Share this page
sai yayi hawayen da bai shirya ba, haka ya shige ya rufe kan shi. Humaira tana komawa cikin parlon sai kuma abinda tayi ya fara bata dariya, a ranta tace kullum fa Daddy sai ya mata faɗan yawan tsoron ta, faɗawa kan kujera tayi tana ta dariya, can ta tuna ko wayanta fa bata karɓa ba, sai tayi saurin tashi don tabi bayan shi ta karɓi wayan. *MAI DAMBUN AUNTY NICE, WANNAN SHAFI NAKI NE KE KAƊANKI, KIYI YADDA KIKE SO DASHI, AUNTY NICE TANA MAI KARA JINJINA MIKI, KUMA AMIƘA MUN GAISUWA GUN MAI SUNAN ƳAN GAYU, (JAN PARIH)* *©AUNTY NICE•*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:35] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_          ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 2📑* *__________📖* Daddy duk yaji daɗi ya lulluɓe shi don ganin Humairah cikin farin ciki, a haka yakama hannun ta har kan dinning suka zauna, yana dubanta cike da farin ciki yace. "sweet heart ci abincin ki bani labarin school", itama tana murmushi ta fara cin abincin wanda a tsarin sune idan kana cin abinci babu magana, saboda haka har tagama ci bata ce uffan ba, saidai ta ɗago ta dubi Daddy suyiwa juna murmushi, har ta gama ci sannan ta dubi Daddy tace. "Daddy bari naje na ɗan watsa ruwa sai nazo na baka labari", shima murmushi yayi yana jijjiga kai yana dubanta, itama da sauri ta shige ɗakinta, batafi 20mnt ba sai gata ta fito cikin wando three quater da rigan shi, sai zuba ƙamshi takeyi, gefen Daddyn ta tazauna tana lanƙwashe ƙafanta akan kujeran tana duban Daddyn, cikin zumuɗi ta ringa bashi labarin school ɗin tare da hiran lecturers ɗin. Haka sukayi ta hiran su har lokacin sallan magrib yayi, dukkan su tashi sukayi kowa ya shiga ɗakin shi, bayan sunyi ishaa Daddy ya saka ta ta fito da books ɗinta yana tayata dubawa, dayake shima Accounting yayi sai yana ƙara mata haske akan abinda ya gani a book ɗinta. Daddy bai tafi ba sai da ya mata 2wks, yaga ta ɗan sake sosai tukun ya fara shirin tafiya, Allah sarki Hummairah ranan da zai tafi kaman zatayi hauka takeji, haka tayita kuka har ya tafi, bayan nasihohi daya mata masu shiga jiki. Tafiyan shi da 1wk ta ɗan samu nutsuwa, ta mai da hankalinta akan karatun da tazoyi, zuwa wannan alaƙanta da Vicky ya koma kawai su yi gaisuwa ne, saboda ita Vicky tafi son rayuwa cikin maza, ita kuma Humairah sai suka ɗinke da wata Balarabiya mai suna Amal, wacce sai da Humairah tayi 2wks da zuwa tukun ita tazo, duk da tazo first week da aka fara lecturers, ta kuma gida saboda tana fama da ciwon sickle cell, toh bata dawo ba sai bayan 3wks, anan Humairah taga tafiyan su zaizo ɗaya, saboda Amal akwai son karatu ga kuma nutsuwa. Ranan wednesday around 10:00 muke da *ECONOMICS* dai-dai lokacin wata kyakkyawar indiyar budurwa wanda bazata wuce 30yrs ba ta shigo, wanda ita ke ɗaukan mu economics ɗin, gaskiya matar taji kyau sai wani yauƙi takeyi kamar wata ƴar 16yrs, fuskanta a ɗaure take mana lectures ɗin, wanda ko kaɗan bai mana wuyan fahimta ba, duk da babu wanda tafi takurawa da tambaya irin mu matan class ɗin, don naga daga dukkan alamu macece mai son ƙure mata ƴan'uwanta. 