Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [7/9, 22:35] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     *SHAWWAL/JUNE.* ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_          ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *SADAUKARWA WA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 1📑* *__________📖* BARCELONA Duk yadda naso nayi bacci abin ya gagara, tsabar farin ciki tun lokacin sallan Asuba bai yiba na shiga toilet nayi wanka na ɗauro alwala, ina fitowa a parlon na kalli ɗakin yadda aka ƙawata mun shi, nika ɗai na naji na sake fashewa da dariya, murya a bayyane na furta. "Wayyo Daddy nah, ni a rayuwa mai zan maka na nuna maka irin farin cikin da ka sakani a rayuwata"? Na faɗa ina maida hannu na da kyau ina ƙara kankame towel ɗina. Sallaya na shimfiɗa nayi raka'atul fajir, na cigaba da jan carbi inata istighfari, har naji wayata tana sanar dani lokacin sallan Asubah tayi, don tunda zan kwanta Daddy ya karɓi wayana ya saka mun alerm. Tashi nayi nayi sallan Asubah sannan na zauna ina askhar, fuskana ɗauke da murmushi, ina gamawa na ɗauko qur'ani na na fara bitan karatu na, har saida gari ya fara haske tukun na miƙe na tafi gaban mirrow. Wata Red dogin riga na nasaka, wanda yayi bala'in fito da kyau na da ƙuruciyata, wanda banfi 16yrs ba, don banfi 5month da cikawa ba, dai-dai lokacin naji muryan Daddy yana ƙirana dai-dai da buga ƙofan da yakeyi. Da sauri naje na buɗe ƙofan ina dariya na ɗan sunkuyo dai-dai fuskan Daddy ina faɗin, "Good morning my dad," zaro ido Daddy yayi cikin mamaki yana kallona, a hankali yasa hannu akan haɓan shi yana cewa, "sweet heart har kin shiryah"? Dariya na fara yi ina kallon Daddy nace, "ae nayi 2hrs da shiryawa Daddy", sannnan na fito daga ɗakin na saka hannu na riƙe na Daddy mukayi hanyan parlon, inda cikin rawan kaina kaman zan koma cikin shi nace, "Daddy kasan daɗin dana ji kuwa? Daddy kullum zan ta maka addu'a Allah ya baka abinda kake so duniya da lahira", na faɗa ina duban fuskan Daddy da yake ta murmushi. Muna zama a kan dinning ya dube ni hannun shi riƙe da nawa yace, "sweet heart ni abinda nake so ɗaya zuwa biyu ne a wurinki, na farko ki maida hankali akan abinda ya kawoki kinji?, na biyu kuma ki riƙe mutuncin kanki saboda Allah kinji HUMMAIRAH nah". Jikinta duk yayi sanyi ta ƙurawa Babanta ido, kaman bazata yi magana ba, can kuma sai tace insha Allahi Daddy bazaka same ni da aikata wani mummunan abu ba, kodan ma....." sai kuma ta sunkuyar da kanta tana zubar da hawaye. Daddy runtse ido yayi kaman shima zai zubar da hawaye, yana girgiza kanshi, can ya dube yace, "komai zakiyi sweet heart kiyi shi saboda Allah bawai don kina gudun maganan mutane ba, shi zai ki gyara rayuwar ko ko babu idon kowa, kisaka wa ranki Allah yana kallonki kinji". Muna gama shan tea, Daddy ya sakani na fito muka fita har bakin titi, wanda tunda muka fito kallon unguwan da muke nakeyi, wanda yayi matuƙar ɗaukan hankalina, kaman Daddy ya san tunanin da nakeyi ya ƙara damƙe hannu na yace, "BOCABELLA, PASSATGE. sunan street ɗin da kike kenan sweet heart, ya miki kyau"? Murmushin da