ya kalle mu yace, "yau kuma fallashe-fallashe akeyi a gidan nan ko?" sannan ya dubi Faisal da yake ta howa yace, "kaima kazo kaji tonan asiri da ƙannen ka suke yi, kaima kazo muji ko sun san naka", Abbu ya ƙarasa da murmushi a fuskar shi.
Ya mutsa fuska Faisal yayi yana turo baki yace, "Abbu ae ni Humairah nake so, amma naga wani hali da sis Amaal ta ke nuna mun akan wani chan daban", ya faɗa yana hararan Amaal, gefe na yazo ya zauna kusa da ɗayan ƙafan Ummi.
"Amma baka da hankali ne son? Yarinyar da ta ke da wanda ta ke so, yasan mu, muka san shi zaka ɓullo da wani shiririta kuma? Kai kan ae matar ka bata wuce ss1 ba a secondry, saboda haka kada na ƙara jin wannan shirmen a bakin ka daga yau", Abbu ya faɗa cike da ɓacin rai.
"Gaya mishi dai Abbu don na lura Faisal yana son ya chan ja halayen shi masu kyau da muka san shi dasu zai kwaso wasu, kuma hakan ba dai-dai bane, da wani ido Dr zai kalle mu? Wands basu san alƙawari da amana ba?
Faisal sai wani ƙara tamƙe fuska ya keyi yana hararan Amaal a fakaice, wanda ita kuma sai murmushin iya yi ta keyi, nidai kasa ɗaga ido nayi na dubi kowa, wasa kawai da yatsuna nake tayi, domin koma meye Faisal ya ban tausayi, domin ganin yadda kowa ya nuna mishi bai kyauta ba sai yaban tausayi.
"Humairah bana son ki bar yaron nan ya shiga rayuwar ki, domin bazan ji daɗi ba idan Dr ya fahimci da akwai shirmen Faisal na cewa yana sonki, zanji kunya don zai ganni ƙaramin mutum, na ɗauko ki na kawo gidana, ɗana kuma yana nemanki, gaskiya bazan so faruwar haka ba, kaima ka kiyaye kana jina ko Faisal"? Abbu ya faɗa cike da ɓacin rai.
Amsawa a hankali Faisal yayi cike da jin haushi, bai kuma ɗau wani lokaci ba ya tashi yayi sallama da jowa ya wuce ya bar parlon.
Ummi ce ta bishi da kallo fuskanta ɗauke da murmushi tace, "in banda rikici irin na Faisal ina zai kai Hummy? Kawai neman kada a zauna lafiya ne", Abbu ya harari ƙofan da yabi yace, "shiririta dai irin na yara, amma ae Humairah ba sa'ar shi bace".
Dariya Amaal ta kwashe da shi tana kallon Abbu tace, "Abbu sai kaga irin hararan da ya bini da shi, kuma ina ganin sai da ya ta ke hannun Hummy kafin ya bar wurin, amma ta yi wani shiru bata ce komai ba, da nine kan ae sai gadon asibiti", ta ƙarisa faɗi tana dariya.
Kowa a parlon dariya ya fara Ummi tana duba na tace, "doug kodai kina son shine kada muyi shishshigi"? Dariya nayi na sunne kaina akan cinyan Ummi .
"Ta isa tace tana son wani bayan Dr", inji Abbu. "ae sai na ɗaura auren gobe naga yadda zata saurari wani, shima Faisal rikici ne ae".
Hutun mu tare da Dr yamana daɗi sosai, don kullum sai yazo ya fita damu, mune zuwa shan ice-cream, mune zuwa nan mall ɗin miyi shooping, wataran muje park mu zauna ayita shan soyayyah, gaba ɗaya rayuwar sai naji ban taɓa jin daɗi irin na wannan lokacin ba, a haka har hutun mu ya ƙare, a na saura 2dys mutafi, shi kuma Faisal ranan ya koma school, lokacin da zai tafi ya shigo har ɗakin Amaal, dai-dai lokacin na fito daga waka ɗaure da towel a jikina.
