tausayi take bani na rasa wani irin so ta keyiwa Hussain ne?.
Cikinta yana cika 9month gaba ɗaya tayi wani irin kumburi, a wannan lokacin kuma Aunty hauwa suka zo da mijinta da ƴarta fatima, a wannan zuwan a Narabi suka sauƙa, bata daɗe ba tazo har jos don ta duba Aisha, ranan duk da ina namiji kuma mijinta da yakamata naji kishin Hussain a raina, amma kuka nayi kaman mace, saboda tausayin da uwar da ƴar suka saka ni, na sako ƙafa zan shiga parlourn Aisha domin mugaisa da Aunty Hauwa kawai sai naji muryan kukan su inda naji Aunty hauwa tana ce mata.
"Aisha wallahi ina sonki fiye da komai a rayuwata, don kece abin farin cikina ina dubeki, tou amma girma da darajan Ummi yafi ƙarfin naƙi bata ke, kuma alƙawari nayi bazan taɓa nuna mata cewa nina haife kiba, amma bawai ina ƙinki ba, kuma rashin jina da kikayi game da abinda ya faru wallahi Aisha nafi kowa shiga damuwan abinda ya sameki, domin burina da addu'a na kullum naga na haɗa zuri'a da Adda na, kuma babu wanda ya kwanta mun irin Hussain a raina, wallahi nayi kuka ne saboda inaji ina gani za'a haramta aure tsakanin ki da Hussain, wanda shine burin mahaifinki, amma kiyi haƙuri Aisha wallahi ina sonki sosai sama da komai a rayuwata".
Itama Aishan kukan takeyi tana gayawa uwarta irin son da takeyi mata, amma kuma ta tayata addu'a ta daina son Hussain ta so ni a zuciyarta, faɗin haka yasa dukkansu suka fashe da kuka.
"Mamie nah wallahi ina so na cire yayah Hussain a zuciyata, domin na faranta wa Baban Ahmad, yayi haƙuri dani sosai amma nakasa, kimun addu'a", ta faɗa tana ƙara rungume uwar.
"Aisha babban damuwa na a duniya guda ɗaya ne yanzu ya saura mun, naga Hussain ya dawo cikin mi ya zauna, sannan kuma naga aure ya haɗa shi da zuri'a ta, shiyasa nake addu'ar naga na haɗa shi da Fatima idan ya amince", cewar Aunty hauwa .
Raba jikin su Aisha tayi ta turo baki gaba tace, "naƙi wayon ni zan haifawa Yayah Hussain mata, don ni ya chanchanci na zaɓa mishi mata, Mamie ni zan haifa mishi mata, da ina son na haifi ɗa namiji don na saka sunan yayah Hussain, amma yanzu mace nake so, na saka mata Aisha juniour don na bashi ya aura, kuma na saka shi yayi ta mata son da bai mun ba", ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi.
Ranan naga soyayyah tsakanin uwa da ƴarta, haka dai na koma ban shigo ba awanann lokacin, sai kusan magrib na dawo muka gaisa.
Bayan kwana biyu da zuwan Aunty hauwa Aisha ta tashi da naƙuda mai zafin gaske, wanda tun safen mukayi aisibiti da ita ana ganin haihuwar kaman yanzu amma abu shiru har azahar, dole ta saka na gayawa Umminta da Aunty hauwa, ganin yadda take ta neman su, da yake Ummin suna tare da Aunty hauwa a bauchi, ae kafin la'asar har sun iso Jos, kai hattah Baban Narabi sai da yazo, ranan naga dangi da irin soyayyar da suke nunawa Aisha, don Uncle Abdallah har labour room ya shiga, amma ganin yadda Aisha ta kumbura da kuka ya fito yana a nemo mishi likita ya cirewa ƴar shi cikin, gaba ɗaya hankalin su ya tashi ganin yadda Uncle Abdallah yake zubar da hawaye.
