shugaban su.
Abba basu aka basu gawan ba sai wurin Asuba, inda Abba ya bawa shugaban su Baba Umar number Baban Narabi akan ya gaya mishi, da ƙyar yayiwa Baban Narabi bayanin rasuwa, wanda shi kuma Baban mai ƙarfin imani yayi ta godiya wa ubangiji, sannan yace su taimaka su taho mishi da gawan zuwa jos, yana son a rufe su anan, haka shugaban ya bashi tabbacin zasu aikata.
Shawara Dr ya basu akan a musu wanka a asibitin saboda ɗaga hankalin mutanen gidan, kuma su Abba sukayi na'am da hakan, ma'aikatan asibitin suka wanke gawawwakin, aka shirya su a cikin likkafani, sannan su Abba suka wuce gida domin sanar musu, tunda sukayi parking Abba ya kifa kanshi akan sitiyarin motan ya fashe da kuka, Kawu auwal ne ya saka hannu ya riƙo uncle Baba da ƙarfi ganin zai fita da gudu yaje ya tayar musu da hankali, zaunar da shi yayi yace, "ka zauna a motan bari na fara shiga".
Yana shiga ya tarar da dukkan mutanen gidan zaune zuru-zuru a parlourn, gefe ɗaya kuma Aunty hauwa ce kwance akan cinyar Mama sai kuka ta keyi, da sauri ta tashi ta nufi kawu auwal, jiki na rawa ta kamo hannun shi tace, "ka kaini wurin miji na yayah auwal, ina sukaje ne shida Aunty suwaiban"?, duk yadda yaso ya daure kawu auwal ɗin sai ya kasa, kawai samun kanshi yayi da fashewa da kuka ya rungume hauwa gam a jikin shi, Addagana ganin haka ya saka ta sunkuyar da kanta tana ta wasa da ƙasan hijabin jikin ta, ga wani haki da ta ke tayi lokaci ɗaya, Ummi ce ta matso jikin su tana tambayan kawu auwal, "ina sauran suke? Me yasamu Baba umar ɗin ne? Ya samu rauni ne sosai"?.
Buɗe ƙofan yasa hankalin kowa ya koma kan Uncle baba da ya kafe a wurin yana kuka kaman ƴa mace, da gudu Aunty hauwa ta je ta rungume shi tana, "ɗan'uwa na kai ne kafi kowa damuwa dani, nasan zaka gaya mun komai, don Allah ina mijina da ƴar'uwata? Sun koma gida lafiya ko"? Uncle Baba yana ɗaga mata kai yace, "tabbas mijinki da ƴar'uwar ki a yau sun koma gidan su na gaskiya, tabbas sun amsa ƙiran ubangijin mu a lokaci ɗaya, sun tafi sun bar mu da tsananin kewar su a zuciyar mu," ya saka hannu ya dafa shoulder Aunty hauwa ya cigaba da faɗin, "tabbas ƴar'uwata yau kam zuciyar ki ta ƙuna, yau kinyi rashi mafi girma a rayuwar ki, yau kam mun rasa jarumi, nagarin mutum Baba umar da matar shi, sakamakon harbi da iskan gari suka mishi a hanyar komawa gida, lallai sun jefa zukata dawa cikin maraici ƴar'uwata, Allah yajiƙan su da rahma".
Kumawa da baya da baya Aunty hauwa ta farayi tana bin uncle baba da kallo bakinta a buɗe, har saida tayi tuntuɓe da ƙafan mutum tukun ta tsaya, a hankali ta juya tana bin kowa da kallo, bata iya cewa komai ba bata cigaba da kukan ba, sai ido da take ta buɗewa kaman zasu fito su faɗi ƙasa, a hankali ta riƙe hannun Ummi tace, "Ummi Baba umar da Aunty suwaiba wai sun rasu? Wai sun mutu dukkansu yau, kinsan me Hero yace mun ɗazu? No baki sani bama, ni kaɗai na sani", sai ta sake hannun Ummi ta juya wurin Addagana da ta fara share hawaye da ƙasan hijabinta, har ƙasa ta tsuguna ta dafa ƙafan Adda tace, "Adda mijina ya rasu, baban ɗiyata wancar", ta nuna Aisha da ta kwanta a jikin sister Babanta da take ta kuka kaman ranta zai fita, sannan ta dawo da kallon ta kan Adda ta sake cewa, "mijina ya rasu yau, mijin na ya rasu shida suwaiba yau," sannan ta sake mikewa ba tare da ta furta komai ba, ta tafi gefen Mama ta kwantar da kanta a kafaɗan mama.