Faisal yana shigowa ya tsaya ya ƙura mun ido, ganin kallon na shi bana ƙare bane jikina a ɗan firgice nace, "kana neman Amaal ne"?.
Ina jiran naji amsan da zai bani amma sai naga ya maida ƙofan ya rufe ya kuma murɗa key ɗin ɗakin.
Wani irin mummunan faɗuwar gaba naji ya zo mun, wanda har sai da naji kaman wani guntun fitsari ya ɗigo mun, jikina yana rawa na sake tambayan shi, "Amaal kake nema ne bros"?
Munafukin murmushi yayi yana matsowa inda nake tsaye yace, "wurinki nazo muyi sallaman da kowa bazai taɓa mancewa da ɗan'uwan shi ba har ƙarshen rayuwar shi, kuma ina so yau ki yadda dani kika dace ba wannan tsohon ba".
Juyawa nayi da sauri zan koma cikin toilet ɗin, amma sai naji charaf ya chafke ni.
Ban san lokacin da zunduma wani uban ihu ba iya ƙarfina.
_Ni Aunty Nice nima sai da naji zuciyata zata buga domin jin irin ihun da Humairah tayi, wanda sai danaji shi har cikin ƙwaƙwalwata, wanda naji typing ɗin ma yana neman gagara na, don ni kaina na razana da Faisal, amma kada ku gajjiya da alƙalamin Aunty nice, ku jiraye ni zuwa bayan sallah idan Allah ya kaimu da rai da lafiya, kuma kada kumanta da naman sallah, kowa ta ƙullah mun na bawa Babyn Baby._
*©AUNTY NICE•*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/6, 12:11] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*MISS XERKS (BESTY NAH)*
*AISHA ALIYU GARKUWA*
*UMMI GARKUWA (ZAIBAI)*
*SADNAF*
*NABILA RABI'U ZANGO*
*MAIDAMBU*
*KHALISAT HYDAR*
wannan shafin nakune domin kuɗin daban ne a cikin duniyan marubuta, kunmun alkhairin da baki bazai iya furta kalman godiya ba, hannu bazai iya rubutawa ba, har abada godiyata da girmama *AL'AMARIN* ku bazan gajiya ba, *NAGODE!* *NAGODE!!* *NAGODE!!!* Allah ya kare mun ko da zuri'an ku duniya da lahira
*SHAFI NA 29📑*
*__________📖* Da sauri Faisal ya sakeni yana duba na a razane, domin shima ba ƙaramin razana yayi ba da jin irin ihun dana yi, ƙura mun ido yayi shi kanshi jikin shi rawa yakeyi, dai-dai nan mukaji buga ƙofa da ƙarfi.
A razane ya juya yana kallon ƙofan, domin jin muryan Ummi da Abbu, ta ɗayan gefen kuma Amaal ce ke ta faɗin, "sis Hummy ki buɗe ƙofan, mai ya sameki ne"? Da ƙarfinta ta ke ƙirana, ni kuma ganin hankalin mugun yayi jikin ƙofan, sai nayi wuff na faɗa toilet da danna key a jikin ƙofan, bansan lokacin da na furta "wayyo Dr nah, wayyo Daddy nah kuzo kada ya cuceni don Allah, kuzo ku fitar dani a cikin gidan", da ƙarfina nake faɗi ina wani irin kuka kaman raina zai fita, don idan kun gani alokacin sai kunyi tunanin ko mutuwa aka mun.
Amaal ko da taji kuka na, gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa tana duban iyayenta tace,"Ummi kuyi wani abu mana, bros ne hala a ciki, Ummi kada ya cutar da ita fah", ta faɗa tana zubar da hawaye.
Jin haka ya saka Ummi ɗaga murya da ƙarfi tana ƙiran sunan Faisal, "Faisal ka buɗe ƙofan nan kuma kabar yarinyar nan, wallahi ka yadda wani abu ya sameta ban yafe maka nono na da kasha ba, banyafe maka ba Faisal" ta ƙarisa faɗin kalmarta tana kifa kanta jikin Abbu tana kuka, cikin ɓacin rai Abbu ya sake buga ƙofan da ƙarfi yace, "idan baka buɗe ba Faisal yanzu zan ƙira securities su buɗe ƙofan kuma a tafi da kai a matsayin mai raping, kuma kasan irin hukuncin da ƙasan nan zata yanke maka, secondly kuma zan yafe ka cikin ƴaƴa na.
