Share this page
ke, ganin haka ya saka na matsa kusa da ita, a hankali na saka hannu na a kafaɗanta cikin hankali na ce mata, "Ummi don Allah ki kwantar da hankalinki, wallahi ni babu abinda zai raba mu fah, wannan abin mu ɗauke shi a Ƙaddara ne da yazo mana, don Allah Ummi ki kwantar da hankalinki, nasani kina damuwa ko Daddy na zai ƙullace ku ko? Toh ina mai tabbatar miki babu abinda zai faru, don Daddy na mai fahimta ne", ajiyan zuciya Ummi tayi ta juyo tana duba na cike da damuwa, "Humairah wallahi bana son kuga kaman mun bar Faisal bamu ɗauki wani mataki akai ba, kuma ina tsoron hala Daddyn ki yaƙi tarayyan ku da Amaal, gaskiya Faisal bai kyauta mana ba ko kaɗan", ta ƙaresa faɗi kaman zatayi kuka. Ƙara shigowan motan su Abbu ne ya saka mu saurin sauƙowa downstairs nida Amaal, da sauri nayi hanyan waje domin taryan Daddy, ina ganin shi da gudu na ƙarasa na faɗa jikin shi, lokaci ɗaya naji hawaye yazo mun, amma don bana son hankalin Daddy ya ƙara tashi sai nayi dabaran dana mayar da shi, ina rungume da shi na ɗaga kaina kawai sai naga Dr na a bayan Daddy yana duba na da murmushi. Abbu ne yayi gyaran murya da nufin mu karasa parlor, Daddy yana rungume dani a gefen shi muka ƙarasa parlon, gaba ɗaya idon Dr yana kaina kaman zai jawo ni jikinshi. Haka muka ƙarasa kowa ya nemi wuri ya zauna, Ummi ta fito fuskanta ɗauke da murmushi. _*JAMA'A DON ALLAH KUMUN HAƘURI WALLAHI YAU MUNA TA BIKI NE, PAGE ƊIN BABU YAWA*_ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/10, 16:43] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 31📑* *__________📖* Tunda muka zauna nake kwance gefen jikin Daddy nah, amma gaba ɗaya hankali da idon Daddy yana kan Dr Hussain, sai kallon shi yakeyi yana tunanin ina ya taɓa ganin mai irin kamannin shi, haka dai ya haƙura da kallon aka shiga gaisawa. Abbu sunyi tarya wa Daddy na girmamawa, dole Abbu ya saka Faisal ya zo ya gaida Daddy, Abbu yana kallon Daddy yace, "Alhaji Mohd ko zakaje ka ɗan huta ne kafin zuwa dare muyi abinda ya tara mu? don maganan gaskiya ka ɗauko gajjiya yakamata ka ɗan huta". "No babu komai Alhaji, idan babu matsalah ya kamata mu tattauna abinda ya kamata", Daddy ya faɗa hannunshi ɗaya ya na dafe dakai na, amma yawanci idon shi yana kan Dr, wanda gaba ɗaya Dr yakasa sakewa. Cikin mutsuwa Abbu ya lallaɓa Daddy, babu yadda ya iya haka ya haƙura akabar zaman sai anyi sallan ishaa. Ana idar da sallan ishaa Daddy da Dr Hussain suka iso gidan, da yake Dr yaja Daddy sun tafi hotel ɗin da ya sauƙa, anan sukayi dinner sannan aka taho cikin main parlon gidan aka zazzauna. Dubawa Abbu yayi yaga babu Faisal, da hanzari ya ɗauki wayan shi ya ƙira shi, babu ɓata lokacin ya shigo duk jikin shi a sanyaye, gefen ƙafan Abbu yaje ya zauna. Addu'a Abbu yayi ya buɗe taron da addu'a, sannan ya karanto wa Daddy duk abinda ya faru daga farkon neman mu da Dr har zuwa case ɗinmu da Faisal, da kuma niyyan da Dr yayi na bada labarin shi sai dai yagaywa Daddy, daga nan ya fara