Share this page
da aka yanka na layyan bana ba, ƴar ƙuƙur kenan". cewar Aisha lokacin da ta rutsa ni a kitchen tana mitan neman corper da na ke yi. Kallon Humaira na yi sannan na bata irin amsan dana bawa Aisha a wancan lokacin, wanda shi ne kawai nasan zai sa ka ta rufe bakin ta, "to ke bakiga irin kyawun da ta ke da shi bane? Ina ruwa na da wani tsayin ta tun da ni ina dashi ai ya ishe mu, kawai kyawunta da yasa bana iya ganin na kowacce mace ne ya ɗibe ni na aure ta, kuma har yau bana ganin wacce ta fita a ido na, kowa ganin ta na ke yi kaman biri a gaba na don muni". ya faɗa yana wani jujjuya kanshi alaman abin ya mishi daɗi. Fita nayi daga kitchen ban ko bi ta kanshi ba, wucewa ɗaki na kawai nayi don ganin su Abbu basu fito ba. Ina wucewa ya yi dariya shi kaɗai yana tuna Aisha wanda lokacin ita tsabar haushi kuka ta fashe da shi taje tana gaya wa Ummi wai nace tana kama da biri, wanda Ummi ta ƙira ni tana cewa, "saboda Allah Hussain ko wani kaji ya cewa ƙanwar ka tana kama da biri ai sai in da ƙarfin ka ya ƙare, ko dan Albarkacin ita tayi kamanni na ai za ka ce tafi kowa kyau a duniya". Hassan ne ya amsa da wuri yana cewa, "Ummi to wai ita meya sa ta damu da sai Hussain yace tana da kyau? Saunawa ina gaya mata kafin a samu mai kyawun ta sai antona, saboda kaf zuri'ar mu babu mai kyawun ta, amma nawa baya burgeta sai na amininta ta ke jira ya faɗa, wanda har ta mutu bazai faɗa ba, kuma ta haɗu da aiki wallahi, garama ta haƙura mijin auren ta wataran zai gaya mata". Hararan shi Aisha ta yi tace, "kafin nayi auren miji na yace ina da kyau, Yaya Hussain ɗin nake so yace ina da kyau, ai kai na gajji da faɗan da ka ke yi na shi kaɗai na keso ya faɗa, tun da shi ai bai taɓa faɗa ba". sannan ta kalli Ummi tace, "Ummi nah don Allah kice mishi ya faɗa mun ko sau ɗaya ne". ta faɗa tana kwanciya a jikin Ummin. Ummi ce ta dube ni da faɗa tace, "bana wasa da kai Hussain kazo kagayawa ƴar uwar ka tafi kowa kyau a cikin matan duniyan nan, idan kana so mu zauna lafiya da kai yau a gidan nan". Dariya na yi har ina buga ƙafa na, muka tafa da Hassan sannan nace, "Allah Ummi bazan faɗawa wata mace tana da kyau ba har sai matar da zan aura, ita ma kuma har sai ta shigo gida na zan gaya mata, domin zai fi mata daɗi, amma haka kawai na ƙarasar da kalma mai girma da daraja tun a waje? Lokacin da ya kamata na faɗa kuma ya zama bai mata daɗi ba? Gaskiya Ummi na ma gudu". da gudu na fita a ɗakin Ummi, wanda ina jin dariyan Hassan kaman zai tada Parlon ita kuma Aisha sai kuka ta ke tayi, Ummi na bata haƙuri. Fita ya yi a kitchen ɗin cikin jimamin rashin familyn shi da ya yi na shekaru da dama a tare da shi? Ko ya ya Ummi ta ke? Ya ya Hassan zai ji idan ya buɗi ido bai ganshi ba a rayuwar shi? Duk da suna yawan faɗa amma suna son junan su wanda babu wanda ya ke shiga tsakanin su, don ko suna faɗa idan wani ya saka baki to sun daina, sai dai su rungume junan su suna dariya, kuma ko ya ya Aisha ta ke? Ko yanzu yaran ta nawa? Wata aura? Allah sarki Abban su ko ya ya zai ji idan babu ni a rayuwar shi? Duk da sun kasance ƴan biyu amma Abba yafi nunawa Hussain soyayya, Allah sarki Aunty Hauwa ita kam yasan hala sai tafi Ummi shiga damuwa. Har ya shiga part ɗin shi hankalin shi a tashe, yarasa me yasa tun haɗuwar shi da Hummy ya zama kullum suka haɗu sai ta tuna mishi da wani abu na familyn shi. Kwanciya ya yi a parlor, sannan ya ƙira ni, ina ɗauka muryan shi a hankali yace, "Babyn baby na tafi don Allah ki bawa baƙin nan abincin, naga kin wuce ɗaki bamuyi sallama ba". "Naji yanzu ma ina kitchen ɗinne, gudnyt". na faɗa mishi ina kashe wayan, don har yanzu raina a ɓace ya ke da shi. *#Comment, Vote & Share.