Share this page
lokacin da na sauƙe ajiyan zuciya mai ƙarfi ba, wanda saida Faisal ya buɗe idon shi ya ɗaura su akaina, shi kuma baby daga ɗayan gefen shima ajiyan zuciyan yayi, murya ƙasa-ƙasa yake cewa, "baby ko dai na zo ne kina da buƙatan ganin babyn ki kusa da ke"? kasa bashi amsa nayi saboda maida hankali da nayi kan Faisal domin na ture hannun shi da yake mun yawo da shi akan cinyana, wanda yanzu yake shirin kaiwa kan gwiwa na, kuma lokaci ɗaya naji numfashina yana shirin ɗaukewa, bansan lokacin dana furta, "wayyo don Allah kabari inajin wani iri". Faisal murmushi ya farayi batare da ya daina ba saima ƙoƙarin kai hannun shi kan gwiwa na yakeyi, daga ɗayan ɓangaren kuma cikin wani irin murya mai cike da shauƙi naji Dr yana cewa, "wayyo baby nima abinda nakeji kenan ki daure na samu Daddy ko auren muyi daga baya sai muyi bikin auren yadda kike so", ya faɗa yana sauƙe ajiyan zuciya mai ɗan ƙarfi. Runtse ido na nayi da ƙarfin don abinda Faisal ya keyi yafara shiga jikina, amma da Allah ya taimakeni kawai sai naji muryan Amaal da ihu tana cewa, "meye haka bros"? Da sauri ya tashi ya zauna ni kuma nayi saurin kashe wayan na ƙura mata ido bayan na miƙe tsaye. _Kallona besty nah miss xerks tayi, cike da damuwa tace, "besty dama ma'anan sunan book ɗin naki kenan yau nake gani a tare da Faisal da Hummy"? Ba tare dana ce mata komai ba na runtse ido na cikin damuwa na cije lips ɗina_ Don Allah ku yi subscribing channal namu da ke dandalin youtube, ku latsa wannan link ɗin. Kar ku manta ku taya mu yaɗawa ga ƴan'uwa da abokan arziƙi. Mun gode. https://www.youtube.com/channel/UCeThSFXe9yNlA2iJA_IAqqA *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/23, 11:52] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 26📑* *__________📖* "Amaal me kike nufi da wannan irin ihun da kikayi? sai kace wani mummunan abu kika samu munayi"? Faisal ya faɗa kaman mai shirin kai mata duka, hankali a tashe Amaal ta dube shi tace, "abu mara kyau kake aikatawa mana bros, saboda Allah Hummy fah amanace a wurin mu, amma duk kabi kana son chanja mata rayuwa, haba bros ka daina abinda kakeyi mana, ba halinka bane fah", ta faɗa idon ta ya ciko da ƙwallah. Jan ƙafana nayi a hankali na ƙara gabanta, duk hankalina a tashe domin tunda na kashe waya Dr yake ta ƙirana amma tsoro ya hanani ɗauka, hannu na saka na riƙo na Amaal murya a hankali nace. "Amaal ba laifin shi bane, laifi nane dana bashi yake zuwa inda nake, kuma bana son na ɓata mishi raine saboda danganta kar ku da shi, amma ki sani bazan taɓa juyawa Dr baya ba, ae soyayyan Dr bata da abokin haɗi a wurina, don Allah kiyi haƙuri kuma bana son maganan nan yaje wurin su Ummi, ya tsaya a tsakanin mu insha Allahu zamu magance komai haka bazai sake faruwa ba",na faɗa nima hawaye yana zuba mun don ganin yadda hankalin Amaal ya tashi. "Hummy na yadda akwai laifinki, amma gaba ɗaya laifin nawa ne dana taho da ke ƙasan mu, yanzu idan wani abu ya faru