Share this page
juya da gudu nayi cikin ɗakin mu ina dariya, da yake duk abun da mukeyi wayan mu yana kunnen mu bamu wanda ya kashe, inajin dariyan shi ta cikin wayan yana cewa, "ƙarya na miki? Kuji mun ƴan matan nan da wayo, kina birkita ni da salon soyayyah ki kuma kina cewa baza muyi aure yanzu ba"? Ina jin shi nayi sauri na katse wayan nima ina dariya, kan bed ɗin na faɗa ina dariya ni kaɗai na. "Don Allah ki koma parlor ki kwanta, sai kiyi ta sakarcin dariyan ki achan, yarinya anje an kunche miki kai da soyayyah zaki dawo ki sauƙe mun buhuhhunan haukan anan ko? Toh baki isa ba, koma kije chan ko kwana kuna gigita junan ku", Amaal ta faɗa tana turo ni daga kan gadon. Dariya nayi ina faɗin, "baza ki gane bane Amaaƙ ɗita, bansan me nakeji ba acikin zuciyata ga me da Dr, ina mishi wani fitinannen so, wanda yana nema ya fi ƙarfin xuciyata", na faɗa ina dafa zuciyar bayan na runtse idona. Kallon mamaki Amaal ta ke mun, "kice bazamu gama school ba za a muku aure"? Hararan ta nayi, "kaji mun Amaal, bamu gama school ba kuma a mun aure? ae ban girma ba tukun, gara dai sai nagama masters sai amana, lokacin na ƙara girma". "Chabb ae ko ba son shi kikeyi ba, tun da har son ya fara fin ƙarfin zuciyar ki ae sai a tattara mishi ke a haɗa ku gida ɗaya, ku cinye kanku da soyayyah, amma ni bazan yadda kije ya birkita ki kizo kina hana ni bacci ba, ehen gara ma ki gane", Amaal ta faɗa tana komawa tana kwanciya. Rayuwar yana ta tafiya, a yau muka fara exams ɗin wannan semester, gaba ɗaya mun koma wasu iri, domin dukkan mu muna so mu fito da sakamako mai kyau, duk da irin zafin da muke bawa kanmu, bamu rage komai ba ga me da soyayyah mu, duk abinda muke yi dole sai mun bada lokaci na musamman wa junan mu,una yiwa junan mu so na fitar hankali, gashi bamu iya ɗaukan lokacin bamu neme junan ba, haka wurin Amaal da Dr Abdallah, kullum suna tare da juna, duk yadda kake tunanin sun wuce wurin, domin wani irin kula Dr yake bawa Amaal, kaman ya maida ta ciki. Daddy hankalin shi ya kwanta sosai, gashi Abbun Amaal yace mishi idan munyi hutu zai haɗa ni da Amaal muje muyi hutu tare a wurin su, domin shi Daddy yace baya son nazo hutu har sai na gama karatu na gaba ɗaya, saboda shi baiga me zai saka na taho hutun ba, gara shi idan anyi hutun ya zo mun, amma jin cewa Abbu yace zamuje wurin shi sai Daddy ya samu nutsuwa, domin dama tunanin shi ko naje gida bawani daɗin zama zamuyi da su Mama ba, gashi anyi auren Adda hafsat Adda Halima ce a gida, shima Yayah Ahmed dama na taho ana shirin auren shi, ganin basu damu dani da rayuwa ta ba, Daddy bai ko gaya mun anyi auren Yayah Ahmed ba. Ranan da mukayi final exam ɗin mu, rana ce da bazan taɓa mantawa ba, domin a wannan ranan zuciyata ta aminta da irin son da Dr nah yake mun, sannan a wannan ranan na barwa zuciyata ko bai taɓa furta mun kalmar I Luv U ba, toh zan iya ƙarasa rayuwata da shi, domin ya nunawa duniya babu wata mace a zuciyar shi sama dani. Bayan mun gama paper muna ta sallama da ƴan class ɗinmu, shi kuma yazo ɗaukan mu domin mu wuce gida, Amaal ta gajji da jirana saboda complain da ta keyi na ƙafan ta da yake ɗan mata ciwo, sai ta wuce cikin motan ta zauna, shi kuma Dr nah ya buɗe mun gaban motan yana jira nah, duk i da nayi idon shi yana kai na, chan na gama abunda na keyi na taho zan shiga gaban motan inda yayi sauri ya buɗe mun daga inda ya ke zaune. Ina dab da zan shiga kawai sai naji anyi wulli da ni