Share this page
zuwa parlourn Ummi nake ta yata ɗan hira, wanda gaba ɗaya Ummi ta kasa samun lafiya, bata kwana biyu bata kwanta BPn ta ya hau ba, ita kuma Aisha gaba ɗaya ma bata fitowa parlour, kullum tana ɗaki tare da Umma da aka ɗauko ta daga misau suna kwana tare, kuma hakan wataran Umman zata zo tayita yiwa Ummi faɗan yadda ta hana kanta saƙat. Shi kuma Hassan idan mun haɗu da safe da ƙyar yake iya ɗaga ido mu gaisa, nima kuma sai ina jin shi kaman wani baƙo, bana iya sakewa kuma da shi. A haka lokaci yayita tafiya har Aisha ta cika wata uku da faruwan abin, wanda zan iya cewa baifi sau 2 na taɓa ganin ta ba tunda abin ya faru, ana saura kwana uku ta cika wata ukun na ganta tana fitowa a ɗakin Ummi da bata da lafiya tana kwance, ni kuma zan shiga duba jikin Ummin, gaba ɗaya sai danaji zuciyana ya yanke, domin wani irin rama da Aisha tayi babu komai fuskarta sai karan hanci, muna haɗa ido tayi sauri ta sunkuyar da kanta, bata iya ce mun komai ba ta ratsa ta gefe na ta wuce, haka na bita da kallon cike da tausayinta. Ina shiga ɗakin Ummi kuma na samu Umma sai faɗa take tayi mata akan ta daina yawan zama tana wannan kukan, kallon Ummi nayi ganin yadda duk itama ta rame ta fita hayyacin ta kawai sai naji kuka ya zo mun, gaskiya Hassan ya wargaza mana duk wani farin ciki na zuri'ar mu, don Aunty hauwa kullum mukayi waya don taji jikin Umm, kawai kuka zakaji tana yi, wanda ni nakasa fahimtar meye matsalan Aunty hauwa, halin da aka jefa ƴarta ce yake da munta ko kuma halin da Ummi take ciki ne damuwan ta? *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [9/10, 10:38] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 47📑* *__________📖* Zuwa nayi daff da Ummi na zauna, a hankali na kwantar da kaina a kafaɗanta ina ta share hawaye na, "haba Hussain! Me yasa kai da zaka kwantar mata da hankali sai ya zama kai ne kake tayata kukan? Shin da wanne zataji, da abinda ya faru ko kuma da ciwon da yake damunta"? Umma ta ƙarasa maganan itama tana share hawayen da suke ta zubo mata akan fuskanta. Ranan jumma'a bayan an idar da sallan Azahar sai ga Baban Narabi Uncle sabo ya kawo shi, zama sukayi a parlour aka kawo musu ruwa da abinci, bayan sun gama ya saka a ka ƙira mu dukkan mu harda Hassan muka zo parlourn, kusa da Ummi Aisha taje ta zauna, wanda tun shigowar ta Baban Narabi yake ta zolayanta, amma haka ta kasa bashi amsa, sai ma share hawaye da ta ke ta faman yi, ina zaune kusa da Hassan na sunkuyar da kaina ƙasa, don ni babu hali na dubi Ummi na sai naji kaman nayita kuka, ga gefe ɗaya idan naga Hassan nakan ji wani baƙin ciki da ban san irin shi ba, kaman daga sama naji muryan Baban Narabi ya ƙira sunana, a hankali na ɗago da kaina na ƙura mishi ido. "Hussain wannan tafiyan purposly nayi shine domin kai da ƙanwarka, tun naji ta gama watan nin da musulunci ya yardar mata idan tayi anga tsaftar mahaifanta zata iya aure? Toh Alhamdulillah Aisha bata tare da cikin Hassan ajikinta kuma anyi mata duk test da ya