* *©AUNTY NICE CE* ✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* _*RIGIJI GABJI,RANAR KUKE JIRA YAU GATA TAZO MASOYA_* _*MARUBUCIYAR NAN TAKU WADDA TA SABA KAWO MUKU LITATTAFAI INGANTATTU MASU TSUMA ZUCIYAR ME KARATU WATO HASSANA D'AN LARABAWA ,MARUBUCIYAR*:_ _SANADIN HOTO_ DA _HASSANA DA HUSSAINA _ _*YAU TA SAKE DAWO MUKU DA SABON LITTAFINTA WANDA YA ZARCE DUK LITATTAFANTA A KOMAI WATO CIN AMANAR RUHI,KAI DAGA JIN SUNAN KUN SAN AKWAI TAFKA TAFKA DA K'ULLE K'ULLE ,AMMA ZATA WARWARE MUKU K'ULLIN DA ZARAR KUN BIYA 200 DOMIN SAMUN LITTAFIN,KAR KU BARI YA WUCEKU ,DOMIN WANI IRIN LABARI NE DA BAKU TAB'A CIN KARO DA IRINSA KO MAI KAMARSA BA,FAD'AKARWA ,NISHAD'ANTARWA,ILIMANTARWA,TAUSAYI,DA SOYAYYA ME TSAYAWA A ZUCIYA ,TARE DA WATA IRIN CIN AMANA DA BAKU TAB'A RISKAR IRINTA BA,KU DAI KU HANZARTA NEMAN MARUBUCIYAR DOMIN KU SIYA KU KARANTA AKAN KUD'I K'ALILAN 200*_ _*ZAKU IYA NEMANATA AKAN LAMBARTA KAMAR HAKA,08080049548 DAGA NAN ZATA GAYA MUKU YADDA ZAKU BIYA KUD'IN ,KU DAI KU HANZARTA KAR AYI BABU KU ,KU TUNA DA SUNAN LITTAFIN*_ CIN AMANAR RUHI _*NA MARUBUCIYAR KU HASSANA D'AN LARABAWA*🥰🥰🥰🥰_ *SHAFI NA 13 📑* *__________📖* Ni dai ban san me ya faru ba, sai farkawa na yi cikin dare naga waya ta a yashe a gefe na, murmushi na yi ni ɗaya wayan na ɗaura a bedside drower, wato bacci nayi Dr yana mun waƙa ko? Kaɗa kai na nayi na shiga toilet. Bayan na idar da sallan asuba, kitchen na wuce na zauna na fere dankalin, sannan na soya na soya ƙwai da plantain, na so na yi peppesoup, amma ganin babu time yasa kawai na kai musu kan dinning na ajiye ketchup a kan dinning ɗin, flasks na cika da ruwan lipton mai kayan ƙamshi, ina gama jerawa nayi sauri na shige toilet na yi wanka, gudu-gudu na fito na shirya, sannan na ɗauki breakfast ɗin kaɗan naci, note na ɗan rubutawa su Ummi sannan na ɗauki handbag ɗina na wuce zuwa school. Ina fitowa na haɗu da Dr shima ya fito zai wuce school ɗin mu, murmushi yamun nima na mayar mishi, ƙarasowa yayi har in da na ke, sannan ya buɗe mun front sit na shiga, shi kuma ya zagaya wurin zaman driver. Yana ta da motan na gaishe shi, yana kallon kan hanyan ya amsa, sannan ya tambaye ni ya ya baƙi na suka kwana? Ina murmushi na ce mishi, "lafiyan su ƙalau, amma basu fito ba na fito yanzu". "Break fast fa, kin musu dai ko"? Ɗaga kai nayi alaman ehh na musu. "Ni ne kawai ba kiyi dani ba ko?". Hannu na saka na rufe baki na ina dariya. "Hmmm dole kiyi dariya mana, tun da kin cika cikin ki ni kuma kin barni da yunwa, amma babu komai zanje wurin khadija nasan zata soya mun egg nasha da tea", ya faɗa yana murmushi. Hararan shi nayi na turo baki na gaba ina ta ƙunƙuni. "Ki faɗi abinda ya ke bakin ki zaifi miki sauƙi, amma harara na ba zai miki sauƙi a ranki ba". "Ni bance komai ba, tun da nasan matar ka bata iya girki ba, hala ma idan taje soya ƙwan ya ƙone bata san yadda akeyi ba". Dariya ya yi ya na shiga gate ɗin school