ne zamu ce da Daddyn ki saboda Allah? don Allah Hummy ki kiyaye bana son wani abu ya faru da rayuwar ki ko kaɗan". Rungumeta nayi inajin wani irin rashin jin daɗi a zuciyata, domin ko babu komai nasan Amaal ta damu da rayuwata, kuma bata son wani mummunan abu ya faru da ni. Mtsss.... Faisal yaja tsaki yabi ta gefen mu ya fita a ɗakin, ɗagu da kaina nayi na dubi hanyar da fita, sannan na dawo da kaina kan Amaal, fuskana cike da damuwa nace, "Amaal bana so ta dalili na ku samu saɓani da ɗan'uwanki, domin nasan irin son da kuke yiwa junan ku, bana so ta dalili na kuka sa samun fahimta, ni kawai naji ma zan koma school", na faɗa ina juyawa zuwa kan bed ɗin. Takowa Amaal tayi tazo ta zauna a kusa dani tana dubana da damuwa ɗauke a fuskanta, "Hummy don Allah kada ki bari faisal ya ɓata mana jin daɗin hutun mu, don wallahi kikace zaki tafi toh nima binki zanyi mu tafi tare, ni in banda neman fitina ma, sainan da 5dys fa ya dawo, amma narasa wani fitinan ne ya dawo dashi daga kammala exams ɗin shi, yawanci yana ƙara wasu kwanaki kafin ya dawo, amma ji don ya zo ya ɓata mana hutun mu sai ya dawo, ni banji daɗi ba, kema hummy ki daina sake mishi fuska, kuma gashi Dr yana ta ƙiranki bakiyi picking call ɗin ba, har ya fara ƙiran nawa, toh yanzu me zamuce mishi bayan yaji ihuna hala". Cikin damuwa nace, "Amaal toh kisan dabaran da zakiyi kada ya fahimci wani abu don Allah", na faɗa ina zaro ido tsabar fargaba. Ɗaukan wayan Amaal tayi, bayan ta amsa mishi sallaman shi naji tana ce mishi, "wallahi na buɗe ƙofa zan shigo kawai na tafi zan faɗi ban sani ba, shiyasa na yi ihu, ina ga anyi mopping wurin bai gogu da kyau ba, kaman da sauran santsin ruwa a wurin, ita kuma hummy sai ta razana ita da Bros Faisal da yake bina a baya, amma ba komai banji ciwo ba kawai naji tsorone", ta faɗa tana maida abun dariya. A jiyan zuciya na sauƙe, ina dubanta fuskana cike da jin daɗin taimakon da tayi mun a wurin Dr. Miƙo mun wayan tayi tana dariya, da sauri na amshi wayan na kai kunne na, ina karɓa naji dariyan Dr yana cewa, "haba baby gaba ɗaya kin ɗaga mun hankali, na ɗauka wani mummunan abu ya same ki ne? Da wallahi saidai na taho babu shiri, don ko takalmi bana sakawa sai nazo naga halin da kike", ya faɗa yana ajiyan zuciyaa, nima ajiyan zuciyan nayi sannan na ƙara ninka wani ƙaryan da cewa, "na ɗauka fa Amaal zata faɗi taji ciwo ne, shiyasa naji tsoro sosai, toh Allah ma kiyaye Faisal yana binta a baya shi ya riƙeta bata faɗi ba". "Gaskiya baby nikan bana son irin wannan tsarin, ta yayah za'ayi ƙato da shi yana shigowa bedroom ɗinku? Gaskiya banji daɗiba don zai dinga kalle mun mata", ya faɗa ranshi a matuƙar ɓace. "Baby kasan fa ɗakin sister shi ne, ni ban isa ina baƙuwa na hana shi shigaba", na faɗa ina ƙasa da murya na. "Baby shima ba escuse bane, ae ɗakin sister nashi yanzu kina ciki, ke yakamata ya dinga shigo miki anyhow ne? ae ko a musulunci ɗakin ita Amaal ɗinma bai kamata ya dinga