kamata a mata lafiyanta ƙalau, yanzu abu na gaba shine maganan auren ku, wanda ni anawa shawaran ayishi ranan jumma'a mai zuwa, amma idan kuna da wani shawaranku daga kai har iyayenka, tou ina saurarenku", ya faɗa yana maida kallon shi kan Abba da ya sunkuyar da kanshi tunda Baban ya fara magana. Da ƙyar Abba ya buɗe bakin shi yace, "Baba bamuda wani shawara sai wanda ka yanke, ɗari bisa ɗari mun amince Allah ya kaimu wannan rana da rai da lafiya", Abba yana faɗa yaja bakin shi yayi shiru. Gefe ɗaya kuma Ummi ce da Aisha suke ta kuka wanda bansan meye dalilin su ba, wanda ni a tunanina ni yakamata na zauna nayita kukan, tunda macen da na fi so yau an wayi gari ɗan'uwa naafi kusanci dani, wanda ko a ciki tare muka zauna, yayi mata fyaɗe, haba da ne zanji suke tunani? Sunaga zan iya rayuwa da Aisha bayan Hassan yana raye? Kullum da abin zan dinga ganin shi, kuma bazan iya rayuwar aure da Aisha ba duk son da nake mata, a hankali na ɗago kaina na dube su, baki na rawa na fara magana. "Baba kabawa Ummi na haƙuri ta rage irin kukan da ta keyi saboda samun lafiyanta, nidai har ga Allah ba zanji daɗin kullum ina buɗan ido inaga tashin hankali a tare da ita ba, tayi haƙuri don Allah", na samu bakina da chanja abinda nayi niyan faɗa, wanda ina jin tsoron idan na faɗa yayah Ummi zataji a lokacin, kawai nabar wa raina na aikata shi kawai basai na faɗa ba, saboda kada Ummi na ta faɗi abinda bazan iya aiwatar da komai ba. Baban Narabi ne yayita mana nasiha gaba ɗayan mu, wanda Alhamdulillah naga alaman sauƙi a fuskar Ummi na, wanda ganin hakan ya saka ni ajiyan zuciya mai ƙarfi. Bayan sallan la'asar Baba suka wuce Narabi, inda zuwa safiya naga Ummi sun fara shirye-shiryen aure a gidan, daga ɗayan gefen kuma Mama ce tazo daga misau inda Umma suka haɗo suka fara yiwa Aisha gyara na musamman, gida dai naga alaman an rinchaɓe da shiri. Ranan talata wanda ya kasance sauran 3dys auren nagama duk wani shiri da zanyi, zuwa dare hatta mai mashin ɗin da zai zo ya ɗauke ni da Asuba na nema, ana idar da sallan ishaa na wuce parlourn Abba. Tunda na zauna Abba ya maida hankalin shi kaina, sai gaya mun abubuwan daya shafi rayuwar shi kawai yakeyi, zuwa wani lokaci yaje ya ɗauko mum key ɗin gida ya miƙa mun, yana duba na da murmushi yace. "Hussain kaine sanyi idanuna, wannan key na gidana da yake sir kashim road ne na baka shi duniya da lahira, dama na gayawa duk wanda ya kamata su sani, nabawa Ummin ka ɗayan key ɗin wanda tace zuwa gobe zasije suyi jere wa Aisha, wannan kuma nakane, Hussain Allah yayiwa rayuwarka albarka, Allah yasa duk inda kasanya ƙafanka kashiga kaga haske da rufin asiri a rayuwarka, Hussain yadda ka faranta mun ina roƙon Allah yabaka yaran da zasu maka sama da yadda kamun, Hussain duk wani abu da kamun daga ranan haihuwarka har zuwa yanzu har zuwa ƙarshen rayuwarka na yafe maka shi duniya da lahira", duk sai naji kaman nafasa ƙudirina, amma ina bazan iya rayuwa da matar da ɗan'uwa na ya kusance taba, har abada bazan