da ya ke tsaye, gaishe shi muka yi amma ban kalli idon shi ba, sai dai a jiki na naji ni ya ke kallo, tuna maganan Ummi nayi kada na bari ya gane na damu da shi, ina tuna hakan nayi saurin na buɗe sit ɗin baya na zauna, ƙura mun ido suka yi daga shi har Amal, amma naƙi kallon su, sai gyara books ɗi na da suke cikin bag ɗina kawai na keyi.
Ganin zamu ɓata mishi lokaci gashi ni ban fito ba, ita kuma Amal bata shiga ko'ina ba, sai yayi sauri ya dube ni yace "ya ya kika zauna a baya?".
Ina kallon books ɗina nace, "ai duk ɗaya ne da zaman bayan da gaba, ga Amal ta zauna a gaba kada mu mayar da kai driver bayan kai lecturer mu ne".
Shiga ta yi ta zauna, haka yaja motan babu wanda ya sake cewa uffan acikin mu, muna isa Department ɗin mu nayi sauri na riga fita a motan domin na hango su Ezeh zasu shiga class ɗin mu, da sauri na isa in da suke muka tsaya muna gaisawa, sannan na jira Amal ta ƙaraso in da nake muka wuce class.
Muna zama akayita zuwa ana gaishe ta, bayan kowa ya koma sit ɗin shi ta dube ni tace, "me yasa ki ka yi haka Hummy?".
"Me nayi kuma yau?".
Hmm tayi tsaki tana harara na tace, "meye ana cewa ki dawo front sit ɗin ki zauna ki ka ƙi? Bayan kinsan ke ya kamata ki zauna a wurin".
"wani irin ni ya kamata na zauna? Yadda Dr ya ke malami na kema fa malamin kine, yadda Daddy ya bashi amana na, kema fa naki Parent ɗin sun bashi, yadda yake neighbour na kema yanzu ya zama naki, duk ɗaya yake a wurin mu, kuma ɗaya muke a wurin shi".
Tsaki ta sake ja sannan tace, "amma dai kinsan da ke yafara sabawa ko".
"kema zaku saba sosai, yau da gobe ne ai babu wuya, kuma daga yau ke zaki dinga zama a gaban motan saboda ku saba kema da shi".
ina faɗa na juya na bar maganan da mu keyi haka.
Ranan yana shiga mana lectures duk ya maida hankalin shi kaina, duk abunda ya ke yi idon shi yana kaina, sannan tambaya ɗaya zai jeho mun, amma tashi na keyi na mishi bayani babu wani tsoro ko shakku a ciki.
Muna tashi na ɗauko mana handbags ɗin mu har dana Amal muka fita domin tafiya gida, a zaune a cikin motan muka sa me shi, yana ganin mu ya ƙura mun ido, amma sai nayi kaman ban ganshi ba, na kawar da kaina gefe har muka ƙarasa jikin motan, buɗe bayan nayi na shige ,ita kuma Amal ta buɗe gaban motan ta shiga.
Ina ɗaga kaina naga ya sauke mun wani mummunan harara ta madubin motan, murguɗa mishi baki nayi na kawar da kaina, jijjiga kanshi yayi irin alaman zai haɗu da ni, kallon Amal ya yi yace,
"Amal zaku iya dafa wani abu ko muje mu yi take-away?".
Juyowa ta yi ta dube ni, tana jiran taji me zance, ni kuma ganin haka ya saka na harare ta na mayar da kaina window ina kallon waje, ganin haka yasa ka ta juya tace,
"yanzu yunwa muke ji, ina ga muna yin take-away da lunch, idan yaso breakfast da dinner sai mu dinga yi da kan mu".
ta faɗa tana juyo tana kallo na.
"Hakan ma ya yi, amma maganan breakfast kam ai baku san mun, sai dai naji ƙanshi ana soya abu, saboda haka dinner ma ina tsoron na saka a raina zan samu".
ya faɗa yana kallo na ta glass ɗin motan.
Dariya Amal tayi sannan tace, "kayi haƙuri wallahi yau mun makara ne, egg kawai Hummy ta soya mana, muka sha da tea, amma insha'Allahu zamu dinga yi da kai daga yau, kuma dinner ma da kai zamu dinga yi".
Take-away yaje ya mana, muna isowa gida Amal ta ɗauki ledan da ya miƙa mata, ni kuma na ɗauki bags ɗin muka fito, har nayi kusan ƙarasawa ya ƙirani, dawowa nayi wurin shi, kallo na ya yi ganin bance komai ba yace, "wani abu yana damun ki ne?".