ɗin, juyowa ya yi ya kalle ni bai ce komai ba sai murmushi, yana ta rawa da kanshi yana murmushi yana kallo na. Muna isowa ƙofan department ɗin mu ya yi parking idon shi yana kallon wani wuri yana munafukin murmushi. Hararan shi nayi a hankali na dubi in da ya ke kallon, Dr Khadija ce tsaye tana rufe motan ta, gefen ta kuma wata friend ɗin ta ce a tsaye suna magana, dawo da kallo na nayi kanshi, buɗe motan nayi na fita bata re da na ce mishi komai ba, ganin saura 15mnt a shiga mana class nayi sauri na ƙara sa hall ɗin da muke lectures, ina ganin yadda Dr Khadija da ƙawar ta suka bini da kallon mamaki, haka ma wasu daga cikin students da lecturers suka dinga bina da kallon mamaki. Ina wucewa shima ya fito bayan yayi parking motan shi, ko kallon in da suke bai yi ba ya wuce office ɗin shi, ganin haka yasa Dr Khadija bin bayan shi da sauri ranta a ɓace, duk ƙiran da ƙawarta ke mata bata kula ta ba, ita dai sauri kawai ta iso shi taji dalilin shi na ɗauko ni a motan shi. Ina shiga class ƴan class ɗin mu suka yi ta tambaya na ina Amal, wasu na gaya musu bata da lafiya, wasu kuma na sha re su ina duba note ɗin cost accounting da Ezeh ya miƙo mun, kuma ina maida hankali na kaɗan kanshi da naji shi ƙasa-ƙasa yana ce mun. "Beauty dama Dr Hussain brother ɗin kine ko?". Ina kan buɗe note ɗin ban kalle shi ba nace, "Uncle ɗina ne, shi ɗin ƙanin Daddy na ne". "Heyy no wonder mana naga yana tolerating ɗin ki, kaman wancan ranan da ki ka ba shi haƙuri ai ya dawo ya ci gaba da lectures, so yanzu kawai kice zan kama ƙafan ki don gaskiya bana son na faɗi a course ɗin shi seriously, kinsan 4 credit unit ne, kuma ga shi shine *PROGRAMME CO-ORDINATOR* Namu, don ma naji ance Professors ɗin nan ake bawa Heads of Departments, amma da an bashi na department na mu, saboda ƙoƙarin shi a department ɗin". haka muka yi ta magana akan course ɗin, kafin lecturer su fara shigowa. Dr Khadija tana shigo mana ranan naga bala'in ɓacin rai kwance a fuskar ta, sai wani ɓata rai ta keyi kaman an saka ta dole, kuma tambaya ɗaya zata ɗaga ni tayi mun, abinda na lura nema ta keyi ta ga gazawa na, amma daya ke ni ɗin ba kanwar lasa bace, sai ta kasa samun in da zata ƙure ni, domin idan ba yabon kai ba, idan ku ka cire Ezeh to duk class ɗin ba zaka samu na sama dani ba, amma baza kasan hakan ba, sai an taɓo ni, saboda ni karatu na bana nunawa mutane bane. Tana gamawa ta dubi ƙofa dai-dai lokacin Dr Hussain ya iso, dawo da kan ta tayi ta dube ni, fuska a ɗaure cikin shegen haɗaɗɗen turancin ta kaman na tsohuwar baturiyar england tace na sameta a office after na gama lectures. Bance mata komai ba sai bin ta da ido da nayi ta tayi har ta bar class ɗin, a lokacin Dr Hussain kuma ya shigo, ina ganin shi ya kauce ma ta ta fita, domin da yi tayi kaman zata bangaje shi, amma ba zaka gane ya ya yanayin fuskar shi yake ba, saboda babu yabo babu fallasa akan face ɗin shi. Tun da ya fara lectures bai kalli in da nake ba, sannan idan ya yi question baya duban in da na ke ballanta na ya mun tambayan, haka ya gama lectures ɗin shi, yana gamawa ya tako har in da na ke zaune, yana kallon cikin ido na yace, "kada na yadda naga kinje ƙiran da Khadija ta miki kin ji ko". Ɗaga mishi kai nayi alaman naji. Yana duba na fuska a ya mutse yaɗan sunkuyo da fuskan shi saitin in