Ana ƙiran Dr yace babu komai mujira zuwa 1hr idan bata haihu ba sai ayi mata CS ɗin, amma ya kwantar mana da hankali akan cewa haihuwar fari ne ya jawo haka, bayan sallan ishaa, Aisha ta saka aka ƙirani nazo, hannu ta miƙo mun ta riƙe ni gam-gam.
"Baban Ahmad ka yafe mun duk abinda na maka, wanda na sani da wanda ban saniba," hawaye yana bin gefen idonta, kasa magana nayi sai jujjuya mata kaina da nakeyi, Aunty hauwa ce da Ummi da suke zaune a ɗakin suka fara mata magana ta ɗaina irin wannan maganan insha Allahu zata haihu lafiya, haka kowa ma yasha wahalan, murmushi tayi idonta da hawaye ta dube ni.
"Ka nemo mun Yayah Hussain ɗina kabashi abinda zan haifa kace ya riƙe mun amana, na bashi duniya da lahira, idan ba shiba bana so ka bawa kowa riƙon babyn, kai da kanka nake so ka riƙe bawai don nafi sonka a kan iyaye na ba, kawai ina son duk abinda zan haifa ya tashi a gaban mu, hannun iyayen shi, saboda duk abinda zai faru da shi ba za ace sunyi sakaci ba, kasan me yasa"?,
Ta tambayeni, wanda da sauri na jijjiga mata kaina da idona da yake tsiyayan hawaye, alaman ban sani ba.
Murmushi ta sakeyi tace, "Ummi na ta min riƙon da ko Aunty hauwa bazata iya mun ba, ta bani tarbiya da kulan da ko iyayena ba lallai bane su bani, amma abin baƙin ciki lokacin aure na da kai sai naji ɗaya daga dangin Baba na tana cewa, abin tausayi saboda riƙon muguntar da akayi mun da sakaci saboda ni ba ƴar Ummi ba, shiyasa ta bari ɗanta yayi raping ɗina don mugunta, gashi yanzu yarinya ƙarama marainiyar Allah zata ƙare da auren tsohu, ni kuma jin haka ya sa nayi alƙawarin ko bana sonka, zan zauna da kai na maka biyayyah don Ummi na tayi alfahari dani, saboda haka duk abinda zan haifa kai nake so ka riƙe bashi ko kabata irin naka tarbiyan da kulawan, har sai ka samu Yayah na ka danƙa mishi riƙon, don nayi imani da Allah ko mace ne, zai kula da ita bazai iya cutar da ita ba, koda shi kaɗai ne tare da ita ba zai cutar da ita ba", ta ƙarasa tana sauƙe ajiyar zuciya.
Kukan su Ummi ne ya ƙaru, ita kuma Aisha ta cigaba da faɗin, "Ummi ki yafe mun, mamie na ki yafe mun, kucewa Yayah Hassan ɗina na yafe mishi duniya da lahira, kuyi haƙuri bawai na hanaku riƙon abinda zan haifa bane, don nasan duk duniya babu wanda zai kai Ummina son riƙewa, amma bana son ƙara ja mata baƙin jini, kawai na amince ke ko mamie na ku riƙe babyn har zuwa 2yrs, sai ku maida riƙon hannun mahaifinta ko mahaifin shi, ku gayawa Yayah Hussain nayi burin sake ganin shi a rayuwata, amma insha Allahu abinda zan haifah zai nemo shi", ta faɗa tana runtse idonta da ƙarfi.
Likita ne ya shigo yace mu fita za a shiryata suyi mata CS, domin ga chan Babanta a waje sai faɗa yakeyi, jin haka ya saka na ɗan rankwafa na sumbaci goshinta na mata fatan alkhairi, Ummi da Aunty hauwa ma da ƙyar aka fitar dasu a ɗakin, inda nake jin muryan Ummi tana cewa, " Aisha insha Allah ke da hannun ki zaki raini abinda zaki haifa, kuma insha Allahu tare da abinda zaki haifa zaku nemo yayanki", ta faɗa tana ta kuka.
