Share this page
year ɗin sai ayi, domin da iyayenta sun fi son sai ta gama karatun haba ɗaya, amma haka aka tsayar da magana nan da 5month. Ko wani ƙarshen wata sai Baba Umar yazo mata hira har bauchi, toh ganin irin rawan kan da yakeyi ne ya tunzura matar shi ta fara buri, wanda har gidan mu taje tayiwa Ummi kacha-kacha, Ummi ko kaɗan Ummi bata mayar mata magana marar daɗi ba, sai haƙuri kawai da take bata. December Ummi suka tafi misau domin saura 1week bikin su Aunty Hauwa, daɗi nida Hassan mukeji, domin zamuje misau muci masan gidan sarkin dabji, sai murna mukeyi. Ranan thursday Aunty Hauwa tayi walima a cikin fadan sarkin misau, a cikin wani hall mai suna *GWANI MUKHTAR* waliman yayi matuƙar armashi inda malamai mata kusan kala uku sukayi wa'azi, ranan friday 2:300pm aka ɗaura auren Aunty Hauwa da Baba Umar, kuma a ranan akayi wuni, ranan saturday aka wuce da ita kai tsaye chan Narabi, inda dama Baba Umar yayi gidan shi mai kyau, wanda idan sunzo suke sauƙa a wurin, gida ne mai 4bedroom, saboda haka sai aka bawa Aunty 2bedroom inda kowani ɗaki ɗaya yana kallon ɗaki ɗaya, da toilet a tsakiyan su, ɗaya aka maida mata parlour ɗaya kuma bedroom, ita ma Suwaiba haka aka mata, shi kuma Baba Umar aka bar mishi main parlour da toilet ɗin ciki don baƙi, amma ya yanke shawaran yanzu zaina bin ɗakunan su, amma idan ya samu sarari zai zo yayi ɗaki a cikin parlourn. Baba Umar Allah bai taɓa basu haihuwa ba, domin sau biyu suwaiba tana ɓari, amma daga baya abun sai yayi shiru. Ranan Baba Umar ya nuna murnan shi da yaga Aunty Hauwa a gidan shi, kuma matsayin matar shi, daɗin abinma suwaiba ba tazo bikin ba, saboda haka ya samu ya mori amarchin shi da Aunty har na tsawon 2weeks da aka bashi hutu, daga nan ya mata sallama ya wuce lagos, inda ita kuma sauran 3weeks suka ma ajin da shekaran zasu gama, wato sauran mata 1yr ta gama, kuma ya mata alƙawarin duk bayan 2weeks zai dinga zuwan mata, haka suka rabo suna ta begen junan su. Rayuwar babu wuya, yau Aunty hauwa sun dawo hutun first term, kai tsaye misau ta wuce, domin zata jira sai Baba Umar yazo tukun su wuche lagos, domin yace wannan hutun lagos zata je tayi, domin hutun 3 weeks zatayi, shi kuma yaga ya kamata su fara sabawa da suwaiba. Tana shiga gidansu tayi karo da Baba wato yayanta Musa, yana ganinta ya fara dariya yana cewa, " jama'an gidan nan ku fito kuga wata afiruwa kazar mayu", yana dariya lokacin da Goggo hussaina ta fara fitowa yana dubanta yace, "Mama don Allah kiga ƴar ki duk ta wani fige babu daɗin kallo, sai wasu ido girkima girkima kaman na hajiya umma ƴar madara", ya ƙarisa faɗi yana dariya domin yasan ya tsukano Mama, wato goggo hussaina, harara ta bishi da shi tana kaɗa kanta tace, "kayi damu iyayenka ba namu iyayen ba, ɗan tselanƙwa mai ƙananun ido kaman ƙaramar tocilan", ta faɗa tana kamu hannun Aunty hauwa da ta fara zuban hawayen tsokanan da Baba yake mata, domin babu hali su zauna inuwa ɗaya da shi zakaji ya tiso ta gaba har sai tayi kuka, amma yayah Auwal