"Mama mijina ya rasu ya barni, idan mun tashi za a binne shi a kabari shi kaɗan shi, ni kuma za a dinga ce mun kiyi haƙuri," ta juyo da fuskar Mama da ta ke ta kuka kaman ranta zai fita tace, "bazan kula kowa ba, zanyi shiru ina kallon kuwa, hala mijina yaji tausayi na ya dawo, zan kwanta nayi bacci yanzu", ta faɗa bayan ta miƙe ta hau kan tree sitter parlourn ta kwanta.
Kowa da yake parlourn kallon Aunty hauwa ya keyi yana kuka na fitar hankali, don duk sun lura abun ya mata yawa ne, har ta rasa tunanin da zatayi, ita kuma Aunty hauwa rufe idon ta tayi gam, Ummi da sauri ta juya tana kallon kawu auwal da ya durƙusa a wurin yana kuka kaman ba shi ba, "auwal ina Abban su ne"? Ba tare da yace mata komai ba ya nuna mata hanyar waje, a guje Ummi tayi hanyar waje.
Bayan sun idar da sallan asuba Abba ya wuce asibiti shida uncle baba, acan suka haɗu da shugaban ƴan custume da wasu abokan Baba Umar, anan aka yi ta shirye-shiyen tafiya da gawawwakin, bau ɓata lokaci aka gama komai zuwa 9:00am, dukkan su suka shiga jirgi sai jos.
A chan Narabi kuma duk mutanen misau sun iso tun wajajen 9:00 na safe, an cika a ƙofar gidan Baban Narabi, ga mutanen tilde ma duk sun hallara, cikin gida kuma sai kuka mata sukeyi, inda Baban Narabi ya fito ta kofar parlourn shi ya zubawa ƙanwar mahaifiyar Baba Umar da take aure a cikin Narabin da ƙannen Baba Umar ɗin mata da suka rungumeta suna ta kuka kamar ransu zai fita, murya a hankali ya ƙira sunanta.
"Halima! Soyayyar da zaku nunawa Umar kenan? Irin Godiyar da zaku nunawa Ubangijin mu kenan? Don Allah kuyi haƙuri kuyi mishi addu'a don yanzu shi yafi buƙata a gareku, sannan ki kwantar wa yaran da hankali ga shi sun shigo gari da mamatan, kuma zasu shigo dasu cikin gidan domin muga fuskan Umar ɗan aljannah", ya ƙara faɗi muryan shi yana rawa, a hankali ɗan shi na biyu ya riƙe shi suka fita zuwa ƙofar gidan, domin jin tsayuwar mototi da yawa.
Har cikiɓ parlour aka shigo da gawan su Baba Umar, inda Baban Narabi yace maza iyayen Suwaiba da ƴan'uwan Baba Umar su fara zuwa su gansu su musu addu'a kafin mata su zo.
Ɗaɗɗaya aka dinga zuwa ana musu addu'a, tunda bawai fuskarsu aka rufe ba, duk wanda ya musu addu'a cikin ƙanne da iyayen Baba Umar sai sun zubar da hawaye, Baban Narabi ya sunkuya kan gawan Baba Umar Ya mishi addu'o'i masu yawan gaske, sannan a ƙarshe ya saka hannu ya share hawayen shi yace, "ya kai wannan ɗa mai yawan biyayya a gare ni, ina maka albishir da ni kam mahaifinka na yafe maka duk abinda kake tunani kamun da ga zuwan ka duniya Umar, halinka na gari ya bika har cikin aljannar fiddausi, Umar na yafe maka duniya da lahira, Umar ka tafi ka barni da tarin yawan kewar ka a zuciyata, amma Allahn da ya bani kai yafini sonka, Allah ya maka rahma kai da iyalinka", ya saka hannu ya shafa fuskan sanna ya miƙe ya koma kan kujera ya zauna yana jan charbi.
