share hawayen idon Ummi.
"Hakane Aisha ta tabbata zata auri mohd kenan, ƙanin Aunty domin Baban Narabi auren ta kawai yake son ganin, kuma a irin halaccin da ya maku ya kwar da kanshi akan Aisha, ko na rana ɗaya bai taɓa nuna muku ko sa muku ido akan Asiha ba, ya kamata kuma ku daure ka bashi haɗin kai yaga auren Aisha da ran shi", Uncle Abdallah ya faɗa idon shi nakan Abba da Ummi.
Girgiza kai Abba yayi alamar maganan Uncle haka yake, sannan ya maida kallon shi kan Ummi yace, "Fatima naso ace kin haƙura da hukuncin Allah kin yarda an sanarwa Aisha cewa bake kika haifeta ba, idan yaso sai a haɗa aurenta da ɗaya daga cikin yaranki, kinga komai yazo mana da sauƙi, tuwo na maina, amma idan kika bari Aisha ta auri wani daban, tou daga ranan ta fita daga ikon mu, kuma ko ba daɗe ko ba jima zatasan bake kka haifeta ba", Abba ya faɗa da muryan rarrashin Ummi.
Girgiza kai Ummi ta keyi alamar a'a, bata samu daman buɗe bakinta tayi magana ba kawai muka ga Aisha a tsugunee a gefen Ummi, muryan ta cikin rauni tace, "Ummi idan bake kika haife ni ba waye ya haifeni? Ummi kigaya mun wacece ta haifeni bayanke?" tana jijjiga hannun ummi tana kuka.
Runtse idanun ta Ummi tayi da ƙarfi bata furta komai ba, har saida Aisha ta ƙara maimaita tambayanta babu adadi tukun Ummi tace, "Aisha nice nan na haife ki, bakiga kin fi su Hassan kama dani ba? ae nice na haife ki", ta faɗa tana miƙa hannu wa Aisha da nufin ta matso jikinta, amma sai mukaga Aisha ta miƙe ta tsaya, a hankali ta matsa kusa da Uncle Abdallah, hannu ta miƙa ta riƙo nashi, muryanta na rawa tace.
"Uncle duk duniya babu matar da nake so sama da Ummi na, amma cikin ƙasan zuciyata kuma babu abinda nake so dagani koji irin ka Uncle, kaida Baban Narabi ina jinku a raina fiye da tunanin wani mai tunani, wataran ina tunanin kaman nafi jin sonka sama da iyaye na", sai kuma tayi shiru tana sheshsheƙan kuka, a hankali ta cigaba da maganan ta.
"Uncle kaine ka haifeni ko? Don Allah uncle kace mun ehh kaine, don wallahi Yayah Hussain duk duniya nake jin zan iya aure na rayu cikin farin ciki da kwanciyar hankali", ta ƙarasa faɗi tana faɗawa jikin Uncle Abdallah.
Uncle Abdallah ma kukan yake yi bayan ya rungumeta, hala tun rasuwar Baba Umar yana jin bai sake kuka irin na yau ba, hannun ta ya jawo suka zauna, a hankali yafara warware mata komai, tun daga auren iyayenta har haihuwarta, har rasuwar Babanta, har zamanta hannun Ummi.
Tashi Aisha tayi fuskanta da murmushi da hawaye, ƙarasawa tayi jikin Ummi ta rungume ummi, sun daɗe a haka sai Asiha ta ɗago tanata murmushi ta dubi Ummi.
"lallai Ummi na ke ƴar aljannah ce, dubi irin son da kika mun kamar ke kika kawo ni duniya? Lallai Baba Umar yana kwance a kabarin shi hankali kwance don an nunawa gudan jinin shi kulawa, wallahi ban taɓa maraici ba kuma bazan taɓa ba, idan har ke Ummi da Abba kuna raye, kuma bazan taɓa kukan rashin Baba Umar ba, don kuɗin kune shi," tana murmushi ta sake riƙo hannun Ummi tace, "Ummi na kinsan daɗin da nakeji don naji ba ke kika haifeni ba kuwa"? ta faɗa fuskarta da tsananin fara'a, hakan yasa Ummi ta daina kukanta ta ƙura mata ido cike da mamakin maganan Aishan.