neman gafaran Daddy na abinda Faisal yaso aikatawa. Murmushi Daddy yayi ya dubi Abbu yace, "haba Abbu yanzu don wannan tsautsayin da ya faru ne zai saka kayi fushi da Faisal? Ni ae banga laifin Faisal ba sai naku iyayen shi, abinda yasa kuma ɗaya ne, a wannan rayuwa da muke ciki dole ne fah ka hana yaranka maza zuwa sashin yaranka mata, haka zalika suma ƴaƴan mu mata su daina zuwa gefen yayun su mazaa, koda kowa kai musu saƙo ne, domin masifun da yanzu suka mana yawa a duniyar mu, hadda sakacin mu iyaye, wallahi Alhaji zaka sha mamaki idan kaga yadda fyaɗe yayi yawa a wannan lokacin, kuma abin munin sai kaga mahaifi ne yayiwa ɗiyar shi, ko kuma yayah yayi da ƙanwar shi, ko ƙaninka yayi da ɗiyarka ko ƙanin matar ka, munyi sake da barin yaranmu suna chuɗanya kaman jinsun su ɗaya, haka kuma irin suturun da ƴaƴanmu mata suke sakawa a cikin gida, duk yana contributing lalacewan yaran namu, saboda haka mu iyaye mu gyara kafin mu koma kan ƴaƴanmu". Daddy ya dawo da kallon shi kan Faisal da yake ta share hawaye yace, "Faisal Amaal da Humairah dukkan su ƙannen kane, tunda Allah ya kiyaye babu abinda ya faru, toh Alhamdulillah, sai dai nace maka don Allah ka ƙara saka tsoron Allah a ranka, kaga nan gaban iyayen kane kayi niyyan aikata haka, toh ina kuma babu idon iyayenka?" Daddy ya daɗe yana mishi nasiha sannan ya neme kowa ma ya yafewa juna kuma muyi ƙoƙarin kula da zumuncin mu, sannan nima da Amaal ya mana namu faɗan akan mudinga kula da shigan da zamu dingayi, daga nan ya dawo da duban shi kan Dr Hussain yana murmushi yace. "Dr Allah bai sa mun taɓa haɗuwa da kai face to face ba sai yau, duk zumuncin mu through phone muke yi, ashe kuma suruki zaka zama mun ban sani ba", ya ƙarasa faɗi yana murmushi mai kaman dariya, wanda ya nuna tsananin farin cikin Daddy a fuskar shi, kowa da yake cikin parlon saida ya ɗan dara, nidai ban iya darawa ba sai ma ɓoye fuskana da nayi a jikin Daddy, shi kuma Dr ya sake sauƙe idon sho ƙasa. "Toh Dr Hussain muna saurarenka" cewar Abbu da yake bin Dr da murmushi. Ƙara tanƙwashe ƙafan shi yayi a ƙasa yana murmushi, kan shi ya ɗago ya kura mun ido yana duba na. "Alhaji Gambo Aliyu, shi ne mahaifin mu, wanda ya kasance haifeffen garin misau ɗaya daga cikin ƙaramar hukumar Bauchi, misau shi ne asalin garin su mahaifina, sun kasance su uku ne a cikin mahaifansu, yana da yayu guda biyu dukkansu mata, twins ne wato hassana da hussaina, mahaifinmu shi ne Gambon su, wanda sun bashi yakai shekara biyar, bayan an haife sune da shekara biyu suka yi ciwon ƙyanda, idan anan Hassanan Allah yayi mata rasuwa, bayan an haifi mahaifinmu ne suka kasance su biyu kenan a hannun iyayen su, mahaifinsu ɗan kasuwa ne a wancan lokacin, yana kasuwancin shi har zuwa garin jos. Mahaifina yayi karatu har zuwa matakin digiri, wanda yayi a garin jos inda mahaifinshi yake zuwa kasuwanci, a hannun aminin shi ya da suke kasuwanci da shi ɗan garin Narabi dake jos ya barshi yayi karatu, inda mahaifin mu suka shaƙu