shigowa yadda ya mishi ba, shiyasa fitinu suka yi yawa a duniyar mun ta yanzu, rape yayi yawa tsakanin ɗan'uwa da ƴar'uwa, ko kuma tsakanin uba da ɗa, nidai bana son jin yana shigowa, don yau ɗaya kinsa naji hankali na yayi matuƙar tashi, kinsa wasu abu da suka wuce shekaru da yawa sun fara dawo mun cikin zuciyata, baby yanzu muna wani irin rayuwa da rape a gida ɗaya yafi faruwa, don Allah ki kula mun da kanki idan wani abu ya faru da ke, wallahi zuciyata zata fashe, don yanzu bazan sake iya ɗaukan abinda ya faru dani a baya ba, wallahi yanzu kam saidai na rasa rayuwa ta bawai nayi nesa da mutane ba, ina kuma zan sake tafiya"? Ya faɗa daga ji hawaye ne yake zuba mishi. "Wayyo baby wani abu ya taɓa faruwa da kai ne irin haka a baya? Don Allah baby kaban tarihin rayuwar ka, don Allah ka gaya mun wani abu kaɗan akan su Ummin ka da ƴan'uwanka, nima inaji a zuciyata zan iya taimaka ma koda da abu kaɗan ne domin hankalinka ya kwanta". Kashe wayan yayi, daga inda yake kuma ya fashe da kuka kaman ba Dr ba, muryah a raunane ya furta, "Baby na damu da ke, bana son wani abu ya faru da rayuwar ki, ni dama ban amince kin tafi ba, inajin tsoron larabawan nan, domi. Sun kowanne irin mazan duniya fitina akan mace, gashi ya ga irin ki mai wuyan samu, wayyo Allah ka tsare mun rayuwar future wife ɗina, Allah uwar ƴaƴanane ka tsare mun ita", ya ƙarasa yana kuka mai zafi, ya juyar da kanshi gefe ya furta a fili, "wayyo Ummi nah, wayyo Abba nah, ko ina ɗan'uwana Hassan da ƴar'uwata Aisha suke? Ko a wani irin ƙuncin rayuwa suke bayan bana nan? Don nasan abinda ya faru da familyn mu, duk zafin da sukaji zasi sake faɗawa wani yanayi bayan kuma sun tashi rana ɗaya sunga bana cikin su, gashi basu san inda nake ba a raye ko amace, wayyo Allah Aunty Hauwa na ko ina ta ke? Ina kakarmu? Gaskiya ina mssn ahalina, dama na yadda da ƙaddara na zauna da su, nasan da yanzu abun ya bar zuciyata, don nasan yanzu sukan sun samu sauƙi akan ni dana kasa mance komai, saboda nayi nesa da duk wani wanda zai kwantar mun da hankali, gashi zasuji tsoron nema na, saboda irin abunda na bar musu na kada su neme ni bayan sun tarar nayi nesa da su, Allah sarki ɗan'uwa na Hassan ko yayi aure? Ko ya tara iyali"? Sai kuma yayi murmushi shi ɗayan domin tona da Hassan idan yayi wanka yana wani taku, Ummi zatace "sai kuma wurin surkuwata ko twin"? Dariya ya keyi yace "haba Ummi gaye da ni wani batun surikuwa kuma, ae sai na cika 30yrs Ummi nah, kedai kimun fata na samu mai kyau da haɗuwa wanda tafi ƴar ki mummunan nan" zai faɗa yana nuna Aisha tsabar neman tsokana, ita kuma bata jiran komai sai ta fashe da kuka domin ta tsani ka dangantata da muni, domin Aisha ji ta keyi duk duniya babu sauran macen da tafita kyau, sai Ummi ta kwantar mata da hankali tace, "kada ki damu ƴata shima bai isa ya ƙira ki da mummuna ba, don kowa nima zai iya ƙirana da mummuna, kuma duk matar da dukkan su zasu aura ƙarya ne su samu wacce ta kaiki