ɗinta tattalinta yakeyi kaman wata ƙwai, Mama tana hararanshi tace, "zakaje gidan umman neman ɗumamen safe da kunu ae, namaka alƙawarin yau zan tura ɗan saƙo ya gaya mata irin tonon sililin da kake mata", ta jawo hannun Aunty hauwa suka shige ɗaki, ita dai Addagana tana zaune a ɗakinta tana biya karatun ta, bata wani fito ba sai dariyan drammer su kawai ta keyi daga inda ta ke, amma har cikin zuciyarta tana jin wani iri da akace hauwa ta fige, toh komai ke damun ta? Allah kaɗai ya sani. Tunda Mama ta lura laulayin ciki Aunty hauwa ta keyi, domin suna shiga ɗakin ta dawo da bayan kaman zatayi amai tace, "Mama kaman anci miyar stew a ɗakin nan, warin shi na ke ji", mama da sauri ta ɗauki kwanon miyan ta fitar zuwa kitchen, sannan tazo ta ɗaga labulayen ɗakin tana duban Hauwa data faɗa kan gado ta kwanta rub da ciki, cikin kallon tausayawa tace, "buɗɗo nah mai kike so toh a dafa miki?" juyar da kai kawai Aunty haiwa tayi alaman ba tason komai. Mama tana duban ta tace, "haka bazai yiwu ba hauwa, kinga yadda kika fita hayyacin ki kuwa? Kodai bakyacin komai ne a makarantan? Kuma kin takura kanki da karatu ko? Don Allah gaya mun me kike so kafin wannan mai neman maganan yayi gaba na rasa ɗan aika". Juyowa Aunty hauwa tayi tana duban mama fuska a murtuƙe tace, "Mama komai naci amai nakeyi, ni bansan me zanci ba, kawai fanta nake iya sha", ta ƙarasa faɗi hawaye yana bin idonta. Mama na duban ta kaman ta tayata zub da hawayen tace, "toh zakici faten tsaki"? Da sauri Aunty hauwa ta tashi ta zauna tana duban mama tace, "yauwa mama amma na gidan umma nake so, wanda ta ke saka mishi gauta", ta faɗa tana tasowa tayi parlour wurin fridge ta buɗe tana kallon ƙullin zuɓun da mama takeyi na sayarwa, har ƙasa ta zauna tukun ta ɗauki leda ɗaya mai sanyi ta ɓula ta zuƙe shi, mama kuma tayi waje tana ƙwala ƙira wa Baba ƙarami, sannan ta dawo ta neme kujera ta zauna ta ƙurawa Aunty hauwa ido da ta ɗauki leda na biyu ta ɓula tana wani lumshe ido tana sha. Baba ƙarami ya ɗaga labulen ɗakin bayan yayi sallama mama ta amsa, idon shi ya sauƙa akan Aunty hauwa da take shirin ɗaukan leda na uku tasha, da karfi yace, "kutt hauwa inace dai kin bada kuɗin tukun kike sha bawai kinga na bati ba ko"? Ya faɗa yana ƙara sowa cikin ɗakin baki a buɗe yana kallon mama akan tayi magana. Bappah ne ya shigo gidan da sallama, yana dariyan halin Baba ƙarami ya ƙaraso ƙofan mama yana cewa, "kaidai baba ina ruwanka da tambaya, kasan ko duk zuɓun fridge ɗin ma ita aka yi"? "caɓɗi jam, amma ko nima dole nasha ɗaya don ita har uku fa take sha Bappah", Baba ƙarami ya faɗa yana kallon idon mama da take binshi da harara. Yana dariya ya karkata kanshi wurin mama yace, "mama gani ina zanje miki"? "kaje gidan umma kace ina son faten tsaki mai gauta wa Hauwa, yanzu ta dawo daga makaranta ta kasa cin abincin mu, gwaten kawai ta ke son cin kaji". Juyowa hauwa tayi ta gaida Bappah daya nemi wuri gefen mama ya zauna yana dubanta da tausayawa yace, "bakiji daɗin jikin bane baɗɗo nah? Duk kin