Daga jin abin da Abbu ya faɗi Faisal da sauri yazo ya buɗe ƙofan jikin shi yana rawa, da sauri Ummi ta saka hannu ta wanke shi da kyakkyawan marin da sai dayayi namijin gaske kafin ya iya tsayawa da ƙafan shi, bai samu azaban ya sake shiba yaji sauƙan wasu tagwayen mari a fuskar shi, wanda da ƙyar ya samu nutsuwan gane daga inda suka fito, basu ankara ba kuma suka ga jini ya fara biyo hancin shi, saboda tsananin azaban mari, da ƙyar ya ɗaga kanshi ya dubi Abbu da yake wani irin hakki kaman zuciyar shi zai faɗo, da ƙarfi ya furta, "me kayiwa ƴar mutane Faisal? Na rantse da Allah idan ka cutar da ita zanyi shari'a da kai kuma zaka nisanta dani har abadan, shin kasan yarinyar Amana ce kowa a hannun mu? Kasan yadda Mahaifinta yake jaddada mun riƙon amanan ta? Kaico da hali irin naka Faisal", Abbu ya faɗa yana ƙara wanke shi da mari.
Muryan Dr sukaji daga bayan su yana tambayan, "Don Allah ina Aisha Humairan? Fatan dai bai mata komai ba"? Ya faɗa duk illahirin jikin shi yana rawa, suma cikin mamako suke kallon shi, don basu san da shigowan shi ba, domin yayi sallama ya shigo suna gaisawa suka jiyo ihun Hummy, kuma sun manta da shi a wurin suka taho sama.
Amaal ce jikin ƙofan toilet ɗin tana ta bugawa tana ƙiran sunan hummy akan ta buɗe mata, ganin haka yasa Dr shigowa har inda Amaal ta ke ya jinguno da ƙofan muryan shi kaman zaiyi kuka yace, "Baby nah! Baby na ki buɗe mun ƙofan kada na shiga wani hali, ki buɗe na tabbatar da babu abinda ya sameki kafin numfashina ya ƙaurace mun", ya faɗa duk dauriyar sa sai da hawaye ya zubu mishi.
Buɗe ƙofan nayi jikina yana kan rawa har lokacin, ga hawaye na kaman zasu ƙare a wannan ranan, ina kallon su bansan lokacin dana faɗa ƙirjin Dr na ba na sake wani irin kukan da bansan daga inda yaxo ba, muryata na rawa nace, "Dr na tsoron shi nakeji, nikan kamayar dani wurin Daddy na, tsoro nakeji Dr na".
Da sauri ya kankame ni a ƙirjin shi, jikinshi yana rawa yake cewa, "Baby bai miki komai ba ko? Baby nah bazai miko komai ba insha Allah, kiyi shiru zan tafi da ke", ina ƙara kankame shi ina kuma ƙara sautin kuka na nace, "Baby ya razana ni, ya bani tsoro, tsoron shi nakeji, ka gudu da ni, baby ina sonka kai ɗaya bana so ya mun wani abu ka tafi dani baby nah, na yadda kai kaɗai kake sona baka da niyyan cutar da ni".
Kuka Amaal ta keyi kaman zata shiɗe, da sauri Ummi ta ƙaraso ta riƙeta tana faɗin kiyi shiru Amaal insha Allahu wani abu bazai taɓa faruwa da Hummyn ki ba mara kyau, kiyi shiru kada ciwonki ya tashi, da sauri na ɗago kaina daga ƙirjin baby nah, na ƙurawa Ummi ido, ganin ta juyo tana kallo na nayi sairi na tafi jikinta na rungumeta ina kuka, muryah a hankali tace, "babu komai doughter babi abinda zai faru dake insha Allahu, ki kwantar da hankalin ki kibar kuka, fatan dai bai miki komai ba"? Ta faɗa tana ɗago ni daga jikinta, ɗaga mata kaina nayi alaman ehh, sannan ta dubeni tace Amaal ta jirani mu shiryah sai mu same su a parloon ƙasa.