gefe, wanda sai da nayi ƙoƙarin gaske na daka tar da kaina daga faɗuwa, juya wan da zanyi kawai sai naga Dr Khadijah ce ta wullar dani, ita kuma tayi sauri ta shige gaban motan. Da sauri Dr Hussain ya fito daga motan ya taho inda na ke da gaggawa, hannun shi ya saka ya riƙo hannu na, hankalin shi tashe ya fara tambaya na, "Baby bakiji ciwo ba? Babu abinda ya same ki"? Ya na tambayan muryan shi da ƙarfi wanda yaja hankalin mutanen da suke wurin, kuma cikin tashin hankali ya keyi, ni kuma ganin hankalin shi ya tashi kuma duk idon mutane ya dawo kanmu, na juya na dubi Dr Khadijah, naga yadda ta buɗe baki da ido tana kallon Dr cike da mamaki, a zuciyata sai naji na raya bari na nuna mata matsayina a wurin Dr, kuka na fara nayi sauri na rungume shi ina faɗin, "Dr nah kaman hannu na data jawo zai tsinke na keji, Dr nah ciwo yake mun har bayana, ni tsoron ta nakeji Baby nah, kace ta tafi bana son ganinta", na faɗa ina ɓoye fuskana a ƙirjinsh, wai duk na nuna mishi tsoron ganin ta nakeyi. Ranshi a matuƙar ɓace ya saka hannu ya fisgota da ƙarfin gaske daga cikin motan wanda har sai da kanta ya bugu da jikin motan, wuntsilar da ita yayi da ƙarfi har saida ta faɗi ƙasa, sannan ya dawo dani gefen shi na hagu ya rungume ni ta gefe, ya ɗaga hannun shi na dama yana nuna ta da yatsa yace, "daga yau na miki tsakani da matar da zan aura, Khadijah daga yau na miki iyaka da rayuta, wallahi na rantse miki da Allah idan wani abu ya faru da ita daga rana mai kaman ta yau hukuma za ta mana iyaka ni dake, domin, Hummy bana iya haɗata da komai a rayuwata saboda ita ɗin rayuwa tace, itaɗin haskene a gare ni, duk wani abu da ya sameta marar kyau bazan taɓa yafewa kaina ba, saboda haka ki maida hankalin ki, kuma a yau zaki fuskanci waye Dr Hussain Mohd Aliyu, kuma a yau hukumar makaranta zata miki iyaka dani da iyalina, idan kuma ba a ɗauka hukuncin da yaka mata ba, toh dole na haɗaki da hukuman ƙasan ra ɗauka ƙwaƙwaran mataki akan ki, domin taɓa baby", ya saka hannu ya nuna mata ni, "kaman kin gayyato tashin masifar da tafi ƙarfin cutar cirona virus na a wurina, saboda haka ki kiyaye". A lokacin shugaban makarantar dana department ɗin suka iso wurin, ga kuma wasu securities mata da aka ƙira suka iso, gaba ɗaya idon Dr Hussain yayi wani irin ja don tsabar masifah, ga wani rawa da jikin shi ya keyi, hannu shugaban makarantar ya saka ya ɗaga Dr Khadijah wanda gaba ɗaya kunya da tsoro ya kamata, sannan ya bubbuga kafaɗan Dr Hussain a hankali yace, "Dr zamu sake jan kunne wa Dr Khadijah a kashi na biyu, wanda idan bata gyara tsarin rayuwarta ba mun maka alƙawarin Makaranta za ta ɗauki hukunci mai ƙarfi gaske akanta, saboda kowa ya maka shaidah baka da abokin faɗa, kai ka bada rayuwar ka da lokacinka ne kawai akan aikin ka, babu wanda ya taɓa jin tsakanin ka da kowa, sai Khadijah da ta ke maka shishshigi, amma kayi haƙuri ka ɗauki sister ka ku tafi hospital a duba mata hannun, don bamu so iyayen yarinya suji wani abu ya samu ƴar su ta dalilin staff ɗinmu, domin zai jawo mana matsalah mai girman gaske". Sannan ya sallami student ɗin da suke tsatstsaye a wurin da sauran staffs ɗinsu, ya kuma umurchi Dr Khadija da ta wuce office ɗin shi, sannan ya ɗubi Dr Hissain yace, "Dr kamaida su ka taho akwai zama da zamuyi da kai da Khadijah a office ɗina". Muna isowa gate ɗin gidan mu ya juya ya dubi Amaal yace, "zaku iya shiga ciki ko na shigar daku"? Da sauri Amaal tace, "zamu