rame kin wani ɗashe gaba ɗaya kaman bakida jini? Me kike son ci nasaya miki"? Bappah ya ƙarasa faɗi shima yana duban ta da tausayawa. "Bappah ferfesun kayan ciki nake so", ta faɗa tana kwanciya akan ledan tsakar parlourn Maman, "kutt amma hauwa kin tunkuɗu rikici wallahi, ke kaɗanki kin shanye zuɓu leda uku, gashi yanzu kinsa za a haɗa tsuhuwa da aikin yin gwate, a haka ma mai gauta wanda da ƙyar idan umma bata sake cillani kasuwa ba, yanzu kuma kin matsawa bappan mu ya sayo mana kayan ciki a dafa mana, haba hauwa cikin mu ae baxai ɗauki abinci dayawa ba", ya faɗa yana fita da sauri a ɗakin yana dariya, domin irin kallon da mama ta ke mishi kaman zata mare shi, yana tsayawa a tsakar gidan ya kwaɗawa Addagana ƙira yace, "fito kiga halin wariyar da mama da Bappah suke mun, don Allah Addagana nima ki saya mun kazar alka mana na huce", fitowa tayi tana kallon shi tace, "nikan ba aikanka akayi bane Baba"? Addagana ta tambayeshi. Haka ya fita yana cewa daga nan zan leƙa gidan yayah Auwal nace mishi zizar ƴaƴa fa tazo, gida ya kache me da girke girke, shima ya saka ƴar lukutan matar shin nan ta dafa nata ta kawo", yana dariya ya fita a gidan. Da yake anyi auren hauwa december, febuary akayi na yayah auwal, da matar shi da takasance ƴar bappan su ce, Ummi kyakkyawar bafulatana da suke yanayin kama da Yayah Auwal. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/14, 11:45] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 34📑* *__________📖* Murmushi Bappah yayi yana duban mama yace, "kinji abinda ɗanki yake faɗa ko"? Tana dariya ta dubi Aunty Hauwa tace, "kije ki gaida Adda ko", tashi Aunty hauwa tayi ta nufi ƙofar ɗakin Adda, wanda ta shimfiɗa taburma tana ƙulla ayanta mai sugar. Gefen tabarmar Aunty hauwa ta zauna, idon ta na kan ayan, ta gaishe da Adda, bayan sun gaisa ne Aunty hauwa ta saka hannu ta ɗebi ayan ta kai bakin ta, lokaci ɗaya ta rufe idon ta don tsabar daɗin da ya ziyarci ƙwaƙwalwarta, ganin haka Adda ta ɗago wani ledan ta ƙullu mata mai yawan gaske ta miƙa mata, gyara zamanta tayi a gefen Adda ta maida hankalinta kan cin ayan. Adda tana gama ƙullawa ta dubeta tace "ko zakici rogo"? Ido Aunty hauwa ta ɗago tana kallon Addan cikin nutsuwa tace, "dama ki soya mun shi ya koma ƙosan rogo". Tashi Adda tayi ta ɗauko rogon ta saka attaru da ajino da albasa ta kirɓaci yayi laushi, sannan ta haɗa murhunta ta ɗaura mangyaɗa, ta fara soya mata, lokacin kuma Mama ta fito tsakar gidan domin Bappah ya koma ƙofar gida domin fara ƙiran sallan azahar da akeyi. Dukkan su alwala sukayi, bayan sun idar da sallah ne Adda ta zuba mata ƙosan rogon a pilet, tace ta karɓo yaji a wurin Mama, da sauri ta tafi parlourn mama ta karɓo yajin, a tare suka fito ita da maman, kafin kace me ta cinye rogon nan, mama ta miƙo mata zuɓu guda 2, a wurin ta zuƙe su, sannan ta yi hamdala ta wuce ɗakin mama ta kwanta akan three sitter maman, lokaci ɗaya bacci ya ɗauke ta. Ana ƙiran sallan la'asar ta buɗe idonta da ƙaran wayanta ya tasheta, amma bata iya