yake kan fuskana ne ya ƙara ƙaruwa, na damƙe hannun Daddy da ƙarfi kaman zanyi tsalle nace, "Daddy na gode wallahi wurin ya mun kyau, kuma insha Allah na maka alƙawari da first class zan dawo maka, bazan taɓa sakaka kaji kunya ba", na faɗa ina ƙara saurin tafiya ta yadda naga Daddy ma yanayi. Muna isowa kan titin saiga taxi ya tsaya, Daddy ne yace mishi *UNIVERSITY OF BARCELONA* da sauri na buɗe na shiga na zauna, munkai kusan 30mnt kafin muka isa school ɗin, jikina har wani rawa yake yi tsabar yadda naga school ɗin ya mun kyau. Da sauri na kalli Daddy ina ɗan murmushi nace, "Daddy schooƙ ɗin yayi kyau" shima murmushin kawai yayi ƴa tare mana wani bus da naga yana shiga cikin school ɗon da student, wani gini mai kyau naga mun tsaya, nidai kawai bin Daddy nake har muka shiga wani office mai girman gaske, wani bature ɗan luti mai katon tunbi nagani a zaune cikin wannan makeken office ɗin, fuskan shi ɗauke da murna da farin ciki ya taso ya miƙawa Daddy hannu suka gaisa, sannan ya miƙo mun hannu don mu gaisa, amma cikin murmushin da yaƙi barin fuskana, na haɗa hannu na guri ɗaya na matse su a cinyana ina ɗan jujjuya jikina, na amsa mishi gaisiwan shi batare dana miƙa hannu ba, shima dariyan ya ɗanyi yana buga kafaɗan Daddy cikin turancin shi mai daɗin sauraro ya ke cewa Daddy, "Nice doughter ɗin shin"?. Wuri Daddy ya zauna inda baturen ya nuna mishi, nima gefen Daddy na zauna kaman zan koma cikin shi, haka sukayi ta hira a ƙarshe naga ya ɗaga waya ya ƙira wata yarinya, tana shigowa nagan ta kaman zata ɓalle don rama, har inda yake ta ƙarisa ta gaishe shi, daga nan ya mata bayanin department ɗinmu ɗaya da ita, kuma nima doughter shine, saboda haka ta tafi dani har class ɗin da muke lectures. Hannu ta miƙo mun cikin sakin fuska, ban ɓata lokaci ba na miƙa mata muka gaisa inda tana riƙe da hannu na tace, "my name is *VICKY*, ina binta da murmushi nace mata, " *AISHA HUMMAIRAH*" cikin murmushi ta sake cewa, "nice name". Daddy sai binmu da murmushi yakeyi har muka fita, inda kafin mu fita na zo na rungume Daddy nace, "Daddy zaka jirani ne"? yana ɗan dariya ya ɗaura hannun shi a kafaɗa na yace, "zan koma gida akwai abinda zanyi, kina tashi ki nemi taxi ki bashi wannan card ɗin har gidan zasu kawo ki ko sweet heart", ya faɗa yana bina da kallo har muka fita. Muna kan hanya vicky take ta bani labarin yadda last week suka fara lectures, da kuma yadda tayi mamakin tana ganewa, domin ita tun a secondry babu abin da take so irin *ACCOUNTING* Nima murmushi nake binta da shi saboda yadda nake son course ɗin, kuma buri na kenan naga na karanta Accounting, don burina naga na zama chartart acoountant wata rana, har class muka isa vicky sai labarin daɗin course ɗin take bani, amma muna dai-dai da zamu shiga class ɗin take gaya mun wahalar wani course wai shi *FINANCIAL ACCOUNTING* amma ita tanaga tsoron lecturer suke ji shiyasa suke ganin kaman da wahala. Kallonta nayi cikin mamaki nace, "yana baku matsalah ne lecturer"? ɗan ya mutsa fuskanta tayi tana girgiza kanta tace, "no kawai baya dariya ne, kuma yana ɗaukan attendance, kawai dai baya dariya ko