yayiwa Umma halima sallama sannan ya juya ɗauke da Aisha a kafaɗan shi, da ta ke tayi musu bye bye.
Suna fita Aunty hauwa ta dubi Umma halima tace, "Umma kinjo abinda ya faɗa ko? Kadafa ya ƙi dawo mun da ƴa ta"? Umma halima tayi murmushi tace, "bai isa ba ae Hauwa, kada ki damu da maganan shi, babu mai ƙwace miki yarinyar yanzu, ae zata zama miki rarrashi ne, yadda Umar yace haka za'ayi, mu koma duk mai son ganinta sai ya bita inda ta ke, shi kuma Abdallah idan yana son riƙonta ae sai ya haɗa gaba ɗaya ya riƙe ku".
"Chabɗi jam, ae Umma halima ni ban taɓa maganan minti goma da shi bama, kullum sai naga kaman kallon banza ma yake mun, shiyasa ma bana shiga shirgin shi, tayaya ma zan zauna a gaban shi bayan ba ɗan'uwa na bane", ta ƙara faɗa tana turo bakinta gaba.
Dariyan da Umma halima bata shiryah ba yazo mata, tana duban Aunty hauwa tace, "hauwa ae yanzu mun zama ƴan'uwan juna, ae Umar ya haɗa mu tun da yabar mana Aisha a tsakanin mu, kuma akwai yanayin da Abdallah zai iya ajiyeki daga ke har Aishan a gidan shi, mu kan ma zamu fi son hakan, amma yanzu tashi ki koma ɗaki kici gaba da addu'o'in ki, kada mi shagala ko".
Murmushi Mama tayi tana duban idon Umma halima lokacin da Aunty hauwa ta wuce ɗaki tace, "Allah ya amsa mana hakan ae zaifi kawo kwanciyar hankali" umma halima ta juya suka cigaba da zantawa a tsakanin su.
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/24, 14:40] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 38📑*
*____________* 📖 Tashi Aunty hauwa tayi zata wuce ɗaki tace wa Umma halima, "hmmm nikan ae bazan iya zama inuwa ɗaya da Abdallah ba, don wani irin son girma ne da shi, kuma bazan bashi Aisha ba don duka zai na mata, fuskan shi babu fara'a ko kaɗan", ta faɗa lokacin data ƙarasa shiga ɗakinta.
Murmushi Umma halima tayi tana jujjuya kanta, "yaro yarone" ta faɗa ita kaɗai tana murmushi, a haka Mama ta fito suka ci gaba da hiran su.
Uncle Abdallah lecturer ne a ABU Zaria, yana koyar da English, sannan kuma masters yake da shi, zuwa yanzu yana PHD ɗin shi, kuma ya kusa ƙarasawa, shi mutum ne ɗan bokon gaske, saidai wani halinshi guda ɗaya na ƙin son shiga mutane, shine abun da duk familyn su basu so, domin kafin kaga murmushi a fuskar shi toh sai wani muhimmin abu na gaske, kuma baya shigewa kowa kuma koda mahaifin shi ne, da sun gaisa zaka ga yaja bakinshi ya tsuke, saidai yayita bin mutane da kallo, sau dayawa ma idan kaji muryanshi toh shida Baba Umar ne, amma ya wuce shi bazaka ji bakin shi ba, kullum zaka ganshi da laptop kawai ya na danne dannen shi a ciki, Abdallah kenan.
Rayuwa babu wuya, yau ana saura kwana ɗaya Aunty hauwa tafita a takaba, duk wani a halin gidan Baban Narabi sunzo wuni gidan, duk wanda ka dubi fuskan shi zaka ga yanayi na jimami a tare da shi, zuwa azahar su Ummi da Abba suka ƙaraso Narabi, domin mu an bar mu a chan lagos, gidan abokin Abba aka kaimu, da yamma kuma sai ga Uncle Abdallah ya iso, amma ko kaɗan bai leƙa inda Aunty hauwa ta ke ba, aikowa yayi aka ɗauka mishi Aisha kawai, inda suka san shine yazo, ganin haka Aunty hauwa tafara nuna ɓacin ranta da fargaban kada ya ɗauke Aisha, Ummi ce tayita bata haƙuri tana nuna mata ta kwantar da hankalinta Abdallah bai isa ya ɗauki yarinyar ba bada izinin Baban shi ba, kuma ae bayi da mata ina zaikaita? Haka dai Aunty hauwa ta kwantar da hankalinta.