ta tashi ba ta jawo wayan ta kai kunnen ta, muryan Baba Umar taji yana mata sallama, hira sukayi na zuwa wani lokacin yana kuma tambayanta yanayin jikintan, haka dai suka ɗan ɓata lokaci kaɗan, sannan ta tashi ta fito domin yin alwala. Tana idar da sallan mama ta shigo ido ta ƙura mata ganin ta sunkuyar da kanta ƙasa tana jan charbi, a hankali ta ɗago suka haɗa ido da mama. "Hauwa ga gwaten tsakin an kawo miki, amma ina ga bayanzu zakici bako?" murmushi Aunty hauwa tayi tace, "yanzu kai mama, kinji wani irin yunwa dana ta shi inaji kuwa"? Mama ko da sauri ta jawo kulan ta ɗauko pilet ta miƙa mata, wani murmushin daɗi Aunty hauwa tayi, ta ɗauko ta zuba cikin pilet ɗin, sai wani ƙamshin gyaɗa yakeyi, ga tantaƙwashi rututu a ciki, Aunty hauwa dariya tayi tace, "Allah sarki hajiya umma, irin wannan daɗin yau ina zan kaishi"? Sannan ta dubi mama tace, "mama kada abawa kowa duk zan cinye zuwa anjima, don nasan Baba ƙarami yana zuwa ya gani toh sai wani ikon Allahn, don sai yaci", ta faɗa tana ɓoye coolern a bayanta. Dariya mama tayi tace, "muma umma ta mana coolern mu daban, kuma Baba kam ae shi ya kawo, babu yadda banyi da shi bama ya tsaya yaci, amma yaƙi yace pepesoup ɗin kayan cikin kawai yake jira, amma wannan kam ya bar miki". "Chabb ɗi jam, mama kada ma kibashi, ni nafi son saifa da hanji ma kawai, idan akwai yaɗi a ciki ki bashi mama", ta faɗa tana kai loman gwaten, kallon mama tayi tana murmushi tace gaskiya umma badai iya kwamacalan girki ba kam, zwaii kenan", ta faɗa tana maida dariyanta. Hararanta mama tayi, "da yake ta rufa miki asiri ta farfaɗo da ke ae dole ki faɗi haka, amma akwai gobe zan ce kada ta dafa miki komai ta barki da halinki", dariya dukkan su sukayi. Zuwa dare mama har ta mata pepsoup ɗin, ga wani bread muƙeƙe da Bappah ya sayo mata, tana zaune a gefen Adda tana ci, sai zuba santi ta keyi, Baba ƙarami kuwa sai mita yakeyi wai ancika mata kwano, shi kuma an saka mishi ɗan kaɗan, Bappah yana dariyan su yace, "banda kai Baba, ae dole naka yazama kaɗan, saboda yanzu ae tana gaba da kai, kuma ita ta zama baƙuwa, dole a karramata, kai kamma da tuwo miyar kukan ka aka baka, kabarta ta cinye daɗin", gaba ɗaya su mama dariya sukeyi, wanda Baba ƙarami kuma ya turo bakin shi gaba yana hararan Aunty hauwa. Ranan kam anji daɗin hiran, don ana idar da sallan ishaa yayah Auwal yazo, basu sukayi bacci ba sai wurin ƙarfe sha biyu, shima don ganin hamman da Aunty hauwa keyi ne yasa suka tashi. Kwanan Aunty hauwa uku Baba Umar yazo ɗaukanta, acikin kwanakin kuma ta zaga duk inda yakamata taje gidan ƴan'uwa, ranan da yazo duk wani abu namu na gargajiya, umma da Mama da Adda duk sun haɗa mata ita da Ummi, hattah ƴan gabɗori saida suka aiko musu da bushashshen zogale mai yawan gaske, haka Baba Umar ya tattara ta sai *NARABI* kwana ɗaya sukayi suka wuce lagos. Gidan Baba Umar 2bedroom ne, dole sai ya bar mun room ɗinshi, ya zama yana bin ɗakin mune, ranan da naje ansha drammer tsakanin su da suwaiba, don firr ta rufe idonta