Dr yana bina da kallo da ƙyar yabi bayan su Ummi suka sauƙa ƙasa, ni kuma Amaal tazo ta rungume ni tana kuka, dukkan mu kukan muka saka muna rungume da juna, da ƙyar ta lallaɓa ni muka je na wanke idona, duk yadda tayi dani na shafa mai kasawa nayi, kawai wani dogon rigan atamfah na batik ta ɗauko mun acikin kayana na saka, da ƙyar na yadda ta shafa mun wasu turaruka a jikina, na ɗauki wani ƙaramin gyale green mahaɗin rigan na yafa shi akaina.
A parlor muna zuwa naga Faisal zaune a ƙasa wurin ƙafan Abbu, ɗayan gefen kuma Dr nane a zaune ya sunkuyar da kanshi ƙasa, Ummi kuma tana gefe kusa da Abbu suna zaune wuri ɗaya, shigowan mune ya saka dukkansu suka ɗago da kansu suna kallon mu, tsayawa nayi na kasa cigaba da tafiyan domin ganin Faisal zaune a wurin.
Ummi ce ta miƙo mun hanni alaman nazo wurinta, amma ganin Faisal kusa da su yasakani kallonta ban ƙarasa ba, idona na juya gefen da Dr yake zaune naga shima ido ya ƙura mun, kawai bansan yyh akayi ba kawai sai na samu kaina da tafiya inda yake, na zauna kusa da shi na takura sosai a jikin shi, kaman wani zaizo ya taɓa ni nake ji, lokaci ɗaya naji Dr yayi ajiyan zuciya, sannan ya saka hannunshi ya riƙe ni gam ajikin shi, shima a lokacin idan ka dube shi sai kaji kaman kayi kuka, domin gaba ɗaya a wani firgice yake.
Amaal ce ganin haka ta juya ta harari Faisal, murya a raunane tace, "Ummi Hummy na tsoron shi ta ke ji , kice ya bar wurin bazata iya zuwa wurinki ba", ta faɗa tana share hawayenta.
Ummi ta miƙa mata hanni alaman tazo, haka Amaal ta ƙarasa ta kwanta gaba ɗaya a jikin Ummi, shi kuma Abbu yayi murmushi ya dubi Amaal yace, "ki barta a wurin Dr ta, yau inaga idan ba Daddyn ta ba toh babu inda zata samu nutsuwa idan ba wurin Dr ba, a razane ta ke sosai" ya faɗa yana dawo da kallon shi kanmu, nidai ban iya yin komai ba sai na ƙara matsawa jikin Baby sosai, har ina jin yadda jikin shi yake ta rawa, da sauri na ɗago kaina na dube shi, ganin ya ƙurawa Faisal ido kuma jikin shi sai rawa yakeyi, sai naji ya bani tausayi, a hankali na furta, "baby nah kayi haƙuri", muryana ya fita a hankali kuma yana rawa, dawo da duban shi yayi kaina, sai naga hawaye suna zuba a idon shi babu kakkautawa, bakinshi har rawa yakeyi yace, "baby tsoro nakeji a cikin zuciyata, bana so tarihi ya sake maimaita kanshi akaina, ina tsoro sosai baby", sannan ya juya ya dubi Abbu jikin shi yana rawa yace, "Abbu ka ƙira Daddynta kace yazo yau ya ɗaura mana aure, wallahi idan wani abu ya fari da Humairah bazan taɓa yafewa kowa ba, wallahi wannan karon zan ɗauki doka a hannuna, ina sonta sosai bazan iya barinta wa kowa ba, meyasa kullum saini? Me yasa kullum sai abinda nafi so? Wayyo Mama na! Wayyo Babana", ya faɗa yana sauƙowa ƙasa inda nake zaune ya saka dukkan hannayen