Turo baki na nayi gaba kaman bazan yi magana ba, can kuma na dube shi ganin irin kallon da ya ke bina da shi nayi saurin sauke ido na ƙasa ina jin faɗuwar gaba, "ni babu abinda ya ke damu na".
"To me na miki ki ka ƙi zama a front sit yau?".
Ina duban shi nace, "ba Amal ta zauna ba".
"Amal ɗin na saba da ita ne?".
ya faɗa yana hararana da wasa.
Ɗan ya mutsa fuska na nayi sannan nace, "ita ma ai zaku saba, ni yunwa na ke ji sai anjuma".
ina faɗa na juya na bar shi a tsaye a wurin.
Kasa ɗaga ƙafan shi ya yi ya bar wurin saboda mamakin irin yadda na mishi, ko kulawa na ƙi nuna mishi yau, sai yaji babu daɗi a ranshi.
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 14📑*
*MUM SAYYEED YADDA BAKI GAJJIYA DA JINJINA MUN, HAKA NIMA BA ZAN TAƁA GAJIYAWA DA BAKI ƊAN ƘARAMIN KYAUTANA NA SHAFI BA, DUK DA NASAN BA MAI YAWA BANE AMMA KIYI HAƘURI DA SHI, NA BAKI WANNAN SHAFI KYAUTA MUM SAYYEED, ALLAH YA BARMU TARE* 🤝🏻
*__________📖* Kaman bazan yi magana ba kawai na zuba mishi ido, can nace, "Toh ni ai ka zama Uncle ɗi na, kuma ai kamun girma ace kai boy friend ɗi na ne, ai Daddy idan yaji ina da boy friend ranshi zai ɓaci".
na faɗa ina lanƙwasa kai na ina kallon yadda ya ƙura mun ido.
"Na ji abinda ki ka ce, nima nasan tunanin ƴan class ɗin ku baya gaya musu gaskiya, ke ai baki wuce ƴar ciki na ba da nayi aure da wuri, dama ina son naji me zaki gaya musu idan kin koma class ɗin ne, saboda haka koma kice musu ni Baban ki ne".
ya faɗa yana kama hanyar barin wurin.
Da ɗan gudu na bishi a baya ina cewa, "Dr'n mu to egg ɗin fa? Kafasa ci ne?".
"Bana da sha'awan shi yanzu, ki koma bana son damuwa yanzu".
ya faɗa tare da barin wurin da sauri.
Na daɗe a tsaye a wurin ina mamakin yadda ya ɗaure fuska lokaci guda, ya kuma juya ya tafi kaman bai san da ni ba a wurin, haka na ƙara ci tsayuwa na na juya na koma class raina a ɓace.
Ina shiga Ezeh ya zo kusa da ni ya zauna, hannu ya saka ya buɗe text book ɗin *TAXATION* ko tambaya na komai akan Dr bai yi ba, kawai bayani ya fara mun akan in da na tambaye shi ban gane ba, muna cikin yi sai ga Vicky, zama tayi kusa da ni tana murmushi, can ta tambaye ni, "ya ya Amal da jiki?".
bayan mun yi gaisuwa ta ce da yamma zata je ta duba ta, ni kuma na gaya mata hospital ɗin da Amal ɗin ta ke, daga nan muka maida hankalin mu kan karatun da mu keyi.
Ƙaran takun takalmi muka jiwo, da sauri na ɗago na dubi mai shigowan, sanye da takalmi mai tsinin gaske, *Eesha* wannan ƴar india ne wanda ta ke ɗaukan mu *TAXATION* kuma ƙawar Dr Khadijah ce, sun yi kyau sosai, sai dai Dr Khadijah tafi kyau, ita kuma Eashaa tafi gayu, irin kallon da naga tana mun yau sai ya saka ni na kasa samun nutsuwa a class ɗin.
gashi ita ma kaman haɗin baki sai jeho mun quetions masu girma ta ke tayi, amma ko kaɗan basu ban tsoro ba, yadda nake bada amsan sai da ta tsaya wuri guda ta ƙura mun ido, can tace.
"Dr Hussain meye relation ship ɗin ku da shi?".
Ban san ya ya aka yi ba sai samun kaina nayi da ce mata, "Uncle ɗi na ne, don shi ƙanin Dad ɗi na ne".