da nawa ya ke yace, "yunwa na keji Babyn baby". ya ƙarasa faɗi kaman zai mun kuka, juyawa nayi da sauri na dubi ƴan class ɗin amma sai naga duk idon su yana kan mu. ya mutsa fuska na yi ina nu na mishi alaman ana kallon mu fa, amma sai ya wani ɗaga kafaɗa irin ko ajikin shi, ya sa ke sunkuyowa ya kwaikwayi murya na yace, "Baby yunwa, wayyo babyn baby". ya faɗa yana ɗaura hannun shi akan cikin shi. Dariya nayi na miƙe tsaye ina kallon shi, a hankali nace , "to muje gida na soya maka egg ɗin da singulura ta kasa yi maka, muje na samu ladan ka". yana dariya shima ya biyo baya na muka fita a class ɗin. Ko sauƙa a brandan class ɗin ba muyi ba muka ji ihu da buga desk da ƴan class ɗin suka yi, ina jin muryan wani yana cewa wallahi girl friend ɗin shi ce, Ezeh yana ta rantse musu akan uncle ɗina ne. Kallon Dr nayi baki na a buɗe ina nuna mishi yaji mai ƴan class ɗin suke cewa, shima dariyan yayi ya dawo kusa dani yana cewa, "To girl friend ɗin ne ko ni Uncle ɗin ki ne?". Tsayawa na yi da tafiyan ina kallon shi cike da mamaki nace, "kai kuma sai ka biyewa abin da zasu ce maka?". "To ya ya zan yi da rigan da babu wuya? Nikam kawai yau baki isa ba sai kin gaya mun waye ni a wurin ki". "Nikam ba bu ruwa na Dr, kai kawai Dr'n mu ne, kai malamin mu ne". "ni dai baki isa ba sai kingaya mun a tsakanin abin da su ka tambaya". Hararan Aunty Faraa nayi don ganin Hummy zata mishi bayani ita kuma ta wani daka tsalle tana ihu tana cewa, "sai Dr da Hummy Allah ya bar ƙauna ta gaskiya". da sauri Miss Xerks ta jawota da ƙarfi tace, "to kin yiwa kan ki, gobe baza mu ta ho da ke ba, kuma yau zan saka *NEAT LADY* ta turo jet ɗin ƴan gaskiya writers a koma da ke nigeria, saboda ihun nan da kika yi gashi kin sa ka sun yi shiru suna kallon mu". Juyowa ta yi tana duba na irin na hana Miss Xerks sakawa a maida ta gida, hararan ta nayi nace, "wallah komawa za kiyi yanzu yanzu ma, tun da ihu za kiyi a dinga jinmu, da naso ranan da za ace.........". *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* _*NANA FIDDAUSI, ƊIYAR JIKAR KULU WANNAN SHAFI NA KINE KYAUTA, ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR KI, YA KAWO MIKI ƘANNE MASU ALBARKA*_ *SHAFI NA 15📑* *__________📖* Kan bed ɗina na faɗa ina kuka mai zafi a zuciya, ni na rasa me yasa na damu da sai Dr ya yaba ni, bayan nasan ba zai ta ɓa yabawa ba, gara ma nayi haƙuri kawai, ina cikin kukan naji an buɗe ƙofan ɗakin an shigo. Dafa baya na naji anyi, wanda daga dukkan alamu Ummi ce, ban ɗago na kalle ta ba, amma na rage sautin kukan nawa. "Tashi Aisha Humaira muyi magana kinji". cewar Ummi, tashi nayi zaune ina ta sauke ajiyan zuciya. Hannu na ta riƙe gam a cikin nata tana duba na cikin nutsuwa, a hankali ta jeho mun da tambayan da ya kusa sakani dariya, "Humaira kina son Dr ne?". Kallon ta na yi kaman zanyi dariya nace, "Ummi son Dr kuma? Ni kam ban taɓa jin son shi ba, ni Ummi ba bu wanda na taɓa so a duniya irin Daddy na, sai kuma Amal da na ke son ta, ni bayan su bana son kowa". "Har maman ki baki son ta?". Kallon ta na yi ido na yana cikowa da hawaye, juyar da kaina nayi gefe sannan nace, "Mama na ta rasu". Jawo ni jikin ta tayi ta rungume ni saboda ganin hawayen da ya fara gangaro mun, a hankali tace, "Allah ya jiƙan ta da rahma, Allah ya ƙara miki haƙuri da juriya na rashin ta". ni dai ban ce komai ba ina dai kwance a jikin ta nayi shiru hawaye yana bin fuska na, tun ranan da na bar ƙasar mu na daina zubar da hawaye na rashin Mama na, amma yau kuma kewar ta ya dawo mun zuciya ta mai rauni. _*ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU DA SU KA RIGA MU GIDAN GASKIYA, TABBAS RASHIN UWA WANI BABBAN MIKI NE WANDA BAYA CIKEWA, DUK WANDA TAYI RAYUWA BABU UWA GASKIYA ABUN TAUSAYI CE 😭😭😭ALLAH KA KAI HASKE A KABARAIN MAMA NAH!