Fitowar nurse ne ya saka mu saurin zuwa inda ta ke, amma bata ce mana komai ba ta wuce da sauri ta ɗauko abu ta koma, chan bayan wasu mintuna sai gata ta fito da yarinya fara sosai a hannunta cikin farin kayan sanyi, da sauri Ummi ta ƙarasa jiki na rawa ta miƙa hannu tana faɗin, "Alhamdulillahi me muka samu? Yayah jikin ƴarmu kuma"?
"Baby girl" nurse ɗin ta amsa mata batare da wani rawan jiki ba, murmushi nayi kaɗan dana dubi fuskar ƴar bayan Uncle Abdallah ya ɗago mun yana murmushi yace, "kaga mun ɓarauniya, wato ta sato mun kaman nin ƴata kaf ko"? Ya faɗa yana juyo mun da fuskar ƴar dana kasa miƙa hannu na karɓa, Ummi ce da take ɗan murmushin yaƙe tace, "tace kaidai ka gode Allah da kuka samu wannan baturiyar ƴar ta ɗauko kamanin mu sak ita ma bata ɗauko naku ba", murmushi yayi yana duban Aunty hauwa yace, "Hauwa kishi ne haka da gaggawa? Don kinga wacce ta fiki fari da manyan ido"? Ita dai Aunty hauwa yadda nakasa maida hankali kan ƴar ita ma haka tayi, dole aka miƙawa Baban Narabi da Mama kaltun take zaune a gefen shi.
Yana karɓa kuma dr ya fito tare da abokan aikin shi, Hannu Uncle Abdallah ya miƙa mishi yana "sannun ku da aiki Dr, gara ae da akayi aikin, ae kunga uwa da ƴar duk sun huta", ɗaga kai Dr yayi yace, "Tabbas kuwa duk sun huta, domin ita ma Jaririyar ta huta da neman hanyar da zata fito, itama uwar ta huta da rayuwar da muke ciki mai cike da ƙalubale," shiru ya ɗanyi..... chan kuma sai yace, " ina mai bawa ahalin Aisha haƙuri da wannan babban rashi da akayi na wannan baiwar Allahn Aisha, domin a yau Aisha ta amsa ƙiran mahaliccinta, wanda dukkanmu munyi imani da Allah shi muke jira, saboda haka kuyi hakuri, wanda yafi mu sonta ya karɓi abinshi, amma gashi ya bamu madadinta".
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
[9/12, 12:06] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 49📑*
*__________📖* ƙuuuu naji wani ƙaran da sai da yaso firgita ni, a razane kowa ya ɗago kanshi ya dubi uncle Abdallah da ya wanke Dr da mari, jikin shi na rawa ya chakomo wuyan rigan Dr yace, "kana hauka ne zaka ce Aisha ƴata ta rasu? Dubi iyaye da kakanunta da har yayunta duk a tsaye babu wanda ya mutu sai ƴata kake nufi? tou bazan yadda ba, komawa zakayi cikin ɗakin ka ɗauko ta mu chanja mata asibiti, ita kaɗai fah yaya Umar ya haifah, wa kake so na gani a madadin ɗan'uwa na"? kuka kuma ya fashe da shi bayan ya gama surutun shi wa Dr, hannu Baban Narabi ya miƙa ya riƙo Uncle Abdallah, sannan ya fara bawa Dr haƙuri, amma Dr bai wani ɗaga hankalin shi ba, yace wa Baban, "Baba ae haka zafin bugun mutuwa yake, mun saba ganin sama da haka ma, mudai addu'an mu Allah ya jiƙan ta da rahama, Allah ya raya abinda ta haifa".