samu nutsuwa da ita ba, rasa abinda zanyi nayi, kawai sai naje na rungume shi na fashe da kuka, abin mamaki duk dauriya da ƙarfin halin Abba, amma sai kawai naji shi yana kuka kaman mace, wanda nayi imani da Allah tunda abin nan ya faru bai samu ya cire abin a ranshi ba sai yau, saboda haka barin shi nayi yayi iya son ranshi, wurin ƙarfe tara na mishi sallama nace zan duba Ummi ne, da ƙyar Abba ya barni nabar parlourn kaman wanda yasan abunda yake mine ɗina. A zaune a bakin gadonta na sameta tana zuba wasu ƴan kunnaye a cikin kid ɗinta, ganina ya saka tayi murmushi, nima maida mata martanin murmushin nayi, a hankali na karasa inda take, hannu na saka na matsar da kid ɗin na zauna a gefenta, ita ma hannu ta saka ta maida kaina kan kafaɗanta. "Ummi nah!" na faɗa bayan na kwantar da kaina da kyau a jikinta, "Autana!" itama ta faɗa tana shafa kaina, da sauri na ɗago da kaina muka ƙurawa juna ido, daga nan mukayi dariya wa junan mu, domin idan taso raha takance mun yayan auta, yau kuma ta ƙirani da autan, wato ta tabbatar yanzu ni autan tane. Murya a hankali nace, "Ummi na ina sonki, kuma bana son na dinga ganin tears a fuskar ki, ummi bana son na dinga ganin wani ya ɓata miki rai ballantana ni da kaina, Ummi duk abinda na miki daga ranan da kika haifeni ki yafe mun". Shafa kaina ta dinga yi a hankali, chan kuma sai naji muryanta tana cewa, "Alhussain, wallahi tun daga haihuwarka har ka koma ga mahalicci na yafe maka duniya da lahira, ina roƙan Allah ya haska rayuwarku kaida ɗan'uwanka, Allah ya kare mun gabanku da bayanku, duk inda kuke a duniya Allah ya tsare mun ku", shiru tayi na wani ɗan lokacin sannan ta cigaba da cewa. "Hussain damuwa ɗayane, me hauwa zataji a zuciyarya? Na hanata xama da ƴarta, na hanata nunawa ƴarta ita ta haifeta, a ƙarshe kuma ga abinda ɗana yayiwa ƴarta, shin haiwa zata iya mantawa da wannan al'amari kuwa? Kullum sai nayi kukan abinda ya faru, ga tsananin kunyar Aisha da nakeji, domin bansan da wani ido Aisha zata dinga dubana da shiba, gashi tun ranan har zuwa yau ta kasa dogon magana da ni, iyakarta gaisuwa shima ba kullum ba Hussain", Ummi ta ƙarasa faɗi tana kuka. Hakan Nayita kwantar wa Ummi nah da hankali kuma na mata alƙawarin zan fahimtar da Aisha komai, amma nafi son Ummin ta kwantar da hankalinta tukun, haka mukayi ta hira har nagaya mata kyautar da Abba ya bani na gida, amma murmushi tayi tace ya gaya mata, hannu na saka a aljihuna na fito da key ɗin na miƙa mata nace ta riƙe mun idan zanje gidan zanzo na karɓi key ɗin, babu wani tunanin komai ta karɓi key ɗin, wurin 11:00 na dare mukayi sallama da ita na fita a ɗakin. Ɗakin Aisha na wuce, inda na sameta suna shirin kwanciya ita da Mama da Umma, bayan mun gaisa dasu nacewa Aishan tazo parlourn ta same ni, na zauna banfi minti 2 ba ta fito da zunbulelen hijabinta, har ƙasa ta tsuguna ta gaisheni, sai naji wani tausayinta kaman na fashe da kuka, a lokacin naji haushin Hassan ya mamaye zuciyata, ban san lokacin da na furta "Allah ya isa tsakanina da kai Hassan", da sauri Aisha ta ɗago idonta ta dubeni, sannan tayi ƙasa da kanta tace Yayah kana kishi a kaina ne? Kana sonane yayah?" duban ta nayi a zuciyata nace wato Aisha har gobe babu abinda ta keso sama da na furta mata ina sonta ko? Murmushi nayi na dubeta a hankali nace, "meye riban idan nace ina sonki bayan wani ya rigani furta yana sonki"?. Murmushi tayi tace, "Yayah aiko raina ne yake shirin fita babu abinda zan so irin naji kalmar ka kace, "Aisha ina sonki, toh bansan da wani farin ciki zan koma ga mahaliccina ba, domin nayi imani da Allah ko ajiye mu gida ɗaya akayi da kai bazaka taɓa aikata mun irin cin amanan da Hassan yayi mun ba", ta ƙarasa faɗi tana share hawayenta. "Aisha ina sonki! Ina sonki!! Ina sonki!!! Amma kinsaka jikina yana sanyi da ke saboda naga kaman kina fushi da Ummi na, wanda gaba ɗaya kin saka ta daina walwala damu irin nada, Aishan mu banji daɗi ba", na ƙarasa ina jijjiga kaina. Matsuwa tayi da rarrafe har kusa da ƙafana fuskarta ɗauke da murmushi tace, "Yayah nah ko yau Allah ya ɗauki raina burina ya cika, mutumin da na rayu da son shi ya furta mun yana sona sau uku, nagode yayah nah! Nagode yayah nah!! Ummi kuma wallahi tausayinta ne yake saka ni kasa sakewa da ita, saboda Ummi ta nuna mun so sama da abinda ta haifa, amma ɗanta yazo ya cutar dani, shiyasa kullum na dubeta sai naga damuwan abun a kwance a fuskarta, ni kuma sai naji banji daɗiba, kuma ina samun rashin nutsuwa idan na ganta a haka, yayahn mu kuma ni bana so ace Aunty hauwa ce mamana, nafi son Ummin," ta faɗa tana turo bakinta gaba zatayi kuka. Murmushi nayi ina dubanta nace, "tou idan da ba Aunty hauwa bace ta taimaka ta haife ki tou yayah kike tunanin zan furta miki ina sonki"? Buɗe baki tayi tana kare hannunta akai, dariya tayi tace, "nafi son Ummi ta haife ni, ku kuma Auntyn Hauwan". Dariya nayi nace, "tou mun yarda daga yau kece ƴar Ummi mu kuma Aunty hauwa, saboda haka tashi muje muyiwa Ummi albishir ko zata samu yau tayi bacci mai daɗi". Sallama mukayi muka buɗe ɗakin Ummin, lokacin ta fito daga toilet daga gani alwalah ta ɗauro, da gudu Aisha taje ta rungumeta tana dariyanta irin na da tace, "Ummi mun yarda nida yayah na, daga yau kice kika haifeni ni kaɗaina, su kuma Aunty hauwa ce maman su, kinga an raba ko Ummi? Kuma kullum ni kaɗai zakiyi taso". Murmushi Ummi tayi tana duba na kaman tazo ta goyani ta keji, a hankali tace, "Allah yayi muku albarka, tabbas na yadda ki kaɗaice ƴata, kai kuma hussain kaxama surukina saboda haka fita kabawa uwa da ƴarta wuri zasuyi shawara", dariya dukkansu sukayi wanda nima sai da suka sakani nayi bayan hawaye ya cika mun ido, ina dubansu da yadda suka manne da junan su, sai naji kaman kada na tafi na barsu, domin nasan yanzu abu mafi tashin hankali da zasu shiga shine rashina kusa da su, amma kuwa bazan iya buɗe baki nace bazan iya auren Aisha ba, saboda Hassan, kuma bazan iya auren ta ina tunanin Hassan ne yafara kusantar ta kafin ni