ballantana wacce ta fiki, sai dai ƙasa da ke auta na", a haka Ummi ta ke kashe rikicin. Nidai bana ce musu komai sai dai nayita murmushi, domin babu yadda za'ayi a zauna wuri ɗaya Aisha da Hassan basu yi faɗa ba, kuma kullum sai ya saka ta kuka, saidai a barni ko Ummi da aikin lallashi, idan Aunty Hauwa tana nan kuwa ta dinga goyon bayan Hassan kenan, akan sai ya auri wacce tafi Aisha komai da komai, shi yasa Aisha bata cika zuwa kusa da Aunty Hauwa ba, yanzu zakaji kukanta, domin Aunty Hauwa idan ta ga daman saka Aisha kuka sai dai kaji tace mata _CINCIN BREADI_ wai girman jikin Aishan, shi kuma Hassan ya samu abin dariya kenan har sai Aisha tayi kuka faɗan ya ke lafawa. _NI AUNTY NICE SHA RE HAWAYE NA NAYI DON GANIN YADDA DR YAKE SHA RE HAWAYE KUMA YANA SMILLING, GA DUKKAN ALAMU YANA MSSN ƳAN GIDAN SU SOSAI._ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/28, 15:44] Miss Xerks🌺: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°* *1441H/2020M.* ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_ ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* ```RIGIJI GABJI.``` *SHIN KE/KAI KUN TAƁA TSINTAR KAN KU CIKIN ƘANGI NA RAYUWA KAMAR HAKA:* *MUTASIM ya taso bai san su wane iyayen sa ba, be san wane shi ba, be kuma san dangin sa ba, ya tsinci kansa yana rayuwa ne shi ɗaya cikin ƙunci da wahala, Allah shine gatan sa, Mutane na ƙyamar sa, babu wani mai raɓar sa, ba shi da muhalli ba bu makwanci, ba shi da cin yau bare na gobe, talauci, damuwa, gararin rayuwa.* ```KWATSAM!``` *Ta shigo rayuwar sa, ta tausaya masa, taji ƙansa, ta taimaka masa, ta bashi Muhalli da makwanci, ta ba shi ci da sha, suka shaƙu, bata barin sa da damuwa, farinciki da walwala su ka yi masa maraba.* ```KWATSAM.``` *Soyayya mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin su, ƙauna ce zazzafa suke yiwa junan su, idan ba bu ita ba zai rayuwa ba, idan babu shi ba zata rayuwa ba, farin cikin ɗaya baya samuwa sai dana ɗaya, tayi kuka, ya yi kuka, tayi dariya, ya yi dariya, suka yi nisa a so da ƙaunar juna, burin su kasancewa a inuwa guda ɗaya, maganar aure ta shiga tsakani, a ranar ɗaurin aure.* ```KWATSAM!!!.``` *wani murɗaɗɗan AL'AMARI ya faru, aka shiga alhini, tashin hankali, damuwa ta zama sabuwa, farinciki yay ƙaura.* ```SHIN ME KUKE TUNANIN YA FARU? ME ZAI FARU? YA ABIN YA KE?.``` Read Out... *MUƘADDARI! MUƘADDARI!! MUƘADDARI!!!* Mallaki NAKI ko NAKA ta wannan hanya👇🏼 _Tura ₦200 a cikin ɗayan wannan account numbers ɗin 2209854592[ZENITH] & 0005151981[JA'IZ]._ _Ko kuma ɗaukar hoton katin waya na ETISALAT or MTN, transfer ko kuma VTU._ _Aika da shedar biya a yayin da aka yi screeshot ta ɗaya daga cikin wannan numbobin whatsapp ɗin 09066828184 & 08164475119._ *Kada ka bari, kuma kema ka da ki bari a baku labari.