Sai lokacin idona ya kuma wurin su Ummi, amma wayam naga babu kowan su daga ita har Aunty hauwa, sai a lokacin naji muryan nurses ɗin suna basu haƙuri akan su ɗaga Aisha su bari a shiryata, nidai yadda kasan gunki haka nake bin kowa da kallo, sai wani bugawa da zuciyana yake yi kaman zai fito, a lokacin na daure naja ƙafana zuwa ɗakin da Aisha ta ke ciki, abunda na iya tunawa ɗaya ne, ina shiga naga gawan Aisha kwance akan gadon, gefe ɗaya wurin kanta kuma Aunty Hauwa ce ta kife tanata kuka a jikin Aishan, Ummi kuma ta riƙe ƙafan Aishan tana kuka tana magana, wanda gaba ɗaya bana fahimtan me suke cewa, ban ƙarasa sanin me ake ciki ba, sai zuwa wani lokaci naji muryan Baban Tilde yana cewa.
"Alhamdulillah! Muhammadun ma ya farfaɗo, a dakata yaje yayi mata addu'a", haka naji muryan Baban Tilde akaina.
Jin haka ya saka ni da sauri na miƙe zaune, da ƙarfi na furta, "Baba da gaske ne Aishan nawa ta rasu? Ko dai na razana da wuyan haihuwar da take shane nayi mafarkin ta rasu? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ina Aishan ne take Baba"? na faɗa ina miƙewa tsaye.
Mutumin da ake ƙiran shi Abban Aisha shine ya saka hannu yana share hawaye ya riƙe ni, a taushashe yace, "kayi haƙuri mohd, Aisha ta amsa ƙiran wanda yafi mu sonta, kayi haƙuri kaje kamata addu'a yanzu za'a sallaceta", yana gama faɗin haka na juya na fita a parlourn, har inda ake shiryata na shiga, sunkuyawa nayi kan gawanta da nufin yi mata addu'a, amma sai zuciyata tayi rauni, kuka na saka ina riƙe da ita, da ƙyar na daure na mata addu'a, ina riƙe da ita naji maganan Aunty hauwa tana kuka, "shikenan Aisha bazamu rayu da ke irin na uwa da ƴarta bake nan har abada, da gaske mutuwa kikayi Aisha?" miƙewa nayi na bar wurin saboda wasu surutai da Aunty hauwa take tayin su babu tsayawa.
Kwanan Aisha bakwai da rasuwa kowa ya watse, a ranan kuma akayi sunan yarinyar da ta haifa, wanda taci sunan Aishan, amma mukayi mata laƙabi da Humairah!", dakatawa Daddy yayi da bamu tarihin shi ya ɗago da fuskana da nake ta kuka tunjin lokacin da Daddy na ya fara kuka, ƙura mun ido yayi yana ɗan murmushi yace.
"Sweet heart! kece yarinyar da Aisha ta haifa mun, kece farin cikina sama da komai a duniyata, kece farin cikin zama dake ya maye gurɓin baƙin cikin da na shiga a rayuwar baya", sannan ya juya ya nuna mun Dr Hussain yace, "wannan shine ɗan'uwan mamanki da take burin zaki nemo mata shi, gashi kuma kin nemo shin, wanda soyayyah ya shiga tsakanin ki da shi har ta kai ku da tunanin aure, ni dai zan cigaba da baku labarin yadda na reniki, daga baya zamuyi tambayan shin akwai aure tsakaninki da ɗan'uwan mahaifiyar ki? Kuma wanda yayi soyayyah da ita"?
Da sauri na juya na dubi Dr mu, duk sai najini a tsorace kada ace babu aure tsakanin mu da baby, amma sai kawai naga ya kashe mun ido ya mun alaman kada na razana, a hankali kuma naga saitin bakin shi yayi alamar furta mun, "I luv u babyn baby"! Murmushi nayi na maida kaina inda Daddy ya cigaba da bayanin shi.
Washe garin sunan Hummy su Ummi sukayi shirin tafiya da ita, amma da ƙyar na daure suka ɗauke ta, bayan na ɗaura ta akan cinya na ina duban tsantsan kaman da sukayi da Aisha, wanda har tsoro yake ban, nayi mata addu'a ina kuka kaman zan shiɗe, a haka Babana ya saka hannu ya ɗauke ta ya miƙawa Ummi da ita ma kukan take tayi.