Washegari Baban Narabi yasaka aka taho da ita chan main house ɗinsu, inda lokacin kuma ƙanin Bappanta da kuma Uncle Auwal sunzo daga misau, a lokacin ne taga limamin garin da wani alƙali da wasu ƴan'uwan Baban Narabi guda biyu, abin tausayi a ranan aka raba gadon Baba Umar kaf, bayan anyi mishi addu'o'i, dukkan ilahirin gidan kuka sukeyi, abin tausayi hattah Baban kasa daurewa yayi, shima kukan ya dinga yi kaman yau aka mishi rasuwan.
Bayan komai ya lafa, Baban Narabi ya danƙa gadon Aisha gaba ɗaya a hannun Abba, sannan ya ɗauki kason shi daya gada ya raba shi kashi uku, ya ɗauki kashi biyu ya ƙarawa Aisha, sannan ya ɗauki kashi ɗaya ya danƙawa Uncle Abdallah yace, "Abdallah wannan dukiyar dana gada ne a wurin ɗan'uwa, amma ina son duk wani abu da zai kai lada kabarin shi kamun da shi, yazamo sadaƙatul jariya wa Umar ɗina", ya ƙarasa yana share hawayen shi, shima Uncle Abdallah sunkuyar da kai yayi yana share hawayen shi.
Baban Narabi hana su Aunty hauwa tafiya yayi a ranan yace su bari sai gobe da safe idan Allah ya kaimu, babu yadda suka iya haka suka kwana a gidan, washe gari da safe motan Uncle Abdallah yazo ya ɗauke su har misau, amma bashi ya kaisu ba wani abokin shine, Ummah halima tayi kuka kaman ranan aka mata rasuwan, haka dukkan su ƴan gidan suka haɗa mata da kaya mai ɗumbin yawa wai na fita takaba, mazan su da matansu, har da iyayen Aunty suwaiba sun aiko mata kusan kala uku da kaya wa Aisha, uban gayyan kuma akwati guda ya haɗawa Aisha, amma ita ko zani ɗaya bai mata ba.
Sun koma misau basu fi kwana biyu ba Ummi ta tattara su suka wuce lagos,ta kai kusan wata uku acan aikin ta ya samu a specialist hospital bauchi, lokacin ya zama dole ta yaye Aisha, bayan ta tafi ne kuma Uncle Abdallah yazo ya duba Aisha.
Duk yadda mutane suka so auren Aunty hauwa da Uncle Abdallah abin yaci tura, don Baban Narabi babu yadda baiyi da uncle Abdallah ba amma sai yace wai ae ita bata ƙiran shi ta gaishe shi, haka Baban zaiyi ta faɗa amma Uncle Abdallah yayi shiru.
Aisha tanada 3yrs mu kuma muna da 8yrs uncle Abdallah yayi aure, inda ya auri wata yarinyar ƴar zaria, student ɗin shi ce, a lokacin ya fara tayar da maganan shifa so yake riƙon Aisha ya dawo hannun shi, ganin haka Abba ya neme shi yayi mishi kacha-kacha, yace mishi koda Baba Umar yana raye tunda yayi mishi alƙawarin ya bashi Aisha, to ko shi bai isa ya karɓi Aisha ba ballantana shi Abdallan, shima Baban Narabi bai ƙyale shi ba, inda Umma Halima da Aunty Amina suka nuna mishi bai kyauta ba, dama ya yadda ya auri hauwa ne toh ko hutu sai Aisha ta dinga zuwan musu, amma bayi da ikon karɓan Aisha a hannun Baba Gambo, haka suka mishi babu daɗi, rai a ɓace ya miƙe yana duban Aunty hadiza da tunda aka fara maganan bata ce uffan ba, ita dai kuka kawai ta keyi, ya dubeta yace, "kin sa mutane a gaba kina ta kuka, toh ni kuma yayah kuke so nayi? Kullum sai kuce wai na auri Hauwa, meye riban auren tan bayan ba bani riƙon ƴar za'ayi ba? Kuma ita kun taɓa ce mata ta aure ni? Kala kusa yarinya ta rainani nace ina sonta", ya faɗa kaman zaiyi kuka.
