ta samu Dr da Aunty suna cin abinci, yana dubanta yace, "amaryah kinci abinci kuwa"?.
Hararan shu tayi bata ce mishi komai ba tayi hanyar waje, tana fita yayi murmushi ya dubi bayanta yace, "zama ki ɗame ae", suka cigaba da cin abincin su shida matar shi, wanda ta ke ta mitan ya dinga bin ta a hankali da lallaɓi, bawai yayita ɓata mata rai ba, shidai dariya kawai ya keyi bai ce mata ƙala ba.
Tana shiga office ta samu wanda zasu karɓe su suna shirin tafiya, gefe ta samu ta zauna, bayan sun gaisa taji wayanta yana ringing, da sauri ta fito da shi kawai sai taga Baban Narabi ne, jikinta yana rawa ta ɗauka sannan ta miƙe ta bar office ɗin tayi waje.
Bayan ta gaishe shi ne ya fara mata maganan yadda auren ya taso sannan ya bata haƙuri na gaggawan da aka mata, Aunty hauwa ce mishi tayi babu komai ae sun isa da ita ne, amma tana maganan tana kuka, jin haka yasa Baba yayita saka mata albarka daga baya yayi mata nasiha sosai, wanda har saida sautin kukanta ya dinga fitowa, suna gama wayan ta ƙira Ummi har lokacin kuka ta keyi, itama Ummin haƙuri tayita bata tana rarrashinta da kalamai masu daɗin gaske, wanda Aunty hauwa ita kuma tayita mitan yayah zata iya zama da Abdallah bayan ya raina ta, itafa matar yayan shu ne kawai din raini yazo ya aureta?
Ita dai Ummi haƙuri ta ke bata chan ƙasa-ƙasa kuma tana dariyan hauwan da ta je ta maganan wai ya rainata, haka suka gama maganan Aunty hauwa ta koma ciki, nan kuma an kawo masu haihuwa har mutum uku, dole ta zage ta fara aiki.
Tunda Abdallah yaji an ɗaura mishi aure da hauwa, farin ciki ya taso shi gaba, jiki na rawa ya ƙaraso gida wurin Baban shi, inda shi kuma Baban ya fara mishi nasiha da yayi adalci a tsakanin matan na shi, kuma ya gaggauta gayawa fadilah abinda ya faru, sannan ya mishi nasiha sosai.
Abdallah yana fita a parlourn Baba ya ƙira fadila, cikin nutsuwa ya mata bayanin komai, amma abin mamaki bata nuna mishi damuwarta ba, kawai fatan Allah ya basu zaman lafiya tayi, daga baya ta tambaye shi yaushe zai dawo zaria? Jiki a sanyaye yagaya mata zuwa gobe ko jibi, haka sukayi sallama ya shige motar shi yayi cikin garin jos gidan Aunty Amina.
Washegari da safe Abdallah ko karyawa bai yiba ya kama hanyar garin bauchi, amarya tayi ƙira, tunda yaje yake ƙiran wayarta amma firr taƙi ɗagawa, yananan ƙofar gidan saiga Dr ya fito wurin 9:00am zai wuce office, mamakin ganin Abdallah yayi a kofar gidan, cikin mamaki yace, "Hauwan bata san kazo bane?" ya tambaye shi da sauri, yana murmushi kanshi a ƙasa yace, "yanzu na iso ina shirin ƙiranta kenan", Abdallah ya faɗa yana ɗaga wayan shi alaman zai ƙirata.
Da sauri Dr ya koma ciki, inda ya tarar da Aunty hauwa a tsaye gaban dinning tana tattare kayan da yayi breakfast da su, "mantuwa kayi Dr"? "babu wallahi, kawai na fita sai naga mijin yarinyar nan Abdallah tsaye a ƙofar gidan, daga dukkan alama ya nemeta taƙi fitowane, don daga gani ya daɗe a ƙofar gidan", ya faɗa yana wucewa zuwa ɗakin su Aunty hauwa, daga ƙofar ɗakin ya tsaya yana ƙiran sunan ta, amma firr tayi shiru kamar mai bacci taƙi amsawa, ganin haka Aunty uwani ta shiga.