kaɗan". Haka muka shiga class ɗin, abin mamaki sai naga bamu fi mu 15 ba, cikin mamaki na dubi vicky nake tambaye ta "ina sauran ƴan class ɗin"? Tana murmushi tace mun mu 15 ne dama, amma kusan class uku ne ko wanne 15, sai lokacin exam zamu haɗu dasu a hall ɗaya. Muna zama bamu 5mnt ba sai ga wani lecturer ya shigo, kana ganin shi kaga ɗan gayu, gashi bayida wani tsayi amma sai wani bouncing yake yi, ƙasa-ƙasa vicky tace mun, "mr solomon, yana ɗaukan mu *COST ACCOUNTING* Ina jijjiga kai batare da na dube ta ba na maida hankalina kanshi, abin sha'awa duk da yau na fara shiga class ɗin amma na fahimci lectures ɗin mutumin yadda baku tsammani, inda yamana wani topic *BUDGET CONTROL* gaskiya na gane lecturers ɗin sosai, haka mikayi lectures huɗu a ranan, a ƙarshe mace ce ta shigo ta mana *TAXATION* india ce amma taji turanci na fitar hankali. har gate muka zo da vicky, inda na samu taxi har gida ya kawo ni, gaskiya na daɗe ina sha'awar kasar spain, inda yau Allah ya kawo ni ɗaya daga cikin state ɗinta, da farin ciki na shigo gidan, daga ɗaki Daddy ya fito yana ware mun hannu, da gudu naje na faɗa jikinshi. *Masoya novel ɗina wannan karon kumun uzuri ba zan dinga typing kullum ba, haka pages ɗina ba za suna yawa ba, nagode da ƙaunarku* *HAKA ZALIKA MRS ZERKS BAKI BAZAI IYA FURTA KALMAR GODIYA ZUWA GAREKI BA, NA BAKI KYAUTAR WANNAN SHAFI BESTY NAH, ALLAH YA BAR ƘAUNA* *©AUNTY NICE•* ✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:35] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_          ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 3📑* *__________📖* Girgizamata kai kawai nayi alamun babu wani dangantaka a tsakanin mu, wuri ta nema kusa dani ta zauna ƙasa-ƙasa tana gaya mun wai yanzu taji wani ɗan class ɗin mu yana cewa a tarihin Dr Hussain bai taɓa fita a class ya dawo ba, sunyi mamaki da sukaga ya dawo, shiyasa suke tunanin ko yasan ni ne. A hankali na dubeta sannan nace, "Vicky ban san shi ba, a school ɗin nan na fara ganin shi, kuma shima ina tunanin bai sanni ba, don na lura ko kallon fuskana bai yi ba, kawai may be yaga laifina na farko ne, shiyasa yamun uzuri". na faɗa ina kallon ta, ita ma girgiza kai tayi alamun magana na haka yake. Bayan mun dawo break ne muka yi lecture ɗaya sannan muka ta shi, Amal ta dube ni lokacin muna fita a school ɗin tace, "Hummy yaushe zamuje muyi shooping ne? Don gaskiya akwai abubuwan da nake son na ƙara"......kaman bazan yi magana ba saboda tunanin daya cika zuciya ta, har ta manta dani sai kuma na samu bakina da furta, "Mu bari ranan saturday sai muje wani mall dana gani kusa da inda nake, naga wurin yana da kyau da girma, ina ga zamu samu duk abinda muke buƙata a wurin". dafa kafaɗa na tayi muka tsaya dai-dai lokacin da ta tsayar mana da taxi, BAILEN, CARRER DE ta faɗawa mai taxi ɗin sunan unguwan da take, nima na gaya mishi inda nake, saboda ni nafita kusa da school ɗin, haka muka shiga har inda nake na sauƙa ita kuma ta wuce. Ina ƙarasowa gidan da nake wanda gida huɗu ne a compound ɗin gidan, wanda yake kusa danawa ban taɓa ganin an buɗe gidan ba, sai biyun da suke gaban namu