A haka iyayen suwaiba da ƙannenta da yayunta mata suka shigo suka mata addu'a, daga nan aka shigo da Aunty gauwa da ta ke rungume a jikin Ummi, da sauran ƴan'uwan Baba Umar mata da umma halima da su umman misau da su Mama, kuma har zuwa lokacin babu hawaye a fuskar Aunty hauwa, gefe ɗaya kuma ƙanwar shi na rungume da Aisha a hannunta.
Umma Halima ce ta sunkuya akan Baba Umar tana kuka, addu'an ma kasawa tayi, ganin haka Mama ta riƙo hannunta ta matsar da ita, tana ta bata haƙuri, Ummi ta riƙo hannun Aunty hauwa har gaban gawan suka durƙusa kusa da fuskar su, murya na rawa tace, "Hauwa kiyiwa mijinki addu'a, ki yafe mishi shi da ƴar'uwar ki.
Murmushi Aunty hauwa tayi tana kallon Ummi tace, "bai mun komai ba, na yafe musu gaba ɗayan su", "toh ki musu addu'a Hauwa" cewar Baban narabi daga inda yake zaune.
A hankali Aunty hauwa ta dinga yi musu addu'an samun rahma, sannan a ƙarshe ta miƙa hannu aka bata Aisha, ta dubi fuskar Aunty suwaiba ta dubi fuskar Aisha tace, "wannan maman kice ta tafi ta barki ba tare da ta jira girmanki ba, din naso kada tayi kukan rashin haihuwa irin yadda maman mu batayi, amma sai ta tafi ta barmu tun yanzu, Aisha mun yafewa Aunty suwaiba duniya da lahira, kuma zamuyita mata addu'a har ƙarshen rayuwar mu ko Aisha"? Sannan ta dubi fuskar suwaiba tace, "dama mutuwa zakuyi tare shine kuka mun wayo kuka tafi tare ku kabarni ni kaɗaiko?" ta shafa kan Aunty suwaiba tana share hawaye taja likkafanin ta rufe mata fuska, ƴan'uwan Suwaiba kuma sai kuka sukeyi ganin yadda hauwa ta yi, sannan Aunty hauwa ta juya saitin Baba Umar tace.
"Baba Umar ɗina, zan tamaka addu'a yadda kace, ban san da gaske mutuwar zakayi ba da na biyoku mun tafi tare, bansan me kake so nayi ba babu kai ka tafi kabarni, bayan Ummi zata kula da Aisha, Abba zai maye gurbinka a wurin Baban Narabi, me yasa kuka tafi babu ni? Sannan ta juya ta dubi Baban Narabi wanda lokacin muryanta ya fara rawa tace, "Baba nifa ina son mijina, amma yanzu kowa zai ta cewa mijina ya rasu nayi haƙuri, toh ta yayah zanyi haƙurin?" ta ɗago Aisha ta nuna mishi tace, "Baba sunanta marainiya, ni kuma maman marainiya, Baba ina zan rufe kaina na yita ƙiran mijina da ƙarfi har sai ya tashi? Ina so Baba Umar yaji tausayina ya tashi muyita zama, ni kuma nayita haihuwa ina bawa Aunty suwaiba har yara goma sha biyu, vazan gajji ba, yadda ta keso hakan zanyi," sannan ta dubi mutanen da ke parloun da suke ta kuka tace.
"kowa ya fita ya barni da su, zanyi ta xama dasu, idan sun tashi sai mu fito tare, amma ina son so, sukuma sun tafi sun barni, bazan iya ba Ummi, bazan iya zama babu su ba , Baba nah", ta kara sa tana kuka mai ƙarfin gaske, dukkan su ƴan parlourn kuka suke yi, hattah Baban Narabi kukan yakeyi bai hanata maganganun da ta keyi ba.
