Alameen ne suka doshi Daddy da alfarmarsu na ya yafewa mahaifiyarsu kurakuranta, domin hakika tayi nadama mara iyaka. Daddy sai ya yi murmushin sa mai nufin alamura da dama kamar koyaushe zai yi wata magana mai muhimmanci. Ya ce, “In don ni ne ai ba abinda tayi mun, ban da kaunata da take da ku yayan ta. Wadanda ta zalinta kam suna can inda suke, don haka ta je na yafe mata duniya da lahira. Amma maganar wai ta dawo dakinta bata taso ba, domin mai hali baya fasa halin sa. A yanzu kam girma ya hau ni, ina bukatar hutu, bazan iya jurar tashin hankali ba. Don haka ku je ku tambayeta idan har ta shirya zama na amana da zuciya daya da duk wanda na kawo cikin gidan nan na ajiye, to ana maraba da ita. Idan kuma akasin haka ne a zuciyarta to don Allah ta nemi wani gidan don wallahi a yanzu bazan iya jure halinta ba! To bayan dogon kai ruwa rana da kyar da sidin goshi Aunty Saratu ta shawo kan Daddyn ya yarda da komen Hajiyar da babu shakka ta darastu da rayuwar duniya. Har kasa ta tsugunna neman gafarar Saratun tare da alkawarta mata tazo ne su yi zama na amana da aminci na har abada. Saratu ta tabbatar mata duniya da lahira ta yafe mata domin yayanta sun gama mata komi a rayuwa. Ta nemi Intisar domin neman gafarar ta, inda ake sanar da ita tana Alkahira tana karatu. ***** Bayan Shekara Daya Faisal Bello Makarfi ke taka matattakalar da zata sadashi da falon Daddy Makarfi cikin sassarfa, sanye cikin farar shirt product din DKNY da bakin wandon Tokyo da misalin karfe shidda na yammacin ranar Lahadi. Isowar shi kenan cikin garin, kamar kullum, a yau ma ya saya kwayar idanun shi cikin bakin gilashi domin boye halin da kwayar idon shi ke ciki. Ya yi sallama a babban falon kana ya jinkirta har ruwa sanda Daddyn yayi masa iznin shigowa. Zaune yake ya tasa allon computer (Laptop) a gabansa bisa tebir inda suke musayen sako da diyarshi Inteesar tana bashi labarin karatun su a makaranta. Ba tare da ya dauke hankalin shi daga computern ba ya amsa sallamarsa tare da nuna masa wajen zama daga gefen sa. Aunty Saratu ta shigo dauke da babbar warmer da kofunan shan ruwa ta aza daga can kan dining tana murmushi tace aah bakin Ikko ne sai yanzu, kai da tun jiya muke tsammanin ka. Ya ce wallahi kuwa shirye shiryen tafiyana ne ya tsaida ni, kin san babu biza mai wuya irin ta U.K. A sannan ne Daddy ya cira kai ya bishi da kallo na mamaki. Sannu a hankahi kuma cikin dan kankanin lokacin yayi nazarin wasu muhimman abubuwa da dama a tare da yaron. Ya sa hannu ya fidda mudubin idonsa ya kara duban Faisal sosai. Ta fahimci uban da dan na bukatar privacy domin tattauna matsalolinsu sai bata matsa da tambayar me zai je yi ba ta ce Allah ya shige mana gaba. Daga haka ta ba su waje. Daddy ya ce cikin wata murya mai kama da umarni. Faisal ina zaka je? Yayi dan dawurwura na dabarbarcewa da rashin kwakkwarar hujja ya ce am eh, Daddy, admission dana nema tun shekarar baya a can Birmingham domin karo Ph D dina, har na manta kawai sai shekaranjiya suka aiko min, to shine nazo in yi muku sallama, zan ta fi. Daddy ya ce Faisal, me ke damun ka? Kana kallon kan ka a mudubi kuwa? Tun bayan rasuwar Alameen na ke lura da kai babu cigaba a alamarinka, kullum kara lalacewa ka ke. Wannan ramar da kake tayi a kullum kamar kudin guzuri ta mece ce? Yaji idanuwan sa sun ciko taf da hawaye amma yayi kokarin maida su. Cikin jarumtaka yace Allah babu komi Daddy. Yace to kaima Faisal ko dan uwanka zaka bi ne ku barni ni daya? A wannan lokacin duk jarumtakarsa saida hawayen suka balle. Ya zare gilashin sa a lokacin ne Daddyn ya samu damar ganin yadda idanuwan sa suka fada sosai, baya ga kadawa da suka yi sukayi jawur kamar gauta. Ya ce, “Ina adduar Allah ya bani tsawo ran da zan kula da kai a gaba dayan ragowar rayuwar ka, kamar yadda ka sadaukar da kuruciyarka wajen kulawa, hidimar mu da tarbiyyantar da mu.� Ya ce, “In haka ne Faisal me yasa zaka bar ni? Me yasa baka son tsugunawa a waje daya? Yau kana can gobe kana nan kamar wani tsuntsu. Ka kasa tsayawa ka ginawa kanka rayuwa ta da namiji. Ba ka ko tunanin yin

Chapter 32 of 38