suma wasu students ne a ciki amma dukan su maza ne, ina ƙarasowa wanda muke haɗe da shi naga yau alaman akwai mutane a gidan don ina zuwa kusa da wurin naji ƙamshin kaman ana soya ƙwai, har cikin zuciyata naji daɗi domin ina tunanin ko macece a gidan nima na samu wacce zatana tayani hira wani lokacin. Naso ace naga wanda take gidan amma har na shiga gida na ban ga kowa ba, ina shiga direct toilet na shige na ɗan watsa ruwa, riga dai-dai gwiwa na nasaka domin na samu sakewa na ɗan taɓa karatu, ina shiga kitchen naji nayi missing Daddy da yanzu har ya dafa mana abinci, amma yanzu gashi yunwa na keji kuma ina jin lalacin dafa komai, KunKumi na na riƙe ina hararan kitchen ɗin kaman shi ya haɗa ni da yunwan, zuwa can na juya na koma parlon na zauna akan dinning ina ta tunani. Kaman an zabure ni na miƙe na shige kitchen ɗin da sauri, egg guda uku na ɗauko na fasa na fara soyawa saboda na tuna ita ma neighbor nah ma shi naji tana soyawa, ni kaɗai na fara murmushi a zuciyata ina cewa Allah kasa macece a gidan. Bayan na gama na dawo parlor na sauƙa akan ƙwaina gefe ɗaya kuma na haɗa cornflakes ina sha, ko cin rabi banyi ba naji ana nocking ƙofa na, dariya naji ya ɗan suɓuce mun a fuskana, a zuciyata nace hala neighbor na taji na dawo shine ta zo duba ni, sai kawai nayi tsalle na miƙe, ko duba kayan jikina banyi ba saboda murna da ɗaukin zuwa ganin neighbor. Ina buɗe ƙofan sai naji da ƙaran buɗe ƙofan da bugawan zuciyata sunyi a lokaci ɗaya, da ƙarfi na rike ƙofan don kada na faɗi, idona kuma a zare kaman zasu zazzago ƙasa, kuma alokaci ɗaya naji na kasa rufe bakina dana buɗe zanyi magana. Haka zalika shima a gefen shi ba ƙaramin faɗuwar gaba da gigita yayi ba, domin bai taɓa tsammanin ganina ba, domin yayi tunanin namiji ne a gidan don last week kaman namiji yagani ya fito ya daɗe tsaye a ƙofan gidan, shi kuma tun ranan Allah bai nufa ya dawo gidan ba sai yau. Sake juya idon shi yayi yana Ƙara zuba mata ido kuma zuciyar shi tana harbawa kaman zata faɗo ƙasa, kaddai wannan yarinyar da yaji muryanta sak ina na *AISHA* ce a gaban shi, yarinyar da tunda yaji muryanta ɗaxu faɗuwar gaba yaƙi barin shi da wani irin mummunan tsoro a zuciyar shi, duk da ɗazu bai kalli fuskarta sosai ba, kawai muryanta da tsarin maganan ta babu maraba dana Aishan. saidai zuwa yanzu duk ta kunce mishi notinan kanshi daya ga hattah zaro idonta da ɗan bakinta data buɗe kaman na Aisha, kai shi idan ba karya yake so yayi wa zuciyar shi ba sai yaga hatta fuskan kaman na Aisha aka maka mata, sannnan kuma tsayin ta ma kaman na Aishan ne, ba zuciyar shi ba yau yana ji hatta huhunshi ma kaɗawa suke yi, yau wani irin gamu yayi? Shiyasa tunda tayi mishi magana yaƙi yabar kanshi ya dubi fuskanta ɗazu. "Dr mu kai...ne...a..nan...wurin?" Lokaci ɗaya ta samu kanta dayin in'inan da bata san ko tana yi ba ko yanzu ne ya zo mata. Shi dai bai ce mata komai ba sai kaɗuwan da zuciyar shi ta sake yi don jin yadda tace mi shi wai, "Dr mu". innalillahi ya furta a zuciyar shi, kaddai Aisha ce tazo har inda yake? Wato duniyan ƙaramar wuri ne ko? Duk inda kaje sai an tarar da kai? A hankali ya