* 👏🏻👏🏻 "A hannun wa kika tashi?". ta jeho mun wani tambayan kuma. "Hannun Daddy nah da matar shi wanda muke ce mata Mama, tana da yara guda uku, Yaya Ahmad shine babba a cikin yaran ta, sai kuma Yaya Aliyu shike bin shi, sai Yaya kabir shi ne ƙara min su, shi kuma ya bani 2yrs, yanzu haka yana karatu a ATBU, ni kuma ni kaɗai Mama na ta haifa, kuma ni kaɗai ce ƴa mace a wurin Daddy nah, shi yasa ya ke sona sosai". na faɗa hawaye yana ɗan bin fuska na kaɗan kaɗan ina sharewa. "Hummy tunda kince ba son Dr ki ke yi ba, to zan baki shawara a matsayi na na mahaifiya a gare ki, daga yau ki daure ki daina damuwa idan baice kina da kyau ba, ko baice kin iya abinci ba, yaga kin damu ne shi yasa yake bawa zuciyar ki wahala, saboda duk ranan da ya tunkari zuciyar ki bazai samu matsala ba, saboda ya gama lugwaigwaita ta da soyayyar shi, kowa ya ganki yasan tsakanin larabawa da indiyawa sai anyi da gaske a samu mai irin kyawun ki, saboda ranan da na fara ganin ki na ɗauka aljanu ne zasu buɗe mun ido, Humaira ke ɗin ɗiya ce mai kyau da daraja, kada ki yadda da ga yau Dr ya sa ke saka ki kuka kin ji, daga yau ki nuna mishi baki son yabawan shi tunda ke mai kyau ce, kuma kin iya girki mai daɗi da kwanci a zuciya, domin ina hankalce da shi, lomar farko da yafara yi sai da ya lumshe idon shi don daɗi, saboda haka ko ya faɗa ko kada ya faɗa, girkin ki ya mishi daɗi". ta faɗa tana mun murmushi, saboda ganin nima na ke ta murmushi. "Humaira kin ji daɗi ne da nace miki yaji daɗin girkin?". Dariya nayi ina ɗaga mata kai alaman na ji daɗi. Lumshe ido tayi ta buɗe a hankali, a zuciyar Ummi tana jin tausayi na, domin tasan babu yadda za tayi na riga da nayi nisa a son Dr, sai dai fatan Allah yasa shi kuma ya riƙe amana, tasan komai zai ta gaya mun ba zaiyi tasiri ba, saboda bani da wayon da zan fahimce ta, saboda shi wayo bawai a shekaru bane, kawai baiwa ne, wasu kuma zama da iyaye suna nusantar dasu abinda ya kamata shi ke sakawa su fahimci rayuwa, wasu kuma irin mutanen da suka zauna dasu yake sakawa su fahimci rayuwa, amma abin tausayi tasan ni nayi rayuwa ne da giɓi na rashin uwa. "Ummi to ya ya ake jin so ɗin?". Na jeho mata tambayan da ba ta yi tsammani ba. Shiru tayi na wani lokaci, sannan ta ɗago ni zaune tana duban fuska na, "zaki na yawan tunanin mutumin, Za ki na yawan jin kishin wata akan shi, za ki na yawan jin tausayin shi, Za ki na son kina yawan ganin shi, ba za ki na gajjiya da jin muryan shi ba, Za ki na so kiga komai ki ka yi ya yabe ki, Komai aka faɗa na laifi akan shi baza kina gani ba, zai zama kullum hasken shi ki ke gani Za ki na ......". abubuwa da yawa Ummi ta lissafo mun akan yadda za ka ji kana son mutum. Da sauri na dafa zuciya ta ina lumshe ido na, duk wani tsoro naji ya kamani, a hankali na sa ke buɗe ido na ina kallon Ummi, "Ummi