2hrs lecturers ta mana, dai-dai lokacin kuma Financial accounting ya iso ƙofan class ɗin, fuskan shi ɗauke da glass wanda yayi masifan karɓan shi, Dr Khadijah tsayawa tayi da lecturers ɗin ta ƙura mishi ido, abin mamaki ɗaurarren fuskanta lokaci ɗaya ya wadatu da murmushi, ta mishi wani ƙayataccen kallo, ɗagowa yayi ya dubeta sai kuma ya maida hankalin shi kan wayan da yakeyi yana jiran ta fito, haka ta gama yauƙinta ta juya tayi hanyan waje, dai-dai inda yake ta tsaya suka ɗanyi magana kaɗan, shi ya shigo ita kuma tayi hanyan waje. Tunda ya shigo muka maida hankalin mu kanshi domin kowa yana tsoron a wuce shi da abu ɗaya, don munji yace next shigowan shi zai mana text ne, yana cikin lectures kawai sai ƙaran wayata ta karaɗe class ɗin, wanda hankalin kowa ya dawo kaina saboda dokan shine duk ranan da aka bar waya a kunne yana class ɗin toh zai fita. Barin abinda yake yayi yana duban inda ringing ɗin ya fito, har idon shi yakai kaina lokacin dana kashe wayan na ɗago a tsorace ina kallon shi, don bantaɓa tsammanin nabar wayan a kunne ba, don ni babu wani silent danake sakawa kasheta gaba ɗaya nakeyi, saboda ni idan ba Daddy ba babu wani danake da shi da zai ƙirani. Ina buɗe da bakinshi naga yana tattare books ɗin shi ya nufi hanyan waje, fuskan shi ɗaure tamau, yana fita duka class ɗin suka min chaaa akaina, kowa da abinda yake furtawa wanda duk na kasa gane mai suke faɗi tsabar tsoron da nakeji cikin raina. Banyi aune ba kwai na samu kaina da miƙewa cikin gudu nayi hanyan waje, kai tsaye inda nake kallon shi na nufa da gudu, ina isa wurin shi kuma ya buɗe marfin motan shi zai shiga, banyi wani jinkiri ba na sha gaban shi na riƙe marfin motan da saurina ina sauƙe numfashi da sauri da sauri kaman zan shiɗe. Tsayawa yayi yana kallo na cike da mamaki, don shi a iya sanin shi babu wanda ya taɓa gigin taɓa mishi mota ballantana har a sha gaban shi. Cikin hakki na ɗago da sauri ina duban shi nace, "sorry sir, wallahi bantaɓa barin wayana a kunne ba idan na shiga class yauma akasi aka samu, da kuma Allah ya ƙaddara zan maka laifi, ina haɗaka da Allah ka mun uzuri a karo na farko kada laifina ya shafi mutanen class ɗin", sannan na sake murfin motan na haɗa hannaye na wuri ɗaya na ɗaga su, alaman ina neman yafiyan shi, idona suna zubar hawaye na karkata kaina na sake cewa. " plz Dr kamun uzuri kada ƴan class ɗin su tsane ni, wasu zasu gayawa parent ɗinsu, kaga idan Daddy nah yaji zaiyi fushi dani, ka kuma ni kuma zan fita har sai ka gama lectures ɗin kaji Dr mu"! ........ Da sauri ya ɗago yana kallo na da alama zuciyar shi cike take da mamaki na. Baice komai ba ya juya ya koma class ɗin, ni ma na bishi har wajen class na zauna ina ta share hawayena, na nemi wuri na zauna ban sake komawa class ɗinba, tunda ya shiga baice musu uffan ba a game da abinda ya faru ba, kawai ya cigaba da abinda yakeyi, ni kuma ina waje ina sauraran shi, kuma Alhamdulillah duk da bana class ɗin amma ina picking wasu daga abinda yake musu bayanin. Yana gamawa ya fito amma ko kallon inda nake baiyi ba, har zai wuce ta inda nake, sai na samu kaina dacewa, " Nagode Dr mu Allah ya haskaka rayuwar ka yasa kagama da iyayenka lafiya, yadda kamun Uzuri kaima Allah yasa duk wanda ka ɓata mishi ya maka, Allah ya albarkaci rayuwar ƴa'ƴanka" na faɗa ina share hawayen da ya zubo mun. Ina kallon shi yadda ya ɗaga ƙafan shi amma sai ya kasa maida ƙafan ƙasa, gaba ɗaya sai ya kasa tafiya a wurin, har Amal ta ƙaraso ta miƙa mun hannu, hannun ta na riƙe mukayi hanyan class, har muka shiga ina waiwayo wa ina kallonshi bai bar wajen ba, sai naji babu daɗi don bansan meya saka shi kasa tafiya ba. Muna shiga class naji Vicky da ƴan class ɗinmu suna magana akan sunyi mamakin dawowan *DR HISSAIN* sai ɗaya yace, "yadawo ne saboda yariɓyar ƴar country ɗin sune, bakuga har suna wani ɗan kama bama? Toh hala ƴar'uwar shi ne", yana faɗa Vicky ta juyo da sauri tana duba na, sannan tazo wurina tana tambayana dama Dr Hussain ɗan uwa nane?. *HUSAIN 80K, WANNAN SHAFIN NAKANE, IDAN KASO KA SAMMA HASSAN KAƊAN, AMMA NI AUNTY KA AUNTY NICE WA KAI KAƊAI NABAYAR, INA KUMA SANAR MAKA KAI ƘANINE MAI AMANA, NAGODE*. *©AUNTY NICE•*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_          ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 4📑* *__________📖* Ina zuwa ƙofan shi na tsaya ina murmushin gudun da nayi, a zuciya ta nace _hala shima ya razana ne yasa ya tafi ya barni a wurin_ ko kuma shima tunanin shi iri ɗaya ne da Yaya Ahmad ɗin mu, don shi kullum cewa yake al'janu nake da shi shiya sa nake yawan jin tsoro, tunanin haka ni kaɗai sai ya sakani dariya domin tunawa da nayi wata rana bayan Yayan mu ya gama mun faɗa akan yawan jin tsoro na, na juya zan tafi ɗaki fuskana a ɗaure kawai sai naji ihun shi ya tashi da gudu yayi ɗakin Maman su. Nima bayan shi nabi da gudu har ɗakin Maman, sai naji yana cewa Maman, "Gatanan ma sun sakata ta biyo ni, don Allah Mama ki koreta a ɗakin nan wallahi ina mata faɗa sai naji wani abu yabi ta ƙafana ya wuce mai shegen laushi". yana faɗa duk zufa ta jiƙa fuskan shi. Da tsawa Mama ta mun magana akan na fita na bata wuri da shegen ido na irin na mayu, cikin sauri na fito ,ina zuwa parlor sai ido na ya sauƙa akan ƴar kyanwata da ɗazu na same ta a wurin Baba maigadin mu, dariya ne ya so suɓuce mun don sai yanzu na gane abinda yabi ƙafan Yaya Ahmad wato wannan ƴar magen ne yaji laushin jikin ta a kan ƙafar shi, shi kuma yayi tunanin jinnu ne, ina ƴar munafukar dariya naje na ɗauketa na fita da sauri zuwa wurin Baba maigadi, miƙa mishi magen nayi a hankali nace, "Baba ɓoye mun ita anjima zan kawo maka madaranta da kuɗin ƙosai idan Daddy nah ya sauƙo, yanzu