Ganin bazata fitoba yasaka shi shiga ɗakin ranshi a ɓace, kaman zai wanka mata mari yake mata masifah, "ke hauwa wa kika ɗauka yaronki ne a gidan nan? Kinsan Allah idan raina ya gama ɓaci bansan me zan miki ba, banzar yarinya mai masifar tsiya, ke har kin isa iyayen mu su zartar da abu kidawo kina nuna basu isa ba? Ke wacece? Wuce kifita kije wurin mijinki kafin na nuna miki ɗayan halina ɗin".
Fuska a ɗaure ta fita wurin Abdallan, shi kuma Dr yazo ya mishi tasss akan kada ya fara sakewan da Hauwa zata raina shi, gara ya rage nuna mata damuwan shi akanta kafin raini ya biyo baya.
Tsayawa tayi a gaban motan sai cin magani ta keyi tana harare-harare, tsayawa yayi na wani lokaci yana dubanta, chan ya koma Abdallan shi yana dubanta fuska a murtuƙe yace, "nifa bana son rashin hankali, hakan yayi miki mutunci kizo gabana kina wani jiye-juyen jiki kamar ke kaɗaice mace a duniya? Ko kuma haka aka ce miki ana taryan baƙo? Toh ni bazan ɗauki rainin hankali ba", ya faɗa mata fuskan shi a murtuƙe, da sauri ta juyo da ɓufin ta maida mishi martani, amma ganin fuskar shi ya sakata juya da fuskarta gefe tace, "toh ni nace maka kada ka shigo ne,? Ni ae jira nakeyi ka shigo", ta faɗa tana ta murguɗa bakinta ta gefen shi.
"Nidai koda wasan wasa kada ki nemi raina mun hankali, maganar auren nan nayi ne don samun kwanciyar hankalinki gaba, amma k8na ta wani nuna isan ke wata ce, bayan na samu Baba nace mishi bana son maganan abarki ki auri wanda ki ke ganin kun dace amma firr ya tafi akan maganan, ni bana son nunawa iyayena ban haihu ba a wurinsu shiyasa na amshi buƙatun su da hannu bibbiyu, amma hakan bazai saka ki raina mun hankali ba don ina da wacce ta fiki komai a gida", ya faɗa yana tafiya hanyar shiga parlourn.
Baki a buɗe ta bishi da kallo cike da mamakin shi, tana tambayar kanta dama ba wai sonta yake ba? Har yana nufin matar shin tafita komai da komai, kodai don ita matar shi yana sonta ne yake ganin ta haɗu? amma ita dai taga photon matar da ta je gidan Umaima, kuma bataga ta fita komai ba, banda ma wani bleaching da ya ɓata mata fuska gata gajeruwa lukuta sosai, tsaki taja ta bi bayan shi zuwa parlourn.
Gaisawa ta samu su nayi da Aunty uwani, itama ta nemi gefe ɗaya ta zauna, har Aunty uwani ta fita bata ɗaga kai ta dube shi ba, shi kuma babu abinda yakeyi sai kallonta, domin ba ƙaramin shiga ranshi tayiba, shiru zuwa wani lokaci yace, "ke kam Hauwa baki ɗauki halin kirki irin na ƴan gidanku da iyayenki ba, amma har yaushe baki san yadda ake mutunta baƙo ba, ballantana kuma ina da ƙarin darajar matsayin miji a gare ki, kina son albarka kuwa"? Ɗago kai tayi tana duban shi, murya cike da sonyin kuka tace, "ba kai bane kace dole aka maka ka aureni, kuma wai ban kai matar ka komai ba, kuma wallahi na gani na fita kyau, kawai faɗa ne baza kayi ba don ita kana sonta", ta ƙarasa faɗi kaman zatayi kuka.