Bappah ne ya taso daga inda yake ya saka hannu ya ɗago ta daga kan gawan da ta kefe tana kuka, bai iya ce mata komai ba, ya miƙar da ita tsaye, suna haɗa ido ya dinga jijjiga mata kai alaman tayi shiru, bai iya cewa komai ba sai hawaye yakeyi, "Bappah miji nane fa kwance a ƙasa wai ya rasu, Bappah kuna nufin mun rabu kenan da shi har abada? Wallahi Bappah ina son mijina sosai, nifa yarinya ce, kaga gawan mijina, amma ka chan mijin Ummi shi bai rasu ba sai nawa, Bappah kai ma fa ka tsufah kaida Baban Narabi amma duk kuna nan sai mijina da bai tsufah ba", ta rungume Bappan tana kuka mai ƙarfi.
Liman ne ya bada umurnin a fitar da gawawwakin, ana ɗaga su za'a fita Aunty hauwa ta ƙwala ƙara ta faɗi a wurin a sume, lokaci ɗaya kuma Aisha ta saka kuka mai figitarwa, tana kallon Abba tana "Dada, dada".
*KULLU NAFSIN ZA'I KATUL MAUTI, TABBAS DUK MAI RAI SAI YA ƊANƊANA ZAFIN MUTUWA, HAKA SHI ZAFIN MUTUWA BAYA FITA A ZUCIYAR MU DUK TSAWON SHEKARU, WAYYO MUTUWAR MIJI AKWAI CIWO SOSAI*
*FAUZIYA A.A, WANNAN SHAFI NAKI NE, DOMIN TUNAWA DANAKEYI NA ZAFIN DA KIKAJI NA RASUWAR MIJINKI ALIYU BABAGANA ZAKI(ABBA)*
*TUNDA NA FARA PAGE ƊIN NAN KE KIKE FAƊU MUN ARAINA, INA JIN RAƊAƊI A XUCIYATA KAMAR YAU MUKA SAMU LABARIN RASUWAR ABBA, ALLAH YA JIƘANSHI YA MISHI RAHMA, ALLAH YA ƘARA MANA HAƘURI AKAN RASHIN MAZAJEN MU, IYAYEN ƳAƳAN MU, ABIN AƘFAHARIN MU* 😭😭😭😭😭
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/19, 12:27] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 37📑*
*__________📖* Kowa kaga idon shi a gidan zaka san ba ƙaramin taɓa su mutuwan tayi ba, ko wani ɗaki ka shiga bazaka ga ana surutu irin na gidan rasuwa ba, kowa zaka ganshi yayi jigum, wasu hannun su rike da charbi, wasu kuma suna karatun qur'ani, ɗaiɗaiku ne kawai zaka ga suna magana ƙasa-ƙasa, amma duk da haka wanda sukayi shirun sun fi yawa.
Ɗakin mahaifiyar su Baba Umar nan aka buɗewa Ummah halima da ƙannen Baba Umar mata, da ƴan'uwan Aunty suwaiba, sannan akwai wani ɗaki a gefen shi, shima ciki ne da parlour, nan aka ajiye Aunty hauwa da ƴan'uwanta.
A ƙofar gida kuma tun Baban Narabi da Bappah suna rarrashin Abba har suka gajji suka zuba mishi ido, sai addu'a kawai suke mishi a zuciyar su, uncle Baba ma gaba ɗaya ya shiga wani yanayi, da yake shiɗin dama mai rauni ne, ko gaisuwa aka musu sai ya share hawayen shi, a na ɗan ɗaukan wani lokaci kuma zai tashi ya shiga har ɗakin da Aunty hauwa ta ke zaune, har gabanta yake ƙarasawa ya tambayeta ko tana son wani abu? amma haka cikin kuka ta ke nuna mishi bata buƙatan komai, haka zai fito jiki a sanyaye.
Aisha kuma gaba ɗaya sai kukan rikici ta keyi wa mutane, firr ta ƙi karɓan kowa sai nida Hassan, idan taji yunwa mu haɗa mata tea tasha, mu sake fita da ita, nono kam zan ce a ranan bai fi sau uku muka kaita ta sha ba, shima tana sha, ƙafanta yana ɗaure akan cinyan ɗayan mu, saboda kada mu gudu mubarta.