Hararan shi Aunty Amina tayi sannan tace, "dalilin ka kenan da yasa kaje ka auri wanda ta kusan sa'ar ka? Don wallahi wannan mata taka fadilan tayi kusan sa'ar ka, kuma tunaninka ita hauwan ce yakamata tace tana sonka? Ina ka taɓa ganin anyi haka"?
"Toh ae sai kuce mata kun bata ni bawai ni ayita mun masifan naje na zubar da girmana a gabanta ba, ga shi dama yarinyar ba kunya bane da ita, sai tayi tayiwa mutum kallon sa'anta, ni ko na aure ta wallahi bazan ɗauki raini ba a wurinta, gashi ita tana bauchi ni ina zaria yayah za a yi"?
Yana gama faɗin abinda yake ranshi yaja tsaki shi kaɗai, murmushi Umma halima tayi, tana duban shi tace, "tun farko mai yasa baka ce kai girman kai bane yake damunka a ranka, har saida komai ya ƙure tukun zaka nuna mana gaskiyan abinda na daɗe ina ganin zahirin shi a fuskar ka"?, Aunty Amina ta dubi Umma halima tace, "kaman yayah lokaci ya ƙure Umma"?.
Ajiyan zuciya Umma halima tayi, "Amina wallahi tun rasuwar Umar Allah yaga zuciyata naso Abdallah ya auri matar nan hauwa, saboda gaskiya ƴar mutuncine, amma Abdallah yaƙi ɗaga kai, toh ni muna zumunci da iyayenta sosai, yau baifi sati ba Mamanta ta ke gaya mun wani likita a wurin aikin su ya tura manyan shi domin neman auren ita hauwar, kuma iyayenta sun amince da shi, yanzu maganar danake miki ma zuwa nanda wani watan auren za'ayi".
Share hawayen ta Aunty hadiza tayi ta dubi Umman su tace, "toh Umma ayi wa Baba magana mana a tura maganan yayah Abdallan, ina ga ae zasu fi sun na yayah Abdallan akan wani daban", ta faɗa kaman zatayi kuka.
Shima Abdallan shiru yayi yana jiran yaji mai Umma halima zata ce, amma abin mamaki sai Umma Halima tace, "gaskiya bamu isa yanzu mu tura maganan Abdallah ba, bayan tun farkon rasuwar Mahaifinta sai da yayi magana da Baban ku akan ko zai tuntuɓi Abdallah akan Hauwan? Amma firr Abdallah yaƙi maganan, toh yanzu kuma ae bamu da bakin cewa muna so".
Tashi yayi bai ce musu uffan ba ya bar cikin ɗakin Umma haliman, dukkan ido suka bishi da shi babu wanda ya hana shi fitan da zaiyi.
Aunty hauwa tana zaune a gidan wani cousin ɗinta wani likitane, yayah Aunty Ummi matar uncle auwal, yana zaune a cikin drs quaters da take kusa da asibitin, da yake night duty ta keyi ranan tana gida babu inda taje, suna zaune da matar yayan nata mai suna Aunty uwani, matace mai matuƙar kirkin gaske, duk yadda mutane suke nuna mata illar zaman Aunty hauwa a gidan ta bai dame ta ba, kowa yana ce mata mace kyakkyawa kuma yarinya ƙarama bata tsoro ta aure mata miji? amma ko kaɗan bata kula su, a haka har Aunty hauwa ta haɗu da wani Dr ɗan garin Azare wato Dr basheer.