"Aisha akwai wani mummunan abu dana miki ne a riƙon dana miki har kike murnan bani na haife ke ba"? Ummi ta faɗa a razane, tashi Aisha tayi ta tsaya tana duban Aunty Hauwa tace, "Aunty duk duniya babu mai zuciyar imani irinki keda Ummi na, ke kika sadaukar dani gareta don ta samu kwanciyar hankali, ita kuma tayi riƙo da Amana ta riƙe tamkar ita ta haife ni, kuɗin iyayena ku ƴan aljannane, zumunci ku ba kowa zaiyi ba, naji daɗi zan auri Yayah Hussain ɗina, Ummi na ta ko ina zata zama mun uwa, bani da matsalan komai a rayuwata, yau zanje wurin Baban Narabi na rungume shi nace mishi ɗan tsohu mai ran ƙarfe", ta ƙarasa maganan cike da farin ciki a fuskarta.
"Aisha baki isa ki auri Hussain ba, ni nan ni zaki aura ko kin ƙi ko kinso, saboda ni nake sonki ba Hussain ba", Hassan ya faɗa yana matsuwa kusa da ita.
Da sauri Aisha ta matsa kusa dani, "Yayah Hussain ka gayawa yayah Hassan kana sona, kagaya mishi yau ya sani, don ni kai kaɗai nakeso a rayuwana, kuma bazan iya son kowa bayan kai ba", ta faɗa tana riƙo hannuna.
Hannu na saka na janye nata, ina duban ta cikin ido nace, "na taɓa cewa ina sonki? Ni har abada ke ƙanwata ce, amma Hassan shi yana sonki, saboda haka shi zaki aura, ni zan jira Fatima ce ta girma".
Ihun Aisha ne gaba ɗaya ya firgita kowa da yake parlourn, da guda Aisha ta faɗa jikin Ummi tana cewa, "Ummi ki basu umurni mana Ummi na, kice yayah Hussain shi zai aure ne, dole Yayah Hassan yayi haƙuri, ni ba shi nake so ba", bata jira me Ummi zata ce ta tashi taje da gudu ta rungume Aunty hauwa, murya da ƙarfi tace, "mamie nah!".
Runtse ido Aunty hauwa tayi, don Aisha bata taɓa furta mata mamie na ba, kullum Aunty hauwa ta ke ƙiranta, "mamie na kice musu ni yayah Hussain nake so, yayah Hassan yayi haƙuri", ta faɗa tana ƙanƙame jikin Aunty hauwa.
Duban kowa Hassan ya tsaya yanayi, chan yace, "naga wanda zai aura miki Hissain ɗin bayan ni nake sonki, wallahi saidai kowa ya rasa daga ni har Hussain ɗin, idan yaso a bayar da ke wa ɗan'uwan kin chan kowa ya rasa a nan", ya faɗa cike da ɓacin rai.
Abba ne ya saka kowa ya nemi wuri ya zauna, haka yayita ƙoƙarin kwantar mana da hankali, nidai na danne duk wani abu da nakeji game da Aisha a zuciyata, domin ina son farin cikin mahaifiyata da ɗan'uwa na, amma narasa mai yasa Hassan ya kasa fahimtar komai, kodan shine *ƘADDARAN DA YA RIGA FATA* akanmu?
A lokacin Ummi ta nunawa kowa abinda taji tsoro ya faru a tsakanin mu, muryah a raunane tace, "na daɗe da sanin Allah ya saka ƙauna mai girman gaske a zuciyar ƴaƴana akan Aisha, tou su ƴan biyu ne, wa zan zaɓa wa Aisha wa zan bari? Don Allah ku fahimceni, nasan Hussain da irin haƙurin shi, duk irin son da yakeyiwa Aisha zai iya haƙura wa ɗan'uwan shi, amma kuma an shiga hakkin shi, don tun tana baby yake ce mun wannan ne wife ɗina idan muka girma ko? Tou Hassan kuma nasan halin shi ko na rana ɗaya bazai taɓa haƙurawa ɗan'uwan shi ba, kunga kuma Aisha ita hankalinta nakan Hussain ne, ta yayah zaman su da Hassan zai kawo mana farin ciki? Saboda haka nabar mu wuƙa da nama ku warware komai", sannan ta dawo da kanta kan Aunty hauwa tace.