"To me yasa yake yawo da ke? Kuma naga baya sakewa kowa fuska ya mishi murmushi amma ke yana miki? Kin tabbatar the same parent su ke da Dad ɗin ki ko kuma cousins ne?".
"The same parents su ke da Dad ɗina, Dr Hussain ne ƙaramin su, sai Aunty Aisha, ita muna kama da ita, shi kuma yana kama da Dr Hassan".
lokaci ɗaya naji na mata ƙarya don su rabu da ni, tun da naji yace ina kama da Aisha sai na gaya mata hakan.
Murmushi tayi tana kaɗa kanta alaman ta yarda, sannan tace, "me yasa Dr Khadijah Khan tace ki same ta a office ɗin ta baki je ba?".
Tsuru-Tsuru nayi da ido, can kuma sai wani dabaran yazo mun da sauri nace,
"Dr'n mu yace na daina yawon zuwa office, na ce mishi tace naje yace mun no, bai yadda naje ba, amma ita ta tambaye shi tun da yana son ta zai yadda".
Murmushi tayi ta matso in da na ke yadda ba maijin mu tace,
"ya ya ki ka san Dr yana son Khadijah?".
Juya ido na nayi kaman wata mai shirin yin bacci nace, "shi ya gaya mun tana da kyau, bai taɓa ganin mai kyau irin ta ba".
Murmushi ta sa ke yi tana duba na, "har ke duk kyawun ki bai gani ba sai na Khadijah?".
Turo baki na nayi gaba nace,
"shi ai ko sister'n shi Aisha bai taɓa cewa tana da kyau ba, ballanta na ni, amma ita Dr yana gaya mun tana da kyau kuma ai wife ɗin shi yace mun".
Jin haka ko ɓata lokaci Eashaa ba tayi ba ta fita da sauri tayi office ɗin Dr Khadijah, daga gani zata isar da saƙo ne wa Dr ƙawar ta.
Ni dai daɗi na mun rabo da su lafiya, sai suje suyi ta damuwar su a tsakanin su da Dr.
Lokacin break ya yi ni dai ban so ba haka na fita na sayi coke na sha, sannan naje nayi sallan azahar mosque.
Lectures ɗaya muke yi bayan mun dawo a break, saboda 2:30pm muke ta shi, haka aka yi muna tashi kai tsaye na wuce gida.
Sallah nayi sannan na yi wanka, ina fitowa da sauri na shirya na fita domin zuwa duba jikin Amal, ina fitowa naga motan Dr Hussain alaman yana gida, hararan gidan shin nayi, sannan na murguɗawa gidan baki na wuce na fita abuna.
Ina shiga ɗakin da aka kwantar da Amal na same ta zaune suna ta hira da Abbu da Ummi, sai dariya Amal ta keyi kaman bata yi jinya ba, wuri na samu na gaida su Abbu, sannan na tambaye su me zasu ci naje nayi mana take away?
Ummi ce ta miƙo mun wani ledan Mrs Bigs, wanda na buɗe naga fried rice ne a ciki sai queter kaza, tana murmushi tace,
"ai tun wurin 2:00pm Dr Hussain ya kawo mana abinci, yace ke sai kusan 3:00 zaki shigo, saboda haka gana ki ma, mun gode mishi da ɗawainiyan shi a gare mu wallahi".
Haka na zauna ina cin abinci na hankali kwance, ita kuma Amal sai zolaya na ta ke tayi wai, "ina Dr'n ki ne baby?".
tana yi tana dariya, amma ni ko kallon ta ban yi ba, Abbu ne kawai ya ke ta taya ta dariyan Ummi kuma tana ta mata mitan ai zasu tafi su bar ta da ni ak, kuma tana bayan nima na rama abinda ta mun.
Wurin 6:00 Dr Abdallah yazo ya bamu sallama, yana cewa Abbu jikin da sauƙi sosai, sai dai duk bayan 2wks ya kamata tana zuwa follow-up, haka muka tattara kayan mu Dr Abdallah ya maida mu gidan, sannan ya dube ni yana murmushi yace,
"ki gaida Yayan ki kuma friend ɗin ki".
ya faɗa yana mun murmushi, ni dai ko kula shi ban yi ba, haka muka shige gidan muka barshi da Abbu suna tattaunawa.