iya gara kaje tun da ana nemanka da sauri a school, Dr kuma don Allah kayi haƙuri kaji". Kallona yayi bai iya amsa abinda Amaal ta faɗa ba, a hankali naji yace, "Baby hannun yana ciwo? Zaki iya daurewa na dawo sai na kaiki hospital, ko kuma na ƙira Dr Abdallah yazo ya duba mun hannun ki"? Sheshsheƙa na fara yi alaman zanyi kuka, nayi sauri na kwanta akan ƙirjin shi inda na ɗauki hannu na na ɗaura a daidai saitin heart ɗinshi, inajin yadda heart ɗin ya ke bugawa da sauri- da sauri na fara kuka ina cewa, "baby ni na daina jin ciwo a hannuna, kawai inajin ciwon ta ɓata mun ranka ne, baby kaji heart ɗinka yadda yake bugawa da sauri da sauri, idan wani abu ya saman mu kai wallahi bazan yafe mata ba, ni wallahi sai na faɗawa Daddy na", na faɗa ina ƙaea sautin kuka na. Ɗago ni yayi a hankali yana duba na yace, "baby kada ki gayawa Daddy, zaiyi tunanin na gaza da baki kulawa ne, kiyi haƙuri babu abinda zai same ni insha Allahu, kawai na damu ne don bazan iya barin wani ma haluƙi yaci zarafin ki ina gani ba, kuma ina baki tabbacin baxan taɓa barin Khadijah ta sake maimaita miki ba, sai dai ta bar school ɗin nan, nidai kiyi haƙuri bari naje na dawo sai muje hospital ɗin". "kada ka damu baby na, zan shafa maganin Amaal, dama damuwa na kai ne, kaje sai kadawo my dear, Allah ya tsare mun kai", na faɗa ina buɗe motan, haka yaja ya tafi, ni kuma na dubi Amaal muka shigo cikin gidan. muna shigowa Amaal ta kalle ni tace, "munasira babu maganin da zan baki ki shafa, don nasan babu inda yake miki ciwo, sai tsabar sakalcin soyayyah da yake ɓuɓɓula duk wani gaɓa na jikin ki, toh yau hankalin ki ya kwanta , Dr Hussain ya nuna wa duniya babu kaman ki a zuciyar shi ƙorafi ya ƙare daga yau", ta faɗa tana buɗe mana gidan mu. Dariya nayi na faɗin ƙasan carpet ɗin ina ta juyi a ƙasa ina cewa, "wayyo my one and only, wayyo babyn baby, wayyo my heart, wayyo honey na, yau kasa ina maka ɓulɓulan so, babu abinda ya saura sai kadawo na riƙe ka wunin yau inyi ta shagwaɓa iya son raina, kai kuma kayita jinya", na faɗa ina ƙara kwashewa da dariya. Harara Amaal ta mun tace, "amma ke baki da imani, kibar bawan Allah nan yaji da tafiyan da zamuyi gibe mubar shi, har na tsawon 1month, kibari kuyi sallama basai kin ɗaga mishi hankali ba". Tashi nayi na zauna ina kallonta, "lallai ma Amaal, ae saina lugwaigwaita mishi zuciya, wanda idan na tafi tsanani ya daure yayi 1week bai bi baya na ba, kina ganin zan iya 1month babu shi kusa dani? Bazai taɓa yiwuwa ba, tunda Abbu suka ɗauki nauyin Hummy toh dole su haɗa dana Dr nah", na faɗa ina ƙyalƙyala dariya, ganin yadda Amaal ta bar abinda ta keyi tana kallo na. "Hmm Hummy kice yau na yi laɓe naga yadda zaki birkita mun kan Dr"? Dariya na sakeyi nace, "ki tsaya gulma dai kada kije ki birkita kan naki Dr, nidai babu ruwana idan kinga Dr na ya biyoni ke kuma na barki da zaman hira da Ummu". "Hummm ni Hummy yanzu gaba ɗaya mamaki kike bani, yadda kika iya ɗauke hankalin wannan babban mutumin, babu wani fargaba yau ya yanƙwana ƙatuwar mata kaman Dr Khadijah akanki"? _Nima Aunty Nice mamaki nakeji na yadda mutumin da bazai iya furta kalmar so ba, amma yayi mata abinda yafi ƙarfin furta kalmaɓ so ɗin ma yau a idon student da malaman su, besty ta dubeni tace "humm Aunty nice mamakin namiji kikeyi?ae ya wuce haka ma idan akan abinda yake sone, kawai yanzu ki bari mujira da wuwan shi muji yayah za ayi sallaman nan", kallonta nayi nace , "toh bari na tafi na nemo neat lady, saboda mutane suna ta neman book ɗin ta amma ni ban san ina take laɓewa ba, gara naje har gida na fito da ita taxo tayi typing dole yau_. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/10, 14:46] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 22📑* *__________📖* Babu ɓata lokaci muka shiga bedroom ɗinmu muka fara haɗa kayan mu, muna cikinyi akayi azahar, muna idar da sallah Dr ya ƙirani a waya yace, "Baby kije bakin gate akwai masinjan mu ya kawo muku abinci, don Allah kiyi haƙuri har yanzu bamu gama case ɗinnan ba", haƙuri na bashi sannan na mishi godiya. Wajen gate ɗin na fito na karɓi ledan da aka mana take-away ɗin, na shigo haraban gidan muka haɗu da Peter da David, murmushi suka fara mun, Peter kuma yana harara na da wasa, domin fuskanshi ɗauke yake da murmushi, "preety wato Dr ya ɓoye mana ke ko"? Ya faɗa yana duban ƙofan gidan Dr. Dariya David yayi yace, "ba dole ya ɓoye mata mai kyau ba, kaga laifin shi ne bros"? Nima dariya nayi ganin sun harbo jirgin mu, ina duban su nace, "baku fahimta bane Dr ba soyayyah muke yi da shi ba, yayah nane fah". Dariya sukayi suna kallon junan su, peter yace "mun yadda ba soyayyah kukeyi ba, amma yau meye ake faɗa a depertment ɗin mu? Ko ina ka tsaya guys sai labarin tashin hankalin da Dr yayi akan ki ake tayi, toh duk wannan ma ba soyayyah bane ko"? Zaro ido nayi na juya ina dariya nayi hanyan side ɗinmu, suma dariya sukeyi suna cewa na gudu don naji zasu faɗi gaskiya. Barin duk abinda mukeyi na shirin kayan mu mukayi, muka zauna muka ci abinci, da yake dama yunwa mukeji, muna gama ci muka ɗauko apple juice da mukayi tun daren jiya muka sha, kallo na Amaal tayi tace, "nikan bacci zanyi kafin la'asar" ta miƙe tayi hanyar bedroom, nima tashi nayi na bi bayan ta. Bamu muka tashi ba sai wurin 5:00pm, saboda rashin bacci da bamu samu kwana biyu ko alarm bamu ji ba, da sauri mukayi sallan, sannan Amaal ta kalle ni tace, "Hummy yau kam muhuta ɗaura abinci, kawai musha cornflakes da dare, don wallahi duk wani ciwon jiki nake ji, addu'a na ɗaya musamu mu bar ƙasan nan lafiya ciwo na bai mutsa ba", ta faɗa tana daddana ƙafan ta da kanta. Duban ta nayi nace, "Dr fah me zai ci kike nufi"? Harara na tayi tace, "sai yaje yayi abinda ya saba tun da chan baya", ta fara tana dubana da dariyan tsokana. Turo bakina nayi gaba nace, "ke kika sani bari yazo na gaya mishi, kuma babu inda zaki bimu idan yace muje shan ice cream", na faɗa ina tashi tsaye don zuwa na duba abubuwan da suke kitchen ɗin mu. Dab za'ayi sallan magrib Dr Hussain ya dawo, knocking gidan mu yayi, da sauri kaman jiranshi na keyi naje na buɗe, tsayawa yayi yana dubana da murmushi a fuskar shi, nima mayar mishi nayi, sannan na bashi hanya ya shigo ciki. Yana zama na wuce kitchen na haɗo mishi sauran cake ɗinmu da apple juice mai sanyin daɗi, gefen shi na samu na xauna ina zuba mishi juice ɗin a cup. Sai bina da kallo yake yana murmushi, a hankali nace, "Dr nah me yake saka ka farin ciki bayan gobe zan yi maka nisa"? Dariya yayi mai ɗan sauti sannan ya dube ni yace, "ina farin cikin hukuncin da akayi wa Dr Khadijah ne kawai baby, kinsan an mata doka mai tsanani akaina da ke baki ɗaya, kuma management sun tabbatar mata da cewa idan har ta sake maimaita makamancin irin haka zasu dakatar da ita, kuma tayi mugun razanan, don har aka tashi a taron bata daina sha re hawaye ba", ya faɗa yana ƙara murmushin kan