Suna zaune akan dinning ita da ƴar Aunty uwani mai suna Nabeeha, tana ta mata assignment ɗin da aka bata, ita kuma Aunty uwani tana cikin parlourn tana zaune tana kallon wani indian film.
Ringing wayan Aunty hauwa ya fara, ganin baƙon number ta daɗe tana kallo har sai da ya kusa tsinkewa tukun ta ɗauka, "idan kina gida ki fito ina ƙofar gida", abin mamaki ya bata, ɗago wayan tayi ta duba numbern sannan ta mayar da wayan kunnenta tace, "ban gane da wa nake maganan ba, don banida number"?, "Baban Aisha ne, kina gida ne"?
Jiki a sanyaye ta amsa mishi da "ehh" bai jira wani abu ba ya kashe wayan, shiru tayi tana duban Aunty uwani da ta ke kallon ta ita ma, ta gane mai wayan tun ɗaukan ta taji irin muryan Baba Umar, amma tsoronta shine, bai taɓa ƙiranta ba a rayuwar shi, toh ko lafiya yau yazo har inda take"?
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/25, 13:41] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 39📑*
*__________📖* Bata daɗe ba ta fito daga cikin gidan, hannunta ɗauke da tray, har inda yake ta ja table ta ɗaura akai, juq ne cike da zoɓo mai ƙamshin gaske, sannan cooler kuma cike yake da jaloop rice, wanda yaji kayan haɗi har da hanta, bayan ta zuba mishi ne ta koma cikin gidan ta barshi a wurin.
Busmillah yayi ya fara cin abuncin yana ɗan sipping zoɓon kaɗan-kaɗan, sai wani lumshe ido yakeyi na jin daɗin zoɓon, haka yayita ci har yaji ya ƙoshi, bayan ya gama ne ya ɗauki jug ɗin ya cika shi da zoɓo, sannan ya ɗauki wayan shi ya danna ƙiran Aunty hauwa, tana ɗauka yace, "ki fito nagama".
Zama tayi a kan kujeran sannan ta fara gaishe shi, bayan sun gaisa ta ce, "naganka kwatsam ina fatan ba wani abu mukayi maka ba ko"? ta ƙarasa faɗi tana duban shi, murmushi yayi mai kyaun gaske yana kurɓan zoɓon yana kallon ta har cikin idonta, sannan yace, "nazo tafiya da ke ne".
Hararan shi tayi, "ni kayace da zaka zo kace zaka ɗauke ni ne"? Murmushi yayi yace, "zanje na aurar da ke ne, don naji ance baki iya zaɓe ba kin zaɓo mana wani sunduƙi", ya ƙarasa faɗa yana ajiye cup ɗin zoɓon.
"Hmmm batun yau ba na ke zaɓo sunduƙan ba kenan, tunda bashi kaɗai na fara zaɓa ba", fuskan ta a murtuƙe ta faɗa masa.
Zuba mata ido yayi batare da yace komai ba, hakan yasa ta kasa cigaba da maganan ta ta sunkuyar da idonta ƙasa.
"Hauwa bana son wannan auren da kike shirin yi, domin ina kishin wani ya aure matar ɗan'uwa na, saboda haka ni nan zan aure ki domin kada ki haɗa mana zuri'a da wasu irin kuma daban".
Tashi tayi tsaye tana bin shi da wani irin kallon mai cike da raini a ciki, "lallai Abdallah idonka baya cike da kunya, ni matar yayankan zaka duba kace wai ni zaka aura? Toh a wani hujjan? Ina ce ana wannan auren idan da akwai yara a tsakani ne? Toh ni babu wani sauran abu a tsakanina da kai, yarinya kuma ko nayi aure ba wurina zata zauna ba ballantana kace zataje gidan wani baka so, saboda haka gara ka farka daga baccin da kakeyi, ni Hauwa nafi ƙarfin na auri yaro mai raina mutane irin ka, kaje chan ka ƙarita da tsohuwar matarka ni bana so", tana faɗa ta juya cikin gidan ta bar shi zaune a parlourn yana murmushi mai cike da ɓacin rai.