* *SHAFI NA 27📑* *__________📖* Amaal ce ta shigo ta sa me ni nayi nisa cikin tunani, maka mun duka tayi a lap ɗina tana hararana da wasa tace, "a haka kaman kina son Dr, amma kuma ƙasan zuciyar ki tsantsan yaudara ne". Tashi na yi zaune ina sosa inda ta maka mun marin nace, "amma kina aikata babban saɓo Amaal, ni kike gayawa bana son Dr? to ki gaggauta zuwa ki kuskure bakin ki a toilet, don kin yi mun babban laifi wanda ya kai na miki hukunci". tashi nayi na miƙa mata hannuna alaman ta riƙe ni na miƙe tsaye. Hararana tayi ta neme wuri ta zauna, "gaskiya Hummy ki daina kula Faisal, ni na haɗa ku ne don Dr ya razana ya ƙara baki muhimmanci, yasan ba shi kaɗai bane, amma ki kuma sai kina son wuce gona da iri, gaskiya ki canja tsari". ta faɗa kaman za tayi kuka. Dariya nayi mai ɗan sauti, "Amaal wallahi bana tunanin akwai wani namiji da zai juyar mun da hankalina akan Dr, babu shi saboda haka kima manta da maganan Faisal, zan kula da wannan". Faisal gaba ɗaya ya saka na daina zaman cikin ɗaki, saboda babu hali nayi wasu mintuna zaka ganshi ya shigo, kuma babu inda yake dusa sai kan bed inda nake zaune ko nake kwance, ganin haka da yake yi naji duk hutun ya fita mun a rai, saboda haka kullum ba zaka rasa ni a kitchen wurin Ummi da masu aikin gidan ba, ko kuma ina parlor ko ɗakin Ummi, abin haushi kuma babu hali yaga ina waya da Dr zai fara ƙoƙarin kai hannun shi jikina, ni kuma idan naga haka na gwammace na kashe wayan na bar wurin, wanda hakan yake saka ran Dr nah yana ɓaci. Ranan da Faisal yayi 3weeks da zuwa Ummi ta fara mishi maganan komawan shi school, amma firr yaron nan ya ƙafe shi bazai tafi ba sai ranan da zamu tafi. "Kasan dai hutunka ya ƙare, su kuma sauran 1week, to ina ruwan ka da zaman su ne kam Faisal?". Ummi ta faɗa tana duban shi. "Ummi gaskiya ni na gaya miki auren Hummy nake sonyi, to ya ya za'ayi nabarta ita kaɗai ni kuma na tafi? gaskiya ni sai ranan da zasu tafi tukun na tafi". ya faɗa da wani yanayin shahwaɓa. "Hmmm ka gamu da wahala wallahi, na gaya maka Humaira akwai wanda ta ke so, me yasa kake da son haɗa fitinane? kawai ka kama hanyar komawa ko na haɗa ka da Abbu". Ummi ta faɗa tana binshi da harara. Dariya ya yi ya tashi ya fita a ɗakin, yabar Ummi da mamakin yaushe Faisal ya canja hali haka ne wai kam?. "Baby mai kake so na shirya maka? Kasan daɗin da nake ji kuwa yau?". na faɗa mishi cike da jin daɗin wai gobe zai zo, idan munyi 5dys sai mu juya tare da shi, shi dai bai faɗa mun abinda yake so ba sai dariya na da yake ta yi. Ranan tun safe Ummi ta saka mu tashi muka fara aikin abinci domin zuwan Dr, ni dai banda farin ciki babu abinda na keji, sai snacks muke ta haɗawa iri da kala, wasu bamu soyawa ake saka su kawai a friedge, ga wani ƙaton cake da Amaal tayi baking ɗinshi, yayi matuƙar kyau sosai an rubuta sunan shi a jiki, ni dai sai farin ciki kawai na keyi. Driver ne ya ɗauke mu nida Amaal domin tafiya taryo Dr, lokacin da mukayi ido biyu da shi sai da naji gaba na ya faɗi, domin ganin irin raman da yayi, amma ya yi kyau sosai, tsabar farin ciki bansan lokacin da na tafi da gudu na rungume shi ba, shima tsabar