Muna sallan magrib na shiga kitchen, in da Ummi ta biyo ni, amma nayi ta roƙan ta dole ta fita ta barni, cous-cous na dafa wanda ya yi green, domin yaji food colour, sannan nayi vegetable soup wanda hanta yaji kacha-kacha a ciki, juice kala biyu na mana, ɗaya 5alive na mana, ɗaya kuma Apple ne kaɗai nayi blanding wa Amal.
Ina gamawa na wuce ɗaki nayi sallah, ina fitowa naga Abbu suna zaune da Dr Hussain suna ta magana a hankali a tsakanin su kaɗai suke jin abinda suke faɗi, gefe kuma Ummi ce da Amal ke zaune suna kallo, Amal ta kwantar da jikin ta a kafaɗan Ummi.
Shirya abincin nayi akan dinning, sannan na musu maganan su zo suci abincin, Amal ce ta fara ƙarasowa tana mun magana a hankali dai-dai kunne na tace, "Ke za kiyi saving Dr ko?".
Tana faɗa taja kujera ta zauna tana murmushin shaƙiyan ci.
Hararan ta nayi cikin wasa nace, "to sannu Mama na".
Dariya tayi mai sauti lokacin kowa ya zauna har shi Dr ɗin, "ni na isa na haifi zabgegiyar budurwa mai tashen farin jini irin ki? Wacce ni ai nayi kaɗan".
Ta faɗa tana saving kan ta tana ta dariyan ta.
"To ku mana shiru muci abinci, idan yaso sai ku tashi daga in da ku ka tsaya".
Ummi ta faɗa tana zubawa Abbu abinci, bayan ta zuba nata ta turawa Dr shima ya zuba.
Wurin gaba ɗaya ya yi shiru baka jin komai sai sautin ƙaran TV sai kuma ƙara spoons ɗin mu, kowa ya maida hankali kan abinda ya keyi, gashi daga ganin abincin ya yi daɗi, sai bin kowa da ido na ke yi, can nace.
"Abbu amma dai abincin nan ya yi daɗi ko?".
Girgiza kai kawai yake tayi, "Doughter ban taɓa cin cous-cous da ya mun daɗin wannan ba, har tunani na ke yi ko zaki gwada wa Ummin ko yadda ki ka yi, idan mun koma ta na yimun".
Dariya nayi tsabar daɗin jin abinda ya faɗa, ina kallon Ummi nace, "Ummi kema ya miki daɗi?".
Tana murmushi tace, "sosai ma, don ni ban damu da cous-cous ba, amma daga yau nima zan dinga yi saboda gaskiya ya mun daɗi, don Abbun ku da sauran ƴan uwan ku duk suna so, ni kaɗai ne bai dame ni ba, amma daga wannan naji ina so, gaskiya ya yi daɗi, Allah ya miki albarka".
ta faɗa tana duba na.
Bansan lokacin da nayi tafi ba tsabar jin daɗi, kallon Dr nayi amma shi ko alaman yabawa ban ga ya yi ba, turo baki na nayi gaba kaman zanyi mishi tambayan, amma sanin yanzu zai kushe kawai sai na fasa.
Dariya Amal tayi sannan ta ajiye spoon ɗin ta ta dubi Dr,
"Dr kai ka ɗai fa Hummy ta ke jira taji ka yaba mata, don ni ko na yaba ko kada na yaba ba zai burge ta ba".
ta faɗa tana ƙunshe dariyan ta.
Ko ɗago kan shi baiyi ba, naji yana cewa, "To ni ai kunyar Abbu ne ya saka ni cin abincin, tun daga ƙamshin girkin har ɗanɗanon shi bai yi mun ba, kawai babu yadda na iya ne, amma girki kaman ba a saka maggi ba".
Bansan lokacin da kuka ya zo mun ba da ƙarfin gaske, tashi nayi tsaye ina kallon Abbu nace,
"Abbu kaji shi ko? Wallahi bai taɓa cewa nayi abu dai-dai ba, kuma ko wani irin kwalliya nayi baya cewa nayi kyau, kuma gashi a gaban ka yace abinci na ko maggi babu, don Allah Abbu kace yace ya yi daɗi, idan ba haka ba wallahi ihu zan tayi".
na faɗa ina ƙara sautin kuka na.
Banda dariyan mugunta babu abinda Amal ta keyi, kaman bada ga gadon asibiti ta taso da ƙyar ba, amma ganta yadda ta ke dariyan mugun ta.
"Ummi kinga Amal ko".
Na sake faɗa ina kukan.