shi ya rungume ne dasu, kanshi ya ɗaura akan wuyana, muryan shi na rawa yace, "Baby kinsan ina sonki, idan wani ya sameki mutuwa zanyi, kinsan me yafaru dani abaya? Kinsan me ya baroni da family nah? Kinsan zafin danaji na rabuwa dasu da abinda nake so da akayi raping ɗinta? Kinsan gararin da rayuwata ta shiga ta dalilin wancan mummunan ƙaddaran? Toh yanzu kam mutuwa zanyi wani ya yi gangancin cutar mun dake, don ban taɓa jin irin son da nake miki ba akan kowa", a hankali ya sake ni ya matsa a kusa dani ya ɗaga hannayen sama hawaye suna zuba a cikin idon shi yace, "Astagfirullah! Astagfirullah!! Astagfirullah!!! Allah na tuba, Allah don girman zatinka, don tsarkakayen sunayenka guda chasa'in da tara, don darajan wanda ka fifita fiye da kowa da komai, babban masoyinka annabin rahma, kayi mun maganin abinda ke faruwa dani da abinda dake faruwa da rayuwata, kaine masanin sirrin sarari dana ɓoye, nasan kafini sanin halin da nake ciki, da abinda ke faruwa dani,, Allah ka dubani da idon rahma kaji ƙaina ka sassauta mun abinda ke damuna, Allah kaine mabuwayi babu abin bautawa da gaskiya sai kai, a gareka na dogara, kaine mai kawar da baƙin ciki, mai yaye ɓacin rai, mai amsan addu'ar mabuƙata, Allah ka tsare mana gaban mu da bayan mu, Allah ka kare mu da aikata zina da ƙuwaɗi da maɗigo, damu da ƴaƴa yenmu da na ƴan uwanmu, ka nisan tamu da aikata shi, Allah ka kare mun wannan baiwa taka, ka tsare mun ita daga dukkan sharrin masharrata, Allah ka kawo mun nutsuwa a zuciyata, Allah ka kare dukkan musulmai gaba ki ɗaya", yana gamawa ya sunkuyar da kanshi ƙasa hawaye yana bin fuskan shi.
Hawaye Ummi ta share, tana duban mu cike da tausayi tace, "Abbu inaga ya kamata ka ƙira Daddyn tan, don bansan yayah Dr yakeji ba a ranshi, amma a matsayina na uwa nasan da ciwo a rayuwar shi, yakamata a hanzarta mallaka mishi Hummy", ta faɗa tana ƙara rungume Amaal da take ta zubda hawaye.
Hmmm abin tausayi hattah Faisal kuka yakeyi, yana duban Dr yace, "don Allah Dr ka yafe mun, wallahi sharrin sheɗan ne, ni wallahi ban taɓa zina ba, kuma ban taɓa kusan tan shi ba, kawai sheɗanne yau yaso ya buga mun gangan shi, kuma Allah ya kare ni, wallahi dama a razane nake, na gode Allah kuma da kukazo, domin ni kuka taimaka, kuma nayi alƙawari ba Humairah ba ni ko waccce mace ma a duniya zan kiyaye kaina daga gareta, domin gudun faɗawa mummunan ƙaddara", sannan ya riƙo hannun Abbu yana kuka yace.
"Abbu don Allah ku yafe mun wallahi nayi nadama tsakanina da Allah, kuma bazan taɓa maimaita hakan ba, kuyi haƙuri naci amanar tarbiyar dakuka daɗe kuna mun, wallahi wani abokina ne nagaya mishi yadda ake ciki, shi ne yace idan nayi raping ɗinta dole za a haƙura abarni na aureta, amma wallahi nayi nadama bazan sake aikatawa ba".