Idan muna zaune a waje kuma duk yadda mutane abokanan Babanta suka zo, zasuyi tazo wurin su sai ta ƙi, idan kaga ta karɓi mutum toh daga ni da Hassan sai Abban mu, sai kuma Baban Narabi da wani ƙanin Baba Umar mai masifar kama da shi, duk inda yabi zaka ga tana ta bin shi da kallo, idan ya karɓeta kuma kuka zai fara, ya kifa kanshi akan ta yayita kuka, dole zakaji Baban Narabi yace, "Abdallah! Na haneka da zubar da hawaye wa ɗan'uwanka, shin ba addu'an mu Umar yafi buƙata ba? Don Allah ayi haƙuri da kukan nan, baka ga ita kanta Aishan kuka kuke sakata ba"? Haka Uncle Abdallah zai share hawayen shi, ya kuma kasa riƙe Aishan saidai ya miƙo mana ita, amma yana barin wurin kuma zata fara kuka, a dole Abba yace mu koma cikin gida da ita.
Rayuwa babu wuya, a kwana a tashi kwana sai tafiya yake tayi, yau har an wayi gari Baba Umar ya cika sati ɗaya da rasuwa, inda kowa ya fara shirin tafiya.
Baba Umar shine babba a wurin mahaifiyar su da mahaifin su, sannan aka haifi mace tukun Uncle Abdallah, sannan aka sake haihuwar wata macen, a lokacin kuma Baban Narabi ya ƙara aure da wata ƴar cikin Narabin, inda suka sake haihuwa tare da mama Aisha, bayan ta haifi yara mata guda biyu, wanda ƙaramar su itace sa'ar Aunty hauwa, wacce taje musu hutu lagos, wato indo, a haihuwarta maman su Allah ya karɓi ranta, inda aka maida sunan maman su.
Aunty Amina ita ke bin Baba Umar wanda yanzu ta ke aure a cikin jos, sai uncle Abdallah, sai Aunty Hadiza wanda ita ma ta ke aure cikin garin jos ɗin, sai mai bi mata kuma Aunty Umaimah, wanda ta ke aure a cikin garin bauchi, duk cikin su mijinta yafi wadata sosai, sai ƴar auta kuma Aunty indo, wanda itama ake shirin auren ta kwanan nan, da wani ɗan Azare, amma mazauna garin kano, shiɗin kuma abokin uncle Abdallah ne.
Ɗayan ɗakin kuma, wanda take amaryar Baban narabi mai suna Baba kaltum, tana da yara guda huɗu, babban su shine, uncle sabo, wanda shi sa'an Aunty umaima ne, sai mata uku da suka biyo bayan shi,Aunty asma'u, Aunty Nana khadija, Aunty Zahra, duk gidan basu da irin halin ƴan ubancin nan, don ko kaɗan Baban Narabi bai yadda da wannan a gidan shi ba, shi mutum ne mai tsayin daka a gidan shi sosai,.
A ranan su Bappah suka koma misau, inda Bappah ya gana da Baban Narabi cewa Aunty hauwa idan tayi 40dys za su maida ita gida, amma Baban Narabi bai amince ba, lokaci guda hawayen da ya daɗe yana ɓoye su cikin mutane suka fara zuba, yana duban Bappah yace, "Ni da nafi son tayi takabanta gaba ɗaya a ɗakinta, yanzu haka shawaran da muka yanke da ƴan'uwan Umar zata koma gefen shi Umar ɗin, zasu tafi da Indo,da kuma mata biyu wanda zasu tayata zama, kaman ɗaya daga gefen ko, sannan ita ma Uman shi tace zata zauna dasu har su gama takaban, amma idan kace zaku ɗauke ta sai maga kaman akwai kasawan mu", ya ƙarasa maganan hawaye yana zuba mishi babu kakkautawa.
"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wallahi ba haka nake nufi ba, amma tunda kun shawarta hakan babu komai, dama ita Maman suce zata zauna tare da ita, saboda haka duk yadda kuka tsara ɗaya ne ae, ae ko babu Umar ae munzama ɗaya, ga Aisha a tsakani", Bappah ya faɗa cikin yanayin shi na nutsuwa.