murnan ganina rungume ni yayi ƙamƙam a jikin shi, ita kuwa Amaal tana tsaye a inda ta ke sai murmushi ta keyi cike da tausayin mu, don daga ganin mu kaman mun shekara dayawa ba muga juna ba. Da ƙyar ya iya ɗago da fuskana yana murmushi domin ganin murnan da nake yi ya koma zuban hawaye, yana goge mun hawayen yana fitar da na shi, murya a hankali yace, "to ba gani nan na zo ba, kiyi shiru ana kallon mu fa, kada wata ta balarabiya ta ƙyasa miki babyn ki". ya faɗa yana sauƙe hancin shi kan nawa. Buga ƙirjin shi nayi da ɗan ƙarfi nace, "ni kan babu mai sonka sai ni ɗaya, kuma kai baby nane ni kadai, baby naji daɗi dana ganka, nayi mssn ɗin ka sosai". shi dai murmushi yake tayi yana matsamun kafaɗa na bayan ya ɗaga idon shi daga kaina ya dubi Amaal wanda tayi saurin share hawayenta, tana murmushi ta ƙara so inda muke tsaye. Bag ɗin hannun shi ta karɓa, tana mishi sannu da zuwa, shima miƙa mata yayi yana tambayanta ya ya su Ummi? Bayan sun ɗan gaisa ne yana riƙe da hannu na muka wuce wurin motan. Gaskiya su Ummi sun yi mishi kyakkyawan tarya, daga Ummi har Abbu sun nuna jin daɗin zuwan Dr, bayan ya huta yaci abinci, sai ya gaya musu zaije ya nemi masauƙi, duk yadda su Ummi suka yi dashi ya zauna anan gidan firr ya ki amincewa, babu yadda suka iya haka suka barshi driver ya kai shi wani hotel da yake kusa da gidan su, banji daɗin ƙin zaman da yayi ba, amma da muka fito domin yi mishi rakiya, yana riƙe da hannuna muna tsaye a jikin motan ya ƙura mun ido, don sai wani shagwaɓa nake ta sauƙe mishi akan banji daɗin ƙin sauƙan da yayi anan ba. shi dai dariya kawai yake yi baice mun komai ba, can sai ga Faisal ya fito daga side ɗin shi, tunda ya ganmu tsaye da Dr ya wani ja birki yana kallon mu cike da mamaki, ganin haka ya saka Dr ya ƙara riƙe hannu na gam. Tafiya kaɗan Faisal yayi ya iso inda muke tsaye, ina tunanin zai wuce amma kawai sai yaja ya tsaya yana bin Dr da kallon banza, "Me ya fito da ke waje wurin wani bayan kin san ina sonki?". ya faɗa yana ƙoƙarin saka hannu ya jawo ni. Murmushi Dr ya yi ya maida ni ta ɗayan side ɗinshi ya rungume ni sosai a jikin shi, nima da sauri na saka hannuna duka biyu na rungume shi, hannu Dr ya miƙa mishi alaman su gaisa, amma Faisal tsaki yaja mishi yana duban idon Dr yace. "Yayah zaka shigo har gidan iyaye na kuma ka rungume matar da zan aura a gaban ido na? Kasan duk wani abinda na maka kai kajawo". *©AUNTY NICE•*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/29, 20:10] Miss Xerks🌺: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     *SHAWWAL/JUNE.* ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_          ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 28📑* *__________📖* "Yayah zaka shigo har gidan iyayena kuma ka rungume matar da zan aura a gaban ido na? Kasan duk wani abinda na maka kai kajawo". Murmushi duk na ya sake yi yana duban Faisal da ya koma kaman wani ɗan ta'adda, sai wani zare ido yakeyi kaman tsohon maye, "saurayi kayi haƙuri nazo har ƙofsn gidan mahaifinka ina ɓata maka rai, very sorry ƙanina ban so hakan ba, matsalan da aka samu na biyo wife ɗinane, amma babu komai zamu kiyaye", Dr ya ƙarasa faɗa yana ta zuba smilling yana kallon idona. Ban shiryah ba nima na samu kaina da maida mishi martanin murmushin, wanda gaba ɗaya muka maida Faisal kaman wani gunki a tsaye a kanmu, ranshi a matuƙar ɓace yaja tsaki ya wuce cikin gidan yana ta wasu ƙananun surutai wanda bamu jin abinda yake faɗi. Dawo dani gaban shi Dr yayi yana duban cikin idona, cikin nuna mun zallan so da ƙauna yace, "Baby nah don Allah ki kula mun da kanki, kinsan dai yaran larabawa ba kirki bane da su akan mace, saboda haka don Allah ki maida hankali da yaron nan, don akwai rawan kai na yarinta a kanshi sosai". Murmushi nayi ina mai ƙara damƙe hannun shi nace, Dr nah baka da matsalah da wannan, insha Allahu zan kiyaye babu abinda zai faru da yardar Allah, nidai kawai bana son wulaƙanta shi ne bayan nazo gidan su". "Toh ce mishi akayi kema baku da gida? Yasan ae kin wuce sa'ar shi a maganan soyayyah amma banda rawan kai irin na yara zai wani tsaya cike da rashin kunya a gaba na ko? Toh ya maida hankalin shi kan karatu yabar masu abu da abinsu", ya faɗa yana kanne mun ido ɗaya, "baby kinga abunda nake gudu da sauƙa a gidan nan ko? Yanzu yaron nan da anan na sauƙa zai dawo yana mun rashin kunya na kwana a gidan su ina mishi hira da mata, while kuma matar tawa ce". Murmushi nayi na sake hannun shi, marairecewa yayi shi ba zai tafi ya bar ni ba, da ƙyar na sha kanshi mukayi sallama na dawo ciki. A parlor na same su suna zaune dukkan su, daga Abbu har Ummi suma suna zaune, gefe ɗaya kuma Amaal ce zaune a kusa da Ummo, chan kan dinning kuma rasa kunya ne yake cin abinci. Zuwa nayi kusa da Amaal na zauna ina duba abinda ta keyi cikin wayanta, murmushi tayi ta ɗago mun screen ɗin wayan don naga abinda ta keyi, "abinda kika fita yi nima shi nakeyi daga nan magulmaciya", ta faɗa ƙasa-ƙasa yadda ba mai jin mu tana dariya. Nima dariyan nayi na sunkuyo dai-dai kunnen ta nace, "naku salon ba irin namu bane, mu bamu kwaikwayo amma ke gashi kinayi". Hararana tayi tace, "me na kwaikwaiya ƴar rainin wayo"? Dariya nayi ina buge bayan ta nace, "dubi abinda yake kan screen ɗinki kiga yadda kika kwaikwaye mu nida Baby". "Toh mayun soyayyah an kwaikwaya ɗin, tashi ma a kusa dani ki dena ƙare mana tanadi". Ummi ce ta dube mu fuskan ta ɗauke da murmushi tace, "sirrin me kukeyi ne ƴanmata nah"? Dariya nayi na ƙara sa gefen Ummi na zauna a ƙasa kusa da ƙafanta ina dariya nace, "Ummi kwaikwayon mu da Dr suke yi, yanzu naga ta tura mishi txt wai baby nah me kake yi? Bayan salon mu ta kwaikwaya", na faɗa ina ɗaura kaina akan cinyan Ummi ina dariyan Amaal da ta buɗe baki tana kallona. "Ashe Hummy har yanzu kina nan da halin ki na kwafsi? Toh wallahi idan kin wasa kema zan faɗi abinda kike turawa Dr". Abbu ne

Chapter 14 of 28