fuskan shi. Ina kallon shi da mamaki, "Dr mu toh meye yake saka ta kukan"? Yama ajiye cup ɗin bayan ya shanye wanda na zuba mishi ya dube ni yace, "Ni wallahi baby har tsoron irin son da Khadijah ta keyi mun nakeji, kinsan bayan ance ta bani haƙuri, saida ta ban tausayi, domin a hankali babu maiji tace, zan bar ƙasan nan tabbas sabida kai Dr, domin zuciyata bazata ɗauki ganinka da wata ba bayan ni", Ya faɗa yana dariya. Wani iri naji cikin zuciyata, domin ko babu komai macece ƴar uwata, kawar da maganan nayi ina duban shi nace, "Baby nah yau kaman mun gajji, ko zakayi take-away ne da dinner kaci? Muma cornflakes kawai zamu iya sha duk muna jin gajjiya yau a tare da mu", na faɗa ina duban shi da alaman damuwa a fuskana. Shima turo baki yayi yana kwaikwayo na yana buga ƙafa a ƙasa yace, "nikan bazan yadda ba, yau abincin Baby zanci, ni wallahi bazan yadda da wayon nan ba", dariya muka farayi ni dashi a tare, ina kallon shi nace, "haba baby ni da yakamata nayi shagwaɓa sai kaine yau zakayi, toh ni yayah zakayi dani idan kai kanayi"? "Kawai sai a raba kowa da turn ɗin yin sakalcin shi, idan nayi na 2dys sai kema kiyi na 2dys, kowa yayi ta fama da ɗan uwan shi ko ba haka ba"? Dariya nayi na miƙe ina cewa, "bari naje kitchen ɗin na duba me zan dafa maka". Da sauri ya kamo hannu na bayan shima ya tashi ya tsaya, dab da bayana yazo ya tsaya kaman wanda zai jinginu da ni a hankali yace, "Baby nah bana son ki wahala, kawai ki gayawa Amaal idan anyi ishaa zamu fita muci abinci ko, bana son ƴar baby nah ta wahala", ya faɗa yana ɗaura haɓan shi a kafaɗa na, da sauri naja jikina na shige bedroom ɗinmu da gudu, dariya ya fara yi yana girgiza kanshi, ya juya ya fita a gidan, sai da na tabbatar ya bar parlon tukun na fito na rufe ƙofan na ƙoma bedroom wurin Amaal. Zama nayi ina ajiyar zuciyar mai ƙarfi, juyowa tayi tana hararah na tace, "zakuji da shi dai magulmata". Murguɗa mata baki nayi ina jujjuya mata ido nace, "ki shiryah anjima zamu fita dinner da Baby nerh"! Hararana tayi tace, "sai ki fita da Babyn ki, nima Hubby nah zai zo mufita yawon sallama kafin ya iso ni a *DAMMAM*". Zaro ido nayi ina dubanta, "laillai yarinyar nan wuyanki yayi kauri, toh babu inda zaki tafi da shi ke kaɗai, Ummi idan ta samu labari ranta zai ɓaci, saidai yaxo mu fita tare dukkan mu, ina gadinki kina gadina", na faɗa ina rawan india a gabanta. Gaba ɗaya daga ni har Amaal ƙamshin daɗi mukeyi, gashi munyi shigan wasu english wears masu masifar kyau, munyi rolling kanmu da wani gyale mai kyaun gaske, nawa colour red and green, na Amaal kuma red and black, haka muka fito muka shiga bayan motan Dr Hussain, inda shi kuma da Dr Abdallah suna gaba. ranan munyi yawo kam bayan mun ci abinci, har wurin 11:00pm tukun muka je muka sauƙe Dr Abdallah, sannan muka dawo namu gidan, Amaal sallama tayiwa Dr nah ta wuce ciki, mukuma muka zauna a parlon, ƙura mun ido Dr yayi, ni kuma ganin kallon bana ƙare bane sai na matsa nesa da shi ina ta kame-kamen abinda zance, don gaskiya ni bana son irin kallon da yake mun. "Baby yanzu gobe kenan zaku gudu ku bar ni ko"? A hankali na dube shi ganin yadda yayi mun maganan kaman bazai buɗe bakin shi ba, juyar da kaina nayi na bar duban shi, nima murya cikin nutsuwa nace, "Baby ko na zauna ne nayi hutun anan tare da kai"? "Ban isa ba baby, ki tafi kawai nima xan fi so naga kin samu masu ɗebe miki kewa", haka mukayi ta hira, da ƙyar muka rabu wurin 