buɗe baki yana kallonta yace," *AISHA*" Zaro ido Humairah tayi da sauri tana duban shi cikin mamaki, sannan tace, "lahhh kaima Aisha kake son ƙirana da shi? Kasan kakana ne kawai suke ce mun Aisha, Daddy yace mun duk ranan da yace mun Aisha sai ya wuni bashi da lafiya, dama kasanni ne? Shiyasa ɗazu dana baka haƙuri sai kaima kamun uzuri a rayuwa ko? Don kasan laifin da mutum zai yi a farko yaka mata ana mishi uzuri, idan ya sake kuma sai ace gangancine ko kuma da son ran shi yayi, ta ƙarisa maganan tana mishi murmushi, wanda lokaci ɗaya yaji faɗuwar gaban shi ya ƙaru, wanda baisan ya dafa jikin bangon gidan da ƙarfi ya furta. "Aisha ya ya kike bina kuma a rayuwa ta, meye ya saura kuma? Bana ce......". sai kuma ya rufe bakin shi da hannun shi da ƙarfi, ya kifa kan shi a kan hannun shi ɗayan daya dafa bangon yana mai runtse idon shi, a hankali yana bawa kanshi haƙuri yana gayawa kan shi ba zai taɓa yiwuwa Aisha ta zauna yadda take kaman daba, bayan yanzu rabon shi da ita ya kai 18yrs, wannan da take gaban shi kuma bazata wuce 16yrs zuwa 17yrs ba. Ya kamata zuwa yanzu ace Aisha ta kai 35yrs, tunda shi dai yanzu yana 39 zuwa 40yrs. Sake ɗago idon shi yayi yana kallonta wanda ita ma zuwa lokacin ta fara tsorata da yanayin da taga ya shiga, tana bin shi da kallo cikin damuwa tace, "Dr mu baka da lafiya ne? Na baka paracetamol?". Juyawa yayi da sauri yayi hanyan gidan shi, duk illahirin jikin shi kuma yana rawa, wannan wani irin kamane tayi da Aisha hatta yanayin yarintar su da shagwaɓar su iri ɗaya ne, idan bai manta ba babu hali da ya zaina yayi shiru za kaji Aisha tana cewa, "na kawo maka paracetamol? Wato ɗabi'un suma ɗaya ne, to ko dai ita ce? A haka har ya wuce gidan shi ya rufe kanshi, sannan ya runtse idon shi bayan ya faɗa kan gadon shi. Humairah tana tsaye har saida ta daina ganin shi tukun ta koma nata parlon ta zauna, sai da ta daɗe idonta yana kallon abincin tana tunanin meye ya samu mutumin nan? Can taji kan ta ba zai ɗauki tunanin ba kawai sai ta share ta cigaba da cin abincinta. Har ranan friday Humaira bata sake ganin Dr ba a cikin compound ɗin su, ko alaman ana zama a gidan ba taga anayi ba, kawai sai tayi tunanin ko yana tafiya wurin familyn shine, don bata jin motsin mata ko yara a gidan, can kuma ta saka hannun ta da riƙe haɓanta kaman mai tunani zuwa can sai tayi dariya tace yes hakane ma tunanina dai-dai ne, wato matar shi da yaran shi suna wani gida, may be matar shi tana aiki a wani wurin ne shiya sa ya barta da yaran shi, shi kuma nan yafi kusa mishi da school ɗin da yake aiki, wataran ya zauna anan wataran ya koma wurinta, sai tayi tsalle ta jinjinawa kanta tana dariya irin tunaninta dai-dai yake. Ranan friday suna da Dr Hussain a 8:00 to 9:30, tun 7:30 suka shiga class, don duk ƴan class ɗin suna tsoron Dr Hussain, suna zama class reps ya tashi yace, "duk ku kashe wayoyin ku gudun abinda ya faru ran monday". kaman ance na bar wayana a kashe sai duk aka juya ana kallona, murguɗa musu baki nayi na juyar da kaina gefe, dai-dai lokacin da ya shigo class ɗin, sai kaji kaman babu sauran wasu halittu masu numfashi a