da ɗan Baban Narabi mai suna Umar, wanda dukkansu sun kasance masu ilimi sosai. Goggo Hussaina tayi aurenta a garin misau, amma har zuwa girmanta Allah bai bata haihuwa ba, sai daga baya mijinta ya ƙara aure, inda abokiyar zamantan ta haifi yara kusan huɗu, kuma dukkan su zaka ɗauka Goggo Hussaina ce ta haife su, don tsabar kulawan da ta keyi da su, abin babu wuya Abban mu suna final year a digiri ɗin su Allah yayi rasuwa wa mahaifin su, inda suka shiga cikin tsananin tashin hankali, amma da yake basu da yawa sai Baban Narabi ya ɗauki ɗawainiyar karatun Abba har suka gama. Abba na lagos aka tura shi service, shi kuma Baba Umar kaduna, haka suka tafi suna kewan junan su. Bayan 1yr suka gama suka dawo jos, babu ɓata lokaci Baban Narabi ya tsaya kai da ƙafa har saida ya nema musu aiki, inda Abba ya samu aiki da Central Bank, shi kuma Baba Umar ya samu aiki da Custome. Zuwa wani lokaci komai ya fara musu daidai, sun fara fin ƙarfin komai, sai Abba ya fara neman auren wata yarinya a garin misau, ana shirin auren su Allah yayi mata rasuwa, gaba ɗaya Abba ya shiga cikin wani irin tashin hankali, har sai da yafara kasa aikin shi, ganin haka mahaifiyar shi Umman Misau ta nemi shawaran Goggo Hussaina akan ko zasu bashi auren babbar ƴarsu da yanzu ta gama secondry school a wannan shekaran mai suna *FATIMA* babu ɓata lokaci Goggo Hussaina ta amince kuma ta bar maganan zata je tayi shawara da iyayen yarinyar, basu wani ja ba dukkansu suka amince inda mijin Goggo Hussaina Alhaji Abubakar dama ya kasanceai matuƙar haƙuri magana ma nan baza kaji shi yana yi ba, malamin gidan gona ne, idan baya wurin aiki toh kullum yana ƙofan masallacin unguwar su da yake manne da gidan shi yana zaune, jama'a da dama suna mutunta shi da halinshi na dattaku, itama mahaifiyar Fatima wato Aishatu itama ba mai magana bace, ta kasance bafulatanan garin gabɗori, duk wanda yasan garin misau ya san gabɗori garin wasu farare kyawawan fulani ne a wurin, gashi ta kasance mai haƙuri da kawaici, ana ƙiranta da suna Addagana, tun ranan da malam Abubakar ya aureta babu wanda zai ce ya taɓa jin tsakaninta da mijinta ko abokiyar zamanta Goggo Hussaina, kuma ta ɗauki iyayen Goggo Hussaina kaman nata iyayen, domin ita ta kasance marainiya ce, babu uwa babu uba, kuma ƴan uwanta sun mata riƙon wahala, toh da ta samu Gogho Hussaina irin mutanen nan ne masu amana da maida ɗan wani nasu, sai ta rungumeta suka zama kaman ƴan'uwa ba kishiyoyi ba, suma iyayen Goggo Hussaina sai suka riƙeta kamar ƴa. Lokacin da ta haifi Fatima bata cika shekara ba ta samu cikin ɗanta na biyu, dole Goggo Hussaina ta karɓi riƙon Fati ya dawo hannunta, bayan Addagana ta haihu, an samu Muhd Auwal, ko shekara baiyiba sai ga wani cikin a jikin Addagana, haka Goggo Hussaina ta sake karɓan shi ta haɗa da fatima ta riƙe shi, yana da shekara ɗaya da ƴan watanni Adda gana ta haihi ɗanta namiji inda Malam Abubakar yayi kara ya saka sunan mahaifin su goggo hussaina wato malam musa, amma