"Hauwa kinga dalili na tun farko ko? Bawai bana son mu haɗa ƴaƴanmu aure bane, kawai ina son kwanciyar hankalin Aisha ne fiye da komai, don idan ba tare da Hussain ba bazata taɓa samun nutsuwa ba, shi kuma Hassan ba zai taɓa bamu haɗin kai ba", Ummi ta faɗa tana share hawayenta.
Murmushi Uncle Abdallah yayi sannan ya gyara zaman shi yana fuskantar kowa, "tou ae ina ganin daga Hassan har Hussain mu muka haife su, basu suka haife mu ba, inaga tou babu wanda yafi ƙarfin mu a cikin su, yadda Hussain zai iya haƙuri da farin cikin shi don ɗan'uwan shi ya samu, tou me yasa shi Hassan ɗin bazai iya yiba? Ita fa Aisha ta riga da ta raba gardama, ta nuna Hussain shi ta aminta dashi, tou mai zai hana bazamu bata shiba? Shi kuma Hassan sai yaci girma ya haƙura, Allah zai bashi wacce tafi Aishan idan yayi haƙuri".
"Bazan taɓa haƙura da abinda nake so ba, dole ne ma a bani Aisha ko kuma dukkan mu a hana kowa, amma bazai yiwu dukkan mu ku kuka haife mu ba amma zuciyar ku kullum sai tayita karkata kan ɗaya, don nafi kowa sanin dukkanku kunfi son Hussain akaina, shiyasa kuka nunawa Aisha son shi tun tana ƙarama, dama da niyyyanku akan shi shikaɗai ko"? ya faɗa yana hararan inda nake.
Tsawa Abba ya daka mishi, muryah a hargitse Abba yace, "na rantse da Allah Hassan babu mai baka Aisha, kuma idan ni na haife ku gobe zamu tafi wurin Baban Narabi a ɗaura auren Hussain da Aisha, domin mu muka haife ka bakai ka haife mu ba, kuma Hissain yafi dattaku da kamala, yafi ka chanchanta da auren Aisha, idan ya maka zafi ka gyara halinka, saboda haka kowa ya tashi ya bani wuri, kuma ku kwana da shirin tafiya Narabi gobe idan Allah ya kaimu da rai da lafiya".
Duk parlourn babu wanda bai razana da ɓacin ran da Abba ya shiga ba, domin shi mutum ne mai haƙuri da kawaici, daga gani Hassan ya kure shi ne, shiyasa yayi wannan masifan, ganin haka kowa ya tashi yabar musu parlourn, kowa jiki a sanyaye, na miƙe zan tafi Abba yace, "Hussain kaida Abdallah ku tsaya."
Duk jikina rawa yake yi, ina tsugune dai-dai ƙafan Ummi, chan naji muryan Abba yana faɗin, "Hussain nasan kai mai haƙuri ne da ƙoƙarin nuna kulawa akan damuwan naka, wanda Hassan yakasa koyi da halinka, kuma a jikina inajin ko bayan raina kaine zaka tsaya mun akan gidan nan, Hussain na baka auren ƴata Aisha, ina son ka riƙe ta da amana tsakanin ka da Allah, kuma bana son kayi gaba da Hassan, don nasan tabbasa sai ya nuna maka, amma kaja girmanka, kuma ku kula da kwanciyar hankalin mahaifiyar ku don bata da Lafiya kada a ɗaga mata hankali da fitina kaji? Jeka Allah yayi muku Albarka".
Ummi hannu ta saka tana shafa kaina, amma bata iya cewa komai ba, sai hawayen dana lura yana ta bin fuskanta, kiss na mata a forehead ɗinta sannan na miƙe na bar su a parlourn.