Haka sukayiwa Aunty hauwa sallama tana kuka suka tafi dukkan su, gidan yazama babu kowa sai mu, wanda muke shirin tafiya gobe, a ranan muka koma da Aunty hauwa gidanta, da yake tun kwana biyu su Aunty hauwa sukaje suka gyara gidan tsaf, ranan da aka koma Aunty hauwa da su Ummi na sun yi kukan rashin Baba Umar ba kaɗan ma.
Washe gari tun safe muka tafi domin zuwa airpot, Aunty hauwa tayi kuka lokacin da zamu tafi, rungume Ummi tayi tana ta kuka, gefe ɗaya kuma Umma Halima da Mama sai haƙuri suke bata, ita kuma Ummi bata iya cewa komai sai kukan da ta keyi, don zan iya cewa Ummi na tayi kukan da ko Aunty hauwa batayi shiba a rasuwan nan, domin cewa ta keyi, ciwon hauwa ae nata ne, kukan haiwa shima na ta ne, Abba fita yayi bai musu sallama ba, domin bazai iya ba, amma ya bada kuɗi mai yawan gaske a hannun Mama akan idan ya tafi ta bawa Aunty hauwa, suma su Maman da Umma halima ya basu masu yawa.
Lokacin da muka ajiye Aisha a parlourn zamu tafi, kuka ta fara nida Hassan sai muka kasa fita, muma kukan muke tayi muna tsaye muna kallon ta, a haka uncle Abdallah yayi sallama ya shigo, ganin kukan da mukeyi sai ya ɗauki Aisha da ganin shi ya sata tayi saurin hawa jikin shi ta kwanta tana ta ajiyan zuciya, hannun shi ɗaya ya saka ya riƙo mu muka fita waje inda motan uncle Abdallah ta ke, wanda dashi za' a kaimu airpot, uncle sabo ne zaune a mazaunin driver Abba yana gefen shi.
Muna tafiya Uncle Abdallah ya koma parlour ɗauke da Aisha a kafaɗan shi, zaunawa yayi suka gaisa da su Umma halima da suke ta share hawayen su, gefe ɗaya kuma Aunty hauwa ce a tsugune a ƙara ta rungume ƙafan Mama tana ta kuka mai ƙarfin gaske, kaman zuciyata zai fito.
Runtse idon shi yayi da ƙarfi na zuwa wani lokaci kuma ya buɗe su akan Aunty hauwa, ya daɗe yana duban ta kaman bazaice uffan ba, chan kuma ya ƙira sunan ta a hankali, " *HAUWA*"! bata amsa ba amma ta rage sautin kukan, bai sake cewa uffan ba har zuwa wani lokaci da yaji sautin kukan nata ya ragu sosai.
Juyawa yayi ya dubi Umma halima yace, "Ummah ku ae haƙuri zakuna bata bawai idan kunga ta fara kuka kuma kuyita tayata ba, kukan rashin Yayah Umar idan muka ce yin shi zamuyi tayi, toh ina mai tabbatar muka har mu koma ga rabbana bazamu daina ba, domin shi ya zama mana wani jigo acikin rayuwar mu, kuma wani haske ne a cikin zuciyar kowanmu, toh manta shi a zuciyar mu abune mai matuƙar wahala, kuka bashi bane mafita addu'a ne zai zama muna mishi", yayi shiru yana bin kowa da ido, wanda umma halima tana share hawayen ta tana ta amsa mishi da hakane, daga nan ya juya yana duban Aunty hauwa a hankali yace, "Hauwa kina jina"? ɗaga kai tayi alaman taji, sannan ya ci gaba da kwantar musu da hankali yana ta nuna musu ƙarfin addu'a da haƙuri shi zai rage musu zafin a zuciyar su.