Dariya yayi yana dubanta cike da nishaɗi a ranshi yace, " kin taɓa ganin inda aka fi son wata mace sama da uwargidan ka? Toh ki daina ruɗin kanki matar farko baka ganin wacce ta fita a komai, ballantana wanda kukayi soyayyah kana sonta tana sonka", ya ƙarasa yana gyara zaman shi.
Turo baki tayi gaba, " hmmm nidai nasan Hero duk da a ta biyu ya aure ni yafi sona akan Aunty suwaiba, kuma kullum ce mun ya keyi ina da kyau, saboda haka nasan ni mai kyauce, don muna secondry school *Hauwa golden girl* ake cemun", ta faɗa tana jujjuya idonta.
Kallonta ya tsaya yanayi a cikin zuciyar shi yace, "wato duk matar mamaci magana ɗaya sai ta kwatanta da mijinta ko? toh yanzu don Allah idan da ba don ɗan'uwan shi bane da yaya zaiji a ranshi?" a fili kuma yace, "shiɗin ae ya aure ki yana sonki ne duk da ma ance Abba ne ya tura mishi ke, shi kuma yayi biyayyah ya karɓa kaman yadda nima nayi yanzu, shi kuma bansan dalilinshi na ganin kyaunki ba? nikan bana gani gaskiya, ko dan banji ina sonki bane ohoo", ya faɗa yana wani ya mutsa fuska.
"Wallahi baka isa kace mijina baya sona ba, don ni nafi kowa sanin irin son da yake mun, kaidai da baka sona kai ka sani, don ni ban maka dole ba, idan baka so akwai mai so kabar mishi ni kawai zai fi mana zaman lafiya", ta faɗa tana share hawayenta.
Dariya yayi yace, "nima haƙuri zanyi don kada iyayena suga ban mutunta su ba, amma ke idan kinga zaki nunawa duniya iyayenki basu isa da ke ba, toh kiyi gaggawan taimaka mana ki gaya musu baki sona, ko nima zan samu kwanciyar hankali".
Shiru tayi na zuwa wani lokacin, sannan ta dube shi baki ta murguɗa mishi tace, "da yake nice wanda akace jeki kya gani ko? wanda bansan darajan iyaye na ba, toh bazan faɗan ba, kai da baka son kaje ka faɗa".
Miƙewa yayi yana zurma hannun shi cikin aljihun shi yace, "nidai babu ruwana ban iya jayayyah da yayuna bama ballantana iyaye na ba, ke kuma na barki lafiya da halinki na rashin mutunta baƙo, zanje gidan umaimah nayi breakfast na wuce, domin gobe da safe xan wuce Zaria wurin my luv ɗita", yana dariya ya ajiye mata kuɗin da yakai 20k a cinyarta yace, "ki dinga transport kafin na dawo ko".
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/28, 14:26] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 41📑*
*INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, MISS XERKS, NEAT LADY, INA MUKU TA'AZIYYAH DA WANNAN RASHI DA AKA MUKU, ALLAH YA JIƘANTA DA RAHMA, ALLAH YASA TA HUTA*
*__________📖* Duk yadda Aunty hauwa taso ta dinga ƙuntatawa Uncle Abdallah abin ya gagara, domin ya riga da ya tsare gida baya ɗaukan raini ko kaɗan, duk bayan sati biyu yake zuwa dubata, kuma kullum da irin rikicin da akeyi a tsakanin su, shi zaice sai ta bishi inda ya sauƙa, ita kuma ta dinga surutun ya raina ta kenan, haka za'asha dirama a tsakanin su har ya koma.
Wani ranan jumma'a Abdallah yazo Narabi inda ya samu Baban su ya tashi babu lafiya, duk hankalin ƴan gidan a tashe, haka ya ɗauke shi da uncle sabo suka kaishi asibiti a cikin jos, don Baban su bai cika son zuwa asibiti ba shiyasa yaƙi faɗawa kowa bayida lafiya, suna zuwa a ka basu gado, domin an tarar yana ɗauke da hypertension, ga kuma diabetics, duk hankalinsu ya tashi, inda Aunty Amina da Aunty hadiza da suke zaune a jos duk suka hallara a cikin asibitin.