Amma abin mamaki lokacin da suka isa bauchi sai Ummi ta ɗauki Humaira ta ɗaura akan cinyar Aunty hauwa, tana dubanta tace, "hauwa bazan tauye ki a karo na biyu ba, ki riƙe ƴar Aisha ko zaki ɗan samu sauƙi a zuciyarki kada abin ya haɗu ya miki yawa, ni kuma zanji da jinyar da yake damuna, don tabbas rashin Aisha wani giɓi ne na lafiya a jikina, inaga banida ƙarfi da kuzari a zuciyata na iya wani abu mai muhimmanci, don idan naji kukar ƴar nan, zai iya tarwatsa mun zuciya na", ta ƙarasa maganan tana share hawayenta.
Ita kuma Aunty hauwa bata ƙi ba, haka suka ƙira ni ita da Uncle Abdallah suka gaya mun zasu tafi da Humairah, ban ƙi ba don nima ina maijin tausayin Aunty hauwa ba kaɗan ba, daba don Aisha tace tafi son riƙon Humaira a hannu na ba da babu abinda zai hanani barwa Aunty hauwa, haka naje na musu sallama, na ɗauki makuɗan kuɗaɗe na bawa Aunty hauwa domin sayen madara dasu pampers ko wani abu da zai taso a sayawa Humaira, amma ranan naga kalan masifar Aunty Hauwa da Aisha ke bani labari.
Dariya Daddy yayi yana duban Dr Hussain da shima dariyan yakeyi, ni kuma na zunɓuro baki ina kallon Daddy, don babu shakkah nasan halin irin masifar Kaka, don idan tazo dubani kullum sai tayi masifar wai su yayah Ahmad basu da mutunci, har sai Goggo mai raino na tayita bata haƙuri takeyin shiru, wani lokacin ceea zatayi ɗakin su zataje ta tsitstsigale su, nidai dariyanta zan tayi har ta huce, nima dariyan nayi ina duban Daddy da yake tayi kaman ba yanzu ya gama kuka ba.
"Aunty hauwa ranan ta balbaleni inda take cewa mai na mayar da ita, ƴar Aishan ne zance zan biya ta ciyar da ita?" daga nan kuma sai ta fashe da kuka tana cewa, "me nayiwa Aisha a rayuwar duniya wanda uwa ta keyiwa ƴarta bayan shayarwa? Duk fa Ummi nane rayi mun hidiman da uwa ta keyiwa ƴarta, gashi Aisha ta bar duniyan ban nuna mata irin nawa soyayyah ba don ina jin kunyar Ummi na, don Allah kabarni na nunawa Humaira irin soyayyar da uwa ta keyiwa ɗiyarta", dole na mayar da kuɗina bayan na zauna na tayata kukan, ina ji ina gani aka tafi mun da sweet heart ɗina.
Da ƙyar na daure sukayi 5month da tafiya nabi bayan su, haka naje na musu 2weeks, naji daɗin ganin irin kulawan da Aunty hauwa da ƴaƴanta suke bawa Hummy nah, kai hattah abokiyar zamanta Fadilah da ɗanta ba ƙaramun so sukeyiwa Hummy ba, haka na dawo cike da kewar ƴata.
Babu wuya a wurin Allah, hummy tana shirin cika 1yr Aunty hauwa ta gaya mun, ae babu ɓata lokaci nayi shirin tafiya tare da mahaifiyata wanda ta matsa da son zuwa ganin jikarta, ranan da muka isa naji farin cikin da bazan taɓa mantawa ba, domin Sweet heart na samu babu inda bata zuwa da ƙafarta, gashi ko ɗaya bata mun ƙiyuwa, cikin jin daɗi akayi partyn cika shekaranta ɗaya, inda mukayi ta ɗaukan pics da ita, kuma abin sha'awa duk inda na saka ƙafa na yarinyar nan sai ta bini, gashi bakinta ta iya furta, Papa, kaka, Dada, mama, wato uncle Abdallah ne papa, yadda su fatima suke ƙiranshi, Aunty hauwa kaka, ita da Aunty fadila, fatima kuma mama, don firr fati tace itace uwarta, ni kuma abin daɗi wai Dada, tana nufin Daddy, naji daɗin da nakasa ɓoyewa a gaban kowa.