Kuka ta keyi mai ƙarfin gaske inda taje ta samu Aunty Uwani ta zube tana ta kuka, Aunty uwani duk ta ruɗe sai tambayarta ta keyi mai ya faru amma taƙi faɗa mata komai sai kuka da ta keyi, ganin bazata kula ta ba yasa, ta wuce parlour wurin Abddallah, inda ta samu ya miƙe yana shirin tafiya.
Bayan sun gaisane ta tambayeshi abin da ya faru, cikin girmamawa ya gaya mata komai, yana kuma ƙasƙantar da kai alaman yana neman ta tsaya mishi akai, Aunty uwani ta yaba da Abdallah shiyasa ta bashi tabbacin zata samu ɗan'uwanta da maganan, shi kuma godiya yayi mata ya kama hanyar shi sai misau.
Tunda ya isa Bappah yake ta nannan da shi, bayan kuma ya gaya mishi abinda ya kawo shi, Bappah ba ƙaramin jin daɗi yayi ba, ƙiran Uncle Auwal yayi a waya yazo ya same shi, bayanin komai Bappah yayi mishi, shima abun yayi mishi daɗi, domin sanin kirki da karancin iyayen Baba Umar.
Bappah ya ƙira Abba ya gaya mishi duk abinda ake ciki, Abba ya nuna farin cikin shi amma yace a haƙura har sai ita Hauwan ta amince, sannan Bappah ya ƙira Baban Narabi ya zayyana mishi komai, shidai Baban Narabi murmushi yayi, a zuciyar shi yace dama yasan za'a rina wai an saci zani mahaukaciya.
Uncle Abdallah a misau ya kwana, da safe ya kama hanyar bauchi, lokacin da yaje yayi dai-dai da dawowar Aunty hauwa daga duty, tana ganin shi ta wuce bata kula shi ba, ko damuwa baiyi ba, wucewa kai tsaye yayi har parlour yayi salllama, inda Aunty uwani da yayan su Aunty hauwa suke zaune, wurin zama suka bashi cike da kulawa, bayan sun gaisa aka haɗa mishi breakfast, amma yace musu yayi a misau.
Zama sukayi shida dr Alƙali, yayan su Aunty hauwa sukayi magana mai muhimmanci, amma firr Aunty hauwa da aka mata maganan taƙi basu haɗin kai, da yake Dr Alƙali ba mai yawan magana bane sai yabawa Abdallah haƙuri akan ya tafi zai shawo kanta daga baya, babu yadda ya iya haka yayi musu sallama ya tafi, Abdallah irin mutanen nanne masu ƙin yadda suga sun faɗi a neman abu, kuma shi idan yaso abu nacin shi yana dayawa, ballanta wannan da yake ganin idan ya rasata toh zai sha kunya, a ransa ya saka duk abinda zatayi zai daure, don shi Allah kaɗai yasan irin son da yake yi mata kawai ƙarfin hali ne da kuma kada a gane ya damu da ita shiyasa bai nuna ba, kuma a tunanin shi ae Hauwa yarinya ce, dole zata koma tayi karatu ne bawai maganan aure ba, hakan da yayi niyyah ya saka shi wucewa Narabi.
A parlourn Baban Narabi ya zauna ya dinga sauƙe mishi rikicin shikan aje a nema mishi auren hauwa, inda hali ma a tafi da sadaki, Baban Narabi ƙura mishi ido yayi har na tsawon lokaci, saida ya karanci ehh tabbas Abdallah da gaske ya keyi son Hauwa ya keyi tsakani da Allah, sai yayi gyaran murya yace, "toh in banda abinka Abdullahi tun yaushe aka bika akan ka aureta kaƙi, sai yanzu da yarinya ta haɗu da wanda ta keso zamuje muce ga zance ga magana? Ina ce Aishan ko ka aureta ba baka ita za ayi ba, toh meye dalilinka na auren Hauwa?"