ba, haka na ɗaga musu hannu alaman bye-bye, na juya zan fita. "Yayah mu!" naji muryan Aisha a hankali ta ƙirani, a hankali na share hawayena na juyo ina duban su, "Yayan mu yau a ɗakin Ummina zan kwana, saboda haka kada kamana sammakon zuwa da sassafe, kabar mu sai mun neme ka", ta ƙarasa tana rungume Ummi, ni kuma kasa ce mata komai nayi tsabar tausayinta, murmushi kawai nayi na juya na fita. Ƙiran sallah asuba ya tashe ni, da wuri naja jaka na wanda kaya na basu da yawa a ciki, saidai dukkan credentials ɗina suna ciki, ɗakin Hassan na buɗe na ganshi a dunƙule yana jin sanyin Ac, rage AC nayi na dube shi na share hawayena, sannan naja ƙofan na fita, ina zuwa ƙofar gate naga bangies mai achaɓa, hawa nayi mukayi gaba dashi. *BARCELONA* Shine inda ya mun na taho, saboda nan ne inda na tabbatar su Abba baza suyi tunanin zuwa na ba, duk da lettern dana bawa bangies nace yabawa Abba nah, nagaya mishi dalilin tafiyana, kuma na basu tabbacin kada ma su fara nema na, don nayi nisa kada su wahalar da kansu. Yana zuwa nan ya ɗago da idon shi da sukayi jaa ya ƙura man shi, nima share hawayena nayi ina duban Daddy da naga shima hawaye yake tayi babu ƙaƙƙautawa, a zuciyana ina jin tausayin Dr nah babu adadi, duk da chan ƙasar zuciyata inajin zafin Aishan tunda ya taɓa furta mata kalmar so, wato ya taɓa son wata kafin ni kenan. Daga nan Dr Hussain ya cigaba da bawa su Daddy labarin haɗuwar shi dani a school da irin alƙawarin da mukayi wa junan mu, ya basu labarin har zuwa tahowa na saudi. "Ikon Allah Daddy ya furta da ƙarfi yana duban Dr yace, *ƘADDARA TA RIGA FATA* shine labarin ka kam Dr, toh yanzu ma jikina yana bani akwai aure kuwa tsakaninka da Hummy? Gaskiya ina tantama Dr" Daddy ya faɗa yana share wani hawayen. Da sauri Abbu ya ɗago yana duban Daddy yace, "kasan shine? Kuma kasan wani alaƙa ne tsakanin shi da Hummyn"? Duk a firgice Abbu ya jeho da tambayoyin wa Daddy. Shima Dr a razane yake duban Daddyn, yana kuma jira yaji me Daddyn zaice. "Kunsan danganta kar dake tsakanin Hummy da Aisha da kuma Hassan ne"? _TOH MAKARANTA KARATUN ƘADDARA TA TIGA FATA KU KASANCE DANI A SHAFI NA GABA DOMIN JIN ME ZATA KASAN CE, MEYE KUMA DANGANTA KAR HUMMY DA HASSAN DA KUMA AISHA, NIDAI BAZAN FASA SANAR DAKU DUNAN BOOK ƊIN BA, *ƘADDARA TA RIGA FATA*_ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [9/11, 17:42] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 48📑* *__________📖* Hannu Daddy ya saka ya matso da ni kusa da shi, jiki na rawa na kwantar da kaina a kafaɗan Daddy, duk wani tsoro da firgici ya gama bayyana a fuskana da gangan jikina, don har a zuciyana ina gudun abinda zai sa aure tsakanina da Dr ya haramta, a zuciyana sai addu'a nake Allah yasa Daddy na shine mahaifina, Allah yasa ba riƙo na Daddy yayi ba, a fakaice na maida kallona kan Dr mu, amma dukkan hankalinshi da nutsuwar shi yana kan Daddy, dole na dawo da dubana kan Daddy da naji yana gyaran murya. "Ranan monday na dawo daga office kenan na samu ƙiran