"Allah Amal zan saɓa miki idan bakiyi shiru ba, ke koda wasa za kiyi quater wannan girkin ne? Ke banda indomie me ki ka iya dafawa".
Cewar Ummi da ta ke hararan Amal.
Abbu ne ya dubi Dr Hussain yace, "haba Dr, yanzu tsakani da Allah haka zanta fi na barka da ƴaƴan amanan kana saka mun su kuka? Yanzu fa akan ido na ƴata tayi girki mai daɗin gaske amma ka ƙi yabawa? Ashe kuma dama haka ka ke kushe mata girkin ta, yau ne Allah ya kama ka ka yi a gaba na? Sannan mai kyau kaman tauraruwa amma baka taɓa yaba kyawun ta ba? Ka gaya mun akwai sauran wata mai kyau da ka taɓa gani sama da ita?"
Ɗago kai ya yi yana duba na kaman yaga kashi, sannan ya dubi Abbu yace,
"Allah Abbu bana ganin kyawun yarinyar nan, kuma ni girkin ta tayar mun zuciya ya keyi, kawai saboda kaine na ci, amma yarinyar nan jagwalgwale kawai ta keyi mutane suna ci basu sani ba".
ya faɗa yana ajiye spoon ɗin hannun shi.
Ban jira mai za ace mishi ba na juya da gudu nayi ɗaki na, ina kuka kaman ance yau ba'a ga iyaye na ba.
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 18📑*
*__________📖* Gari na wayewa muka haɗa break, a wani food wormer na zuba na Dr, mu kuma mukaci namu da sauri, muna fitowa muka samu Dr shima yana buɗe motan shi, bayan yagama duk abinda zai yi ya matso kusa da mu, muka shiga kowan mu ya gaishe shi, muna isa school na miƙa mishi breakfast ɗin shi, mu kuma muka wuce class.
Mr Solomon ya shigo mana cost accounting, bayan ya gama lectures yace next week muna da test, duk sai mukaji kanmu ya ɗau zafi, kowa ya fara maida hankalin shi kan karatu.
Dr Khadijah ce ta shigo mana ta saka wani yellow sarii, sai wani ƙamshi ta keyi mai masifan daɗi ga wani yauƙi da ta keyi kamar tarwaɗa, ina ganinta naji raina ya ɓaci, amma babu yadda na iya haka muka zauna muna binta, muna haɗa ido zata mun wani smilling, a zuciyata nace, "kazar mayu kawai, tanata wani smilling irin na neman gindin zama, irin ga ƴar uwar miji", tsaki nayi a fili wanda bansan nayi ba ma, har saida Amal ta taka mun ƙafa.
Tana gamawa Dr Hussain yana shigowa, sai wani smilling ta ke mishi lokacin da zata fita, amma shi kaman bai san da ruwan tsironta a wurin ba, amma ita abin haushi sai rangaɗi ta keyi.
Yana gama lectures yace mu shirya test ɗinshi next week monday, yana fita bai daɗe ba naji wayata tayi haske, ina dubawa naga txt ɗin shi ya shigo, da sauri na buɗe ina muushin ganin abinda ya turo,
_"babyn baby ya naga kaman maganan test ɗin nan ya firgita ki? Kada ki rasana babyn ki zai koya miki komai"_
muna tashi Dr yazo ɗaukan mu, muna fitowa muka ga Dr Khadija ta fito da sauri ta biyo shi, ganin haka yasa naja na tsaya saboda naga kaman Dr Hussain masifa yake mata, ita kuma ta tsaya a gaban shi kaman zatayi kuka, yana gama maganan ya nuna mu fuskan shi a ɗaure yana cewa, " baby kuzo mu wuce gida".
Take-away ya mana muka wuce gida, da yamma ya ƙirani a waya akan na fito na same shi a wurin da muke karatu, wanka na shiga nayi, ina fitowa na yi shiga mai kyau, sai ƙamshi nake zuba mai daɗin gaske.
Cake na ɗauka na tafi mishi da shi, bayan na haɗa da juice na coconut da muka haɗa da kanmu, ina kai mishi ya karɓa yana murmushi, ajiyewa yayi a gefe yana kallona da murmushi yace, "Baby mai kika yiwa babyn ki ne"?
Buɗe mishi plet ɗin nayi ina murmushi, ɗaukan ɗaya nayi na miƙa mishi, "Dr mu muna dawowa fah mukayi baking wannan, Allah yasa ya maka daɗi", na faɗa ina binshi da murmushi.