Da yammah Uncle Abdallah ya ƙira Aunty hauwa yake gaya mata suna asibiti da Baba shi yasa bai samu daman ƙarasowa ba, jikinta a sanyaye ta gaishe da jikin Baban, kuma tace mishi gobe insha Allahu zata zo ta duba shi da jikin, bayan sun gama wayan ne ta gayawa Dr Alƙali da Aunty uwani da suke zaune a parlourn tare, Dr yace "babu komai suma zasuje idan yaso sai su dawo a goben ita kuma ta kwana", turo baki gaba tayi tana duban Dr tace, "mu dawo dai tare yayah, ni kuma kwanan me zanyi a can, kawai mu tafi tare mu dawo tare".
Dariya yayi a hankali yace, "Hauwa problem", Aunty uwani dariya tayi tana, "ni dai bansan me yasa kike gudun wannan haɗaɗɗen mijin naki ba, gaskiya hauwa ki gyara halinki da ɗabi'un ki, idan ba haka ba za'a ƙwace miki miji da gaggawa",.......turo baki tayi a hankali tace, "ba sai a ƙwace ba ni na damu da shi ne, yaje chan su ƙarata da buskuɗan matar shi", ta faɗa bayan ta tashi ta kama hanyar ɗaki tana ta mita.
A chan asibiti kuma bayan anyi sallan magarib mama kaltume suka zo tare da uncle sabo a motar uncle Abdallah tare da Nana khadijah da Zahra, don Aunty indo da Aunty Asma'u tare akayi auren su, yanzu kusan shekara 2 kenan, yanzu haka maganan auren Nana khadijah akeyi, suna shiga ɗakin Zahrah ta ƙarasa gefen Baban ta zauna bayan ta riƙe hannun shi, cikin shagwaɓa da nuna ita ɗin auta ce tace, "Baba da wai mama tace baza a zo dani ba, ni kuma nayi ta kuka tukun yayah sabo yace suzo da ni, amma Nana khadijah kam don baƙin hali zuga mama tayi wai kar azo dani, Baba don Allah a airar da ita na ɗan huta".
Ganin autar ta shi ya sauƙar mishi da farin ciki, yana duban ta cike da so da ƙauna yace, "Duk yadda kikace haka za'ayi Fatin Baba, nima na gajji da zama dasu, na fi so gidan yazama daga ni sai ke nayita saya miki abinda kike so, kina walwalanki yadda ya kamata", sannan ya juya gefen Mama kaltum da Nana khadijah yace, "ina mai jan kunnen ku akan autata, na sake jin wani ya ɓata mata toh ni dashi a gidan nan, ke kuma Khadijah tunda kina takura mun yayata danafi so a duniya Nana Fatima toh zan dawo da ranan auren kin baya idan yaso ayi ta samu sakewa" ya faɗa yana hararan Khadija da wasa.
Murmushi Zahrah ta farayi tana gwalo wa Nana Khadija, Mama kuma ta kai mata ranƙwashi tace, "ke ɗin tabbata zakiyi ae a gaban Baban naki ko? Toh ki shiryah ke kam ma baɗi war haka ana shirin kaiki nako gidan, ki bar ma murna", dukkan su ɗakin dariya sukeyi na rikicin Zahrah da Babanta, Aunty Amina tana kallon Zahra cike da kulawa tace.
"Autar Baba Umaimace fah mai sunan maman Baba, amma ke kuma sunan yayarshi kikaci amma yafi ji da ke, kodai don kin zamo auta ne aka fi son ki"? Ta faɗa tana bin ta da murmushi.