Nasiha sosai ya musu sannan ya miƙe ya tako har gaban Aunty hauwa ya sunkuya hannun shi riƙe da Aisha, jin ƙamshi turaren shi ya saka Aunty hauwa ɗago da kanta ta dube sho, zuciyarta ya buga da ƙarfi domin tsananin kaman da sukayi shida Baba umar, bambanci kawai yafi Baba Umar tsawo da farar fata, sannan Baba Umar mutum ne kowa ga fara'a da mutane, amma shi kuma Abdallah sai ya so ya ke kula mutane, kuma kullum fuskar shi a ɗaure ta ke tamau, baya wasa da kowa, a hankali ta mayar da idon ta ƙasa jin wani hawayen mai zafin gaske ya taho mata, don hattah muryar su iri ɗaya ne da yayan shin.
Miƙa mata Aisha yayi akan ta karɓeta, amma firr Aisha taƙi yadda kuka ma ta fara mishi alaman bazata je ba, ganin haka yayi murmushi ya lakuce kumatun Aishan, sannan ya dubi Aunty Hauwa yace, "toh bata nono tasha sai mutafi gidan Baban Narabi", girgiza kai tayi alaman bazata bata ba.
Hararanta yayi murya ƙasa-ƙasa yace, "dole kuma ki bata tasha abincinta, ko na ɓata miki rai", ya faɗa babu wasa a fuskar shi, ganin haka Aunty hauwa ta turo bakinta gaba ta miƙa hannu ta karɓi Aisha, sannan ta dube shi ta gefen ido tace, "toh ka tashi a kusa da ni mana", ta ƙarasa maganan tana murguɗa baki kaman zatayi kuka.
Kallonta yayi na wasu seconds, sannan ya miƙe ya koma gefen Umma halima ya zauna suka shiga magana da shi, wanda da wuya ka dinga jin muryan shi idan yana magana, kawai sai dai kai da kake hiran da shi ne zaka dinga jin muryan shin, ita kuma Mama tashi tayi ta wuce kitchen wurin Indo domin ta yata ɗaura abincin rana, wanda tun jiya Uncle Abdallah ya cika store ɗin da kayan abinci.
Hijab ɗinta ta ɗaga ta saka Aisha a ciki ta fara bata nonon ta cika, sannan kuma duk bayan wasu seconds sai ta share hawayenta, duk abinda ta keyi a fakaice Abdallah yana kallon ta, kuma zafin kukan da ta keyi ya keji, suna haka har Aisha ta sake nonon ta ɗago da kanta da ya cika da zufa tana kallon Abdallah, da gwalantayin ta ce ,"Dada"! Da sauri ya dubeta yana tambayan Aunty hauwa wai me ta ke faɗa ne?
Kallon Aishan tayi cike da tausayi tace mishi, "wai Daddy ta ke ce maka, halan tana maka kallon Baban ta ne", ta faɗa tana cigaba da share hawayen tan, hararan ta yayi yace, "dama waye idan ba Daddyn ta ba? Ni yarinyar nan ma da wuri zaki yaye ta ki bani ita, don naga baza ki iya kula mun da ita ba", ya faɗa yana miƙawa Aisha hannu ganin ta taho da gudu wurin shi tana buɗe hannu alaman ya ɗauke ta.
Hararan shi Aunty haiwa tayi sannan tace, "Daddyn ta ranan da zai rasu yace ya bawa Ummi ita kyauta duniya da lahira, kuma yace a barta tasha nono sosai, saboda haka ni bazan baka ƴata ba, bayan baka da mata, kuma ni bazan yayeta da wuri ba", ta faɗa tana share hawayenta.
"Wannan kuma tunaninki na shirme kikeyi, ke zaki hanani auren ne? Zan ɗauki ƴata, don yayah haifa mun yayi ya tafi ya bar ni da ita, kuma bazan barki da ita ba don naga baki san yadda ake renon yara ba, don kema baki wuce rainon ba", ya faɗa yana miƙewa tsaye, dai-dai lokacin indo ta shigo parlourn tace.
"Yayah Abdallah da gaske nima ina zaune a wurin yace yabawa Abban kyautar yarinyar shida Ummi, kuma yace kada a yaye mishi ƴar shi da wuri", hararanta yayi yace, "ina wasa dake ne? Nawa Haiwan ta ke da za abarta da yarinya"?.
Tsaki yaja, sannan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 28