"Allah yasa ba jagwalgwale kika mana ba" ya faɗa yana tauna cake ɗin yana murmushi, hararan shi nayi na murguɗa baki na.
"Dr Khadija inaga tayi kusan 5yrs ko 6 tana sona, tun lokacin da muka je karatu na fahimci tana sona amma bata samu fuskana a lokacin ba, saida muka dawo daga karatu, a lokacin gidan da aka bani a staff queters itace neighbour nah, yau da gobe na bata fuska muka fara gaisawa, har wataran takan nemi alfarman na shiga da ita school, na amince mata, kawai sai ta takura rayuwata, duk inda nayi tana bibiyata, ni kuma ganin zata ta kura ni sai nazo na kama wannan gidan, nagaya mata nayi aure daga country ɗinmu, a wancan shekarun sai na samu sauƙin ta, amma yanzu kusan 2yrs ta na neman ta kurani, shiyasa nake ƙin amsa gaisuwan ta, domin akwai uncle ɗinta, daya same ni akan ta amma na nuna mishi ina da mata kuma bana ra'ayin zama da two wifes, toh abin yayi ɗan sauƙi, saidai daga zuwanki naga alaman tana neman dawo da abin baya, wanda idan kin kwantar da hankalin ki bazan taɓa cewa ina sonta ba".
"toh meyasa na ganku a wannan mall ɗin ranan tare? Kuma me yasa kake tafiya chan ka kwana"?
Murmushi yayi yana kallona, "wallahi idan kin yadda a wurin muka haɗu da ita, kuma na koma gidan ne saboda naga alaman tana son neman inda nake shiyasa wancan lokacin na koma na daɗe a wurin, shi ne lokacin da Daddyn ki ya kawo ki, tafiyan danayi na baya kuma ke kika mun laifi shiyasa nayi yaji", ya faɗa yana faɗaɗa murmushin shi, sannan ya ɗauki coconut juice ɗin ya sha, ina ganin shi ya runtse idon shi ya sauƙe a kaina, sannan yace, "Juice ɗin nan baimun daɗi ba, kaman sugar yayi yawa".
Hararan shi na sakeyi cikin wasa, "Drn mu toh ni bana son Dr Khadijan, ka daina kula ta".
"Duk yadda kika ce haka za ayi, nima bana sonta don bani da burin auren mace sama da ɗaya".
Zaro ido nayi ina kallon shi da mamaki nace, "toh kana da matar ne dama"?
"ina dai shirin yi yanzu"...
"a ina zakayi auren? Wacece zaka aura"? Na tambaye shi cikin sauri.
"Uhmmm wata yarinya nagani nake so idan ta amince zan aure ta, yarinya ce amma haka nake son aurenta idan ta amince", ya faɗa yana dubana idon shi a kanne.
Miƙewa nayi zan tafi na bar shi a wurin, yayi charaf ya riƙo hannu na yana bina da kallon mamaki.
"nidai ka sake ni zan tafi gida", na faɗa ina buga ƙafa na a ƙasa kaman zan mishi kuka.
"Toh ae bamu gama labarin mu ba zaki tafi ki barni"?
ya faɗa yana dawo dani kan kujeran da na tashi.
"nidai bana son labarin, kaje ka auri duk matan duniyan ma ni bani da case da kai, kawai ka barni na tafi, bana son ganinka", na faɗa hawaye ya fara bin fuskana.
Tashi yayi da sauri ya tsaya yana riƙe da dukkan hannu na, cikin murya mai sanyi yace, "babu ruwanki da ni kuma ina zan saka kaina naji daɗi baby"?
"wurin matan da zaka aura wanda kake son so mana" na faɗa ina juyar da kaina gefe ɗaya, bana son ganin face ɗinshi.
Shiru yayi na wani ɗan lokaci kaman bazai tanka ba, ni kuma sai kuka na ke tayi, kuma har lokacin yana riƙe da hannu na.
"Baby zaki iya ƙarasa rayuwar ki da tsoho kaman ni? Baby zaki iya bani kafaɗan da zan jingino na share hawayena daya ki tsaya a rayuwata na tsawon wasu shekaru? Baby zaki bar zuciyar ki ma wannan tsohon da yayi miki zarra da nisa a shekaru"? Ya faɗa bayan ya kulle idon shi.
_Wayyo na gajji gaskiya yau, kumun haƙuri bazaku samu jin amsan Hummy ba a yau sai a wani karon, don zanyi hutu_
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 28