Baba tashi yayi ya zauna yan bin ƴaƴan shi da kallon so da ƙauna yace, "Adda na Fatima ta nuna mun ƙauna, lokacin da take makaranta duk kuɗin tara idan an bata bazata sayi komai taci ba sai tayi ta asusu, idan kuɗin ya taru zata ɗauke ni ta tafi dani kasuwa duk kayan dana ke so zata saya mun, lokacin aurenta kukan ta na rabuwa dani ne bawai na tafiya tabar iyayenta ba, ranan da za'a kaita gidanta da yake garin toro sukayi hatsari ita da wata goggon mu Allah ya karɓi ransu a wannan lokacin, mutuwar ta taɓa mana zuciya ba kaɗan ba, wanda ni har gobe na tuna sai nace zafin danaji yafi na mutuwan iyayena ma, naso tun haihuwar Amina na saka sunanta, amma sai mahaifin mu ya umarce ni da saka sunan jatumar shi, Hadiza kuma ya umarceni da saka sunan kakarku ta wurin uwa, umaima kuna na saka sunan tawa mahaifiyar, haihuwar indo kuma yazo da rashin mahaifiyar ku wanda dole sunan ta ya chanchanta na saka, da na haifi Asma'u kuma na saka sunan goggona wanda suka rasu tare da Adda fatima, Nana khadija kuma nayi karawa Maman ku kaltume na saka sunan nata mahaifiyar, kinga autata taci soyayyah uku, na farko sunan Adda na, na biyu sai ta ɗauko kamnnin Adda na ɗin, shiyasa suke ɗibi da Umar da Abdallah, sannan na uku kuma autata, kunga dole ta zama aminiyata".
Gaba ɗaya dagowa sukayi suka dubi Baba suna dariyan yadda ya ƙarasa maganan shi cike da zolaya, Uncle Abdallah da tunda ya zauna bai tanka musu ba sai lokacin ya dubi Baban su yace, "Baba insha Allahu idan na haifi yara zan saka sunan yayah Umar da sunan Fatima, domin na ƙara faranta maka, don na lura baka haɗa son su da kowa a duniyan nan, ni kuma insha Allahu zan sake faranta maka da maimaita sunan su a ƴaƴana".......murmushi Baba yayi yace, "kaiɗin daban kake acikin ƴaƴana Abdallah, tun kana yaro burinka ka dinga faranta mun, kaima ina maka Addu'a Allah ya faranta maka duniya da lahira, tabbas ina jin Umar da Zahrah a zuciyata daban a cikin ƴaƴana, saboda sunan wanda suka ci a zuciyata, haka Indo ita kuma nafi jin tausayinta sama da kowa a cikin abinda na haifa, shiyasa babu garin Allah da zai waye ban ƙirata naji yayah ta tashi ba acikin ku, duk ranan da ban kira ta ba sai naji kaman nayi rashin wani abu a tare dani, dukkanku ina sonku kuma kowa da irin rawan da yake takawa acikin ku, Allah ya muku albarka da zuriyar ku gaba ɗaya".
Aunty Hadiza ne ta dube shi tana murmushi tace mukan bansan me muke takawa ba a cikin ƴaƴan, don Baba baka cika faɗin abu akaina ba," ta faɗa kowa tana mata dariya, don duk tafiso ɗan zafi kaɗan, toh abu kaɗan sai ya tunzurata.
Gyara zaman shi Baba yayi fuskar shi ɗauke da murmushi yace, "Umar, Amina, sabo duk cikin yarana ba masu haƙuri da zumunci irin nasu, ke kuma Hadiza duk kinfi kowa son nuna mun ƙauna keda Abdallah a cikin yarah na, kuma kunfi kowa nuna tausayawa a al'amurana ku ɗin kuna da wani shashi na musamman a raina, wanda bana haɗaku da kowa, kuma araina inaji idan daku kowa baziyi maraici ba dije na.
Uwata umaima kuwa ita da Nana khadija, babu masu kawo farin ciki da walwala a cikin gida na irin su, wani lokacin idan suna raha da zolaya a cikin gida na sai naji anya akwai wanda nakejin son su irin waƴannan biyun kuwa, domin basu bar kowa ba, bani ba ba manaku ba wurin zolaya da neman magana, su ɗin kurwan gidana ne, idan babu su cikin gidan sai kaji maraici ya isheka, shi yasa da umaimah tayi aure sai danayi zazzaɓi, haka yanzu maganan auren Nana khadijah, idan na tuna sai naji kaman na bita gidan ta mu zauna kawai, don gidana zaiyi maraicin masu raha a gidana", yana faɗa Nana khadija tayi tsalle tace.