suna ƙiran shi da Baba, Addagana wanannan karon bata sake haihuba, don tayi ɓari kusan sau biyu kuma ta haihu kusan sau uku suna komawa, ba ita ta sake haihuwa ba har saida Fatima ta kai shekara goma sha uku, Auwal yana da shekara gima sha biyu, Baba kuma yana da shekara goma da rabi, sai lokacin ta haifi *HAUWA* Fatima da hauwa sun kasance suna tsananin kama da mahaifiyar su, domin kana ganin farinsu da gashin su babu abinda suka bari na Addagana, Auwal kuma da Baba duk mahaifinsu suka ɗauka, duk da suma farare ne amma basu yi kyaun su Fatima ba. Fatima da ƙannenta sun kasance yara masu tarbiya da nutsuwa, domin Goggo Husaina babu abinda ta bari daga tarbiyan su, ta riƙe su kaman ita ta haife su, babi wani mugunta a tarbiyanta, sai kuma yaran suke sonta kaman itace mahaifiyar su, Baba ne kawai wani lokacin sai ya koma ɗakin Addagana, idan sun ɓata kuma ya tattaro ya dawo ɗakin goggo hussaina, kowa zaka ga yana mishi dariya, akan yarasa wurin zama guda ɗaya. Lokacin da aka gayawa Abban mu maganan auren shi da Fatima bai wani ja ba ya amince, amma ita Fatima sai da tayi ƙorafin ita fa kawun tane kawu Gambo, amma da taga ran Yayah zai ɓaci sai ta amince, da yake haka suke ƙiran Goggo Hussaina, don duk sunbi bakin Addagana ne. Ba'a ɗauki lokaci ba akayi auren Abba da Ummi nah, aka kaita garin bauchi inda Abba na yake aiki, sun zauna a wani unguwa wai shi dutsin tanshi, gida ne ɗan madaidaici ma ɗakuna biyu, sai kitchen da wani ɗan store, babu laifi gidan ya dace da sabbin ma'aurata. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/11, 11:08] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 32📑* *__________📖* Abba na da Ummi na suna cika shekara uku da aure Allah ya basu mu, inda aka same mu nida ɗan'uwa na Hassan, daga lokacin Allah yayita buɗi wa Abban mu, inda aka maida shi branch ɗinsu na lagos, babu ɓata lokaci muka tattara tare da Aunty Hauwa muka koma chan, ita kuma tana taimaka wa Ummin mu da wasu ƴan aikace aikace, inada a lokacin tana tayata har renon mu don bamu fi six month ba, ita kuma Aunty hauwa tana 14yrs kuma zata shiga ss 2 a lokacin, haka Abba ya sama mata wani private school kusa damu ta shiga. Muna cika 2yrs Aunty hauwa ta gama rubuta waec ɗinta, murna kaman zatayi yayah, haka muka ɗunguma muka taho Misau mukayi hutu. A wannan hutun ne Baba Umar yayi aure da wata yarinya ƴar tilden fulani, ƙanwar matar abokin shi ce mai suna suwaiba, shi kuma a wannan lokacin yana katsina da zama. Result ɗin su Aunty hauwa na fitowa Ummi suka yi shawara da Abba akan a sama mata school of nursing bauchi, haka Abba yayita fafutukan nema har Allah ya yarda da rabonta a ciki, tafiyan ta ummi taji babu daɗi, domin Aunty Hauwa akwai kazar-kazar ɗin aiki, saidai akwai yawan faɗa, wanda kullum akace ta ɗauki Hassan sai ta zungure shi tayita mitan ya cika yawan kuka, amma idan Ummi zatayi aiki tafi so ta bata riƙon shi, don aikin zai fi tafiya mat, domin ni duk inda akayi dani haka nakeyi bana