class ɗin duk an ɗauke wuta. Yafi minti uku a tsaye yana duban books ɗin da suke hannun shi, ba tare da ya dubi kowa ba, can ya rufe ya fara musu lectures yana yi yana ɗan zaga class ɗin, wanda bai taɓa musu haka ba sai ranan, yana zuwa dai-dai inda Humairah take zaune ya tsaya ya cigaba da bayanin shi yana tsaye a wurin, can ya miƙa mata hannu alaman ta bashi abu. Duk sai taji ta ruɗe ta waiwaya ta dubi class ɗin taga kowa ita yake kallo, haka shima Dr idon shi yana kanta ya ƙura mata su, batare daya daina bayanin da yake mata ba, a hankali ta nuna mishi bata fahimci mai yake nufi ba, abinda bai taɓa yiba yayi shine ya saka hannu ya buɗe handbag ɗinta ya ɗauko wayanta ya duba yaga a kashe yake, amma duk da haka bai maida mata ba, sai kawai ya jefa a aljihun shi, ya wuce gaban class ɗin inda yake tsayuwa da. A haka yayi musu lecture har ya gama ya fita, kuma ko tunanin ya miƙa mata wayan bai yi ba kawai fitan shi yayi, ita ma ba tayi wani yunƙurin tashi ba ballantana ta nemi ya bata. yana fita Amal ta dube ta tace, "Hummy yaya baki karɓi phone ɗinki ba"? Juya ido tayi cikin yanga da yabi jikinta tace, "idan yana so zai bani ai, ba lallai sai na bishi ba". Amal ta sake cewa, "yaufa friday ne Hummy, kinga sai monday ne fa ya dawo class ɗinnan, zaki iya zama babu wayan?". "idan bai bani ba yaya zanyi Amal?". Kowa class ɗin da abinda yake faɗi, can uwar rawan kai ta taso jiki na rawa ta zo wurin su ta zauna tana cewa, "Humairah yaya me yake faruwa ne?". Humairah ta juya idon ta kaman mai jin bacci tace, "me yasa kuke damun kan ku ne?". Sai ta juya tana buɗe book ɗin da yake gaban ta ba tare data ce komai ba, ganin ba zata ce komai ba sai kowa ya ƙunshe guntun gulman shi yayi shiru, har wanda yake ɗaukan su Eng ltr ya shigo. Har na kai yamma banga alaman Dr a compound ɗin gidan mu ba, duk damuwata yau friday kada Daddy ya ƙirani yaji wayan a kashe ko kuma a hannun wani, nasan Daddy ba zai ji daɗi ba. Can nayi tunanin bari na leƙa ɗayan neighbor na da yake yawan gaishe ni idan zan fita na tambaye shi ya bani aron wayan shi, idan na ƙira phone ɗina naji a kashe, sai na kira Daddy nace mishi na manta wayan a school ne, ina fitowa na kusan cin karo da mutum a ƙofan shigowa gida na, sai dana razana ban san lokacin dana saka ihu ba na juya da gudu kaman wanda naga ƙadangare. Ido ya sake rutsewa yana tunawa wani yanayi kaman irin haka daya taɓa faruwa tsakanin shi da Aisha, ta fito daga kitchen shi kuma zai shiga kitchen suka haɗu, a take ta zunduma ihu ta juya da gudu har saida ƴan gidan suka fito ana tambayan lafiya? Shi dai kallon su ya keyi yana nuna ta da hannu akan su tambayeta shima bai san me ya saka ta ihun ba, duk kan su dariyan Aisha su keyi suna maganan tsoron ta, sai yaji hawaye ya cika mishi ido a ran shi yana cewa, _to ita wannan yarinyar wacece ita ne?_ Duk kamanin su da yanayin su iri ɗaya ne da Aisha, shi yau ina zaiga Aishan shi ya nuna mata mai irinta, amma ya saka wa ranshi yadda ya bar nonon uwar shi to ya bar Aisha har abada, sai yana jin wani hawaye mai zafin gaske wanda duk ranan da yayi wannan tunanin

Chapter 1 of 28