tayita zazzaga mishi rashin kunya, a dole babu inda Aunty hauwa zata kwana a gidan, ae tana da gidan ƴar'uwa ta tafi ta kwana mana acan idan ba neman magana ba, a wurinta kenan. Kusan dukanta Baba Umar yayi tukun ta nutsu, Aunty hauwa kuma ko kallun ta batayi ba, ɗakinta da aka nuna mata ta wuce, bata jira komai ba ta wuce toilet don yin wanka, tana fitowa ta ɗaukin wayanta dayake ta ringing, ganin sunan Ummi akai ya saka Aunty hauwa murmushi, da sauri ta kai wayanta kunnen, suna gama gaisawa, ummi ta mata sannu da zuwa, sanin halin Aunty hauwa da rashin haƙuri, suwaiba kuma da baƙin kishi, yasa ta ja kunnen Aunty hauwa sosai, dariya Aunty hauwa ta je tayi, "Ummi kenan, kina ga daga zuwan mu mata ta so ta maida gidan kaman filin sambisa, toh nidai na yau nayi shiru saboda naga yadda mijinta zai ɗau mataki, amma wallahi! Wallahi!! Ummi zuwa gobe kam zan nuna mata hauwa'un kule mage", Aunty hauwa ta ƙarasa faɗi tana kwashewa da dariya. "yanzu hauwa saboda Allah kin mun dai-dai? Ina gaya miki komai haƙuri akeyi amma kina nuna mun ke baki san da haka ba? Toh wallahi naji kinyi wani abu na rashin mutuncin toh zaki haɗu da ɓacin raina", ummi ta karasa faɗa ranta a ɓace. Aunty hauwa dariya tayi tayi kaman bata damu ba, haka sukayi sallama kowa ya ajiye wayan. Duk yadda suwaiba take tunanin hauwa ta wuce saninta, domin da Aunty hauwa ta buɗe buhun bala'inta har saida suwaiba ta daina zaman parlour, kullum sai da kaji ta a ɗaki ta ƙure volume ɗin wayanta tana jin waƙa, wai don ta ɓata ran Aunty hauwa, dayake Aunty hauwa bata son hayani sai ta zama shine hanyar ɓata mata rai, amma Aunty hauwa ko kula ta batayi, watarana, sai da tabari suwaiba ta cikata da ƙaran waƙeƙe ta gama, ta fito zata shiga kitchen ɗaura abincin rana, da yake girkin suwaiba ne, wanda sukeyi kwana ɗaɗɗaya, Aunty hauwa ta ɗauko wani wayan cavel, ta samu suwaiba a gadon baya ta dinga tsula mata tana, "ni sa'ar kice da zan ce na hana ƙure vulome a gidan nan amma zakiyi kunnen uwar shegu", suwaiba irin ƴan firit ɗin nanne masu ƙaramin ruwa, kuma ga ruwan ciki, amma sai neman faɗa, Aunty hauwa kuma ƴar duma-duma ce, ga faɗa inda ta shiga bata nan ta ke fita ba, sai da tayiwa suwaiba lilis, kuma tace dole ta dafa musu doya da miyan stew don yau ita shi ta ke kwaɗayi, babu yadda suwaiba ta iya haka ta tafi kitchen ta fere doya tana kuka ta ɗaura , a zuciyar tana ƙissama abinda zata gayawa Baba Umar idan ya dawo, don ita bazata iya da dukan Hauwa ba, don yau shi ne rana na biyu kenan, gashi Aunty hauwa sauran ta 10days kafin ta koma, ita kaman bazata iya zaman kwana gima tare da ita a gida ɗaya ba, haka tayita aikinta tana share hawaye. Baba Umar sai dare ya dawo gida, da yake kullum sai 8:00 na dare yake shigowa, idan ya tafi tun 7:00am na safe, ko ruwa bai shaba, suwaiba ta fashe da kuka ta fara zayyana mishi irin dukan da Aunty hauwa ta mata, har da ƙari saida Suwaiba ta faɗa, shidai kallonta ya tsaya yana yi, wani zubin sai yaji kaman ya fashe da dariya, amma ya dake