da rikici inji Ummin mu, shi yasa ita bata damu ta ɗaga hankalinta akaina ba, sai dai kullum rikicin Hassan ke rikota su dukkan su gidan. Aunty hauwa tana 2yrs a school of nursing, taxo mana hutu lokacin muna 4yrs, a lokacin kuma Baba Umar an dawo da su Lagos, ranan da tazo Abban mu tare da Baba Umar suka je ɗaukota a airpot, tunda Baba Umar ya ganta hankalin shi yayi mugun tashi, sai tambayan Abba ya keyi "yaushe Hauwa ta girma haka? Kaga fa yadda ta koma kaman Fatima sak, har ma tafi Fatima tsayi da fari wallahi", ya faɗa yana duban Abba da ya ƙura mishi ido. Murmushi Abba yayi mishi yana duban Aunty Hauwa ta mirror yadda duk ta kasa sakewa sai wani kunya ta keji kaman ta nutse a ƙasa, yana ɗan dariya yace, "haba Umar duba dai da kyau ka gani, ta ina Hauwa ta kai Fatima kyau? Tsayi kuma don ita yanzu yarinyace batayi jiki ba, amma Fatima nah tafi komai, wannan da wani hancinta da baikai na matata kyau ba", ya ƙarasa yana dariya domin ganin yadda Aunty Hauwa tayi saurin ɗago idon ta tana kallon shi da mamaki, chan kuma ta saka hannunta ta shafa hancin ta, muryah cike da shagwaɓa tace, "yayah da Bappan mu sunce nafi Adda Fatima kyau, wataran Addagana ma tace nafi kowa kyau a gidan, kuma ka tambaya yayah kaji", ta faɗa kaman zatayi kuka. "kwantar da hankalin ki Princess babu ta inda Fatima ta fiki kyau, kawai haushi ya keji don matar da zan aura tafi tashi matar kyau, kada ki wani ɓata hawayenki zan karɓa miki ba sai kin ɓata yawun bakin ki ba", ya faɗa yana kai duka wa Abban mu, wanda shi kuma sai dariyan su yake tayi yana chigaba da driving ɗinshi. Har suka iso gidan mu faɗan bai ƙareba, mu kuma nida Hassan da gudu muka zo muka rungume Aunty Hauwa, itama da murnan ta ta rungume mu, kaman zatayi yayah don daɗin ganin mu, Hassan yana duban ta yace, "Aunty Hauwa inace kinfi sona akan Hissain? tunda nine babanki ko?" ya faɗa yana shan gaba na kada na matsa kusa da Aunty Hauwa. Tana dariya ta sunkuya ta riƙo hannun mu tace, "dukkan ku ina son ku iri ɗaya, amma kai nafi sonka saboda sunan Baba na kaci, shi kuma nafi son shi saboda shiɗin rayuwata ce, Hassan farinciki nane, Hussain kuma rayuwata ce, kaga dukkanku ina sonku, amma yanzu zan fi son wanda yafi jin magana a cikin ku", ta ƙarasa faɗi tana miƙa mana sweet wasu manya-manya dasu kowa uku-uku a hannun shi. Haka muka fara tsalle da murna, domin gaskiya Aunty Hauwa ba dai nuna mana so ba duk masifanta amma akwai ta da alheri, gashi ko cin abu zatayi taga idon mutum toh babu yadda zatayi sai ta baka, ita dai abunta bai rufe mata ido ba, kaman ƴan garin su mamanta idan sunzo, duk da tasan irin muguntar da sukayi wa mamanta amma haka zata tattaro kayanta ta basu tace suje su raba, gaskiya halinta babu abinda ta bar na Goggo Hussaina, kaman tasha ne a nononta, saidai faɗa kam sai a hankali, wasu sukance ta ɗauko wani yayan Baban sune amma ya daɗe da rasuwa, domin wuni yakeyi akan kujeran katako a ƙofar gidan shi, duk wanda ya wuce sai yayi masifa, shi