idan Yaya Ahmad ya gani zai mun jifa da ita don yana tsoron mage". na faɗa ina komowa cikin gida da sauri na. Ina tsaye a bakin ƙofan Dr Hussain ina ta dariyan abinda ya faru sai kawai naga ya buɗe ƙofan yana kallo ne. Da sauri na saka hannu na na rufe bakina ina maida dariya na, ido na cikin na shi nace, "Dr mu kaima kaji tsoron ko ina da al'janu ne yasa ka gudu ko? Kasan a gidan mu Yaya na Ahmad bai taɓa yadda cewa bani da al'janu ba tsabar tsoron shi, kaima kana tsoro ne?". Na faɗa ina mishi dariya. _*Hasbunallahu wa ni'imal wakil*_ ya faɗa cikin zuciyar shi, bayan ya ƙura mun ido, ganin abinda na faɗa ya sake tuna mishi cewa wataran fa *AISHA* ta taɓa faɗin irin wannan kalman, nacewa ko yana mata kallon mai jinnu ne?, runtse idon shi yayi har zuwa wani lokaci, kaman ba zai buɗe ba amma sai ya sake jin muryana ina cewa. "Dr mu don Allah kayi haƙuri ka bani phone ɗina zan gaishe da Daddy ne, kuma ina tsoron ya ƙira yaji shi a hannun wani kaga ba zai ji daɗi ba, kasan Daddy ya damu da rayuwa ta, kullum yana cemun na nisanci tarayya da maza saboda basu da amana, kaga idan yaji yana hannun ka zai ce amma yarinyar nan ƴar kawai ce, ita dana turo ta karatu me ya haɗata da maza? Bai san kuma kai ɗin ba maza bane kai Dr mu ne ba zaka cuce ni ba ko?". na faɗa ina turo kaina gaba irin ina jiran ya bani amsa. Zuciyar shi ce ta sake yankewa, domin tunawa da irin wannan kalaman daya taɓa ji a wurin Aisha, kuma tsarin maganan Aisha ne cewa, "Yaya Hussain ɗin mu". komai zata faɗa mishi sai ta dangana shi da shi nasu ne, kuma Aisha ce mace a duniya daya taɓa ganin idan bawai mutum ya cuce ta bane ta bata taɓa ƙin yarda da shi, ita kullum tunaninta zuciyar kowa mai kyau ne, saboda haka ita duk macuci sai ya nuna kaman shi, to yau ga wata Aishan a gaban shi irin Aishan su tana mishi irin maganan ta, da kuma nuna mishi yarda a lokaci ɗaya. Hawayen da yake ɓoye wane suka gangaro mishi, amma gudun kada wannan yarinyar mai surutun tace yana kuka a gaban ta sai yayi sauri ya saka hannun shi a al'jihun wandon shi ya fito da phone ɗin ya miƙa mata. Zuba mishi ido nayi cikin alamun rashin jin daɗin yanayin dana ganshi a ciki, a hankali na ɗan matso kusa da shi a hankali nace, "ka tuna da Maman kane?". Sai kuma na ɗan leƙa cikin parlon da kaina, kaman ina neman wani abu, a hankali na dawo da kaina waje cikin ƙasa-ƙasa da murya nace, "Kunyi faɗa da matar kane? Bata maka abinci bane?". Ina kallon shi idona duk a waje domin jiran me zaice mun. Babu shiri naga yayi murmushi kaɗan, kuma sai ya maida fuskar shi irin tada, baice mun komai ba naga yamayar da ƙofan ya rufe shi kuma yana shirin zuwa jikin motar shi domin ya fita a compound ɗin gaba ki ɗaya. Gudu-gudu na ƙarasa inda yake, kaman zan riga shi shiga cikin motan, ganin haka ya saka shi tsayawa yana kallo na cikin mamaki, ni kuma ɗan murmushi nayi sannan nace. "Dr'n mu hala zaka tafi weeƙend wurin wife ɗinka da yaran