yace ta ƙira mishi hauwan. Aunty hauwa tana fitowa cikin wani jeans da t.shirt mai shegen kyau, ta ɗaure tulin gashinta da wani yellow ribon kalan t.shirt ɗin, har inda Baba umar yake zaune taje ta tsuguna a gaban shi ta gaishe shi cike da ladabi, ga wani juya ido da take mishi, sai wani ƙamshin daɗi ta keyi, fuska a sake ya amsa mata yana ta duban fuskanta da yasha kwalliya, har yaso manta dalilin ƙirantan da ya saka aka mishi, don ba ƙaramin son ƙamshi ya keyi ba, amma ga suwaiba sam taƙi turare, sai tace wai yana sakata mura da ciwon wuya, haka ya haƙura da ita, iya kacinta ta guga roll-on. Bayan Aunty hauwa ta gaishe shi sai ta gyara zamanta a ƙasa dai-dai inda ƙafafunshi suke tana mai binshi da murmushi, sai wani rangwaɗa ta keyi, gaba ɗaya ya maida hankalin shi kanta, sai jin muryan suwaiba yayi cikin kika tana cewa, "bazaka mata maganan abinda ta mun bane, ka tsaya kana kallonta"? Kallonta yayi fuskan shi a ɗaure yace, "me kika gaya mun tayi miki ma"? Hararan Hauwan tayi tana turo baki alaman zata fashe da kuka tace, "babu abinda na mata ta kamani ta min dokan kawu wuƙa, kuma wallahi bazan yadda ba sai ka sakata ta tsaya na rama duka na". Murmushi mai inganci Aunty hauwa tayi, muryah ƙasa-ƙasa irin na cikakkun mata da suka san kansu a gaban miji tace, "Hero kaci abincin tukun ka huta sai ka saurari haushin da ta keyi, Allah ya huci zuciyar ka, haushi mana zance domin miji ya wuni a waje nema mana halal ɗin mu, ya dawo a gajjiye ko ruwa bai sha ba, ki haushi da ƙorafi akan kishiya? Gaskiya Suwaiba ki gyara tsarinki, ta yayah hero zai samu nutsuwa da mu? Ya dawi bamu san a wani hali yake ba mu hau kai ƙara wurin shi? Ki bari yaci abinci yayi wanka, idan yazo parlour ya xauna sai ki kawo mishi ƙaran yau ni Hauwa na dake ki da kika ce mun karuwar gwamnati, ni kuma na kasa haƙuri nayi miki dukan tsiya domin kada bakinki ya saba da faɗin mun gama karuwanci mukayi aure, kinga idan na haihu ɗanmu yaji abinda kike jifan iyayen shi da shi bazai ƙira ki da mummy ba, kuma ni nafi so yarana suce miki mummy, ni kuma mamie, Hero kuma daddy", ta ƙara faɗi tana wani kanne mishi ido tana shafa cikinta tana ta rausayawa. Kuka suwaiba ta fara murya da ƙarfi ta faɗi,"wallahi da gaske ki karuwar ce hauwa, domin duk wacce taje school of nursing sunan ta karuwa, kuma karuwancin kikayi ae kika aure mun miji, yanxuma shi kikeyi agabanshi, jaka karuwa kawai", ta ƙara tana kuka mai sauti. Rausaya kai Aunty hauwa tayi kaman zata yi kuka ta dubi Baba Umar bayan ta miƙe tsaye tace, Hero zan koma ɗaki, don bazan iya cigaba da jin kalmar karuwa da matar ka ta ke yawan jifa na dashi ba, saboda bana son hayani, nafi so kaɗan huta tukun sannan ka sanar mata yadda na kawo maka budurcina lafiya ƙalau gidanka, kuma ka....." sai ta kasa ƙarasawa ta yi ɗakinta tana share hawayen idonta. Juyawa yayi yana hararan suwaiba, zuciyar shi sai tafasa ta ke mishi don jin kalmar karuwa da ta dangana matar shi mai daraja da tayi. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/17, 14:32] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 35📑* *__________📖* Cikin muryan ɓacin rai Baba umar yace, "wallahi suwaiba na rantse miki da Allah, kika sake jifan matata da sunan karuwa, toh a bakin auren ki, ke idan kina da hankali koda karuwa na aura tana shirin haifa mun ɗa ko ƴa, ya kamata ki jefe ta da sunan karuwa? Ni na ɗauka idan kinji mai ƙiranta da wannan sunan sai inda ƙarfinki ya ƙare, amma kece da bakinki kike faɗa? Gaskiya banji daɗi ba, kuma bana son sakeji da ga yau", ya karasa maganan yana miƙewa tsaye ya wuce toilet ɗin da yake parlourn, don wataran yafi son shiga wurin, especially idan dare ne, don yasan lokacin babu baƙon da zai shigo ballantana yaga fitowan shi. Suwaiba kuma haɓa ta riƙe tana mai matuƙar jin tsoron furucin Baba umar, gashi ta sha dukan tsiya, ga rashin iya maganan ta da kula da miji ya jawu ko ta kan maganan ta ba abi ba, juyawa tayi ta dubi ƙofan ɗakin Aunty hauwa da ta leƙo ta ƙurawa suwaiba ido tana murmushi, a hankali Aunty hauwa ta ƙaraso cikin parlourn ta zauna gefen suwaiba tana ta jujjuya idon ta tana rausaya jikinta, ta gefen ido ta kalli suwaiba tana murmushin iskanci tace, "suwie darling! Wato ke baki san ta yadda ake bariki ba kuma kice zakiyi bariki? ae ba'a kishin banza yanzu, an waye suwaiba, ana kishi ne na nuna kulawa da miji da tsafta da kyautatawa, bawai banzan kishi irin naki ba, idan kince irin shi zamuyi toh ina mai tabbatar miki kece a ƙasa, gara ma ki saduda mu zauna lafiya, don ni babu mugunta a zuciyata, idan kace zaka shiga gona nane kawai zan taka maka burki iya sanin ka, so ina mai jan kunnen ki da babban murya suwaiba, idan kunne yaji toh jiki ya tsira", bata jira mai suwaiban zata faɗa ba ta wuce ɗakinta ta barta tana share hawayenta. Wani irin kulawa Aunty hauwa ta ke nunawa Baba umar, har sai da yakai ranan da zata karɓi girki dole sai ka gane rawan kan shi, don ko zaman parlour ba ya iya yi, a haka har hutun Aunty hauwa ya ƙare, tazo gidan mu yakai kusan sau biyar, wani lokacin Ummi zata je damu gidan mu ɗauki Aunty hauwa muje shan iska cikin lagos, wataran muje gidan abokan su Abba da Baba umar, a haka har Aunty hauwa ta koma Narabi, ko kwana biyu bata wuce ba ta koma school. Ten october 1980, shine ranan da aka haife mu nida Hassan, yau kuma ya kama 10 october 1985 Aunty hauwa ta haifi ɗiyar ta mai masifar kama da ita, lokacin da Aunty hauwa ta haifi ɗiyarta munyi tsalle da murna nida Hassan badon komai ba, sai don jin daɗin date of birth ɗinmu yazo ɗaya da sabuwar ƙanwar mu, ranan Aunty haiwa saida ta gajji da amsan wayan mu, don ko ta ajiye bata wuce 1hr zamu sake ɗauka muce, "Aunty ki saka mana kukan sistern mu", ita dai dariya kawai ta keyi, a dole sai ta ɗan bugi babyn ta fara kuka. Munajin muryan kukanta zamu fara tsalle nida Hassan muna tambayan Aunty, "Aunty don Allah muryan babyn irin na waye a cikin mu"? Dariya Aunty ta keyi tace, "muryan kukanta na rikici irin na Babana hassan ne, idan kuma tayi

Chapter 17 of 28