"yehhhh daga dukkan alamu Baba yafi son mu nida Aunty umaima," ta juya tana duban Zahra hannunta riƙe da ƙugunta ta karkace tace, "auta ki kiyaye ni kinemi sulhu dani, don daga dukkan alamun bayanin Baba bawai sonki yafi ba, kawai kinci darajan wasu ne, ni kuma tsantsar sone yake mun, don yace gidana ma zai bini", ta juya tana kallun Baba tace, "Baba yanzu zan gayawa mahmood ya nemi gida mai ɗaki uku, domin kaima tare zamu taho, kuma kasan wani abu ma Baba? Saboda kai zan daina baccin safe na tashi na maka ƙosai da kunu don ka karya, shima kaga zai samu kulawa saboda kai", ta faɗa tana ta rawan ta kaman ba a asibiti suke ba.
Duk yadda Uncle Abdallah yakai da ɗaure musu fuska amma sai da yayi dariya yace, "mama dama hankali bai wadaci Nana khadijah ba? Yanzu anata haukan sai fa tagaya wa mijin nata tare da Babanta zasu taho"?.
Dariya Baba yayi yace, "kai baka san umaima dole na lokacin da tayi aure ba nake zuwa bauchi gidanta? Ina zuwa zata gyara mun ɗakin su na parlour tace Baba yau fa agidana zaka kwana, haka zan ta lallaɓata da ƙyar zata haƙura na tafi, lokacin da ta haifi ɗanta na fari, naje ina riƙe da ɗan, kawai sai ce mun tayi Baba da ina labour room da naji azaba nace, nagode Allah da Baba na bai zama mace ba, da bazan so kasha wahalan haihuwa ba Baba na am, gara su mama da mama ƙarama su karata da wahalar akanka," Baba yana cigaba da dariya yace, "wallahi tun ranan nace bansan ranan da Uwata zata yi hankali ba, hala sai tayi suruki", ya ƙarasa dukkan su suna dariya.
Aunty Hadiza tace, "nikan Baba baka taɓa zuwa gida na ba wallahi", ta faɗa tana turo baki gaba, Mama ta dubeta tace, "Hadiza kefa baki sati bakizo duba babanki ba, ae inaga shiyasa baya zuwa miki, ae ke kinfi kowa damuwa dashi,"
Baba dariya yayi ya koma ya kwanta, rufe ido yayi yana ɗan murmushi, a hankali yace, "damo sarkin haƙuri ma ae ban taɓa zuwa mata ba, kuɗin ae kune yanzu iyayena, ku zaku dinga zuwa duba ni, su kuma yaran zan dinga zuwa duba su," damo da Amina yakeyi, wanda yana yawan ƙiranta haka.
Washegari da safe su Dr suka kama hanyar Jos, wurin ƙarfe 10:00am, suka iso cikin asibitin, bayan anyi gaishe gaishe, Baba ya tambayi Aunty hauwa ina labarin amaryar shi? Tana murmushi bata ce komai ba, Aunty Amina ce ta dubi Aunty hauwa tace, "sun ma san kuwa Baba na asibiti"?....... "ni bandai gaya musu ba, amma bansan ko uncle Abdallah ya faɗa ba", Aunty hauwa ta faɗa kanta na sunkuye a ƙasa.
Uncle Abdallah ne ya shigo idon shi akan Baba yace, "wallahi sai yanzu kafin na iso mukayi waya da Abban ta nake gaya mishi, amma yace mun shi da kansa zaizo zuwa gobe ya duba ka, amma bansan ko tare zasu zo ba".
"Abdallah am da baka ɗago shi ba wallahi, yau baifi sati biyu bafa yazo ya gaishe ni, kawai ku ƙiramun amaryar tawa naji muryan ta", ya faɗa yana tashi zaune.