Kallon Baban yayi sannan ya sunkuyar da kanshi ƙasa, "nidai Baba ina sonta ne, ae nima zata haifa mun irin Aishan, ko basu bani riƙon Aishan ba hala ta haifa mun mai kama da Aishan".
Dariya baba yayi yana duban Abdallah cike da ƙaunan ɗan na shi yace, "Abdallah wato kaima sake zakayi hauwa ta sake haifan me kama da ita ba mai kama damu nan ba ko? Wani irin so kukeyiwa Hauwa ne kam"? Baba ya ƙarasa yana murmushi mai cike da jin daɗin al'amarin.
Sunkuyar da kai Abdallah yayi ƙasa, "Baba don Allah kuje ko gobe nema, naga hauwan so ta keyi ta mun yarinta, gara aje da wuri kada ta auri wancan ɗayan, ni bana son zamanta a bauchi ma wallahi don zasuna haɗuwa".
Wannan lokacin dariya mai ɗan ƙarfi Baba yayi, yana duban Abdallan cike da mamakin irin nashi kishin, "toh ka gayawa ita maiɗakin kane zaka ƙara aure"? Baba ya jefa mishi tambaya.
Abdallah ya dubi Baba yace, "Banida matsalah da Fadilah nidai damuwata a fara zuwa gidan su hauwan".
Babu ɓata lokaci Baban Narabi washe gari da ƴan'uwanshi mutum biyu, sai uncle sabo ƙanin uncle Abdallah dayaja zuwa misau. Bappah ba ƙaramin karɓa ya musu ba, bayan sun gaisa sun sha ruwa Baban Narabi yayiwa Bappah bayanin abinda ya kawosu, Bappah tashi yayi ya ƙira ɗan'uwanshi wanda yake mahaifi wa Aunty Ummi da Dr Alƙali, da yake shi bamai son wargi bane yace su tsaya ana sallan azahar a ɗaura aure kawai, babu maganan jeka ka dawo a tsakanin su, Bappah ma yayi na'am da batun ɗan'uwan shin, suma su Babam Narabi sunji daɗi ba kaɗan ba da irin dattakun da aka musu.
Ana sallan azahar aka ɗaura auren Aunty hauwa da Uncle Abdallah a masallacin ƙofan fada da yake garin misau, hattah su Mama dasu Addagana sunji daɗin wannan auren ba kaɗan ba, domin farin cikin yaxama musu biyu, inda Uncle Auwal yazo musu da labarin aikin shi daya samu da NNPC, inda Baban Misau, kuma ɗan Mutanen Misau, Dr maikanti baro Allah yajiƙanshi da rahma ya sama mishi aiki a wancan lokacin. *ALLAH KAJIƘAN DR MAIKANTI BARU, ALLAH KASA YANA CIKIN RAHMAR UBANGIJI, ALLAH KA DUBA BAYAN SHI KASHIGA AL'AMURAN SU YADDA SHINA YA SHIGA NA MUTANE, ALLAH YA HASKAKA RAYUWAR IYALANSHI*
Lokacin da aka gama ɗaura aure Baban Narabi da kanshi ya ɗaga waya ya ƙira Abdallah yana murmushi yace, "Albishir Abdallah!" cikin zaƙuwa ya amsawa Baban nashi da "goro".
"Toh yau dai Allah ya nufa an ɗaura aurenku da Hauwa, sai ka shiryah mana goron Albishir ɗinmu", Baban ya faɗa mishi cike da murna, ae babu shiri Abdallah yace, "Baba nabaka kujeran zuwa umrah kaida su Bappah, insha Allahu ku uku kushiryah tafiya zuwa nan da sati biyu", murmushi mai cike da dattaku Baban ya amsa mishi da sun gode, tukun yace ya bar maganan tarewar har sai ita hauwan ta shiryah, daga nan sukayi sallama ya kashe wayan.