kane ko? To meyasa su basu zuwa maka sai dai kullum kai kaje? Ko kuma kaine kafi son zuwa ita bata so?". Shi dai kallo na kawai ya keyi cike da mamaki na, bai iya yace mun komai ba sai ido daya ƙura mun, murmushi na sake mishi sannan na cigaba da magana na, wanda ko kulawa da rashin bani amsan da yayi tun fitowar shi banyi ba, nace "Dr'n mu to ka kawo mun yaran ka mana, kaga Daddy ya hanani yawo da naje na gan su, kuma na gajji da zaman shiru ni ɗayan nan". na faɗa ina ya mutsa fuskana alaman har zuciya ta zaman ya ishe ni. "AISHA ki koma kije ki ƙira Daddyn ki, ni kuma plz ki bar ni na fita akwai abinda zanyi". kaman daga sama naji muryan shi yana faɗa mun haka. Matsawa nayi har ya shiga motan ya zauna, ni kuma hannu na yana riƙe da marfin motan, cikin shagwaɓa nace, "Dr'n mu yaushe to zaka dawo? Don Allah ka dawo yau, ni nafi soma ka dawo da su nan na dinga ganin mutanen da zan dinga hira da su". "Hira aka kawo ki kiyi ko karatu?". Ya faɗa yana rufe ƙofan shi, ina kallon shi bai sake cewa komai ba har ya fita da motan shi, na buɗe baki na zanyi magana kawai naji ƙiran Daddy na yana shigowa, da sauri na koma nawa side ɗin domin na nutsu muyi hira da Daddy na. Duk zuba idon da nayi ganin Dr ya dawo yau amma shiru har dare bai dawo ba, ina zaune ni kaɗai na naja tsaki sannan nace, _hala a wurin su zai kwana, to shi in banda shiririta meye na raba gida da matar ka? Kawai ka dawo ku zauna a wuri ɗaya ai ina ga zai fi bada ma'ana._ a zuciya ta nake faɗin hakan, can kuma na faɗa murya a bayyane nace, "Nikam ni Humaira bazan taɓa yadda na raba gida da miji na ba, duk in da yake to nima a wurin nake". ni ka ɗai sai na bawa kaina dariya ni da bani da ko saurayi mai ya kaini ma tunanin wani miji kuma? To idan ma zanyi auren wani irin miji nake so? Kuma ya ya irin tsarin mijin dana ke so zai zama, rufe idona nayi ina wassafa ya ya tsarin shi da kamanni shi yake. Nifa ina son miji fari, ina son miji dogo kaman Nuhu Arabi marigayi, to amma kuma ina son miji mai son ado da kuma son saka turare, to ya ya zai kasan ce kamanin shi?......... Da sauri na tashi daga jingunuwan da nayi domin gaba ɗaya sai naga yanayin Dr nake so, kuma kamanni shi ne suka bayyana mun a zuciyar tunani na, baki na buɗe nace, "Dr kuma ai ya girma da yawa, don daga ganin shi yana da ɗa ko ƴar da ta kai 10yrs, kai haba ba zai yiwu ba, wannan daga gani mata ɗaya ta ishe shi don tsarin shi duk na turawa ne". na faɗa ina kuma kwanciya ta a kan kujeran parlon. Agogon ƙasa ya nuna 10:00pm, ni kuma dai-dai lokacin na fito a wanka, rigan bacci iya gwaiwa na nasa ka, sannan na shafe jiki na da turaren Humra da na taho da shi, hula na mai kama da net na saka, ina cikin gyara gado na wanda ya bi jiki na dole idan zan kwanta sai na sake gyarawa, a lokacin naji an buɗe gate ɗin gidan, kuma naji ana shigowa da mota, da sauri naje na leƙa ta window kawai sai naji dariya ya suɓuce mun ganin Dr ne ya