Da asuba na tashi na shiga toilet nayi wanka nayi alwala na fito nayi raka'atul fajir, naiƙe zan fita zuwa mosque domin yin sallan asuba, kawai wani irin mummunan ihun Ummi na naji har cikin ƙwaƙwalwar kaina, da gudu na fita nayi hanyar side ɗin Ummi, ina zuwa daidai parlourn ta naga Aunty hauwa ma da Uncle Abdallah da Daddy da sauri sun ƙaraso bakin ƙofan ɗakin Aisha, inda a kasan wurin muka ga Ummi ta faɗi kaman wata gawa, da sauri Abba yayi kanta shida Aunty hauwa, ni kuma nida Uncle Abdallah muka leƙa ɗakin Aisha da yake ƙofan a buɗe.
Wani mummunar faɗuwa gaba naji wanda tunda na zo duniya ban taɓa ji ba, wani irin jirine naji yana shirin kaini ƙasa, badon komai ba sai don ganin Aisha ƙanwata, rabin raina kwance gaba ɗaya jini na malalae a jikinta, ban tashi fahimtan komai ba kawai naji ni na zuɓe ƙasa, babu abinda na kara ji sai ihun Aunty hauwa itama tana faɗowa kaina".
Dr Hussain yana kawuwa nan ya sunkuyar da kanshi yana zubar da hawaye mai masifan yawan gaske, duk illahirin jikin shi rawa, yana wani kuka ko mace albarka, murya a bayyane yana cewa, "shikenan Aishan mu, Allah sarki Aishan mu".
Hummy ganin yanayin da Dr ya shiga ya sakani tafiya inda yake da sauri na rungume kanshi ina kuka nace, "Mutuwa tayi? Aishan dama ta mutune baby? Wayyo baby na kayi shiru don Allah, ina su Ummi"? Na faɗa ina ƙara rungume shi a jikina, shi kuma baiƙi ba ya manna kan shi a ƙirjina yana kuka mai sautin gaske.
Gaba ɗaya su Abbi kukan suke shi da su Ummi, faisal ma kuka ya keyi kaman mace, Amaal kuma zuwa tayi ta rungume Ummi tana nata kukan.
Jijjiga kai Daddy yake tayi yana faɗin "wannan shine ikon Allah, wannan duniya ƙaramar wurine, ikon Allah humaira wani ƙaddaran ne yake shirin maimaita kanshi kuma, yau kuma mai nake sake ji da gani a rayuwata?" yana kuka ya ƙarasa wurin Dr Hussain ya ɗaga shi daga jikin Hummy, duban irin yadda idon Dr ya koma ya saka shi jawo jikin shi ya rungume shi ƙam a jijinshi yana kuka yana bubbuga bayan Dr.
Ni Aunty nice juyawa nayi na dubi miss xerks da ta wangale baki tana shaftara kuka kaman ance mata yau za' a mata auren dole da Hassan nace, "besty zo mu koma nigeria muyi kukan sai mudawo gobe idan Allah ya kaimu muji me yake faruwa ne? Hala ma mum sayyeed da jikar kulu suna ta vibration dom suji me yake wakana, haka muka fita sum sum sum mu ka bar su suna kukan su.
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[9/9, 21:42] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 46📑*
*__________📖* Uncle Abdallah kuma da Abba ganin nida su Ummi duk mun suma a wurin sai sukaji hankalinsu yayi matuƙar tashi, jiki na ɓari Abba ya ƙira number Dr su, shi kuma Uncle Abdallah yadda kasan tsohon soja haka jikin shi yake rawa, daga ya dubi Aisha sai yaji kaman yayi ta ihu don tsananin tausayinta da shiga tashin hankali, a zuciyar shi kuma yana ayyana duk wanda yake da hannu a cikin raping ɗin Aisha da akayi wallahi bazai barshi ya sarara ba.