wayan Baba nah, inda yace mun duk abinda nakeyi ya bani zuwa gobe da safe na taho Tilde, tambayan shi lafiya nayi tayi amma ya amsa mun da lafiya kawai yana nema nane da gaggawa. Lokacin ina zaune a cikin garin jos, ina da mata ɗaya da yara uku, dukkan su maza, akwai Ahmad wanda shine babban su, sai Aliyu mai bi mishi sai kuma Kabir wanda lokacin ana shayar dashi bai wuce 1yr ba, Ahmad kuma yakai 11yrs, Aliyu kuma yana 6yrs, akwai tazara tsakanin haihuwar yaran mu, wanda lokacin da mukayi aure saida matata tayi 9yrs tukun ta samu haihuwa, don har mun cire rai da samun haihuwar, escuse na ɗauka a wurin aiki na taho Tilde domin halartar ƙiran Baba nah. Bayan mun gaisa da mutanen gidan ne na shige kai tsaye zuwa parlourn Baban mu, bayan gaisuwa da tambayan iyalina na tattaro duk kan nutsuwa na da hankalina na miƙa mishi, don sauraron abinda zai ce mun, gyaran murya yayi sannan ya fara da. "Muhammadu a jiyane surukin marigayiyah ya zo har nan Tilde inda yake sanar dani dukkan abinda yake faruwa da jikarshi ƴar wurin Umar marigayi", anan dai Baba nah yayi mun bayanin dukkan abinda ya faru da Aisha da kuma tambayana ina nan akan bakan zan aure ta ko kuma su barta ta koma karatu? Ajiyan zuciya nayi lokaci ɗaya naji wani irin kwanciyar hankali ya ziyarceni, domin haka kawai Allah ya saka mun ƙaunar Aisha a raina, duk da idan da na haihu da wuri, tou da zan haifi wacce ta kaita, amma ina jin wani irin ƙaunarta a raina, don ko da Baba na ya mun bayanin raping ɗinta da ɗan'uwanta yayi bai sa naji bazan iya aurenta ba, na daiji rashin daɗi, amma kuma Allah yana gani ina son ƴar kyakkyawar yarinyar mai fara'ar nan, babu ɓata lokaci na sanar da Baba abinda yake zuciyana na amince da auren, shi kuma Baba yace mun tou cikin satin nan yake so ayi auren idan yaso daga baya sai ta tare, amma ban ƙi wa Baba ba, na amince kuma na gaya mishi ayi auren da tarewa gaba ɗaya, ina tafiya zanje na sama mata gida a cikin jos ɗin. "Muhammadu bazaka haɗa matanka gida ɗaya bane kake nufi"? Baba ya jeho mun tambayan. Murmushi nayi ina duban shi, "Baba banida ra'ayin haɗa su gida ɗaya yanzu, saboda nasan iyalina bata da haƙuri, kuma ta haifi Aisha zaman su wuri ɗaya zai kawo matsalah, amma nafara ginina, idan Allah yasa na gama shi dukkansu zan haɗa su wuri ɗaya, saboda gidan yana da girman gaske kowa da side ɗinta, inaga hakan zaifi sauƙi", na faɗa mishi fuskana cike da murnan bani Aisha da akayi, gawani daɗi da nakeji da bansan irin shiba, haka nayi sallama da Baba na wuce jos. Gida mai 2bedroom na kamawa Aisha a cikin garin jos, haka sati na zagayowa aka ɗaura auren mu da Aisha, duk yadda naso na samu haɗin kan iyalina mu zauna mu fahimci juna abin yaƙi yiwuwa, don wani irin masifa da tashin hankali ta tayar mun, inda daƙyar iyayenta suka shiga cikin maganan aka samu sauƙin ta, don ta dage dole sai na haɗasu da Aisha, a ganinta idan ba munafurcin namiji ba wai me yasa zan rabasu gida ɗaya, a haka na sanar mata insha Allahu nanda wata shida