dawo, kaman wani ɗan'uwa na naji zuciya ta ta yi haske. Da gudu na fito a ɗakin nayi hanyar waje, ina buɗe ƙofa na shi kuma yana rufe motan shi, hannun shi riƙe da wani leda mai ɗan girma, banyi shiri ba kuma banyi shawara da zuciya ta ba, kawai na samu kaina da zuwa da gudu na saka hannu zan karɓi ledan hannun shi, fuska na cike da farin ciki ina faɗin, "oyoyo Dr'n mu, dama jiki na ya bani yau kam zaka dawo, ba zaka kwana a can ba, ka taho da ƴaƴan ka ne?". Na faɗa ina leƙa bayan motan. Ina tunanin ya sake mun ledan, amma sai na ji ya ƙi sakewa, da sauri na dawo da fuska na kan ta shi fuskar nace, "Dr'n mu ka bari na ɗauka maka mana, kasan na kasa bacci ina ta tunanin zaka dawo ko ba zaka dawo ba? Kasan ban ci abinci bama saboda tunanin ba zaka dawo ba, yanzu kuma ka ƙi yarda na ɗauka maka kaya? Haba Dr'n mu". na faɗa cikin sakalci da muryan kuka. Sai ji nayi ya sake mun ledan a hannu na, ni kuma da sauri na ƙarasa na shi ƙofan, wanda muke jere da shi, kuma namu yana kallon na waƴan can, ina tsaye ya ƙaraso har in da nake, baice mun komai ba ya saka key ya buɗe ƙofan ya miƙa mun hannu alaman na bashi ledan. Ido na zuba mishi alaman ya barni na wuce mishi da shi ciki, runtse idon shi yayi ya buɗe ya sauke akan nawa, kaman bazai ce uffan ba, sai kuma ya dube ni sama da ƙasa sannan yace, "Dubi irin shigan da kika yi Aisha? Ba kiji Daddy'n ki yace kada ki shigewa maza ba domin zasu iya cutar dake? To ke baki jin maganan Daddy'n kine ko kuma sakacin daga kece? Baki tunanin ni na cutar dake? Duk da kince ni ba namiji bane ba ko?". Ya faɗa yana ɗan buɗe mun idon shi a kaina. Turo mishi baki na nayi gaba kaman zanyi kuka, ina kallon shi nace ai samari ne suke cutan mata ko ƴan matan su, kai kuma ai Malamin mune idan babu idon iyayen mu ai kune iyayen mu ko? Kaga kenan kai ba zaka cuce ni ba, kuma zaka ga ai kaman ni ƴar kace tun da ban riga dana zama budurwa ba, 16yrs fa nake, kasan Daddy da wuri ya saka ni schhol". na faɗa ina langaɓar mishi da kaina. Baice mun komai ba ya juya ya shige parlon, da sauri ni kuma na bishi a baya hannu na ɗauke da ledan, wanda gaba ɗaya nauyi yamun, muna shiga nayi karo da wani daddaɗan ƙamshi mai masifar tafiya da tunanin mutum, ajiye ledan nayi ina lumshe ido, ina buɗewa muka haɗa ido da shi, ya ƙura mun ido yana kallon yadda nake nuna jin daɗi na akan ƙamshin da naji. "Yaya Hussain kai fa ɗakin ka idan mutum ya shigo sai yaji kamar kanshi zai kunce tsabar daɗin ƙamshin da yake yi, ni wallahi duk duniya ban taɓa ganin ma'abocin son ƙamshi ba irin ka, motan ka ya kama ƙamshi, kai kanka ƙamshine sunan ka, ɗakin ka kuma kaman shine company turare". muryan Aisha ya tuno wani lokaci yace ta dafa mishi indomie ta kawo mishi ɗakin shi yaji a kunnen shi kaman yanzu abun yake faruwa. Buɗe ido nayi ina duban yadda ya runtse idon shi, abin sai ya ɗaure mun kai, matsuwa nayi kusa dashi na kira sunan shi a hankali, "Dr Hussain". A