Dr su biyu suka zo, da yake Daddy ya gaya mishi case ɗin da yawa, zuwan su gaba ɗaya suka fara aikin ceto rayuwar mu, babu ɓata lokaci nida Aunty hauwa muka farfaɗo, amma Ummi dole suka ɗauketa akayi mota da ita, muna tashi daga ni har Aunty hauwa da gudu mukayi wurin Aisha, zuwa lokacin naga an rufe mata jikinta da bedsheet, ba kaman zuwan mu tana kwance haihuwar uwarta ba, rungumeta Aunty hauwa tayi tana kuka kamar ranta zai fita, nima haka na haɗasu na rungume ina tayata kukan, da ƙyar Uncle Abdallah ya sa muka sake ta, shi ya ɗauketa mukayi hanyar zuwa asibitin Dr Basheer, wato *CITY CLINIC* da yake wannan asibitin su Ummi suke zuwa, muna zuwa asalin babban likitan wato Dr Basheer yayi kan Aisha shi da wasu nurses guda 2, ita kuma Ummi ɗayan Dr sani ya rufu akanta.
Ni dai ranan na koma kaman mace, kafaɗan Aunty hauwa kawai na kwantar da kai na sai kuka muke ta rerawa nida ita, daga Abba har Uncle Abdallah kallon mu sukeyi ba tare da sun iya furta komai ba, gaba ɗaya kansu suke ji ya kulle, waye zai shigo har cikin gidan ya iya wucewa har ɗakin Aisha yayi mata wannan mummunan illar ba'a ganshi ba? Gaskiya abun yayi matuƙar ɗaure musu kai, kawai sunyi shiru ne suna jiran farfaɗowar Aisha da Ummi ne kawai, sai su shiga bincike.
Ummi bata daɗe ba ta farfaɗo, amma Aisha sai da tayi rabin awa tukun ta farfaɗo, hakan ma tana farfaɗowa suka mata alluran kashe zafi don su samu su mata ɗinkin wurin, domin ba ƙaramin jin ciwo tayi ba, bayan an gama komai su Abba suka bi Dr basheer har cikin office ɗin shi, inda yayi musu bayanin BPn Ummi yayi mummunan hawa, ya kamata a kiyaye abinda zai dinga tayar musu hankali, sannan case ɗin Aisha kuma yayi musu jajen abinda ya faru, sannan ya ce su neme police a cikin case ɗin, don ma abinda ya kamata suyi ne tun farko, wato saida police tukun ya karɓi Aisha, a haka muka wuce zuwa ɗakin da Ummi take kwance idonta a rufe kaman mai bacci, amma kuma ba baccin ta keji ba, kawai tana sauraren kukan da Aunty Hauwa ta keyi ne, wanda ta kejin shi kaman zai fasa mata heart ɗinta.
Gefen Aunty hauwa Uncle Abdallah ya zauna yana ta rarrashinta, yana kuma roƙonta da ta je wurin Aishan ta zauna da ita, shi kuma Abba zuwa yayi ya riƙe hannun Ummi, wanda tana jin zuwan shi inda ta ke ta buɗe idon ta a hankali , ƙurawa Abba ido tayi nata idon ma ya fara zubar da hawaye.
"kiyi haƙuri Fatima, insha Allahu yanzu zamuje mu miƙawa police case ɗin, kuma ina da tabbacin zasu gano wanda ya shiga har gidan ya aikata wannan mummunan aikin wa Doughter, insha Allahu zamu bi mata hakkin ta", Abba ya faɗa yana jijjiga kan shi alaman abinda yake faɗa babu fashi, hannu Ummi ta miƙo mishi ya ɗaga ta, zama tayi fuskanta ɗauke da wani irin ƙunci, amma sai da tayi ɗan murmushi kaɗan, ido ta ƙurawa Aunty hauwa na zuwa wani lokaci, sannan ta dawo da kallonta kaina da nake tsaye a bakin ƙofan ɗakin tun shigowan mu ina kuka a tsaye a wurin, sannan ta karkaɗa kanta, ta dawo da kallonta kan Abba, hannuta ta ɗaga ta ɗaura a kan saitin zuciyarta, "Abba wani police zaku nema akan wanda yayi fyaɗe wa ƴata? Bayan wanda ya aikata yana cikin gidan da kuke?" runtse ido ta sakeyi hawaye yana zuba a fuskanta da gudun gaske.