Yana kuka ya ƙara sa gaban Ummi, riƙo hannunta yayi zaiyi magana amma sai ya kasa, domin ganin irin kukan da Ummi da Amaal sukeyi, kawai sai ya rungume su duka yana faɗin, "Ummi nah, Ummi nah ki daina mun kuka kada Allah yayi fushi dani, na tuba Ummi na", ɗagowa Ummi tayi tana shafa kanshi tace, "na yafe maka Faisal kuma nayi imani da Allah ba halinka bane na yadda sharrin shaiɗanun abokaine yake wasa da rayuwar ka, kuma na raba ka da wannan abokin, na kuma raba ka da hidiman mace idan ba ka tashi aure bane, ni ina kuka domin tausayawa Dr ne, amma bana zubar maka hawaye, domin ina addu'an Allah yasa ku gama damu lafiya, ku gama da duniya lafiya".
Gyaran murya Abbu yayi, kowan mu sai da ya ɗaga ido ya ƙura mishi, jiki a sanyaye Abbu ya saka tissue ya sha re hawayen dayake ta biyo kan kyakkyawan fuskar shi, a hankali ya dube mu gaba ɗayan mu, sannan ya sauƙe idon shi akan Faisal yace, "Ɗana Allah ya kare mun ku daga sharrin abokai da rayuwa, kuma ni bazan ce na yafe maka ba har sai naga hummy ta bar gidan nan lafiya, kuma ina mai ƙara jan hankalinku daku ji tsoron Allah a duk inda kuke, kuma kada kayi tunanin cewa aboki ya sakaka a abu, toh wallahi ranan lahira Allah zai maka hukunci da abinda ka aikata, bawai za ace a barka ba saboda kai abokine ya saka ka, shiyasa ake so ayi abota dana gari, kuma wallahi duk inda kake kasa ka tsoron Allah a zuciyar ka, babu abinda yake cikin zina sai masifa da azaba, kuma sai anrama kaima akanka watarana", sannan Abbu ya dubi Ummi yace, "Muma muna da laifi domin mun bar Faisal yana shiga ɓangaren Amaal kaman ɓangaren namiji ɗan'uwan shi, kuma hakan babban kuskure ne, shiyasa yanxu alfasha yayi yawa ko acikin ƴan'uwa ma, amma insha Allahi daga yau nayi duba da kuskuren mu, daga yau Faisal ka tsaya iyaka naka ɓangaren sai kuma nan parlor, amma bana so ka ƙara zuwa ɗakin Amaal, kema Amaal ban yadda kije ɓangaren shi ba daga yau, sai kuma mu nemi yafiya a wurin ubangiji".
Dawo da kallon shi yayi kaina yace "Humairah kiyi haƙuri, bansan haka zai faru ba amma duk da haka kiyi haƙuri insha Allahu zamu ƙara saka ido akai", sannan ya dubi Dr yace, "kai ma kayi haƙuro Dr da yadda aka ɗaga maka hankali, kuma insha Allahu zan ƙira Daddynta zan mishi bayani kuma inda hali zan ce mishi yazo nan ya same mu sai muyi dukkan magana da zamuyi a nan, ina fatan kowa zai yafewa ɗan uwanshi", gaba ɗaya kowa ya yafe wa ɗan'uwan shi, sannan akace mu tashi mu tafi ɗaki, ɗago ido nayi ina kallon idon Dr, wanda shima kallo na yake, da ƙyar ya sake mun hannu na ya tashi ya yi sallama dasu Abbu ya tafi.
Jikina a sanyaye na riƙe hanjun Amaal muka wuce ɗaki, inda muka bar Abbu da Ummi da Kuma Faisal a parlor.
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/7, 17:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 30📑*
*__________📖* A daren Abbu ya ƙira Daddy ya mishi bayani, hankalin Daddy na a tashe ya ƙirani, "Humairah nah kimun bayanin da zan fahimta, kina cikin ƙoshin lafiya dai ko? Kinaga babu wani matsalah na zamanki a gidan kafin na zo"? Duk cikin rawan jiki da tsoro Daddy yayi mun tambayoyin.
Share hawaye na nayi, na ƙwaƙulo murmushin ƙarfi da yaji na ɗaura shi a fuskana, tukun na amsa mishi a cikin nutsuwa, son bana son hankalin shi ya ƙara tashi, "Daddy na babu komai da ya faru, Allah ya kiyaye kuma ina cikin tsaro sosai yanzu, ka kwantar da hankalina Daddy nah, yaushe zakazo"? Na ƙarasa tambayan cike da rauni a maganan nawa.