Uncle sabo ne ya ɗan taimaka mishi ya gyara zaman shi, shi kuma Uncle Abdallah ya ƙira wayan Ummi, bayan ta ɗauka ne sun gaisa yake gaya mata Baba ne baiji daɗi ba, Ummi hankali a tashe take tambayan yayah jikin shi? Daga nan ya miƙa wa Baba wayan suka gaisa, bayan sun gama Aka bamu muma muka gaisa da shi, don mu ganin kaka muke mishi, duk magana da akeyi a handsfree aka saka mu, Aisha ce ta karɓa daga ƙarshe, muryar ta mai cike da rawan kai tace, "kakan ƙauye bangan kaba"?
Baba zuciyar shi cike da ƙaunar yarinyar yace, "amaryar birni nazo nayita ɓata a garinku ban gane gidan ba, sai aka sakani a boot ɗin jirgi aka wurgo ni ƙauyen mu".
Dariya tayi mai ƙarfi cike da yarinta tace, "sun maka turanci ne baka iya ba, shine suka saka ka a boot ɗin jirgi suka wirgar da kai ko?" tana ci gaba da dariyanta tace, "ka sake zuwa ina son naja gemun ka, ina son ka saya mun gyaɗa da ummm....mango", ta faɗa tana dariya.
Shima dariyan yayi yace, "toh zaki koya mun turancin sai na dawo na kawo miki"?....... Dariya tayi tace zan gayawa Abba na da Ummi na su saka ka a school sai Uncle ɗin school ɗin mu su koya maka turanci, Yayah Hussain ɗina da Yayah Hassan ma sun iya suna koya mun, kaima zasu koya maka sai kayi tayi".
Duk kansu ɗakin dariyan hiran Baba da Aisha sukeyi, ita kuma Aunty Hauwa sunkuyar da kanta tayi tana murmushi, uncle Abdallah kuma kallonta kawai yakeyi babu ƙiftawa.
Bayan anyi sallan azahar Dr Alƙali da matar shi suka musu sallama suka kama hanyar bauchi, ita dai Aunty hauwa duk sai tajita wani irin tunda su Dr suka tafi, duk yadda Aunty Amina tayi tajata suɗan sake irin na da duk ta kasa, ganin haka Uncle Abdallah yace bari ya maida Mama Narabi ya dawo.
Tunda ya tafi bai dawo ba sai bayan Sallan magrib, daya dawo bayan ya gaida Baba bai kula kowa ba sai danne danne kawai yakeyi a cikin wayan shi, ana sallan isha su Aunty Amina suka yi wa Baba sallama suka tafi tare da Aunty Hadiza.
Wurin 9:30pm, Abdallah ya yiwa Baba da ya fara bacci sallama, sannan ya miƙawa Uncle sabo hannu sukayi sallama, kallon Aunty hauwa yayi yace ta taso su tafi.
Kaman zata tashi kaman bazata tashi ba, haka ta ke kallonshi, Baba ne yace, "kuje mana Hauwa kada dare ya muku", haka ba don ta so ba ta tashi jiki a sanyaye tabi bayan Uncle Abdallah, suna shiga cikin motan ya ɗan dube ta sannan ya kawar da kanshi, baice mata uffan ba har suka iso wani hotel a cikin jos ɗin mai ɗan banzan kyau, zaro ido tayi baki a buɗe tace, "na ɗauka Narabi zamu tafi fa"?
"Toh ki ajiye anan zamu kwana" ya faɗa bayan ya fita yana tattara ledodin da suke bayan motan shi, ganin ya ƙura mata ido fuska a ɗaure tayi sauri ta buɗe motar ta fito.
Cikin hotel ɗin suka shiga hawa na biyu, inda taga ya ɗauko key ya buɗe ɗakin da yake number 38, haka tabi bayan shi suka shiga ɗakin da yake da matuƙar kyau da tsari, sai ƙamshi yakeyi ga wani sanyin AC da ya cika ɗakin, gefe ɗaya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 28