Da sauri Abba ya dubeta yace, "ban gane me kike faɗa ba Fatima? Kina nufin kinga shigowan wani ne cikin gidan, ko kuma me kike nufi"? Ya faɗa gaba ɗaya hankalin shi a tashe.
"Abban su kana tunanin akwai wani daban da zai aikata wannan mummunan aikin bayan ɗanmu Hassan? Tabbas Hassan shi ne yau ya saka hawaye mai zafi da ƙunan xuciyar da bamu san ranan ƙarshen shi ba a rayuwar mu, Hassan yau shi yasaka na kejin kunyar duban idon Abdallah da Hauwa, yake sani jin da wani idon zan dubi Baban Narabi, yayah zanji ranan da Allah ya haɗani da Baba Umar yaji irin saken da nayi na riƙon amanan da ya bani?" kuka Ummi ta saka mai ƙarfin gaske, wanda daga ni har Aunty hauwa ma kukan mu keyi, jiki na rawa Abba ya sake buɗe baki yace.
"Fatima ban fahimci me kike nufi ba, shin kinga Hassan ya shiga ɗakin ta ne? Don Allah ki fahimtar dani Fatima, komai ya kulle mun", ya faɗa kaman shima raunin shi zai saka shi zubar da hawayen.
Juyawa Ummi tayi ta dubi kowa da yake cikin ɗakin, sannan ta dubi Abba tace, "gamu nan dukkan mu a hallare a ɗakin, shi kaga Hassan a cikin mu? Baka tunanin mai ya hana shi zuwa inda muke? Wallahi jikina ya bani Hassan ne ya aikata wannan mummunan illar wa rayuwar Aisha, domin yayi katanga wa ɗan'uwan shi na auren Aisha, shi kuma a bashi aurenta, kuma nayi alƙawari idan har nono na Hassan ya sha tou na haramta mishi auren Aisha har abada".
Waya da sauri Abba ya ɗauko ya shiga dialing number Hassan, wanda dukka layin shin a rufe suke, haka Abba ya ajiye wayan shi jiki a sanyaye, ɗago idon shi yayi ya dubi uncle Abdallah yace, "muje mu miƙa case ɗin zargin Hassan da mukeyi a wurin police" Abba ya faɗa jikin shi yana ta rawa, wani zufah mai azaban zafi yana karyo mishi.
Murmushi Uncle Abdallah yayi ya matsar da Aunty hauwa dake lafe a jikinshi ya ƙaraso inda Abba yake, hannu ya dafa a kafaɗan shi yace, "haba Yayah! Kana ganin ni da kaina zan iya shari'a da ɗana ne akan ƴata? Wallahi Allah ya sauwaƙa, nasan koda Baba Umar yana raye bayida abinda zaiyi sama da addu'a da haƙuri, ae Hassan ɗan mune, kuma idan ba rashin godiyar Allah irin namu ba, ta yayah zamuyi shari'a da kai? Don kuwa yin shari'a da Hassan tamkar da kai mukayi, wannan abun mun ɗauke shi a ƙaddaran rayuwar Aisha, kuma wannan shine *ƘADDARA TA RIGA FATA* munyi fatan haɗa aure tsakanin Hussain da Aisha, amma ƙaddaran da ta gifta tsakanin Hassan da Aisha ta saka dole mu haƙura mubar Hassan ya auri Aisha, mudai fatan mu Allah ya bata sauƙi, don ni tun ganin Aisha ban zargi kowa ba sai Hassan, saboda irin kalaman shi da yayi tayi a daren jiya, dama duk hankalina bai kwanta ba, Allah-Allah nake gari ya waye muje Narabi akan maganan auren Hussain da Aisha, toh amma ga abinda Allah ya aiko mana, dole muyi haƙuri".
"Idan kai kanaga ka haƙura tou ni ban haƙura ba, dole sai nayi shari'a da Hassan, kuma babu abinda zai hana auren Aisha da Hussain, don abinda yayi bai isa yasa mu chanja ra'ayin mu ba, nayi rantsuwa koda mazan duniya sun ƙare tou har abada Aisha bazata taɓa auren Hassan ba, sharrin shi ya koma kanshi", Abba ya faɗa yana miƙewa don tafiya wurin police.