Abin haushi da iyalaina suka mun shine ina dawowa nigeria, jikina yana rawa na kai musu pics ɗin Humaira su ganta, amma buɗan bakin maman su Ahmad sai cewa tayi, "kana tunanin cewa ƴaƴana suna da wata chan ƴar ubane? ae sam kada ka fara gigin haɗa su da ƴar matar ka, don kuwa inada labarin bawai ƴar ka bace ƴar matar kane wanda tazo da cikinta gidan nan, domin babu abinda ya haɗa yarana da ƴar ta, babu abinda zai saka mu kalli photon ta chan ta matse muku", tana gama maganan ta bar mun wurin da nake zaune, yaranta kuma suka bi bayanta, ranan nayi kuka kaman raina zai fita, amma haka na bawa kaina haƙuri na shige ɗakina, zuciyana cike yake da tausayin Humaira.
Kasa zama nayi a ɗakuna na wuce chan ɗakin Aisha, inda na fara bin ɗakin da kallo, chan kan dressing mirrow ɗinta na ɗauko wani paper na buɗe, kawai sai ganin saƙon da ta bar nagani.
"Baban Ahmad don Allah nabaka amanan abinda zan haifa, idan namijine kasaka sunan Yayah Hussain, idan mace ce ka saka mata sunana don tunawa dani, kuma bana son kabada riƙon ta wa kowa idan ba a hannunka ba, bana so taje ko'ina da sunan hutu don gudun abinda ya faru dani kada ya faru da ita, Kagayawa Ummi da Aunty hauwa duk mai son ganinta yazo har inda take ya ganta amma ban amince ka kaita inda suke ba, zumuncin yanzu shaiɗan ya shiga, ina tsoron wani yayi mata illar da nawa ɗan'uwan da nake ganin ciki ɗaya muka fito ya mun, bana so kabari rayi sabo da kowani cousin ɗita, ban yadda da kowa ba banda yayah Hussain ɗina, sannan kada kabar matar ka da yaranta su wulaƙanta mun ƴata ko ɗana, don kullum sai ta furta mun na kawo musu cikin shege gidan su, kona rana ɗaya bana son ta zauna a hannunta, kasama mata mai kula da ita mai hankali dattijuwa, nagode Allah ya musu albarka".
A hankali Daddy ya maido da kallon shi kaina yace, "sweet heart kinji tushen da ban barki kin shaƙu da kowa ba, don bin umurni da kuma shawarar mamanki, nima sai naji ina gudun kije wani wurin don kada ki wulaƙanta, kuma ko a gidana ɗana lura basu sonki sqi ban barki da suba, kiyi haƙuri kinji", ya faɗa yana shafah kaina, nima murmushi nayi bayan na mike zaune ina share hawayen ido na nace.
"Daddy! amma mummy na da ta rayu dani baƙa ramin so da kulawa zata nuna mun ba, gashi Allah ya amshi addu'anta na nemo mata yayah Hussain ɗinta, kuma shi kona rana ɗaya bai taɓa nufina da niyyan cutarwa ba, kullum ma ƙara nuna mun hatsarin zuwa inda maza suke yakeyi, ashe zuciyar Drn mu mai kyau ne tun asali", na faɗa ina duban Dr da murmushi cike da fuskana.
*©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻
*°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*
*1442H/2020M.*
*AL-MUHARRAM/SEPT.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
```🎐G•W•A🎐```
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼
*NA MARUBUCIYA:-*
*AUNTY NICE✍🏼*
*@wattpad AuntyNice.*
*SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-*
*NABEELAH ARABI*
*NUHU ARABI*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*
*SHAFI NA 50🔚📑*
*__________📖* Shekaran Humairah biyu a hannun Aunty hauwa naje na taho da ita, ranan da zamu dawo na tausayawa Aunty hauwa da uncle Abdallah, domin kaman yara ƙanana, zama sukayi suna kuka kaman ance musu mutuwa tayi, haka na baraso cike da jin tausayin su, Fatima kuma ranan barin gidan tayi har saida na bar gidan tukun ta dawo.