Saida akayi sallan La'asar tukun su Baban Narabi da bappanun Abdallah suka dawo Narabi cike da murnan abinda ya faru, suma mutanen gidan kowa ka ganshi cike da murna a fuskar shi.
Bappah ne ya ƙira Dr Alƙali yagaya mishi an ɗaura auren Aunty Hauwa, sannan kuma yace ya sanar mata, sannan ya ƙira su Ummi ya sanar musu, ita dai Ummi taji daɗin wannan haɗin, don ko baɓu komai, baza'a rabawa Aisha hankali yadda zata fahimci wani abuba, duk ranan da taje wurin Aunty hauwa zataje ne a matsayin gidan Ummanta, Abdallah kuwa Mijin Ummanta, kenan komai zai zo mata cikin sauƙi, gaskiya Ummi taji daɗin abun ba kaɗan ba.
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[8/27, 12:09] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 40📑*
*__________📖* Dr Alƙali yaji daɗin al'amarin ba kaɗan ba, dama yana zaune a office ne, kawai sai yaji kaman yayi tsuntsuwa ya koma gida, haka ya daure ya gama duba patients ɗin da suke gaban shi, yana gama ganin su ya kamo hanyar gida.
A parlour ya samu Aunty hauwa tare da Aunty uwani suna cin abinci suna kallo kuma, yana murmushi yace, "ƴan mata sai yanzu kuke cin abinci? Laillai kuna jin daɗi fah", ya nemi wuri gefen matar shi ya zauna.
Bayan sun gaishe shi ne, suka cigaba da cin abincin sun hankali kwance, shidai sai duba abu yake a wayan shi batare da yace uffan ba kuma, suna gama ci Aunty hauwa ta miƙe zata bar wurin domin mata da mijin su samu sakewa, ganin haka yasa ya ɗago da manyan idanunshi yana murmushi yace, "amaryah dawo ki zauna, tafowan da nayi ae duk don ke ne".
Wurin data tashi ta koma ta zauna tana kallon shi, "yauwa Hauwa ɗazu Bappah ya ƙirani yake gaya mun cewa na gaya miki yau ya ɗaura miki aure da ƙanin mijinkin nan Abdallah"........ Wani irin miƙewa tayi da murya mai ƙarfin gaske tace, "a wani hujjan za'a ɗaura mun aure da mutumin da bana so" wallahi auren nan bai ɗauro ba, ko sama da ƙasa zasu haɗu toh aure bai haɗu ba", ta faɗa tana zare ido kaman zata kai duka wa Dr.
"Saboda ke kin isa da kanki ko? toh ki sani bawai barinki ake yi ba kike abinda kika gan dama hauwa, kuma baki isa kija da iyayen mu ba, aure an riga da an ɗaura ya rage naki kiyi biyayyah wa mijinki ko akasin hakan", yana gama faɗa ya miƙe yayi ɗakinshi, ita dai Aunty uwani sai juya kanta take tayi alaman bata so hakan ba, tafi so abi komai a hankali, hakan yasa ta fara rarrashin Aunty hauwa, ita kuma bata sararara ba kawai ihu da kuka ta fara, daga baya ta fita da gudu zuwa ɗakinta, inda suke tare da yaran Aunty uwani, kwanciya tayi ta fara rera kuka mai azabar taɓa zuciya.
Har akayi magrib Aunty hauwa kuka ta keyi bata saurari kowa ba, bayan tayi sallah ne ta shiga wanka domin tayi shirin tafiya night duty da ta keyi, wanda yau idan tayi zata shiga up na 1week, tana wanka ta shirya, lokacin aka ƙira ishaa, babu ɓata lokaci tayi sallan ta miƙe ta ɗauki jakanta ta fito domin tafiya, a parlourn
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 28