Uncle ne ya ɗauki waya ya ƙira Baban Narabi, a handsfree ya saka, sannan yayi sallama ya gaida Baban, murya a raunane ya shiga zayyanawa Baban abinda yake faruwa, a ɗaya ɓangaren kuma sai, "innalillahi wa'innah ilahir raji'un" Baba yake ta maimaitawa, bayan Uncle ya gama gayawa Baban komai, sai Baban yace ya bashi Abba, nan Uncle ya gaya mishi wayar tana handsfree kowa yana jin shi, gyaran murya Baba yayi sannan yace.
"Gambo! Wallahi kaji Allah ɗaya yake ko? Toh idan ka fitar da wannan magana waje har wani daban ma yaji, toh ban yafe maka ba duniya da lahira, daga kai har Fatima sai nayi shari'a daku agaban ubangiji, kuma ban yafewa duk wanda yayi mummunan furuci wa Hassan ba tsakanin kai da Fatima ba, mu ƴan halal ne ba butulu ba, munyi imani da ƙaddara mai kyau da marar kyau, shin idan ɓarawo ne ya shigo gidan yayi mata haka yayah zakuji? Hassan fa mun sanshi mun san kuma shaiɗan ne yafi ƙarfin zuciyar shi ya saka ya aikata mata haka bawai don halin shi bane, saboda haka kubar maganan mun yafe duniya da lahira, kuma Aisha tana gama istibira'i za a yi auren su da Hassan ɗin", Baban Narabi ya ƙarasa maganan cikin dakiyar zuciya, ina jin su nayi sauri na runtse ido na, amma jin muryan Ummi da maganan da ta keyi cikin kuka ya saka ni buɗe ido na ƙura mata shi.
"Baba don Allah kayi mun rai, wallahi Hassan idan ya auri Aisha bazan rayuwa ba, duk ranan da aka aira mishi Aisha ranan ni kuma zan koma ga ubangiji na, Baba Hussain na amince ya auri Aisha, idan muka bawa Hassan zai ga kaman yayi nasara ne akanmu, kuma Hassan bayi da halin kirkin da zai riƙe mun ɗiyata cikin mutunci, tunda baiji tausayinta ba ya aikata mata haka, baiji tausayin wani hali mu iyayen shi da ɗan'uwan shi zamu ji ba ya aikata mana wannan mummunan aikin ba, toh bazai samu abinda yake so ba cikin sauƙi, Baba tunda kace baka yafe ba idan munyi shari'a da shi ba ko kuma muka bishi da mummunan fata ba, tou Baba muma kamana adalci mu samu sauƙi a zuciyar mu, ka amince babu aure tsakanin Aisha da Hassan har abada", Ummi ta ƙarashe tana fashewa da kukan da ban taɓa gani tayi irin shi ba.
Da gudu Aunty hauwa ta ƙarisa jikinta ta rungume ta ƙam a jikinta itama tana kukan gaske, murmushi Baban Narabi yayi cikin ƙarfin hali yace, "naji Fatima Allah ya muku albarka, ya baku haƙurin jure wannan babban damuwan a zuciyar ku, na amince kubawa shi Hussain ɗin idan bazai damu ba", sannan ya musu sallama ya ajiye wayan.
Aisha ba ita ta samu kanta ba sai da tayi sati biyu a asibitin, bayan an sallame mu mun koma gida ne, sai uncle Auwal ya zo tare da Hassan wanda gaba ɗaya duk yabi ya lalace, duk yadda uncle auwal yayi Ummi ta daina kuka da ta ga Hassan amma kasawa tayi, dole saida Mama tazo daga Misau suka haɗu akayita kwantar mata da hankali, da ƙyar ta amince shima da sharaɗin ba zai sake shigo mata side ɗinta ba, hakan ba yadda aka so aka amince, ita kuma Aunty hauwa bayan sati ɗaya suka wuce da uncle Abdallah, haka gidan ya dawo shiru babu daɗi, nine ma dole nake
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 28