Kafin na ɗauko Humairah dama akwai wata goghon mu wanda Allah bai taɓa bata haihuwa ba, ƙanwar mahaifin muce, kuma ita kaɗai mahaifiyarta ta haifa agidan su Baban mu, mijinta ya rasu, tou ita Baban mu yayiwa magana ta taho domin kula da Humairah, tadawo gidan da kwanaki kaɗan na taho ɗaukan Humairah, muna dawowa na danƙa mata amanan kula da Humaira, amma bawai na sakar mata komai na Humaira gaba ɗaya ba.
Idan har na dawo gidan tou zamanta dawowa yake yi inda nake, domin side ɗina sai da nayi mata ɗakin wasanta, babu abinda ban zuba mata ba a ɗakin, duk lokacin da take wurina tou biyeta nake yi muyita wasan tare, wanda hakan baya yiwa matar gidan daɗi, ganin haka ya saka ta rage shigowa side ɗina sai dai idan kwanciya zatayi.
Allah ya jarabce ni da son Humairah sama da komai a rayuwata, sannan duk inda zanje hankalina da tunanina yana gareta, shiyasa duk wani tafiya da zan daɗe na daina shi.
Humairah na da shekara tara, Allah ya karɓi ran dattijon kirki, wato Baban Narabi",......... Da sauri Dr Hussain ya ɗaga kai ya dubi Daddy a razane yace, "Baban Narabi ya rasu"?.
"Baban Narabi ya rasu Dr, mun shiga tashin hankali na rasuwar wannan dattijon, wanda bamu wani daɗe da shiga cikin jimamin rasuwar shi ba, Allah ya sake aiko mana na Baban Tilde, tsakanin su wata uku daidai, don ko takaba mama kaltum bata fita ba Baban mu ya rasu", tsayawa yayi da labarin, saboda ta'aziyan da Abbu da Dr suka fara yi mishi, kuma da alama Dr yaji rasuwar Baban Narabi ba kaɗan ba.
"Humaira nada shekara 10 chif-chif akayi auren Fatima da Dr Hassan", ...... Da sauri Dr Hussain ya ɗago yace, "Hassan yayi aure da Fatima"?
Murmushi Daddy yayi yace, "yanzu auren su shekara shida kenan, don yanzu haka yaran su biyu, Babban cikin ne, Aliyu haidar, inda akace sunan ka yaci, amma suna ƙiranshi da Haidar, ta biyun kuma sunan Ummi taci, amma suna ƙiranta da Nabeeha, yanzu haka suna zaune a garin Abuja, inda Hassan yake aiki achan, kuma yana da chamber shi na kanshi a chan.
Aunty hauwa duk lokacin da tazo nigeria sai tazo tayi kwanaki a wurin Humaira, amma yanzu rabonta da humairah kusan 2yrs kenan, tun zuwanta sunan ƴar su Hassan Nabeeha bata zo ba sai last month, Fatima ma idan tazo tana zuwa ta duba Humaira haka ma Ummin ku, nidai sau kusan biyu nakan ɗauki Humaira muje har misau da bauchi gidan Ummi nakai musu Humaira mu wuni mu dawo, don tana ƙarama sosai ma nakan kaita mu wuni a bauchi mudawo.
Kunji tarihi na da Humairah kenan a taƙaice.
Shikuma Dr a zuciyar shi yana cewa, "lallai Aisha ba so na mata ba, duba da yadda zuciyata gaba ɗaya ya nace akan humaira, gaba ɗaya inajin ban taɓa son wani abu sama da ita ba, idan na rasa yarinyar nan ban san yayah zanyi na dawo dai-dai ba", ya gama magana da zuciyar shi yana kan binta da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 28