Ajiyan zuciyar Daddy naji, chan kuma yace, "Gobe insha Allahu zan taho, domin a yanxu har na neme wani egent a Abuja ya bani tabbacin gobe akwai jirgin da zai tashi kuma zai san yadda zaiyi na samu mu taho, don Allah ki kwantar da hankalinki, idan nazo ma kawai zan taho da ke Berselona ki ƙarasa hutun ki tare da ni kinji sweet heart".
Har mun fara bacci nida Amaal sai mukaji ana knocking ƙofan mu, a razane muka tashi dukkan mu, da yake yau Ummi tace mu rufe ƙofan, mudaina barinshi a buɗe, a tsorace Amaaƙ tayi ƙarfin halin ta tambayi waye ne?
Muryan Ummi mukaji tana ƙiran Amaal ta zo ta buɗe mata ƙofan, da sauri Amaal ta sauƙa taje ta buɗe ƙofan, wanda nima dole na natashi na zauna ina kallon bakin ƙofan da Ummi zata shigo, riƙo hannun Amaal tayi suka shigo cikin ɗakin a tare, har gefe na Ummi tazo ta zauna, kuma har lokacin idona duka suna zube akan ta, ko ƙiftawa banayi na ƙura mata su don ganin yadda sukayi ja sosai, alaman bayan tafiyan mu taci kuka ba kaɗan ba.
Hankalina gaba ɗaya naji ya tashi, lokacin da Ummi ta saka hannunta ta riƙo nawa kawai sai ta fara kuka mai ratsa zuciya, ganin haka ya saka ni ƙarasawa jikinta na rungumeta, ina kuka nace, "Ummi na mai ya sameki kuma"?.
"Humairah gobe mahaifinki zaizo, inajin tausayin shi bakaɗan ba, kuma inajin tausayinki, zai ga kaman da gangan muka bar ɗan mu zai keta miki daraja, wallahi Humairah ba halin Faisal bane, narasa dalilin da ya saka shi aro wannan ɗaɓi'an, kiyi haƙuri Hummy kada zumuncin mu ya ɓaci, don Allah kiyi haƙuri"? Ta ƙarasa tana mai matuƙar zubar da hawaye.
Jikina a sanyaye na fara share mata hawayen idon ta, "Ummi don Allah kidaina kuka, insha Allahu har abada zumuncin mu yana nan, ni ae ke uwace a gare ni, kuma Faisal yayah nane, kawai yanzu ma sharrin shaiɗan ne ya shige shi, amma insha Allahu zakiga Daddy nah ya fahimci komai, kuma zumuncin mu yana nan Ummi, sai ma abinda ya ƙaro", na ƙara ina kuma jikinta na kwanta ina kukan, wanda Amaal daga inda ta ke a takure itama ta ke nata kukan.
Wannan ranan dai kam mutanen gidan gaba ɗaya basuyi bacci mai daɗi ba, duk zuciyar kowa babu daɗi har asuba tayi.
Wunin ranan gaba ɗaya Dr kin zuwa gidan yayi,dana gajji da rashin shi na ƙira shi amma sai ya nuna mun kanshi ne yake mishi ciwo, amma zuwa dare zai zo.
Haka dai muka wuni sukuku a gidan, kai hattah Faisal ɗin ma sai dana dawo ina tausaya mishi, sbd duk yadda akayi ya shigo gidan ƙi yayi, da aka matsa mishi yazo ayi breakfast sai ce wa yayi ya tashi da azumi, haka kowa ya zauna ranshi da zuciyan shi a dagule.
Daddy sai washegari da asuba jirginsu ya sauƙa, da yake ta sowan dare sukayi, jiki a sanyaye Abbu yaje taryenshi tare da driver, mu kuma aka barmu da haɗa breakfast, na lura Ummi gaba ɗaya a rashin walwala ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 28