12:30pm, bayan ya tafi na shigo ɗaki, baki a buɗe nake kallon Amaal da mamaki, ta wani bararaje akan gado sai wani luv ta ke kwasa a waya ita da Dr Abdallah, ganin haka na wuce toilet nayi wanka nazo na kwanta ina ta ja mata tsakin sun dame ni. Saida mukayi wanka muka saka kayan mu tukun aka ƙira sallan asuba, jirgin mu 9:00am zai tashi gashi airpot ɗin da nisa shiyasa muka tsayar 6:00 zamu fita domin tafiya, tunda muka shiryah nake ji kaman nayi kuka saboda tafiyan da zanyi na bar Dr nah shi kaɗai, a haka jiki a sanyaye muka shiryah. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/13, 18:31] Miss Xerks🌺: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* ```13/07/2020.``` *ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!!!.* *a yau GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION na cika shekara ɗaya da kafuwa.* *muna roƙon ubangiji Allah ya ƙara ɗaukaka wannan ƙungiya mai tarin albarka tare da mutanen cikin ta, Allah ka ci gaba da basu nasara da sa'a, Ya ƙara wanzar da zaman lafiya, fitina da sharrin masu sharri da idon maƙiya Allah duk ka kauda akan wannan ƙungiya da jama'ar cikin ta. Allah muna roƙon ka kaci gaba da bawa wannan ƙungiya da jama'ar cikin ta ikon faɗakar da Al'ummah ta hanyar GASKIYA hanyar da ta ke dai-dai bata kaucewa ba. Allah kar ka nufi wannan ƙungiya da fitar da abinda zai zama yaɗa fasadi ne zuwa ga Al'ummar Annabi Muhammad {S.W.A}, Allah ka bawa wannan ƙungiya ikon tsarkake alƙaluman ta ba tare da ta rubuta shirme ba, sai dai abinda Al'ummah zasu karanta su amfana da shi.* *AMEEN YA HAYYU YA QAYYUM.* Jinjina zuwa ga shugabar wannan ƙungiya *UMMU NABIL.* Allah yaci gaba da taimakon ki da ke da members na ki. _Shafin Sadaukarwa ne ga Gaskiya Writer's domin murnar cika shekara guda._ *SHAFI NA 23📑* *__________📖* Duk wanda ya dubi fuskan Dr Hussain sai ya ji tausayin shi sosai a ranshi, kuma sai kayi mamakin wani irin so yake yiwa Hummy, domin Dr Abdallah kaɗai yake ta fice-ficen tafiyan su, amma sam Dr Hussain ya kasa yin komai, yana zaune gefe na ya kama hannu na kaman wani zai ƙwace mishi ni, muna nan haka Dr Abdallah ya dawo ya zauna gefen Amaal, yana duban Dr nah yace, " Dr saura 15mnt jirgin su ya tashi, gashi an fara neman passinger su shiga jirgi, ina ga ya kamata mu barsu haka su wuce ko?". Da sauri na ɗago kaina don jin irin ƙanƙame mun hannu na da Dr Hussain ya yi, shima ƙura mun ido ya yi kaman zai furta abu amma ya kasa, sai lips ɗin shi kaɗai na gani suna ta motsawa, matsowa na yi kusa da shi na kwantar da kaina a kafaɗan shi, lokaci ɗaya na ji hawaye yana bin fuska na, murya ƙasa-ƙasa nace, "Dr nah zamu tafi, don Allah ka kula mun da kan ka". ina gama faɗa mishi na miƙe tsaye, wanda shi ma haka ya saka ya miƙe amma hannun shi yana riƙe da nawa hannun, murya ƙasa-ƙasa shima ya furya. "Baby bana son ki tafi ki bar ni, kin amince na sanar da Daddy'n ki relationship ɗin mu". Damƙe hannun shi na yi da ƙarfi cikin nawa, "Dr bayan zu ba, kabari mugama wannan session ɗin tukun ya sani, kayi haƙuri Baby nah, ni dai ka kula mun da kan ka". "Baby ki kula mun da kan ki, kiyi hankali da larabawan nan, don Allah ko brother Amaal bana son ki bashi fuska kin ji baby nah". haka muna ji muna gani muka tafi muka bar su Dr da sai ɗaga mana hannu suke yi. *DAMMAM.* Abbu da Ummi ne suka zo taryan mu, haka muka shiga motan su in da driver ya ke jan mu har gida, a hanya Amaal kaman zata

Chapter 12 of 28