ne ƙiran mai gyaɗa, shi ne mai gujjiya, mai rogo bata tsira ba, kuma yana saya yana masifa, toh haka Aunty Haiwa ta ke, domin gidan su family house ne, duk yaron da ya shigo sai ta hantare shi, amma kuma kullum jakanta da sweet tana raba musu, Allah sarki Aunty Hauwa nah", Dr Hussain ya ƙarasa faɗa yana sha re hawayen shi, kuma lokaci ɗaya ya sunkuyar da idon shi a ƙasa yana ta share hawaye, gaba ɗaya parlourn kowa sai jikin shi yayi sanyi, babu wanda yace uffan, sai Faisal ne ya tashi ya ɗauko goran ruwan sanyi ya miƙa mishi, karɓa yayi ya sha kusan rabin roban, sannan ya ɗago idon shi ya dube ni, ganin ina share hawaye na sai yayi murmushi ya maida idon shi ƙasa. "Ummin mu da fara'a ɗauke a fuskarta ta miƙa hannu ta rungume ƴar uwarta, itama Aunty Hauwan tana murmushi ta rungume Ummi, bakinta bai rufu ba tace, "Adda Fati kiji mijinki wai kinfini kyau? Nidai da mutanen gida duk mun san muna kama da ke amma maganan gaskiya nafi kyau, ni banma taɓa jin wanda ya taɓa cewa kinfini kyau ba, haba dubi ido na kaman ni na ɗusana abuna, kowa ya ganni sai ya sume da kyaun idona", ta ƙarisa faɗi tana murguɗa baki tana juya idon nata. Dariya gaba ɗaya parlourn sukayi, Abba yana hararanta da wasa yace, "amma Hauwa bakida wayo, waya ce miki kinfi Fatima kyaun ido? Ke baki san ana zolayanki bane ake cewa kuna kama? ae kinfi kama da Auwal da musa, domin Fatima ae ta muku zarrah a kyau, don ke macece shiyasa ake kwatanta kamanin ku, kuma kunfi su Auwal fari". Kuka Aunty Hauwa ta fara tana duban Ummin mu tace, "don Allah Adda Fati ki gaya mishi gaskiya saboda Allah, wallahi yayah Auwal da Yayah Baba ƙananan ido suke da shi, sufa irin idon su Bappanmu suke da shi ƴan ƙanana, kuma hancinsu bai kai namu ta shi ba, Adda kimishi bayani ya lura, wallahi ni ina da kyau mai ɗaukan hankali, ranan fa zan wuce wani DPO yazo wucewa kasa tafiya yayi yace sai yaga gidan su wanann mai kyaun, wallahi yanzu a school Hauwa beauty ake cemun, ko Hauwa golden girl", ta ƙara sa maganan tana share hawayenta, wato Aunty Hauwa komai zakayi kada kace bara da kyau domin ita ta yadda ita mai kyau ce, saboda haka kullum Ummin mu idan zata saka ta aiki ta mata babu ɓacin rai, zakaji tace zizar gidan mu, autar Adda da yayah da bappanmu, maza tashi kimun aiki, toh babu musu zata tashi tayi yadda ya dace, shiyasa Aishan mu ta gaji halin Aunty Hauwa, gashi kuma kullum ɗabi'un da Humairah ta keyi kenan, wanda shi yaja hankalina gareta, don ni tun ina yaro abinda Aunty hauwa ta keyi burgeni yakeyi, ban fahimtan komai amma idan tana rikicin tafi kowa kyau, abin daɗi yake mun. Domin wataran sai ta jamu cikin ɗaki nida Hassan ta tsaya gaban mirrow tayita kallon kanta, ta juya ta gyara tsayunta, ta lanƙwashe nan ra juya na, ta baza gashinta mai azaban kyau tana duban mu zata ce, "yarana amma dai duk ƙasan nan kafin a samu mai kyauna za a sha wahala ko? Kunga irin kyaun ido na kuwa"? Hassan idan ya kalleta zaice amma baki kai Ummin mu ba fah, toh hannu