daga shekara nawa ka ke ji ka fara son wani?". Dariya ta yi mai ɗan sauti, sannan ta dube ni tace " soyayya bata da shekaru, ba ta da lokaci, ba ta shawara, bata zaɓe, duk lokacin da Allah ya hukunta za ka fara to babu makawa ko kashirya mata ko baka shirya ba zaka fara". "Na shiga uku Ummi, to wallahi zuciya ta tana son Dr Hussain, amma ni kam bana son shi Ummi". na faɗa ido na yana cikowa da hawaye, saboda gaskiya ni ban shirya yin soyayya ba, kuma bamuyi haka da Daddy na ba. "To ita kuma zuciyar ki ta shirya karɓan soyayya'n Dr, to ya ya za kiyi kenan?". Cewar Ummi. "Ummi ni kam bana son shi". "Me yasa baki son shi? Yana da wani problem ne?". "Ummi ni fa saurayi na ke son aure kuma yaro iri na, amma shi fa yana da mata, kuma ya yi mun tsufa, kuma Daddy yace mun kada nayi soyayya da kowa saboda maza basu da kir ki". Shiru Ummi tayi har zuwa wani lokacin tukun tace, "to ai ke baki da Laifi, tun ke baki san kin fara son shi ba, kawai yanzu abu ɗaya za kiyi ki kare kan ki". Da sauri nace "me zanyi Ummi"? "Kada ki gayawa kowa kina son shi, ko da Amal ce, shima kada ki bari ya gane kina son shi, don zai gayawa Daddy'n ki, itama Amal idan taji zata gayawa Abbu'n ta, shi ma zai iya faɗawa Daddy'n ki". zaro ido nayi ina duban ta da tsoro, sannan a hankali murya can ƙasa nace, "Ummi to ai bazan taɓa gaya mishi ina son shi ba, ban ma san ina son shin ba". na faɗa kaman zan yi kuka. "Yauwa ɗiya ta Hummy, kada ki bari kowa ya sani, shima ki daina damuwa da matar shi, ki dena damuwa da sai yace kina da kyau ko kin iya abinci, amma kiyi ta kwalliya da abinci mai daɗi kina bashi yana ci, kuma kada kina shiga gidan shi ke kaɗai, kina zuwa tare da ƴar'uwar ki Amal kuna kai mishi, ina miki albishir wataran da kan shi zai furta miki kin fi kowa kyau, amma sai kin kama kan ki, ki daina nuna kin damu da komai, kuma idan mun tafi duk abinda ya shige miki duhu ki kira ni ki gaya mun, ni kuma na miki alƙawarin warware miki komai kin ji doughter na". Abun tausayi yau jirgin ƙarfe 12:00pm na dare su Abbu suka tashi, ba Amal ba har ni sai dana yi kukan tafiyan su, saboda tun da nazo duniya ban taɓa jin na shaƙu da wata mace ta nuna mun ita uwa bace a gare ni sai ita, gara-gara kakanni na guda biyu duk sun nuna mun ƙauna, wanda ta haifi Daddy na ina primary 6 Allah ya mata rasuwa, amma ina tuna yadda ta ke masifa idan an mun abu ba dai-dai ba, sai kuma wanda ta haifi Mama na, duk da ba wani yawan ganin ta na keyi ba, saboda bata ƙasan, sai tayi shekaru kafin ta zo, amma duk ranan da tazo gani na takan nuna mun soyayya kaman ita ta haife ni, amma Daddy baya taɓa barin ta ta tafi dani gidan ta, haka kuma bai taɓa sakawa ta nuna ɓacin ran ta ba, saboda a gidan mu gefe na daban ne, in da ya zama na Mama na shi aka gyara mun, ina tare da masu mun aiki, so ko tazo ma takan iya wuni guda bata ga Matar gidan ba, a sake muke zama da ita. Basu bar mu mun rakasu airport ba, saboda yanayin jikin Amal, basu suka dawo ba sai wurin after 1, domin naji shigowan motan Dr Hussain. Da safe bayan mun yi wanka, sauri-sauri na soya mana egg muka sha Tea da bread da shi, haka muka fito domin tafiya school. A waje muka haɗu da Dr Hussain yana tsaye jikin motan shi, daga dukkan alamu mu ya ke jira, rufe ƙofan mu nayi, sannan muka ƙarasa in

Chapter 8 of 28