zanyi ƙoƙarin ganin na gama ginina mun koma gaba ɗaya, tunda dama aikin gidan kaɗan ne ya saura, nan ma ban tsira ba ta fara masifar wai dama ɗayan side ɗin nayi niyyan ƙara aure ne yasaka nayi shi, bayan da nace mata wa Ahmad nayiwa, nidai ganin masifar bana kare bane ya saka na ƙyale ta nabar mata gidan, don ranan aka kawo Aisha daga bauchi, haka na tafi na sallami baƙi ni kuma na wuce gidan Aisha. Aisha nada wata uku a gidana ta fara laulayin cikin ɗan satin da basu fi uku ba, tasha wahalan gaske wanda bata iya aikata komai akanta, dole ta koma Bauchi wurin Umminta, Aisha sai da tayi wata uku da tafiya a cikin na huɗu tukun ta samu sauƙi, lokacin cikinta ya kai 5month, sai lokacin Ummi ta dawo da ita, mukuma muna ta shirin komawa sabon gida, ganin haka Ummi tace tou zasu dawo bayan 2weeks idan zamu tashi su taya Aisha parking. Haka kowa akayi, bayan 2weeks muka koma gidan mu, inda dole saida Ummi ta ɗauko yarinya daga garin misau mai suna buɗɗo tazo ta ke taya Aisha da aiyukan gida, duk yadda Aisha taso suyi zumunci da maman su Ahmad amma firr taƙi suyi, haka dole itama Aishan ta haƙura, kuma gashi har wannan lokacin bata wani iya zama dani tayi hira, saboda har lokacin zuciyarta yana ga Yayan ta Hussain, don idan ina son zama da ita muyi hira tou dole na saku mata labarin Ummi da Hussain, tou ranan zan sha labari kam, ta dinga gaya mun cewa Hussain yayi kaza yayi kaza, wataran kuma zata dube ni tace, "idan na haifi ɗa namiji sunan Yayan mu Hussain zan saka, idan mace ne kuma sunan Ummi na zan saka", idan ta faɗa sai dai na bita da tou don mu zauna lafiya. Aisha tunda cikinta ya shiga wata takwas sai ta fara kumbura, kuma lokacin babu garin Allahn da zai waye bata ɗauko kayan sanyin da muka saya ba ta ware su, zata saka rigan acikin showel ɗin ta ɗaga sama kaman tana wasa da babyn, "Yi shiru babyn Mama, yi shiru baby nah, kana so kaga yayah hussain ɗina ko? Tou yayah hussain ya gudu ya barni, ya gudu yaƙi aure na, amma kai zakaje kanemo mun yayah na, ka kawo shi har gida, idan kaje kace mishi mummyn ka tayi missing ɗinshi sosai, mummy tayi kuka babu adadi, amma na yafe mishi ya dawo ya kula da Ummi da Abba da ni da kai, kace mishi muna son shi sosai", tou ranan zata kwanta tayita kuka. Da ƙyar nake samu na shawo kanta, shima sai na mata wayo nace mata, idan ta haihu lafiya nida ita da babyn mu zamu tafi neman yayah Hussain duk inda yaje, tou ranan zanga farin cikinta haka zata fara mun shirmenta tana cewa, "hmmm muna ganin yayah na zanyi tsalle na chafke shi nace bai isa ba dole sai ya tsaya munyi aure, don bazan taɓa iya ƙarasa rayuwa na babu shi ba", tana gama faɗa kuma zata fara kuka, tana mun rantsuwar wallahi tana sonshi, na mata alƙawari zan nemo mata shi sai na barta ta aure shi. Haka zan bawa kaina haƙuri nace mata idan ta kwantar da hankalinta ta haihi lafiya, ni kuma zan nemo mata yayah ta, kuma zan bar mishi ita ya aure ta, tou zatayi ta mun addu'a da godiya, wanda ni kuma

Chapter 25 of 28