ta ke sawa ta kai mishi ran ƙwashi ta fatattake shi a ɗakin tana cewa, wannan kam kuskure akayi aka saka maka sunan mahaifinmu, ɗan banzan yaro mai goshin tsiya dama isubu aka saka maka, sunan wani ɗan ajinmu a lungun fada, ko kuma a saka maka gedau ko kantara, shashan yaro kawai," sannan ta dawo da kallonta kaina, "kaifa me kace"? Murmushi nakeyi ina da shekara huɗu amman nasan wayon ince mata, "kinfi Abba da Ummi kyau, kinyi irin india", tsalle ta keyi ta ɗaga ni sama tace wani abunma sai naje turai na ɓaro kyau tukun yaro na mai kama da larabawa, nima daɗin abinda ta ke faɗi nakeji. "Dr na toh ina ita Auntyn Hauwan yanxu ta ke? Nima naji ina sonta, don nima ina son ace ina da kyau, duk da nasan ina da kyau amma ina son ace nafi kowa wallahi", na faɗa ina duban dr da yake kallona idon shi na zubar da hawaye bakinshi kuma da guntun murmushi. "Toh ae ke baki mun kama da ƴan india, asali ma ni banga kyaunki ba, kaman Aishan mu da Aunty Hauwa sunfi kyau", Dr ya faɗa yana fito da sautin murmushinshi, kuma hawaye yana kanbin fuskan shi, gaba ɗaya parlourn dariya aka fara mun, yadda na turo bakina gaba kaman zan falla ihu. Amaal mai ta samu banda dariya, tana duban Dr tace, "ga goshin ta kaman na gedau da kantara", gaba ɗaya parlourn dariya akeyi, Dr yana dariya yace, "Amaaƙ sunan kakanunae fah na wurin uwa, ƙannen maman umman mu ne fah, in kinyi wasa sai na haɗa ki da gedau babu ruwa na". Daddy ƙurawa Dr ido yayi duk yana cikin ruɗani, duk dariyan da akeyi shi bayayi, idan ya dubi Dr ɓa wani lokaci sai kuma ya dawo da idon shi kaina, nidai ina satan kallonshi kaman wani mai nazari, chan kuma sai naga yana share hawayen da bansan me yasa suka zubu mishi ba, gaba ɗaya hankalina sai ya tashi, kawai sai na fashe da kuka na riƙe shi ina tambayan shi, "Daddy me yafaru kake kuka"? Murmushi yayi ya riƙo hannuna muryah a hankali yace "babu komai na tuna da mahaifiyar kice", ya faɗa yana sha re hawayen shi. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/13, 11:38] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 33📑* *__________📖* Ana haka magana ya fara ƙarfi tsakanin Aunty Hauwa da Baba Umar, domin wani so sukeyiwa junan su kaman me, amma Ummi nah ita bata so hakan ba, domin tanaga kaman Suwaiba zata ce ita ta haɗa ƙanwarta da mijinta, amma koda Abba yace mata babu ruwanta, kada ta damu da maganan mutane sai kawai ta yi shiru ta bisu da addu'a. Ranan da Aunty Hauwa ta gama huta, Baba Umar ya matsawa Abba akan shifa dole su tafi tare da ita, domin aje anema mishi aurenta, don bada wasa yakeyi ba, kada yana chan lagos wani yazo ya ƙwache mishi ita, babu yadda Abba ya iya dole suka biyota. Tadawo da washe gari mutanen jos sukazo har misau neman aure, babu wani wasa da hankali akayi komai cikin mutunci da dattaku, a ranan iyayen Aunty Hauwa suka bawa Baba Umar auren ta, shi kuma Baban Narabi ya sake neman a saka musu auren bada daɗewa ba, da ƙyar dai aka yadda akan idan tagama wannan

Chapter 16 of 28