razane ya buɗe idon shi ya kalle ni, sannan a zuciyar shi yace _wannan hatta muryan da yadda Aisha ke kiran sunan shi irin nata ne_. wuri ya nema ya zauna bai kalle ni ba yace, "nagode ki tafi kije ki kwanta dare yayi". yana faɗa ya komar da kanshi ya kwantar a saman kujeran da yake zaune yana runtse idon shi. "Dr gobe nayi breakfast da kai? Kana son cin ƙosai da kunun gyaɗa? Kasan ina da abin markaɗa wake, kuma last week ma nayi kunun gyaɗa na saka mishi milk yayi daɗi irin wanda ba a bawa yaro mai ƙiwuya tahm! tahm!! tohm!!!". na faɗa ina jijjiga kaina alaman idan yayi wargi bazan bashi ba. Ƙura mun ido yayi ya sake faɗi a cikin zuciyar shi _wannan kam ko dai Aisha ce su Abba suka turo ta wuri na? Don daga Ummin shi sai Aisha suka fi kowa sanin abinda yafi so da irin girkin da yafi so, to idan ba Aisha bace ya ya aka yi tasan yana son ƙosai da kunun gyaɗa kuma a saka milk a ciki?_. "AISHA Abba ne da Ummi na suka ce kizo nan ki same ni? Sunce miki idan kinzo ki gaya musu ina nan ne?". Ya faɗa idon shi a kaina. A hankali na tako har inda yake na zauna a hannun kujeran da yake, ina duban shi a nutse nace, "Daddy na bai san ka ba, amma yace mun a kwai wasu a gidan da kake, saboda lokacin da ya kama gidan ance mishi dama saura na mutum ɗaya ne, amma bai san ka ba, kuma da ya san ka daya gaya mun don ba ya ɓoye mini komai". na faɗa ina maida fuska na kaman zanyi kuka, don ganin yadda hankalin shi ya ta shi. "Don Allah kije ki kwanta nima kwanciya zanyi". ya faɗa mun ba tare da ya buɗe idon shi ba. Tashi nayi tsaye ina gyara ɗan riga na sannan nace, "don Allah nayi breakfast ɗin da kai"? Jijjiga kanshi yayi alamar eh. "What time kake ta shi saboda nasan time ɗin da zan yi so that kada ƙosan ya yi sanyi, kasan shi idan yayi sanyi baya daɗi, kuma idan an saka shi a cooler zufa ya keyi, baza kaji daɗi ba, shida indomie halin su ɗaya, kawai kyan su ana yi aci a lokacin". "Ya Rabbi". ya sake faɗa a fili bayan ya sauƙe idon shi a kaina, wanda zuciyar ji yake kaman zata ɓalle ta fito tsabar al'ajabin abinda yake faruwa. Ganin nayi hanyar waje da sauri ya buɗe bakin shi yace, "10:00am is okay". ka ɗa mi shi kai kawai na yi na buɗe ƙofan na fita. Ni Aunty Nice to meye wannan ruɗanin da yake damun Dr Hussain? na tambayi Miss Zerks da muke bin bayan Humaira, ita ma duba na tayi cikin mamaki ta ce ni fa Aunty Nice abin yana ɗaure mun kai, don kawai kada kiyi fushi ki kore ni ne kawai yasa ban tambayi Dr Hussain ɗin me yake faruwa ba. tsayawa nayi da tambayan nawa nayi ina kallon ta nace, "ko tayi kama ne da Aishan?". watsa hannun ta tayi alaman bata sani ba, sannan ta ce, "nidai Aunty Nice zan tambaye shi, amma don Allah kada ran ki ya ɓaci, haba hankalina duk yana kan nasan me yake faruwa". hararanta nayi da sauri tace, "Na fasa to". _Plsss and Plsss comment kunji mutanen kir ki._ *©AUNTY NICE•*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*

Chapter 2 of 28